Rabi Danja Complete Hausa Novel

 


🥰rumaisaaliyuinuwa🥰: *💫RABI DANJA💫*           

                     *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA


          *marubuciyar Littafin 1- RAUDHA*

               *2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

        *3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*





           *Littafin RABI DANJA yazo muku da sabon salo wanda ban taɓa zuwar muku da irinsa ba, wannan salon na daban ne, dan haka ku biyo ni danjin yadda zata kaya a cikin sabon littafina mai suna RABI DANJA.*



*Ban yarda wani ko wata ya juyan Littafi na ba fasaha tace dan haka idan kika/ka juya min tofa kasan menene zai fito a bakina ba komai bane sai nabar mutum da fitowar rana da faɗuwarsa, kuma idan littafina yayi dai-dai da rayuwar ka/ka to ban sanki bama bare na rubuta labarinki, wannan daga ƙwaƙwalwata yake kuma banyi da zummar cin zarafin kowa ba.*





*Inaiwa ɗaukacin musulman duniya BARKA DA BABBAR SALLAH BABBA, ALLAH YA MAIMAITA MANA YA KAIMU BAƊI.*




*Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai, ina fatan samun nutsuwa da zallar  fasaha ya Assamadu, ka bani dama na rubuta abinda ya dace, Allah nayi tawassali da kyawawan sunayenka guda ɗari babu ɗaya ka dafa min ya hayyu ya ƙayyum.*




          *Na sadaukar da wannan littafi ga Ƴan uwana jinina ababen tinƙawona masu sanya ni farin ciki da walwala, sune rayuwata, Yaya Sa'adatu da Ƙanwata Khadija Maman Abuturab da Unaif, Allah ya wanzar da farin ciki a cikin rayuwarku ya dafa muku ameen.*




*Fatan Alkhairi gare ku Ƙungiyata abar tinƙawo na wato ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION Allah ya ƙara ɗaukaka mu mu zaga inda zato bai taɓa zato ba ya hayyu ya ƙayyumu.*




*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




page *1-2*

>>>>>>>>>>>>>"Kaiiiiiii Malam Ubanka", ta faɗa tare da rugawa a guje har zanin dake jikinta yana niyyar kwancewa, shima wannan mutum bai ƙasa a gwiwa ba ya rufa mata baya suka bawa hammata iska, gudu take sosai dan ganin ta ƙarasa mafakarta, shima gudu yake domin ganin ya kamota ya hukunta ta, abinda zai baku mamaki babba ne shi sosai dan sosai zaiyi jika da wannan ƴar ƙaramar Yarinya, sai hanya ake basu  dan kaucewa bangaza daga gare su dan kowa yasan halin wannan Yarinya wajen tsokana da neman tashin hankali ga al'ummar gari, sai dai kowa yasha mamakin ganin magidancin da suka kaso tsere da wanga Ƴar jaririyar Yarinya.





Cikin ikon Allah ta iso wani madaidaicin gida ta afka, shima wannan mutum bai ƙasa a gwiwa ba ya rufa mata baya har ciki,.




"Ni Saratu ina wannan Yarinyar ta shiga tin sha ɗaya na safe har yanzu shuru, kuma na aika ko ina bata nan, ni dai Allah yasa tana cikin ƙoshin lafiya ya kare mana ita a duk inda take", cewar wata matashiyar mata da baza ta wuce shekara Arba'in ba, tana zaune tana shirya Carbi, ga sunan a gaban ta da yawa da alama sana'arta ce, wani matashin mutum ne ya fito daga bayan gida da alama ruwa ya kama, ya kurkure bakinsa ya zubar ya aje butar yana gyaran murya, "ai Innar Rabi kema dai kinfi kowa sanin tana lafiya, tinda batin yanzu ba hakan take faruwa idan ta fice sai sanda hali yayi zaki ganta Allah dai ya shir......", bai ƙarasa faɗa ba yaji anyi tafiyar yaji da shi har wularsa na faɗuwa a ƙasa, Innar Rabi kuwa da take shirin Carbi gaba ɗaya ya kelaye a ƙasan siminti ya watse, ɗaki ta shige ta banko ƙofa, basu gama tsaida hankalinsu ba suka ga ƙaton magidanci a tsakiyar tsakar gidan su yana huci da numfarfashi, Baban Rabi da ya ɗakko hularsa a ƙasa yana kallon ikon Allah da rana tsaka, "lafiya Malam me haka ka shigo gidan mutane da girmanka da komai", cewar Baban Rabi.



"Wallahi bamai hana ni cin uwar wannan Yarinyar, harni zata kira ta zaga wai Ubana, yana ƙasa ƙasa ta rufe masa ido, to wallahi ku fito da ita na dake ta dan kutumar ubanta", cewar wannan mutum.




Cikin mamaki Baban Rabi yake kallon wannan mutum, dan shi mamakin abin yake na wannan mutum, "Amma malam bakada hankali, ka keto hanya da girmanka da komai ka biyo ƴar tatsitsiyar Yarinya ka kuma keta shari'a ka shigo har gidan mutane kace kuma mu fito maka da Ƴa ka daka, harda zaginta, to ka fice min da gani kona tara maka mutane wallahi".




"A'a Baban Rabi kayi haƙuri kayi masa uzuri na tabbata bashida lafiya, dan da lafiyayye ne bazai shigo mana gida kuma yace mu kawo masa ƴar mu ya daka ba gashi geme-geme da shi", cewar Innar Rabi da lamarin mutumin yasa take tunanin ya kwance.




Wannan mutum jin za'a tara masa mutane yasa ya ce "Wallahi ku rubuta ku ajiye duk inda naga Yarinyar nan saina mata mugun dukan da saita dena ganewa", yana faɗa ya ja tsummar babbar rigarsa ya fice.





Kallon juna Inna da Baba sukai kana suna murmusa dan lamarin mutumin da tabbacin baida lafiya ishashshiya.






"Rabi zonan", Baba ya ƙira ta, ta taga ta ƙyallo idanunta manya dasu sunyi zuru-zuru ta ce "Baba na gaji bacci zanyi, idan ma na fito zancen ɗaya ne zaku tambayeni ne mai nayi wa wannan mutumin, kuma ba haka kurum na zage shi ba, masifa naga yana yiwa wata mai saida Ƴar bagalaje shine na zage shi, kai wallahi na gaji bacci zan Baba na gaji", tana gama faɗa tabar jikin tagar tayi kwanciyarta a kan gadon Innarta.





Fatan shiriya sukai mata dan lamarin Rabi yanzu ya fara sawa suna tunanin anya ba Aljanu ne a jikinta ba, dan idan tana abu kamar ifritu, bata ji ta addabi maƙota da mutanen gari, kullum ne Allah mai kullum sai an kawo ƙararta daga sassa daban-daban na wannan gari, shi yasa aka sa mata *RABI DANJA*, hatta baƙo yazo garin to indai ya haɗu da Rabi saita san yadda tayi ta nemi tarangahuma awajensa, Iyayenta har taimako suke nemowa Rabi amma abu kamar gaba-gaba yake, yanzu Addu'a kawai suke mata.






Wannan kenan




Comment ɗinku shine ƙwarin gwiwa ta, ku sambaɗo comment kuyi ta ganin posting akai-akai.






*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*




*By Rumy*

[30/06, 3:03 PM] 🥰rumaisaaliyuinuwa🥰: *💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 3-4*

>>>>>>>>>>>>>Saida taci baccinta hankali kwance ta farka da ƙiran sunan Allah a bakinta tare da Adduar tashi daga bacci, sunan Inna take ƙira, Inna dake Madafa tayi mata banza tana cigaba da sakin ɗanwake.




Gajiya tayi da ƙwallawa Inna ƙira ta buɗe  ɗakin ta fito tana mitsitstsika ido, buta da ɗauka ta nufi bayan gida bata jima ba ta fito tayi Alwala tayi sallarta kamar ba ita ce wannan RABI DANJAR ba mai neman tashin hankali kullum, tana idarwa dama sallar la'asar ce, zuwa tayi ta gaida Inna da take madafa, amsawa tayi tare da nuna mata kwanon Abincin ta, kalla tayi ta ce "zan ci Inna bari naje gidan su Kattume na amso littafina yanzu zan dawo, kafin Innar tayi yunƙurin mata magana ta fice a guje, girgiza kai Inna tayi.





Tana fita tayi cikin unguwa, cincirindon mutane ta gani shiya ɗau hankalinta ta nufi wajen, ture mutane take a wajen tana kutsa kai wajen dan ba tsawo ne da ita ba balle ta gani daga baya, tana isa ta hango faɗa ake wasu mata  sai dambe suke a bakin hanya kuma gasu kitika-kitika, sai yagar juna suke suna nishi, wata tsohuwa sai son raba su take ta kasa da take sai a bangajeta ta dawo baya, faɗi take "wallahi Biba da Baraka kun shiga uku a rayuwar ku, kishi hauka ne kunzo bakin hanya kuna saida hali, kamar balamomi, shashashun banza da wofi", sosai take faɗa har jijiyoyin wuyanta suna fitowa sa bo da masifa.




Rabi tana tsaye ta gama haddar abinda wannan tsohuwar ta faɗa, ta matsa kusa da matan da taji ance kiahiyoyin juna ne basuyi aune ba suka ji idanuwan su cike da ƙasa rabuwa sukai da juna kowacce ta fara murza ido tana son ganin  ta ya dawo, ɗayar ce ta ce "Kutmar ubancan Biba ni kika watsawa ƙasa dan kaza-kazan ki tsinanniya jaka, wallahi yau koni koke", wadda aka kira Biba dake hidimar goge ƙasar da ta cika idanunta ta ce "Au ni zakiwa ɗiban albarka matsiyaciya ballagaza ki watsan ƙasar kice ni na watsa miki, to wallahi ni barkono zan watsa miki idan kika sake na buɗe ido na ganki".





Rabi dake tsaye tana ta tintsira dariya jama'a suna kallon ta suna ganin ƙarfin halinta, Tsohuwar nan ma kallonta take ita a tunaninta ma Yarinyar taɓaɓɓiya ce, wasu a wajen suna Rabi ta birge su da tayi haka wasu kuma da suka san Rabi suke jin haushinta suka hau zagin ta, suna ai zata aika tayi wanda yafi haka ma.




Rabi kuwa zuwa tayi ta kamo hannun Baraka ta ce "Bari na taimaka miki Baba", Baraka kuwa washe baki tayi tare da faɗin "yawwa Ƴar albarka kin kyauta min kuwa", tiryan-tiryan ta damƙi hannun Baraka suka nufi hanya, Baraka taita kwantanta mata hanyar da zasu bi, kamar abin arziƙi suna tafiya sannu a hankali kamar makaho da ɗan jagora, sai da ta je inda ba mutane sosai Rabi ta buɗe murya ta kurma ihu tana faɗin "ga Balo mahaukaci nan mu gudu Baba", ai jin haka yasa Baraka gudu tana yi tana harɗewa ga ido a rufe ƙasa ta cika shi, janta Rabi take tana faɗin "gashi nan saitin bayanki fa ki ƙara gudu kar ya kamo ki kuma Alkur'ani duka yake", ai nan take Baraka ta ƙara gudu akan nada, gata a mulmule ƙatuwa, dariya sosai gudun yake bawa Rabi, sai sai batayi yadda Barakan zata ji, "na gaji Yarinya Alkur'an ban iya gudu ba...", dai-dai nan ta afka wata ƙatuwar kwata mai tsananin ɗoyi da hamami, kuma a ƙalla zurfin kwatar yakai saitin ƙwanjin ta, "Wayyo Alllah na shiga uku ni Baraka ina ne nan?", ta faɗa tare da ɗago hannunta ta kai hancinta dan tabbatar da inda ta faɗa, Rabi kuwa dariya ta hau yi harda faɗuwa da riƙe ciki, "Baba kwata ce Alkur'an kike cikinta gata nan" cewar Rabi da  ta kasa riƙe kanta dan dariya.




Jin sautin dariyar da Rabi take mata yasa ta ce "ke dan Uwar ki ni kikewa dariya, na zaci ke ƴar arziƙi ce ashe ƴar iska ce ke", tana faɗa yana ƙoƙarin ganin ta fito, zagin da tayiwa Rabi shiya tsaida dariyar da Rabi take ta kafa mata ido kana ta ce "ni kika zaga Baraka?", "na zage ki dan ubanki shegiya mara kunya, wato har sunana kike faɗa dan fitsara inaa kika kai Baban da kike ƙira na da shi", aikuwa jin ta ƙara zagin ubanta ya sa ta hasala ta hankaɗa Baraka tare da faɗin "Ba'a zagin Uwata ko Uba na a zauna lafiya, kuma ni na watsa muku ƙasa ke da kishiyar ki", Baraka dake cikin kwata wannan karon babu inda kwatar bata ɓata ba har fuskarta saida ta shiga, ta ɗago da fuska duk kwata ta fashe da kuka ta ce "amma wallahi Allah ya kwashe miki albarka, tsinanniya matsiyaciya gantalalliya kai wannan wadda ta haifo ki Alkur'an ta cuce ni", "au ƙara zagar min uwa zaki Baraka kinsan dai ga halin da kike ciki zan iya ƙara auna ki ciki", ganin mutane suna tawo wa yasa Rabi barin wajen ta ruga a guje ta koma wajen faɗan Baraka da Biba dan ganin ya Biba ta kasance.




Baraka kuwa masifa take a kwata ita a tunaninta Rabi tana wajen bata san ta bar wajen ba, sai zage-zage take tana nuna saitin da take jin muryar Rabi, tana a haka har mutanen nan suka ƙaraso suna ganta a haka ganin tana nuna waje tana auna ashar yasa sukai tunanin mahaukaciya ce ɗaya ne ya ce "baiwar Allah ki fito a cikin kwatar nan mana", "yawwa bawan Allah dan Allah kama Yarinyar nan idan na fito naci Uwarta, ita ce silar kasancewa ta a wannan hali", mutumin kallon wajen yayi yaga ba kowa ya ce "baiwar Allah ai bakowa a wajen ke kaɗai muka taras", "to wallahi guduwa tayi amma da wata Yarinya nake tare, nan ta basu labarin komai, "anya ba aljana ce ta miki haka ba kuwa, ƙaramar Yarinya ba zata aikata abinda kike faɗa ba, nan take tsoro ya kama ta bayan ta fito suka taro mata ruwa ta wanke idonta ta sheƙa sauran a jikinta kwatar wata ta wanku wata bata wanku ba tayi musu godiya ta nufi gida a tsorace dan tabbas duk mai wannan halin sai dai Aljanin.







Rabi tana isa wajen ta taras Mijinsu Rabi Malam Tukur ya zo wajen sai masifa yakewa Biba sai zaginta yake, ita ma tana ramawa Tsohuwar nan da take uwar mijin su Biba sai cewa take "ka sake su ni dama wannan ƙaddararen auren ba sonsa nake ba, duk sun uzzira maka faɗan yau daban na gobe daban dan ɗiban Albarka, to Kwarankwatsa na gaji kasan yadda zakai da waɗannan mutanen da basu san komai ba sai tozarta ka a bainar jama'a", Tukur kam da gani bazai iya sakin  nan ba,  cewa ya ke "Muje gida tukun Inna muje kome za'ai ayi a can, gida suka nufa Rabi dake tsaye taso taga ƙarshen chakwakiyar hakan bata faru ba, hanyar gida tayi abinta tana waƙe-waƙen ta abinta, a hanya kuwa ta daki Yaran mutane da yawa, idan sukai mata Allah ya isa sai ta ce "da bai isa ba da baiyi wance da wane ba", sai ta ambaci sunan Iyayensu a haka ta isa gida ana ta ƙiran sallar Magriba.






Baraka tana zuwa gida a firgice Yaranta dake tsakar gida suna ta faɗin Baba Baraka sannu da zuwa ko kallon su batai ba, ta shige ɗaki ta cire kayan jiƙaƙƙu ta saka wasu yamutsatstsu ko tunanin wanka babu, ta yarɓa wanda ta dawo dasu a jikin ƙofar ɗakinta, ta haye gadonta da yake a hargitse ta kwanta ta rufe jikinta ta rintse ido, tsoro ne fal a ranta tana ta fargabar kar Yarinyar tazo mata, sai faɗi take "Allah yaso idona a rufe yake banga halittarta ba,Allah na gode maka", Yaranta duk wanda ya shigo saita firgita.







Tana shiga gida ta rafka sallama, Inna da take ƙokarin yin Alwallar sallar magriba ta kalle ta ta ce "ina kika je Rabi?", "Innata kinsan me?, banje ni gidan su Kattumen ba saina tafi Unguwar gini naga mutane da yawa......", labari ta bata amma bata gaya mata abinda ta aikata ba, Inna da take Alwalla ta nunawa Rabi buta kana ta ƙarasa Alwalar ta tashi  tana faɗin "Allah ne kaɗai yasan yau abinda kikai Rabi daga Allahn daya halicceki sai ke, Ubangiji ya shirya min ke akan tafarkin Allah madai-dai ci Rabi", da Ameen Rabi ta amsa tayi cikakkaiyar Alwalar ta ta ɗakko hijabi tayi sallar ta , saida ta gama ta ɗakko abincinta kalan taci dan bata son cin abinci da yawa,  ta shiga bawa Inna labarin kishiyoyi da yaƙi ƙarewa a bakinta, ita dai jinta kawai take, suna a haka Baba ya dawo, Murmushi ya yi ya ce "yau dai kam lafiya komai yake naga alamu, ya faɗa yana zama a mazauninsa da indai ya dawo nan Inna take saka masa Tabarmarsa da daddumarsa, dariya Inna tayi ta ce "aikuwa dai sai sam barka, sai dai an fita rangadi", duk abinda suke da Rabi suke sai dai ba zata gane ba dalilin ƙarancin shekaruntaa, sannu da zuwa tayi masa ya amsa da walwalarsa tare da sa mata Albarka da Adduar shiriya da kullum basa dena mata....✍️








*HAPPY EID MUBARAK*








*ALƘALAMIN MU ƳANCIN MU✍️*




*By Rumy*

[30/06, 3:03 PM] 🥰rumaisaaliyuinuwa🥰: *💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 5-6*

>>>>>>>>>>>Washe gari Monday da safe na hangi Rabi sanye da kayan makaranta Milk da wando ruwan ƙasa, ta sanya toms da safa tayi kyau abinta, sai jakar goyo mai kyau itama, "Inna zan tafi", ta faɗa tana cuno baki, "yawwa ɗiyar Albarka dan Allah ki taimaka ki nutsu kije lafiya ki dawo lafiya banda dukan Yaran mutane banda tsokana kinji Rabi'atu ɗiyar Innarta", ta faɗa tana ciro mata Naira ɗari a aljihun doguwar rigar Atamfar dake jikin ta, "yawwa gashi Baban ki ya baki hamsim nima na ƙara miki", karɓa tayi ranta fes dan gaba ɗayan haƙoranta ta ta washe, "nagode Innata da Baba na Allah ya baku Abokan zama na gari ya sa idan kunyi aure ku zauna lafiya", ta faɗa kanta tsaye kuma da alama addu'ar ta da gaske take yinta zuciyarta ɗaya, Inna data saki baki tana jin jawabin Ɗiyar tata ta ce "ke ni yimin shuru abokan zaman ubanwa, nida uban naki.....", sai kuma tayi shuru ta ce "maza tafi Allah ya taimaka, kika kuskura kika nemo mana magana wallahi barin mutanen da kika tsokano zamuyi suci ƙaniyar ki", gwanar kuwa ficewa tayi tana faɗin "saina dawo Inna", Addu'a tayi mata ta fice.







Kattume ta biya wa suka fito suka tafi, Kattume ƙawa ce ta rai da rai ita da Rabi tin suna Yara, sai dai Kattume tana shan duka a wajen Rabi, duk sanda wani abu ya haɗa su za'ayi tashin hankali kamar ba za'a ƙara ƙawancen ba amma in sha Allah basu ƴan mintuna zakiga sun jone, sai dai duk wanda ya taɓa Kattume to fa sai inda ƙarfin Rabi ya ƙare, shi yasa ko da wasa ba a shiga harkar su, kuma babu mai taɓa Kattume.







Tafiya suke suna hira tana bata labarin unguwar da suka je ita  da Kakar ta, har suka iso cikin madaidaiciyar makarantar su suna hira gwanin sha'awa, suna shiga suka taras an fara dukan makara, tsayawa Rabi tayi tare da kamo hannun Kattume ta ce "Alkur'ani babu mai dukan mu a wajen nan", ta faɗa tana kallon Malamin da yake dukan makaran.



"A'a nidai gaskiya karki jaza min wanke Banɗaki, kinsan haka kikai mana wancen satin kuma kika zauna kina kallo na ina ta wanke ƙazanta kika ce ke ba zaki ba", Kattume ta faɗa tana ƙoƙarin ƙwace hannun ta.




"Ke banza ce da dukan ai ƙwara wancen, kinga ba'a taɓa lafiyarki ba", Rabi ta faɗa tana  hararar Kattume.



Fuzge hannunta tayi ta nufi wajen dukan tabar Rabi tana mai jin haushin hakan, ita ma wajen ta nufa, Ɗalibai uku aka yiwa sai Kattume, bayan ya gamaiwa Kattume ya juyo kan Rabi kallon-kallo aka fara da Rabi da Mallam Ɗan lami, "ke jiranki zan ne?", "Mallam Ɗan lami dan Allah zan iya tambayar ka?",  ta faɗa ta tsire shi da ido.



"Au har damar tambaya kika samu kenan" ya faɗa yana miƙewa ya yo kanta ta goce ya daki iska, "Mallam Ɗan lami dan muyi muku tambaya fa  aka turo mu, idan bamuyi muku ba taya zamu iya kenan, nifa kawai cewa zan wai daɗin me kake ji idan kana dukan Ɗalibai?", "Ubanki nake ji shegiya mai ido ƙwala-ƙwala", jin ya aunawa ubanta zagi kuma ya ƙira ta da mai ido ƙwala-ƙwaka yasa ta hassala ta ce "Eh ai magana ce ta domin Allah, haka kurum kaita dukan Yaran mutane kuma kai kaɗai aka zaɓa aka bawa wai dispiling master yake kome, to cutarka sukai wallahi", ta gama faɗa tana murguɗa baki.





Ran Mallam Ɗan lami idan yayi dubu to fa a yau ya ɓaci, mamakin Yarinyar yake na yaddaa take auno magana kamar faɗa mata ake, anya ba Aljanu bane da wannan Yarinyar?,  ya tambaya a zuciyarsa, a fili kuma cewa yayi "ke ni sa'an wasanki ne, ni kike gayawa haka dan kan uwarki, to wallahi yau saina ci Ubanki a wajen nan", baya tayi tana ƙoƙarin gudu ya cafko ta yahau duka baji ba gani, ihu take tana auna masa ashar shi kuwa zagin da take masa ne yasa ya ƙara ƙaimi a dukanta, hankalin Malamai ne ya yo kansu, aka iso ana tambayar lafiya Mallam Ɗan lami kake mata wannan dukan, to dama da Rabi ta hango sun tawo saita yi shuru da zagin da take masa ta dena ihun suna zuwa tayi luuuuuu da ido zata faɗi wata Malama Fauziyya ta tare ta tana faɗin "Subhanallahi meye haka Mallam Ɗan lami ka kashe musu Ƴa, mai tayi maka da zafi haka?", huci yake yana maida numfashi, ita kuwa Rabi ɗauke numfashi tayi da ta ƙyalla ido taga za'a kalle ta saita ɗauke numfashi da an maida hankali kan Mallam Ɗan lami saita cigaba da numfashi.






"Wai harni Yarinyar nan zata kalla ta gayawa magana Malama Fauziyya", nan ya kwashe komai ya gaya musu, amma hakan bai gamsar da su ba dan sun san halin Mallam Ɗan lami da mugunta, duk da sun san halin Rabi na rashin kunya amma bai kyautu yayi mata wannan dukan a matsayinta na ɗiya mace ba.







