Bakar Inuwa 25

 


Episode 25_*



..........*_8:15pm_* 


       Gagarumar dinner ɗin da su Alhaji yaro glass da Shugaban ƙasa mai sauka suka shiryama su Ramadhan ɗin ta fara gudana. Ƴaƴan manya ne da manyan ƙasar kansu kawai kake gani a wajen. Amarya da ango sunsha ƙyau har sun gaji. Dan zaman

bayyana ƙawatuwar shigarsu da docration na wajen ma ɓata lokacine. Anci ansha daga kayan daɗi kamar babu gobe. Yayinda ango ya hana amarya tashi daga inda suke zaune ko sau ɗaya. Dan haka wanda sukai musu liƙi ma anan suka iskesu wajen zamansu sukayi. Cake ma nan aka kawo musu suka yanka a zaunen basu tashi ba. Humm sabon salo kenan wai rawa agaɓar gacci. Dan kuwa ƴan jarida da masu jiran ayi suce tuni sun sami abin faɗa. 

     Sai faman cece kuce suke na cewar wai mi Ramadhan ɗin ke ɓoyewane da ya hana a ga matar tasa yanda ya kamata. Dan kuwa duk da kwalliyar da taci yau fuskarta sanye take da facemask, kuma shine da kansa ya sanya mata sanda suke tahowa a mota. Ita kanta ta kasa fahimtar minene dalilinsa na son ɓoye mata fuska a duk sanda suka haɗu? Shin *_BABU SO! MIYA KAWO KISHI?!_* (Wannan littafi na nan tafe a gareku ba babu so miya kawo kishi? Insha ALLAH😉🤗😄). Bata da mai bata amsa dan haka ta haɗiye a ranta.

        Ƙarfe sha biyu dai-dai aka tashi, bayan mawaƙa kala-kala sun baje basirarsu tunda daga kan na hausa har zuwa na turanci. Hakama masu wasan barkwanci. Kamar sanda suka taho yanzu ma sun koma gidane bisa tsaron na musamman daga jami'ai. Kamar kuma ko yaushe har suka iso ɗin ko kallo bai haɗasu ba ita da shi balle magana. Yay mata rakkiya har ɗakin Anne da basu riga sun iso ba su yay wucewarsa nasa part ɗin ya barta da sakin numfarfashin data tara a ƙirji. Duk da ko sau ɗaya bai wani taɓata ba, dan ko hannunta bai riƙeba a wajen dinner ɗin ƙamshin turarensu ya cakuɗe dana juna har baka iya banbance wanda take yi saboda ƙarfin nasa, ta kwanta lamo a gefen gadon Anne batare data iya cire ko zobe a yatsanta ba. Batasan mi zatai tunani ba a yanzu, girman mijin nata a mulki, ko auren nasu da baida alƙibilar kwatantawa?. Rabuwa da iyayenta ko shiga BAƘAR INUWAR da su suke hasashen Ni'imtacciyar inuwa ce a gareta?. Manufar su aunty Hannah a kan kashe su, ko tsananin ƙiyayya da ƙyamar da take hange a idon uwar mijinta da sai a yau wajen dinner tasan matsayinta na mahaifiya ga Ramadhan ɗin?. *_“Ya ALLAH kaji tausayina. Nayi tawassali da sunayenka ƙyawawa masu tsarki. Da kai na dogara dan bani da kowa sai kai ɗin tun farkon fari. ALLAH ka ƙyautata ni'imarka garemu a ƙarƙashin wannan BAƘAR INUWA da kowa kema kallon Ni'imtacciyar inuwa a garemu.”_*

    Hawaye masu zafi suka gangaro daga cikin idanunta zuwa kumatunta har saman facemask ɗin fuskarta da ta gagara cire koda shi ne. A wannan yanayin gidan ya fara ɗaukar hayaniyar mutane alamar an dawo dasu gida suma. Dole ta miƙe ta fara zare sarƙa da tarkacen jikinta gudun kar Anne ta zargi wani abu. Duk da kuwa a ranta yanzu hankalinta yafi karkata da kwanciya akan ta tunkari Anne da batun da taji a bakin su Aunty Hannah. Sai dai kuma bata son tozarta yayar mahaifiyar tata dan koba komai bata da kamarsu a duniya, tunda gashi har ana aibantata da halayensu da suka aikata tunkan haihuwarta.


