Hamshakiyar Uwa Book 1 Complete Hausa Novel
*HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Kuɗin Karatu 600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
_Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai komai,tsira da amincin Allah su tabbata ga annabi Muhammad(S.A.W)._
_Kamar yadda na fara lafiya,Allah ka bani ikon gamawa lafiya,Allah ka bani ikon faɗakarwa gwargwadon iyawata,Ya Allah ka yafe min duk wani kuskure da hannuna zai rubuta,Allah ka bani ladar faɗakarwar._
*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Free Page 1*
Kan shi a ƙasa bayan ya zube a gaban ta gwiwoyin sa suna ƙasa tamkar mai neman gafara. A hankali ya furta Hajiya Barka da dare.Ta ɗago kai daga kan TV da ke nanne a bango cikin wata ƙatuwar ma'ajiyar ta bango guda. Ta maida kanta gare shi ta na nazarin fuskar shi, sannan ta dubi yarinyar da ke zaune a ƙasa tana shafa mata man zafi a ƙwauri ta ce, "Azima ta shi ki je ki kwanta." Cikin sauri yarinyar ta miƙe ta re da faɗin sai da safe Hajiya. Allah ya tashe mu lafiya, Hajiya ta furta a hankali. Ta maido kallon ta ga gareshi sannan ta soma magana cikin isa "Shamaki zauna da kyau Allah ya yi maka albarka." Ya ce Ameen Hajiya. Ta ce "Bisa dukkan alamu ka ga wadda ta yi wa ranka, ko dai birgewa ko kuma ta baka shi'awa, faɗa min wani abu dangane da ita."
Ya sake gyara zama bai yi mamaki game da kalaman mahaifiyar ta sa ba,domin ita mace ce mai tsananin basira tare da karantar ɗan Adam, in har za ku yi zaman minti talatin da ita ba ko shakka zata iya zayyana maka abubuwa da dama daga cikin ɗabi'u ko halayyarka. Sannan babu abinda tafi saurin ganewa irin ka yi mata ƙarya. Ya ce Hajiya so ɗaya na ganta zata je Islamiyya na tsaya zan yi mata magana ta ja tsaki ta wuce, maimakon in fusata sai kawai na ci gaba da bin ta a baya bata sani ba har ta shiga makaranta.
Na san cewa kamar shidda sun ta so na koma sai ban ganta ba, yau na bi ta layin da na ganta cikin sa'a sai na hange ta a wani shago tana siyayya,na jira ta gama na bi bayan ta na ga gidansu yanzu ina neman iznin zuwa ne in Allah ya sa an bani izni.
Hajiya ta yi shiru kamar ba zata ce komai ba, zuwa can ta ce "Je ka kwanta amma kafin hakan ina son ka yi sallar istikhara da safe ka zo ka kuma bani wannan labarin da ka bani." Ya miƙe a hankali tare da faɗin na gode a tashi lafiya. "Allah ya maka albarka." Ta furta tare da ɗaukan goran ruwa a gefen ta ta buɗe da zumar sha.
Firgigit ya farka ya na kallon ɗayan sashen da take kwance, mafarkin yana dawowa a zuciyar sa, babu ko shakka sai ya yi wanka domin ya cimma hakan a mafarkin sa, bai taɓa samun hakan ba duk zaman gauran takar sa, kila gara lokacin da ya ke saurayi farkon balaga. Ya yi addu'a a sallar sa, domin bai samu zuwa Masallaci ba sakamakon makara,ba zai iya tuna lokacin da ya rasa jami'in sallar asbahi ba. Ya jima kwance jikin sa lankwas wanda yin hakan ba al adarsa ba ce. Sai ya ji kamar wani ɗan zazzaɓi ya na sarfatar sa. Cikin hakan ya ji ana kwankwaso ƙofarsa, ya tashi zaune sannan ya bada iznin a buɗe. Ta turo ƙofar ta na sanye da kayan makaranta, Azima ce. Ta ce"Yaya Shamaki Hajiya ta ce in duba ka." Ya ce ki sanar mata ina zuwa. Ya miƙe ya ɗauki jallaiya bulu mai gajeren hannu tasha aiki da sirfani mai ruwan zaiba ya saka.
Yana fitowa falonsa Meema ta na shigowa ta nufeshi da gudu tana faɗin "Dadi! Ya sa hannu ya ɗaga ta sama ya sata a jikin sa tare da faɗin Mamana Ina Mubina ina Anisa? Ta nuna mishi hanyar ɗakinsu tare da faɗin "Suna ciki Rahin tana shirya su." Ya lakaci kuma tun ta ke fa? Ta ce "Ni'ma yanzu za 'a shirya ni." Ya dire ta to maza kar ku yi latti ki tafi a shirya ki. Ta ruga da gudu. Shi kuma ya nufi sashen Hajiya.
Tana zaune a kan sallayar ta ƙafafun ta a miƙe sanɓal ta rufe kanta da hijabi na alfarma ƙamshin ta na tun fil"azal ya na tashi tana riƙe da carbi tana lazimi. Ya samu gefe ya zauna zama irin na girmama wanda ka ke gaban shi. Ya kalle ta cikin darajawa tare da faɗin Hajiya ina kwanan ku? Ta sauke numfashi cikin ƙasaita, sannan ta amsa da "Lafiya lau Shamaki, me ya same ka yau ba ka je sallar asbahi ba?" Ta yi tambayar cike da kulawa. Ya sunkuyar da kai, jikina yau na tashi babu daɗi sam, kuma sai na makara. "Me ya biyo bayan neman zaɓin da ka ba Allah ajiya! Ka ji wata damuwa game da yarinyar ko kuma Allah ya haska maka wani al'amuri a cikin baccin ka?"
Ta jeho masa tambayoyi. Shamaki ya ce eto har zuwa yanzu ina jin ƙaunar ta kuma na yi mafarkinta. Ya sunkuyar da kai domin ba zai iya bada labarin mafarkin ba. Hajiya ta ce "Ina sauraron ka." Ya sa hannu ya shafa fuskar sa sannan ya saci kallon ta ta tsira mashi ido,ba ko shakka so ta ke yi sai ta fahimci ko zai mata ƙarya. Ya ce cikin wani yanayi muka haɗu Hajiya Allah dai ya kyauta.
Ta yi ɗan murmushi da alamu ta fahimci ina ya dosa. Shike nan, ka sake bani labarin da ka bani jiya game da yarinyar. Ya gyara zama ya zayyana mata komai kamar jiyan. Ta numfasa tare da faɗin shike nan ka je ka fara bincike a kanta kafin ka je gurin ta. Sannan kar ka manta. da sharuɗɗa na akan duk wata mata da za ka aura. Bana son ka sake sakin mace daga guda ukun nan da ka yi, amma ka sa a ranka matan ka huɗu ne in Allah ya ƙaddara ina aɗdu"a. Kaje ka shirya yau kai zaka kai yaran ka makaranta domin tun jiya suka nemi alfarmar hakan.
Sannan in kaji zazzaɓin zai matsa sai ka sha magani, duk da nafi zargin zazzaɓin na soyayya ne. Ta kai ƙarahen maganar da 'yar dariya irin ta manya cikin ƙasaita.
Ya shafa kanshi tare da yin murmushi mai sauti,ba ko shakka zolayar sa Hajiya ke yi.
Ya ɗan rusuna. zan yi yadda ki ka ce insha Allahu Hajiya. Sanna ya miƙe ya nufi ciki. A mota tare da 'yan yaran sa mata su uku, Meema da ke zaune a gefen shi ta ce "Dadi za ka dawo ka ɗauke mu?" Ya dube ta sannan ya girgiza kai, Bazan dawo ba Mamana zan tafi kasuwa ne fa. "To zaka raka mu har ajin mu?" Ya kai hannu ya shafi kanta me zai hana zan raka ku in kuna so. Anisa ta sako hannuwan ta daga can baya ta shafo kumatun sa, Dadi muna so 'yan ajinmu suna cewa basu taɓa ganin Babana ba. Mubina ta ce Nima haka Dadi za ka raka mu kowa ajinta. Ya ce to shike nan sai mu fara kai Anisa ita ce Smaller ko sai mu kai Mubina, sai in kai Anty Babba ko Meema? Cikin jin daɗi ta ce e Dadi na.
Sun yi kamar yadda suka tsara da 'ya'yan na sa sannan ya ciro kuɗi ya raba wa malaman sannan ya tafi suna ta godiya sannan ya kama hanyar kasuwa.
Tun da ya zauna a ofishin sa da ke babban reshen manyan katunan sa wato Zeena Galary da ke ƙatuwar plazarsa mai suna Gidan Zeena a babbar kasuwar kwari da ke Kano. Dukan yaransa na katin sun fahimci ya na da 'yar damuwa, kasancewar ba haka ya saba zuwa ba. Shi kansa tunda ya ke bai taɓa samun kansa cikin wannan yanayin ba game da matansa da ya aura a baya. Ko matarsa ta fari bai ji irin abinda ya ke ji a wannan lokacin ba. Yana jin in bai fita ya nemo yarinyar nan ba kafin yamma akwai matsala.
Suna idar da sallar Azahar ya cire agogo da zobe da duk wani abu da zai nunashi a mai kuɗi, ya fita ya saka salifan da ke ƙofar banɗakinsa na ofishin ya fita ba tare da ya yi wa kowa magana ba, ya je titi ya tari ɗan sahu ya hau tare da faɗin kaini Ɗan a gundi. Dai dai bakin lungun ya tsaya ya ciro kuɗi Naira ɗari biyar ya miƙa masa sannan ya sa kai cikin lungun, shi dai Ɗan sahu ya ciro canji ya ɗago kai ya ga baiga Alhaji ba, cikin jin daɗi ya yi tafiyar sa.
Na siyo gawayi ina sauri zan dafa mana taliya 'yar murji ni da ƙannai na kasancewar Umman mu bata nan taje awon ciki. Na taka dakalin ƙofar gidanmu sai naji ance "Salamu alaikum. Na waiwayo sai naga wani Mutum wanda wanda ba zan iya siffanta shi a take ba. Na amsa sallamar ina jira ya min tambaya domin dai ƙila wani gidan yake nema a lugun namu.
Ga mamaki na sai naji ya ce "Zan iya magana da ke?" Me zai hana.Na bashi amsa ba tare da na fahimci me ya ke nufi ba. Ya ɗan ƙara matsowa ya dafa bangon gidan mu ya soma magana "Sunana Aliyu amma anfi sani na da Shamaki, kusan kwana uku baya na ganki kuma gaskiya ba wata kwana Ni ina son ki!" Na ɗan ja baya da sauri domin ban zaci inji haka daga gare shi ba,hasali ma ni ba a taɓa furta min kalmar so ba,dan haka sai na rikice ina sake kallon shi. Ya ce ,"Na ga kin firgita da gaske na ke yi." Zan shige gida ya ce "Tsaya mana ya kamata ki bani amsa ko da rashin amincewa ce." Na ce abinci zan dafa wa ƙannai na suna jin yunwa. "In dawo anjima da dare?" Ya tambaye ni da sauri. Na sake duban fuskar sa, nifa bantaɓa zance ba,bansani ba ko Abban zai bari. "To ki tambaya in sun dawo amma zanzo anjima ɗin." Na ce to shike nan.
Ina girki ina tunani, duk da mutumin ba yaro bane amma naji ya birgeni, sannan kalmar so da ya furta a gare ni ta zama baƙuwa a gurina, dole ma in amsa masa ko na shiga sahun 'yammata da ke zance a lungunmu bayan wasu ma na girme su nesa ba kusa ba. Shekaruna ashirin da haihuwa jarabawar kammala Sakandire muke yi, a Islamiya ina ajin sauka, amma ban taɓa samun wanda ya ce yana sona ba ko da sunan wasa ba. Na sha kallon kai na a madubi duk da ban kasance fara me shegen kyau ba,na tabbata ba za a sakani a layin munana ba, kuma dai dai gwargwado ina da hankali da kamun kai.
Cikin wannan yanayi na gama girki amma sai na kasa ci, haka a Islamiyya yau sai tambayata a ke yi lafiya kuwa. Domin na zama shiru sai tunani, in har iyayena sun laminci in yi soyayya da shi ba shakka zan ji daɗi domin har na fara jin cewa na ƙosa in sake sauraron muryar shi.
Bayan magariba Umma tana zaune kan tabarma ta idar da salla ta na cin ɗata, na zauna kusa da ita na ce Umma ɗazu wani mutumi ya zo ƙofar gidan nan wai gurina ya zo. Ta ɗago kai da sauri "Me ya ce miki ?" Na ce wai yana so na, nace sai in na faɗa.a gida. "Ɗan ina ne?" Ta tambaye ni, na ce wallahi bansani ba, ya ce dai zai dawo da daren nan. Tace Allah ya sa dai na gari ne,dama ranar nan sai da Umman su Fati ta gwaɓa min magana wai an saka ranar Fati ita dake suyar awarar dare, masu zuwa haddar Kur'anin dare shiru. Kuma nasan ta gwaɓa min maganar ne saboda na ce ta hana Fati yin dare sosai a gurin tuyar awara wani lokacin har shaɗayan dare take kaiwa Abbanku in ya zo sai ya yi ta faɗa. Wai an bar yarinya gurin daga ita sai yaran nan maza marasa kunya. Na ce ai yanzu faɗar gaskiya ta zama matsala Umma. Ta ce haka ne ke dai ki kula da kanki in ya zo ki fita ki saurare shi in kuma Abbanku ya dawo kafin lokacin zan faɗa masa.
Jamila ƙanwata ta matso kusa da mu tace Umma Yaya Baby ce zata fita zance? Na ce to sarkin tsegumi. Umma ta ce "Menene a ciki in kin faɗa mata, Jamila ai ƙawa zaki maida ita,na faɗa miki komai ki ke yi tare da ita shekarunta sha bakwai fa yanzu." Na kalleta nayi murmushi tare da faɗin to ƙawata baƙo zan yi. Ta ce Allah na gode maka mu ma Allah ya sa ayi biki a gidanmu. Umma ta ce "To kije kiyi wanka ki gyara jikin ki." Na ce har sai na yi wanka kuma, na yi da safe fa. Jamila ta ce, au da me ki ke nufi, haka zaki je kina zufa? Na tashi na je na ɗebi ruwan sanyi abinda bana wanka da shi amma dan zumuɗi na faɗa banɗaki na yi wanka aiko ina ta atishawa, cikin zuciya ta kuwa fargaba ce tana saƙamin ko ma dai ba zai zo ba.
Na idar da sallar Isha'i a ɗakin Umma na zabga tagumi gefe ga kayana sabbin na sallar bara da Umma ta ce in saka. Jamila kuwa ta tasani agaba sai fadi ta ke "Anty Baby ki tashi ki saka kayan kar ya zo baki shirya ba." Na ce Jamila ni yanzu fargaba ke duka zuciya ta,ji na ke kamar ya fasa zuwa,kila ma ya canza shawara.Ta ce "Karki faɗi haka Anty, shifa ya zo da kansa tun farko ba ke ce ki ka nemo shiba." Sauke ajiya zuciya ta sun zo dai-dai da sallamar Abbanmu. Umma ta amsa tana masa sannu da zuwa, muka leƙa muka yi masa sannu da zuwa ya amsa. Nace to Jamila bari in shirya ɗin,ke ki je ki kaiwa Abba abinci. Ta fita tare da faɗin "To."
Ina jiyo Umma ta na sanar da Abba game da baƙon da zanyi,na yi kasaƙe inji me zai faɗa,sai ga muryar wani yaro ta ratso gidan da sallama. Umma da Abba suka amsa. Ya ce,"Ana sallama da Abban gidan nan inji wani mutum." Abba ya ce to ka ce ina zuwa. Umma ta ce baka tambaya ko waye ba,yace Malam Sani ne mun yi da shi zamuje wani aiki gobe,to nasan kan maganar ne,kinsan yadda rayuwa ta ke yanzu in ka samu aiki ƙoƙari ka ke ka je in ba haka ba sai aba wani. Ta ce "Haka ne Allah yasa mu dace." Ya ce Ameen bari in dawo yanzu.
Na gama cire rai da zuwan mutumin har takwas da rabi na yi danasani da ban saurare shi a lokacin ba, na kwance ɗankwalin da na ɗaura dan ya soma damu na,nafara ninke shi sai naji sallamar Abbanmu. Ya na kuma tambayar ina Baby?" Da sauri na amsa gani Abba, ya ce "Kije baƙonki yana waje yana jiran ki." Gabana ya yanke ya faɗi, na ce to.Jamila ta miƙo min yar kwalba tare da faɗin ga Humra ta Umma ce ki shafa ajikin ki. Na ɗan goga na fita da sauri. Umma ta ce "Baby in kinje fa ki gaida shi ." Abba ya ce haba kema dai yaran yanzu kar suke kallon kowa. Umma tace kasan wannan ce farkon fitar ta zance dole a tuna mata. Abba ya ce "Jamila kai masa tabarma. Can na tsaya a bakin ƙofa ina shaƙar ƙamshi turare mai daɗi irin wanda na ji ɗazu, yana can gefe jingina da bango sanye da farar shada riga da wando ba hula a kanshi, gefen shi ga keke irin mai kwando a gaba na manya ya jingina. Jamila ta shimfiɗa tabarma a kan dakali sannan ta gaishe da shi ta koma ciki. Na taka a hankali na isa kusa da shi,nace sannu da zuwa Yaya. Basan lokacin da baƙi na ya furta hakan ba. Cikin yanayin jin daɗi ya amsa da "Yawwa ƙanwata." Na nuna kishi tabarmar Yaya ka zauna. Ya ce to, ya isa bakin dakalin ya zauna,na tsugunna a gefe ya ce, ,"kema dawo nan ko ki hau sama ko ki yi irin zaman da na yi." Na zauna sannan na rusuna na gaida shi,ya amsa "Hajiya ta ce in gaishe ki, na ce ina amsa wa amma, sai kuma na yi shiru. Ya ce amma me? Na ce nayi mamaki ya aka yi ta sannu. Yace, "Ta sannu tun ranar da na fara ganin ki, tasan na yi magana da ke ɗazu, kuma ta san ina nan yanzu." Na ce Allah sarki to ina gaishe ta in ka koma. Sai da tuni zuciyata ta shiga fargaba e ko matar sa ce Hajiyar domin daga ganinsa ka san dai yana da iyali.
Ya katse min tunani da tambaya. "Baby Ya sunan ki na gaskiya? Saboda ko sunan ki Ni bansani ba yanzun da na yi sallama da Abba na ji yana cewa Baby." Na ce Amira, amma na asalin gaskiya Rabi'atu sunan Maman Abbanmu ne, sai ake ce min Amira,Baby kuma Ummanmu ta ke faɗa min sai kuma ya rinjaya. Ya numfasa. "Ni ma dai Babyn ya fi min daɗi, amma zan kira kowanne in na so ko?" Na Ɗaga kai alamun eh.
Ya yi 'yar gyaran murya "Baby gaskiya ina son ki kamar yadda na faɗa ɗazu, in har ki na sona to aure ya kawo ni kamar yadda na faɗawa Abba ɗazu. Sanna bazan ɓoye miki komai ba,ina da yara uku duka mata,kowacce mun rabu da mahaifiyar ta... Saboda me? Na jeho masa tambaya ba tare da na sani ba. Ya ɗan yi dim, sannan ya ce "Saboda Allah, kar ki damu sannu zaki san komai. Ya ci gaba Ni ƙaramin ɗankasuwa ne ina tsare shagon mai gidana a Kantin kwari. Fatan kin fahimta?" Na ɗaga kai tare da faɗin umm. Take zuciyata ta sare kuma ta soma tuhumarsa. Mata uku, kuma ba ko ɗaya yanzu, gaskiya ya kamata insan dalili. Ya katse min tunani da cewa, "Baby ta bakin ki na ke son ji ko kina so na kuma za ki iya aure na? Ni dai komai na ki ya yi min. Na numfasa cikin sanyi jiki na to gaskiya ni dai bansani ba ko ina son ka domin ban taɓa samun kaina a cikin shi ba to bansan ya yake ba. Sannan magana aure Allah shine mai ƙullawa, in har ya ƙaddari hakan zan amsa hannu biyu. Yace "Har yanzu dai ban samu amsa ba,amma zan baki zuwa jibi, kiyi nazari kuma ki ƙoƙarta ki gano ko kina so na." Na ce, to na gode kuma zanyi yadda ka ce. "Bani lambar wayar ki zan kira kafin jibin inji wannan sanyayyar muryar." Na ce sai dai in baka ta Ummanmu, saboda har yanzu Abbanmu bai sai min ba, yace sai mun gama walimar saukar ƙur'ani. Yace to bani ta ta ɗin, na faɗa masa sai ya yi flashin yace, "Inkin shiga sai kuyi sebin domin inna kira kai tsaye kinsan ni ne." Nace, to. Yace "Nine ɗan auta a gurinta, kuma ni kaɗai ne namiji, yayinda huɗu duk mata, Yaya Zainab ce babba,sai Maryam A'isha da Fatima duk suna aure a nan cikin gari." Na ce masha Allah kaji daɗinka. Ni kam bani da yaya hasalima ni ce 'yar fari sai ƙanena uku Jamila da Jafar da kuma Habu,sai wanda za a haifa mana yanzu. Yace "Allah ya sauke ta lafiya dama ina ganin Abba na raya a zuciyata cewa ƙila ke 'yar fari ce." na ce Ameen, gani ka yi ba tsoho ba ko? Na tambaye shi ina 'yar dariya. Yace "E mana." Shima cikin dariya ya amsa. Nace, haka in 'yan makarantarmu suka zo sai su ce wai Ummanmu Antinmu ce. Muka ƙara yin dariya tare. Ya ce "To Ni dai bari in zo in tafi kar dare ya yi sosai,na kalli kekensa nace danma kana da abin hawanka balle ma ka ce zaka rasa ɗansahu. Yace haka ne." Nace, Ka gaida Hajiya da kyau. Ya faɗaɗa fara'a "Zan faɗa mata Insha Allahu." Shine ya nannaɗe tabarmar ya tako har bakin soro yana faɗin in gaida su Umma.