Ruwa ake shafa mata amma taƙi ta farka, zuwa yanzu Mallam Ɗan lami ya fara tsorata da lamarin, dar dashi a masu cewa a kaita Asibitin Unguwar gini, nan take aka sata a babur Malama Fauziyya tahau baya aka riƙe ta akai Asibiti da ita, ta langwaɓe kai  ka rantse ta rasu kuma ta saki jikinta, basu jima ba  suka isa, Mallam Ɗanlamin ne ya ɗauke ta kasancewar tana da nauyi, ya nufi cikin Asibitin da gudu yana kiran azo da gaggawa, aikuwa nan take aka shigar dasu wani ɗaki aka basu gado, aka ce ya fita, jikinsa har rawa yake dan tashin hankali, tinda yake muguntar sa bai taɓa haɗuwa da wannan iftila'in ba, Malamai haushinsa suke ji, shi yasa da ya fito ko kallonsa basuyi ba, a ransa faɗi yake "dole ma a canzamin muƙami a yau naji na tsani wani suna wai shi Dispiling master wallahi", ya faɗa tare da share ƙwallar data biyo fuskarsa.





Wani likita ne ya duba ta ya tabbatar lafiya take, sai dai bata bari ya gano ta ba, dan Rabi Yarinya ce ammaa uwa ba Yarinya ba idan tayi maka abu saika rantse kace wada ce da fuskar Yara, shekarunta 12 a duniya amma ta ƙware wajen makirci da iskanci kala-kala amma duk wannan abin nata ba kowa take yiwa ba sai wanda yake da halin rashin ɗa'a  su take tabkawa rashin mutunci, dan indai kaga Rabi tayi rashin kunya ga babba to ba tsohon arziƙi bane, hakan yasa wasu da yawa suke mamakin yadda takewa wasu wasu kuma sai girmamawa.






Malamai sunyi cirko-cirko suna jiran sakamako, kwatsam saiga Likita ya fito sanye da lapcourt ɗinsa da tasha jiki, dan Asibitin nan ne na ƙauye wanda Likitocin cikinsu ba wasu ƙwararru bane kawai sun iya abinda suka iya ne, yana fitowa Malam Ɗan lami ne farkon tararsa ya ce "Likita ya take?, ta farka ne?", "Alhamdulillah  ta farka, firgita tayi ne shine ta suma yanzu tana ciki ta farka kuka take tana ƙiran Innar ta da Babanta ya kamata ku kira su", cewar Likita.



"Yanzu Likita ba zamu iya tafiya da ita ba, idan har batada wata matsala", Malama Fauziya ta faɗa.




Gyara zaman Lapcourt ɗin jikinsa ya yi kana ya gyara zaman Glass ɗin da yake idanunsa ya ce "Eh zamu iya baku sallama", ya faɗa yana tafiya tare da cewa Malam Ɗan lami da yafi kowa na wajen shiga halin ha'ula'i ya ce ya biyo shi, dan tunaninsa Ƴarsa ce ganin duk ya ruɗe.



Binsa ya yi su kuma sauran Malaman da ke su uku ne har Malam Ɗan lami, shiga cikin ɗakin da aka kwantar da Rabi sukai, sai dai me wayam suka gani ba Rabi babu dalilinta bayan gida suka duba nan ma bata nan, sai jakar Makarantar ta da Sandal ɗinta, hankali tashe suka fito ɗauke da jaka da takalminta hakan yayi dai-dai da fitowar Malam Ɗan lami "tana  ina an sallame mu", ya faɗa da fuskar sa wasai, Jaka da Sandal Malama Fauziya ta nuna  masa, "Eh Jakarta ce wannan na gane ta, ina ita Rabin?", "Babu Rabi fa babu dalilinta Malam Ɗan lami, mun duba har Banɗaki baka ciki", cewar Ɗaya malamin.




"Ban fahimci me kuke nufi ba Malam Sa'idu, kaya ce ita da zaku cee kun duba bata nan", cewar Malam Ɗan lami.



"Wallahi bata ciki Malam Ɗan lami", cewar Malama Fauziyya, ratsewa yayi ta gefan su ya shige ya duba ko ina shima bai ganta ba, fitowa yayi ya nufi ofishin Likita, "Likita!!!! Likita!!!!!!" kuzawa Likita ƙira yake kamar wanda zai haukace, Likita jin ƙira mai ƙarfi da yake fuskanta daga ƙatuwar murya mallakin gardi yasa shi miƙewa, ganin wanda sukai sallama da shi cikin aminci yayi wujiga-wujiga, "Inaaaa Yarinyar da ka gama dubawa yanzu har ka bamu sallama, ina kuka kaita!!!!", da ƙarfi yake magana kamar yana magana a wajen yaƙi, Likita da baisan hawa ba bai san sauka ba ya ce "Tana ɗakin da muka duba ta a kwance, mukuwa ina zamu kai ta?", "ku kuka sani maƙiya Allah mugwaye, Allah ne aranku nace Allah ne a ranku?, babu Allah a ranku, zaku iya sace ta ai wannan aikin ku ne mafi sauƙi, ya za'ai kace tana ɗakin ta, mun duba ƙasa ko sama bata ciki, sai jakarta muka gani da takalmin ta, ka gayan inda kuka kaita", cewar Malam Ɗan lami da yake ta auna masifa ya tara mutane a wajen sai kallo suke ciki harda wasu majinyatan sun taso su kashe kwarkwatar idanunsu ko sa samu suji daɗin jikinsu.




Lamari fa ya kai ya kawo kwalar Likita ce a hannun Malam Ɗan lamj, ya cikwikwiye shi saiya fito da Rabi, shi kuma sai rantsuwa yake inda ya duba ta nan ya barta tana kuka tana ƙiran sunayen Mahaifan ta, amma wannan zance da Likita yake dan kare kansa baisan cewar ƙara hassala Malam Ɗan lami yake ba yana ƙara jin tsanar Likitan nan a zuciyarsa, dan sosai yake jin tsanar Likita, ƙwatar Likita akai a hannun Malam Ɗan lami idon Likita ya fito yayi bulu-bulu sa bo da azabar shaƙa.






Abinda su Mallam Ɗan lami basu sani ba shine, lokacin da Likita ya fito ya barta ta tashi ta tintsire da dariya ta ce "wallahi Malam Ɗan lami sai kasan ka zagi ubana kuma ka dake ni, yau saina saka a uku, yanzu ma guduwa zan na tafi yawo na naƙi zuwa gida sai dare ta yadda nasan lokacin Malam Ɗan lami yasha wahala a rayuwarsa", tana gama faɗa ta miƙe ta fara haɗa jakarta zata sa takalmi saita ce "kai bazan tafi da komai ba dan ma ya sani shi  zai kaimin wallahi ta yadda zai bayani a wajen su Baba da Inna', nanma tana gama faɗa tasa dariya, kana ta aje  komai inda ta ɗauka ta nufi ƙofar fita, ganin sun juya baya suna magana yasa ta fice babu wanda ya ganta ta nufi hanyar fita daga Asibitin, tana tafe tana siyan kayan ƙwalama da ɗarin da Inna ta bata, wani gurin ta zauna saita cinye wani kuma idan ta siya a hanya take ƙarasa ci.





wannan kenan




*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*





*By Rumy*




PLS SHARING FISABILILLAHI👏

[30/06, 3:03 PM] 🥰rumaisaaliyuinuwa🥰: *💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 7-8*

>>>>>>>>>>>Asibiti fa ya hargitse hankalin kowa ya tashi, Likita ya tsorata dan wannan lamari na ɓatan mara lafiya ba ƙaramun abu bane, dan zai iya rasa aikinsa, an cika anyi maƙil a cikin Asibiti dan kuwa Malam Ɗan lami muryarsa kaɗai ta isa ta cika cikin Asibitin nan, dan ƙarami ne kamar wani gidan, faɗi yake shi wallahi a cikin ɗakin ya barta tana kuka, shi kuma Malam Ɗan lami ya ce dole saiya fito masa da Ƴar mutane, Malama Fauziya da Malam Sa'idu sai taraddadi suke suma kansu hankalinsu a tashe yake, ku na taƙaice muku batu wannan rana ita Malam Ɗan lami ya ƙira da baƙar rana dan kuwa ya tabbatar shima aikinsa yazo ƙarshe, albashin da yake tutiya da shi ya rasa.






RABI DANJA kuwa gararinta take a hanya hankalinta kwance ta tsokani wannan ta tsokani wancan, babu takaimi a ƙafarta kuma ita hakan bai dame ta ba, fatan ta yau Malam Ɗan lami ya ɗanɗana kuɗarsa , tana cikin tafiya ta hango Baraka mutuniyarta mai kishiya wadda ta baɗa musu ƙasa a ido ta kuma cilla ta kwalbati, da sauri ta ƙarasa wajen da take tsaye tana sarin Daddawa, tana zuwa ta ce "Baba Baraka yau ma mun haɗu", cewar Rabi.




Da wani irin sauri Baraka ta juyo dan baza ta taɓa manta wannan murya ba,   kallo ta tayi tare da faɗin "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ni Baraka, dan Allah Yarinya kiyi haƙuri karki cutar dani, wallahi tallahi bazan kuma zagin kowa ba balle ke, nayi nadamar zaginki wallahi", dariya abin ya bawa Rabi taita ƙyalƙyala dariya, hakan ya ƙara tabbatarwa da Baraka cewar tabbas wannan ba bani Adama bace jinsin Aljanu ce, nutsuwa sosai Baraka tayi dan kartayi wani motsi ran Aljanarta ya ɓaci.




"Baba Baraka kenan wallahi kin bani dariya, yau Daddawa kika zo siya?", cewar Rabi data bar dariyar ta jefawa Baraka wannan tambaya.



"Eh wallahi baiwar Allah nazo sarin Daddawa ne dake ina sayarwa", ta faɗawa Rabi cikin ladabi.



Buɗar bakin Rabi sai cewa tayi "Ina so kibarwa Tsohuwar nan kuɗin Daddawar kinga yadda rana take gasa ta wallahi abin tausayi duk ta gaji, ki bar mata kuɗin kawai zaki samu lada", saurin ɗagowa Baraka tayi ta kalli Rabi, aikuwa gani tayi Rabin ta kafa mata ido harda ɗan zaro shi, ai tuni ta ce "wallahi nabar mata", Baraka ta faɗa a tsorace dan zuwa yanzu cikinta ƙugi yake ga tsoro ga tashin hankalin data shiga na kyautar da batayi niyya ba, dan Baraka ko sadaka batayi bare kyauta, ta tsani fitar da kuɗi a tarihin rayuwarta kowa ya santa da tsinannan son kuɗin tsiya.



"Ina son ki juya ki cewa mai Daddawa kin bar mata kuɗin taci gaba da juyawa", Baraka ta tsinkayi muryar Rabi tana faɗa mata, aikuwa babu musu ta juya ta sanar da tsohuwa tayi mata kyautar kuɗin Daddawa ta fasa sara, aikuwa nan take tsohuwa tahau shiwa Rabi Albarka dan taji komai, sannan ta yiwa Baraka da zuciyarta take ta rawa dan kuka take son tayi amma tana tsoron ta juya Aljanarta tayi fushi in taga hawayen, "Baraka wace wannan Yarinyar mai kirki haka", cewar mai Daddawa, shuru Baraka tayi ta juya dan bata son tabar Aljanarta a tsaye bata juyo ba kar tace ta wulaƙanta ta, aikuwa tana  juyawa taga wayam bakowa a wajen, wato a yadda Baraka tayi zato Aljanar ta ɓace, aikuwa ganin haka ya bawa Baraka damar fashewa da wani irin kuka, bakomai ne ya sata ba sai kuɗin ta data barwa tsohuwa mai Daddawa, "Subahanalla Baraka kukan me kike haka?", nuna wa tsohuwa tayi wajen da Rabi take amma bakowa a wajen, ita ma tsohuwa ta tsorata dan bata ga tafiyar Rabi ba, "ina kuma tayi?", cewar mai Daddawa.



Cikin kuka Baraka ta bawa Tsohuwa labarin komai, kuma karkuce cikin lisilama ta bawa Tsohuwar labari a'a cikin fushi da masifa dan ji tayi duk duniya babu wadda ta tsana irin tsohuwa mai Daddawa, dan da bata zo sayan Daddawarta ta tuni tana tare da ƴan kuɗaɗenta, a zuciyarta kuma sai ashar take ƙunduwama Aljanarta, ita dai tsohuwa jin Aljana ce tasa aka bar mata kuɗi taita murna tana Allah ya shigo da dubun irin Aljanun Baraka cikin rayuwata aita bar mata kuɗi tana ƙara jari, haka Baraka tabar wajen tana tsinuwa da Allah ya isa amma a ranta dan taƙi ta fito da ko kalma guda fili dan kar Aljana taji.






Ita kuwa Rabi bayan Baraka ta juya dan sanar da tsohuwa an bar mata kuɗi ta silale tabar wajen, hanya ta kuma ɗauka tana dariyar Baraka data maida ta Aljana.







Makaranta har aka tashi babu su Malam Ɗan lami, haka aka tashi Ɗalibai kowa ya kama hanyar gida, Kattume kuwa tunani tayi ansa Rabi wankin Banɗaki shiya bata damar zuwa banɗakin taga wayam, bayan ajima ta duba ba Rabi babu alamunta, haka ta baro Makarantar tana tunanin ta gudu gida, dan su Ɗalibai ba wanda yasan Rabi an samu matsala da Malam Ɗanlami an tafi Asibiti dalilin suma da Rabi tayi, Malamai ne kawai suka sani.






Tana zuwa gida ta shiga gidan su Rabi, "Assalamu Alaikum Inna", amsa sallamar tayi ganin Kattume ita kaɗai yasa Inna cewar "A'a ina Ƙawar taki na ganki ke kaɗai?", "Inna dama Rabin bata dawo ba?", cewar Kattume, "kajini da Yarinya da ta dawo zan miki wannan tambayar, baku tawo tate bane?", Inna ta faɗa.




Nan Kattume ta bawa Inna labarin abinda ya faru zuwansu Makarantar, aikuwa hankalin Inna tuni ya tashi, dan Rabi bata taɓa yin haka ba, suna tsaye Baba ya shigo ya tambayi abinda ya faru ganinsu haka, nan Inna ta bashi labarin abinda Kattume ta shaida mata, aikuwa ba shiri Baba ya ce su je Makarantar su duba, Kattume suka ce ta koma gida ta ce ita saita bisu, Baba ne ya ce taje gida takai jakarta ta sanar da Kakarta, aikuwa tana zuwa ta aje komai ta fito ko kayan Makarantar bata cire ba suka rankaya, suna zuwa Makaranta suka tarar ba kowa sai mai gadi suka tambaya ya ce ai babu kowa an tashi har headmaster ma yanzu ya fita, aikuwa nan hankalin Inna da Baba ya tashi, suka hau salati Inna kuwa Malam Ɗanlami take ta yiwa Allah ya isa, anan Maigadi ya ce "Bayin Allah ko kune Iyayen Yarinyar daya daka ɗazu ta suma, indai kune to sun kaita Asibiti amma har aka tashi banga sun dawo ba", ai jin haka yasanya Inna ƙara tsurewa Kattume kuwa kuka ta sanya ita ma, dan taji batun har Asibiti, Baba kuwa cewa yayi suzo suje Asibitin, aikuwa nan take suka nufi Unguwar gini dan nan ne Asibiti yake.








Zuwa yanzu fa takai ta kawo Malam Ɗanlami kuka yake wiwi idanunsa sunyi ja ga baƙar fuskarsa ta ƙara baƙi, faɗi yake "wallahi bazan bar Asibitin nan ba sai kun fito da wannan Yarinyar, wallahi tallahi ko na ɗebo muku hukuma yanzu", ya faɗa cikin zubda hawaye, su Malama Fauziya kuwa kowannensu gida suka tafi dan Malama Fauziya Yaranta suna can suna jiranta, shi kuwa Malam Sa'idu dama ya riga ta tafiya, dan shima yana da tafiya yau, tafiyarsu sukai bayan sun aje masa jakar Rabi da sandal ɗinta, Likita yana zaune ya rasa inda zai sa rayuwarsa, dan yayi iya rantsuwar daya kamata ace Malam Ɗanlami ya yarda dashi amma kamar zuga shi yake, haka ya zauna lokacin tashin sa yayi amma tafiya ta gagara, har saida mai karɓarsa ya zo ya taradda shi tare da Ɗanlami, nan ake sanar dashi abinda ya faru, aikuwa shima da yayi ƙoƙarin kare abokin aikinsa yasha ashariya ta uwa ta uba, "Tsinannu maƙiya Allah da Annabinsa ai bakinku ɗaya, wallahi na ƙara jin bakinka anan saina maka matsiyacin duka", aikuwa ba shiri yayi shuru dan kuwa yadda Ɗanlami yake a murɗen nan yasan bazaiji da daɗi ba, nan aka zauna da shi Abokin aikin Likita ana fuskantar tashin hankali.








basu jima ba suka iso sa bo da Adaidaita sahu suka hau, cikin asibitin suka sa kai, suna shiga suka tambayi ɓangaren marasa lafiya aka nuna musu suka shiga cikin tashin hankali, Inna da Kattume sai kuka suke Baba kuwa ransa sai suya yake masa dan ransa a matuƙar ɓace yake da wannan Malamin, suna ida shiga suka jiyo wata murya tana ta kwarara ashar tare da barazana, basu tsaya bi takan abinda suka ji ba dan basuyi tunanin case ɗin nasu bane suka hau tambayar wata nurse "Yawwa dan Allah baiwar Allah an kawo wata Yarinta mai irin shekarun wannan Yarinyar kayan Makarntar su ma iri ɗaya ne", nan take Nurse ɗin ta shaida Yarinyar da ake bata kashi akanta yanzu, oficce ɗin Likita ta nuna musu tayi gaba abinta, aikuwa suna shiga da sallama, Kattume ta hangi Malam Ɗanlami "Laaa Baba ga Malam Ɗanlamin ai anan"..........✍️








Wannan kenan



*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*








*By Rumy*






Pls ku taya ni sharing fisabilillahi👏

[30/06, 3:03 PM] 🥰rumaisaaliyuinuwa🥰: *💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 9-10*

>>>>>>>>>>>"Laaaa Baba ga Malam Ɗanlamin ai anan", cewar  Kattume, ɗago kai sukai gaba ɗayansu daga Malam Ɗanlamin har Likitocin, saurin miƙewa yayi yana raba ido, Baba kuwa banda kallon tsana babu abinda yake aunawa Malam Ɗanlami, Inna kuwa cewa tayi "Ina Yarinyata take ance kai mata dukan da saida ta suma, ko ka ƙarasata anan ɗin?", ta faɗa tana kuka, "wallahi idan har ka kashe min Yarinya sai nayi shari'a dakai, tana ina ne ana tamabayarka kayiwa mutane shuru", Baba ya faɗa cikin ɗaga murya .



Malam Ɗanlami ya kasa magana sai nuna Likita yake bakinsa yana motsi ya kasa cewa komai, "Uban me Likita zai mana, mu kai muke tambaya kodai ka kashe ta?"  Baba ya faɗa yana kama kwalar Malam Ɗanlami, ai tuni Inna ta sanya kuka tana faɗin "ai shikenan magana ta ƙare ya kashe ta, gashi ya kasa magana, ai wallahi sai kaga gatan mu a cikin garin nan, sai ka biya ni Yarinya ta wallahi saina sa an maka hukunci dai-dai abinda ka aikatawa Rabi", kuka take sosai kamar ranta zai fita, Baba kuwa ya damƙi kwalar rigar Malam Ɗanlami yana cewa "ina Rabi take?", Likitocin nan kuwa duk sun ruɗe dan kuwa sun san Rabi bata cikin Asibitin kuma laifin har da su, Abokin aikin Likitan nan ne ya yi ta maza ya ce "Bayin Allah ku tsaya  ku kwantar da hankalin ku, Yarinyar ku bata mutu ba, sai dai gaskiya bata cikin Asibitin nan, bayan an gama duba ta aka shiga ɗakin da take amma ba a ganta ba sai Jakarta da Takalmin Makarantar ta, kuma wallahi......",  shaƙar da yaji an kai masa shi ya hana shi ƙarasa abinda zai faɗa, dan tuni Baba ya saki kwalar Ɗanlami ya kama ta Likita mai jawabi, "Me kake so kace, kana nufin sace ta akai, to wallahi bazan lamunta ba saikun fito min da Ƴata, tinkan nakai ƙararku ku fito min da Ƴata inda kuka kaita", gaba ɗaya ya rikice Inna kuwa zaman daɓaro tayi a ƙasa tana salati, Kattume ma kuka take sosai jin Aminiyarta ta ɓata, Office ya rikice Baba sai zafgawa Likita mari yake yana tsine masa, Malam Ɗanlami yayi tsamo-tsamo da shi sai wurga jajayen Idanunsa yake, dana sani yake na dukan kawo wuƙa da yake yiwa Yaran mutane, a ransa faɗi yake "in sha Allah in anyi duniya dan Manzon Allah bazan kuma ko kallon banza ne ga Ɗalibai ba bare takai ga nasa hannu na dake su, bazan kuma ba ya Allahu wahidul ƙahhar, wallahi bazan kuma ba", ya faɗa tare da fashewa da kuka, wannan kuka nasa shiya janyo hankalin Baba ya juyo gare shi bayan ya cika Likita bokon turai, ai Baba baiyi ƙasa a gwiwa ba ya daddage ya shararawa Ɗanlami mari ya ce "au kuka ma ka samu damar yi mugu azzalumi, dama ta daɗe tana bamu labarin yadda kake zagewa kaita dukan Yaran mutane kamar an kawo maka jakai, to daga rana irin ta yau ka dena dukan kowace Yarinya a rayuwarka, sai kayi birsin wallahi indai ka salwantar min da Rabi, saika shiga uku wallahi", sosai fuskar Ɗanlami tasha mari babu ƙaƙƙautawa.








Rabi kuwa bayan ta gama wasanninta a gari, ta takali wannan ta takali wannan, har ta isa gida ƙafarnan tata tayi futu-futu sa bo da datti, aranta kuwa faɗi take "nasan yanzu su Inna basa nan sun tafi nema na bari naje ƙofar gida na kwanta kamar a sume nake", tana gama ayyana haka ta nufi gida, tana zuwa ta kuwa taras gidan a rufe ai babu ɓata lokaci ta samu waje a saitin ƙofar gidan ta kwanta kamar matacciya, Allah yasa ba mutane da yawa a wajen, tayi lamo da ita kamar gaske.








Baraka kuwa tana tafe tana kuka na takaicin yadda Aljana ta taso ta a gaba, yanzu bata ta Biba kishiyarta ta kanta take dan ko Biban ta tsokaneta shuru take mata, dan faɗan da sukai a rannan shiya janyo mata haɗuwa da ifrituwar Yarinyar nan, haka ta ƙarasa gida idanta luhu-luhu, gashi duk ta gaji, haka ta shiga gida Yaranta suma mata sannu da zuwa ko kallonsu bata yi ba ta shige ɗaki, aikuwa tana shiga ta tuna kyautar da Aljana ta sa tayi da kuɗin ta aikuwa kuka nan da nan ya kufce mata tahau rerashi da muryarta mai girma.







Asibiti kuwa Baba da Inna sun rikice musu, wata Tsohuwa ce mai jinyar Ɗan ta ta shigo Office ɗin ta ce "dan Allah bayin Allah kuyi haƙuri, wannan duk ɓata lokacine kamata yayi a fita neman Yarinyar nan, ko kanta ya juye ta fita, amma ba'a dinga yanke hukunci cikin fushi ba, ku fita ku nemo ta, na tabbata baza ta ɓata ba in sha Allah, aje akai cigiyarta", da wannan shawarar suka fita neman Rabi harda Likitan da alhakin duba ta yake kansa, tin daga bakin gate suka fara da kwatance da kayan jikin Kattume, aikuwa Maigadin Asibitin ya ce "tabbas naga Yarinya mai kaya  irin wannan, sai dai banyi tunanin majinyaciya ce ba", "da kanta ta fita ko da wani ka ganta", Baba ya tambaya.