★★★


     WASHE GARI aka gudanar da rantauwa ga shugaban ƙasa da gwamnoni. Kum harda Raudha shugaban ƙasa Ramadhan yaje wajen. Sai dai tana cikin dogon farin hijjab da facemask yau ma. Abin ya sake burge jama'a musamman talakawa. Da kuwa idan akai dubi da yanda mafi yawan matan gwamnonin suka cakire cikin shiga ta rashin mutunci da kece raini a yau ɗin. Ga gwalagwalai dake ƙyalli da walwali a jikinsu tako ina. Hatta da Hajiya Fanta da aunty Hannah matan vice president shigar tasu ba'a magana. Sai dai a kallo guda zaka gane ran Hajiya Fanta a ɓace yake saboda kasancewar aunty Hannah a wajen bayan mijin nasu yace mata da ita kaɗai zaije banda Hannah. Dan tunda aka maida aurensa da aunty Hannah suke tafka rigima har yanzu kuma babu daɗi a tsakaninsu, tace sai ya saki aunty Hannah ɗin. Shiko ya tabbatar mata hakan bamai yuwuwa bane dan Hannah nada muhimmanci a tafiyarsa ta yanzun.

       Ga ƴan siyasa kuwa sai suka fara takale-takale da zungure-zunguren batun saka facemask da amaryar ta shugaban ƙasa ke yawan yi, dan tunda ya far bayyanata wa duniya ranar zaɓe ba'a taɓa ganin real face nata ba sai da facemask. To yau ma al'amarin yaci uban na da, dan farin siririn gilashi da Raudha ta saka a idonta saboda kumburin da ya ɗanyi na kuka da rashin isashen barci ya ƙara mata wani ƙyau da burge mai kallo. Ga facemask da ya saka ba'a ganin ainahin face nata kuma. Sai haka ya zam ba'a ganin komai nata a waje sai tafukan hanunta kasancewar hijjab ɗin data saka mai hannu ne.

    Uban gayyar shima fararen kayane a jikinsa na wani haɗaɗɗen boyal ɗinkin babbar riga. Ya kawo hularsa tangaran data fita a fice ya murza. Bayan kammala Rantsuwa suka wuce wajen bikin da aka shirya gudun mawa da ga Mai-martaba. Ƙarfe biyu aka tashi aka dawo da Raudha kawai gida, shugaban ƙasa Ramadhan kuwa gidan gwamnati aka tafi masa rakkiya. Bayan idar da sallar la'asar aka gabatar da walima da addu'oi daga manyan malamai har zuwa ƙarfe shida na yamma. Daga haka taro ya tashi lafiya kuma zuwa anjima za'aima amarya rakkiya gidan gwamnati insha ALLAH tunda angonta ya tsufa acan.


         ★★★_______★★★


     An yima amrya shiri na musamman domin miƙata gidan gwamnati da zasu zauna insha ALLAH. Ba wasu mutane masu yawa bane zasuyi rakiyar, dan haka da wuri aka kaita ga gimbiya Su'adah da su Adda Asmah da sauran matan Pa su Hajiya Mufida.

       Duk da a lulluɓe fuskar Raudha take da golden color na veil hakan bai hana gimbiya Su'adah jefa mata kallon tsana ba. Da ƙyar ta iya dauriyar cewar “ALLAH ya bada zaman lafiya”. Daga haka ta tsuke bakinta. Sai su Addah Asmah ɗinne keta karaɗin kwarara addu'oi ga amaryar da ango. Abinda gimbiya Su'adah tayi yasa mutane da yawa fara tsarguwa, dan kuwa basuji daɗin yanda ta sallami surukar tata matar ɗanta na farko ba kuma namiji tallin tal.

        Raudha da dai ba sanin mi ake ciki tai ba. Dan kanta a duƙe kuma a lulluɓe. Tunda ba wani farin sani tai musu ba bata iya tantance muryoyin da sukai magana ba. Daga part ɗin Gimbiya Su'adah part ɗin Hajiya Shuwa aka nufa da ita. Itako ta mata ƙyaƙyƙyawar addu'a harda ƙyauta da babu wanda yasan minene a cikin dan an riga anyi packaging nashi da leda mai ƙyalli alamar gift. Hakama Hajiya Mufida tarba ta mutuntawa taima amaryar da doguwar addu'ar zama lafiya harda fatan nan da baɗi a sake taron suna. Itama dai tayima amarya ƙyautar cheque na kuɗi da babu wanda yasan adadi tunda a ninke takardar take. Sai wani ɗan box a cikin ƙaramar bag.

