Makauniyar Kaddara 25

 


Page 25*


............“Kajimin ja'iri, basai ka tsaya ka kamata ba kuma? Kinga Inno na tashi muje ni na rakaki”.

        Zinneerah da tonon sililin Granny yasata fahimtar shine zai kaita asibitin tace, “Granny dan ALLAH muje da wani cikinsu aunty Abidah ko su Meenal basai shiba”

       “Keda kike a wannan halin sai kin zaɓi mai tafiya. Kinga maza miƙe karma ya tafi dan shi ba saiti ne da shi ba wani lokacin”.

      Dole ta miƙe Granny ta kamata badan taso ba. Tsaye suka samesu su duka a jikin mota, shi yana waya Farah na tsaye jingine tana danna tata wayar. Batare da hajiya iya ta damu da ganinsu su biyunba ta buɗe gaban motar ta saka Zinneerah shiga. Sai lokacin suka lura da zuwanta. Farah tabi Hajiya iya dake duban inda Yah Adnan ɗin yake da kallo. “Moddibo kuje dan ALLAH, kasan shi mai ciwo ƙosawa ne da shi”.

       Kansa ya jinjina mata kawai batare daya bar wayarba ya buɗe murfin zai shiga Farah da haushi ya kume tace, “Granny ai sai dai ta dawo baya dan tare zamuje”.

      “Asibitin? A'a idan kin bisu ni motsinwa zanji kuma tunda su Jamal basa nan. Kinga muje ciki muyi hira mai sunan ƴan gayu”. Ta ƙare naganar dajan hannun Farah batare data jira abinda tai niyyar faɗaba.

      Ta cikin mirror Yah Adnan ke kallonsu. Ya danne murmushin dake neman suɓuce masa a fuska saboda rigimar Granny. Daga haka yay horn yana harba motar zuwa gate.


         Tunda suka hau hanya baiyi ko tari ba duk da yana jin shashshekar kukan Zinneerah daka ƙudundune kanta cikin ƙafafunta data naɗe sama gaba ɗayanta ta dunƙule a kujera. Sai dai duk kiran wayarsa da akeyi tunda ya gama ta farko bai sake ɗagawaba har suka iso Shira hospital. 

     Duk da darene ko ina cikin haske yake kamar ka yarda allura kaga abunka. Sai da ya gama dai-daita fakin yaɗan dubeta ya ɗauke kansa. Wayoyinsa biyu ya ɗauka batare daya mata magana ba ya buɗe ɓangarensa ya fito. Sai da ya rufo murfin ta fahimci ya fita dan haka ta ɗago cike da ƙarfin hali fuska shaɓe-shaɓe da hawaye.

    Tana ɗaura hannunta akan handle ɗin ƙofar da niyyar buɗewa ta fita tunda tasan bacewa zai ta fito ɗinba sai taji ƙofar ta buɗe. Akansa idanunta suka sauka da mamaki, sai dai ganin yanda yaci toka yasata saurin maidawa ƙasa. Gudun kartai laifi ya sata ziro ƙafa ɗaya zata fito ɗayar kuma ta riƙe. Tsareta da ido da yayi ga kuma azabar da takeci yasata sakar masa kuka.

        A ransa yace (sai shagwaɓan tsiya). a fili kam sai ya girgiza kai kawai ya ɗauke kai yana miƙa mata handkerchief. “Malama goge waɗanan hawayen tunda ba satoki naiba”.

         Duk da halin da take a ciki saida tace (bama gara wanda ya satoni da kai ba) amma a zuciya😂. A zahiri kuwa baki ta tura gaba da amsar handky ɗin nasa da keta uban ƙamshin turarensa tahau share hawayen. Shi kuma yay gaba abinsa cikin asibitin batare daya jirataba duk da ya fahimci bazata iya taka ƙafarba dan tun'a gida ya lura dama da ɗingishi ta fito sanda Granny ta kamota.

          Kanta ta ƙara maidawa cikin ƙafafu ta dasa sabon kukan takaicinsa dana ciwo. A haka Nurse ɗin daya turo tazo ta sameta. Itace ta taimaka mata ta fiddota a motar suka fito. Da ƙyar ta taka ƙafar data ƙara riƙewa zuwa cikin asibitin. Suna shigowa a bazata sukaci karo da Khalipha.