"Gaskiya ban kula ba sa bo da lokacin zan buɗewa Mota ƙofa ban kula ba", cewar Maigadi, ai jin haka yasa suna fita da sauri suna take suna duba hanya, Likita kuwa ji yake kamar ya kurma ihu, Ɗanlami kuwa Allah-Allah yake ace ga Rabi an gani ya samu sa'ida a rayuwarsa, a ƙafa suka isa gida, aikuwa suna zuwa suka ci karo da Rabi a sheme an cika ƙofar gidan ana taraddadin abinda ya same ta, kutsa kai sukai cikin mutane, ganin Rabi a wannan hali yasa Inna rugawa tare da tallafota jikinta yana ƙiran sunanta a jere "Rabi!, Rabi!!! Rabiiiiiii!!!!! meya same ki na shiga Uku ni Saratu, Baban Rabi bata numfashi fa",  ta faɗa tana sakin kuka, Baba kansu yayo haka Malam Ɗanlami da Likita da komai abisa larura yake yi, dan zance na gaskiya ya gaji, sunanta suke ƙira, suna salati, ruwa aka miƙo musu Kattume ce tayi gudu taje ta ɗebo ruwa a kwanan sha ta kawo har Kakarta saida ta biyo ta jin abinda yake faruwa, nan take Baba ya karɓi ruwa ya yayyafawa Rabi aikuwa nan take ta buɗe ido tana jan numfashi kamar gaske, rumgumeta Inna tayi tana  hamdala ga Allah, haka Baba, sai Uwa Uba Malam Ɗanlami da yafi uban kowa murna, har wani ajiyar zuciya ya yi, sudai su Inna gida suka buɗe suka shiga da Rabi, da ƙafarta ta shiga, hakan ya bawa Likita damar barin wajen yana hamdala ga Allah subhanahu wata'ala, shima Ɗanlami ganin yayi free ya yanki hanya yana ajiyar zuciya.






Rabi tana shiga ta ɗau buta tayi hanyar Banɗaki, tana fitowa ta ɗaura Alwala, su Inna sai kallonta suke, bata kula kowa ba ta yi sallarta ta nufi ɗakin girki, abinci ta zubo ta zauna acan gefe tayi bismilla ta hau ci, Inna ce ta kalli Kakar Kattume a marairaice ta ce "nikam Baba Saude anya ba wani abu Mugun Malamin nan yayi wa Rabi ba, kinga fa yadda taƙi kulamu", ta faɗa tana share ƙwalla.





"A'a Innar Rabi mu kyautata zato hankali zaiifi kwanciya, kin manta Rabi ne wai keda kika haife ta, zata yi magana ne, yunwa take ji ne shi yasa taƙi magana",  cewar Kakar Kattume.






Aikuwa tana gama ci ta ce "Alhamdulillah, Inna ina yini, Baba ina yini, Baba Saude ina jini", a tare suka haɗa baki wajen cewa "lafiya ƙalau Rabi".





Inna ta ce "Rabi meya sa kika baro Asibitin kuma meya faru muka ganki a sume a waje meya faru?".






"Inna na gaji ne shi yasa na baro Asibitin, dana tawo sai jiri nake ina zuwa ƙofar gida na faɗi", cewar Rabi, numfashi Baba da Inna suka sauke jin ba wani abu bane.





"Alhamdulillah Allah ya kiyaye gaba, mu zamu wuce Allah ya kyauta gaba", cewar Baba Saude, Kattume kuwa bayan tayi wa Ƙawar tata sannu tabi Kakarta suka tafi.



Godiya su Inna sukaiwa Baba Saude.







Ya kamata na bayyana muku asalin Baba da Inna.



Asalin su mutanen Garin Taraba ne a wani gari Membila, gari mai yalwar kayan itaciya mai cike da albarkatun kayan gona, gari ne gashi nan washar dashi ga sanyi mai daɗi, kasancewar garin kan dutse ne, Iyayensu Baba da Inna wato Saratu da Umar shine asalin sunansu, to Iyayensu anan suke ƴan asalin nan ne, da Mahaifin Baba da Mahaifin Inna Uwa ɗaya ne Uba ɗaya, Auren zumunci akai musu tin suna Yara, kasancewar su haka suke da sun yanke shawarar wance ce matar wane to babu makawa sai anyi wannan aure, sai bayan Yara sun girma a sanar dasu, sai dai idan Allah bai nufa ba,



Rayuwa ake a wannan gari mai daɗi ga zaman lafiya babu hayaniya, Ruga ce dasu mai kyan zama ana ƙiran rugar da suna Rugar Harɗo Bello wato Mahaifin Inna shine babba a rugar ana girmamashi sosai, gashi Allah ya albarkace shi da dukiyar Shanu, Zabbi, Kaji, Talo-talo,  da dai sauran ko wace dabba, mutum ne shi mai son mutane da haba-haba da su, Matarsa guda Innawuro ita ce mahaifiyar Inna Yaransu goma biyu sun rasu dalilin saran maciji, yanzu saura takwas, akwai, Ado shine babba, Hamisu, Hamza, Bashir, Shatu, Rufa'i, sai Saratu, sai autan su Rabi'u, sun taso cikin kyakykyawar  tarbiyya, da son junan su,  dukanninsu suna da Aure,  autan su Rabi'u shine ya fara karatun boko a gidan Harɗo Bello hakan yasa yake zaune a garin Kano, dan anan B.U.K ya kammala degree ɗinsa, yana da ƙwazo sosai a fagen karatunsa, yana yawan zuwa Rugarsu ganin Iyayensa, zuwa yanzu ya samu sana'arsa a Kano kasuwanci yasa a gaba sosai yana harkar Atamfofi, Lesuka, Shaddodi, sosai ya bunƙasa, ya zamana har Yaran shago ne da shi masu taimaka masa, yayi Aure a garin na Kano da Matarsa Sumayya, yanzu yana da Yara maza biyu da mace ɗaya,   Babban sunansa Bello wato sunan Kakansa aka sa masa ana ƙiransa  Saheeb, sai mai bi masa Muhammad shi kuma yaci sunan Mahaifin Sumayya wato Mahaifiyar su, sai Auta Amina ana ƙiranta Khausar.




Inna da Baba kuma suna zaune a garin Bauchi dalilin sana'ar Baba da ta kawo shi wannan gari na Bauchi a cikin wani ƙauye mai suna Yana, yana harkar sana'ar fata, Allah ya rufa masa Asiri sosai yana samu da harkar kafin Rabi sun haifi Abdulrahman wanda yanzu yana can yana Karatu a garin Maiduguri wato Barno, yakan zo gida duk hutu, yana Ƙaunar Ƙanwarsa sosai wato Rabi duk wani abin more rayuwa yana kawo wa Rabi, duk sanda Hamma Abdulrahman yazo sukan samu lokaci duk ƙarshen shekara suje Membila, dangi gaba ɗaya suna Membila Alhaji Rabi'u da su Inna ne kawai sukai nesa da gida, Mahaifin Baba wato Baffa Aminu baiso Ɗan nasa yayi nesa da shi ba dan shi kaɗai ya haifa yaso ya gaje shi a harkar kiwo, sai dai Harɗo Bello daya sa baki ba yadda ya iya haka ya barshi ya tafi.






Ahaline da su Harɗo Bello sosai a ƙalla yanzu yana da jikoki sunkai hamsin, ciki harda Rabi  wadda duk cikin jikokinsa yafi ƙaunarta baya taɓa iya ɓoye son Rabi a idon kowa, indai tazo Ruga duk abinda ta nuna tana so to shi ake mata, wannan soyayyar ta samo asaline sa bo da son da yakewa Mahaifiyar ta wato Inna Saratu, Rabi abarso ce a Rugar Harɗo Bello, sai dai suna shan fitina idan taje, bata ji ko kaɗan sai dai abinda zai burgeka da Rabi tana da son Addininta Sallah bata wuce ta, ga son karatu, shi yasa take da ƙoƙari a makaranta.



Inna ƴar gata ce sosai, Yayunta suna taimaka mata tako ina, Ƙaninta dake Kano yana yawan zuwa da Iyalansa, Hajiya Sumayya, Saheeb da Muhammad da Khausar wadda ta girmi Rabi sosai dan Inna bayan ta haifi Hamma Abdulrahman ta jima bata haihu ba sai daga baya ta haifi Rabi.












Wannan shine tarihin Iyayen *RABI DANJA.*







Wannan kenan




*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*



*By Rumy*

[30/06, 3:03 PM] 🥰rumaisaaliyuinuwa🥰: *💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 11-12*

>>>>>>>>>>> 

            *KANO*

Aka ce ta dabo ci gari ko dame kazo an fika, cinkoson ababen hawa ne maƙil a titin da zai sadaka Jan bulo, duk da wannan gada da akayi dan rage go slow hakan bai hana titin cunkushewa ba, Ransa a ɓace ya fito daga cikin rantsatstsiyar Motarsa wadda daka ga motar kasan mai feshi ce kuma kuɗi yayi kuka, farar ƙafarsa ce ta fara fitowa wadda ko wata macen iyakacin ta kenan, dan fes take har jaja take kamar ka taɓa jini ya fito, fitowarsa daga cikin motar ne yasa na tsaya kallon sarautar Allah, wato kai daka ga jinin fulani kasan sune dan kuwa haiba kamala tsantsar kyau da zati da Ubangiji ya tsara game da wannan Saurayi ta tsaru, sai dai kawai na taƙaita muku dan kar na saku tunani, sanye yake da rantsatstsen farin yadi cotton mai ɗankaren tsada da kyau, ya sanya rantsatstsen agogon hannu mai tsada shima, glass ɗin idonsa baƙi ne sosai hakan yasa ya ƙara fito da hasken fuskar sa, sai takalmansa na fata ziryan shima baƙi, ɗan ƙaramin bakinsa ya ciza hakan ya bawa dogon hancinsa bayyana,  cikakken gashin girarsa ya motsa wanda Allah ya tsara masa cikin hukuncinsa, batu na gaskiya Saurayin ya haɗu .



Komawa yayi cikin motar yana tsaki, da alama sauri yake gashi kuma hanya bakyau, a haka a daddafe aka fara wucewa har Motarsa ta ratsa tabi titin da zai sada ka rijiyar zaki, da gudu yake tuƙin hakan ya sanya ya iso wani katafaren gida mai tsantsar kyau, kai da gani ba sai an faɗa maka ba mamallakin gidan yana da abin hannunsa, horn yayi bai jima ba Maigadi ya zo ya wangale masa gate ɗin ya watsa hancin motarsa ciki,




Gida ne na gani na faɗa wanda ya amsa sunan sa gida, plate gida ne me kyau madaidaici, ya tsaru da fulawowi masu kamshin shaƙa, wajen da ake parking motors ma kawai abin kalla ne, ga motoci nan reras wajen ƙwara goma sai wanda kaso zaka hau, parking yayi ya fito ko takan Maigadi da yake masa barka da zuwa baibi ba, ya sa kansa inda zai sada shi da cikin gidan, wani waje ya nufa inda yana shan kwanaya shiga tamfatsetsen falo, wanda komai na cikinsa Green ne, wata kyakykywar mace ce zaune da wata budurwa wadda daga gansu kaga wannan saurayin kasan akwai halaƙa, "Mammy na gaji wallahi", wannan saurayi ya faɗa bayan yaje saitin ta ya zauna, shafa fuskarsa tayi ta ce "Son baka ji ko, na gaya maka sallama wajibi ce a wajen ko wane musulmi indai ya shigo inda musulmai suke, amma har yau idan nayi maka magana sai kace ai kana yin sallama jine bama yi", ta ƙarasa faɗa tana harararsa,



"Mammy Allah ina sallama, kune dai bakwa ji, kuma ai mala'ikun Allah sunji kuma sun amsa, amma Mammy kiyi haƙuri zannayi da ƙarfi dan kiji kuma ki shaida", ya faɗa yana rumgumota, murmushi tayi mai ƙara mata kyau.




Duk wannan abu da ake wannan budurwar tana wajen tana danna waya bata ko kalli inda suke ba, hankalinta nakan abinda take, "Khausar!", Mammy ta faɗa da ƙarfi, "Na'am Mammy", ta faɗa a ɗan razane, "wai ni wannan wayar idan kina tare da ita baki ji baki gani ne, wallahi zan ƙwace ta tinda har ba zaki dena wannan ɗan iskan chart ɗin na ba gaira ba dalili ba", Mammy ta faɗa ranta a ɓace,




"Mammy kiyi haƙuri wallahi muna wani program ne a group ɗin mu na School, Hamma Muhammad yaushe ka shigo?", ta faɗa da mamaki da alama bata ga shigowarsa ba da gaske, harara ya ɓalla mata baice komai ba ya miƙe ya nufi wani side da alama nan yake rayuwa, "Mammy kingan shi ko nayi masa magana ya share ni", Khausar ta faɗa cikin shagwaɓa, "eh na gani ai hakan ya dace dake, wallahi ki fita idona na rufe dan lamarin son chart ɗin nan ya ishe ni, zan ɗauki mataki a kanki", "Mammy dan Allah kiyi haƙuri, in sha Allah na dena ɓata miki rai akan wannan wayar", ta faɗa bayan ta dawo kusa da ita ta rumgumeta.






Shi kuwa Hamma Muhammad falonsa ya nufa, komai na ciki White ne da alama shi ɗin ma'abocin son farin abu ne, toilet ya faɗa yayi wanka ya fito, mayuka ya shafa ya feshe jikinsa da turaruka ya sanya jc fara da kore yayu masifar kyau yadda ya kamata, fitowa yayi falo ya  nufi kan diny ya bubbuɗe komai kana yayi saving ɗin kansa Sinasir ne da miyar Agushi sai farfesun kayan ciki, nan ya fara azawa cikinsa babu wasa, yaci sosai ya goge bakinsa da tissue ya koma kan kujerun falon ya zauna, wayarsa ya ciro daga Aljihun wandon jc, ƙira ya gani ratata a wayar, murmushi ya yi ganin wanda ya ƙira, shi ya fara ƙira bata jima ba aka ɗauka ya sa a hansfree "Bro kana me ina ta ƙiran wayarka kaki ɗauka, kafi kowa sanin na tsani na ƙira waya aƙi a ɗaga, ƙwara na ƙira a kashe da na ƙira aƙi ɗauka", wata sansanyar murya ce take wannan ƙorafi, kuma namiji ne, "Sorry Hamma wallahi na sata a silent ne kuma akwai dalilin hakan, but kaina bisa wuya na Hamma na", ya faɗa yana cije lips da alama sabon sa ne hakan, daga can aka ce "Ok ina Mammy da Khausar, hope suna lafiya, Daddy munyi waya ɗazu shima ashe bai dawo ba", "Hamma suna lafiya, Daddy kam ina ga sai satin gaba zai dawo, Hamma kaima ya kamata ka dawo dan Allah, we missing u so much", cewar Muhammad.



."I will come back soon dear, but ka kula min da kanka da su Mammy da Auta, anjima zan ƙira su muyi magana", "Ok Hamma takecare".




Suna kammala wayar ya miƙe ya koma side ɗinsa dan hutawa.




Ɓangaren Mammy kuwa bayan sun gama da Khausar side ɗinta ta wuce ita ma Khausar Ɗakinta ta nufa dan yin Sallah.





Familyn Alhaji Rabi'u kenan, Yaya ga Inna Mahaifiyar Rabi, suna ƙaunar junansu matuƙa, basa son ɓacin ran ɗaya daga cikin su, sai dai kowanne da halinsa, Muhammad yana da zuciya da saurin fushi, sai dai ba'a zuwa ko ina yake sakkowa, baida riƙo,  Khausar kuwa shegen tsokana ga son chart idan tana yi bata ji bata gani, gaba ɗaya tattara hankalinta take akan wayar, shi yasa suke yawan faɗa da Hamma Muhammad da Mammy, sai uwa uba Hamma Saheeb shi kam mutum ne mara son magana da hayaniya, duk inda yake to fa wajen shuru ne, dan hayaniya kan sashi ciwon kai, baya son ƙazanta shi yasa idan yana ƙasar baya cin abincin kowa saina Mammynsa, miskili ne na bugawa a jarida, gashi ba'a taɓa gane gabansa bare bayansa, ma'ana baka sanin halinda yake ciki, bai son raini, yana da  kirki sai dai idan baka zauna da shi ba bazaka gane masa ba.




Wannan shine kaɗan daga cikin halin Familyn Alhaji Rabi'u.






*ƘAUYEN YANA*



Washe garin abinda ya faru tsakanin Malam Ɗanlami da Rabi, ta shirya zata Makaranta Baba ya ce ai kuwa dashi za'a tafi dan yaje yayi tsakani da Rabi da Ɗanlami, haka kuwa akayi, tare suka je, suna zuwa yasa aka kaishi gaban shugaban Makaranta, bayan sun gaisa ya shaida masa duk abinda ya faru, Rabi tayi wiƙi-wiƙi gaban Heardmaster sai zare ido take wai ita an daketa ta suma, shugaban Makaranta ya bada haƙuri kuma ya ce daga yanzu bazai kuma dukan kowace Yarinya ba, 



Malam Ɗanlami da kansa ya zo har gaban Baba ya bada haƙuri, bayan nan Baba yabar Rabi a Makaranta ya tafi wajen sana'arsa.





Rabi tana shiga Aji bata kula kowa ba har Kattume ta nemi guri ta zauna tana harare-harare,  Ƴan aji kuwa ganin haka yasa kowacce  tasha jinin jikinta dan sun san duk wacce ta shiga shirgin Rabi to yau ta shiga uku, shi yasa ba wacce ta kula ta, haka aka fita break nan ma Rabi bata kula Kattume ba, ita ma Kattume taƙi kula Rabi, ashe wannan abu da Kattume tayi ran Rabi idan yayi dubu to ya ɓaci, kuma ta sa aranta yau saita koyawa Kattume hankali, da wannan ta wuni a Makarantar har aka tashi, 




Aikuwa ana tashi Rabi ta kama hanyar gida, bata zame ko ina ba sai gidan su Kattume, tana shiga ta samu Baba Saude tana aikin tuƙa tuwo, "Salamu alaikum Baba Saude ina wuni?", Rabi ta faɗa tare da tsugunawa, "lafiya ƙalau Rabi, ina mutuniyar taki ba tare kuka tawo bane?", cewar Baba Saude.




Kuka Rabi ta fara hawaye sharrr kamar an kunna fanfo, "Subhanallahi Rabi lafiya, meya faru?, ko wani abun ne ya sami Kattumen?", Baba Saude ta ruɗe tana tambaya, Rabi kuwa sai shashsheƙa take kamar Uwarta ce ta rasu, Baba Saude kuwa zuwa yanzu ita ma kukan ta fara, tana faɗin "nikam yau na shiga uku ni Saude, dan girman Allah ki sanar dani Rabi menene?", buɗar bakin Rabi sai cewa tayi "Baba Saude yau ni Kattume ta buɗi baki ta zage ni, ta zagi Babana, sannan ta ƙira sunan Inna ta ta zaga, bata tsaya anan ba Baba Saude ta ƙira Hamma Abdul ta zaga, wai yana  can ƙila ma ya mutu bamu sani ba, Baba Saude me nayi wa Kattume da zafi haka?, ban fa yi mata komai ba Baba Saude banyi mata komai ba Allahhhhhh", taja maganar da kuka, Baba Saude kuwa ta haukai ta zauna ran nan nata ya ɓaci jin Kattume da wannan ɗanyen aiki, "Rabi yi shirinki, wallahi yau sai naci Uban Kettume a gidan nan, ki tashi kije gida kar Innar ki ta neme ki, kuma karki gayawa Innarki kinji, zanyi maganinta da kaina", haka Baba Saude ta lallaɓa Rabi ta fita, aikuwa tana fitowa sukai kiciɓis da Kattume, ko kallonta Rabi batayi ba ta wuce, binta da kallo Kattume ta yi, tana nazarinta, aikuwa tana shiga gida Baba Saude ta damƙe ta tahau duka, tana zaginta, wai ta zagi Rabi da Ahalinta, ita dai Kattume sai faɗi take bata san zancen ba, ita bata zagi kowa ba, amma ina Baba Saude idan ta hango kukan da Rabi tayi sai ta ƙara gasgata zancen Rabi, saida ta gaji ta bar Kattume, kuka take akan bata san hawa ba bata san sauka ba Rabi ta mata sharri.✍️✍️✍️✍️






Wannan kenan





*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*





*By Rumy*

[30/06, 3:03 PM] 🥰rumaisaaliyuinuwa🥰: *💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 13-14*

>>>>>>>>>>>Gida Rabi ta nufa bayan ta share hawayen ta, Inna tana zaune ta shiga bayan ta mata sannu da gida ta amsa, Ɗaki ta shiga ta canzo kaya ta shiga Ɗakin girki ta ɗakko abincin ta, ta fara ci, bayan ta kammala, ta dawo kusa da Inna dake shirya carbinta hankali kwance, "Inna wai yaushe ne Hamma na zai dawo gaba ɗaya?", Rabi ta faɗa.



"Ya kusa dawo wa Rabi, ai karatun nasu ya zo ƙarshe bazai daɗe ba zai dawo kinji kita masa addu'a", Inna ta faɗa cikin kulawa.




"Inna yaushe zamu gidan Baffa ne, munfa daɗe bamu je ba, kuma kince da Sallah zaki kaini amma baki kaini ba, ina son zuwa wallahi".



"Zamu je mana Rabi, ki kwantar da hankalinki, zaki gidan Baffan ki, kiga Yayun ki", cewar Inna cikin rarrashi.



Baki Rabi ta cuno ta ce "nifa Inna bana son wannan koɗaɗɗen wallahi, idan aka je baya dariya sai dai yayi ta fushi, shi yasa bana son sa, nafi son Hamma Muhammad yafi saimin wannan abin na cikin leda me ƙyalli me zaƙin nan", "Rabi Ɗan uwan naki ne kike cewa bakya so?, bana son sakalcin banza fa, bama zaki je ba", cewar Inna.



"Kiyi haƙuri Inna dan Allah bazan kuma ba, kinji", harararta Inna tayi ta ce "to duk sanda naji kince kin tsani wani wallahi sai ranki ya mugun ɓaci, kinji na gaya miki, Ɗan uwanki ne haka halittarsa take", "To Inna nafa ji", ta faɗa tare da miƙewa ta bar gun, Inna ta bita da kallo.







Washe gari bayan sun je Makaranta Kattume taƙi koda kallon Rabi sanadiyyar sharrin da taje tayi mata a wajen Kakarta, har hakan ya sa aka dake ta, Rabi kuwa ko a jikinta zuwa tayi ta zauna kusa da Kattumen tana janta da hira, kamar bata san abinda tayi mata ba, ƙarshe dai Kattume ta saki ranta abinka da Yarinta suka shiga wasannin su.





Da yamma wajen huɗu aka cika a filin kusa da gidan me Unguwa, masu Dj ne suka kafa sifiƙu manya guda huɗu, sun ware kiɗa Ƴan mata sun shiga filin suna kece rainin rawa, kowacce ta dage tana baje basirarta, can na hango wata tasha penti a fuskarta idan banyi kuskure ba sai nace kwalliya ce akai mata wadda foudation ɗin wani gurin ya biyu wani gurin be biyu ba, taci wani yadi net me kore sai ƙyalli yake, ga yellon abin ɗauri da yellon Takalmi, yelluwar Jaka, kai da gani ba sai an faɗa ba wannan ita ce tauraruwa da ta tara mutanen da suke cashewa a wannan fili, da alama Amaryar ce, dan naga wasu masu ankon Atamfa ƴar gadagalle ne suka jero suka saka ta a tsakiya kowaccen su tasha foundation a fuskarta da jagiya me conceller, abin dai sai ni dana gani,




Ba kowa bace wannan Amarya sai Harira Ƴa ga mai Unguwar Yamadawa wato Unguwar su Rabi Danja, bikinta ake yau da ɗan gidan Liman, yau ake rantsatstsen fatyn ta, wanda suka daɗe suna tsara shi kafin bikin, sai yau Allah ya nufa, Dj Isiya  sai saka musu waƙoƙi yake na ban mamaki, zuwa yanzu Amarya ya ƙira da Ƙawayenta domin fitowa filin rawa "Ehemmmm Amarsu ta Ango ta fito, muna miki barka da zuwa wannan fili, bari mu sa miki waƙar da ta dace dake Amarsu Harira Amaryar Harisu Ango",  tini ya ware musu irin remix ɗin nan me kama da za'a tayar iskokai, nan take Ƙawayen Amaryar da ita kanta Amaryar suka hautsine suka fara wata iriyar rawa, ko kaɗan basa bin kiɗan, can na hango wata ta botse tana girgiza ɗuwawuka wanda idan banyi karya ba sai nace kamar na ɗan kwikwiyo, haka fili ya kasance ana ta rawa babu kama ƙafar yaro, kowacce ƙoƙari take taga ta kere Ƴar uwarta a rawa, musamman da suka ga maza a wajen burin su su burge su.