       Bisa jagorancin Hajiya Mufida aka kai Raudha ga Pa. Inda shima yay masu doguwar addu'a da nasiha ga Raudha tare da ƙyautar key na mota galleliya. Sai sashen su Yafendo inda can ɗin ma tasha addu'oi da kyauta ga dangin su Ramadhan ɗin. Daga haka aka sake maidota wajen Bappi da Anne suka sake musu addu'oi, Bappi ma yay mata ƙyauta a dunƙule wadda babu wanda yasan minene. Hakama Anne, koda yake gara na Anne da alama harda kayan turare dan ƙamshinsu tuni ya addabi hancin kowa. _Sisters turarurrukan *AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902* daban suke dana saura. Zaka tabbatar da haka ne kawai yayinda ka mallaki naka. Ba turare kawai take saidawa ba. Harda kayan gyara amarya galla-galla na musamman da sai an gwada akan san na ƙwarai. Sirrinsu daban ne, idan nace na daban, ina nufin na daban dana saura😉😘😘🤗_.


       Har cikin mota Anne ta kawota, tare da sake musu addu'a domin tuni ango shi ya shiga fadarsa. Amaryarsa kawai yake jira a kai masa.

          Har suka iso a tafiyar da bata gaza mintuna a shirin ba saboda jiniya da aka sakama motocin yasa akaita basu hanya, wannan yasa suka iso cikin ƙanƙanin lokaci. Amarya dai bata buɗe ido ba yanzu ma. Sai dai kunnuwanta naji mata yanda ƴan rakiyar tata ke ta yaba wannan katafaren gida first class. Tsirarun ƴan uwanta kuwa da akazo dasu rikicewa sukai. Bataga laifinsu ba, dan masu shiga ƙasashen duniyar ma da kuɗin ƙugunsu sun yaba balle su.

       Ita dai babu komai a ranta sai addu'oi, dan zuciyarta sai faman tsinkewa takeyi musam da kalaman su aunty Hannah ke dawowa a cikinta tamkar bitar karatu, sai dai Alhmdllhi mafitar data samu a safiyar yau da matakin data ɗauka tana fatan zuwa yanzu an kauda matsalar farko da takema fargaba kafin masu zuwa. Kamar yanda Anne ta gargaɗeta da yin addu'a haka ta dingayi a duk takun da zatayi har suka iso ainahin cikin babban falon farko na gidan.

      Gaban Raudha yay masifar faɗuwa. Tai azamar rumtse idanunta tana ambaton sunayen ALLAH masu tsarki, daga haka bata sake fahimtar komai ba har suka iso inda aka sanar mata falonta. Kamar yanda Hajiya Zuhrah da suka iske gidan suna jiransu ta ambata, ita da ƙanen Ramadhan biyu dake aure Mardiyya da Safina, sai wata cousin ɗin su Pa itama mace mai kirki hajiya Mariya, tun sanda za'ai rakkiyar shugaban ƙasa suka shigo tawaga akai masa rakkiya tare da su.

          “Inaga mu barta iya nan kawai, shi mijin nata idan ya shigo da kansa sai ya kaita ɗakin da yaga ya dace su zauna ko?”. 

    Cewar Hajiya Mariya. A tare su hajiya mama suka nuna gamsuwa. Sai dai aunty Hannah ta taɓe baki dan tasan sun riga da sun zaɓa musu ɗakunan da zasu rayu ta hanyar saka ƙaramin symbol a saman ƙofar bedrooms ɗin ta ciki bisa shirinsu. Dan haka cikin kwantar da murya tai magana tana duban hajiya Mariya da murmushi. “Amma auntyna ayi amarya a falo? Kodai muyi haƙuri a kaita nata bedroom ɗin yazo ya sameta kamar kowacce amarya shima, koba komai zai tabbatar shima a yau ba shugaban ƙasar NAYA kawai yake ba, ango mai amarya fil a ledarta ne”.

     Yanda ta ƙare maganr da ɗan shakiyanci ya sakasu sakin dariyar manya. Hajiya Mariya mace mai sauƙin kai da fahimta. tace, “Kumafa kin fini gskiya ƴar uwa, dan gara ya tabbatar da gaske muke yau muke son jika da izinin ALLAH”.