🖊️🖊️🖊️
[3/16, 13:07] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank ko Katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Free Page 2*
Har tsakiyar dare bacci ya ƙi zuwa min sai juyi na ke akan "yar katifarmu Jamila ta na ta baccin ta, tufka na ke ina warwara abu biyu ke ɗaga min hankali,menene dalilin rabuwa da matansa? Kuma komai nasa dole sai Hajiya ta sani? Zuwa yanzu nasan cewa Hajiya dai ba matarsa ba ce, ko dai mahaifiyarsa ko kuma uwar ɗakinsa. Da safe ina raba mana abin kari awara ce da koko duk muna tsakar gida harda Abbanmu. Umma ta dube ni,"Ke kuma lafiya duk jikin ki a sanyaye?" Nace, lafiya lau, kawai yau kasala nake ji. Ta dubi, Abbanmu tace, "Abban Baby kace ka yaba da saurayin nata jiya?" Ya ce gaskiya Salamatu na yaba sosai, in har sun dai-daita zanyi farin ciki domin alamu sun nuna shi mai hankali ne.Umma ta ce "To ɗan unguwar nan ne?" Yace, A a yace min shi ɗan Gama ne can aka haifeshi amma yanzu suna nan haka ko gurin Janbulo ne, ya ce da ɗan gidan sa a gurin da ya gina suna zaune da mahaifiyar sa. Kuma yace a kwari yake tsaron shagon wani mai gidansa, amma yace asali su 'yan Gaya ne. Umma ta ce "To, Allah ya daidaita su.
Ni dai bance komai ba,mutumin ya maƙale a zuciyata duk yadda na auno matsaloli sai zuciyata ta kawo wani uzri ta wanke shi. Haka nan har naje makaranta na dawo ina tunanin Aliyu Shamaki.
Da dare muna 'yar hira da Umma, ta tambaye ni da cewa "Ni ko Baby mutumin nan ya yi miki kina ganin cewa zaki iya aurenshi?" Na ce to Amma Ni dai ina ta waswasi. "Game da me?" Ta katse ni da tambaya. Na ce aurensa uku duk sun rabu da matan, 'yayansa uku duka mata kuma duka sunan mahaifiyarsa ya saka, sai ina jin tsoro ko mahaifiyarsa ce bata barin matan. Umma tace "Karki fara lamarinki da zargi, tabbas dole ki damu game da rabuwa da matansa, shawarar da zan baki shine ki sa hankalin ki sosai ki gano raunisa da fushin sa, ta haka zaki iya samun zaman lafiya da shi. Baby a irin tarbiyyar da nake baku ina sa rai ko mutum yana fidda wuta ta baki dan bala'i za ki iya zama dashi, haka duk wata kissa ko kisisina, ko shirka bai kamata kiji ɗarba." Na yi 'yar dariya haka ne Umma.
wayar Umma ta yi ringin Jamila tace Yaya Baby lambar jiya ce da kika ajiye. Gabana ya faɗi harda juyawar ciki,take naji banɗaki kawai na ke son shiga. Na amshi wayar na shige ɗakin Umma ina jinshi yana sallama, sai da na zauna sannan na amsa sallamar da wata murya da bansan ina da itaba. Na gaida shi,ya amsa na tambayi Hajiya da yara,yace duk suna lafiya. Yace, "Shine ko ki kira ni kiji ya naje gida jiya." Na ce to kayi haƙuri amma gaskiya na so in kira ka sai kuma na yi tunanin kar kana kan Kekenka kuma in tsaida kai, har kuma bacci ya ɗauke ni. Ya numfasa "To na amshi uzrin ki, amma ya kike gani zuwa yanzu a zuciyarki ta kuwa fara sona?" Na kwanta tare da ƙara manna wayar a kunnena. Ba zan iya tabbatar da haha ba Yaya,sai dai ka faɗamin yaya son ya ke ko zan gane.
Ya yi yar dariya. "Bani labarin bayan rabuwa kin tuna da ni? Sau nawa? Kina tuna hirar mu? Wacce a ciki?" Na numfasa, gaskiya na tuna ka sosai amma ban lissafa dadin ba. A hirar mu dai nafi tuna batun auren ka guda uku,sai in ji fargaba. Yace, "Alhamdulillah Baby kin fara so na, karki damu da maganar matan da na rabu da su, ko tunanin dalilin rayuwar mu, zai fi kyau ki maida hankalin ki akan irin rayuwar auren da za mu yi. Zanzo gobe,ki tanadi labari mai daɗi da za ki bani." Nace,to Insha Allahu Allah ya taimaka a gaida Hajiya. "Zan faɗa mata." "Yaran ki fa?" Cikin sauri na ce agaida min su don Allah, koda bansan sunayen su ba. Ya ce "Haka ne ban faɗa miki ba, dukansu sunansu Zeena." Kamar yaya na tambaye shi cikin rashin fahimta. Yace Ƙwarai kuwa duk sunan Hajiya suka ci, amma kowace da laƙaninta Babbar Meema, mai binmata Mubina sai ƙaramar su Anisa." Na sauke ajiyar zuciya, gaskiya abin ya birge ni kuma har naji ina son in gansu. "Karki damu ke da 'ya'yanki kuma ke ma zaki haifa mana wata Zeena ɗin ko?" Kunya ta sa na yi saurin faɗin sai da safe, na kashe wayar sannan na yi rigingine a gadon ina jin farin ciki gami da fargaba. Dole in yi magana da Umma.
Kamar kullum ya zauna a gefe yana jan carbi yana jiran Hajiya ta gama addu'o'inta kafin ya gaida ita kuma su yi 'yar hirar da suka saba. Bayan ta kammala suka shafa tare, ya matsa gabanta sosai ya rusuna ya gaishe ta. Ta amsa tare da kai hannu ta shafa masa kai tana faɗin "Allah ya albarkaci rayuwarka, da ta 'ya'yanka, ya yi albarka a cikin neman ka, ya albarkaci abinda zaka samu. Allah ya tsare ka daga dukkan sharri mutum ko Aljan da duk wani abinƙi." Shi kuwa yana ta maimaita ameen. Bayan sun kammala sai ta gyara zama sannan ta ce, "Jiya Maman sani ta zo game da maganar abincin sadaka na ranar juma 'a wasu abubuwa sun ƙare, na ce ta lissafi kamar yadda aka saba, kuma ina son wannan karon za'a saka sunan mutum ɗari a kayan salla yara marayu, sai mu ba Zeena Foundation dama su nemo yaran da suke dace da buƙatar tallafin nan a ba su. sannan ɓangare kayan ɗaki Amina ta. Kawo sunan mutum biyu kuma sun gama bincike tabbas yaran mabuƙata ne duk marayu ne na ce taje gandu su yi magana a Zeena funitures da manajan kamar dai kowane lokaci. Ya ƙara yin ƙasa da kai cikin girmamawa to Hajiya duk yadda ki kayi dai-dai ne. Ta dubi fuskar shi, "Baka sanar da ni ko ka tattauna da yarinyar nan ba." Eh na samu ganin mahaifinta kamar yadda ki ka bani shawara, kuma ya min 'yan tambayoyi kafin daga bisani ya shiga ya turota. "Kamar wace tambaya ya yi maka?" E ya tambayi unguwarmu sannan ya tambaye ni game da addini da sana'a da aƙida. Ya gamsu duk da ce masa da na yi ni yaron shago ne, yace buƙatar kawai ace da sana'ar komi ƙanƙatar ta Allah shine mai buɗawa in yi magana da ita in har mun sasanta ya bani ita. Hajiya ta ɗan yi jim,sannan ta ce, "Mecece hikimarka ta ɓoye matsayinka? Ya gyara zama, Hajiya ina son in samu soyayya ta tsakani da Allah bata abin hannu na ba, ina son in shimfiɗa sabuwar rayuwa ba irin ta baya ba." Ta yi ɗan murmushi cikin ƙasaita ta ce "Wannan yaro na ne, tabbas akwai hikima cikin abinda za ka yi. Na amince da haka, to ita yarinyar ta karɓe ka ya kuka yi?". Ya sunkuyar da kai,to har yanzu dai ban same ta sosai ba, na yi mata uzri yarinya ce sosai yanzu ne zata gama Sakandire su za suyi sauka a Islamiyyar su, haka nan kuma ni ne saurayin ta na farko. To ta kasa gane ko tana sona. Hajiya ta yi hiru cikin nazari, sannan ta ce Allah ya zaɓa mana abinda yafi zama alkhairi, za mu ci gaba da addu'a." Ya ce Ameen ina godiya sosai. Haka suka kasance cikin tattaunawa har zuwa lokacin da Juma ta shigo ta na jera flas na ƙosai da hankali da wainar ƙwai da na ruwan zafi ga kunun gyaɗa ga kuma kayan shayi. Shamaki da kansa ya Haɗawa Hajiya Shayi mai kauri kamar yadda ta buƙata, ya shirya mata komai sannan ya saka abinda kanshi ke so ya shiga ci suna ƙara tattaunawa.
🖊️🖊️🖊️
[3/16, 13:07] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu 600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank ko Katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
Mamakin kansa ya ke yadda ya ƙosa dare ya yi yawan murmushin da ya ke in ya yi shiru ya sa yaran kantin suka soma tsegumin cewa maigida ya faɗa soyayya, musun da suka yi ya sa ɗaya daga cikin yaran mai suna Ɗahiru ya ce bari ya gwada shi. inhar haka ne zai gane. Ya kunna waƙar Hamisu Breaker ta soyayya. Yaje ya zauna a bakin Office ɗin yana ci gaba da shi'anin gaban sa. Daga ciki kuwa Shamaki ya yi tsam da ransa yana sauraron yadda mawaƙin ke yin falsafa akan so, sai kawai ya ƙwala wa Ɗahiru kira, ya amsa ya shigo cikin girmamawa yace "Gani Alhaji." Wai ku bakwa rabo da jin wakane duk da ita wannan naji ta yi daɗi da ma 'ana, amma waye ya yi ta ne, tura min ita a waccan wayar in yi wani nazari a kanta. Ya ɗauki wayar ya fita yaje yana basu labari suna dariya. Ranar haka ya yini jin waƙar. Da yamma ya kira Malam Bala direbansa ya ce a wanke mota zai fita bayan Isha'i. ya kuma fara lissafin zai bi ta Zeena Store ya kwashi alawoyi yaje Zeena Factory ya haɗa mata kayan ƙwalam na Snacks. Kamanta gurin wa zaka kuma wane matsayin kake a idon ta? Zuciyarsa ta jeho masa tambaya. ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya ce sai dai in nemi ɗata ko yalo? Ɗan tsaki ya saki sannan ya yi maganar da ƙarfi Ayaba da Lemo zan siya. Hassan dake cikin Office ɗin yana rubuta wani rasit ya ce "Karɓo wa za ayi Alhaji?" Ya dubi Hassan me nace? Yace,"Naji kana maganar Ayaba da Lemo." Ya yi ɗan tsaki eh da za a karɓo ne amma bari sai na fita sai in siya kawai.
Nikam kafin Isha'i na shirya tsaf, ba sallah zan yi ba don haka na kame ina jiran zuwansa, gabana kuwa sai faɗuwa yake ina ayyana yadda zanji idan mun kasance muna hira,ina ta baiwa kaina shawarar ya kamata ace ina zaɓo kalamai inzan furta masa,sannan kuma kar inyi masa magana da irin muryar da nake yi wa kowa hakan zai sa in ƙara birge shi. Take na gamsu da hakan,kuma na yarda shi na musamman ne.
Shamaki ya wahala kafin ya samu kayan da za su nuna shi a talaka,suma dai yadine fari mara nauyi, yanada mugun tsada amma ba kowa zai iya gane hakan ba sai wanda ya san kaya. Ya zube wayoyinsa guda huɗu a kan gadonsa, sannan ya saka mai boturan wadda ya sawa sabon layi domin ita kaɗai a alajihu agogo da zobe na azurfa duk ya zube su. Ya nufi sashen Hajiya.
Ta ƙare masa kallo sanna ta amsa gaisuwarsa. Ya ce zanje gurin Rabi a ne kamar yadda na sanar da ke tun shekaran Jiya. Ta ce "Na fahimta,kaje Allah ya bada nasara,kuma ka ce ina gaisheta. Sannan ka tabbata ka sami zuciyarta a yau,domin na lura kana matuƙar sonta. Allah ya yi muku albarka gabaɗayan ku." Ya ce Ameen sannan ya miƙe ya fice da sauri. Ta bishi da kallo a fili ta furta akwai matsala ya kamu da yawa, ni da nafi son ya samo wadda ta fi son sa dole inyi wani abu.
Ya dubi Malam Bala yace, in ka isa gurin masu Lemo na ɓawo za ka karɓo. Da suka isa ya rasa na nawa ya kamata ya siya yace Malam Bala ga dubu biyar su yi kashi biyu. Da aka kawo ya ga da yawa yace Malam Bala ka dauki kashi ɗaya. Sai da suka gota lungun sannan ya sauka,yace ka je zan kira ka nan da awa biyu. Ya taka da ledoji biyu a hannunsa ya dawo ya shiga lungu.
Jafar ya shigo da ledoji suna rinjayarsa, yace Umma wai gashi inji wani mutum wai yace Yaya Baby taje. Cikina ya juya da sauri na ɗauki buta zan shiga banɗaki, Umma ta ce "Ke dakata lafiyarki da tun ɗazu kuna zaune sai da yazo zaki tarki shiga banɗaki?" Nace wallahi Jafar yana faɗa sai naji cikina ya juya, na shige da sauri. Ina jiyo Jamila tana tsaki tana mitar "Yanzu da wari zaki gunsa?" Na fito na sake shafa turare sannan na fita na samu har Jamila ta shinfiɗa masa tabarma ta aje masa ruwan fiyawata.
Cikin girmamawa na gaida shi, na kuma tambayi Hajiya da yara. Yace tana gaida ni kuma duk suna lafiya. Nace shine harda wata ɗawainiya haka? Ni fa karka matsawa kanka a irin wannan yanayin ba sai ka min wata ɗawainiya ba. Ya ce "Karki damu, ina da halin yin hakan ne, yanzu ki bani labarin soyayyata. Na ƙosa mu soma musayar ta ni da ke, domin har na soma zama wawa ina kasa jurewa tunaninki." Nace koda bansan so ba, na tantance kai na musamman ne, duk wani kai kawo nawa kana zuciyata kuma na kasa gano aibunka, zuciyata tana faɗa min cewa in maka uzri kuma in amince ka zama mijina. Na gamsu sosai da shawarar zuciyata kuma na amince ka zama mijina in ina gidanka sai ka koya min soyayyarka. Na kai ƙarshen maganar tare da rufe ido. Ya ce "Alhamdulillah wannan yanayin da ki ke ji shima alamun so ne Baby, yanzu sai mu yi maganar aure, zuwa wane lokacin ya kamata mu zama miji da mata?" Nace ai wanna da su Abba zaku yi magana. Ya numfasa "An saka ranar da zakuyi walimar sauka?" Nace har an fitar da katin manyan baƙi an raba tun wancan satin. Na mu sai wannan satin insha Allahu zan baka ina fatan zaka zo ka ga karatunmu? Ya ce "Ai ina tunanin a haɗa bikinmu da saukar ki... Kai! Na katse shi. Na yi ƙasa da murya. Saura sati biyar fa ayi walimarmu yaushe aka shirya? Ya numfasa "Wane irin shiri kike magana a kai?" Na sunkuyar da kai, yaushe ka kawo kuɗi har aka sa rana, kuma ga maganar lefe su Abbanmu ga maganar kayan ɗaki abin da za a ci abiki, kaga duk abin dubawa ne. Yace "Kinyi gaskiya, amma zan ɗauki wani kuɗin dashi na zan bada kuɗi cikin satin nan a kawo dubu hamsin, sannan nasan dai ko ba lefe zaki aure ni ko?" Har a zuciyata zan iya hakan Yaya, sai dai matsalar iyayena basu da halin yimin kayan ɗaki a cikin wata guda, yanzu ma suna ta abinda zasu fiddani kunyar walimar saukar nan da zamuyi. Yace to ke da me za kuyi a saukar? Nace walima ce kawai a gida, ya ce nawa zaki kashe... Na katse shi da A a bazan ɗora maka nauyi ba, kar ka rene ni da haka, kabari in saba da yanayinka na asali,ka koya min yadda zamu rayu a lokutan akwai ko na babu. Ya ɗaga hannunshi ɗaya tare da faɗin kinga dakata kiji. "Inada shine shiyasa, kuma ba roƙona ki ka yi ba, kawai ki faɗa min nawa zai ishe ki ko inje in ɗauki kuɗin da zan kawo miki na aure inyi gaban kai na da su.". Na ce Umma za su min faɗa, duka yau ne zuwan ka na biyu fa, kuma... "Kuma me?" Nace shike nan dubu uku ne. Ya ce "To zan baki sai kuma me?" Na ce shike nan. Yace "Ankon walima da hijabi Lemo da kalanda kinsan dai nima na taɓa saukar nan nasan ya ake yi. Na ce ai duk Abba da Umma sun sai min. Ya ce to shike nan zan kawo miki dubu uku jibi mu koma kan maganarmu in turo a kawo kuɗin ko?"Nace bari in faɗawa su Umma, yace don Allah da kin shiga ki sanar musu,kuma zan kira komai dare yau inji ko sun amince." Na ce to shike nan, amma nima zan nemi wata alfarma a gurinka. Ya tattaro hankalinsa gurina "Faɗi da sauri in har zan iya kin samu." Ina son in ci gaba da karatu ko da makarantar koyon aikin jinya ne. Ya yi shiru can yace "Bazan miki alƙawari ba,saboda wasu dalilai amma mu aje maganar zuwa gaba." Nace to shike nan. Ya kwai kwayi muryata "Na gode Babyna." Na sa hannu na rufe fuska ta. Yace to bari in tafi, nace yau naga baka zo da Kekenka ba? Ya ce tayar ce ta yi faci ɗazu ina hanyar dawo wa daga kasuwa, na ce to Allah ya tsare ya ce "Ameen muka yi sallama cikin shauƙi da ƙauna.
Na samu Abba yana ta faɗa wai ko dai nice nace wa Aliyu zan sha Lemo domin yaran zamani ba abin yarda bane. Na zauna na ce Abba wallahi ban roƙeshi ba yanzu ma dan baku san ya mu ka yi da shi ba ne, cewa ya yi in faɗa masa abinda zan kashe a walima lokacin sauka zai bani kuɗin nace a a ya bari shine ya ji haushi. Umma tace "Abban Baby na faɗa maka ko Jamila bazata yi roƙo ba, bare kuma Baby, duk da ba 'a shedar 'yan zamani akwai abinda zaka shedi ɗanka dashi, yace "To Allah ya muku albarka dukanku har da ke Ummar ta su,domin tarbiyyar ki ce, shi kuma Allah ya saka masa da alkhairi ya jiƙan magabata." Muka ce Ameen ya ce "To sai a yanka aba kowa, ku rage akai gidan Yaya ba ma ci mu kaɗai ba." Jamila ce me yankawa Ni kuma na yi zugum ina tunanin ta ina zan fara sanar da iyayena saƙon shi. Umma ta ce, lafiya ke kuma ai Abban na ku ya gane ba roƙarsa aka yi ba. Nace ba wannan ba ne, haka ya ce wai a satin nan za a kawo kuɗi, kuma wai in kun yarda za a yi biki tare da walimar saukarmu... Tarin Umma ya sa nayi shiru ta ƙware da ayabar da ta ke ci, na tashi da sauri na kawo mata ruwa ina yi mata sannu.Abba ya taso shima cikin sauri yana mata sannu. Bayan ta samu kanta tana maida numfashi tana magana, "Baza a yi gaggawa ba gaskiya sai anyi bincike, kuma bamu da halin biki a wata ɗaya." Abba ya ce ki daina magana kin ƙware ki yi shiru tukunna. Sai da ta samu natsuwa sannan Abba ya ce, "Inda haka zata samu zanfi kowa murna ace na aurar da Baby a ranar saukar ta. To amma hidimar da yawa ga haihuwarki ko yau ko gabe." Umma tace, ta haihuwa mai sauƙi ne, ba taron suna zanyi ba Allah dai ya sauke ni lafiya. Abba ya ce "Ameen, dama tun farko ya faɗa min aure ya zo, sannan ya taɓa aure kinga dole ya buƙaci aure da wuri, ina ga abinda za a yi mu amince su fara kawo kuɗin sai mu yi maganar da ta dace." Umma ta ce to shikenan ke sai ki faɗa masa in yazo. Na sunkuyar da kai na ce yace infaɗa masa a waya zai kira a ta Umma in yaje gida. Abba ya ce to. Sai ki sanar dashi. Da wayar Umma na shiga ɗakinmu ina ta jiran kiransa har bacci ya kwashe ni.