       “Kai! Beauty lafiya kuwa? Ke da wa haka?”. 

        Bata iya bashi amsaba sai dai ganinsa yasata jin sanyi har cikin rai. Shima bai damu da rashin amsawar tataba ya maida dubansa ga Nurse ɗin. “Sister Sadiya ita da waye sukazo?”.

      Cike da girmamawa tace, “Ogane nidai yace naje na shigo da ita sir”.

    Yasan Yayansu suke cema oga a asibitin. Dan haka cike da mamaki yace, “Yana ina shi ɗin?”.

     “Dr Mahmud office sir”.

“Okay kuje ina zuwa nima”. Ya faɗa yana nufar wani hanya alamar akwai abinda zaiyi.


        Sai da Nurse Sadiya tai sallama aka basu izinin shiga sannan ta shigo riƙe da Zinneerah da ganin Khalipha yasaka kukan nata tsagaitawa. Miƙewa Dr Mahmud yayi yana mata sannu, shiko kansa yana duba wani file bai ɗagoba balle ya nuna yasan sun shigo office ɗin. A kujerar dake kallon wadda yake zaune Dr Mahmud yasa Nurse ɗin ta zaunar da ita.

         “Sorry ƙanwarmu kukan ya isa ko?”. Dr Mahmud ya faɗa yana murmushi da kallon Zinneerah ɗin a zuciyarsa yanaji kamar yasan fuskarnan.

       Kanta taɗan jinjina masa tana ƙara takure kanta waje ɗaya a cikin kujerar dan kusancinsu ya sakata jin ta takura, duk ya cika wajen da kwarjininsa. Kallonsa taɗan sata taga har yanzu yana a yanda suka samesa. ta janye tana maidawa ga Dr Mahmud daya jeho mata tambaya.

       “Ƙanwarmu mike damunki ne?”.

Ɗan jimm tai kamar bazatace komaiba dan har sai d Yah Adnan dake saurarensu ya ɗan ɗago ya dubeta ya maida kansa. Fahimtar da Dr Mahmud yay kamar tanajin nauyin maganar saboda AK ya sashi faɗin “To ko dai zamu tada boss a wajen nan ne? Ranka ya daɗe kamarfa........”

     Saurin katsesa tai da cewa, “Cikina ke ciwo”. 

     AK daya ɗan ɗago ya dubeta a karo na biyu saiya girgiza kansa kwai kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya sake maida kansa ga takardun hannunsa. Takarda da pen Dr Mahmud ya tura mata, “Idan babu damuwa rubuta anan kawai”. 

        Har cikin ranta taji daɗin hakan, babu musu taja takardar ta fara rubutawa tana cije baki. Koda ya amshi takardar ya duba yaga mita rubuta sai baice komaiba ya jin jina kansa yana nuna mata ɗan gadon duba marasa lafiya dake can gefe.  “jeki kwanta acan ina zuwa”.

         Miƙewa tai cike da ƙarfin hali ta nufi gadon ta kwanta. Shima sai ya miƙe ya bita da wani ɗan dogon roba a hannu da syringe. Tambayoyi ya ɗan ƙara mata tana bashi amsa cike da jin nauyinsa. Daga haka ya ɗiba jininta.

     A dai-dai nan Khalipha yay sallama ya shigo office ɗin. Ɗagowa Yah Adnan yay ya dubesa da ɗan mamaki. Amma baice komaiba. Khalipha da hankalinsa duk yana ga yanda yaga Zinneerah ɗin ya ƙaraso yana faɗin, “Yayanmu barka da dare”.

        “Dama kana nan?”.

  “Eh wlhy ban jima da zuwaba. Dr Muneer ne ya kirani mukai wani aiki. Miya samu Beauty ɗin ne?”.

       Wani ɗan luu da idanu yayi da tsatstsare Khaliphan da idanu tamkar baiji miya faɗa ba. Shima Khaliphan sai yanzu ya fahimci katoɓarar da yay na cema Zinneerah beauty ɗin. Ya ɗan sosa gefen wuyansa yana murmushi. “I'm sorry yayanmu”. 

        “For what?”. 

Ya faɗa cike da salon basarwar tasa yana maida kansa ga file ɗin hannunsa.