Rabi da Kattume ne suka ci ado suka nufi filin gidan mai Unguwa, Doguwar rigar les ce a jikin Rabi, tayi kyau kasancewar bata sa komai a fuskarta ba a cewarta sauri suke, kar a gama disco basa nan, Kattume Atamfa ta saka riga da zani, ita ma bata tsaya tayi kwalliya ba kasancewar Rabi tace mata sauri take, sauri suke harda gudunsu, aikuwa suna zuwa suka taras da waje ya hautsine da rawa, cikin wajen rawar suka shiga, nan suka fara takawa suma, yi suke suna ƙarawa, lamari yayi lamari, har takai ta kawo wata bata gane wadda take kusa da ita, ana cikin haka Dj ya sanarda zuwan Ango da Abokansa, tare da cewa "Aha Amarya da Ƙawayenta zamu so ku bamu fili domin kuwa Angonki ya iso wannan waje, dan haka kowa ya koma baya ku bamu aron filin",  nan aka fara matsawa ana barin fili, bayan kowa ya matsa Dj ya kalli fili yaga wata Yarinya a tsaye ta kama ƙugu,  "Yarinya kema ki koma baya!!!!!", cewar Dj Isiya cikin lasifika, ko gezau Rabi batayi ba tana tsaye tayi tsaiwar alo tsiya alo danja, Angwaye ne suka ƙaraso hakan yasa Dj Isiya hankalinsa ya koma kan kirari ga Ango, wato shima Ango shiga yayi irinta Amaryarsa, shi kuma Yadi ya samu kore shima irin me sheƙin nan, wanda ko ya tsufa baya dena ƙyalli, sai hularsa yello da takalminsa daki bari shima yello, kafin ya ƙaraso fili aka jera su shi da Amaryarsa aka sanya waƙar "Lokacinki ne yayi Amarya ƴar amana, je kije ki zauna da miji Aure ibada ne", a haka suka isa fili, Rabi na tsaye tana kallon komai a tsakiyar fili.





Rabi kuwa dariya ce take cinta ganin Fuskar Amarya da tayi yanzu, dan ɗazu da suka zo hankalinta na kan rawa bata kula ba, aikuwa suna tsayawa taje saitin Amarya kamar wadda zatai mata Allah ya sanya alkhairi ta ce "Harira kinga fuskarki kuwa yadda tayi?, wallahi kamar a tatsi mai, ɗaurinki saiya mai dake kamar Karaba babar Kiriku", nan ma tana faɗa ta ƙara tintsirewa da dariya, Ango Harisu yana jin komai, ita kuwa Harira, zuciyarya sai tafarfasa take, dan wallahi da badan bikinta ake ba yau da saita sumar da Rabi, haka Rabi ta tsaya kamar wadda suke hira da Amarya nan kuwa sai ci mata fuska take, daga ƙarshe aka sa waƙa ta sanya su a gaba taita rawarta har sauran ƙawaye suka shigo, Kattume ma ta shigo aka ci gaba daga inda aka tsaya, Magriba nayi aka kashe kiɗa danyin Sallah, ganin haka yasa Rabi hankalinta yayi gida, sai dai data tuna cewa ɗazu Dj ya harareta lokacin tana tsakiyar fili, shiya sa ta ce saita rama zata tafi,  wani tunani tayi ta sanya dariya, can inda aka ajiye sifiƙun kiɗan taje, aikuwa tana zuwa ta taƙarƙare ta hankaɗa su suka zube a ƙasa, batai ƙasa a gwiwaba ta yi kan Amarya dake tsaye da ƙawayenta, ta ja zargen da tayiwa zanin dake jikinta, aikuwa ta tafi da shi, saiga zani a ƙasa sai wani baƙiƙƙirin ɗin under daya ji jiki ta bar mata, ai kuwa ta durƙushe a ƙasa tasa kuka, Dj Isiya kuwa kan kayansa ya nufa yana ɗura ashar, Rabi kuwa ƙafa me naci ban baki ba, ta falfala da gudu tayi hanyar gida, Abokan Dj Isiya da Ƙawayen Amarya suka mara mata baya, Kattume kuwa ɓuya tayi dan karta jaza mata salalan tsiya, tabi ta wata hanyar ta koma gida.






Inna da Baba ne zaune suna hira, Abinci Baba yake ci Inna tana masa fifita, jin banko ƙofa da ƙarfi yasa su kallon hanyar shigowa, Rabi ce a guje ta shigo tayi hanyar Banɗaki, su maƙarraban Dj Isiya ne suka shigo sai Amare dake bayansu, "Wallahi saita biya, a fito mana da ita!!!", cewar Samarin Dj, ƙawayen Amarya kuwa faɗi suke "wallahi sai mun mata shegen duka!!", Inna da Baba kuwa miƙewa sukai suna jin bakin kowanne, wasu ne suka shigo daga baya,   dubawar nan da zanyi na hango Amarya da Angonta Harisu da mai Dj wato Isiya.✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️





Wannan kenan



*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*





*Bu Rumy*



*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 15-16*

>>>>>>>>>>>Sudai su Inna tsayawa sukai suna kallon iko na Allah, wannan shi ake kira ɗan kuka shike jawa uwatar jifa, kallon kallo ake tsakanin su Baba da basawan da Rabi taje ta tsokano.




Baba ne yayi ƙarfin halin dakatar da hayaniyar da ake "Bayin Allah mu samu guri mu zauna kuyi min bayani, ba yadda za'ai na fahimci abinda ya kawo ku kuna hayaniya", "ba wani zama da zamuyi, wallahi nidai a biya ji kayan sana'ata kawai na tafi", cewar Dj Isiya da gashin kansa kamar sheƙar ungulu.



"To naji bayanin ka, idan na fahimta Rabi ce tayi maka ɓarna ko?", cewar Baba, "ƙwarai kuwa ita ce  ta fasa min sifiƙu na".



"Tom shi kenan ka faɗi nawa ne kuɗin", cewar Baba.



"Dubu biyar ne kuɗi na", cewar Isiya.



"Shikenan babu damuwa", Baba ya faɗa sannan ya saka hannu a aljihu ya lalo kuɗin Isiya Dj ya bashi, ya amsa yaja zugarsa sukai gaba.




Sai kuma Baba ya maida hankalinsa kan Amare da Angwaye, fuskar Amarya da tayi jage-jage Baba ya kalla ya ce "to ku kuma maiya faru?", nan wata zaƙaƙura mai suna Sabira ta ce "Muna tsaye da Harira kawai sai tazo ta cire mata zani, a filin Allah ta'ala a wajen bikinta, wannan ai tozarci ne da tonon silili", cewar Sabira.




"Subhanallahi, wannan ai kamar Harirar me unguwa?", Baba ya faɗa.



"Ita ce mana, ai yaune ake bikinta", Inna ta faɗa.



"Ashsha amma wallahi Rabi bata kyauta ba, kuma saina hukunta ta, dan Allah kiyi haƙuri, babu abinda zance sai haka, kiyi haƙuri, zan ɗauki mataki akan Rabi, kaima Harisu kayi haƙuri dan Allah", Baba ya faɗa, kafin ya ciro kuɗi a aljihunsa ya danƙawa Harisu sannan ya danƙawa Harira ya ce gashi ayi alibidin biki, ai nan take zance ya mutu suka tashi suka fita suna godiya.



Numfashi Inna da Baba suka sauke, ran Baba da Inna wannan karon ya ɓaci sosai, lamarin na Rabi ya tiƙe su "Kina ina fito!!", Inna ta ƙwalla mata ƙira wanda kana ji kasan ranta a ɓace yake, Rabi dake bayan gida taji duk yadda aka ƙarke, tana kan kujerar zama tayi wiƙi-wiƙi, jin Inna na ƙira yasa ta tashi ta fito kamar munafuka, ganin fuskar Iyayen nata a ɗaure yasa tasha jinin jikinta, batai aune ba Inna ta janyo ta ta hau jibga tana faɗin "Na gaji da wannan iskancin naki Rabi, ace kullum saikin janyo mana abin faɗa, baki yayi miki yawa a gari, ko wane gida suna zaune luf da Yaransu lafiya amma ban da mu, har nuna mu ake idan mun fita, to wallahi na gaji zan ɗauki mataki a kanki Rabi bazan bari hawan jini ya hauni sa bo da ke ba", dukan ta take tana faɗa, Baba daƙyar ya ƙwaci Rabi da take ta kuka, tana bawa Inna haƙuri amma inaa Inna zuciya taciyo ta, "ya isa haka Ƙanwa", cewar Baba daya janye Rabi daga Inna, "Baban Rabi na gaji wallahi, haba ace ƙanƙanuwar Yarinya amma tabi ta addabi mutane kowa magana yake a kanta, Allah ba zai yuwu ba dole musan abinyi, ba komai nake tsoro ba illa wata ran ba fata nake mata ba ta tsokano wanda zai cutar da ita, ko ta tsokani Aljan, kawai zanyi magana da Rabi'u tinda dama ya ce yana so ya ɗauki Rabi ya maida ta binni", ta faɗa bayan ta zauna tana hararar Rabi data raɓe a gefe tana maida ajiyar zuciya.




"Yanzu dai kiyi haƙuri ki nutsu, zamu tattauna batu akan haka, amma ki kwantar da hankalinki, in sha Allah wataran sai labari, amma duka babu abinda zaiyi, nasiha da Addu'a ita zamu dage mata", Baba ya faɗa.



"Kinyi sallah ko baki ba?", Inna ta daka mata tsawa, "A'a banyi ba", Rabi ta faɗa tana shashsheƙa, "to Uban me kike da bazaki tashi kije ki ɗau buta ba", tashi tayi ta je ta ɗauki butar tayo Al'walla tazo tayi sallah, tana idarwa ta je gaban Baba ta gaishe shi kamar yadda ta saba, amsawa ya yi yana shafa kanta, juyowa tayi ta gaida Inna tayi mata banza, kuka ta saka sosai, tana jin babu daɗi akan Inna tadena mata magana shi kenan wuta Allah zai sata, Baba ne ya ce "Ya isa Rabi'atu Inna bata jin daɗin abinda kike haka nima ban jin daɗi, Rabi'atu keɗin Yarinya ce bazaki gane abinda muke miki tsoro ba, ki tsokani wannan yau ki tsokani wannan gobe hakan bai dace ba Rabi, dan Allah ki nutsu Rabina, idan kika dena Innarki da ni kaina zamuji daɗi kuma zamuyi miki Addu'a Allah ya saki a Aljanna kinji, dan haka ki bawa Inna haƙuri", juyawa tayi ta kalli Inna da duk ta cukule "Inna kiyi haƙuri bazan kuma ba kinji, dan Allah kimin magana", ta faɗa tare da fashewa kuka, tausayi ta basu barin Inna da nan take taji ba zata cigaba da fushi da ɗiyar tata ba, yasa ta kamo hannunta ta dawo da ita kusa da ita ta rumgume tana faɗin "Na haƙura Adabiyya ta, sai dai idan kika kuma zanta yin fushi  kuma bazan ƙara kula ki ba", "eh bazan kuma ba Inna", nan taita sata dariya harta saki, Abinci suka ci a kwano ɗaya, dambun masara tayi yaji gyaɗa da zogale, sai tashin ƙamshi yake.







Kwana biyu shuru babu wani abu da Rabi tayi, ta nutsu zata fita lafiya kuma zata dawo lafiya ba tare da ta tsokani kowa ba, gari ya samu lafiya kwana biyu, gefe guda Inna takan zaunar da ita taita mata nasiha da hikima.






Zaune suke a tsakar gida Inna tana tsefewa Rabi kitso, wanda yaci ubansa ko tsaga babu sa bo da rashin son kitso, bata son batun tsifa, shine yau Inna ta tirke ta take mata tsifar, sallama akayi daga soro, "Rabi wa nake ji kamar Hamman ki?", ta faɗa tana ƙara saurara, ai kuwa a ɗari Rabi ta fincike kanta daga hannun Inna ta fita a guje, ilai kuwa Hamma Abdul ne yake ɗakko kayansa daga ɗansahu yake sawa a soro, ai sai ihun Rabi yaji tare da ɗafe shi, tana faɗin "Oyoyo Hammanaaaaaaa!!!!!",  ta faɗa da ƙarfi a kunnansa saida ya toshe, shima murna yake na ganin tilon Ƙanwarsa da babu kamarta a rayuwarsa, juyi yayi tayi da ita kana ya sauke ta yana maida nunfashi, "litle kin ƙara nauyi Allah", cewar Hamma Abdul, "Hamma mene kuma litili?", dariya yayi sannan yace "muje zan gaya miki".






Gaba tayi da wasu kayan tin daga zaure ta fara ƙwala ƙiran Inna "Inna ga Hamma na ya dawo!!!", Inna miƙewa tayi tana "Maraba lale baƙin Maiduguri", dukda tana jin kunyar ɗan fari hakan bai hana ta nuna farin cikin dawowarsa ba, shikam zuwa yayi ya rungumeta harda sumbatar ta a kumatu, aikuwa tureshi tayi tana faɗin "kaga Yaro da tselen uwa", "Inna nifa Allah ana tauye ni, kibar kunyar ɗanfari ki nunan soyayar da kike min",  ya faɗa yana mata dariya, ita ma dariyar tayi, nan ta cika gabansa da kayan ci da sha irin namu na ƙauye, fura yasha mai kyau da garɗi, Rabi kuwa ta samu guri ta zauna a gefansa sai kallonsa take kamar taga sabon abu, kula yayi da ita "dear mene haka kika tsare ni da ido?", "Hamma dan Allah kaine kuwa?", cewar Rabi, "A'a ikon Allah kina kokonto ne Ƙanwata?", "gani nai ka girma wallahi", dariya yayi sosai, Inna ma saida ta dara, "Boɗɗo wai har yanzu baki dena shirme ba?", baki ta cuno jin yace tana shirme, ganin zatai kuka yasa shi rarrashi "Idan kikai kuka zan koma, kuma bazan baki tsarabar da na kawo miki ba", jin ance tsaraba yasa ta wangale baki, haka suka zauna abin sha'awa yana ta janta da wasa sunai suna dariya.






Abdulrahman kenan, Yaya da Rabi, Kyakykyawa ne sosai fari yana da tsaho sosai, murɗaɗɗen jiki ne da shi, gashi gwanin fara'a, suna kama sak da Rabi sai dai ita batada ido kamar nasa, ita Idanuwanta masu haske ne idan tana kallon ka sai kagan su a tsaitsaye, barin idan ta tashi rashin mutunci,






Baba yana dawowa ya taras da Abdul ya dawo sosai yayi murna da ganin Ɗan nasa, kuma an samo abinda aka je nema, karatun Addini yaje yayi, babu littafin da bai haddace ba, daga baya ya shiga Boko nanma yanzu yayi NCE ɗinsa, ya dawo gida gaba ɗaya yanzu.







*KANO*


Shiri Mammy take na tarbar Maigidanta Alhaji Rabi'u, yau zai sauka, girke-girke suke ita da Khausar, sai mai aikinsu Jimmala da take taya su, babu ɓata lokaci suka kammala komai, aka ƙara gyara gida aka turare ko ina da turarukan ƙamsasawa, nan take ko ina ya ɗauka, Muhammad ne zaije ɗakko shi, Khausar sai magiyar ya tsaya suje tarbo Daddyn tare take amma yaƙi, haka ba yadda ta iya ya tafi, ƙarfe 12 dai-dai jirginsu ya sauka a Aminu Kano Airport, basu jima ba suka fito, can na hango wani ɗan matashin mutum mai cikar kamala da tsantsar kwarjini suna kama sosai da Innar Rabi, sanye yake cikin ƙananan kaya baƙaƙe, yayi kyau matuƙa, farin Bafulatani kenan, Jakar kayansa dake hannunsa brown, Muhammad daya hango shi ya iso yana zuwa ya faɗa jikinsa yana faɗin "Oyoyo Daddy" 



Rumgumarsa Daddy yayi tare da faɗin "Oyoyo my heartbeat Muhammadu".


Jakarsa ya amsa ya isa Mota ya buɗewa Daddyn ya shiga shima ya shiga yaja suka nufi gida, suna tafe suna hira yana tammayarsa mutan gida.







"Naga garin naku Malam Tsalaha akwai Yaranda muke buƙata, amma kai sai anyi magana da kai kaita kakkaucewa wannan harkar ta ƙaruwa ce zaka ƙaru nima zan ƙaru, siyasa ta matso wallahi Ogana yana buƙatar Ƴan shila, waɗanda basu fara jinin al'adha ba, kuma basu fara Nono ba",cewar wani mutum.




"Alhaji Nura nifa harkar nan bana iyata wataran asiri ya tonu kuɗin da zan samu bazai min amfani ba, kuma kace min Bokansa ne yake cewa a kai Yaran kaga kenan tsafi za'ayi dasu, gaskiya bazan iya ba", cewar Malam Tsalaha.





"Hmmmmm kadaiyi tunani, nidai wallahi ina son na janyo ka daga ƙangin talauci, dube ni ka gani, naje hajji sau uku, mota ta biyu, ina da gidaje biyu da filaye, ga mata har huɗu, ni zan iya komai akan kuɗi kaganni,  kayi tunani zan kuma iya samun wani yayi min a ciki garin nan ka sani", Alhaji Nura ya faɗa.






Jim Tsalaha yayi yana nazari, can ya nisa ya ce "zanyi tunani Malam Nura ka bani ɗan lokaci", "zan baka lokaci amma  daga nan zuwa jibi, idan baka ƙare a zan nemi wani", yana faɗa ya shige motarsa yabar wajen, Tsalaha ya tsaya a wajen yana nazari.





Tofa me wannan yake nufi?.




Wannan kenan




*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*






*By Rumy*



*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 17-18*

>>>>>>>>>>>Alhaji Nura bayan ya shiga Motarsa ya baza ta kan hanya, gudu yake kamar zai tashi sama, wayarsa ce tayi ƙara ya rage gudun ya duba, ganin me ƙiran yasa shi tsayawa kana ya ɗauka cikin girmamawa "barka dai ranka shi daɗe", daga can ɓarin aka ce "kazo inda muke haɗuwa yanzu", bai bari Alhaji Nura yayi magana ba ya datse ƙiran, wuta ya ƙara bawa motar ya tafi, wata hanya ya yanka wadda daka ganta kasan babu masu rayuwa a cikinta, bai jima yana tafiya ba ya fito, ya kulle motar ya fara takawa da ƙafa yana bin hanyar, hanya ce babu ko kiyashi me rai, ga shi surƙuƙi, baka jin kukan komai, shi kuma da alama ya saba bi dan ko alamar tsoro babu tare da shi, ya jima yana bin hanyar, sai gashi a wani fili, da ɗan wani madaidaicin gida, wanda da alama babu wani mahaluki daya san gidan sai su, yana isa ya shiga cikin gidan wasu mutane ne gasu nan da jajayen kaya, idanuwansu a tsaye basa ko ƙiftawa tin daga bakin ƙofa yake cin karo da su, kuma ko gezau haka ya ƙetare su ya shiga abinsa, yana shiga wani ɗaki ya ya tsaya ya cire kayansa tik daga shi sai naman jikinsa, ya ɗauki jar riga doguwa irinta waɗan nan mutane ya sanya,




Bayan ya sanya ya shiga ta wata ƙofa, yana isa naga Mutane ne fal a ciki duk da wannan shiga ta jan kaya, yana isa ya nemi gu ya tsaya sannan ya duƙar dakai, wata Tsohuwar mata wadda babu ko ɗigon imani tattare da ita, babu riga a jikinta Nonon nan yayi raɓeɓe, sai zazzare ido take tana kallon kowanne, tsaida idanunta tayi akan wanda yake gefan ta, cikin wata murya ta ce "Autan Dodanya zuwa yanzu mum gaji da uzirirrikan da kake kawo mana, da dai baka mana fashi idan muka buƙaci abu, amma yanzu ka lalace, gaskiya wannan karon ba zamu lamunta ba, dole ne ka kawo mata Ƴan matan da Dodanya ta buƙata", ta faɗa tana zare ido, wanda akaiwa wannan magana ne ya ɗago kai ya dubi Alhaji Nura, kai ya sunkuyar kana ya ce "Dodanya ta taimake ki, a ƙara min ɗan lokaci zan kawo".




Wani gurnani Tsohuwar tayi sannan ta miƙe ta ɗauko wani ƙoƙo ya miƙawa shi wannan Autan Dodanyan da naji ta ƙira, karɓa yayi ya kurɓi abinda yake ciki, ya bawa na kusa da shi a haka har saida kowa ya sha sannan aka dawo dashi hannun Tsohuwa ta amsa ta aje, daga nan ta sallami kowa yayi nasa waje, suna fita kowannan ya shiga ɗakin da yake kwaɓe kaya, bayan sun sanya suka fito, babu wanda yayi magana sai da suka yi nisa da wannan gidan sannan, Autan Dodanya ya kalli Alhaji Nura ya ce "Kasan dai babu lokaci, amma na rasa sanin me ka tsaya yi har yanzu baka samo su ba, ko dai zan bawa wani aikin nan ne?", ya faɗa ransa a ɓace.



"Kayi haƙuri Oga wallahi ina iya bakin ƙoƙari na, yanzu haka ma daga ƙauyen Yana na fito, ina sa ran anan za'a dace, sai dai kuma dole sai anyi takatsantsan, ka ƙara min ɗan lokaci", numfashi ya sauke kana ya ce "shikenan kayi dai abinda ya dace", bayan sun gama tattaunawa suka isa motarsu kowanne ya shiga ya bata wuta ya wuce.





Tofa waɗan nan kuma su waye masu neman duniyar?.






Daddy yana isa gida a filin farfajiyar gidan ya haɗu da su Mammy da Khausar, da masu aikin gidan, cikin farin ciki suka tarbe shi haka shima, amsawa kowa gaisuwarsa yake, daga haka suka nufi cikin gidan, direct side ɗinsa Mammy ta jashi dan zuwa ya watsa ruwa, side ɗinsa a sama yake, suna isa wani ƙaton falo suka ɓulla kalar kujerun falon da cotton ɗin duk dark blue ne, ya tsaru matuƙa, sai tashin ƙamshi yake, bayan ta taya shi ya rage kayan jikinsa, ya shiga toilet, yayi wanka da ruwan da ta haɗa masa mai ɗauke da sinadaran ƙamshi, bayan ya fito tini ta fito masa da kaya marasa nauyi, Jamfa ce da wandonta sai white t-shirt, taya shi tayi yasa ta feshe shi da turare, kamo ta yayi ya rumgume tare da sumbatar goshin ta ya ce "ina kewar ki abar ƙauna, gaskiya yau ki tarbeni anjima", kallonsa tayi cikin son mijin nata da kewarsa ta ce "ina maraba dakai Mai martaba", ta faɗa tana mayar masa da sumbatar da yayi mata, "muje kar Abincin ka ya yi sanyi", "ni dama kibar abincin kizo ni wannan abincin yafi min wancen", dariya tayi ta ce "Daddyn Saheeb Allah fitinarka yawa gare ta, kazo muje kasan dai Yaranka suna can kai suke jira", ta faɗa tana janyo shi kamar ƙaramin Yaro.