Shamaki ya ƙosa ƙwarai ya sallami mutanan da yakan gansu in an idar da sallar Isha'i, suka tsare shi, yana sauraron buƙatunsu wanda zai yi a gurin kamar kuɗi marasa yawa ya basu wanda sai ya tura su je Zeena Foundation sai ya tura su. Ya ƙagara sosai dan tun jiya ya so jin yadda Baby suka yi da mahaifanta, amma da yaga dare ya yi sai ya barwa yau. Ya dubi Malam Sabitu wanda shi ne limamin masallacinsu da ke jikin gidansu ya ce, Malam zan shiga gidan gobe zan baka kati ka ba mutumin sai a kaishi Zeena Hospital za su min magana game da abinda za' a biya. Ya ce "To Allaji Allah ya ƙara arziƙi muna godiya." Shamaki cikin ƙosawa ya ce ba komai, Malam Aba sauran jama'a haƙuri ina da uzri a ciki. Liman ya ce "To insha Allahu Ubangiji ya rufa asiri."
Kamar ya wuce amma dole ya shiga gurin Hajiya, tana lazimi, Azima tana gefe tana jira ta kammala dan ta mirza mata manta na ƙafa. Ya zauna shima yana jira, zuciyarsa ta tafi matuƙa ga tunanin Baby, nan da wata ɗaya tana gidansa zai bata rayuwa mai kyau, zai maida ita sarauniyar shi.,.. Yaya Shamaki! Muryar Azima ya ji ta kira sunan shi da ƙarfi, a firgice ya waiga ya dube ta tare da faɗin Baby lafiya?" Sai kuma ya dawo cikin hayyacinsa ya dubi Hajiya wadda ta tsare shi da ido, yace sannunku Hajiya. Bata amsa ba sai ta kalli Azima tace je ki dawo. Ta maido duban ta gare shi, "Aliyu." Ta ambaci sunan sa, ya ɗan zaro ido kafin ya zabura ya amsa da cewa na am Hajiya. Cike da Tsoro ya ke Domin a duk ranar da ta ambaci sunansa to ya tabbatar ranar ya kai maƙura gurin ɓata mata rai. Ta numfasa "Faɗa min tunanin me ka ke yi?" Yace ba wani abu bane waya nace wa yarinyar nan zan mata tun jiya to ban samu na cika alƙawarin ba. Ta nuna shi da yatsa shi yasa ka shigo gida da wuri ba domin ka gama jin matsalolin mutanan da ke da buƙata a gurinka ba? Ni kuma ka zo ka tasani ka faɗa kogin tunani, to in na janye amincewa ta da wannan yarinyar ya zaka yi kenan?" Gaban shi ya yi mummunar faɗuwa cikin sauri yace, Nasan baza kiyi haka ba Hajiya! Ta kuma zaro ido cike da mamaki, abinda ta tsammani zataji shine Duk yadda ki ka yi daidai Hajiya. Ta lumshe ido cike da damuwa, can ta ce "Shikenan yau nasan baza muci abincin dare da kai ba,bare muyi wasu bayanai ko wani lissafi,ka tashi kaje ka yi wayar." Ya san gatse ta yi masa,dan haka sai ya ce, za muyi lissafi Hajiya, abincin ne yau cikina duk a cushe ya ke. Ta kuma yin shiru tabbas ko ita yau abincin nan ba zai ciyu a gareta ba, ta numfasa sannan ta kai hannu ta ɗauki wayar ta a gefe ta shiga neman Hassan. Ya ɗauka cikin girmamawa suka gaisa, ta ce dama zan tambaye ka yau da aka kawo abinci kasuwa Shamaki ya ci Hassan ya ce "A'a kayan marmari ya ci sosai yau." Ta ce to na gode. Ta sake maida kallon ta ga Shamaki, tashi kaje za muyi magana da safe, yanzu kam bana zaton kana iya fahimtar duk abin da zan ce maka." Ya ce haba dai Hajiya karki tashi hankalin ki, wallahi abin ba kamar yadda ki ka zata bane. Ta nuna masa hanyar sashensa "Je ka yi waya." Tsam ya miƙe cikin sanyin jiki ya ɗan kuma risnawa tare da faɗin mu tashi lafiya Hajiya Allah ya huci zuciyarku. "Allah ya maka albarka." Ta furta cikin kallon gefe. Ya tafi ta bishi da kallo ranta ya sosu ƙwarai in da ne Shamaki ba zai tafi ba da tace ya tafi, zai tsugunna ne yana bata haƙuri ƙilama sai ya zubar da hawaye har sai ta huce, sannan zai ci abincin ko da baya jin yunwa,haka kuma za suyi lissafin kamar yadda suka saba. Lallai dole ta ɗauki dukkan mataki kafin abin ya wuce gona da iri, ta koma ta jingina sannan ta ɗauki waya ɗaya a cikin wayoyinta. Ta danna kira, suka gaisa da malamin wanda shine yake taya su da addu'o'in neman tsari da samun kariya. Ta ce Malam akwai wata matsala da ta soma tunkarowa cikin ahalina yaron nan Shamaki ya faɗa soyayya da wata yarinya, yadda ya koma kamar wawa abin ya tsorata ni. Ina son amin bincike shin ba wani abu yarinyar ta yi masa ba! Kuma tsakaninsu ina son in sani akwai alkhairi ma kuwa!Malam yace "Insha Allahu Hajiya za kiji sakamako zuwa gobe, za ayi bincike sosai zamu iya samun sunan yarinyar?" Hajiya ta ɗanyi shiru sannan ta ce ina zuwa. Ta katse layin ta soma kiran wayar Shamaki, ya gama shirin kwanciya kenan yana ta sauri dan ya kira masoyiyarsa, cikin sauri ya ɗaga kiran Hajiya gaban shi yana faɗuwa. Tace "Ya sunan yarinyar da kake so?" Cikin sauri yace Baby Amira ko Rabi atu duka suna kiranta da shi. Ta kashe layin ba tare da tace komai ba. Sai da ya gama komai sannan Ya danna kiran layin wayar mahaifiyar ta sannan ya kwanta a kan tsakiyar gadonsa ƙafafun sa na ƙasa.
Na jigata sosai da tunanin abinda ya hana Yaya Aliyu kira na, sai naji kamar in kira shi sai kuma wata zuciyar ta hane ni,har na kasa cin abinci a yinin na kuma shiga kaiwa Allah kuka in har da akwai matsala ina roƙon Ubangiji ya kauda matsalar, yanzu kam na samu tabbacin cewa ina son Aliyu har lokacin da muka je makwanci banji sautin wayar Umma ba, na sadaƙar cewa ya canza ra'ayi. Ƙarar kiɗan Nokia ya tashe ni zaune, na kasa kunne inji ko Umma zata kira ni, har kiran ya yanke, na tashi da sauri na fita, daidai lokacin da wayar ta sake daukan kiɗan na yi sallama a ƙofar ɗakin ba a amsa ba, na shiga Umma bacci ta ke wayar na caji Abba kuma bai shigo ba, na ɗauki wayar da sauri na nufi ɗakin mu ta kuma katsewa kafin in ɗaga, na fara danna lambobin cin bashi amma sai kira ya ƙara katse hakan, da sauri na faɗa kan lamammiyar katifar sannan na manna wayar a kunne tare da sallama. Ya amsa tare da tambayar ko dai har na yi bacci? Na ce masa e bacci ya fara ɗauka na. Ya ce "Ki min afwa abubuwa sun sha kaina ban kira ba kamar yadda na yi alƙawari." Na sauke numfashi hakan kuwa ya yi matuƙar ɗaga hankali na, na yini a damuwa ko dai ba lafiya ne, in kuma na yi kamar in kira ka, sai zuciyata ta faɗa min cewa in kana cikin wani uzri fa, yanzu dai da tunanin haka na kwanta. "Alhamdulillah! Ina da tabbacin kina so na a yanzu, kuma naji daɗi dan Allah karki dinga ɓoye min duk yadda ki ka ji a kaina ko daɗi ko akasin haka ina son wannan kinji Baby?" Nace To zan ke faɗa maka Yaya. ya ce "Yanzu faɗa min ya kuka yi da su Umma?" Na ce sun amince ka kawo kuɗi amma kamar yadda na faɗa maka baza su amince da auren lokacin walimar saukarmu ba, domin yanayi,kuma kai ma bana son ka takura kanka, kuma malamai suna cewa gaggawa yawancin ta daga sheɗan ne, abi a sannu. Ya numfasa "Gaskiya kika faɗa Rabi'atu amma ina son ki gane wani abu, na taɓa aure nasan daɗin shi kuma ina buƙatar shi. Bazan jure dogon zama ba, tunda har zaki iya sadaukarwa game da lefe, me zai hana ni ba zan sadaukar game da kayan ɗaki ba. Ko ba domin ni za ayi ba?" Na ce domin kai za 'ayi mana,amma kasan mutane akwai su da munafinci sosai za ayi ta gulma cewa ko kayan ɗaki iyayena ba su sai min ba. Lefe kuwa zamu iya cewa ankai ajiya. Yayi murmushi mai sauti, "Gadon ma sai muce kafinta bai gama ba." Ya faɗa cikin yanayin nishaɗi. Na ce in har su Umma za su yarda da haka ni bani da matsala kaine abinji nan katifar da nake kwance da kaɗan ta fi tabarmar kauri. Ya saki dariyar da sai kuma naji kunya ta kamani. Yace "Ina da katifa babba kuma Hajiyata ta na da tukunyar girki dan haka ni matata kawai na ke buƙata." Wani daɗi ya tsirga min da ya ambace ni da matarsa. Allah ya nuna min na faɗa a zuci, "Ameen Babyna." Nace kai araina nayi addu'arfa. Yayi "yar dariya,araina na amsa fa ke ma kinji ne?" Nace e mana, yace "A lallai mu na musamman ne gaskiya kunnuwanmu suna iya sauraron abinda zukatanmu suke faɗa kenan gaskiya mu gode wa Allah. Yawwa Baby in tambaye ki wani abu?" Na lumshe ido na sake yin ƙasa da murya domin bacci yana ɗan bibiyata. Na ce tambayi ko me ka ke so. "Zaki iya zama da uwar miji?" Cikin sauri na wartsake, a son zuciyarta shi ne 'a 'a bisa ga yadda na ga Umma tana fama da kiyayyar dangi Abba, kuma ta bamu labarin abin ya fara ne tun daga tsanar da mahaifiyar Abba tayi mata kafin ta rasu. "Kinyi shiru Baby." Yafaɗa da sanyi jiki. Nace mamaki na ke yi da wannan tambayar kuma ina nazarin dalilin yinta. Yace "Kar ki damu da dalili, ki faɗa min me kike mamaki." Nace to ya zaka tambaye ni cewa zan iya zama da mahaifiyar da ta haife ni? Na marairaice murya ina magana cikin yanayi shagwaɓa. Yaya in har yadda nake jin ka a zuciya shine so to tayaya Mahaifiyar ka baza ta zama tawa ba? Sannan in har wani zai tambaye ni cewa zan iya zama da mahaifiyata me zai hana in so jin dalilinsa cikin mamakina? Ya yi shiru Yarinyar ta gama gigita shi ta sukurkuta shi,dan haka ya fara da faɗin "kiyi haƙuri Babyna nasan mata da yawa suna gudun zama da Uwar miji wannan shine farkon matsala ta da matata ta fari Maman Meema, amma ba wai dan wani abu na yi wannan maganar ba." Nayi ɗan murmushi domin ganin na soma gano wasu abubuwa game dashi, kuma rauninsa ba zai min wahalar ganewa ba. Ya katse ni da cewa "Kin lashe babbar jarabawar da na fara miki kuma zan turo ranar Lahadi ni kuma zanzo jibi in kawo miki dubunki uku ta walima." Ba gobe kace min ba a jiya? Na katse shi, Ni ba damuwata kuɗin ba domin sai da na sha faɗa akan Lemon da ka kawo jiya, Abba yana zargin ko dai roƙon ka na yi ka siya min, Ni kuwa ina jin daɗin hirar da kai ne kawai ina son in ganni gani ga ka." Ya katse ni da cewa "Alhamdulillah na ci nasara Baby wallahi kin kamu da sona Baby dan Allah ki furta ki ce Aliyu ina sonka dan Allah! Ki faɗa inji." Na sunne kaina cikin ɗan yamusashshen filo na Na ce wayyo Allah Yaya kamin afwa zan faɗa maka amma banda yanzu. Ciki shagwaɓa yace haba Babyna." Gyaran muryar Abbanmu naji banji sallamar shi ba, nasan zai zo ne ya duba mu kamar yadda ya saba,don haka sai nace Yaya Abba ya shigo sai goben ka yi haƙuri, na kashe wayar ya taɓa ƙofar na yi laf, ya haska sannan ya yi addu'a ya tofa gabas da yamma kudu da arewa na ɗakin, sannan ya ja ƙofar ya fita.
🖊️🖊️🖊️
[3/16, 13:07] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Free Page 4*
Ta amsa gaisuwarsa tamkar ba wani abu, suka ci gaba da lissafin da ya kamata ace sun yi a jiya. Ya saki jiki ya karya duk da ta gano cewa ya yi ne domin ta huce daga saɓa matan da take ganin ya yi, amma ta ji daɗin hakan. Ya so matuƙa ta tambaye shi wani abu game da Baby domin ya faɗa mata yana son a tura a cikin satin amma ta ƙi maganar sam,wanda hakan ya sa dole ya bari sai zuwa yamma, duk da tana son taji yadda suke ciki amma ta bari sai ta ji daga Malam. Su Meema suka shigo da gudu duk suka nufi Hajiya suka tsugunna suka gaisheta, ta shafa kansu tare da yi musu addu'o'in da ta saba,sannan suka nufi jikin Dadin su suka gaida shi,ya amsa tare da sa musu albarka Rahin ta fito da kwandunan su da jakunkuna Azima ta kama musu hannu suka wuce suna ɗagawa Dadinsu da kakarsu hannu. Shamaki ya sallami Hajiya ya koma ɗaki don ya shirya ya fita kasuwa. Komai ya ke yana tuna Baby so biyu yana ɗaukar wayar sai ya danna kiran layin Umman su sai kuma ya katse. Ana ukun ya jure tayi ta ringin aka ɗaga tare da sallama. Ya amsa Umma ce, ya gaida ta cikin ladabi, ta amsa cike da jin kunya.ta ce "Sun tafi makaranta kasan ita jarabawa ta ke yi ta fita." Ya ce e ta faɗa min Umma, Allah ya bada nasara, dama na kira ta ne mu gaisa a gaishe su. Umma ta ce "Ba komai a gaida magabatan da kyau don Allah" Yace za suji, ya kashe wayar ya shirya ya fita. Hajiya tun tana sallar walaha wayarta ke ƙara, sai da ta idar ta yi addu'a sannan ta miƙa hannu ta ɗakko wayar Malam ne,don haka sai ta danna kiran shi,ya ɗauka suka gaisa ta tambaye shi abinda ya fuskanta game da binciken, yace "To alal haƙiƙa Hajiya abinda na gani shine, abu na farko dai aure babu fashi, abu na biyu kuma taurarin yarinyar masu haske ne sosai tana tare da arziƙi irin su ko matsiyaci suka aura albarkacin su yana ganin faraga, mai arziƙi kuma tamkar wuta ce sai a zuba mata fetur a bin nufi akwai alkhairi tare da ita,abu na uku Allah ya ɓoye min ban fuskance shiba amma shima ina zaton alkhairi ne,sannan yana sonta sosai irin wanda in ya rasata zai cutu kuma irin wannan son ba zai taɓa ganin aibunta ba ko da ita bata son shi. Wannan sune abubuwan da na gani." Hajiya ta sauke ajiyar zuciya ta ce Malam kuma an bincika ba wani asiri ta yi masa ba? Malam yace "Abinda na fara dubawa kenan ita yarinya komai nata a rufe ya ke abin nufi bata taɓa ziyarar wani malami ba domin wani aiki. Sam babu kuma wata niyya ta cutar da shi ko kaɗan." Hajiya ta sauke ajiyar zuciya,shike nan Malam a tayamu da addu'a ita ma ta kamu da son shi fiye da wanda yake mata, yace "Wannan mai sauƙi ne in har za taci abin da zan kawo." Hajiya tace ina zan ganta har wani taci wani abu? Amma ka kawo ɗin sai muga ya za ayi. Yayi yar dariya "Hajiya ko gida zaku iya aikawa,kuma koda kowa yaci bazai yi aiki akan saba sai ita da akayi da sunanta sai dai matsalar in har wata mai irin sunanta ta ci to ita ma zata kamuwa da sonsa." Hajiya tace babu damuwa ka aiko ɗin zan san yadda za ayi amma shi abin menene? Yace,Dabino ne ƙwaya bakwai da za a samu ta ci duka zai wahala in bata zo ta tare a gidan ba kafin bikin kamar tai masa sujada haka zaki ga tana yi. Hajiya ta ce na gode sosai Suka yi sallama. Hajiya ta lushe ido ta nutsa cikin tunani, tabbas zata barshi ya auri yarinyar amma dole ta so shi da yawa domin bata buƙatar ta janye masa hankali. Duk da hakan kuma zata sa shi ya kawo mata yarinyar ta ga wace irin wayewa ce da ita wadda har ta ɗaukar masa hankalin yaro haka. Dole sai ta gano wasu abubuwa game da yarinyar domin ta saita mata sahunta don bata son rawar kai. Kuma ta gane ba a mulki sarakuna biyu aka karaga ɗaya. Sam bataji sallamar Anty Zainab ba sai gaisawa da taji suna yi da Juma. Ta buɗe ido ta kai kallo inda taji muryar Zainab ɗin, ta ɗago ta gyara zama tana faɗin yaushe kika shigo Maman Umar? Anty Zainab dake zaune can gefe cikin girmamawa tace "Naga kuna ɗan gyangyaɗi ne shiyasa na yi shiru." Ta gaida Hajiya cikin girmamawa. Hajiya tana tambayar yara, tace duk suna makaranta. Anty Zainab ta kira Juma tace ki zo ki ɗau ledar can ki wanko wa Hajiya tuffa da Inibi har gwabar da fiyar sai ki haɗo mata. Juma ta ɗauki ledar ta fita. Hajiya ta kalli babbar 'yartata tace Maman Umar Allah ya yi albarka har Fiya ta shigo kenan ta ce "Ta shigo nima jiya naje Store in duba jadawalin abinda ake buƙata shine naga sunsa harda Fiya a ɓangaren 'ya'yan itatuwa." Shine nace bari inje in duba miki a wani gurin." Hajiya ta ce Allah ya jiƙan mahaifinku. Zainab ta ce "Ameen Hajiya Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana. Sannan ta gyara zama ta ci gaba da magana. "Hajiya wata yarinya na gani na yiwa autanki shi'awa yarinyar tana da hankali sosai kuma tana da ilmi duka biyu,kuma iyayen ta dattawa ne, Babanta Farfesa ne a BUK." Hajiya ta ce,to ki kira shi ki faɗa masa in ya amince sai yaje ya ganta. Kira shi yanzu kiji amsar da zai baki.
Zainab ta kira wayar Shamaki na farko ta katse na biyu ya ɗauka tare da faɗin "Anty Maman Umar ya gida ya yara?" tace lafiya lau autan Hajiyarmu ƙaraminmu babbanmu. Suka yi 'yar dariya ya saba da wannan kirarin nasu, musamman tunda shike sa hannu a duk wani kuɗi in zai fita daga ko wane sashen ZEENA. Tace Shamaki mata na samo maka mai hankali,ga kyau 'yar gidan ilimi. Yayi 'yar dariya "Kin makara Anty,dan cikin satin nan za a kai kuɗina an bada ni Anty." ya kai ƙarshen maganar cikin tsokana. Ta ce bafa wasa nake ba, shima yace"Allah da gaske na ke yi kuma dama na daina auren haɗi abarni in gani da kai na." Tace shikenan amma duk da haka ka zo gidana zan sa a kira ta sai ka ganta,dama ban musu magana ba, bari na yi inji ta bakinka. Yace Ba sai na ganta ba, domin bazata kai Amira a komai ba, na gode da kulawa zanzo mu yi maganar yadda za a haɗa min lefe irin na yar manyan mutane,dattijai." Tace shike nan sai na jika suka yi sallama. Ta dubi Hajiya ,ashe ya samu? Hajiya ta ce shiyasa na ce ki kira shi,saboda wata irin soyayya naga ya fara mai ban tsoro ku taya shi da addu'a, bana son ya kawo macen da soyayyar ta zata kawo mana hari a cikin gidan nan, ina nufin ta yi amfani da hakan ta cutar damu, Shamaki shine jigon gidan kin san dai abinda nake nufi."Anty Zainab ta ce haka ne,to anyi bincike a unguwar su? Hajiya ta ce na kammala da duk wani bincike bana buƙatar inji me mutanen unguwarsu za su faɗa, yanzu kawai ina son ya dawo in faɗa masa,ya kawo min ita ne in yi mata jarabawar ƙarshe in ta haye shike nan in yana buƙata sati ɗaya kacal za a iya ɗaura musu aure in haka ya yi wa iyayenta. Zainab ta san Hajiya ta ƙare magana don haka ta ce Allah ya sanya alkhairi. Ameen Hajiya ta amsa tare da saka yankar fiya da aka jere mata a cikin tire. Anty Zainab ta tashi bari in shiga kicin ko akwai abinda zan iya ci a abincin gidan. Hajiya dai ta maida kanta ga TV inda wani malami ke nasiha ga 'yan mata masu fitowa suna fitsara a manhajar TikTok. Anty Zainab ta fito ɗauke da plate ta zubo kuskus ta kalli TV tace ai gaskiya yara suna fitsara a wannan TikTok ɗin. Hajiya ta ce "Wai Ni menene shi TikTok ɗinnan?" Zainab ta ɗakko wayarta tana nunawa Hajiya. Taga yadda 'yanmata kyawawa suke tallar tsiraici,da kuma yadda ƙananan yara da iyayen suke ɗora su suna maganganu na aure da haihuwa yaran da ko magana ba su gama iyawa ba. Hajiya ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Allah ya kyauta wannan zamani, to wannan me za a kira su,ta yaya ɗanka zaka bari ya auro maka irin wannan yarinyar ya kawo maka gidanka! Wannan dai na tabbata harga Allah dole ta juya namiji da iri wannan karuwancin,dan su mazan irin abinda suke so kenan."Anty Zainab ta ce Allah ya shirya mana zuri'a kuma akwai Malamai ma su wa'azi da masu tallata abubuwa. Hajiya ta ce Allah dai ya tsare mana zuri'a gaba ɗaya da duk ɗan musulmi baki ɗaya. Anty Zainab ta a amsa da ameen ta kama cin abincinta tabar Hajiya da tunanin dole ma ta ga yarinyar ko dai ita ma tana cikin masu irin wannan rawar.
