Daudar Gora Book 2 page 34

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (34)



..........Wani irin tashi tsigar jikinta ta shigayi da salon kallon nasa, yayinda bugun zuciyarta ke amsa kuwwa cikin ƙirjinsa. Numfashi ta ɗan ja a hankali ta maida idanunta ƙasa, batare da ta sake gigin ɗagowa ba dan haka yafi mata kwanciyar hankali.

         Ganin bazatace koman da yake buƙatar ji ba ya wani ɗauke kai gefe cikin son basar da shock ɗin da ya fahimci maganarsa ta jefata yana wani lumshe idanunsa. Sai kuma ya buɗe da sake juyowa ya ɗan ɗage gira sama, “Tunda bakin ya mutu mu cigaba da maganarmu ta ɗazun?, dan da gaske ina son muyi aiki tare”. 

       Ƙin ɗagowa tai yanzun ma ta jin jina masa kai kawai alamar eh. Shiru ya ɗanyi na wani lokaci kamar mai tunanin abinda zai fa ɗa, sai kuma ya nisa da ƙyar ya furta, “Abinda ya faru ki ɗaukesa kamar bai faru ba, tana cikin fushine kawai. Duk abinda kike buƙatar sani da ga gareni na baki da ma”.

       Yanzu ma kanta ta jinjina masan tana wasa da yatsunta, ta fahimci akan mahaifiyarsa yake magana. Batare da ta dago ba ta ce, “Miyasa ka yarda da ni, bayan na sanar maka duk abinda ke raina game da kasancewa da kai? Har ma na aikata, na kuma amsa na aikata”

     Ɗan murmushi ya saki kaɗan yana mai bin yatsun kafarta da take wasa da su da kallo, sai kuma ya kauda kan gefe yana ɗan lumshe idanun da buɗewa. Kai daka ga yanayin nasa ka tabbatar bazai iya jure doguwar maganar ba, duk ma a takure yake da yawan surutun. Iffah da ke binsa ta kasan ido da kallo sai ta samu kanta da kasa daina kallonsa, a zuciyarta kam ayyanawa ta ke (murmushi yana masa ƙyau). Kamar ya fahimci mi take ayyanawar kuwa ya tsuke fuskar. Wayar da ya ajiye a gefensa ya ɗauka, yay ɗan rubutu ya ajiye gabanta. Rinannun idanunta ta sauke akan wayar.

      _“Ki faɗamin gaskiya ya akai kika san an saka abubuwan can na ɗazun?”._

     Shayinta ta cigaba da sha kamar bazatace komai ba. Sai kuma taja ajiyar zuciya, cikin muryar nan tata dake shaƙe ta bashi amsa. “Kamar yanda na sanar maka a mafarki na gani. Iya gaskiyar kenan”.

       Bawai bai yarda da ita bane, dan ya fahimci ita tana cikin mutane marasa ɓoye abinda ke ransu koda kuwa laifi ne a kansu. Amma zuciyarsa rawa take da amsar tata kasancewar al'amarin bazai kama hankali ba, musamman ga irinshi da ba wani gama sanin abubuwa irin waɗan nan yay ba da ƙyau. Wayar ya sake ɗauka ya rubuta, “Miye alaƙar wanda kukai aikin farko da wannan?”.

       Wayar ta ajiye tana ɗan murmushi, “A baɗinin abinda na gani suna da alaƙa, a zahiri kam bani da shaidar tabbatar da hakan dan ni kaina ban yarda mafarki na zai zama gaskiya ba”.

          “Ina son na sansu”.

      “Bita kawai kake buƙata amma nasan ka sansu”.

   Jin yayi shiru ta sake nisawa da ajiye kofin. “Bayan nan mi kake son sani?”. Kansa ya jinjina mata alamar babu. Ta ƙara faɗin, “Ni zan iya tambaya?”. Nan ma kan ya jinjina mata alamar eh. 

     “Kace baka san duk matan da aka aura maka ba sai ni, a ɗan gajeren labarin da naji kuma ance sai an kawosu sashen nan suke rasa ransu ai, bayan mutuwarsu ka taɓa ganin gawarsu?”.

       “Miyasa kike son sanin wannan?”.

  “Saboda kace zamuyi aiki tare”.

“Wannan baya cikin aikinmu”.

“Shine mafi muhimmanci ma acikin aikin da zamuyi tare, dan nafi alaƙa da shi fiye da wanda kake son alakantani da shi. Inaji a jikina mutuwar matanka bata da alaƙa da yunƙurin waɗan nan Uncle's ɗin naka. Su  nasu yaƙin da banne da wannan”.

        Kallonta yake kamar idanunsa zasu zubo. Itako ta kauda kan gefe kamar ba daga bakinta lafuzzan suka fito ba.

       “Mi kike son faɗa?”.

    “Abinda ya dace ka faɗa kafin faɗata. Ni nasan kasan su wanene Uncle's ɗin ka da burinsu a kanka. Masu kashe matanka kawai kake buƙatar sani in har da haske bakai bane ba”.

      Tsabar yanda maganarta ta masa dirar mikiya a zuciya da brain bai ma san sanda ya juyo da ƙyau yana fuskantarta ba. Eh tabbas ya jima da sanin su wanene Miran Arshaan da Miran Jasim har da ma burinsu a kansa, tun kuma randa ta bashi guba yaji a ransa su ɗinne, hakama kisan matansa da su yake dangantawa, su kuma yake bibiya da son tabbatarwa. Amma magana mafi ɗaukar hankalinsa da ga gareta furucinta na ƙarshe. “Basu bane ba fa?”. Zancen zuciya ya fito fili batare da ya sani ba. 