Suna sakkowa ilai kuwa Muhammad da Khausar suna zaune suna jiran su, ganinsu yasa su miƙewa alamar girmamawa, yana sakkowa ya kamo hannu Khausar ya ce "Auta ya karatu, hala dai kina bada himma ko?"  ya faɗa cikin kulawa, "Daddy ina dagewa sosai, Exam ma muke da niyyar farawa", "good Ɓoɗɗo na, ki dage Allah ya baku nasara", ya faɗa yana  duban Muhammad, "kai kuma ya naka karatun?", sosa kai yayi ya ce "Daddy next week zan koma dake munyi Exam sai muka ɗan samu hutu", "ok kadai dage, na kusa maka transfer zuwa University of Mama Taresa dake Mumbai, yanayin karatun ka nanan baya tafiya yadda nake so, gashi kana son zama Medical Doctor, dole can ne ya dace da ka tafi, ina ta maka preparation akwai wanda zan haɗa ka dashi", ya faɗa bayan ya zauna akan dinny chair Mammy ta fara saving ɗinsa, Muhammad kuwa ya tsani barin ƙasarsa, amma ba yadda ya iya tinda Daddy ya matsa, haka suka ci abincin cikin nutsuwa, babu mai cewa komai, (haka ƙa'idar cin abinci take ga dukkan  musulmi, idan yayi bismilla saiya maida hankali akan abinda zaici, harya gama karyayi magana sai idan ta zama dole, hakan sunna ce, Allah yasa mu dinga yi karmu manta ameen).




Bayan sun gama falo suka koma suka zauna ana hira cikin soyayyar ahali, Khausar ce ta ce "Daddy wannan karon ina zamu at the end of this year?", Daddy ya ce "ku zaɓa ku darje sai inda kuke so", Muhammad ne ya ce "Daddy nikam ina son zuwa Bauchi dan jiya munyi waya da Hamma Abdul ya dawo, ya kammala karatun shi", "Ah Abdul ya ƙare karatun shi, masha Allah, munyi waya da Giɗaɗo kuma bai gaya min ba, shi kuma Abdul wayarsa bata fiye shiga ba", (Giɗaɗo da ya ce yana nufin Baba Umar Mahaifin Rabi, dan haka suke ƙiransa a Ruga).




"Ah masha Allah, lallai Abdul an zama alaramma", cewar Mammy, "aikuwa dai ai Yaron akwai himma, sai dai ina son shima ya koma makaranta, dole ma zamu Bauchin, Ga Adda bata son riƙe waya,  sau uku ina saya mata tana yarwa", cewar Daddy.



"Haka zaka kuma saya mata wata idan zamu mu tafar mata da ita, dan ina son na dinga ƙiranta wallahi ba dama, ga shi ina son naji ya Ɗiyata take yanzu, dan nasan ta girma", Mammy ta faɗa.



Dariya Muhammad yayi ya ce "cafɗi wallahi kwanaki da naje Mammy bakiga zugar da ta tsokano ba daƙyar na samu na saita lamarin, ai wallahi su Inna suna fama", "hmmm aini Hamma Muhammad wannan Yarinyar ta shani na warke, daga cewa ta raka ni gari na zaga, ta kaini wani guri cike da ƴan mata irin su, bayan ta nuna ni wai Yayarta ce ta binni, sannan ta ƙara ɗiba ta bamu zame ko ina ba sai wani gida, ina tambayarta ina ne nan taimin banza, ƙarshe muna shiga ta ce "to masu cewa suna da Ƴan uwa a binni, to ga Adda ta na kawo muku ku ganta, ƴar gayu kuma Baffana na birni shine ya haife ta dan kutumar uban ku", ai kuwa Hamma banyi aune ba naga zuga guda ta gidan tayo kan mu, gani ban iya gudu ba na tsaya ina lailaya jiki, sai jin duka nayi kota ina, ita kuwa almura ta jima dayi min nisa, kuka nake ina basu haƙuri amma basu jina saida sukai min lilis suka barni, na fito na hango ta wai Yarinyar nan ba saita hau min dariya ba, wai wallahi Adda Khausar kamar fidodido haka kika koma, kinga kafaɗunki kuwa, ban san sanda kuka ya kuma kufce min ba dan takaici, aikuwa ranar tasha duka wajen Inna", ai ba Muhammad ba hatta Daddy, Mammy dariya suke sosai, cikin dariya Mammy ta ce "wallahi shi yasa nake son a dawo min da Adabiyya nan, ina son comedyn Yarinyar, ina sonta wallahi", Daddy ya ce "ai sun hana ni, amma idan sun san wata ai basu san wata ba, zanje Mambila na haɗa su da Harɗo", "Daddy ta dawo nan fa kace?", cewar Khausar, "Eh mana nan zata dawo fidodido", ya faɗa da tsokana, ai kuwa cikin shagwaɓa ta miƙe tayi ciki, Muhammad dariya harda riƙe ciki, "Wallahi na samu suna", cewar Muhammad,




Daddy faɗi ya ke "dawo mana Auta na kiyi haƙuri", Mammy kam in banda dariya babu abinda take.







Wannan kenan






*Alƙalamin mu ƴancin mu✍️*






*By Rumyn Royal Star*



*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




                                                

"Ka ambaci Ubangijinka a cikin zuciyarka, kana mai ƙasƙantar da kai da kuma jin tsoro, ba da ɗaukaka murya ba, (tsaka tsakiya) safiya da maraice, "(A'araf, 205) wasu kenan daga cikin Ayoyin falalar zikiri.

Kaɗan kuma daga Hadisan Annabi (s.a.w):

Manzon Allah (s.a.w) ya ce "Misalin waɗanda suke anbaton Ubangiji Allah da waɗanda basa anbaton sa kamar misalin mutum ne mai rai da kuma mara rai".

Allah yasa mu dace da Ambaton Allah a kowane lokaci ameen.





*Page 19-20*

>>>>>>>>>>>>>Yau kwanan Hamma Abdul huɗu da dawowa, wannan yasa Rabi bata fiye fita ba dan ya hana ta, daga makaranta sai gida, data dawo daga ta boko zai kora ta ta Allo, tana dawo wa suyi lesson a gida, wannan yasa yanzu gari yayi lafiya, bakin su Inna ya zauna babu kaya-kaya.



Hamma Abdul ne cikin shirin sa na fita gari, yayi wankansa sai ƙamshi yake, yai kyau abinsa, ƙananun kaya yasa kalar green da white takalminsa green yayi kyau, gashin kansa da yake tarawa irinna fulani tsarin da yayi mata ya ƙara masa kyau, "Inna na fito zan ɗan fita gari", "aikuwa ya kamata, tinda ka dawo banga ka leƙa ko ina ba, Allah ya tsare ya kare", cewar Inna data leƙo daga ɗaki, da sauri Rabi ta bankaɗo labule sanye take da wata doguwar riga baƙa tayi mata  kyau sosai dan harda mayafinta, takalminta ja toms duk jikinsa stone, tayi kyau sai haskenta ya ƙara fitowa sosai, "Hamma dan Allah mu tafi tare, na gaji da zaman gidan kaji", "Rabi'a ki zauna wajen Abokaina fa zani, kawai kuma saina tafi dake, hala ƙafarki ce take ƙaiƙayi?", "Allah Hamma zazzaɓi nake idan ka tafi ka barni ƙara rufe ni zaiyi", dariya ce ta kama Hamma Abdul sai dai baiyi ba ya sha mur ya ce "bana son musu babu inda zaki, idan kuma kika fita nida ke ne, kuma batun zazzaɓi da kike idan kika kwanta zai dena, kar inji kar in gani, tom", ya faɗa tare da ƙaraiwa Inna sallama ya fita.





Yana fita ta zube a wajen ta kurma ihu, tana shure-shure Inna kuwa ɗakinta ta koma ta cigaba da sabgoginta hankali kwance, sosai Rabi ta tumurmusa kayan jikinta suka ɓaci, duk da siminti ne  amma akwai ƙura, bayan ta gama ihunta da tumami a wajen bacci yayi gaba da ita.







Tsalaha yayi iya tunaninsa akan lamarin nan da Alhaji Nura ya kawo masa yaga cewa kawai ya amince, tinda ya ce babu wanda zai gano su, wayarsa ƙirar Tecno irin keypad ɗin nan, ƙatuwar nan me tsinannan ƙara ya ɗakko, bayan ya nemo layin Alhaji Nura ya  ƙira, bugu uku ana huɗu ya ɗaga "Salamu alaika Alhajin Allah, barka da warhaka", ya faɗa da ɗaga murya yana washe haƙora irin ta shiga yana jina ɗinnan, daga can aka ce "Malam Tsalaha barka dai ka yini lafiya?", "lafiya ƙalau Alhaji", sai kuma ya sassauta murya yayi ƙasa-ƙasa da ita ya ce "dama  wannan batun ne na yanke sahawarar na yarda Alhaji",




"Masha Allah haka nake so naji, kaga yanzu ka zama ɗan gari, zan ƙira ka mu tsara yadda abin zai kasance", cewar Alhaji Nura.



"To madallah Alhaji, saina jika ɗin", yana gama wayar ya sauke ajiyar zuciya sa'an nan ya maida wafceciyar wayarsa a aljihu, juyowar nan da zaiyi sai sukai ido huɗu da Matarsa Rakiya, ai nan take ya birkice yahau masifa "a duk duniyar nan na tsani munafunci, ashe zuwa kikai kika gama  jin abinda nake cewa sa bo da kin riƙa a harkar munafunci ko, to a hir ɗinki wallahi ki kiyaye ni bani da kyau kinji na gaya miki", tsayawa tayi tana kallon ikon Allah, Rakiya irin ruguza-ruguzan matan nanne masu teɓa, shirgegiya ce ajin farko da aukinta, timbinta zuguda guda, ya haɗe da  naman bayanta, idan tana tafiya hannunta har wani buɗawa yake, idanuwanta a zagaye kamar na kura, hancinta kuwa kamar gajeran wandon da robarsa ta saki, bakinta kamar na mai shan wiwi baƙiƙƙirin  leɓanta, binsa tayi da kallo, tare da yin ƙwafa,





Shi kuwa Tsalaha irin siraran mutanan nanne kamar an tada akuya a tsaye, ko kaɗan bashida ƙiba, fuskarsa fal gunduƙuƙi, bakinsa a wadace yake da sharɓeɓen leɓe, hancinsa ɗan ƙuƙit kamar an ɗiga masa, shi yasa idan yana magana da hanci yake yinta, Idanunsa kuwa kamar na wakilin kwarto, a firgice yake totally ɗinsa, ficewa yayi daga gidan yana ta tsaki, yana faɗin "wallahi aure zanyi ina samun yadda nake so, shegiyar mace kamar tubali kin sani a gaba ga baƙin talauci gaki, kin uzzirawa rayuwata, wallahi na gaji", ya faɗa tare da auna wani dogon tsaki.








Inna fitowa tayi taga Rabi a kwance tana sharɓar baccinta hankali kwance, murmushi tayi kana ta girgiza kai, tayi hanyar madafa, girki take ƙoƙarin ɗorawa, ganin magriba ta gabato ya sanya ta zuwa ta tashi Rabi, ɗan bubbukata take tana faɗin "Ke tashi Magriba ta gabato, ba'a son baccin irin wannan lokacin", tashi tayi ta zauna, har Inna ta juya dan komawa madafa sai jin ihun Rabi tayi, tana yi tana shushahura ƙafa, wai ashe tuna abinda ya faru tayi ɗazu, ai kuwa da sauri Inna ta dawo da niyyar make ta, ai ganin haka yasa ta miƙe tayi ɗaki da gudu, "da ki tsaya dana ci ƙaniyarki wallahi, Yarinya sai iya shege kala-kala", a ɗakin ma zama tayi tana ƴan ƙananun koke-koke duk dan an hanata fita.






Shi kuwa Hamma Abdul yana fita gari ya shiga suna gaisawa da Abokanansa, gidan su Abokinsa yaje Kamilu a ƙofar gidan ya tsaya ya aika Yaro ya ƙira masa shi, aikuwa da Yaron suka fito, "kai wa nake gani kamar Abdulrahman nawa?, anya ba gizo bane?", ya faɗa da farin ciki a tare da shi, "nine Kamilu, kana  mamakin ganina ne?", 


"Wallahi Abdul ka wani irin canzawa kai kaganka kuwa, anya ba Aure kayi ba kuwa, kai ana karatu a rame amma kai murmurewa kayi abinka" cewar Kamilu.



"Yanzu dai dan Allah ka ƙyaleni haka mu samu guri mu zauna, sai kayita zaro zancen naka" Hamma Abdul ya faɗa yana dariyar Abokin nasa.




Wani kututture suka zauna, hannu ya bashi suka gaisa "kan ubancan wallahi hannunka kamar bana maza ba, kai ka ji kuwa, Abdul gaskiya karatu ya amshe ka hannu bibbiyu", dariya sosai Abdul yake dan mamakin Abokin nasa yake da shiririta, "kaga Malam dan Allah ka tsaya haka, yau kwana na huɗu da dawowa, ban samu fitowa gari ba sai yau, yana same ka, yasu Baba Hauwa da Ƙannenka?", "Masha Allahu, wallahi kowa lafiya yake, amma ai zaka shiga kafin ka wuce ku gaisa, dan tana yawan min zancen ka wallahi, ni kasan tin wani lokaci da mukai waya dakai, wallahi bamu ƙara ba idan na ƙira ka bata shiga, haka tin inai na haƙura", cewar Kamilu.




"Eh gaskiya akwai matsalar network, wataran ɗaukewa yake ɗif wallahi", hira sukai tayi, daga ƙarshe ganin magriba ta gabato suka shiga gidan su Kamilu suka gaisa da Mahaifiyarsa, fitowa sukai Kamilu ya rako shi hanya  dan tafiya gida.






Kattume ce zaune a gefan Baba Saude tana cin tuwon dawa miyar bushashahiyar kuɓewa tasha wake, bayan ta haɗiye lomar data kai bakinta ta ce "Baba kwana biyu Rabi bata fitowa, daga makaranta sai gida, dan Allah zani na ganta, idan na gama cin tuwon", "ki fita a wannan almurun, ki barwa gobe mana, amma ba zaki fita da wannan duhun daya kawo kai ba, kuma Rabi na tabbata Yayanta ne ya hanata fita, kinga Innarta kwana biyu zata huta da sallallami", ta faɗa bayan ta ƙarawa Kattume miya a tuwon ta da taga ta shanye, ba haka Kattume taso ba haka ta haƙura.









             *Kano*


"Ok dear Allah ya kaimu, gaskiya munji daɗin dawowarka, atleast three years fa ai dole munyi missing over, Khausar tana Makaranta, Muhammad kuma yana tare da Daddyn ku a Kasuwa", da alama waya take da wani mafi muhimmanci dan naga farin cikinta ya kasa ɓoyuwa, tana kammala ƙiran wani ƙiran ya shigo, da dariya ta ɗaga tare da cewa "ai wallahi nayi fushi Yaya Talatu, ke fa kika cemin jiya zaki zo amma naji ki shuru maƙatau", daga can ɓarin aka ce "wallahi Nawwara ce bata jin daɗi shine tasa rigima ni zan kaita taga Doctor shi yasa kika  jini shuru, naso na ƙira ki wallahi na manta shaf, ya kike ya su Khausar?", cewar Talatu.



"Ayya kice Doughter ce ba lafiya, me ya same ta haka?", cewar Mammy




"Wallahi zazzaɓi da mura ne suka kama ta, kuma yawan shan iceream ne da take, nayi-nayi ta dena ta ƙi", "Ai Yara sai haƙuri, Allah ya bata lafiya, amma dai yanzu da sauƙi ko?", "da sauƙi sosai tama je Makaranta, dama na ƙira ki ne na baki haƙuri jina shuru", 




"Ba komai Yaya Talatu, ga albishir gare ki", cewar Mammy



"Ɗanki nanda kwana biyu zai shigo Ƙasar bayan shekara Uku da yayi baya cikinta", Mammy ta faɗa cikin nuna farin cikin ta.




"Kai amma wallahi naji daɗi, kice muna da babban baƙo, dan ya zama baƙon mu yanzu kam, masha Allah, rabbi ya tsare shi ya dawo mana da shi lafiya, jibi muna tafe tarbar Babban Yayansu", cewar Yaya Talatu.





Cikin jin daɗi Mammy ta amsa, daga nan sukai sallama ta aje wayar, miƙewa tayi dan shiga Kitchen, dan Mammy bata yarda da Ƴar aiki tayi mata girki ba, sai dai ta taya ta suyi.



 (haka ake  buƙatar mace, mara ƙiwa a lamuran gidanta, karki ce zaki sakarwa Ƴar aiki komai ita zatayi, a'a ki tashi kema kiyi duk abinda kika san na mijinki ne da hannun ki, akwai lada mai tarin yawa, sannan zaki ƙara ƙima da daraja a tare da shi, dan Allah mu kula mata).





Asalalin Mammy Ƴar garin Kano ce a Unguwar Daneji, wato cikin gari, Mahaifinta Alhaji Muhammad haifaffen wannan Unguwa ne, asalima shine mai Unguwar Daneji, da Mahaifiyar su Mammy Hajiya Batula, mace mai kirki da sanin yakamata, su uku Iyayen su suka haifa, Yaya Talatu ita ce babba sai Mammy sai kuma Ƙaninsu Alhaji Habibu, 



Alhaji Habinu Yaron Daddy ne a Kasuwar Kantin Kwari, dalilin haɗuwar Mammy da Daddy sunje Kasuwar duba Ankon bikin Yaya Talatu, to anan Daddy ya yaba da hankalin Mammy na nutsuwa da sanin yakamata, akasin Yaya Talatu mai wani irin hali, dan gaɓuwa ce sosai idan tana wani abin kamar bamai ilimi ba, Mammy da Alhaji Habibu sune kaɗai sukai halin Iyayensu, 




Wannan haɗuwa ita ta sanya soyayyar Sumayya wato Mammy a zuciyar Alhaji Rabi'u, bayan tafiyarsu ya ke tambayar Alhaji Habibu akan anwa Mammmy Miji, ya ce masa bata tsaiwa da kowa, to daga nan Daddy ya  cusa kansa ga Mammy wadda nan take ta amince dan ita ma yayi mata, sun jima suma soyayya har akai bikin Yaya Talatu ta haifi babban Ɗanta Hafiz, sannan akai auren Mammy, 





Tinda akai auren Yaya Talatu take zuga Mammy akan ta tatsi Daddy son ranta tinda ya tara, kuma tayi ta zuga ta akan karta sake ta bari dangin sa na ƙauye suna zuwa inda yake, duk wannan zuga da Talatu takewa Mammy bata ɗauka, hakan yasa Yaya Talatu take mungun jin haushin Mammy, ranar da dubunta ta cika, lokacin tazo gidan Mammy suna ɗaki sai zugata take akan ta yagi abinda ta yaga, bata zauna haka sai abinda miji ya ɗakko ya bata shi zata haƙura da shi ba, ran Mammy idan yayi dubu ya ɓaci dan ta gaji da wannan rashin hankali na Yayarta "kinga Yaya Talatu ki barni haka nan nayi rayuwar aurena yadda ya dace, ina kin daɗe kina min huɗubar nan, ya dace zuwa yanzu ace kin gaji, dan wallahi bazan taɓa aikata abinda kike faɗan ba, mijina babu abinda ya rage ni da shi dan haka Alhamdulillah", "gaya mata dai Ƴar albarka, wato Yaya Talatu kin bani mamaki, wai kina babba ace ke kike wannan ɗanyen aikin, gaskiya ki canza hali, Allah ya taimake ni ya bani mace mar'atussaliha, da tuni kin canza mata hali, to bari kiji daga yau idan har wannan huɗubar ce zata kawo ki gida na wallahi karki kuma zuwa", Daddy ya faɗa bayan yaji komai shugowarsa, yana gama faɗa ya fice, ita kuwa Talatu kunya ce ta dabaibaye ta, jinta take kamar ƙasa ta tsage ta shiga, ba siɗi ba saɗaɗa ta fice ta tafi, dan tama kasa magana bare tayiwa Ƴar uwarta sallama.



To tin daga wannan lokaci Yaya Talatu ta dena zuwa gidan Mammy, sai dai Mammyn taje, kuma bata ƙara zuga ta ba, sai da Mammy ta haifi Hamma Saheeb sannan ta je, nan ma bata bari sun haɗu da Daddy ba, Mammy ce ta gayawa Daddy cewar "Yaya Talatu tin ranar nan fa ta kasa sakewa bata ma zuwa gidan nan sai ranar dana haihu, baka da wasan ɓuya kuke ba?", ta faɗa cikin damuwa, to abinka da ɗan uwa rabin jiki,




"Zan ƙira ta ko kuma naje can gidan ta", Daddy ya faɗa.





Aikuwa ranar da yaje gigicewa tayi kamar mai kaya ya kama ɓarawo, haƙuri ya bata kuma ya nuna basa jin daɗin abinda take, ya kamata ta manta da komai, to tin daga lokacin ta sake, amma har zuwa yanzu tana jin shakkar Daddy sosai, dan irin mutanannan ne masu kwarjini da cika ido, amma fa har zuwa yanzu  Yaya talatu bata bar son banza ba, kuma ita ma mijinta ba laifi yana da kuɗinsa, bayan Hafiz ta haifi Nawwara ita ce sa'ar Kausar dan ta daɗe bata haihu ba.




wannan shine taƙaitaccen tarihin haɗuwar Daddy da Mammy.




Wannan kenan




*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*






*By Rumyn Royal Star*




*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 21-22*

>>>>>>>>>>>>>Washe gari da safe ta kama Asabar babu Makaranta, zuciyar Rabi a ƙuntace take kasancewar yau ma tasan babu inda zata sai Makarantar Allo, kuma ba yanzu ba saii can yamma, ranta a ɓace yake sai cika take tana batsewa, duk abinda take Inna tana ganinta banza tayi da ita, dan ta gama fahimtar ƙuncin nata.




Hamma Abdul ne ya fito daga ɗakinsa hannunsa ɗauke da brush da makilin a jiki, sanye da gajeran wando iya gwiwa  da riga mai hannun shimi, "Inna barka da hutawa", "yawwa  barka dai Yayan Rabi, an fito kenan?", amsa mata yayi, kallon Rabi ya yi a zaune ta cukule fuskar nan babu walwala kona sisin kwabo, ga bakin nan ta cuno shi kamar kahau kai kayi gaɗa, "Auta ƙalau kike kuwa?", ai kamar jira take ta fashe da kuka tana dirza ƙafa a siminti, "Subhanallah Auta mene ne wai ?" Hamma Addul ya faɗa bayan ya baro wajenda ya ke, ajiye brush ɗin ya yi ya kamo hannunta, ya zaunar da ita kan tabarma shima ya zauna, hannayenta ya kamo ya ce "farin ciki nace fa ke, ko kin manta bana son ɓacin ranki, kinfi kowa sanin haka amma kike ɓata ranki dan ki ɓatan nawa, yanzu me akai miki duk kike ɓacin ran nan?", kukan ta sassauta tana sauke ajiyar zuciya, "Hamma na gaji wallahi, ina son fita waje amma kun hana ni, sannan Inna kullum sai tamin faɗa, dan Allah Hamma na ka barni na fita yau, Allah bazanyi komai ba idan na fita,  kuma zan dawo da wuri kaji", ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka, sosai ta bashi dariya kuma ta bashi tausayi, haka wajen Inna kanta tausayin Rabi taji, dan tsakaninta ga Allah take kukan, kuma gajiyar tayi da zaman, abinka da an saba karakaina a gari.



"Karki damu lelen Hamman ta, zaki fita yau amma kimin alƙawarin banda fitina, sannan ki dawo akan lokaci, amma ba yanzu zaki fita ba ki bari sai munyi karin kumallo sannan ki fita", cewar Hamma, aikuwa nan take Rabi ta fara dariya tana jin daɗi, Inna tana zaune tana kallon su cikin so da ƙaunar Yaran nata.