Ƙarfe shidda mun taso daga makaranta ina tafe ina tunanin kayan da zan sa yau in Yaya Aliyu ya zo. Turus na yi a ƙofar gidanmu ganin shi tsaye da wani ɗan buhu a gefen sa,sai kuma na soma kallon jikina duk da kayan makaranta ne a jikina amma ba su da guga kuma ƙafata duk tayi ƙura. "Ya kika tsaya Baby ki ƙaraso mana. Ya yi kamar bai lura da abinda na yi ba. Nace Yaya bari in cire kayan makaranta. Yace "Karki damu ba ruwana da kayan jikinki, dama na zo ne don in ganki da yamma sosai, ido na ganin ido." Na ɗan haɗe fuska alamun fushi na ce amma sai ka faɗa min ko? Yace to kiyi haƙuri,kinfi kyau a hakanki na ɗaga ido ina kallon shi, yana 'yar dariya ashe harda haƙorin maka fari tas a bakinsa, inda akwai maza masu kyau to ba shakka za a saka Yaya Aliyu a ciki yana da tsawo da kuma 'yar ƙiba harma da wani ɗan tumbin irin na matasan masu kuɗi, tsarinsa ya min ƙwarai. Ya katse ni Kin gama nazarin nawa? Na?" Na ja hijabi na rufe fuska, sannan nace bari to in ɗakko tabarma. Yace a a nan zaki dawo kawai ki zauna ni kuma ina nan a tsaye, ba jimawa zanyi ba dan kar anjima banzo ba ki fara lissafa rashin cika alƙawarina. Zanje aiken maigidana, baya gari ni ke kula da buƙatun mahaifiyarsa." Nace gaskiya na amshi uzrinka babbane,lamarin amana sai masu gaskiya. Ya dube ni, "Har kin bani lambar gaskiya Baby to ina godiya Allah ya sa hakan na ke." Nace haka ne ma insha Allahu. Na isa inda ya nuna min na zauna daidai lokacin da su Jamila suka iso da su Jafar, suka gaida shi,sannan na basu jakata nace su shigarmin da ita ciki, ya nuna wa Jamila ɗan buhun da ya zo dashi ya ce "Zaki iya ɗauka?" Ta kalle ni, nace "Me ka kawo min Yaya zaka ja min faɗa. Ya ce "Ɗauki kinji, shinkafa ce kwano uku ba yawa ki yi girkin walima." Ta ɗauka tana masa godiya ta shiga, nace Allah ya saka da alkhairi Yaya. Ubangiji ya sa a mizani. Yace "Amin mata ta ina godiya." Fatin Maman Fati mai awara ta zo wucewa ta kalle ni ta kalli Yaya,sai ta ɗan taɓa baki ta wuce.Na kalli Yaya ko ya kula sai naga shi ni kawai yake kallo, na yi ɗan fari tare da faɗin ya dai Yaya? Ya yi murmushi bari inzo in tafi gida kar a kira magariba nace har zaka tafi, yanzu fa ka zo. "Ya yi ɗan murmushi sai kin min uzrin zuwa zance, yanzu kawai in zanzo zan kira ki, ya kamata in sai miki waya ko 'yar ƙarama ce." Nace kana ta ƙirƙiro kashe kuɗi don Allah ka barshi. Ya ce "To na bari, tashi ki shiga gida." Na miƙe ya ce "Ga dubu ukunki." Na mai da hannuwana baya na maƙe su, ka barshi ga shinkafa ka sai min. Ya ɗaure fuska sannan yace karɓa, da sauri na miƙa hannu biyu na risina na amsa ina ta godiya da addu'a. Yace shiga gida kawai, na wuce ina waiwayen shi.
🖊️🖊️🖊️
[3/16, 13:07] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Free Page 5*
Umma tana kaɗa miyar kuka ta bini da kallo, "Shine baki shigo gida ki sanar cewa kin dawo sannan ki canza kaya ki fita gunsa ba, sai kitsaya da kayan makaranta. Nace,to Umma ba zan sake ba amma cewa ya yi yana sauri. Naje na miƙa mata kuɗin da ya bani,ta amsa tare da faɗin "Wannan kuma na menene?" Nace wanda ya ce zai bani ne na walima. Umma tace "Ni Salmai wannan wane irin mutum ne ko sati guda fa ba kuyi da haduwa ba. Nace in na ce ya barshi sai ya haɗe rai. Jamila da ke alwalla tace, Umma kinsan wasu mutanan ma su yi ne, Yaya Baby ta yi dace. Umma ta ce "Allah ya zaɓa mafi alkhairi shinkafa 'yar gwamnati gata can amshi kuɗin nan ki kai ki adana a cikin wannan jakata. Allah ya sa kar Malam ya yi faɗa." Na ce to. Gaskiya na yi farin cikin ganin Yaya da rana, na ɗakko hodar Umma na kalli fuskata a madubi ko me yaya ya gani yake sona Ni ba dogo hanci ba, kuma ba manyan ido ba, amma ina da gashin gira sai ƙananan haƙora da kuma wushirya. Muryata ma ina jin ana fadinta, bazan ce komai ba game da surar jiki domin yanzu ne maƙerin ya ke ƙirar.
Shamaki ya yanke shawarar zuwa gurin Baby ne dan baya son Hajiya ta ci gaba da nuna damuwa tun a tashin farko. Ya fi son komai ayi cikin daɗin rai to kuwa dole ya danne zumuɗin shi game da Baby. Lokacin da ya shiga bayan ya kammala da mabuƙata suna cin abinci ta ji bai yi batun yarinyar ba sai ta ce, ɗazu Maman Umar ta ke faɗa min ta maka budurwa ko? Ya ce "Haka ta faɗa amma ta zo a makare, tunda mun gama magana da Baby har ta sanar da mahaifanta cewar zan turo, na ce a cikin satin nan in kun ga hakan ya dace." Hajiya ta yi shiru kamar bataji me ya ke faɗa ba, sai kusan minti biyu har ya gama yanke hukuncin bazata yi magana ba wanda yin hakan alamune na babbar matsala,sai yaji ta ce, "Yaushe za ka kawo ta in ƙara auna yiwuwar abin?" Ya ce yaushe ki ke so,amma ina tsoron ban jima da soma zuwa ba, iyayenta ba lallai su amince su barta ta zo ba. Sai dai zan jaraba yin magana da mahaifinta. Hajiya ta ce za a kai kuɗine bayan ta lashe jarabawar da zan yi mata. Shamaki ya kalli Hajiya sannan soma tunani wace jarabawar ita kuma za 'a yi mata?.
Jamila tana wanke wanke ni kuma ina wanke kayan su Jafar ina shanya yau asabar ce ba makaranta. Yaro ya shigo da sallama ya ce wai ana magana da Abbanku nace,ya tafi aiki. Jim ƙaɗan yaro ya zo Baby wai kizo a baki saƙo nace to.Nace inji wa? Yace wani mutumi ya fita. Na saka hijabi na fita zuciyata ta na zolayar wai ace inga Yaya. Me zai zo yi da safe nan. Tunanina ya tsaya cak, lokacin da mukayi ido huɗu da Yaya sanye da Jallabiya blue mai gajeran hannu sak irin alhazan birni idan ka kalleshi. Tsoro ya tsirga min me Yaya yazo yi yanzu? Ya katse ni da faɗin "Ƙaraso mana gurin Abba na zo ashe har ya fita?" Nace amma dai lafiya ko? Na tambaya idanu na ƙir a kansa. Yace "Lafiya ba lau ba." Na zaro idanu tare da faɗin Meyafaru. "Ƙara so mana Baby ." Na isa gurin shi a gigice,zuciyata na ayyana min yazo ya ba Abba haƙuri cewa aurenmu ba zai yi wu ba. Nace menene ban yi daidai ba Yaya?Wai kafasa ne? Yace "Mu fara da gaisuwa an tashi lafiya?" Nace lafiya ina kwana? Yace "Lafiya lau ya lura na fita hayyaci na yace "Ki daina damuwa ba wani abu bane, jiya da naje gurin maman Ogana shine ta ce tana son ta ganki wai yau ko gobe, ni kuma ina tunani nasan baza a barki kije ba,shine na zo in tambayi Abba da kai na, ko Allah zai sa ya yarda." Nace wai gaskiya ko da kuɗin ka a gidanmu hatta Umma baza ta bari ba bare kuma Abba, kan wannan maganar ma sai kaga an fasa auren nan,ka bata haƙuri kuma zata fahimta tunda itama Uwa ce kuma abinda ke faruwa a zamanin nan kowa ya sanshi.Kuma ka faɗa mata bamu daɗe ba.
Ya ɗan yi shiru, can ya ce "Baby akwai matsala ne, za a iya samun cikas in har baki je ba, saboda ita ta zata mun daɗe domin na jima ina ce mata ina da budurwa, kuma zata sanar da mai gida cewa ban kai ki ba, kuma maigidana shine jigon bikin nan,sai ki ga kan wannan yabar maganar nan inje ga wata to abin da nake tsoro kenan." Na zuba mishi ido cike da zargi,kodai cutar da ni zai yi ya dage haka,ƙila ma sai da yaga fitar Abbanmu sannan ya zo dan ya yaudare ni. Nace Humm Yaya ka yi haƙuri gaskiya ni kai na na soma zargin wani abu, dan Allah kar ka cutar da ni wallahi ina son ka da gaske... "Cutarwa kuma Amira? Me zai sa in cutar da ke kuma meye ribar hakan idan nayi? Ba ɗan iska bane ni ban taɓa zina ba ko lokacin da ina saurayi, kuma bazan fara a yanzu ba. Ko zan yi Baby ai ba zan yi da matar da zan aura ba." Na sauke lumfashi Yaya bazan hana zuciyata yin kowane irin hasashe ba,sai dai in ƙi gaskata abinda ta hasaso. Ka yi haƙuri ko ƙanwarka ce in ka mai da abin a kan ta zaka ga ba za ka amince da irin hakan ba. Ya sunkuyar da kai "Kin fini gaskiya ko ta wane fanni Baby amma taimakon da za kimin ciki harda sana'a ta. Mahaifiyar maigidana mace ce mai kirki da mutunci,ta ɗauke ni kamar ɗanta. To tana da irin nata ƙa'idojin dan Allah ki taimakawa mijinki." Zuciya ta ta soma tunanin munafurtar iyayena, amma ta Yaya kuma wane tabbaci ne da ni kan cewa bazai cutar da ni ba? Ya sake katseni "Nasan haka rashin kyautata ne musamman ga iyaye amma sadaukarwa a soyayya ibada ne, kuma ɗan gyaran babbar ɓarna yin ƙaramin kuskure ba aibu bane. Wallahi ki yarda da ni Rabi'atu wallahi ba zan cuce ki ba." Na zuba mishi ido wata ƙaunarshi na ke ji a zuciyata ga tausayin shi kamar inyi kuka. Na sauke a jiyar zuciya. Yaya Aliyu ban taɓa yi wa iyayena ƙarya ba, kuma ban taɓa munafurtar su ba, zan sadaukar kan so da ƙauna,zan munafurce su so ɗaya a yau kuma zan musu ƙarya, amma karka maida hakan ya zama nadama a gurina ka tabbatar da kyau tata maka zato da na yi. Na shirya sai ka tsara min yadda zan yi duk abinda kake so batare da sanin iyaye na ba.
Ya sauke wata ajiyar zuciya "Alhamdulillah! Kina da ƙawa wadda za kuje tare domin ki ƙara samun mutsuwa?" Na girgiza kai, ba ni da ƙawa. Yace, "To Jamila fa? Kiyi magana da ita matsayin ta na 'yar uwarki zata iya fahimtar ki sai kuje tare, matsalar ina zaki ce zaku?" Na ce Yaya komai zai faru da ni ni ce mai son ka don Allah banda Jamila. Yayi 'yar dariya kirata nace kibar wannan a hannu na zamu yi magana anjima a wayar Umma sai dai muje gobe kenan.
Yace yauwa daidai ke nan gobe bamu cika fita kasuwa da wuri ba,insha Allahu zan kira muyi magana. Mukayi sallama ya ce in shiga gida kafin nan ya wuce.
Jamila tana shara na shigo ta dube ni,"Lafiya Yaya Baby naganki sukuku haka? Nazo na leƙo naga saurayin ki da safen nan. Nace Umma bata tashi ba? Tace e kinsan sai gurin shaɗaya zata farka, na nufi ɗakinmu na dubi Jamila na ce,zo. Ta saki tsintsiya ta shigo cike da fargaba tana faɗin wai ya fasa ne Yaya Baby? Na ce zauna, muka zauna kan katifa, na ce Mahaifiyar maigidana ce ke son gani na, in ba haka ba zata bashi wata,kuma inya bijire zai iya rasa aikinsa. Jamila tace "To kije mana." Nace baki da hankali su Umma baza su bari ba, shine nike tunanin yadda za ayi ki raka ni batare da sun sani ba,sai muce zamu je gaida su Baba kinsan Abba zai yarda sai muje gidan daga can sai muje mu gaida su Baba ɗin ko? Jamila ta ce haka ne, amma kafin lokacin islamiyya zamu dawo gara ke maraja'ar sauka kuke yi." Na ce ba damuwa,zan faɗa masa, amma sai mun ji ta bakin su Umma. Bayan Isha'i ya kira ni na faɗa masa duk yadda muka yi,kuma na faɗawa Umma ta ce mu tambayi Abbanmu. Yace "Na gode sosai,amma ita Baba ɗin wacece? Nace ita ce ta riƙe Ummanmu har ta aurar da ita bayan rasuwar mahaifiyar ta,kuma mun jima bamu je ba,tana son mu sosai. Yace Ni ma ya kamata inje in gaisheta wata rana nace gaskiya ne. Yace "Wace unguwa take?" Nace Kurna ta ke, yace "To ba matsala gobe kamar ƙarfe nawa zaku fito?" Na ce kamar shaɗaya Ummanmu ta farka a bacci mu kuma mun gama aiki, ya ce haka yayi zan zo amma sai dai in tsaya can gurin ƙofar fanfo sai ku zo mu wuce." na ce to. Bayan mun yi sallama na damu sosai yadda zan ha inci iyaye na amma sai wata zuciyar tace khairan insha Allah. Abba yana cin abinci Jamila ta ce Abba zamu samu kuɗin mota gabe muje mu duba Baba tunda ta yi zazzaɓi nan Ummanmu bata samu zuwa ba muma haka, yace to zan sama muku, daga nan kwa bata labarin saurayin na Baby kar taji daga sama. Umma tace aiko aji murna gurin Baba,bata da burin da ya wuce auran Baby. Ni dai duk tausayinsu nake ji domin na ha'ince su.
Washe gari Abba ya bamu na mota sannan ya bamu ɗari biyar ya ce mu bata. Umma kuma ta bamu Naira ɗari ta ce mu sai mata goro. Jamila dama ta saƙe wayar Umma sai da muka fita ƙofa muna gefen babban titi sanna nace Jamila yanzu yaya za ayi Yaya yasan mun fito? Ta ciro wayar Umma ta miƙo min tare da faɗin "Taimakon farko." Na karɓa tare da faɗin na shiga uku,in Umma ta nema fa.? Jamila tayi dariya wa ke kiranta banda Abba sai kaɗan daga dangi, ƙila har mu dawo ba a kira ba, in ma an kira zamu ɗaga muce tana gurin mu. A zuciya ta nace in ma munga zai cutar damu sai mu kira Abba. Na kira shi na ce mun fito ya ce to ku samu keke kuce Janbulo ƙofa ta biyu ni sai zan jira ku a daidai BUK tsohuwa. Muka ce to.
Cikin sauri yake shiri tun jiya ya sanar da Hajiya cewa su Rabi"a za su zo yau da misalin shabiyu saboda islamiyya ta ce Allah ya kawo su, dan haka ta soma duk wani shirinta. Sun sake kira shi da suka zo inda ya kwatanta musu,sai yace Kuɗan jira,ko da yake ba mai adaidaita sahun mu yi magana." Na bashi ya yi masa kwatance ya ce ya gane,sai yace ya bani wayar,na amsa sannan yace zai kawo ku kusa da gida sai mu ƙarasa. Mun tsaya kusa da wata baƙar mota sai kiranshi ya shigo kune kuka tsaya yanzu naɗan leƙa ko zan ganshi ina fadin e mune. Sai naga ya buɗe motar ya fito yazo yace wannan motar tace ku biyomu. Na ce to cikin fargaba. Gaban wani damfareren gida muka tsaya ga wani ƙaton gate kamar ƙofar kasuwa, dan ƙareren masallacin da na kalla a jikin gida kuma fentinsu iri ɗaya shine ya sa na ɗanji sauƙin fargaba. Mai gadin ya buɗe,naga anyi masa magana daga motar sai ya nufo gurin mu yace da mai keke ya shiga. Muka shiga hamshaƙin gidan mai keke yace ashe zan shiga gidan Hajiya ZEENA a rayuwa. Nace kasan ta ne? Yace e mana masu ZEENA Foundation ina ne ba'a san su ba a ƙwaryar Kano.Har muna haɗa baki gurin faɗin muna jin tallolinsu a Radio muka tsaya nace nawa ne kuɗin? Yace bari Alhaji ya bani nan gidan ai ba 'a rowa. Nace Alhaji baya nan wannan yaro shagon sa ne. Daidai lokaci da Yaya yace Amira,na waiwaya, ya yafito ni da hannu naje gurin sa yace nawa ne kuɗinsa? Na ce yaƙi faɗa, yace to tsaya nan ina Jamilar kirata bari inje gunsa. Nace Jamila zo,ta fito shi kuma ya nufi gurin mai keke,abinda yake gudun shi ya faru,mekeke ya soma faɗin ranka ya daɗe ina gaisuwa Shamaki ya ciro kuɗi bai ƙirga ba ya bashi tare da faɗin jeka Allah ya tsare. Shiyasa ya yanke shawarar ƙin jiransu domin tabbas mutane za su gane shi kuma komai zai fallasa.Ya shiga gaba ku zo muje.
🖊️🖊️🖊️
[3/16, 13:07] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Free Page 6*
Muna shiga ƙofar da ya buɗe wani ƙamshi ya bugu hanci mu wanda baza mu iya tantance ƙamshi abinci ne kona turare ba, na raɗawa Jamila cewa ki kama kanki sosai. Ta ɗaga kai alamun taji. Mun isa wani falon da na zata nan ne sai muka ga ya ƙara buɗe wata ƙofar,muna shiga wani falon ne na alfarma da ya ɗara wancan. Ya nuna mana kujera,ku zauna a nan ku jira in faɗa mata.