      Dariya Khalipha ya ƙyalƙyale dashi yana barin wajen ya nufi can inda Zinneerah da Dr Mahmud suke. “Oh oh sweet sister sorry, dama haka kike ragguwa ashe?”.

        Dr Mahmud ne ya bashi amsa cikin dariya. “A'a Khalipha karfa ka cika baki, dan sai na bata labarin naka rakin kaima”.

       “Lalala Yah Mahmud yi haƙuri kar kaja ta rainani, mike damunta ne? Naga kamar sun shigo tana ɗingishi”.

     Kai tsaye Dr Mahmud yace, “Tana complain ne na mara, inaga zamuyi mata text mugani, duk da ina zargin dai bazai wuce....” Sai kuma yay shiru yana ɗan duban sashen da AK yake zaune.

      Addu'ar samun lafiya Khalipha yay mata yana ɗan murmushi da kauda zancen ta hanyar cewa, “Bara naje da jinin lab to”. Daga haka ya fita. Duk abinda suke tattaunawa Yah Adnan na jinsu. Amma saika rantse ma baya office ɗin, daga ƙarshema waya ya kira har Khalipha ya dawo bai gamaba.

        Drip Dr Mahmud ya sakama Zinneerah ya dawo inda AK yake ya zauna suka cigaba da tattauna abinda ya shafesu har Khalipha ya dawo da result ɗin da magunguna daya sayo.

      Bayan Dr Mahmud ya amsa ya duba yace, “Dama abinda nai zargi kenan, bazai wuce harda Imfection ɗin ba, zamuyi treating ɗinsa insha ALLAH zai barta tunda baiyi ƙarfi ba. Tunda ma ka haɗo maganin inaga kai mata allurar nan kawai”. 

        Miƙewa Khalipha yay yana faɗin, “Okay ALLAH yasa dai bata tsoron allura to”. Dariya kawai Dr Mahmud yayi, shima bayan ya mata allurar duk da barci naɗan figarta sai ya fita ƙarasa uzirinsa. Yabar Dr Mahmud suna cigaba da tattaunawa da Yayan nasu da ya koma kamar baya office ɗin.


★★★


        A gida kuwa Farah tamkar zatai ƙaramin hauka a cikin ranta. Tanada kishi sosai wanda ita kanta wani lokacin abun har tsoro yake bata, dan Adnan dai ba taɓa mata alƙawarin bazai ƙara aure yayi ba. Ko lokacin da su Hajiya Iya suka takura masa saiya ƙara aure badan tsayawar Mammah a kansa ba da babu abinda zai hanashi ƙarawar duk da ba nuna mata yanada buƙatar hakan yayiba.

       Tsaf hajiya iya tana lure da ita. Kuma dama da biyu ta hanata bin nasu. Dan haka ta shige ɗaki abunta tai shirin barci ta kwanta tunda tasan dai ba binsu Farah ɗin zataiba a yanzu.

               Kamar yanda ta ƙware akai ƙara wajen Mammah yanzu ɗinma sai da ta faɗa mata tana kuka. Ran Mammah ya ɓaci sosai jin yarinyarma ba'a cikin ƙannensa takeba kamar yanda ita Farah ɗin tace tana tunani. Koda Mammah ta kirasa ashe wayar a nan gida ya barta, bai fita da ita ba, na hannunsa na alaƙar business ɗinsa ne kawai. 

     Wannan abinne ya ƙara ƙular da Farah ta dinga kai kawo tsakanin ɗakinsa da falo ita kaɗai dan hajiya iya dai ta shige. yaran kuma da suka dawo basu shigo nanba dan a gajiye suke.


         ★★


      Sai kusan sha ɗaya ruwan da aka sakama Zinneerah ya ƙare suka nufo gida. Tana a baya ita kaɗai, Khalipha ne yanzu ya amshi driving ɗin, shi kuma yana a gefensa zaune. Babu mai magana a motar dan duk sun gaji kwanciya duk suke buƙata, sai sanyin ac daya takurama Zinneerah, hakan ya sata dunƙulewa waje guda barci sama-sama nason figarta.

         Koda suka iso gidan Khalipha ne ya buɗe mata ta fito, ganin yanda take ɗan tangaɗin barci dana rashin ƙwarin jiki yace, “Ƙanwata kodai na kamaki ne?”.