Alhaji Nura da safe yayiwa Unguwar Yamadawa dirar mikiya dan tattaunawa da Tsalaha, bayan ya ƙira shi ya sanar dashi gashi a inda suke haɗuwa, can wani guri ne babu mutane sosai, ba jimawa ya isa wajen, mota Alhaji Nura ya buɗe suka shiga, Tsalaha sai washe baki yake kasancewar ya shiga mota mai raɓa, sai dube-dube yake kamar yayi ajiya a motar, da alama kuma mungun birge shi tayi, "Tsalaha motar tayi maka ne haka kake ta murmushi kana ƙare mata  kallo?", Alhaji Nura ya faɗa,



Dariya Tsalaha yayi cikin muryarsa da take fita ta hanci ya ce "wallahi harga Allah Alhaji wannan motar tayi, idan na samu kuɗaɗe irinta zan siya, kaji fa wani ƙamshi da yake tashi a cikinta, ga wani sanyi me daɗi har cikin ƙashina, Alƙur'an ta haɗu", ya faɗa yana kai hannu gaban mota ya taɓa irin tsuntsun nan da ake ado dashi a gaban mota, "kaga fa wani abu da surar tsuntsu alaji", dariya Alhaji Nura yake yana ganin lamari a wajen Tsalaha, 


"Kaga Tsalaha ka tsaya muyi abinda ya kawo ni na wuce", cewar Alhaji Nura,


gyara zama Tsalaha ya yi ya nutsu ya ce "ina sauraren ka",



"Naji daɗin amincewar ka Tsalaha, kuma hakan yasa na tawo maka da wani abu da zaka more na ƴan kwanaki kafin lamarin ya faɗa, sannan abu ɗaya zakai shine duk sanda kaga wasu Yara mata ƙanana to ka ƙira ni a waya ka sanar dani ni kuma zansa masu aikin suzo sune zasu kwasar mana su, aikinka kawai ƙiran waya ta, gashi wannan shine na katin waya", Alhaji Nura ya faɗa tare da miƙawa Tsalaha damin kuɗi Ƴan dubu-dubu dubu ɗari kenan, ai cikin azama ya amshi kuɗin nan yana rawar baki "ka.....ka ....kana nufin kace wannan du nawa ne Alhaji?", "ƙwarai naka ne wannan somin taɓi kenan, ka jira nanda wani ɗan lokaci zaka zama attajiri, sai dai dole ka kula, ta yadda ba za'a fahimci wani abu ba", cewar Alhaji Nura,




"Ai karka ji komai Alhajin Allah, babu wata matsala da zata faru, ƙiran waya kawai fa zanyi, to kaga ai wannan aikine mai sauƙi", Tsalaha ya faɗa yana mamuƙa kuɗinsa a aljihu.





Sallama sukai ya ja motarsa ya tafi, shi kuma Tsalaha rasa wace hanya zaibi yayi saboda ruɗewa da farin cikin samun kuɗi, yanke shawara ya yi ya tafi gida yana tafe yana buga murmushi, dan jinsa yake babu wanda bazai iya karawa dashi ba a masu kuɗin garin na Bauchi da kewayenta.







A ƙagare Rabi ta kammala cin karin kumallon ta, Inna ce ta ce "ga kuɗin kitso kije gidan Rakiya ta kitse miki  gakin nan, yau kwanansa biyar a tsefe na wanke miki shi, amma nayi-nayi kije kitso kinƙi, to maza kije a fara miki kitsan", kasancewar son fitar take batai musuba ta karɓa ta fice, gidan Rakiyar ta nufa dan tayi mata kitsan  ta shiga gari, sauri take ta bugawa a hanya, dake ba nisa nan take ta iso gidan Rakiya, kafin ta shiga gidan bata gani ba ya tawo ta tawo ta bangaje shi, shima ɗin bai ganta ba dan baya ji baya gani kuɗin jikinsa yake ta lissafa abinda zaiyi da shi, dan har aure saida ya lissafo "ke bakya gani ne shashasha, kin tawo bakya kallon gabanki saboda tinkiyanci", cewar Tsalaha kenan da ya taƙarƙare yana masifa, Rabi kallon sa take tana ƙare masa kallo, ganin sirantarsa da kuma yadda hannunsa yake nuna ta, ada tayi niyyar bashi haƙuri ganin yadda yake faɗa yasa ta fasa, kuma taji haushin tinkiyar da ya ƙirata da shi, kuma a ranta take ayyano abinda zatai masa ta huce, yana gama masifar ya shige cikin gidan, ita ma Rabi gidan ta shige, 




Rakiya dake zaune bakin murhu tana fama da kara, ta botse sai hurawa take da baki, shigowar Tsalaha ne ya ɗago da ita, "A'a Baban Adahama ka dawo na zaci kasuwa ka wuce?" cewar Rakiya data taso daƙyar tana nishi, cikin fara'a wadda Rakiya ta jima bata gani ba ya ce "wallahi na zo ne na shirya tukun na tafi, me kike dafa mana ne?", "ɗumame ne nake so ya ɗumama na sauke",



"To gaskiga kuci kawai ni bari na fita ko kwaki na nema nasha a kasuwa", Tsalaha ya faɗa, tare da shigewa ɗaki, Rabi da tin ɗazu ta shigo ta zauna tana jinsu, kallon sa take tana jin zafin tinkiya da yace mata, Rakiya ce ta juyo ganin Rabi a zaune ta ce "Rabi yau kuma babu sallama kika shigo gidan, haba Rabi wallahi kin tsorata ni", "ina kwana Innar Adahama?", "lafiya ƙalau ya Innar taki?", "tana nan lafiya, nazo kitso Innar Adahama dan Allah kimin manya kinji", cewar Rabi,




"Rabi manya saurin me kike ke kuwa?", Rakiya ta faɗa tana sauke ɗumame, sai da ta kashe wutar murhun sannan ta ɗakko kibiya, buɗe gashin tayi, tubarkalla kallabi tubani, Rabi akwai gashi ga santsi ga tsawo ga cika, gashin ta har kusan girarta, baƙi ne siɗik, basu jima ba suka gama kitson jelar har gadon bayanta, kuɗin kitsan ta bayar ta tashi, har tayi hanyar ƙofa ta waigo ta ce "Innar Adahama, kinsan me?, dazu dazan shigo naji Baban Adahama yana waya yana cewa karki damu a kwanakin nan zan aiko magata na, kuma kuɗi ne a aljihunsa idan kika duba zaki gani, amma dan Allah kar kice na gaya miki, dan kafin na shigo da yaga naji shine yace idan na gaya miki saiya sa almakashi ya datse min gashin kaina", ta faɗa ta yadda dole ma sai an yarda da ita, Rakiya kuwa nan take tahau kai ta zauna, zuciyarta sai tafasa take, ganin haka Rabi ta fice jin motsin Tsalaha zai fito, ita kuwa Rakiya sai nishin masifa take, 




Tsalaha daya fito da zafin sa zai fice yaji an damuƙo shi an wullar a gefe, daƙyar ya samu ya riƙe gini, "ke Rakiya kina lafiya kuwa me haka ko bakya gani ne?", 




Rakiya da ta gama fusata ta ce "Ƴar gidan ubanwa zaka auro?, kuma da wane kuɗin zakai aure kaida tsiya ta samu gurin zama a jikinka, to wallahi saika gayan wace zaka auro, kuma yau saika caje min jikinka tsaf zaka fita, dan naga kuɗi a aljihunka ɗazu da ka shigo",





"Keeeeee!!!! Rakiya ki shiga hankalinki, kin fara shan giya ne da zaki dinga min magama  haka, ni bansan zancen auren wa kike nufi ba, kuma batun kuɗi ban sansu ba, ko sisi babu a tare dani", cewar Tsalaha kenan daya fututtuke, a ransa tunani yake akan shidai yayi zancen aure amma da zuciyar sa, tunanin da yake ne ya katse jin an rarumoshi kamar kara an ƙara jefar dashi wannan karon a garken Akuyoyin da Rakiya take kiwo ta jefa shi, kafin yayi wani yunƙuri akwai wani fusataccen Ragon Rakiya mai ƙaho manya-manya, shine ya ƙara tunkuɗa Tsalaha sai gashi cikin wata ƙatuwar Tukunyar ƙarfe irin me cin kwano goma sha biyar ɗinnan, ruwa ne a ciki hakan ya sa Tsalaha shigewa ciki kamar Yaron da za'aiwa wanka, zai ɗago ya kasa sai da ƙyar ya iya fitowa yana hakki, duk ya kukkurje, gashi yayi tsamo-tsamo kamar ɗan tsakon da ya shiga ruwa aka fito dashi "Rakiya anya kina cikin hankalinki kuwa?, ni kike hankaɗawa?, wallahi tallahi babu wani aure da nake nema, shin ke wane ya gaya miki?", ya faɗa yana tafiya daƙyar dan ya bugu,





cikin fusata tace "Yarinya zatai maka ƙarya ne Tsalaha?, da bata jika kana waya da wata ba ai baza ta zo ta shirya maka ƙarya ba, kuma ta tabbatar min akwai kuɗi a cikin jikinka, shine saboda mugunta ka barmu mu muci ɗumame kai kaje ka samu abu maikyau kaci ko, to asirinki ya tonu wallahi saika bamu muma mun sayi abu mai daɗi munci, kuma batun ƙara aure babu,  Tsalaha kaida ƙara aure har abada, sai dai idan bana raye Tsalaha, ka rubuta ka ajiye idan ma akwai lissafin aure a zuciyarka to ka cire", shi mamaki yake ance Yarinya ce ta faɗa to wace Yarinyar?, tambayar da yakewa kansa kenan, "Rakiya wace Yarinya kike magana ne wai?", Yarinyar da nayiwa kitso mana, zatai maka ƙarya ne munafuki", kina nufin wadda ta zo kitso wajen ki?", "ita fa", ta bashi amsa tana harararsa, sai a lokacin ta tuna Rabi tace karta gaya masa, amma zafin kishi yasa ta faɗa,







"Gaskiya wannan Yarinyar makira ce , ƙanƙanuwa da ita tasan ta tsara irin wannan tuggun, to wallahi sai nayi maganinta", ya faɗa yana girgiza kai, "karka fara yiwa Ƴar mutane wani abin, da bata ji ba ai ba zata faɗa ba".








Ba yadda Tsalaha ya iya saida ya bawa Rakiya ɗari biyar sannan ta sakar masa mara, canza kaya yayi ya fita yana jin tsanar Rabi yana ayyana abubuwan da yakamata yayi mata.







Rabi  kuwa bayan ta haɗa borm bata zame ko ina ba sai gidan su Ƙawarta Kattume, kiciɓis sukai ta fito zata gidan su Rabin "laaaaa wallahi gidan ku zani", "yawwa to zo muje muyi yawo dan na jima banje ko ina ba", cewar Rabi.






Hanya suka yanka.







       *Kano*


Gobe ne Hamma Saheeb zai dawo sai shirye-shiryen tarbarsa ake, Khausar tafi kowa ɗigimi, an gyara masa side ɗinsa an canza komai na ciki an saka sabo, Daddy ne yake waya da alama da mutanenn Membila yake, dan naji ya canza harshe fillanci ke tashi sai farin ciki yake da alama da mutan gida yake wayar, Mammy dake kusa da shi ya miƙawa wayar nan itama naga har risinawa tayi da zasu gaisa, ita ma da filatancin take magana, da alama Daddy ya koya mata, sun jima suna waya daga bisani suka ajiye, "Daddy kaji Harɗo yana cikin damuwar rashin jin Adda Saratu kwana biyu, kuma wayar mijin ta bata shiga, ga ta Abdul ma haka", Mammy ta faɗa,







"Ina tunanin rashin network ne dan gaskiya garin akwai matsalar sa, amma zanyi ƙoƙari na same su ko dan na sanar  musu dawowar Son, kinga munsa lokaci zamu sai ga dawowar Son, kinga  maje har shi", cewar Daddy.






"Aikuwa dai Adda taga  Ɗanta", hira suke akasari akan ɗangi da ƴan uwa.







Khausar ce zaune a falo da yamma tana aikin nata na chart, jin mutum tayi ya faɗo jikinta, zata kurma ihu kenan wata ƴar budurwa ta toshe mata baki, ƙwace bakin ta tayi dan ranta ya ɓaci "haba Nawwara me haka dan Allah ko sallama baki ba kuma ki faɗo min jiki, wallahi kin ɗau alhakina", "Sorry Habibty, nayi laifi bazan kuma ba" ta faɗa tana kama kunnenta, Mammy ce ta shigo falon ganin haka yasa Nawwara miƙewa taje tayi hugging Mammy  "Oyoyo my Daughter", "Mammy yana same ki?", cewar Nawwara,




"Lafiya ƙalau nake ya Mommyn naki, kin baro ta ƙalau?", "lafiya ƙalau ta ce na gaishe ki gobe tana tafe", "masha Allahu Allah ya nuna mana.






Wato Nawwara Yarinya ce kyakykyawa ajin farko, sai dai Mahaifanta sun ɓata ta, sangartacciya ce ta bugawa a jaridu, bata ji shaye-shaye, neman maza zuwa gidan rawa duk tayi haddar su, tana da masoya da dama amma bata taɓa son wani ba sai Hamma Saheeb shine a ranta tin bata kai haka ba, sai kuma ta samu uwa mai taya ta son wanda baisan ma tana yi ba, Yaya Talatu bata da burin daya wuce a haɗa auren Nawwara da Saheeb, ƙudirinta kenan idan Saheeb ya dawo ta cusa masa Nawwata ta shiga jikinsa ta yadda soyayyarta zaisa shi  da kansa ya ce ita yake son aure, abinda bata sani ba shine Nawwara ta daɗe tana cusa kanta a wajen Saheeb sai dai ko kallonta baya yi gaisuwa ce kaɗai take haɗa shi da ita, idan yaga tana masa rawar kai ya bata wajen, tin kan ya tafi Ƙasar Ukrain take nuna masa yadda zai fahimci tana son shi amma bata gane masa, wata ran ma idan tazo gidan hutu bata yawan ganinsa, akwai sanda tayi ƙoƙarin zuwa side ɗinsa, abinda yayi mata ta tsorata da shi,  tin daga ranar bata ƙara yunƙurin zuwa ɓangarensa ba, tana mahaukacin son Hamma Saheeb, har bata iya control ɗin kanta, wataran idan soyayyarsa ta tayar mata shaye-shayenta take tayi mankas taita sambatu har tayi bacci, wannan zuwan na yau  dan shi tazo.






Troly guda tayo da alama  zaman bana ƙare bane, ɗakin Khausar suka nufa ita da Kausar, tana aje trolyn ta nufi toilet, Kausar kuwa taɓe baki tayi ta nemi gu ta zauna ta cigaba da abinda ya fiye mata.








Su Rabi suna tafe ta hango wani mai kifi karfashe "zo muje wajen mai kifin can Kattume", cewar Rabi da tuni ta nufi wajen, tana zuwa ta tsaya a wajen ta ce "sannu mai karfashe", "yawwa sannu Yarinya na nawa za'a baki?", ya faɗa bayan ya miƙe "na ɗari uku zaka bani", ta faɗa



"Ah Yarinya kice yau zakuci daɗi keda Ƴan gidan ku", mai kifi ya faɗa bayan ya ɗakko takarda, sai da ya gama lodawa a cikin takardar ta ce "mai kifi kaga maida kifin ƴan ɗari-ɗari na mutum uku ne", ta faɗa hannunta a ƙugunta, ransa ne ya ɓaci amma baice komai ba ya yi yadda tace, ya miƙa mata zata wuce ya ce "Yarinya kin manta kuɗin baki bani ba", dawowa tayi ta ce "Baba Tukur dama Baba Baraka ce ta ce nazo na karɓa idan ka koma zata baka kuɗin, baƙinta ne mu na wajen Iya mai daddawa", "to to to madallah ku gaida Iyar", cewar Baba Tukur.




Idan baku manta ba, Malam Tukur shine mijin Baraka da Biba, masu dambe a gari, kuma Rabi taji sunan Malam Tukur ne a wajen rabon faɗa, shi yasa ta gane shi, duk wannan kitumurmurar Kattume tana can nesa bata bari ta bita ba dan tasan bazai wuce wata masifar zata janyo ba.✍️✍️✍️✍️







Wannan kenan



*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*









*By Rumyn Royal star*






sharing saboda Allah👏



*09130984617*

*09062174393*




*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 23-24*

>>>>>>>>>>>>>Daga can nesa Rabi ta hango Kattume a rakuɓe tana wurga idon ganin masifar da Rabi ta kalato tayi ta kanta, hango ta da tayi ƙalau ba tare da wani ya biyo ta a guje ba taji hankalinta ya kwanta, sai leda da ta gani a hannunta, 



Rabi na isowa ta zabgawa Kattume harara "ai tinda kika ƙi rakani wajen mai kifin can ko ƙaya ba zan baki ba", ta faɗa tana ƙara galla mata harara.




Kattume ta ce "kai Rabi ina kika samu kuɗin da kika siyo Kifi?, naga dai bakida ko anini", 


"ban sani ba, kedai kici kifi kawai" cewar Rabi tare da danƙawa Kattume ɗauri guda na ɗari kenan.




Ita dai karɓa tayi tana  mamakin Rabi, a hanya suka zauna a wani dandamali sukaita cin Karfashen su hankali kwance, can tsautsayi yasa ƙaya ta tafarwa Rabi ta tsaya mata a maƙogwaro, ai ba shiri ta watsar da ragowar kifin ta fara kakari tana neman luɗifin Allah, can tayi tana tari idanuwanta sunyi bulu-bulu, ganin haka Kattume hankalinta ya tashi ta shiga jerowa Rabi sannu babu ƙaƙƙautawa, "Ruwa......R....Ruwa Kattume zan mutu!!", Rabi ta faɗa tana riƙe maƙogwaranta, gigicewa Kattume tayi ta fashe da kuka ganin halinda Karfashe ya jefa Ƴar uwarta Rabi, gidan da suke a zaune Kattume ta afka tana hawaye ita ma tuni ta yarda takardar kifin, tana shiga ta roƙe su ruwa hankali tashe, ganin halin da take ciki yasa matar gidan ɗebo mata ta bata, a guje ta fice tana hawaye matar gidan sai faɗi take "keeee kofina ina zaki, dawo min da kofina!!!", ai inaaa Kattume tayi nisa,



Tana fita ta taras da Rabi sai sannu mutane suke mata, a tunanin su badata lafiya, Kattume na zuwa ta bata ruwan ai a wahale Rabi ta karɓa ta kafa kai, cikin yardar Allah tana shan ruwan ƙayar ta faɗa, Idanuwanta da sukai ja ta kalli Kattume ta bata kofin tare da cewa "nagode Kattume Allah ya saka miki da alkhairi", dan harga Allah Kattume ta taimaketa.



Matar da aka amso Ruwa a gidanta da ta biyo kofinta taga abinda ya faru tausayin Rabin taji, Kattume na kai mata kofinta suka kama hanya da Rabi sukai gida, jikinsu duk a mace dan Rabi ta hango lahira, Kattume kuwa sai kallon Rabi take ganin duk tayi sanyi, har suka isa gida babu wanda ya kula wani, kowanne ya nufi gidan su.






Sai can dare Malam Tukur ya nufi gida bayan ya saida Karfashen sa, yau girkin Baraka ne, shiyasa yana shigowa gidan ɗakinta ya nufa, babu batun wanka haka ya zage wai zafi yake ji, sai ƙauri yake yana wari ya nemi waje ya zauna tare da jiran a kawo masa tuwan dare ya narka, 



Can na hango Baraka an nufo ɗaki da langa tuwo da miya, Biba sai yadar mata da habaici take amma ko kallonta Baraka batai ba, dan tinda sukai faɗan kasuwar nan bata kuma faɗa da Biba ba, dan tace  aljanar Biba ce take bibiyarta,




Abincin takai masa ta ajiye, zama tayi a gefansa ita ma sai buga tsami take, sai tsamin jikinsa da nata ya haɗu ya bada wani sinadari na musamman, kuma su da alama warin nasu bai dame su ba ko nace ƙamshi yake basu, tana gefan sa a zaune tana kallonsa shima ita yake kallo yana sakar mata murmushi, irin yau ki shirya ɗin nan, can bayan ya kai laumar farko ya ce "Baraka ɗazu sai naga Yaringa kin aiko, wai in bata kifi na ɗari uku idan na dawo zaki bani, nayi mamaki nace Baraka ce da fitar da kuɗi haka?", ya ƙarasa faɗa yana ƙara kafta ƙatuwar loma a bakinsa, baki Baraka ta saki ta ce "Malam bangane fa me kake nufi ba, wace Yarinya kake magana ne?", 


Malam Tukur ya ce "Yarinyar da kika aika min mana, ke kin faye mantuwa wallahi",



Baraka da mamaki ya kuma baibayeta ta ce "A'a  Malam wannan karon ba mantuwa bace, kaine dai kake sani a kokwanto, ni babu wata Yarinya dana tura maka wallahi",




Zuwa yanzu Malam Tukur ya hassala, rai ɓace ya maida lomar daya datso ya ce "ke Baraka bana son salon iskancin ki, ya zaki aikan Yarinya ki nuna yanzu kamar baki ba, to wallahi idan ma biyana ne bakyaso kiyi to billahillazi sai kin biyani kuɗi na",..





Baraka ita ma ta fusata dan cewa tayi "Malam wallahi bansan zancen da  kake ba, dan wallahi ban aika kowa ba, kuma wai ni tace na aiko ta?",



Malam Tukur da yake ganin kamar rainin wayo Baraka zatai masa ya ce "ke Baraka kalle ni wallahi kar nake kallon ki, kuma duk wani iskancin ki na sanshi, tin wuri muna shaida juna ki bani ɗari uku na wallahi, banci naninba ba yadda za'ai nanin ta cini",




"Kaga Mallam wallahi banga wanda ya isa ya sani biyan abinda ni nasan ban karɓa ba, kuma babu wanda na tura ya karɓa",





"to Yarinya dai ba zata yi ƙarya ba, dan sunanki ta ambata, tace Baba Baraka ce ta aikota, kuma har tace min jikar Iya mai daddawa ce, dan haka ki shirya biyana wallahi Baraka kin......", ihunda Baraka ta kurma ne ya hana Malam Tukur ƙarasa maganar da yayi niyya,




"Wayyoooo na shiga uku ni Baraka, wallahi ita ce!, ita ce take ta bibiya ta, taƙi tabarni, ina murna na  samu faraga ashe tana tare dani, to wallahi Aljana ce Malam, ita ce nake baka labarinta ranar da mukai faɗa da matsiyaciyar can Biba, dan Allah Biba kibarni haka!!", kuka Baraka take tana faɗar waɗan nan maganganu, Biba kuwa jin abinda Baraka tace tana mata ƙazafi harda ƙiranta matsiyaciya ne yasa ta fito ta tawo ɓangaren Barakan tana cewa "me nake ji haka kike faɗa?",






Nan faɗa ya kacame tsakanin Biba da Baraka, Malam Tukur sai ƙoƙarin rabawa yake amma sunƙi rabuwa, Baraka tana faɗin Biba turen Aljana tayi mata ita kuma tana faɗin tayi mata ƙazafi, Biba ce ta wawuro langar miya zata kwaɗawa Baraka Allah baiyi ba sai akan Malam Tukur, miyar ta kelaye masa aka ta zubo har ƙaton timbinsa, gefe yayi ya kama kansa dan da zafi, zama yayi tare da janyo zanin Baraka dake kan ƙyaure ya goge miyar, sai hakki yake, 




sunci dambe dan kansu suka rabu dan Tukur bai ƙara ƙoƙarin rabawa ba ya zauna jinyar kansa, bayan sun gama suka hau zazzagin juna da baƙaƙen maganganu, daga bisani suka haƙura kowa ta nufi ɗakinta, duk abin nan da suke Yaransu suna zaune suna kalla, dan sun saba da halin Iyayen nasu.