Ya shiga wata ƙofaar, da sallama Hajiya ta ɗago ta dube shi,tana riƙe da wani ɗan littafi na addini,a hannunta ya je ya tsugunna,ga su sun iso na ce bari in sanar da ku. Ta aje littafin "Su shigo mana, ya ce amma Hajiya sai dai fa bance nan ɗin gidanmu bane,zan sanar da su Juma yanzu don Allah kar su yi wata alama da zata nuna cewa ni ɗin na gidan ne. Hajiya ta ce "Kasan ban iya ƙarya ba,amma zan iya hikima. Yace hakan ma ni ne da godiya Allah ya ƙara nisan kwana. Ya nufi gurin su Juma a kicin ya faɗa musu cewa kar su nuna cewa shi a gidan ya ke, gaban baƙin nan da za su shigo. Juma ta ce "To Allaji uban ɗamina. Ya zo yaje falon da su ke zaune,ya ce ku zo muje. Ya dubi Baby,"Dan Allah zan nemi wata alfarma a gurinki," Ta me? Ta tambaya cikin sauri da faɗuwar gaba. Yace duk abinda Hajiya ta tambaye ki dan Allah ki bata amsa ta gaskiya, kuma karki fusata. Nace To,,Yaya insha Allahu. Gabana ya tsananta faɗuwa bansan dalili ba, muka cusa kai cikin falon ƙamshi sanyi da laushin kafet ɗin da na taka shine ya ƙara sani a fargaba. Ko ban ɗaga kai na kalli ko ina ba,nasan falon na alfarma ne, na kalli inda aka amsa mana sallama kyakkyawar dattijuwa mai matuƙar kama da Yaya sai dai ita fara ce tas,kuma kamala da isa da bunƙasa sun bayyana kansu a gareta. Ta bimu da kallo tare da furta sannunku da zuwa cikin maganar hakiman mata. Yaya ya tsugunna a gaban ta ta gefen dama yana faɗin Hajiya ga su nan. daidai lokacin da ta nuna kujera tana faɗin ku zauna mana. Sai na zube ƙasa kusa da ita kamar yadda na ga Yaya ya yi Jamila ma tazo muka fara gaisheta cikin mutuntawa. Ta zuba mana ido,cike da mamaki ta ce, "Shamaki naga wasu 'yan tsintsayen yara,raino za kayi ke nan? To wacece a cikin su. Ya nuna ni. Na sake sunkuyar da kai. Tace to madalla. Ya miƙe tare da faɗin "Ina dawowa Hajiya. Tace to ba laifi." Wata Dattijuwa ta shigo da sallama muka amsa tare da gaisheta,ta amsa cikin fara'a tace Hajiya komai an kammala. Ta ce "To ku kawo musu abinci da na taɓawa." Wannan Dattijuwa tare da wasu mata biyu suka shiga jera kayan marmari da kayan fulawa dangin cincin harda alkaki,sai kuma can ga kaji da wata shinkafa ƙamshi kuma tuni yawuna ya tsinke amma ko kallon gurin banyi ba, ta ce "Ga abinci sai kunci ko?" Jamila ta kalle ni wadda nasan ta ƙosa ayi mana ta yi,da ido na nuna mata 'a 'a sannan nace, Alhamdulillah Hajiya mun ƙoshi. Tace aikuwa dai ba a zuwa gidana afita haka dole sai anci wani abu, kuma ansha wani abu. Nace To na tashi na ɗakko robar ruwa na dawo na zauna,ta ɗakko wani ɗan faranti da dabino manya jajir tace, "Ci wannan tunda duk can bakiga abinda zaki iya ci ba." Duk da dabino bai fiya damu na ba, sai na saka hannu na ɗauki guda ɗaya na soma ci sannan na buɗe ruwan na kurɓa. Ta kalli Jamila ke jeki can kici duk abinda ki ke da shi'awa a can. Ta tashi taje ta zauna kusa da gurin sai ta ɗauki alkaki. Hajiya ta dube ni. "Ki cinye dabinon tas tunda kin ƙi cin komai." ban yi magana ba. Na dai kuma ɗaukar wani. Tace "Ina ne asalin garinku?" Nace Ummanmu 'yar asalin Sumila ce, shi kuma Babanmu ɗan Rano ne. "Kece ta nawa a gidanku?" Nace ta fari ce ni sai wannan ƙanwar tawa."Ai ƙanwarki ce! Ina ƙawayenki kike tafiya da ƙanwarki?" Na sunkuyar da kai, bani da ƙawa ita ce dai mu ke komai tare. Ta ce "Ya yi kyau haka,bayan ita kina da wasu ƙannai?" Nace akwai biyu maza ƙanana ne. Ta ɗanyi shiru, can tace, "Ina sauran dangin ku suke?" Na Babana unguwarmu ɗaya akwai kuma wansa da ƙaninsa da kuma ƙannensa mata duk suna unguwanni suna aure, dangin Ummanmu kuma suna Kurna. Ta ce "Madallah. Amma iyayen ki sun kyauta da suka bari kuka kawo min ziyara duk da cewa ba wata magana mai ƙarfi taje musu ba ." Yadda ta yi wannan maganar sai naji kamar habaici, sai nace, Ai basu san zamu zo ba, gaida Kakarmu zamuje shine muka biyo. Na kalli Jamila wadda ta zuba min ido kamar ta kai min duka dan haushi nasan tunanin ta me yasa zan yi wannan maganar, ni kuma nasan dalilina na faɗin hakan. Hajiya ta yi ɗan tsam tana kallona, sai ta yi ɗan murmushi ke nan ƙarya ki ka yi wa iyayenki ko? Kin yi wa iyayen ki ƙarya wazai sha?" Na sunkuyar da kai, kamar shirin Film sai naga hawaye sun soma ciko idanu na, cikin shashshekar kuka nake faɗin ban so yin hakan ba, kuma abin ya dame ni, dole inna koma in nemi gafararsu amma Yaya ne yace shi yana son in zo in gaishe ki, shine muka fake da zuwa gidan kakarmu. Jamila ta ce Innalillahi Yaya Baby meyasame ki haka?" Nasan haka zaki yi wallahi ba zan zo ba, ta aje ballin alkakin dake hannun ta ta koma gefe cikin fushi. Hajiya ta yi ɗan murmushi "To ai kamar ba a yi wani abin kuka ba ko?" Na numfasa ban kyauta musu bane shi kuma Yaya zai ga kamar ban ɗauke shi da muhimmanci bane. Na kalleta bayan na sauke ajiyar zuciya. Ta ce "To shi Yayan da kike faɗa wanene?" Cikin mamaki na tsura wa gefe ido, tsabar rainin hankali ne, ko kuwa dai da gaske bata fahimci wa nake nufi da Yaya ba.Na numfasa wanda ya kawo mu. Ta taɓa baki, "Au wai Shamaki ne Yayan? Kuna da wata dangantaka ne ta kusa ko ta nesa?" Na girgiza kai, babu, kawai bazan iya kiran sunanshi ba ne kai tsaye Hajiya. Na soma ƙosawa da tambayoyin ta ko ita ce uwar shi ai bazata min Wannan maganganu ba. Wata zuciyar ta ce shi yasa ya baƙi haƙuri tun kafin ku shigo. "Menene matsayin karatun ki?" Wata tambayar ta kuma katse tunanina Muna jarabawar kammala Sakandire zamu gama jibi. "Kina da burin ci gaba?" insha Allahu in har Yaya ya amince kuma yana da halin hakan ina son ci gaba da karatuna. Ta yi ɗan murmushi Ki daina kiranshi da Yaya ki faɗa mishi wani sunan ko dai ki kira shi da sunan sa. Na yi shiru cikin mamaki. Ta nuna min ɗan farantin Dabino. "Akwai buƙatar ki cinye wannan dabino." Na kalla na ci guda uku. Sai naji kamar zan zargi a wani abu a cikin dabino. Nace ya ishe ni ne Hajiya ban cika cin dabino ba. Ta maida kallon ta ga. TV kamar ba zata kuma magana ba, na kalli Jamila ta min alamar wai inzo mu wuce.
"Islamiyya fatan dai kina zuwa?" Mu ne zamu yi sauka a makarantarmu nan da sati uku. Na bata amsa nima kamar ina jiran tambayar. Sai na ga ta kalle ni, daidai lokacin Shamaki ya Turo ƙofa tare da sallama. Ya kalle ni sannan ya tsugunna a ɗaya gefen na Hajiya yana mata sannu da hutawa. Ta amsa a ƙasaice ba tare da ta kalleshi ba. Na kafa mishi ido ina son ya kalle ni in masa alamar zamu tafi,amma sai ya ƙi kallo na,ya juya yana faɗin "Kunƙi cin komai ko Amira? Nan ma fa gida ne." Na ce ni naci dabino kuma ga ruwa. Jamila ce bata ci ba. Ya kalli dabinon a gabana, ya dauki ƙwaya biyu ya jefa ɗaya a baki ya fara taunawa tare da faɗin nima dai bari in ci dabinon. Hajiya ta ɗago da sauri ta kalle shi. Tuni ya fito da ƙwallon na farko har ya jefa na biyun. Ta ce na baka ne ka ci? Yace Afwan Hajiya zan kawo dabino na tuna kin ce ya ƙare jiya ko? Sai kuma ya tuna zai tona kanshi dan haka ya miƙe da sauri ina zuwa bari in zo ku tafi. "Zauna." Ta furta fuskanta ba walwala. Ni kuma mamaki na ke yadda ta yi masa a game da dabino,bisa ga dukkan alamu bata so ya ci ba. "Wace sana'ar mahaifinki ya ke yi?" Lebura ne magini. Ta ɗan taɓa baki. "Allah ya bada Sa'a. Ta dube shi, ka yi magana da Juma a kwashe musu kayan marmarin nan su yi tsaraba. Da sauri na ce a'a Hajiya ki yi mana afwa za a yi mana faɗa. Ta ce "Haka ne domin ba'a san kunzo ba ki ka ce ko? " Ya kalleni cike da mamaki kuma da alamu bai ji daɗin hakan ba, ni ko da a kalli iyayena ƙanana gara ace ni ce bani da mutunci. Tace "Ba haka kika faɗa ba?" Na ce haka ne amma yanzu in har muka je da wannan kayan iyayenmu baza su haƙura da haƙurin da zamu basu na laifin ƙarya da muka yi ba, domin za su zargi ko mun canza hali ne mun zama kwaɗayayyu." Ta tsira min ido, sannan ta kalli Aliyu. "Sai ku sake yin ƙaryar da kuka yi a farko ku faɗi wani wanda in shine ya baku baza'ayi faɗa ba." Ai bamu da shi a dangin mu kaf, kuma ba mu yi nasarar ƙaryar farko ba kenan. Ki yafe mu Hajiya watarana zamu sa da kanmu mu ci insha Allahu. Yace gaskiya ne ranar da na kai musu Lemon ɓawo Abbansu yana ta faɗa. Tace "To shike nan Allah ya yi muku albarka za ku iya tafiyar ku yanzu." Sai lokacin ya kalle ni, muje ko? Na ce to na miƙe ina gyara mayafina Hajiya kuwa idanunta ƙyar a kaina. Jamila ta mata sallama ya nuna mana ƙofar da muka shigo ku bi nan muje. Muka fita har falon ƙarshe bai fito ba. Jamila tace gaskiya baki da hankali wallahi Yaya Baby. Daga zuwa gidan mutane kinji sanyin AC kin kama kina ta zuba,to meye sai kin faɗa mata cewa ba'asan munzo ba,ina ruwan ta da sanin su?" Na ce Dalla banza baki san mekefaruwa ba,amma zan wayar miki da kai bari mu hau keke napep. Yace fito Muje in kaiku can inda zaku ta bani mota aro." Yace in hau gaba Jamila ta hau baya. Maigadin yana faɗin adawo lafiya ranka ya daɗe Allaji. Na kalle shi. Ya yi saurin faɗin su wai mutane suna ƙaunar su kai mutum inda bai je ba, daga zuwa wurin ta wai raina ya daɗe kullum haka ya ke faɗa in dai Nazo gidannan." Na sauke ajiyar zuciya nace ai fatan alkhairi ya yi maka.
Ya canza maganar "Kinji daɗin hira da Hajiya?" Na ce sosai kuwa tana da kirki. Ya saki fara'a sai ma kin zauna da ita zaki sha nasiha da albarka. Na ce umm haka ne kam. azuciyata kuwa sai ina faɗin taɓ zama da wannan ai gara in haƙura da auren. Jamila ta sako baki, amma tana da tambayar ƙwaƙwaf wai! Na waiwayo da sauri wa ta tambaya? Ke mana harda kuka fa ki ka yi a gurin bada amsa. Sai ji mukayi mota ta yi ƙuu kamar zata faɗi sannan ya gungura gefen titi, me ta tambaye ki har ya saki kuka?" Nace kar ka damu ba wani abu bane, ki faɗa min don Allah.Jamila ta zayyana mishi komai, ya sauke ajiyar zuciya to kiyi haƙuri kinji ko?" Nace to ai ba ita ta sani kuka ba,ƙaryar da na yi wa iyayena ita ce ta sani kukan, na ci amanar su, zan faɗa musu gaskiya in mun koma. Yace ba wata matsala ko da baƙi faɗa ba,amma zaki iya faɗa in kina ganin haka zai fi sama miki kwanciyar hankali. Kuma za a turo gobe,sai ki sanar dani nan gidan zan kawo su ko kuwa wani gurin ne daban." Nace zan yi magana da Umma sai in faɗa maka duk yadda suka ce. Ya sauke mu ƙofar gidan Baaba ya bamu dubu ɗaya ya ce ku ba Baaba ɗin kafin inzo. Jamila ya miƙawa ta amsa tana godiya Nima na yi masa godiya muka shiga ya juya.
Hajiya ta jingina ta lumshe ido duk wanda ya kalleta zai yi zaton bacci ta ke yi,amma kogin nazarin yarinyar ta faɗa. Ko shakka babu ta lura yarinyar ta na da kafirin wayo, ta goge laifin dana so ɗorawa iyayenta ta maida shi a kanta,har da wani kukan kirsa wai ita ga mai imani, sannan ta bata mamaki yadda ta ƙi amsar komai dan haka ta fasa bata kyautar da ta yi niyya. Ba shakka ta cinye jarabawar da take son yi mata saidai tsaron ta wayon "yar ya girmi shekarunta.Kome ma Shamaki ya gani ita ba sharaɓa ba, ba ƙirjin kirki ba, kuma a fuska ba wata mai kyawun a zo a gani ba. Ta ke ta tuna da dabino da ya ci ta tashi zaune da sauri,a zuciyarta tana rayawa tasan ba matsala tunda yace dan ita aka yi shi.Amma dan ta kore kokwanto sai ta ɗauki waya dan taji ta bakin Malam.
Suka gaisa ta sanar da shi matsalar da aka samu. Ya ce "Subhanallah Hajiya ya ki ka bari ya ci." Tace ban ankara ba malam sai da ya kai na biyun kuma gashi a gabanta ba dama ince ya zubar,dole zata tuhume ni akan me yasa ita na bata. Malam yace sunansa da nata aka yi aikin gashi aikin mai ƙarfi ne, sirrin Ya wadudu ne aka haɗa da basmala ƙafa dubu talatin da wasu haɗe haɗe. Wani mutum da muka yi masa irin aikin nan matar bata son shi Allah da ta ci Dabinon duk inda zashi binsa ta ke, kuma da Allah ya yi masa rasuwa a maƙabarta ta tare. Gaban Hajiya ya faɗi, to kenan gara da bata ci duka ba, yaushe zan so ta zame masa jela ko ina ya saka ƙafa ta mayar. Damuwa ta yanzu shima kenan zai ƙara sonta? Malam yace mu dai jira muga hukuncin Allah,amma dai ki yi addu'a aike mahaifiya ce harshen ki yafi komai. Tace to shikenan, addu'a a kai muke Allah ya yi mana mafi alkhairi. Suka yi sallama ta miƙe domin yin alwallar azahar.
Jamila ce ke baiwa Baba labarin Yaya Aliyu, sai murna take. Ta bata dubun daya aiko mata,tana ta addu'a muka yini har la'asar list munyi mata wanki da kwalemar gidan taji daɗi tace dama ko yaushe ina ta fatan kuzo duk cikin jikoki na kune kaɗai masu yi min irin wannan ƙoƙarin Allah ya baku miji na gari. Mun tarar umma har ta gama tuwon dare nan na amshi aikin miya Jamila ta kama shara ranar dai munyi fashin Islamiya. Da dare muna cin tuwo Jamila ta ce ""Yaya Baby ina ta tunawa da kayan alatun nan yawuna har tsinkewa ya ke." Nace ko ni wallahi amma ke baki so ci bane, ni kinga ba dama inci. Tace "Itama Hajiyar bata so mu ci ba, ai da ta so muci sai ta bamu guri ko ta sa a kai mu falon farko. Na ce taɓ wannan kinga ta yi kama da wadda zata tashi?"Umma ta katse mu da faɗin wacece? Muka kalli juna. Na ce Umma dama zanzo in kawo kaina, na yi muku babban laifi,dan Allah ku yafe min. Na tsame hannu na a tuwon na zo gabanta na zauna na zayyana mata duk yadda abin ya faru. Ta min faɗa sosai kuma ta jamin kunne akan kar mu sake aikata makamancin irin wannan kuskuren. Tace bazata faɗawa Babanmu ba,har ma ta ce gashi munja mata tana yiwa mahaifinmu rufarufa. Na ɓoye mata wasu tambayoyin da Hajiya ta min wanda nasan zata ji babu daɗi.
Cikin dare ina tsaka da bacci sai naji kamar an tasheni, ina farkawar sai na tsunduma tunanin Yaya take na samu kaina da tashi na nufi ɗakin iyayena na tura ƙofar na kalli gurin da nake zaton wayar Umma na ganta kuwa a caji na ciro Abba da ke kwance a ƙasa kan tabarma yace "Waye nan." Take na firgita nace Abba ni ce ban ɗaki zanje haskawa zanyi da wayar Umma. Yace kwan dake banɗakin ya mutune? Nace babu haske dai. Yace "Ɗauka kije." Banɗakin na shiga na kashe hasken sannan cikin rawar jiki na soma neman layin Yaya. Sai a kira na shida sannan ya ɗaga. "Baby lafiya?" Ya tambaya cikin yanayin bacci da kiɗima,. Na ce lafiya lau Yaya, na kasa bacci ne tunaninka ya dame ni. Goben za'a turo ɗin? Cikin matsanancin mamaki yace kije ki kwanta zamu yi magana da safe,na samu kaina da faɗin Yaya ina sonka sosai kaji? Ya ce "Naji Baby na yarda." Nace to kana sona? Yace sosai Baby. "Kije ki kwanta." Nace to Yaya. Na fito na je na maida wayar sannan na kwanta. Ji nake in har banga Yaya ba zan iya rasa rai..A wannan ranar dai ban samu bacci ba. Shamaki ya zauna cike da mamaki yana son ya ƙaryata kanshi cewa Baby ce, kodai ta gane shine Aliyu Shamaki,inhar ta gane to ba shakka zai fasa aurenta duk da irin son da yake mata. Ya soma tunanin abinda ya faru tun daga zuwanshi gidan har tafiyar shi,shin ko yayi wani abu ne ba daidai ba har ta gane. Yakasa tuna hakan,to ko Hajiya ta faɗa mata. Koda ya dawo kai su abinda Hajiya ta ce mishi kawai ka sanar da Alhaji Umaru da kawunka gobe za a tura kamar yadda kake buƙata. Harya tambaye ta ko yarinyar ta cinye jarabawar ne? Tace "Kayi abinda na ce kawai." Ya numfasa bayan ya gama tuno da komai.To
🖊️🖊️🖊️
[3/16, 13:08] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a tura shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Free Page 7*
Nayi sallar asbahi duk na rasa me ke min daɗi na koma na kwanta sai bacci ya kwashe ni. Jamila ce ta tashe ni tana cewa, baza ki makaranta bane Yaya Baby. Umma tace kar a tashe ki ƙila bakya jin daɗi ne, saboda ta tabbatar in har ki ka koma bacci baya sallar asbahi to baki da lafiya. Na yi miƙa Yaya yazo ne? "Wanene kuma Yaya?" Ta tambaye ni cikin mamaki. Yaya Aliyu mana ko mafarki nake yi ne? Har ma yace a ɗaura aurenmu kawai. Jamila ta saki dariya "Don Allah Yaya Baby ki tashi nikam." Na tashi naje na gaida Umma ta ce Abba ya fita, na ce kuma kin faɗa masa yau ne 'yan gidan su Yaya zasu zo?" Ta ce "Na faɗa masa tun juya da kika faɗa min,.amma kin faɗa masa cewa gidan su Abban Zuhra za su kai kuɗin ko? Kuma Abbanku ya ce,ki tambaye shi ƙarfe nawa zasu zo?" Nace to bani wayar ki in faɗa masa. Jamila ta fito ɗauke da jaka tana faɗin Wallahi bazan jira ki ba,gara ke jarabawa ki ke yau ne ma ƙarshe. Sai lokacin na tuna da batun makaranta. Nace dan ma dai daga yau na gama. Sai da na shirya sannan na ɗauki wayar zan kira amma ba kati,gashi bashi ne cankas a wayar. Na Umma ko kati za'a siyo? Tace "Wa zai siyo kunyi latti ki tafi in kin dawo kya kira shi,abinda nasan bai wuce da daddre za su zo ba, tunda gari ɗaya ne." Na ɗauki biro bana zuwa da jaka tunda jarabawa ce muka wuce.
Hajiya ta kalli Shamaki, "Ƙarfe nawa zasu je su kawun naka?" Ya saki fara'a sai da dare in kowa ya gama sabgar sa bayan sallar Isha'i. Tace "To nawa za a kai?" Yace dubu Hamsin kinsan bana son ta san komai da wur ne. Tace "Akwai gejin da dole su sani, tunda za su yi bincike." Yace haka ne,amma kafin lokacin na samu abinda na ke so. Bayan sallar Isha'i Shamaki ya kwashi su Ƙanin Hajiya da kuma ƙanin mahaifinsa sai limamin masallacin gidansu suka nufi kai kuɗi, saidai tun a hanya ya ce musu ba zai ce suyi ƙarya ba, amma yana son kar su nuna shi mai arziki ne ya faɗa masu komai a taƙaice da kuma dalilin sa. Suka ce insha Allahu za su yi yadda ya ke so. Ya ɗauki waya zai kira layin Ummarsu. Sai lokacin yaga miss call da yawa, ya yi mamakin ina ya jefar da wayar har da Baby ta yi masa wannan kiran haka. Ta ɗaga wayar ya ji muryarta can ƙasa, ta gaishe shi, ya amsa tare da tambayar lafiya ya ji muryarta haka. Tace banajin daɗi ne, yace ashsha sannu, kin sanar da Abba mun kusa zuwa kuma nan gidan zamu zo? Ga mamakin sa sai ya ji tace dan Allah kun taho?" Ya ce kinsan abinda za ayi wasa daban ya ke ko?" Tace dama kiran da nake maka kenan ɗazu dan in faɗa maka Abba ya ce gidan wansa za a je,amma babu nisa daga nan gidanmu bari in kira Abban a waya ya fita yanzu." Yace "To faɗa mishi gamu tafe a hanya. Naje da gudu gurin Umma,nace Umma Yaya sun taho da iyayensa. Tace I kon Allah! Wai kuwa Baby lafiyarki ƙalau yau wane irin hali kika canza ne?" Na ce yi haƙuri Umma. Na koma gefe na tsaya. Umma ta ce sai ki kira Abban naku ki sanar da shi. Jiki na ɓari na kira Abba na faɗa masa. Yace gashi nan dawowa gidan.