      Kanta ta girgiza masa a hankali cikin yanayin kasala tana dafe jikin motar dan ji take tamkar zata faɗi. Ɗan matsawa Khalipha yay da ita gab yana ƙoƙarin kai hannunsa zai kamo nata. Yah Adnan dake kallonsu ta gefen ido, amma saika ɗauka gaba ɗaya hankalinsa baya tare da su ya katse hanzarin Khalipha ɗin dake neman kamo hanun Zinnerah, “Besty kaje da takardun nan ɗakinga zuwa safiya idan ALLAH ya kaimu saika dubasu zamuyi magana daga baya”.

     Dole Khalipha ya haƙura daga son taimakon Zinneerah ya juya garesa ya amshi takardun.

     “Kaje kawai sai da safe muma bara mu shige dare yayi. Ke kuma muje”. Ya sake faɗa ciki-ciki yana duban Zinneerah da duk tana saurarensu.

        Dole Khalipha yay musu sai da safe yana nufar sashen samarin gidan. Shikuma ya tasa Zinneerah dake tafiya da ɗan layi na barci suka nufi sashen hajiya Iya. Abin tsautsayi tana tura ƙofar falon da niyyar shiga hannunta ya gota akan handle ɗin saboda tuntuɓe da takalmi da tai. 

     Saurin tarota yay ganin zata faɗi, saboda ya rigada ya kawo jiki ita kuma tayo baya. Sai kuma ya ɗagata da hanzari yana miƙar da ita tsaye sosai akan ƙafafunta. 

      Ɓoyayyen numfashi ta sauke da saurin yin gaba har ƙafafunta na neman harɗewa. Ya ɗan bita da kallo ƙasa-ƙasa harta shige bedroom ɗin hajiya iya. Janye idanunsa yay da zummar nufar nasa ɗakin shima yaci karo da gimbiya Farah mai zamani hakimce cikin kujera tacika tayi fam. yanda tai mugun tsatstsaresa da idanu ya bashi tabbacin tunda suka shigo tana a falon kenan.. Sanin halinta yasa bai tanka mataba ya ɗauke kansa yay gaba.

        Sai da yay kusan mintuna biyar da shigowa sannan ta biyosa. Tana shigowa yana shiga bayi. Duk da tsahon lokacin daya ɗauka bai fitoba a tsaye ya sake isketa ta kuma cika fam fiye da farko.

        Hidimar shiryawarsa ya shigayi yanzunma bai kulataba. Sai da ya gama tsaf cikin kayan barci ruwan sararin samaniya sannan. Kamar zai shareta dan takaici sai kuma ya ɗan dubeta ya ɗauke idanunsa. Inda take ya matsa sosai tare da dafe bangon da hannayensa biyu ya sakata a tsakkiya yana zuba mata fararen idanunsa da alamun barci ya bayyana a cikinsu. 

       A take dukkan fushinta ya fara rauni dan waɗanan idanun nasa suna ladabtar da ita idan tai laifi. Suna kuma tabbatar mata da ɗunbin soyayyarta a cikinsu idan yaso lallashi. Suna kuma mata kwarjini da girmama kimarsa a gareta a duk sanda shi ɗin yazam mai laifi a gareta.

       A karan farko ya saki murmushi ganin yanda ta lumshe nata hawaye na silalowa. Fuskarsa yakai gab da tata suna musayar shaƙa da zuƙar ƙamshin juna. Kafin ya cire hannunsa guda dake dafe da bango ya saƙalo ƙugunta ya sake mannata da jikinsa sosai yana wani sakar mata numfashinsa da ƙarfi akan fuskarta. A take ta saki nannauyar ajiyar zuya da saka duka hannayenta ta zagayoshi ta ƙanƙame itama.

      Murmushin ya sake saki, batare daya ce komaiba ya ɗauketa cak ya nufi gadon da ita. Yana sauketa bargo yaja ya lulluɓa musu, zatai magana ya rufe mata bakin da nashi. Daga haka ɗakin yay tsit kamar ba ita ta gama cin alwashin karta masa shika shikan rashin mutunci cassa'in da tara ba.