Rabi na isa gida bata nemi Abinci ba, bayan ta gaida Inna dake sana'arta ta shirin carbi, kwanciya tayi a kusa da Innar ba shiri bacci yayi gaba da  ita, Inna ganin idanun Rabin yayi ja sai tayi tunanin ƙila wanda yafi ƙarfinta ta tsokano, 





Hamma Abdul kuwa  da yamma ya fita neman Rabin jin ta jima bata dawo ba, gashi harta dawo shi bai dawo ba.








••••••••••••••••••Washe garin Lahadi da ƙarfe sha biyu na safe ahalin gidan Alhaji Rabi'u ne a katafaren Airport ɗin Aminu Kano sunje taro Hamma Saheeb, wato babban Ɗa aka ce magajin Uba, Mammy, Daddy, Muhammad, Kausar, Nawwara, sai murna suke da farin ciki, kowanne bakinsa har kunne, Nawwara kuwa sai iyayi take tana rawar kai,




12:30 cif-cif jirgin ya sauka, bayan yayi settling matafiya suka fara firfitowa cikin nutsuwa, saida kowa na jirgin ya gama fitowa, harsu Daddy suna tunanin anya jirginsu Hamma Saheeb ɗin ne kuwa, Daddy ne ya fara hango shi, Tsarki ya tabbata ga Ubangijin daya tsara halittar wannan bawa naka, sai dai muce Allah ya ƙarawa Annabi muhammad S.A.W daraja da fadeela fil jannati, wato nidai sai dai nace muku iya haɗuwa ya haɗu, dogo ne sosai, jikinsa irin murɗaɗɗan jikin nan ne dashi irinna Tiger wato ɗan film ɗin indian nan, fari ne shi tas kamar balarabe, fatar jikinsa luf-luf mai taushi da laushi, gashin kansa ɓaƙi mai sheƙi da santsi sai ɗaukar ido yake, sexy ayes ɗinsa masu hautsina mace gashi fari tas abin cikin idonsa irinna mage, hancinsa kuwa basaina suffanta shi ba ku kanku zaku hasaso shi, sakkowa yake da sassarfa, Troly ɗinsa mai remote ce da kanta take biyo shi, sanye yake cikin ƙananun kaya farar top ce ta kama jikinsa da sky blue trouser, sau ciki ne  a ƙafarsa fari me mugun tsada, haka Agogon dake ɗaure a kyakykyawan hannunsa, 





Hankalin duka ahalinne yayo kansa kowa bakinsa a wangale sa bo da murna, tashin farko Daddy da Mammy ya haɗe ya rumgume a tare yana sakin ajiyar zuciya, suma haka "Bayan tsawon lokaci yau gani ga Mahaifana abin ƙaunata, kune duniyata sannan kune rayuwata, nayi kewar ku sosai wanda baki bazai iya misaltawa ba", ya faɗa cikin tattausar muryarsa wadda kina ji zaki fahimci wannan muryar  bata son hayaniya,



Cikin haɗa baki Mammy da Daddy suka ce "muna godiya ga Allah daya kawo maka kai lafiya, muma munyi kewar sanyin idaniyar mu", kiss ya manna musu a goshinan su, Muhammad da Auta ne suka matso ganin ya ƙira su da idanunsa suna zuwa suma ya haɗe su a jikinsa ya rumgume yana mai jin ƙaunarsu a ransa, 






Nawwara data yi mutuwar tsaye tana kallon sura, har bata san sanda suka shiga mota ba sai da Mammy tayi mata magana sannan ta shigo suka nufi gida.







"Haƙiƙa ka haɗu Hamma Saheeb, dole saina mallaki jikin nan naka, saina yi yadda nake so dakai, kota halin ƙaƙa saika soni, bazan taɓa bari ka kurce min ba wallahi, zan iya kisan kai a kan na mallake ka ni kaɗai Saheeb, kai ne kaɗai jin daɗi na Saheeb",  duk wannan batu Nawwara ke yinsu cikin zuciyarta✍️✍️✍️✍️✍️✍️





Wannan kenan



*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*






*By Rumyn Royal*





Share pls👏



*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*


*Yau take Jumma'a Ubangiji ya sada ɗaukacin musulman duniya Alkhairin da suke  cikin wannan rana*


*Page 25-26*

>>>>>>>>>>><<<<Cikin farin ciki suka isa gida, tin daga gate akewa Hamma Saheeb barka da sauka, duk masu aikin gidan sun fifo sunyi masa barka da zuwa, da hannu yake amsawa, ciki suka shiga direct side ɗinsa ya nufa dan watsa ruwa, Muhammad ne ya ɗauki ƙatuwar Trolyn kayan Hamma Saheeb ya bishi da su, 



Tin kan ka shiga falonsa ƙamshi ne na musamman yake busowa, yana buɗe falon saida ya lumshe ido, ƙamshin sabuntar kayan furnitures ɗin da aka sa masa da ƙamshin kala-kalan roomfreshner da turaren wuta ne yake tashi, kujeru ne na gani na  faɗa a ɗakin white & golden royal masu ɗankaren uban kyau, naira tayi kuka, shi kansa saida yayi farin ciki, sannan a zuciyarsa Addu'a yakewa Mahaifansa, a falon Muhammad ya aje masa jakar ya masa sallama ya fice, bedroom Saheeb ya nufa, anan ma ya jinjinawa su Daddy, royal bed ne shima white & golden, tankamemiyar wardrop ma haka kalarta take, kan mirror ɗinsa cike da kayan shafawarsa da turaruka gasunan birjik, murmushi yayi wanda ya ƙara masa kyau, toilet ya shiga ya jima yana wanka, sannan ya fito ɗaure da towel wani a ƙugun shi wani yana goge jikinsa, gashinsa  ya fara busarwa da handryer sannan ya fara shafa mayukan sa, na gashi dana jikinsa, saida ya gyare sumar kansa mai yawa yayi mata wani style na daban, turaruka ya feshe jikinsa da su, wato body spray, side ɗin kayansa ya nufa, nanma kaya ne samfir-samfir kowanne nau'i akwai a wajen, hatta boxer, vellet, necktie, dadai sauran su, nan ya zaɓo wasu riga da wando army colour da ratsin baƙi-baƙi a jiki, ya sanya nan ya ƙara tsatso kyansa dan ba ƙaramin kyau yayi ba, tutare ya fesha ya sanya Agogo mai kyau da tsada, combos ya sanya shima army colour da zanen baƙi a jiki, yayi masifar kyau, fita yayi dan cikinsa yana son cin abincin Mammynsa.





Kausar da Nawwara ma ɗaki suka koma suka watsa ruwa suka fito domin yin Lunch, sosai Nawwara taɗau wani fitinannen wanka na wani material mai kyan gaske, sai dai ta ɗame jikinta sosai, ta yadda daƙyar mazaunanta suke juyawa a cikin kayan, Kausar sai kallonta take ganin kwalliyar da take kamar zata biki, gano cewar Hamma Saheeb ya dawo shi yasa ta gane dan shi tayi, sai jujjuya jiki take gaban madubi, turare ta afka a jikinta saida Kausar ta karɓe sannan ta haƙura, turaren yayi ƙarfi da yawa, 



"nayi kyau Kausar?"


"gaskiya kinyi kyau, kamar zaki zaɓen sarauniyar kyau", cewar Kausar



far Nawwara tayi da ido tana maijin daɗin yabonta da Kausar tayi, daga haka suka nufi falo.




Kowa ya hallara Hamma Saheeb kawai ake jira, can kuwa sai gashi ya nufo falon, kafin ya zauna Mammy ta ce "kai muke jira, maza muje muyi lunch nayi maka fouvrite ɗinka", gaba ɗaya suka miƙe suka bisu, Daddy ne ya ce "oh yau mukam mun zama abin tausayi ba'a tatamu yau",



Dariya dukka suka saka, shi kuwa murmushi yayi wanda yake tafiya da zuciyar mai kallonsa, Mammy ce ta zubawa kowa, bayan kowa  yayi bismilla suka fara harraƙa girki.




Abinci ake ci amma ita ta kasa ci, sai jura spoon take kallonsa take kamar taje taita lasar jikinsa, ta kasa control ɗin kanta, kallonsa take tana kissima abubuwa kala-kala, ziciyarta tsantar ƙaunarsa take tare da matsananciyar sha'awarsa, Muhammad ya kula da mayen kallon da takewa Hamman nasu, Kausar ma tana hankalce da ita, ta ƙasan dinning ɗin Kausar ta dungureta, nan take ta dawo hankalinta, abincin ta soma ci amma dukda haka hankalinta na kansa, amma shi ko kallon inda take baiyi, shi besan ma tana yi ba, a yadda Kausar da Muhammad suke tunani kenan, amma duk wani kallo da Nawwara takewa Hamma Saheeb yana ankare da ita, ji yayi kamar yaita jibgarta dan shi a duniya ya tsani kallo, da ba dan ta ɗauke idonta ba so yayi ya daka mata tsawa dai Kausar ta taimake ta.







Bacci sosai Rabi tasha saida Inna ta tashe ta sannan ta tashi, sallolin da ake binta tayi, sai istigfari take faɗa a zuciyarta, dan bata son sallah ta wuce ta, abinci taci, wanka Inna tasa tayi da ruwan ɗumi, saida tayi sallar isha ta koma bacci, har lokacin Baba da Hamma Saheeb basu dawo ba, sai can bayan isha sosai suka dawo suka taradda Rabi na bacci, Abinci suka ci suka ɓarke da hira,


"Dazu mukai waya da Rabi'u ashe mai sunan Harɗo ne ya dawo bayan tsawon lokaci da yayi a turai, sai neman layin mu yake bai samu ba, Harɗo ma sai faɗa yake yana ƙira baya samun mu, kuma duk sharrin network ne wallahi", cewar Baba,



Inna kuwa sai murmushi  take jin mai sunan Harɗo ya dawo, cewa tayi "wallahi kwanakin nan ina yawan mafarkin Baffa na, ina ga buƙatar ganin mu yake dan mun kwan biyu bamu je gida baa, ya kamata muje Baban Rabi",




"Zamu je nima tunanin da nake kenan, kuma zamu tsaida lokaci, dan ma Rabi'u ya ce zasu shigo a satin nan", nan take farin ciki ya baibaye Inna.




Hamma Abdul ne ya ce "lallai kice muna da manyan baƙi, Allah ya kaimu, Inna yaushe Auta ta dawo ne ?",




"Bayan la'asar ta shigo, idanuwanta duk sunyi ja, nace ƙila masu ƙarfi aka tsokano", cewar Inna




Baba ne ya ce "Allah ya shirya mana ita", da ameen suka amsa, sai can dare bayan sun gama  hirar kowanne ya tafi ya kwanta.






Bayan sun kammala cin abincin Alwala  sukai suka nufi masallaci, su Mammy ma sallar sukai, sallama yayiwa su Daddy bayan sun dawo ya nufi ɓangarensa dan yana son ya huta kafin ayi sallar la'asar.





Daddy ma kasancewar Yau Lahadi shi yasa baije ko ina ba, bedroom ɗinsa ya nufa dan hutawa.




Nawwara ma ɗakin Kausar ta shiga tabarsu a falo, tana shiga ta faɗa kan gado tana me rumgumar fillo ta rintse ido, fata take taji ta a ƙirjin Saheeb tana sarrafa shi yadda take so, wani azababben feeling ɗinsa ne yake taso mata, har mararta ce take murɗawa, abu gaba-gaba yake kamar zatai hauka, ba shiri da ɗauki wayarta ta ƙira wani saurayinta abokin cin mushen ta Shamsuddeen akan tana son su haɗu yanzu, nan take ya amsa mata dan yana sonta har aure ya ce suyi taƙi, sai dai duk sanda buƙata ta taso mata shi take ƙira, hakan daya samu sai yaji ai hakan ma normal ne, tashi tayi ta sanya mayafi, ta ɗau makullin motar ta ta fito falo, Mammy ce da Kausar zaune "Mammy zani gidan wata ƙawata na dawo", 




Mammy da bata son yawo ta ce "Nawwara bana son yawo fa, la'asar ta ƙarato ya kamata ace kina gida a zaune",




Jin za'a hana ta fita ta marairaice ta ce "Mammy gobe ina da lucture kuma akwai assignment da aka bamu to ni banje ranar ba, ga shi gobe za'a karɓa, shine zani na amso na wajenta, bazan jima ba zan dawo", Mammy ba yadda zatai haka fa barta ta tafi.






Lokaci na tafiya yini na shuɗewa, yau kwanan Hamma Saheeb bakwai da dawowa, sai shirin zuwa Bauchi su Daddy suke, Nawwara kuwa ta gaza gane wane irin mutum ne Saheeb da ko kallon ta baya yi, idan tana waje har ta gama zamanta ba zai ɗaga kai ya kalle ta ba, gashi kullum idan ta ganshi sai sha'awarsa ta motsa mata, Yaya Talatu tazo washe garin ranar da ya dawo, Nawwara kullum saita ƙira Mom ɗinta ta faɗa mata halin da take ciko na halin ko in kula da Saheeb yake nuna mata, yau uwar ta nemi Nawwara ta koma gida su canza sabon shiri.





Ana i gobe su Daddy zasu je Bauchi Nawwara ta koma gidan su.






A waɗannan kwanaki satar Yara mata ƙanana ta yawaida a wannan Ƙauye, Iyaye hankalinsu a tashe yake, kullum sai an saci Yara sama da biyu, an rasa gane kan wannan lamari, gashi kullum Iyayen Yara jira suke suji an ƙira wayoyinsu ko masu garkuwa ne shuru kake ji, yanzu uwaye su suke kai Yaransu Makaranta su koma idan an taso su dawo gida, Hukuma kullum da wannan case ɗin take tashi ta kwana da shi, suna ta bincike, sun kuma cewa Iyayen Yara da an ƙira su to suje Police station su faɗa, amma har yau shiru kake ji.





Hamma Abdul ya samu koyarwa a Makarantar su Rabi, cikin ikon Allah aka amshe shi hannu biyu, dan suna buƙatar ƙwararren malami, kuma alhamdulillah Yara suna gane duk wani karatu na Mallam Hamma Abdul, Rabi ta nutsu a Makaranta baka jin haya-hayarta da Yara kamar da, dan Hamma Abdul ya yanka mata warning na musamman, shi yasa ta saduda, amma ana tashi zaka fara jin tashin kukan sa'anninta suna Allah ya isa basu yafe ba.





Inna kuwa jin gobe Ɗan uwanta da Iyalansa zasu zo, yasa ta dage danta faranta musu, gyara wani ɓangare akai inda basa amfani da shi, aka gyara shi tsaf, ɗakin Hamma Abdul ma ya ƙara gyara shi kasancewar yasan Hamma Saheeb nan zai saukaa, dai-dai ƙyale-ƙyalensu na ƙauye sunyi kuma abin zai birge ka,



Babu abinda basu tanada ba na tarbar mutanen Kano, duk wata cimar su su Baba da Hamma Abdul sun tanada.




Sai muce Allah ya kawo su lafiya.






Washe gari da wuri su Daddy suka shirya, zaman jiran Hamma Saheeb suke dan shi kam sai an jira shi, shirinsa kamar na mace, suna  zaune ya shigo falon sai azabar ƙamshi yake, ɗanyen boyel cutton mai shara-shara irin me tsananin tsadar nan ya saka, ash colour yayi kyau over har baka iya ɗauke ido daga gare shi, manyan kayan sun masa kyau, baƙin takalmin fata yasa da baƙar dara irin ta yanzu mai shegen tsada, baƙin glass ne a idonsa, yana ɗaura tsadadden Agogonsa ya iso falon yana faɗin "ina mai bada haƙuri Daddy, Mummy kuyi haƙuri", Daddy ne ya galla masa harara ya ce "mata dai aka fi sani da nauyi, amma kai kullum sai an jira ka", marairaice fuska Hamma Saheeb yayi tare da kama kunne, Daddy ne ya kamo kunnen yana faɗin "ai baka kama da ƙarfi ba bari na kama maka", ƴar ƙara yasa yana riƙe kunnen, dariya suka sa sannan suka fita dama an kai musu kayansu but, driver ne ya ja su bayan sunyi addu'ar hawa abin hawa *"(Bismillahi wal hamdulillahi, subhanallazi sakkara lana haza wa makunna lahu mukrani, wa'inna ila rabbana lamunƙalibun, Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, Allahu akbar, Allahu akbar, Allahu akbar, subhanakallahumma inna zalamtu nafsi, fagfirli fa'innahu layagfiruzzunuba illa anta).*



Bayan ka zauna a motar saika ce *"(Astadi'ukumullahal lazi la tadi'u wada'i'uhu)".*




Allah zai tsare ku har kuje ku dawo.





wannan kenan



Ayi haƙuri da wannan ba yawa





*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*




*By Rumyn Royal*




A tayani sharing dan Allah👏


*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 27-28*

>>>>>>>>>>><<<Kasancewar daga Kano zuwa Bauchi babu wata tazara mai matuƙar yawa, awa biyu da rabi sukai suna tafiya suka iso garin Bauchi, har ƙofar gida driver ya tsaida motar kasancewar suna zuwa da shi, hamdala sukai ga Allah daya kawo su lafiya, firfitowa sukai amma banda Hamma Saheeb yana ciki yana latsa waya "Son munfa ƙaraso naga baka fito ba", cewar Mammy "Mammy zan fito ne ina ɗan wani abu ne", shigewa tayi ta barshi, Muhammad da Kausar kuwa da Daddy tuni sun isa cikin gidan.




Inna dake zaune ita kaɗai  a tsakar gida tana gyara rama zata shanya ta, sallama tajiyo kafin ta amsa Kausar da Muhammad sun shigo, "Wa'allaiku salam ƴan albarkana, barkan ku da zuwa lale da mutanen Kano", ta faɗa bayan ta miƙe cikin farin ciki, Daddy ne ya shigo shima bakinnan nasa kamar ya yage sa bo da farin cikin ganin Yayar tasa, suma su Muhammad sai fara'a suke, ƙatuwar Tabarma ta shimfiɗa musu, lokacin Mammy ta shigo, cikin farin ciki ta nufo Inna ta rumgume, "barka da zuwa Nafisa, sannun ku Rabi'u, lale marhabin", dan farin ciki ta rasa inda zata tsoma rayuwarta, lemukan da ruwan da Hamma Abdul ya siyo da Donut manya-manya ta ɗebo su masu sanyi akan ƙaton farantin silver ta dire su a gaban su,  ta kawo musu, sai sannu take musu, Daddy sai binta yake da kallo, yana ƙaunar Yayar tasa, duk cikin Ƴan uwansa yafi ƙaunarta dajinta a ransa,





Bayan ta kawo musu ta zo ta zauna kusa da Mammy, cikin jin daɗi da ƙaunar Yayar Mahaifin nasu Muhammad da Kausar suka gaida Inna, amsawa tayi cikin jin daɗi,  Daddy ya ce "Adda Saratu fatan na same ku lafiya?", ta amsa da cewa "lafiya ƙalau Rabi'u, ya rayuwar binni, ya akaji da kasuwa ina fatan komai lafiya?", Daddy ya ce "lafiya ƙalau wallahi sai hamdala",


Bayan gama gaisawa cikin farin ciki, Mammy ta ce "nikam ina Rabi'atu da Abdul?,



Inna ta bata amsa da cewa "Rabi tana Makarantar boko, shima Abdul yana Makaranta yanzu haka nasan suna hanyar dawowa, dan acan Makarantar su Rabin ya samu aiki koyarwa", 



"Masha Allah, Allah maido su lafiya", cewar Daddy,



"Ina Yaro na ne wai, na ganku ku kaɗai na zaci tare zaku zo?" cewar Inna, tana nufin Hamma Saheeb



Daddy ne ya kalli Mammy ya ce "kece ƙarshen shigowa ina Son ya tsaya ne ?"



Mammy kuwa Muhammad ta kalla ta ce "Babana jeka mota kace masa ya zo", 



"Haba har naji daɗi, harda zance ko gajiyar ce bata sake shi ba har yanzu?", Inna ta faɗa.



Daddy ya ce "Yazo wallahi bansan meya tsaida shi a waje ba".





Muhammad yana fita ya taradda Hamma da Baba suna gaisawa, cikin jin daɗi Baba yake faɗin "masha Allah ashe kun ƙaraso?, naje ta'aziyya ne nan baya", "Ayya Allah ya jiƙan musulmai", cewar Hamma Saheeb, Muhammad daya fito dan ƙiran Hamma ganin Baba yasa shi tsugunawa har ƙasa ya gaishe shi, cikin jin daɗi ya amsa, daga nan ciki suka nufa,




Suna shiga Daddy ya miƙe suka gaisa da Baba cikin so da ƙaunar juna, Hamma Saheeb kuwa kusa da Inna ya zauna ya gaisar da ita fuskarsa a sake, harda riƙo hannunta da alama akwai shaƙuwa sosai tsakanin su, gaba ɗayan su suka ci Donut ɗin da aka kawo musu amma banda Hamma Saheeb dan ya tabbata ba Gwoggonsa ce tayi wannan abin ba, bayan sunyi sallar Azahar ne ta zubo musu haɗaɗɗiyar shinkafa da miya taji kaji, sai ƙamshi take, ga salat da kayan vegetable nan akai, Baba da Daddy aka kai musu falon Baba, Hamma Saheeb nasa daban, Muhammad nasa daban Kausar ma haka, Inna da Mammy tare suka ci, sosai suka ji daɗin abincin, dan babu wanda baiyi santi ba, Hamma Saheeb sosai ya zage yaci Abincin dan yana son girkin Inna, daga girkin  Mammy sai na Inna yake iya ci, acan Ƙasar daya baro kuwa da kansa yake dafa abinda yake so, baya taɓa iya sayen abinci a wani wajen sa bo da ƙyanƙyaminsa.





Hamma Abdul kuwa sai biyu suka tashi, Rabi ya taso a gaba suka tawo gida, sai mitar ita fa fitsari take ji take masa, ga cikinta da yake murɗawa dan yau Ɗanmalele wata ƙawarsu tayo musu shi suka ci, ga uban yaji da suka cika a ciki, kartawa kawai cikinta yake, data fara gudu Hamma Abdul zai dakatar da ita ya ce "gudun da zaki shi zaisa abinda kike riƙewa fitowa, ki nutsu mun kusa ƙarasawa", 


Ita dai batada fata sai na isa gida lafiya ba tare da ta janyo zugar ƙudaje ba,  tana ganin sun iso gidan gata ga shi, ta yanka a guje tare da zubar da Jakarta tana faɗin "Hammana ka ɗaukemin ka tawon dashi yamin nauyi", kai ya girgiza tare da ɗaukar jakar, Motar da ya gani a waje hakan ya bashi tabbacin mutanen kano sun ƙaraso, da farin ciki ya nufi gidan.





Aguje ta shiga gidan ko sallama babu, fitowar da yayi daga ɗakin Hamma Abdul dan fita waje hankalinsa nakan wayarsa ai kuwa bai san hawa ba baisan sauka ba yaji an bangaje shi an wuce ana faɗin "kashi-kashi koma-koma zan yanka maka ragon layya",  tare da ɗaukar buta tayi cikin banɗaki aguje, shi kuwa gogan ransa idan yayi dubu ya baci, dan bama tasan ɓarnar da tayi masa ba, wayarsa da take yashe a ƙasa ya tsuguna ya ɗauka yana tsaki, dan harta tsage, gata mai tsada gaske, tambayar kansa yake wace wannan Yarinyar?, "ina ga dai Yaran maƙota ne, dan wannan dai ba anan take ba", yana cikin zancen zucinsa yaji an riƙo shi, yana juyawa yaga Hamma Abdul, fara'a ya saki "wellcome bro, tin ɗazu nake jiran dawowar ka", cewar Saheeb, rumgumeshi Abdul yayi yana faɗin "wallahi bro yau munyi jinkirin dawowa, ina fatan kunzo lafiya?", 



amsa masa yayi suka ƙarasa ciki, gaggaisawa sukai, sannan ya koma ɗakinsa Saheeb kuwa fita yayi waje ya ce idan ya kammala komai yana jiransa a waje.