Shamaki ya sanar da su wakilan nasa cewa su faɗawa iyayen yarinyar nan yana son auren ne a lokacin walimar saukar karatunsu. Direba ya sauke su bakin lungun ya tambayi Shamaki ko ya jira su? Ya ce e ka jira mana sai ka kai kowa gida sai ka dawo ka ɗauke ni. Yace "To" Abbansu Baby ya fito ƙofar gida ya tari su Shamaki yace ku zo muje can ayi mai gabaɗaya. Suka juya har shamaki. Ƙatuwar tabarma aka shinfiɗa a barandar ƙofar gidan inda dama anan suke salla kuma ana ɗaukar karatu daga gurin limamin da ke jan su sallar maƙocin shi ne. Annan ne Dai suka gaisa cikin mutunta juna sai Shamaki ya miƙe ya ce to bari ya dawo. Tun da aka ce ga su nan na hau ɓare ɓaren gyaran jiki, ina ta kwalliya sam ban damu da yadda Ummanmu ta haɗe fuska ba. Jamila kanta sai da ta tambaye ni wai kuwa lafiya na ke irin wannan abin? Nace me nayi dan kawai na yi kwalliya laifin ne,kar ki manta da daga yau ya zama mijina,kuma kinsan dai matsayin yiwa miji kwalliya ko?
Cikin
"Matsananci mamaki Jamila ta ce "Yaya Baby wai ina kunyarki da kawaicinki suka tafi ne?" Wallahi karki fara kice za ki ke irin wannan rawar kan, wai baki lura ma da yadda Umma ta ke jin haushin canzawar ki tun jiya ba?" Na ce ni banga wani canzawa da na yi ba. Kafin Jamila ta ce wani abu Muryar wani yaro ta ratso cikin kunnuwanmu yace ana sallama da Baby, cikin rawar jiki na ɗauki mayafi na zira takalmi ina faɗin Jamila ki kawo mana tabarma. Umma tace "Baby ki zo nan." Na nufi gurin ta a ƙofar ɗaki kan tabarma na ce ga ni. Ta ce, "Kinsan daga Allah ba wani in har baki haɗa min hankalin ki guri ɗaya ba zamu samu matsala da ke, tun jiya sai wani shashanci kike yi girma hauka ne? Wato kin riƙa kin so aure shine ki ke wannan rawar kan, dama rashin samun saurayin ne ya sa ki ka nutsu kamar ta Allah ko?" Na sunkuyar da kai ina faɗin Umma dan Allah ki yi haƙuri ni ban fahimci me nake yi ba,yanzun ma Jamila ta gama min faɗa wai na canza. Na daina Umma. Bari inje yana jira. Ban jira me Umma zata sake faɗi ba na yi waje da sauri har ina tintiɓe. Umma da Jamila dai abin har tsoro ya ba su. Ina fita yana jingine inda ya saba tsayawa, na isa da sauri ina faɗin sannu Yaya da zuwa. Yaya ce "Sannu Baby " Na gaida shi ya amsa. Na ce Yanzu sun can ana maganar aurenmu? Ya ce e na rungume hannuwana tare da ɗan tausaya wa ina faɗin Alhamdulillah Naji daɗi Yaya zan iya bacci in aka ɗaura mana aure kuwa? Mamaki ya hana Shamaki magana,duk da cewa shima fa yana jin wata ƙaunarta a zuciyarsa wadda bazata misali ba. Ta katse mishi tunani da faɗin lokacin walimar tamu za a saka ko? Yace ban sani ba gaskiya haka dai nace su tambayar min." Nace Kaga Yaya, asa hakan wallahi na yafe lefen, kuma kayan ɗàkin ma zan faɗawa Umma ba takura ko? Yace "Sai ki iya faɗa mata haka baza ta ga cewa kinyi rashin kunya ba?" Nace to wai me na ke yi ba daidai ba? Tun jiya ake cewa wai na canza ina ta zumuɗi, kuma ni ina jin wani sonka ne bansan ya zan fassara maka abin ba. Ina samun nishaɗi da jin daɗi ne kawai in naji muryarka, da na kira baka ɗaga ba har kuka fa na shiga ban ɗaki na yi, sai ina ji a jikina kamar zaka fasa. Yace "Gaskiyar magana kin canza gaba ɗaya kamar ba ke ba. Nima dai ina mamaki." Nace to Allah ya sa dai su amince shine damuwata. Yace "Ya maganar walimar ku?" Na yi ɗan jim sannan nace tana nan, amma gaskiya dai zaka zo min ko,duk da masana cewa kana cikin shirin biki lokacin ai na san zaka so ka ga karatu na. Yace in sha Allah zan zo sannan karki saka a ranki cewa dole sai lokacin da muka ce, in basu yarda ba dole mu jira lokacin da suke ganin ya fi." Na ce Ni fa damuwata kada ka zo ka ce ka fasa, wallahi zan iya mutuwa har lahira. Yace Baby in kinga na fasa aurenki wallahi na mutu ne,matsawar ina numfashi bazan fasa ba. Daɗi ya rufe ni, nace Allah na gode maka. Munata tattauna batun soyayyarmu na ga Abba ya zo ya shiga gida. Ya ce bari inje in sallame su, ki koma gida zan dawo nace to. Na shiga gida don inji yadda suka yi. Anan na samu Abba yana ba Amma labari ya zauna genen tabarmar da yake kai har Jamila ta kawo masa abinci. Yana faɗin "Wato Salamatu Allah ya amshi addu'armu ya kawo wa Jamila mijin ƙwarai ba sai mun bincika komai ba sun wanke shi tas. Limamin Unguwarsu inkinji yadda ya ke yabon sa abin zai baki shi'awa ga neman na kansa ga alheri duk sun yabe shi,ƙanin mahaifiyarsa da ƙanin mahaifinsa banda albarka babu abinda suke sa masa. Kuma sun nemi alfarma ko za a sa aure tare da walimar saukar su nace a a saboda yanayi shima kar ya takura kansa muma haka, amma sai suka dage kan cewa gaskiya yana buƙatar aure sosai kafin nan da azumi. Sanna duk abinda ake dashi bashi da wata matsala akai wa yarinyar. Na ƙara kaso kunne inji me Umma zata ce. Sai naji tace, Gaskiya a sa shekara ya yi haƙuri dan shekara kwana ce Abban Baby, bikin 'yar fari ba mu yi mata komai ba ai sai mun shiga bakin duniya. Ban san lokacin da nace Umma zai fasa inhar aka sa shekara,ni dai gara lokacin da yace ɗin dan in ya fasa mutuwa zany.... Saukar ta kalmi da naji a fuska ta shine ya tuna min cewa bai kamata in tsoma baki a zancan aurena da mahaifana su ke yi ba. Na lalle su dan in gane waya jefe ni,sai naga ashe Umma ce, sai huci take ta rasa abin faɗi dan takaici. Shi kuma Abba ya sunkuyar da.kai, sai suka bani mamaki, domin a magabata banga wani abu na tashin hankali ba, na faɗa musu abinda ni nake so ne, kuma dai su iyayena ne wazan fadawa halin da zan samu kaina in an fasa. Sallamar wani yaro ce ta ratsa shirun da gidan ya yi kamar mutuwa ta gifta, Abba ya amsa sai yaron yace "Ance Baby ta zo." Na tashi da sauri na shuri takalma sai da na kai bakin soro sai na waiwayo dan naji a jikina ni suka bi da kallo dama na zargi haka. Na fita ina tunanin ko dai na kuma wani laifin ne? A fili nace garama amin auren in tafi tunda har sun soma gajiya da ni. Na isa gunsa ina faɗin yau Jamila ta ƙi kawo mana tabarma. Yaya sun tafi ke nan? Ya ce "Sun tafi." Nace amma sun faɗa maka komai yadda aka yi? Yace "bakiji ba da Abba ya shigo?" Na ce Banji matsaya ba a maganar na saka musu baki Umma ta jefe ni sai kuma suka yi shiru. Yace "Subhanallah! Me zai sa ki saka bakinki cikin managarsu?". Na ne Yaya Shekara fa Umma ta ce, kuma kai nasan baza ka shekara bada matarka ba. Yace Banda haka Yaya nima ba zan iya ba. Yace "Baby bai kamata ba kina saka baki a maganar manya. Hajiyata tana da zafi in kinje kina mata irin wannan za ku samu matsala wanda hakan zai kawo matsaloli a cikin zaman aurenmu. Ni kuma bana son a ce ni da ke mun rabu, saboda akan Hajiya zan iya komai. To gaskiya in kina son mu daidai ta ni da ke, to sai kin sawa bakinki linzami in manya suna magana babu ruwan ki." Na sunkuyar da kai, insha Allahu na dai na. Nima jiya ne suka fara wannan kukan da ni,amma bana yi, ko yanzu a maganar ka kaɗai suke cewa na canza. Ni kuma banga canjin ba. Ya ce "Nima na gani dan haka ki dawo kan hanya. Nace to, amma kai ai zamu iya tattauna maganar aurenmu ko? Ya ce "Sosai ma kuwa." Nace to yanzu faɗa min yadda aka tsaya. Yace Abba sunce za su yi shawara, domin shima Wan Abba cewa ya yi tunda na ce abinda ake dashi a kawo ki ba matsala to na shi ganin gara a yi bikin kawai. Shine aka ce a shawarci Ummanki. Nace to Umma tana kiran shekara. Yace Allah dai ya zaɓa mana mafi alkhairi. na ce ameen. Yace "Ni ma dai ya kamata in tafi, da har zan wuce, sai kuma nake tunanin ban muyi sallama ba." Nace yanzu sai yaushe? Yace, "Bazan sa lokaci ba gaskiya tunda an bani ke. amma kowane lokaci za ki iya gani na. Zan bada waya a kawo miki saboda za mu ke yin magana akai akai. Nace "To ɗan Allah kar ka manta da Ni kaji. Ya yi yar dariya sannan ya yi ƙasa da murya, ashe zan mantà kai na. Ina mugun sonki Baby. Cikin farin ciki nace ina sonka Aliyuna. Sai kuma naji kunya na saka hannu na rufe fuskata. Muryar Abba naji yana cewa "Malam Aliyu bari in baka saƙo ka faɗawa magabatan na ka.". Aliyu ya ce to shiga gida sai kin ga saƙon na ce to ka gaida su Hajiya da su Anisa. Na laɓe a soro ko zanji me za su faɗa amma banaji. Dole na shige ciki Umma harta kwanta na leƙa ɗakinta ina yi mata sannu, ko dai ta yi banza da ni, ko kuma ta yi bacci. Na fita na je na saka tuwo na ɗebi ruwa a kofi na shiga ɗakinmu na zauna ina ci. Jamila ta shigo da shirin baccin ta, tace Yaya Baby ki sa su Jafar su yi fitsari in kin gama, yau duk ni na yi aikin ki a gidan nan." Na ce me kika yi nawa da zaki faɗi haka?" Ta ce "Ni na tace gasara kuma na kammala komai." Na yi 'yar dariya. Ni da zan tafi ma gidan mijina daga can zan ke zuwa ina miki akin? Jamila ta yi gialala ta na kallona,sannan ta ce, gaskiya Yaya Baby abinki ya soma wuce tunani, kuma ko a jikin ki. Na kalleta Ni Kuma ke kike bani mamaki, ko da yake na miki Uzri bari ki faɗa soyayyar za ki gane abinda ya same ni. Tace haka ɗazu ki ka yi ta rera wakokin soyayya a gidan nan ke da ko wani ya yi waƙa sai kin masa wa'azi." Na suɗe robar ina lashe hannu, na ce duk ba wannan ba, faɗa min abinda su Umma suka yanke da na fita. Abba ya tsorata da yadda ki ka yi,Ya ce Umma ta yi haƙuri ayi bikinnan a haka yadda ki ke yi ya nuna kin matsu da aure,abinda aka samu a kai miki. Daƙyar Umma ta yarda domin har abin sai da ya kai su kamar za suyi sa'insa, daga bisani Abba ya lallasheta. Amma tana ciki da ke,zaku gauraya da safe. Na ɗanyi jim har ga Allah ni banga abin laifi ba amma dole in ke yin shiru dan in samu zama lafiya. Na dubi Jamila wadda ta kwanta tana ƙokarin rufa. Na ce amma ya suka yi matsaya a ƙarshe. Ta ɗago kai zakiji a bakin Umma da safe, shawarar da zan baki kuma ita ce, ki bawa Umma haƙuri, sannan ki daina magana sam in ana zance.Na miƙe tare da faɗin zan kula sosai. Da safe Umma bata amsa gaisuwa ta ba,to nan ne fa hankalina ya tashi na soma kuka ina bata haƙuri, tace haƙurin me zaki ba ni, ni a su wa ɗanwake a Otal ba dai ɗa namiji bane Baby Allah ya bada sa'a." Na ce Umma wallahi ni fa bansan me zance miki ba ne, kiyi haƙuri na tuba don Allah.Abba ku yi haƙuri ni ban san cewa ba a magana ba. Ya ce tashi kije ki yi aikin ki ta haƙura. Na fita ina sharɓen kuka. Ina jiyo Abba yana baiwa Umma baki, tare da nuna mata cewa ƙuruciya ce,kuma mu godewa Allah Salamatu da ya bamu yara masu kamun kai da nutsuwa, duk tsukunnan yaban su ake Allah ya sa musu albarka karki fusata Allah shine mai rufin asiri abar auren a lokacin da aka sa shi. A ranar wani matashi ya yi sallama muna Islamiya anci sa'a Abba yana gida . Suka gaisa yace Aliyu ne ya aikoshi da saƙo ya baiwa Amira. Abba ya amsa waya ce sabuwa a kwali sai layin da kuma kati wanda ya ce ace in ta saka ta kira shi. Abba ya ce to insha Allahu za a bata, taje islamiyya. Na yi murna sosai lokacin da muka dawo. Umma ta ɗan saki jiki harma ta karɓi wayar ta sa albarka. Tace ki kula irin wannan ta shafawar ba wuya ta fashe. Na ce to. Na saka layi na sa katin na shiga ɗaki na kira wata Number ɗaya daga cikin lambobin da ke jikin wani kati da ya sako a ciki kwalin. Wani ya ɗauka, nace Aliyu nake nema. Yace mai gida baya nan ya yi tafiya. Nace Shamaki fa na ke tambaya? Yace nima shi nake magana ya tafi China ɗazu. Na ja tsaki sannan na kashe waya, ina faɗin Ni Aliyu na ko filin jirgi baya zuwa bare wata China. Na sake ɗakko katin don in duba wata Number. Sai naga ya yi wa wata lamba alama da biro a ƙasa ya rubuta ki kira wannan layin. Cikin sauri na saka na kira. Ya ɗaga "Baby zan kira ki kinji?" Na ce to Yaya na gode, ina jira fa ka kira ni fa. Yace karki damu. Haka dai abubuwa suka ci gaba da tafiya, iyayena suka tada hankali gurin neman kuɗin da za a yi min kayan ɗaki aure saura sati uku da 'yan kwanaki. Umma ta sanar da Baba har Kurna taje,Baba tace Allah ya sa hakan ya zama alkhairi, abinda za ayi yanzu zata sa akama Awakinta guda biyar a saida su, a zo a karɓa a sai min kayan kicin kuma zata sanar da sauran dangi. Shi kuma Abba an sanar da dangi sun nuna murna amma da suka keɓe sai ƙanwar Babanmu Saratu wadda dama basa shiri da Umma tace "Shi Abbana su Babyn da ya kama ya sa rana sati huɗu kila ya tanaji kuɗin da zai yi mata kaya da na abinci da za a dafa. Dija tace Nima dai na yi mamaki muna neman gudunmawar sauka mu bashi, shi kuma ya na tataro aure abinda Allah ya ba ni shi zan bada. Saratu tace ita matarsa dan hauka gata da tsohon ciki shine ta yadda da wannan gangancin koda yake ƙila ma ita ce tace a saka dan a ce yar ta ta riga 'yay'anmu aure. Dija tace ko wane kwashe ne kuma zai ɗebi wannan yarinyar kamar taɓarya oho. Matar waliyin ta taɓa baki tare da faɗin jiya da na shiga murna ai na ga 'yar da wata ƙatuwar waya wai saurayin ya aiko, shiko Abban su Zuhra sai rawar kai shi ga waliyyi nace dubu goma dai ya baka abikin Ummi dan haka sai ka nemi shabiyu kar kaji ance waliyyi ka fara neman siyan gado. Suka sa dariya gara dai ki faɗa masa dan ga sunan riɗa riɗa duk wadda ta samu shima hidimar ce a gaban sa. Haka suka yi ta maida zantuka ta re da alwashin zura ido su ga abin da zai biyo baya.
Har kwanaki biyu ina jiran kiran Yaya, Ni kuma inna kira bata shiga. Hankalina duk ya tashi amma babu dama inyi maganar sai Jamila kawai inna faɗa mata sai ta ce bani da aji wai in jira ya kira ni. Ranar kwana na uku ina zaune a kan tabarma a tsakar gida ina rubuta sunayen waɗanda zan kaiwa katin sauka 'yan uwa da yan makarantar bokonmu. Jamila na ke kira ta raka ni. Umma tace to kuma yaushe za ki kai na 'yan Kurna? Nace sai mu kai ranar Lahadi ko asabar tunda bata da Boko sai muje. Umma tace hakan ya yi saura ku kuma zuwa wani gidan nace imsha Allah babu inda zamu ƙara zuwa. Wayata ta soma kiɗan na ɗauka da sauri. Sanyin zuciyata, haka na rubuta a lambarsa. Na tashi na shiga ɗakinmu. Na ɗauka da sauri. Cikin shagwaɓa na ce sanyin zuciyata shine ka ƙi kazo ko? Yace "My Baby ki yi hakuri tafiyar gaggawa ta taso min." Nace na kira wata lamba aka ce ka tafi China . Yace a a Kaduna na je ina can har yanzu aka wasu kayanmu. Nace to Allah ya tsare shiyasa nace ni Aliyuna ko filin jirgi bana zaton ya taɓa zuwa. Ya yi dariya "Na taɓa raka maigada ba so ɗaya ba ma. " Nace Allah ya sa kai ma wata rana in raka ka. Yace "Ameen Allah ya sa mu hau jirgin tare. Na ce ameen. Ya ce "To ya ake ciki menene labari?" Nace wanne zan baka?" Yace "Sabo wanda ya ke tashe." Na ce kati zan kai in raba na sauka in Jamila ta dawo. "To kuma na bikin yaushe za araba?" Ya katse ni. Kaga karka wani damu da katin Biki duk kashe kuɗi ne, karatun saukaramu asabar ne ɗaurin aure Lahadi sai a faɗawa kowa a haka. Yace "Taɓ aurenmu ace ba kati Baby ko bashi ne ni zanci don in buga mana katin biki." Don Allah karka ci bashi a zo ana sallama da kai. Na faɗa cikin shagwaɓa. Yace "Ai misali na yi.
[3/16, 13:08] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo evidence ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Free Page 8*
Abubuwa sun kankama lokaci yana ta ƙaratowa Munafinci ba ga maƙota ba ba kuma ga dangi ba. Umman su Fati har gida ta zo wai Allah ya sanya alkhairi amma harda cewa Umma ashe ku da tanajin ku,auren Fati sai bayan Babbar salla mu masu ƙaramin ƙarfi. Umma tace Allahn da ya kawo mijin a lokacin da masu gori suke gori shine zai kawo abinda zamu kai mata. Ina jinsu Umman su Fati aka wuce ana borin kunya. Umma tace Allah kai zaka yi mana wannan lamari Allah ka taimake mu. Sauran kwana huɗu walimarmu kwana biyar kuma a ɗaura mana aure. Yaya ya aiko min da katan Lemo guda biyar wai na walima a daran ranar ne ya zo gurin Abba ya nemi alfarmar a ɗaga aurenmu zuwa wani satin. Walimarmu da sati ɗaya kenan. Abba yace ba damuwa, ya shiga ciki ya sanar da Umma sannan ya ce in fito. Mun gaisa yake faɗa min wai gyaran banɗakin gidan za'ayi shine dalili. Na ce to Allah ya kaimu, amma banso haka ba,yace kamar yau ne. Yanzu ki faɗa min me da me kike buƙata a gurina. Na dube shi, kamar na me? Yace "Kuɗin lalle da pati ko baza ki yi ba?" Nace zanyi amma kana da kuɗin ne? Yace Inkinji makaho yana cewa a yi wasan jifa ai ya taka dutse ne ko? Ki lissafa min duk abinda ki ke so na biki zan miki daidai ƙarfina." Nace to kana son mu kira DJ ko baka son kiɗa? Ya yi 'yar dariya. Kinga Baby zan kama miki ɗan wuri ku yi party da ƙawayanki amma banda maza." Na zaro ido karka matsa wa kanka, kila Abba ma ya ce baza a fita party ba. Kawai zan yi DJ na a can filin,na nuno mishi da hannu. Ya kalli gurin "Shikenan zan sa a zo a sa kujeru." Na ce to na gode Ubangiji Allah ya bada yadda za ayi. Yace Ameen ina jin daɗin addu'o'in ki. Zan tafi ki tura min sauran abubuwan ta text,sai in kawo miki ko?" Na ce to yawwa dama zan tambaye ka ko zan iya buɗe Whatsapp? Yace wannan ki bari sai an kawo ki zan buɗe miki da kai na." Na yi murmushin tare da faɗin na gode. Na ce yawa jira ni ina zuwa. Na shiga gida da sauri,na ɗakko katin saukarmu na ɗakko na kawo masa, nace ga shi don Allah ka zo, tunda ma an ɗaga bikin ai dai zaka zo ko? "Insha Allah zan zo, ki shiga gida zan aiko miki da katin auren shima sai na party ki rubuto min yadda ki ke son ya kasance." Zan yi magana ya ɗaga min hannu,kar ki ce komai shiga gida." Na ce to sai da safe.Har na juya yace, yawa na tuna "Baby!" Na waiwayo, ki faɗawa Abba za a kawo lefe zuwa jibi." Zan dawo ya kuma cewa shiga gida kawai." Dole na wuce ina waiwayen sa. Fatana Allah ya sa ba bashi zai ci ba.