______________________________★


       *_DANYA_*


Duk yanda Inna tasoji daga Karima hakan ya gagara. Dan ciwo ta kwanta kashirɓan tun randa ta dawo. Abin kamar wasa sai ga ƙaramar magana na neman zama babba. Tuni Inna ta manta da wani zancen kiranyen dataima Baba saboda ruɗanin halin da Karima ke ciki.

      A rana ta uku duk yanda taso ɓoyewa hakan ya gagara. Dan dole ta nufi gidansu Babawo ta sanarma innarsa. Sunyi mamaki matuƙa. Dan shi dai baice dasu Karima tana Danya ba, kuma koda safe sai da sukai waya da shi. Dole Innar Babawo ta ɗakko gyale ta biyo Inna gidanta. Itama hankalinta ya tashi ganin yanda jikin Karimar yay kaca-kaca da sayin duka ga ciki tsoho haihuwa ko yau ko gobe.

       A ruɗe tace ma Inna ta shirya karimar suje asibitin kusada. Bara taje ta nemo ƙanin Babawo ɗin tunda yanada mashin. Daga haka ta fice ita kuma Inna daketa tsinar Babawo ɗin ta shiga kimtsa Karima.........


_____________________★


    

          Hajiya iya batasan su Zinneerah sun dawo gidanba sai da asuba ta ganta kwance a bayanta. Hannu tasa ta shafa mata fuska tare da gyara mata bargo. Itama cike da ƙarfin hali ta nufi bayi yin alwala dan ƙafarta ciwo take mata tun da daddare dama. Da ƙyarma ta iya kai kanta bayin. hakama da tayo alwalar da gyar ta fito. Duk yanda taso gabatar da salla a tsaye hakan ya gagara sai a zaune tayita. Bayan ta idar kuwa ko azkar yau batayiba ta zame ta kwanta a wajan.


       Itama Zinneerah farkawa tai, sai dai koda taga Hajiya Iya kwance a ƙasa bata kawo komai a rantaba ta shige bayi kimtsa jikinta. Ganin harta fito Hajiya Iya na kwance a wajen sai abin ya ɗan bata mamaki amma batai magana ba ta hau shiryawa dan wanka tayo. Batajin ciwon komai yau sai rashin ƙwarin jiki. Ta shirya cikin siket da riga na baƙin Material mai adon firanni golden. Ganin Hajiya Iya taɗan motsa ya sata zuwa gabanta ta tsugunna tana gaisheta.

     Hajiya Iya ta buɗe idanu da ƙyar tana duban Zinneerah ɗin. Murmushin ƙarfin hali tayi da miƙa mata hannu ta kamo nata. “Inno na yaya jikin?”.

     Kasa amsawa Zinneerah tayi saboda jin zafi jikin na Hajiya Iya. aɗan rikice ta sake damƙe hannun cikin nata tana faɗin, “Granny baki da lafiya ne?”.

        Kamshinsa ne ya katse Hajiya iya dake ƙoƙarin bama Zinneerah amsa. Zinneerah ma sai ta ɗan dubi ƙofar dai-dai ya shigo idanunsa suka shige cikin nata. Saurin janye natan tayi tana maida kai ƙasa dan wani irin matsananciyar kunyarsa taji saboda tunowa da faɗa masa a jiki datai jiya da dare. Ga sirrinta daya gamaji a bakin hajiya iya kafin su wuce da kuma tabbacin ya sakejin wani wajen Dr Mahmud.

      Shima nasa idanun ya janye yana duban Hajiya iya dake kallonsa a kwance. A take ya gano babu lafiya dan yasan hajiya iya sosai a rayuwarsa. Duk da kuwa zaman da yay a wajenta na shekaru tara ne kacal, sai hutun da yake zuwa mata kuma bayan ya koma London karatunsa.

       Ta inda Zinneerah ke tsugunne ya ƙaraso ya ɗan ranƙwafo kansu yana kai hannu goshin Hajiya Iyan. “Granny lafiya kuwa?”.

        “Wlhy ƙafafun nan ne ke neman takuramin kwana biyun nan Moddibo ”.

      Idon Zinneerah na cikowa da ƙwalla tace, “Amma Granny shine baki faɗaba? Wlhy jikinki zafi dan ALLAH ki tashi muje asibiti”.