        Jajayen idanunta ta zuba masa kai tsaye, sai kuma ta saki murmushi mai ciwo. “Sultan ban shigo masarautar RUMAN domin kallon gine-ginen ƙawa da adon zinari ba. Idanuna a buɗe suke fiye da yanda na mage basa barci a cikin dare. A tunaninka na baka gubar da suka bani ne dan ka mutu?”. Ta juya idanunta da suka fara bashi tsoro ma shikam tana sakin ƙayataccen murmushi. “Lala-lala, madarar dana baka sam bata da alaƙa da wadda suka kawo na baka, wadda kuma na baka ɗin tun usil dama bata kisa bace” tai wata ƴar dariya mai ƙayatarwa. “Kayi haƙuri, su fa wawayen karatunsu karanta musu yake amfani suke da ni, basu san Fhareedah bint Zayyan bace ke amfani da su. Bari dai na taƙaice maka karna jaka da nisa. Ni da kaina na kawo kaina nan domin tabbatar da waye masheƙin ƴan uwana. Bani aka kawo domin bama kariya ba....”

         Gaba ɗaya Tajwar Eshaan yama kasa gane suma yayi ne? Ko kuwa ya zama butun butumi ne oho shi bai sani ba. Abinda kawai ya sani idanunsa nakan aljana zai kirata ko mima bai tantance ba. 

       Iffah da ke wata ƴar dariya ƙasa-ƙasa ta yunƙura zata sauka a gadon ganin kamar ya zama gunki ne ma oho. Cak ta dakata jin an riƙota, maidota yay ta koma inda ta tashin yana binta da wani irin shegen kallo data kasa bama fassara. 

            “Wacece ke!?”.

      Kalmar data iya fitowa a bakinsa kenan a cikin dubunan da ke masa kaikawo. Da gaske idanunsa razanata suke, dan haka ta kaudar da natan tana cigaba da murmushinta. “Nikam maimaita wacece ni ko bitar karatu ne ya kamata an haddace. Amma kayi haƙuri, Fhareedah bint Zayyan ce, mai jiƙaƙƙen shirin tarwatsa masarautar ruman kamar yanda suka tarwatsa min ahalina. Wlhy da gaske nake bana yafiya, in har nace sai nayi to sai nayi ɗin koda zan ƙarasa da bugun numfashina na ƙarshe.”

        “Kin san zan iya kasheki a cikin ɗakin nan na binne gawarki kamar ba'ayiki ba”.

      “Shiiii!!”.

    Ta faɗa a hankali da ɗaura yatsanta saman tausasan lips ɗinsa, cikin raɗa-raɗa da ƙyaƙykyafta idanunta cikin nasa dake neman tsaida numfashinsa ta furta, “Da hakan kake da tuni kayi, amma nasan kai ba mai kisa bane bin Haysam Abdul-majeed Qutb....” sai kuma ta saki murmushi tana lumshe idanunta da har yanzu basu washe da ga shaƙar da Malikat Bushirat ta mata ba, tare da yo ƙasa da yatsanta da ke kan lips ɗinsa a hankali tabi takan kakkauran wuyansa tayo ƙasa kan ƙirjinsa da tai matuƙar dannewa kafin ta taɓa ɗin, a saitin zuciyarsa ta tsaida ɗan yatsan da buɗe idanunta dake lumshe. “Wannan zuciyar zinariya ce mai hasken diamond dake bugawa da harbawar numfashin duk wani talakan ƙasata, ba ita kawai ba, kai a karan kanka ZINARE ne ESHAAN”. Ta ƙare faɗa tana mai daddaga yatsan nata akan saitin zuciyar tasa idanunta na cika da hawaye....

         Ji kawai yay ɗan sauran ƙarfin da ya rage masa ya ƙarasa guduwa. Gaba ɗaya jikinsa da yay mata runfa shima ya ƙarasa saki. Miya rage kuma? Miya rage masa da zai faɗa akan wannan aljanar yarinyar yanzu kam? Taci nasara, kawai taci nasara.....


      🥱 Iffah! Iffah! Anya ke ba aljanar da Shahan-shan ɗin yake ambata bace. Ni ma dai ƴar koran taki na sallama a wannan gaɓar.🚶


       ★★.....  ★....


    “Ashe abin kunyar da wancan wawan yayan naka ya aikata mana kenan yau a gidan nan?. Wai shi sai yaushe zai san ya girma ne? A haka yake tunanin mulkar jama'a ko gidansa bai iya adalci ba mtsowww!!”.

         Fuska Miran Arshaan ya yatsine cike da rashin damuwar zagin da Ameera Haifah ɗin kema ɗan uwansa Miran Jasim. A hankali ya zuƙa karan haɗaɗɗiyar tabar da sai lokaci-lokaci yake ɗan sha shima ya fesar. “Kin kirani nan ne domin zagin wani ko yin abinda ya dace?”.

    Tsaki ta ɗan ja tana balla masa harara, “Naga kaima zagin nasa kake ai. Abinda ya dace ɗin kuma ai duk dai a kansa ne. Dan kasan tunda wannan tsohon munafukin Sayeed Fayzul-haq ya sani shi da tsohuwar can sai wannan maganar taje gaban wancan ɗan ALLAH bani in raya gorin (Tajwar Eshaan take nufi🤭), yana sani kuwa kowa kamar ya sani ne, ga shegen yaron nan da kaifin basirar tsiya matsiyacin wlhy zai iya bin ta hanyar ya gano abinda yake fafitikar son ganowa dare da rana. Wlhy na tsani yaron nan shi da uwarsa, dan duk abinda ubansa yamun a kansa zan rama har sai naga baya numfashi a duniya zan huta”.

     Saurin kallonta yay, Dan shi fa wannan tunanin ma baizo kansa ba yanzu tsabar abubuwa sun ma kansa yawa..........✍️


No comments

Powered by Blogger.