Jamila sai murna su ke yi ita da Ummu za a.kawo lefe, ni kam ba ta wanna na ke ba,ɗaga bikin shine abinda yafi komai bani takaici. Saidai ba ni da damar in yi maganar da wani, tunda duk ba su fahimta ta. Ashoben Walimarmu shi aka maida ashoben biki wannan ɗagawar sai ya bada damar zuwa a siyo musamman 'yan uwa da 'yanmatan lungunmu waɗan da suka bayyana kansu a matsayin ƙawayena harda su Fati. Kullum sai sun shigo muna tattauna yadda za ayi party. Tare da taimakon Jamila na rubuta wa Yaya abubuwan da nake buƙata. Kuɗin lalle da wankin kai. kuɗin Party kuɗin kwalliya. Ina tura masa ya rubuto cewa,kin manta da na gyaran jiki. Na yi 'yar dariya shidai Yaya baya rabo da ɗorawa kansa ɗawainiya. Umma ta tashi hankalinta game da kayan ɗaki da safe ta aiki Jamila a kira mata aminiyar ta Umman Amina. Jamila bata jima da da wowa ba Umman su Amina ta shigo, ina jin su daga ɗaki Umma tana faɗa mata zancen kawo lefe, ta ce tunda sunyi lefe maganar kaya katako muma dole mu dage ko ba masu tsada bane. Ummansu Amina ta ce, "Haka ne, dama abinda yasa na ce abar batun kayan katako a sai ka tifa da kayan girki saboda ya ce ba matsala kuma ba shi halin lefe akwai wata mafita guda ɗaya in har Abban su Baby zai yarda, akwai masu bada taimako na kayan ɗaki wani foundation mai suna Zeena. Umma tace ina jin su a Radio suna yi wallahi. Umman su Amina ta ce Da sai a rubuta takarda a tafi da yarinyar a kai musu in so samu ne yau ɗinnan. Umma tace ai damuwar da ƙyar Abbansu ya yarda Umman su Amina ta ce " Akwai mafita, Baby ba tana nan ba, tazo yanzu in faɗa mata abinda zata rubuta ni sai in sata a gaba mukai takardar." Na ɗan zaro ido a inda nake a laɓe, Zeena sune waɗanda Yaya ke yiwa yaron shago fa. Ƙwalamin kira Umma ta yi, na amsa naje a kace in ɗako takarda da biro na ɗakko. Muka zauna Umman Amina tana faɗamin ina rubutawa. Neman taimako ne dan Allah an saka bikin har ana ta ɗaga wa saboda. ba'a samu kayan ɗaki ba, har ma maganar tana nema ta lalace. Wai in sa cewa ni marainiya ce. Sai na rubuta iyayena basu da hali gashi an saka auren kusa. Da na gama aka sa lambar wayata da ta Umma. Ummansu Amina ta ce shirya maza bari inje in barwa Amina sallahun girki, tana fita nace A
Umma Hajiya Zeena ita ce Uwar ɗakin Yaya fa, Mahaifiyar mai gidansa da muka je. Tace "Tofa!" Wannan shine ga ƙoshi ga kwanan yunwa, bari ta zo inji ya za ayi." Data dawo Umma ta faɗa mata halin da ake ciki, sai ta ce ai mu ofishin su na Foundation ɗin zamu je,baza su sani ba ma bare yaji labari. Muka hau Adaidaita sahu zuwa titin Ɗanbare muka je wata Zeena plaza mun shiga ofishin muka gaida wadda muka samu, sannan muka faɗa mata buƙatarmu tace yaushe ne bikin mukace kwana shabiyu, ta ce shine zaku kawo takarda yanzu? Umman Amina ta ce 'yarnan ku yi haƙuri da muna sa rai cewa zamu iya sayen kayan ne sai kuma muka ga ba wata mafita. Ta amshi takardar ta buɗe ta karanta,ta yatsina baki, ku ba ma marainiya ba ce kenan? Kuma gashi babu sa hannun ta bare na mahaifinta. Umman su Amina ta lankwashe murya kamar marainiya tace mana a taimaka mana. Matar ta ce gashi nan an rubuta iyaye na basu da ƙarfi." Umman Amina ta kalle ni, na sunkuyar da kai, tace Hajiya ita ce ta rubuta bata iya rubutun bane a taimaka. Ta yatsina fuska. "Sai ku haifi yara ku kasa amfana musu komai,Hajiyar bata shigo ba,in ta shigo zan bata amma bana sa ran zaku samu domin an cire list na wannan wata." Ta kalli Umman Amina "Kamar kun bada ajiya sai a ƙurarren lokaci irin wannan." Umman Amina sai haƙuri take bata tana roƙonta, ita kuma sai yaɓa mana magana ta ke yi. Baƙin ciki kamar in fice ko in hau matar da duka,ta kalle ni, wannan ce mayar kenan Umman Amina tace ita ce. Ta taɓa baki. "Kada kiji haushina yarinya laifin iyayenki ne, zan bawa Hajiya takardar ku in ta shigo suma suna da bikine bata zuwa sosai. Nan dai mukayi godiya muka fice.
Na ce da Umman Amina wallahi dama a kyale su, dubi yadda sai wulaƙanci ta ke mana. Umman Amina tace ai haka suke irin waɗannan aiki fa aka ɗauke ta karɓar takardar neman taimako, amma sai kace itace ta ce zata bada sai irin wannan rashin mutunci ta ce yi.
Umma bata faɗa wa Abbanmu ba, musamman da taji rashin tabbacin abin. Umman Amina tace in shirya in raka Amina kasuwa zata sai anko da mayafi. Nace to sai dai muje da kyalle tunda mu namu a gurin Safara aka siya. Tace bana son kayan Safara dan zata bada bashi saita Linka kuɗin ga rashin haƙurin bashi. Nace Umma da da kuɗi da kin bada na Jamila da yadin da kika ce zaki sai wa su Jafar da Habu. Tace sai in bada a kuɗin gudunmawar da 'yan Kurna suka aiko jiya, Allah ya rufa asiri kar in Lodi bashin Safara bayan biki ta uzzira min naji da naki saura dubu biyu da naira hamsin. Nace to maje gobe,ranar da za 'a kawo lefena kenan. Gidan su Zuhra za akai, gidan wan Abbanmu. Na shirya nasa doguwar baƙar riga da mayafi Amina ta zo har zamu wuce Umma tace kije gidansu Zuhra jiya Ummansu ta aiko tana tambayar inda za a samu anko.
Muka biya, nan "yan matan gidan aka taso, amarsu mai magar zuma, yau zamu sha lefe. Na ce ku ta lefe kuke. Ina Umma zamu kasuwane sayen anko. Murja tace Zuhra ce zata siya. Umman su ta fito muka gaisheta,ta taɓe baki, "Kaga 'ya'yan aminai to Zuhra ta baku saƙo ko kuwa ta biku?" Nace ta zo muje mana tafiyar zata fi daɗi. Dama tsararmu ce Tare mukayi Candy sai dai makarantarmu ba ɗaya ba, domin su ta kuɗi suke zuwa kasancewar Abbansu ya fi namu ƙarfi.
Muka hau adaidaita muka nufi kwari nace kai gabana sai faɗuwa ya ke yi, bansan ina ne gefen su Yaya ba, fatan karya ganni,sai ƙara kaɗe ƙura nake. Muna ta yawo sai wani ya amshi kyallen yace wannan kayan Zeena plaza ne. Gabana ya faɗi. Na tsaya cak, nace bari in baku kuɗi kuje ku siyo harda ta Jamila. Zuhra tace "Me yasa?" Nace a ɗaya daga cikin irin waɗannan kantunan ya ke yaron kanti. Amina ta ce to ai ba lallai shi a wannan yake ba. Nace to muje. Muna shiga wanda ya kawo mu ya tambaya ko akwai sauran wanna kayan?" Wani ya amsa ya duba yace akwai, muka shiga ƙaton kantin wani yace mu zauna a kawo mana saboda nan ba a bada ɗai ɗai sai dozin bari ya karɓo a ɗaya shagon.
Shamaki ya ɗaga robar ruwan paro ya sha ya aje yana sake juya katin hannun shi, ko shakka babu wannan katin daga makarantar su Baby aka kawo masa gayyata da kuma takardar neman taimako. Yanzu a yaya zaije, ya mata alƙawarin zaije mata yaga karatunta kuma zata so ta ganshi a gurin ƙila ma har ta nuna wa ƙawayen ta cewa ga wanda zan aura. Sannan a ɗaya gefen Hajiya bata son yana wasa da zuwa irin waɗannan wuraren da ake bawa Allah rance. Ya kuma ya jingina bayansa da kujerar ya lumshe ido dan neman mafita. Ya buɗe idanu ya zuba a kan fuskar laptop ɗin dake gaban shi wadda ta ke hasko mishi ko ina na Kantin sama da ƙasa. Ya tsura ido akan wasu 'yan mata dake zaune kan wasu kaya. Ya ɗauki wayar kantin ya danna kira Ɗahiru ya ɗaga, yace suwaye zaune akan kayan nan wasu "yan mata su uku?" Yace Atamfar nan mai ganye suke so, Hassan yaje kawo musu. Shamaki ya ce in yazo kace ya zo ina kiranshi kafin ya sallame su.
Zungureriyar motar ta tsaya a ƙofar gidan Yayan Abban su Baby, Bala direba bai manta gidan ba,dan haka ya fito yace bari ya yi sallama. Wani saurayi zai shiga gidan Malam Bala yace, yaro, dan Allah in kashiga ka yi mana sallama da mai gidan. Tare suka fito domin yasan da zuwansu bayan azahar kamar yadda Abban su Baby yazo ya sanar da shi tun jiya, dan haka ma bai fita ba, kuma ya sanar da ƙaninsu da kuma maƙotanshi kamar yadda suka saba duk lokacin da wani a cikinsu zai karɓi kaya irin haka. Suka gaisa da Malam Bala, sannan ya dubi yaronsa da ya yi sallama da shi, yace Halifa a fito da tabarmi ga baƙin sun iso bari kira Malam liman ya danna kiran maƙocin nasa yana faɗa musu sun iso, dama da suka yi azahar ya tuna musu. Ya kira Abban su Baby ya ce,kazo sun iso, ka taho da ruwa da Lemon kar ka manta. Nan suka hallara sai aka buɗe kujerar baya aka soma fito da akwatuna na zamani haka ma but ɗin motar. Guda shidda ne masu kyau daga gani an zuba kaya masu tsada. Abban su Zuhra ya ce, ba sai an buɗe ba, Allah ya sa albarka ya bada zama lafiya. Suka ɗakko ruwa katan biyu Lemo katan biyu suka ce gashi. Har kawun Aliyu yace su barshi,sai Abban su Zuhra ya ce, ko dai ya yi kaɗan ne?" Suka ce a a haba ba haka bane, Liman da suka zo dashi ya ce a karɓa Allah ya sa albarka.
Suna tafiya aka shiga da kaya ciki dama su Umman su Zuhra suna ciki sun ƙosa su gani koda abin arziƙi ita da yaranta. Nan kuwa jiki yayi sanyi domin Atamfa tirmi talatin ce ga lesuna ga Shadda da dogayen riguna abin dai na girma. Suka haɗa kaya suka aje,tace Hajara kije ki cewa Umman su Baby azo a ɗauki kayannan. Abbansu Zuhra ya ce, ina za a kai su tun yanzu, a bari mana 'yan uwa su gama gani." Tace a a kar wani abu ya ɓace gani da 'yar mata a zarge su, gara akai can kowa yaje can ɗin ya gani.
Ta ƙwarzaba dole yace su Halifa su ɗauka su kai. Suma 'yan lungu suna ganin ana shiga da akwatuna, nan da nan labari ya karaɗe kaffatanin lungun an kawo lefen Baby. Umman su Baby ta aika Jafar ta ce ya kira mata Umman Amina. Itace ta saka ido akan kayan saboda maƙota sun tsaya sai sun gani ba iyayen ba ba yaran ba. Kowa ya sha mamakin kayan Umma kasa magana ta yi saboda tunanin ta kayan ɗaki, suma sun fita kunya,ko da yace baya so shi dai a shiryen sa yake.
Bayan mutane sun watse Umman Amina tace, gaskiya wannan kaya babu batun haƙura da kayan ɗaki. Tashi za kiyi mu koma can gurin tallafi in ba haka ba za aji kunya. Umman su Baby ta ce sai gobe dai yanzu su Baby basa nan ga kayan mutane. Umman Amina tace "To goben dai ya zama da wuri fa insha Allah kamar ƙarfe goma.
Jamila ta yi ta murna da ta dawo makaranta ta ga lefe tace amma gaskiya Yaya Aliyu da tanadin sa, dubi kaya kamar kati!" Umma tace gaskiya ya bada mamaki ya yi mamaya.
Muna jiran mai kawo mana zani, jim kaɗan sai gashi muka karɓa muna dubawa,ya faɗa mana kuɗin. Cikin mamaki na kalli Zuhra kinsa Safara dubu da ɗari biyar ta ɗora akan duk turmin atanfa ɗaya. "Amina tace shiyasa Ummanmu bata yarda da siyan kaya a gida." Zuhra tace dubu da ɗari biyar ta isa ayi ɗinki. Yaron ya katse mu ga ruwa. Ya miƙo mana ruwan Paro mai sanyi. Nace harda ruwa ku ke bayarwa? Yace mai gida yace a baku don daga gani kun gaji. Zuhra ta kalli wanda ke kan teburin a zaton ta shine mai gidan ta ce mun gode.Sai nima na dube shi nace Allah ya saka da alkhairi. Na basu baya ina shan ruwan kamar yadda suma suka nutse a shan ruwa.
🖊️
[3/16, 13:09] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Free Page 9*
Na tuna da yadin su Jafar na cire robar ruwan daga bakina, na dubi wanda dai ya kawo mana atamfar nace, don Allah kuna saida yadikan maza masu sauƙi haka ko shadda irin ishirunka maraya ɗin nan? Yace "Bama sai dawa sai kun koma kan wannan layin nan."
Nace wai gashi mun gaji kyanshi daga nan mu fita. Na zaunen ya ce Ɗahiru zo mana. Yaje, jim ya dawo ya ce ƙanwata kawo a yanko miki yadin, nawa ne kuɗin kuma wace kalar kike so? Nace yadi huɗu ne kala kuma irin dai ta maza ƙanne na za a ɗinkawa. Ya amshi kuɗin ya fita. Abinda ya faru shine Shamaki ya tattara duk wani kallonshi ga motsinshi akan Baby data yi magana sai ya bugawa Hassan waya yana tambayar shi metake so, sai ya sanar dashi, sai yace ka sa Dahiru ya amshi kuɗin ko nawa tazo dashi ya je can shagon ya ɗakko mata shadda yadi biyar,amma karya sake ya ce mata komai, ya bata kawai ya amshi kuɗin. Hassan cikin mamaki ya ce,to Allaji. Muna zaune ya kawo shadda mai kyau, nace gaskiya wannan ta yi sauƙi, amma ka duba ko nawa na baka kuwa? Yace "Na gani ita kaɗai ta rage shiyasa aka bar miki a haka." Nace to mun gode. Muna fitowa bakin shagon sai ga wani mai adaidaita kamar mai jiranmu, nace ɗan agundi. Yace "Dai-dai ina?" Amina tace ko bakin ƙofa ma sai mu ƙarasa. Zuhra ta ce nawa zamu baka? Yace "Ku hau muje kawai. Muka kama hanya. Sai dai yana sauke mu ya wuce wai mubar kuɗin. Muka cika da mamaki sannan muka masa godiya tare da hasashen ko wata ya ke so a cikinmu, amma me yasa bai tambayi lambar waya ba. Haka dai muka wuce zuwa gida muna al'ajabin ɗan sahu. Tun da muka shiga lungun yara suke bamu labarin wai an kawo lefena. Gabana ya faɗi, muka shiga gidanmu har su Zuhra. Mun cika da al'ajabin kaya wanda hakan ni ma ya sa na fara tunanin kayan ɗaki ya wajabta aka iyayena.
Hajiya ta kalli ɗan 'uwanta bayan ya gama yi mata bayanin irin karɓar da akayi musu,yace dattawa ne gaskiya Allah ya sa alkhairi. Ta numfasa, "To sannunku da ƙoƙari kuma Allah ya ƙara zumunci." Yace amin ni zan koma,tace babu damuwa sai ka jini. Bayan fitar shi ta jingina tana nazari,ko shakka babu tunda ɗan uwannan nata ya ce dattawa ne ta tabbatar da hakan, domin da akasin hakanne ba abinda zai hana shi faɗa. A yadda ta karanci yarinyar a ranar da ta zo ta fito daga ƙaramin iyali, kuma kamar ba masu ƙwaɗayi bane, tasan cewa daga lokacin nauyin wannan iyalin zai iya hawa kansu, amma bata son abinda zai wuce gona da iri. Gidanta fadarta ce duk wanda ya shigo dole zai zama a ƙarƙashin ikon ta. Rawar kan Shamaki ya yi yawa a wannan auren ko na farko bai rikice haka ba bare sauran abinda ya ke bata haushi ma yadda yarinyar ta ke kamar an daurawa ƙashi fata, yaron ta lafiyayye ne kuma ta jima da fahimtar cewa shi ɗin mabuƙaci ne, ta yarda cewa ya yi haƙuri shi ne ya sa yanzu ta yarda da wannan auren na gaggawa duk idan ta dunƙule damuwar guri ɗaya tambayar ita ce yarinyar zata iya sama masa gamsashiyar natsuwa?" Bata da tabbacin wannan amsar dan haka dole ya sake aure ba da jimawa ba,domin samun ƙarin wadda zata tare wannan matsalar, zata yi tunani akan yarinyar da Maman Umar ta yi magana. Ta tashi zaune ta zuba wa Azima ido wadda ke zuba mata furar da Juma da dama mata aƙaramin firji da ke kusa da ita wadda ta ke sha bayan la'asar. Tana baiwa Azima duk wata kulawa da wasu ciye ciye na zamani domin amfanin ɗanta,amma har yanzu Azima yar shekaru sha huɗu ce, yar ƙaninta ce data ɗakko tun daga bakin yaye. Tana son Azima ta tashi da irin tarbiyyar da take son matar ɗanta ta kasan ce,sannan Malamin su ya faɗa mata cewa Azima ita ce zata haifi ɗa namiji tare da Shamaki. Sanin Shamaki ba zai jira ba shine yasa ta barshi ya yi duk auren da zai yi kafin Azima ta kawo,kuma Azima ce zata zama Hamshaƙiya a cikin matan sa. ƙaran da wayarta tayi ne ya maido da hankalinta ta kalli wayar wadda ta ware ce don yin magana da iya 'ya'yanta kaɗai. Maryam ce ɗaya daga cikin 'ya'yanta, Ta ɗauka sannan ta ɗaga, ta sa a kunne, acan ɓangaren Maryam cikin girmamawa tace,, "Hajiyarmu barka da yamma." Hajiya ta ce Maman Nana kun dawo ne?" Mun dawo Hajiya sai muka kaji biki kamar daga sama. Hajiya ta ce Allah ya kawo lokacin. Maryam Tace to Allah ya kai mu, zamu shigo anjima da Dadinsu Nana yace in gaisheku kafin mu zo. "To Allah ya muku albarka amma kice masa nace dan Allah kar a zo da wata gudunmawa domin nasan halinsa." Maryam ta yi yar dariya Ɗazu yake ce min ya yi oder wata mota wadda zai bawa autanki a saka lefe a ciki a baiwa Amarya. Hajiya ta yi yar dariya ƙasaita. Ai ba irin wannan yarinyar bace, wata 'yar tsuntsuwa ya samo gata nan dai, kuma gidansu in aka kai wani kayan tsorata za su yi suga kamar za a sayar musu da 'ya, bare a haɗa da mota. Maryam tace Tofa! Bana kuma 'yar talakawa ya samo kenan? Hajiya ta ce haka ne sai dai kuma suna da dattako a yanzu, ba mu san ya zasu nuna a gaba ba." Maryam tace Allah ya sa su ɗore, domin haka mutane suke, in sun samu guri sai su nemi wuce gona da iri. To zan kira Maman Iman in faɗa mata wai ta saka order ta wasu lesuka. "Ki faɗa mata har A'isha duk ki sanar da su, kar kowa ta ɗaga hancinta,ankan wata gudun mawa, lefen ma an kai shi ɗazu. Nan dai suka yi sallama bayan sun tattauna tana Allah ya sanya alkhairi.
Shamaki ya sakko su Hassan suna tsegumin ba susan ya sakko ba, sai yaji suna fadin. Maigida wa yake so a cikin yaran nan Ɗahiru ya ce abin da mamaki irin fa yaran geto ɗin nan ne wasu kyamusassu shi da za ayi auran sa kwanan nan. Hassan ya ɗago daga kallon laptop ɗin da ke gaban shi ya ce "Kaji yadda ya ke min magana a gigice kuwa. "Hassan! ku tabbatar kun samo musu Ɗansahu su bar kasuwar nan. Suka kwashe da dariya bayan Hassan ya kwaikwayi muryarsa. Shamaki ya yi gyaran murya, nan da nan suka haɗa hankalinsu cikin kunya suka yi shiru. Yace "Gara dana ji ku, wadda zan aura tana cikin waɗannan yaran da ku ke yi wa ba'a. Kuma za ku je kuna neman wata alfarma agurinta wata rana. Hassan ya ce tuba muke maigida Allah ya taimaki maigida ayi haƙuri ba mu sani ba,sai ya fasa maganar da zai yi ya juya ya barsu cikin zullumi da kunya.