     Nan ma dariyar suka sanya, tare da kama Raudha da kanta ke lulluɓe har yanzu, dan sam bama fahimtar zantukan nasu take ba ita kam. Har bedroom ɗin da suka zaɓa mata aka kaita, sai dai kuma an samu akasi ba wanda su aunty Hannah suka tanada dominta bane. Amma batace komaiba, ta barwa ranta zata dawo da kanta tasa Raudha komawa can ɗin cikin sauƙi.

      Anan ma dai su Hajiya Mariya Nasiha suka sake mata mai ratsa jiki, kafin su tattara su fito suna mata sai da safe.

      Sai a yanzu Raudha ta samu damar rushewa da kuka. Ta zame ta kwanta kan katafaren gadon da tasan ko bata kallaba ya haɗu harya gaji. Ji take inama ba'a haifeta tazo duniya ba, inama Abbansu bai saki momynsu ba har sukazo Bingo. Inama ranar batazo idi ba har ƙaddara ta sakata shiga hurumin Alhaji Hameed Harith Taura. Inama... Inama.... Inama. Sai dai bakin alkalami ya bushe, bushewa irin wadda idan akace sai an tausasashi karyewa kawai zaiyi yabar tawada dabin yatsun hannu.


     Kuka taci sosai a wajen har kusan rabawar dare, Ba kuma tako ɗaga mayafin nata ba balle ta kalli wani abu daya shafi ɗakin kamar yanda bata kalli falon da gidan ba sanda zasu shigo, wani wahallen barci da zazzaɓi suka fara fisgarta, duk da kuwa kafin yau tasan tana da burin ganin fadar shugaban ƙasa tamkar kowane ɗan ƙasa. Har lokacin babu angon nata babu alamarsa, ta riga da ta fidda rai da shigowarsa, duk da dama bata sanya ran hakan ba tun farko. Tasan bata kai kodarajar ma'aikatan gidansu ba. Ya amshi aurentane kawai saboda halacci ga kakansa. Bazai sota ba, kamar yanda itama batajin son sa ko kaɗan a ranta. Sai dai tana tausayinsa matsayin shugaban ƙasarta dake cikin wani tarko mai wahalar sha'ani da nazari ga wanda baida yawan maida hankali akan abu. Harga ALLAH tana cikin razanin zantukan su Aunty Hannah har yanzu. Dan ko maganar aunty Hannah taji a kwanaki ukun nan ji take kamar ta saki gudawa a wando saboda razana da mamaki. Yanzu miya kamata tayi a wannan ranar da tasan shugaban ƙasa zai fara kwana a ɗakin da take da tabbacin an haɗa Poison da suka ambata cikin ac ɗin tunda bata da tabbacin saƙonta ya kai ga Bappi zuwa yanzun? Zata fito ta sanar masa ko zata jira taga idan saƙon nata yay nasarar kaiwa, ko yaya zatayi?. Wa zata tunkara da sauran batun ya bata shawara ne? Idan ta samu nasarar daƙile wannan ta poison ɗin ac?. Wane damar yunƙurine da ita a wannan dare na farko a gareta na shiga BAƘAR INUWA tare da shugaban ƙasarta?, idan tayi yinƙurin faɗa masa ya tuhumeta da a ina ta sani wace amsa zata bashi?, idan ta iya faɗa masa komai tanada tabbacin zai yarda ba turotan sukai ba kamar yanda su can yake a garesu zasuyi amfani da ita ne wajen cutar da shi. (“Ki daina yaudararsu, ki kuma tabbatar musu ke *_BAƘAR INUWA ce_*. Idan kikai wasa da gargaɗina ni zan zame miki *_BAƘAR INUWAr_* da sai kin gwammaci *_GARA RANA DA NI!_*) furucinsa a randa ta fara ganinsa a TK special hospital tare da kakansa, cikin halin ciwo take amma ya rumtse ido ya faɗa mata waɗan nan kalaman da tasan sune gaskiyar abinda ke a ransa. Inaga yanzu kuma da take cikin mugun ƙullin da bashi kaɗai ba, mutane da yawa ma idan suka ji bazasu fahimceta ba. Dan kuwa ba kowa ya gama yarda domin ALLAH ta bama dattijo Alhaji Hameed Taura garkuwa ba ranar idi, ciki kuwa harda mijinta, shugaban ƙasarta kuma a yanzun..

     Da wannan tunanin barcin yay galaba a kanta.........✍


No comments

Powered by Blogger.