     Yanda ta ƙare maganar hawaye na silalowa ga rawar murya ya sakashi ɗan dubanta, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ɗayan hannun Hajiya iya ya kama shima ya tadata zaune sosai dan tanada jiki itama masha ALLAH. 

        Gaban Hajiya Iyan yay wani ɗan tsuggunne idanunsa na sauya launi zuwa damuwa. Dole Zinneerah ta miƙe saboda kusancin da suka samu yayi yawa. Cikin wayancewa tace, “Bara na haɗo miki kunu kiɗansha sai kisha maganinki”.

     Murmushi Hajiya Iya tai tana binta da kallo harta fice, kafin kuma ta sake maido idonta kan Yah Adnan dake mata tambaya muryarsa a ƙasa.


      Al'amarin kamar almara sai ga jikin hajiya iya na neman rikicewa a wannan yini, dole Dr Mahmud da Khalipha suka rufu a kanta duk da shi bai kammala nasa karatunba ma. Amma kwazon da yake nunawa yasa ko ƙasar yazo yakanje Shira hospital yay wasu ƴan ayyuka dai-dai saninsa.

        Tashin hankalin ruɗewar jikin ya saka Yah Adnan cewa zai wuce da Hajiya Iyan london a yau. Amma sai Baffah da ake saran zai dawo ƙasar yau ya taushesa akan yay haƙuri yana zuwa shima.

    Badan yasoba dole yabi umarnin mahaifinsa da yake zuwa yamma jikin Alhmdllh ya ɗan ɗaga mata. Duk wanda ya kalli Zinneerah yau yasan tasha kuka. tayi wuni firgai-firgai da ita na damuwa. tabi ta nane a ɗakin wajen Hajiya iya ita dasu Jamal. Ko yayansu ya shigo su su Jamal tsoro na sakasu fita da shakkarsa. Itako duk da tanajin shakkar tasa da kwarjin da yake mata saita fiske abinta taƙi fita.

         Dama tun lokacin da jikin ya rikice tai kiran Maman Sadiq ta sanar mata. Itama hankalinta ya tashi matuƙa dan haka tace zuwa yamma zata shigo tare da yara su dubata dan yanzu duk sun wuce makaranta Little ne kawai a gidan. 


    Aiko kamar yanda Mman Sadiq tai alƙawari bayan sallar la'asar sai gata tare da Sadiq, Abdull, Aliyu sai Little. A napep sukazo kasancewar Abba baya nan yaje ɗanmusa duba yayansa da baida lafiya shima.

        A gate ya saukesu mmn sadiq tai kiran Zinneerah a waya dan tazo ta shiga dasu. Duk da tana tare da damuwar ciwon hajiya iya cike da ɗokin ganin ƙannen nata da gudan jininta ta fito zuwa hanyar gate. Sai da suka gaisa da maigadi ta sanar masa baƙine zasu shigo. 

      “To Hajiya bara a buɗe musu”. Ya faɗa yana ajiye butar hannunsa daya ɗauka alamar zaiyi wani abu. Da gudu su Abdull sukayo kanta lokacin da suka shigo. ganin yanda Little ya biyo rububi a guje shima ya bata dariya. Tsugunne yakai da buɗe musu hannayenta duk suka shige su huɗun. Mmn Sadiq dake binsu da kallon sha'awa taɗan murmusa tana ɗauke kanta. Da ƙyar Zinneerah ta samu ta miƙe tsaye hannunta riƙe dana Aliyu tana ɗauke da Little a ɗayan ta dubi mmn sadiq da faɗin, “Mama sannunku da zuwa kumuje ciki”.

       Kai kawai Mmn sadiq ɗin ta jinjina mata tana mamakin yanda ɗiyar tata ta ƙara canjawa a ƴan kwanakin data dawo gidan. Zuwansu tsakkiyar harabar gidan yay dai-dai da fitowar AK daga sashen Hajiya iya kunen sa manne da waya alamar magana yakeyi, sanye yake cikin ƙananun kaya da suka sakko fiddo zallar ƙuruciyarsa da hutu dajin daɗi, ya cigaba da takowa a hankali garesu suma suna nufarsa duk da Zinneerah jitake tamkar zata faɗi dan har haɗewa ƙafafunta keɗanyi..........✍

       

No comments

Powered by Blogger.