Washe gari Abbanmu yana fita Umma ta ce Allah ka gani saboda fita kunya zan fita ba izinin Abban Baby Allah ka sa muyi nasara. Lokacin da suka je sakatariyar bata fito ba, suka zauna suna jira kamar yadda Umman Amina ta bada shawara. Sunfi ƙarfin awa ɗaya sannan sai ga ta ta iso a wata mota. Har da duƙawa suna gaisheta, a wulaƙance ta kalle su,sannan ta kauda kai tana tambayar lafiya? Umman Amina tace dan Allah ki taimaka mana a matsayinmu na mata 'yan uwanki, mune muka zo shekaran jiya don Allah ki taimaka.
Ummansu Baby tace, Ki rufa mana asiri abin nan ya ƙarato gashi... Matar ta ce dan Allah ki min shiru ,me zan muku? Inje in buɗe store ince ga kaya ku ɗiba?" "Me yake faruwa?" Suka ji an tambaya daga bayansu. Duk suka waiwaya. Hajiya A'isha ce wadda Shamaki ke bi mata a haihuwa, kodayake ta bashi shekaru kusan takwas. Itace mai kula da ɓangaren Foundation ta kalli su Umma sun tsugunna a gaban Raliya. Tace ba yin Allah ku tashi,ke buɗe Office su shiga. Ta ci gaba da faɗa,bansan so nawa zan faɗa miki ba, ki daina wulakanta mutane . Wannan Office ɗin saboda su ne muka buɗe shi,kema kuma aikin su ki ke yi. In ba masu buƙatar me za mu yi a nan kenan? Raliya ta shiga bada haƙuri tana faɗin jiyan nan suka kawo takardarsu kuma suna maganar bikinsu sati mai zuwa. Umma ta kalli A'isha tace Hajiya kamar yadda Allah ya rufa miki asiri muma ki rufa mana, ba mu da wata mafita ne bamu zo da wuri bane domin muna sa rai cewa zamu iya siyan kayan .Sai kuma akayi rashin dacen samun kudin. Ko iya gado ne a taimaka Hajiya Aisha tace, "'yar waye a cikinku?" "Yata ce, inji Umman Baby. "To ina mahaifinta?" Ta jeho tambayar. Yana nan amma bashi da ƙarfi wallahi leburane ya buga ko ina amma bai samu halin yi mata kayan ba, ko iya gado ne ku taimaka mana sai mu kaita. To Shikenan zan taimaka amma sai na ga mahaifinta,sannan zan san ya za ayi a saka takardar ku acikin jerin na wannan wata ukun, duk wata uku mutum goma mu ke ɗiba mutum talatin a shekara ai muna ƙoƙari bafa gwamnati bane mu. Su Umma suka ce gaskiya kuna ƙoƙari muna godiya Allah ya saka da alheri ta ce "Ba komai ku zo da mahaifin nata sai munyi masa tambayoyi sannan mu bashi takarda ya cike. Ta dubi Raliya "Dakko min takardar su." Haka suka yi mata sallama suka tafi.
Tunanin Umma tun a hanya shine yadda zata tunkari Abban Baby da zancan nan gani take ba zai yarda ba. Umman Amina ta ce ki bari zanzo in same shi da maganar sai muji me zai ce,ai in ba wai ya samu wata mafitar bane ina mai tabbatar miki da gudu zai yarda. Ummansu Baby tace Allah yasa.
Sun dawo gida suka tarar 'yan Kurna sunzo ganin lefe,ni kuwa dawowar su Umma ta min daɗi domin Yaya na ta kiran waya ina cewa ya yi haƙuri zan kira shi masu ganin lefe ne suka zo. Umma na zama suna gaishe gaishe ni kuwa na miƙe na shige ɗakin mu da sauri na kira Yaya sai da ta yanke zan kuma kira sai ga kiran shi ya shigo. "Baby." Muryar shi ta ratsa cikin kunnuwa na, cike da kasala nace na am. Yace zan miki wata tambaya nace ina jin. ka. "Ke budurwa ce? Gabana ya yake ya yi wata mummunar faɗuwa, cikin rawar murya na ce Yaya ban fahimta ba. Yace kawai ki bani amsa,ke budurwa ce ko kuwa wani abu ya taɓa budurcin ki? Tambaya ta biyu kin iya girki?" Na ce, Kaji wani labari ne game da ni? Yace "Banji ba, amma akwai wata al ada wadda Hajiyata take rayawa,na tabbatar zata yi wannan al "dar a kanki kamar yadda ta yi a sauran mata na,ina son ku faɗa min gaskiya domin in ne mi mafita kafin ranar, saboda Baby wallahi ni kaɗai nasan me nake ji a kanki bazan iya fassara wa ba ai game da son ki." Na numfasa Yaya ina da tabbcin cewa ni budurwace amma bani da tabbaci akan budurcina. "Kamar yaya?" Ya katseni. Nace to ni dai ban taɓa ko wasan banza da wani namiji ko wasan duka banayi har bare ya kai ni ga ashsha, amma wannan ba shine zai sa in yi tutiyar budurcina ba tun da ance yana samun matsala da kanshi. Game da girki kuma irin namu dai na iya nasan kuma shi ku ke ci. Fara da wake mai da yaji, irin su taliya ɗinnan da manya. Kuma na iya tuwo harda ɗan wake sosai,jalaf ma dai zan ɗan iya tunda mukan yi jifa jifa. Ya yi shiru har sai da na ce kanaji na kuwa Yaya?
🖊️🖊️🖊️
[3/18, 17:14] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Free Page 10 Karshen free Pages*
*DIJENGALA ENTERPRISE*
*07031121981*
*Ina Mata 'yan gayu masu son kayan gayu kuzo ga dama ta samu* *DIJENGALA ENTERPRISE ta kawo maku Kayan masu kyau da inganci indai mace tasan gayu to* *DIJENGALA ENTERPRISE ne wajen siyayyar ta.*
💯 London laces
💯 London lafaya
💯Switzerland laces
💯 Dubai laces & Lafaya
💯veils
💯 Atampha
💯 shadda
💯 Voile
💯yadika na maza
💯caps
💯 Necklaces etc...
*Kayan mu ba Wanda suka cika gari bane,bazaki gansu a ko ina ba shiyasa ake mana kirari da Auntyn Gayu ko me kika siya a gunmu zaki ji dadinsa* *07031121981 Ina Wanda zasuyi biki su rasa abinda zasu saka suna tunani kar suyi iri daya d wasu Don Allah ku tuntubeni* *07031121981 zaku Sha mamaki🤔sarkokinmu ba kowane wuri zaku samesu ba wlh sai wurin ya ansa sunansa, haka Laces dinmu ma na daban ne daga Company sai wajenmu💯🥰💞*
*DIJENGALA ENTERPRISE*
Umman Amina ta shigo ƙarfe goman dare ita da Amina, duk muna kwance tsakar gida saboda yanayin zafi. Abbanmu yana banɗaki, ta zauna suna ƙara tattauna yadda zasu yi wa Abba maganar. Ni kuma muna 'yar hira da Amina da Jamila,. amma hankalina baya tare da su, na kan tuno da Yaya ɗazu da muna waya. Bai kuma ce min ƙala ba ya kashe wayarsa, na kira bai ɗaga ba. Tambayoyinsa sun caza min kai kuma al adar da yace Hajiyarsa ta na da ita wadda ya tabbatar za ta gabatar a kai na, suma suna sani faɗuwar gaba. Zan so ya min bayani sosai, sai dai a yadda na soma karantar halinsa, ba lallai ya kuma ɗakko min maganar ba.
Jamila ta girgiza kafaɗa ta tana cewa Amina tana miki magana tunanin me ki ke yi? Na sauke ajiyar zuciya na dubeta me kika ce Amina? Tace Duk tunanin auren ne haka, ina tambayar ki ne za kiyi lalle a saukarku ne?" Nace a'a' ba zai fita ba har inyi na biki. Jamila tace gaskiya kam. Sam ban lura cewa Abba ya fito daga banɗaki ba,sai dai na ji muryarsa ya na faɗin gaskiya talauci na da lalacewata da rashin godiyar Allah na duk basu kai haka ba. Gara inci bashi domin nasan zan biya." Umma ta ce to amma kasan shima bashin ba a samun sa ko? Yace to in ba a samu ba sai mu kaita a haka domin shi yace baya buƙata,me zai sa mu ɗaga hankalinmu akan wannan. Har zuwa yanzu baya ga dubu hamsin kuɗinta da aka kawo bani da ko taro, kuma ban damu ba. Allah ne zai mata komai,amma bana son in kuma jin zancan neman tallafin nan,bayan mun karɓa sai munje 'yan jaridu sunyi hira da mu, an yaɗa a kafafen yaɗa labarai cewa gamu an ba mu, sannan mu yi godiya, ga Allah, shi mijin ya ji zai ɗauke mu da daraja ne?"
Umman Amina ta ce yanzu sai abarshi kenan Abban su Baby bayan ita mai gurin ta karɓi takardar... Ya miƙe tare da tsaki. "Ni kunga fita ta." Ya wuce abinsa. Umma ta ce kin gani ko wani Lokacin Abban su Baby hutsune, da ki ke ganinsa. Umman Amina tace da Abban su Amina zai yarda ai sai muje da shi a madadin Abban su Baby.Umma ta ce, da zai yarda ai da mun fita kunya. Ina jinsu abubuwan sun min yawa, banda ina jin wani mahaukacin son Yaya Allah da na fasa auren nan,kowa cikin damuwa da zullumi ga shi karatun saukar nawa ma duk na kasa nutsuwa inyi maraja'a a gida. Gashi daga gobe an gama sai kuma a filin sauka.
Shamaki ya yi jugum, bashi da wata mafita face ya gana da 'yan uwanshi matan nan su tattauna a samu mafita. Ya ɗaga waya ya kira Maman Umar ta ɗaga da faɗin autan Hajiya, yace Maman Umar fatan dai kina lafiya da yarana duka. Tace "muna lafiya Auta." Yace ba haushe dai yace Babbar ya Uwa ko? Tace "Tabbas." Yace to zan kawo kukana gurinku ku duka, ba ƙara zan kawo ba, fatan zaki banbance ko? Tace "Na banbance." Yace don Allah ki tara su zanzo da magariba gidanki zamu yi wani zama yau ɗaya a tarihi ba tare da Hajiya ta sani ba, kuma karma taji labari. Maman Umar tace "Baka da matsala auta yanzu duk zan kira su." Suna yin sallama ta kuwa kiransu ta sanar da su.
Tun biyar suka haɗu kowacce ta ɗauki mota ta zo. Suna ta hirar su abin gwanin ban sha'awa cikin wasa da dariya. Maman Umar tace "Ni yanzu ko ɗinki ban bayar ba bansan ma wane kayan zan ɗinka ba. Fatima tace naga wasu lessis da atamfofi na tashin kai, har nace zan kira Shamaki ya kamata su kawo irin su. Aisha tasan san Fatima da gayu ta ce Maman Iman a ina kika gansu? DIJANGALA ENTERPRISE Na sha mamaki kunsan ni duk inda kayan gayu yake zaku ganni a gurin kawai naga tallar kayan na duba naga laces yan London da lafaya da atamfofi abin dai sai kingani, naga Number wayar kamfanin, na kira da ta ɗauka mukayi magana ta turo min ke kinga atamfofi na tashin kai.Maman Umar tace kin gansu a hannu ne wasu fa duk hoto ne. Maman Iman ta ciro waya ta fara nuna musu kaya, tace sune na faɗawa Maman Nana cewa na saka Oder kayan London ai ba acan London ɗin na saka ba, gurin wannan kamfanin na sa, gobe zan karɓa. A'isha tace "In naga naki sai in siya nima amma dai in Hajiya taji zata ce duk irin kaya da muke da su a ZEENA baza mu bawa kanmu ƙaruwa ba. Maman Umar tace ai ko ita taga abinda ya birge ta ko muna dashi sai ta siya. Yasunan kamfanin ki ka ce? Maman Iman tace DIJANGALA ENTERPRISE Karki damu zan kawo muku kayan ku gani. Ni Ko tun a waya sun yi min. Suna ta labari har sai da sukaji kiran salla sannan biyu suka tashi suka tafi salla,biyun kuma suka ce basayi.
Umar ne ya shigo daga masallaci yake sanar da Momyn su tare da Uncle Shamaki suka yi sallar magariba a masallacin layinsu.Maman Nana tace har ya zo kenan. Umar yace e mana cikin massalacin. Suna cikin magana sai ga sallamarsa. Suka amsa suna yi masa sannu gami da sunan tsokanar da suke faɗa masa wato ƙaraminmu babbanmu. Yace ga ni nan a bi ni a hankali ko in ƙi sa wa kowa hannu a takardar. Suka sa dariya,ya zauna aka kawo masa abinci dana sha. Ruwa kawai ya ɗauka ya ɗaga robar ya sha kusan rabi sannan ya aje. Ya kalle su, halin da nake ciki bazai barni in iya jin yunwa ba.
Suka tattara hankalinsu akan shi cikin kula kowacce ta zaƙu ta ji menene damuwar ɗan ƙanin na su. Ya numfasa, kafin in yi maganar sai kun min alƙawarin cewa wannan iya ni da ku ne, Hajiya bazata sani ba. Suka ce karka damu. Maman Umar ta ce ranar da ba Hajiyar mune dai iyayenka ba wai ina mana fata bane. Sukace tabbas haka ne. Ya numfasa, Ɗazu ina kasuwa ka wai sai abin ya faɗo min, Hajiya kusan har yanzu akwai wasu al'adu da bata sake su ba duk da cewa ta amshi zamani. Maman Nana tace "Waɗanne iri?" Yace kamar batun cewa sai ta sani ko matar da na aure ta zo da budurci, saboda yanzu zamani da cima ba irin ta da ba ce likitoci suna ta bayani. Maman Iman tace "To menene abin damuwa akan wannan?" Yace dole in damu,karki manta aure na huɗu zan yi, kuma wannan matsalar ita ce silar rabani da Maman Meema mata ta ta farko tun daga tambayoyin da Hajiya tayi min a ranar farko da na kwana ɗakin na bata amsa tace gaskiya banyi aure ba, tace yarinyar ta gama bin mazanta ta ɗora mata karan tsana,wanda hakan ya janyo nima naji na tsane ta. Haka ta rayu da mu duk da bata rasa komai ba amma tana yaye Meema ta zaɓi ta bar gida kamar na mu mai cike da daula, ta koma gidan iyayenta duk da cewar suma ba wai talakawa bane. Haka nan na sallame ta Hajiya ta sa aka haɗa mata da goma ta arziƙi kamar dai yadda kuka sani. Kinji ɗaya. Ita kuma Maman Mubina kunsan daga girki a nan aka fara samun damuwa, domin da Hajiya ta yi min irin tambayoyin da tayimin a daren farko da muka kwana sai na faɗa mata irin abinda ta ke buƙatar ta ji, don haka sai tace to bisa al'adarta za a haɗa komai na girki ta fito ita ce zata ciyar da ƙawayen Hajiya da sauran "yan biki da girkin da ta yi da hannun ta. Sannan tazo ta zuba wa kowa da kanta. Wai manufar haka a ga ko ta iya girki,in kuma ta iya a gurin zubawa a gani ko marowaciya ce ko kuma zata iya jan ragamar gidan a matsayin ta na matar jigon gidan. In baku manta ba,itama anan aka soma samun matsala. Wadda ta zama kullum cikin faɗuwa a duk wata jarabawa da Hajiya ta yi mata. Bisa ga wannan dalilin itama ta ce ta gaji dole na sallame ta kamar yadda Hajiya ta bada umarni. Ya numfasa ta ƙarshe Maman Anisa. Ta tsallake maganar girki da wani budurci domin ita Hajiya sai da ta tsaya ta tabbatar ban yi mata ƙarya game da daren farko ba.Sannan Maman Anisa ta iya girki da kayan ƙwalam na fulawa ina ji a jikina za mu zauna na har abada da ita domin ta iya duk wasu dabaru na riƙe zuciyar miji, to sai Hajiya ta hango aibun wannan kular da ta ke bani, tace ni ne jigon gida kuma ni ne sirrin gida babu wani dalili da matata zata san komai na gidan dan haka in tsuke baki na kar ta na jin komai daga gare ni. Haka na yi wa Hajiya alƙawarin ta dai na sanin komai, to amma na kasa daina faɗa mata musamman in ta sani farin ciki na rasa labarin da zan bata kuma ni labarin kasuwa nafi sani. To Hajiya ta zafafa akan hakan kuma ita bata nemi saki ba,Hajiya ta nemi a sahale mata tare da bata tukwaici irin wanda aka ba 'yan uwanta na baya. To Ni kunji damuwa ta Yarinyar nan da zan aure na ɓoye mata ko ni waye, 'yar talakawa ce, kuma ƙarama ce bata kai shekarun Matana na baya ba. Sannan wata babbar matsalar ina yi mata wani irin so wanda bazan iya fassara shi ba. Ta kai bani da control ɗin kai na game da ita, har yaran Kantina su Hassan sun fara yi da ni akan soyayyar ta. Bana son mu samu wata damuwa da Hajiyata amma nasan zata yi ƙorafi game da soyayyar Baby. Haka ga matsalolin farko dana lissafa muku, ba lallai yarinyar nan ta na da wannan budurcin ba kuma hakan ba yana nufin ta bi maza ba ne, likitoci sunyi bayani zai iya tafiya da kanshi sakamakon cima da wasanni na makaranta tsalle tsalle da guje guje to in aka yi wa yarinyar hukunci da cewa ta bi maza ai bamu yi mata adalci ba. Wannan shi ne kukana. Maman Umar ta numfasa ta kalli sauran ta ce "Ni a nawa ganin Hajiya ba ta yi wannan bane domin ta takurawa rayuwarka, tana yi ne domin ta inganta rayuwarka da mu gaba ɗaya, ka taɓa tambayar dalilin da ka samo suna Shamaki? . Sannan ita ta ba mu kulawa mai tsanani da lallaɓa rayuwarmu domin ganin mun kai mutuncin mu gidan miji, in ka fahimce ta to zaka gane dalilin da take yi maka kiwon Azima. Ta fannin rufe sirri ga mace kuma shima sai inga cewa hakan shima daidai ne, domin kai ne kan komai na gidan dukkan wata dukiya da muka mallaka kai ne ka san komai,lauyoyinmu ma su kula da dukiyarmu kai ne suka sani. Duk wani kaya dazai shigo da kuma wanda zai fita sai ka amince na dukkan rassanmu na jihohi. To mai ɗauke da irin wannan nauyi dole ne ya zama baya cikin shagala ko wani abu mai kama da ɗauke hankali. Ina fatan kun fahimci me nike nufi. Duk suka ce haka ne Shamaki ka yi nazarin maganar Maman Umar.
Maman Nana tace kuma gida kamar namu ba zai kyautu ace marowaciya ce matar gidan ba, akwai hikima cikin gwaje gwajen da Hajiya ta ke yi wa matanka, kuma zaka gane haka nan gaba. A'isha ta ce "Ya kamata dai ta janye maganar budurci nan saboda dalilan da Shamaki ya bada gaskiya haka ne, inzan bada misali da kai na, kwanaki Afra ta faɗi a banɗaki har ta yanke ta gabanta mukaje asibiti damuwata kar dai ya taɓa mata matanci likita yace ko da ya taɓa ba bu wata matsala ya kuma yi min bayani irin wanda Shamaki ɗin nan ya yi. To in kun kula da maganar likita kwalbar nan ta yanke wa yarinyar wannan yanar da ake magana to sai aure ya kai ta inda ake irin wannan al'adar ta ya zata wanke kanta?" Duk suka haɗa baki gurin cewa babu. Shamaki ya yi zugum yana tunanin amsar da Baby ta bashi, "Ni budurwa ce amma bani da wani tabbaci akan budurcina." Ya numfasa, daidai lokacin da Maman Iman ta ce "Ina ganin tun da yanzu duk mun yarda cewa Hajiya ta na kan gaskiya sai dai ɗan gyara kaɗan ta yaya zamu sha kan hakan?" Shamaki yace Yawwa an zo inda nake son a zo, gyara nake so ya kasance in nayi aure na yi kenan kamar yadda ku ke da mazajenku. Ba shakka ina son nima in zama cikakken mutum in kare mutuncina ku sani baya ga karewar Ubangiji matan da suke kawo kansu gurina da yanzu na canza layi na shiga bin matan banza tunda kuɗi suke buƙata ni kuma bani da matsalar kuɗi. Suka ce haka ne Allah ya ƙara karewa. Maman Umar ta ce "To ni a matsayi na na babba a cikin ku kuma wadda in aka samu kuskure a zaman nan laifin zai iya dawowa kai na ina son in baku dama ku kawo na ku shawarwarin sai in haɗa da nawa sai mu tunkari Hajiya. Sai dai amma ina son ku tuna wasu abubuwa kafin ku kawo shawara. Wacece Hajiyarmu? Ya kaifin basirarta yake? Kuma me zata iya amincewa dashi? Ina sauraronku mu fara da Maman Nana tunda ke ce mai bina sai mu gangara har zuwa Shi Shamakin namu.
*Alhamdulillah a nan na kawo ƙarshen free Pages, waɗanda basu biya ba sai suyi ƙoƙari su biya dan samun cigaban labarin,zaku turo ₦600 ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn shima ta wannan number 08140004302*
🖊️🖊️🖊️
Leave a Comment