Rabi kuwa bata san ta bige wani ba balle yasa ran ta bashi haƙuri, bayan ta kammala abinda ya kaita banɗakin tayi wankanta ta maida kayan makarantar, ta fito, kasancewar sunyi sallah a makaranta yasa tayi cikin madafa, ganin bata ga langar da ake zuba mata abincinta ba yasa ta turo ɗan ƙaramin bakinta "Inna ina abincina!!!!?" ta ƙwalla da ƙarfi.



Suna zaune a rumfar jikin ɗakin Inna ana hira, Mammy, Inna, Kausar, da Muhammad, suka tsinkayi muryar Rabi, Inna ce ta ce "iko sai Allah, ga rigimanmiya can ta dawo bari naje", ta faɗa tana yunƙurawa, Mammy ce ta ce "ai da gaskiyarta ai yunwa ta kwaso a makaranta", Muhammad kuwa murmushi yayi dan yana son dramar Rabi, Kausar kuwa gimtse fuska tayi dan bata ma so Rabin tazo taga dariyarta, Inna data miƙe ta ce "ina fa ta kwaso yunwa, kawai iya shege ne irinna Rabi, da bazata bi abu a hankula ba",




Rabi da taji shuru ta ƙara ɗaga murya ta ƙwantsamawa Inna ƙira, "ke bana son iskancin banza dana wofi, bakisan munyi baƙi ba zaki fara nuna hali, to ki shiga taitayinki wallahi, zane ki zansa Hammanki yayi", ta faɗa tana zuba mata abincin, shuru tayi tana nazarin wasu baƙi akayi, dan shaf ta manta da batun Kawunta na birni zasu zo, kallon Inna tayi ta ce "Inna su waye suka zo?"



Inna ta ce "au har kin manta da Kawunki zasu zo?" ai bata ƙarasa ji ba ta fita a guje ta nufi tsaƙar gidan su, dan dama da tazara tsakanin ɗakin girkinsu da inda zai sada ka da tsakar gida, tana isa tayi turus tana washe baki, su kuwa ɗagowa sukai suna kallon yadda tayi, Muhammad ne ya sheƙe da dariya ganin yadda gaba ɗaya ilahirin haƙoranta sun fito, Mammy kuwa  cewa tayi "Yarinyar kirki ƙaraso mana mu gaisa kin tsaya", ƙarasawa tayi cikin shirmen ta ta ce "Maman birni dama dake za'a zo?", 


"Eh mana gashi kin ganni, kuma dake nazo tafiya, ai zaki bini ko?" Mammy ta tambaya,



"Eh zan biku amma saida Inna, kuma ba'ayi mana hutu ba, sai ku jira ni idan anyi hutu saimu tafi", cewar Rabi 




"Sai mu jira ki sai  anyi muku hutu zamu tafi ko, saboda haka muka zoyi duniya", Kausar ta faɗa tana hararar Rabi



Rabi kuwa cikin farin ciki tace "Eh wallahi Adda Kausar, ku tsayani dan Allah", dan ita bata san gatse ba, harara kuwa bata sanma tana yi ba.





Muhammad da yake ta dariya ƙasa-ƙasa dan harga Allah abin ya bashi dariya, Mammy hararar Kausar tayi na ki shiga hankalinki, sannan ta kalli Rabi ta ce "Adabiyya idan akai hutun zansa azo a ɗauke ku har Innar sai kuzo", cikin jin daɗi ta miƙe a sannan ne ta kalli Hamma Muhammad ta ce "Hamma Madu ina wuni?", amsawa yayi da sakin fuska sannan ya ce "wannan Madun ki soke shi, Muhammad nake", amsawa tayi da "to Hamma, Adda Kausar bani wayarki nayi game ɗinnan da kika taɓa kunna min kinji", ta faɗa tana zuwa kusada ita, "au ni zan kunna miki game ɗin, wanda kika gaisar shi zai baki kiyi", cewar Kausar da ba a gaisheta ba,



Baki Rabi ya turo ta ce "kai Adda shifa bashida irinta wallahi, a wayarki take fa",




Kausar ta ce "waya gaya miki, a wayarsa nima na tura ai", 



"Dan Allah ki kunna mata Kausar, bana son jan rai", cewar Mammy.




Bayadda Kausar ta iya haka ta kunnawa Rabi game ɗin  ta bata, tana ta harararta, a haka Inna ta zo ta taradda su, faɗa ta hau yiwa  Rabi na wayar wace  a hannun ta, karta lallata musu, Mammy ce taita kare Rabi, Rabi dai abincin da bata ci ba kenan, ta hau game wadda sai cinyeta ake tana ɓata rai, tana faɗin "wannan karon ni zan cinye ku wallahi", tana ta magana da ƴan Aljanun.





Su Hamma Abdul bayan yaci Abinci suka fice suka shiga gari, harda Muhammad.





Nawwara kuwa bayan ta koma da kuka ta shiga gidan, Uwar na zaune a falo taga shigowar Ƴarta a haka, tashi tayi ta taro ta tana tambayar abinda ya sameta "Mom wallahi ni kawai kiyi magana ayi mana aure da Saheeb, na gaji wallahi baya sona ko kaɗan, ko gaishe shi nayi baya son amsawa, wallahi idan ban aure shi ba Mom zan iya mutuwa, ko kuma ku neme ni ku rasa", faɗa take tana kuka kamar ranta zai fice, Mom kuwa faɗi take "Sweethaert ki kwantar da hankalinki kamar kunyi aure da Yayan ki kun gama, zanyi magana da Nafisan, ki dena ɓata hawayenki a banza, Saheeb mijinki ne", jin haka yasa kukan nata ya tsaya, ta saki murmushi, dan harga Allah ta samu sassauci jin abinda Mom ta faɗa mata, "Mom duk yadda zaki yi kiyi Saheeb ya zamo nawa, dan idan haka bata faru ba, zaku rasa ni, ko kuma na hana shi auren kowa, Mom ina son Saheeb son da ban taɓaiwa kowa shi ba, ki taimakawa kanku ku haɗa aurena da Yaya Saheeb", ta faɗa tare da tashi ta nufi ɗakinta, Mom kuwa kallo tabi ɗiyar tata da shi, tana kissima abubuwa a ranta.






Tsalaha ya zama hamshaƙin mai kuɗi a lokaci guda, mutane sai mamaki suke, kasancewar yasa an rufe bakin mutane yasa ba wanda ya taɓa tararsa da zancen, yasa an bige gidansa anyi na bulo an gyara shi kamar bana ƙauye ba, Rakiya sai fantamawa take, dan yanzu bata kitson ma kwata-kwata, ɗansu ma yanzu makarantar cikin birni yake zuwa, Iyayensa da suka tambaye shi sai ya ce ai kasuwar ce ta buɗe yake samun alkhairai, gyaran takalma yake, amma kasancewar ya rufe bakin kowa wasu kuma kwaɗayi ya rufe musu ido ko binciken basa yi, Yara kuwa sai ɓata suke, wasu Iyayen sanadin haka sun kamu da ciwan hawan jini, wasu ciwan zuƙata, rayuwar garin dai babu daɗi, kowa kaffa-kaffa yake da ɗansa, Tsalaha duk inda yaga Yara mata saiya sanar da Alhaji Nura.






A kwana ɗaya Hamma Saheeb ya fahimci Rabi ƴar ƙaramar yarinyar daya bari kafin ya tafi turai ita ce wannan Yarinya data bangaje shi ta fasa masa waya, abin mamaki, tinda suka haɗu zata islamiyya ko kallonsa batayi ba, yana tunanin zata gaida shi amma haka ta ƙetare shi tayi nata guri, bayan ta dawo ma yana ƙofar shiga gidan a tsaye yana danna waya, yaga tawowarta saiya share bai matsa ba, ita ma da tazo bata ce zata wuce ba, ta tsaya tana jiran ya matsa, ransa ya matuƙar ɓaci, yasan dai gidan Gwoggonsa akwai tarbiyya, amma me yasa wannan tazo a haka, data gaji waje ta samu ta zauna, abin ya mugun bashi mamaki, ransa  sai suya yake, ji yayi ya tsane ta matuƙar tsana, baya son rashin tarbiyya, tambayar kansa yake kodai Mahaukaciya ce?, saida ya gaji dan kansa ya shige ciki sannan ita ma ta shiga gidan, a ranta tana faɗin "ni bana yiwa  arne magana wallahi, ance ƙasar turawa yaje ya zauna, kuma wai Kawu ne da Maman birni suka haife shi, cafɗi Allah bazan taɓa yiwa arne magana ba Allah ya sani a wutar jahannama can-can ƙasa kusa da wannan arnen", can kuma bayan ta kammala wannan nazari sai ta saka kuka, wai na tausayin su Kawu da suka haifi arne, a soron ta gama ta share hawayenta sannan ta shiga gidan.





Tin daga ranar ko kallonta baya yi, ita ma idan yana  waje  bata zama, dan gani take Iyayenta ma suna cikin fushin Allah na zama da arne haka zatayi kuka ta share tana nemawa Iyayenta sassauci wajen mahaliccin mu.






Su Inna sun sha tsarabar Ƙasar waje da Hamma Saheeb ya kawo musu, kaya ne masu kyau, takalma, Agogo, Sarƙa, turaruka da sauransu, su Daddy kuma kayan Abinci suka jido suka tawo musu da shi babu abinda babu, Mammy kuwa lesuka, da Atamfofi ta kawo wa Inna, Dogwayen riguna kala biyar da takalma, kayan kwalliya, na Rabi, Baba ma yasha manyan yaduka masu tsada da shaddoji, Abdul ma kayan Botiq aka kawo masa Agogo mai tsada Hamma Saheeb ya siya masa, Kausar ma ba'a barta a baya ba, ta siyowa abokiyar faɗan ta mayukan shafawa da na gashi, da turaruka masu ƙamshi, Muhammad kuwa dama waya ya sayowa Inna da Baba harda Hamma Abdul, sunyi farin ciki sosai, Inna har kuka tayi dan murna.





Washe garin da zasu tafi, sunata shiri anata neman Rabi ta fita, can sai ganin Rabi sukai a guje still yauma Hamma Saheeb ta bige ta shigo a guje, Yaron da bazai gaza tsawonta ba ne ya biyo ta yana kuka, ita kuwa bayan Mammy taje ta laɓe, Inna ce ta ce "Rabi yau kuma me kika janyo mana?", yaron ne yasa kuka ya ce "kawai ina tafiya ta ina tallan Ɗinya ta akan faranti ta ƙira ni wai zata siya, na sauke ta tambayeni nawa nace mata goma-goma ce shine tace na siyar mata biyu biyar nace a'a muma bamu siyota a haka ba, shine ta kwaɗan mari ta hankaɗa ni na zubar da Ɗinyar a kwata", Ran Inna  ya ɓaci matuƙa, Hamma Saheeb dake tsaye yana jin duk abinda Yaron ya faɗa ya cewa Yaron "zo nan"  zuwa yayi "kema zo nan" cewar Hamma Saheeb da dama neman hanyar hukunta Rabi yake nema, 



"Son karka taɓa min Yarinya a bashi haƙuri a biya shi kuɗin abinsa ya tafi", Mammy ta faɗa



"Mammy babu abinda zanyi mata" sanin da Mammy tayi baya magana biyu yasa tacewa Rabi taje babu abinda zaiyi mata, tana zuwa ya kalli Yaron ya ce "rama marinka da tayi, ganin Yaron yana kallon idon Rabin kasancewar yasan haɗuwarsa da ita babu daɗi ya ce "a'a na yafe marin nidai kawai a bani kuɗin Ɗinyar", 


"Ba za a biyaka ba indai baka rama ba" jin haka Yaro ya taƙarƙare ya wanke fuskar Rabi da mari, Hamma Saheeb ya ƙara cewa ya ƙara mata, saida yayi mata har mari uku masu zafi sannan ya ciro dubu biyu sababbi ya bawa Yaron ya sallame shi Yaro ya fita yana ta murna, Rabi kuwa ko ɗigon hawaye babu sai idanuwanta da sukai jajajir dasu, kuma duk abinda akai bata kalli inda Hamma Saheeb yake ba, mamakin Yarinyar ya shiga yi, "anya ba aljannu bane da ita?", ya tambayi kansa, ficewa Yayi kafin  su Daddy, Baba, Muhammad da Hamma Abdul su dawo su wuce, dan sunje gidan mai gari kai gaisuwa, kasancewar mai garin yasan Daddy sosai,







Su Inna kuwa bayan sunga Saheeb zaiyi sasanci ciki suka shiga basu san wainar da aka toya kenan ba, Rabi kuwa bata gayawa kowa ba ta shige ƙuryar ɗakin Baba tana ajiyar zuciya, har su Daddy suka zo zasu tafi ana ta nemanta ba a ganta ba haka suka tafi, bayan sun tsaida ranar zuwa Taraba garin su na haihuwa.





Rabi kuwa tinda ta kwanta take ajiyar zuciya gashi kukan yaƙi zuwa, ji tayi ta ƙara tsanar arne, kuma saita rama marinda akayi mata, a haka bacci ya ɗauketa tana ta ajiyar zuciya.




RABI DANJA shin akanwa zaki rama marin?, Yaron ko kuma Hamma Saheeb, amsar tana cikin zuciyar RABI DANJA, sai kh biyo ni danjin wa zata mara?.✍️





Wannan kenan




*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*





.

*By Rumyn Royal*




SHARING FISABILILLAH👏




*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 29-30*

>>>>>>>>>>>>><<Kwanci tashi inji hausawa suka ce asarar mai rai, yau kwanakin su Daddy uku da dawowa daga Bauchi, kuma yau ne Yaya Talatu wato Mom ɗin Nawwara taiwa gidan Alhaji Rabi'u dirar mikiya, 



Zaune suke a falo Mammy da Kausar sai Mom, nisawa tayi ta kalli Mammy ta ce "Nafisa magana nazo muyi dake mai muhimmanci, fatana zaki karɓi abin da hannu biyu, dan batu ne na alkhairi",



Mammy data gyara zama ta ce "Masha Allah ina jinki Yaya Talatu, dama mu fatan mu shine muji alkhairi",



cikin karsashi Yaya Talatu ta gyara zama sosai fuskarta fal fara'a ta ce "batu ne akan Yaran mu, wato Saheeb da Nawwara, banida buri sai ganin mun ƙara ƙulla zumunci tsakanin mu, wato nufina mu haɗa su aure, kinga tuwo na maina kuma namana", 



Mammy da taji batun daga sama ta ce "au kajimin ja'iran Yara dama sun dai-daita a tsakaninsu amma bawanda ya sanar dani, ko kunya ta suke ji?", 



"A'a shi baisan da wannan batun ba, ƙwara ma ita Nawwara ta sani dan ta jima tana son Yayan nata", cewar Yaya Talatu kenan,



"ikon Allah, banƙi ta taki ba Yaya Talatu, amma ya kamata kowa a bashi haƙƙinsa, kuma a tambayi kowanne ra'ayinsa, kar muje mu shiga haƙƙin Yara", Mammy ta faɗa,



"kinji ki Nafisa, to wane abu za'a tsaya ana lelegaji dashi bayan gaba ɗayan mu mun isa da Yaran mu", 



Mammy ta ce "ina cewa kikai Nawwara tana son shi?, to shi ɗin ya sani ko bai sani ba?", 



"bai sani ba shine nake so a matsayinki na uwa ki zauna dashi ki fahimtar dashi zumuncin da muke so mu ƙara ƙullawa",



"haka ne zan same shi, idan yaso duk yadda ake ciki zan sanar dake", cewar Mammy 



"yawwa Nafisa dan Allah karki ja lokaci, kuma ki fahimtar da shi ta yadda zai amince nan take, kar kice zai juya ki, a matsayinki na uwa kece zaki juya shi",



Mammy mamakin jin bayanan Yayar tata kawai take, amsa mata tayi kawai dan a zauna lafiya amma ta tabbata Saheeb bazai amince ba, kasancewar halin Yarinyar kowa ya sani a family.






Rabi ta gama tsanar Hamma Saheeb a  rayuwarta, dan ta rantse akan saita rama abinda yasa akayi mata, kullum da marin da yasa akayi mata take kwana take tashi, babu wanda ta faɗawa a gidan ta barwa kanta sanin abinda  ya faru.



Saura kwana uku su tafi Taraba, sai shiri suke, Inna da kanta ta shiga Kasuwa ta siyo kayan tsaraba, farin ciki take zata ziyarci Rugarsu taga Iyayenta da sauran Ƴan uwanta.




Kattume ma basa nan sunyi tafiya Katsina dangin su, wani iri Rabi take ji rashin Kattume.



Fitowa daga gida tayi kasancewar Hamma Abdul ya fita, kara ta samu a hanya tana tafe tana waƙe-waƙenta, wani saurayi taci karo dashi ya tare mata hanya ya riƙe ƙugu yana murmushi "kai Usama dalla matsa na wuce", Rabi ta faɗa cikin tsiwa,



"ni bazan  matsa ba, sa bo da naga  abar sona, kewai bakisan sonki nake ba, shi yasa nake yawan kula ki", cewar Usama


Ran Rabi idan yayi dubu to ya ɓaci, dan ita a rayuwarta kalmar so tana nufin iskanci, kuka ne ya kufce mata ta fara takaici ya gama riskarta, karan hannunta tayar ta faɗi a wajen tana dirza ƙafa tana ƙara ɗaga murya, kuka take sosai bilhaƙƙi, shi kuwa Usama tsoro yaji, ya fara tambayarta meya same ta, wasu magidanta ne suka zo wajen suna tambayar "lafiya maiya faru?"



Kuka take taƙi yin shuru, shi kuma Usama baisan mezaice musu ba dan shima baisan dalilin kukanba, daƙyar wani abokin Baba daya ƙaraso ya taradda abinda yake faruwa ya ce "Rabi share hawayenki ki gaya min meya faru?" nuna Usama tayi tana shashsheƙa tana ajiyar zuciya, kowa kallon Usama yake, nan take gumi ya fara tsatstsafowa Usama idonsa wiƙi-wiƙi ya nuna kansa ya ce "ni kuma me nayi miki?", 


Abokin Baba ne ya ce "yimin bayani mana Rabi", "shine yace wai yana sona, ban taɓa shiga harkarsa ba, amma bansan hawa ba bansan sauka ba yace wai yana sona", ai tana faɗa ta ƙara rushewa da kuka, Usama kuwa abin dariya ya bashi, haka sauran mutanenn wajen, Abokin Baba ne ya ce "kiyi haƙuri bai kyauta ba zanyi masa faɗa, bazai kuma ba kinji", amsawa tayi ta tashi ta nufi gida, dan wannan lamarin ya wuce ace bata gayawa su Hamma Abdul ba dan suje su kaishi wajan ƴan sanda, har sauri take taje gida, aikuwa tana shiga ta sanya kuka, Inna ce ta fito daga ɗakin Baba "to to me kuma ya faru yanzu Rabi ?"



"Ba Usama bane yace yana sona ba, kuma ni yasan ba ƴar iska bace ba, Inna dan Allah ku kaishi wajen Ƴan sanda kinji",



ikon Allah Inna take kallo ganin da gaske Rabin kukan take har da saka gefan hijabinta tana share hawayen, Inna ce ta ce "shi Usaman ne ya ce yana sonki?", cikin sauri ta ce "Eh Inna"



"to kiyi haƙuri zan ɗau mataki akai, amma yanzu ki share hawayenki, karki gayawa kowa wannan gagarumar maganar, kinji", cewar Inna danta ƙyale zancen, dan idan ba haka tayi mata ba, to ba zata bar zancen ba, amsa mata tayi, juyawa tayi da nufin komawa gantalin nata Inna ta dakatar da ita, ta ce ta samu waje ta zauna, tana kumbura baki ta  zauna dan ba haka taso ba.






~~~~~~~Yau ne tafiyarsu Inna dasu Daddy Taraba, a yadda suka tsara tinda su Inna ne a hanya, zasu biyo su ɗauke su, to hakan ce ta faru, dama su Inna sun gama kimtsawa, Hamma Abdul, Baba har Rabi sun kammala shirinsu, jiran su Daddy suke, wayar Hamma Abdul ce tayi ƙara, yana dubawa yaga saƙon Muhammad cewa gasu sun iso inda zasu haɗu, aikuwa ba ɓata lokaci ya sanarwa su Inna suka kwashi kayan tsarabarsu, suka fita, aikuwa suna fita suka samu wani mai taxy ya kawo wasu mutane, shi ya ɗauke su ya fitar dasu inda su Daddy suke, bayan sun sakko, drivern Daddy ne ya saka musu kayansu a but, su kuma suka shiga ƙatuwar motar dasu Daddy suka zo da ita, irin motar nan ce jeap maicin mutane da yawa, hakan yasa koda suka shiga babu wanda ya matsi wani, 



Cikin farin ciki suka gaisa da juna, Hamma Saheeb yana daga bayan motar shi da Muhammad da Abdul, Kausar tana gefan Mammy, Inna tana kusa da Kausar, sai Rabi a gaba kusa da Baba da Daddy, Addu'a sukai kana mota ta miƙa zuwa Taraba Jalingo, karatun kur'ani aka saka, shi yasa kaji motar tsit kowa saurarar ƙira'ar yake, 




Tafiya ta miƙa sosai dan driver gudu yake sosai, Rabi sai kalle-kalle take data ga abu zata kalli Daddy ta tambaye shi, shi kuma ya biye mata sai amsa yake bata, surutunta ne kawai yake tashi a motar, Hamma Saheeb kuwa jin surutunta yake kamar a ƙwaƙwalwasa, ta takura masa, sai ƙananun tsaki yake, can da tafiya tayi nisa Rabi ta kalli Daddy ta ce "Daddy fitsari nake ji" ta faɗa bayan ta kwaɓe fuska, Daddy cikin riritawa ya ce "tom my daughter, driver dakata anan Rabi zata kama ruwa", bayan an tsaya Daddy ya kalli Kausar ya ce "Kausa rakata can wurun ta kama ruwa, babu gidan wanka a kusa", ran Kausar a ɓace taje ta raka ta can nesa tayi fitsarin, robar ruwan faro ta bata kallon robar Rabi tayi ta ce "meye wannan Adda Kausar?", "ban saniba malama amshi kiyi tsarki mu tafi, kina ɓatawa mutane lokaci", Rabi kuwa ta dage akan ba zata taɓa tsarki da wannan ruwa ba a samo mata ruwan rijiya, Kausar ranta ya ɓaci sosai, kasancewar da ƴar tazara, yasa ta ƙira layin Mammy "hello Mammy kinga sai fama nake da ita akan tayi tsarki mu tafi wai ita ba zatayi amfani da ruwan faro ba saina rijiya, wallahi Mammy zan tawo na barta", Mammy jin haka yasa ta murmusa ta sauka ta bisu bata gayawa kowa DANJAR da Rabi take a wajen fitsari ba, tana zuwa daƙyar ta lallaɓa ta tayi tsarkin suka koma mota, Hamma Saheeb kuwa ji yake kamar a maidota kusa dashi yayi ta jibgarta har saita nutsu, ya tsani tsaye-tsaye a mota.






~~~~~~~"Nayi magana da Nafisan nasan kuma zata sa shi ya aure ki, ke kanki kinsan yadda suke mata biyayya, wannan ba komai bane a gurin Saheeb, ki nutsu dan Allah ki dena wannan shaye-shayen, kuma duk wani club da kike zuwa Nawwara dole fa saikin dena, bana son ya hango wani tazgaro a gare ki" cewar Mom kenan, Nawwara kuwa a buge take dan saida tayi tatul ta dawo gida, jin uwar kawai take, dan bata jin zata dena shan komai tana jin daɗin rayuwarta a haka,





"Mom! Mom!! Mom!!!"


Mom dake ɗakin Nawwara ta jiyo muryar Hafiz babban ɗanta yana kuza mata ƙira kamar sa'arsa, fita tayi tana faɗin "haba Hafiz mene haka ne?, wannan ƙira kamar ba uwarka kake ƙira ba", "Mom gaskiya na gaji da abinda Dad yake min, tinda na dawo daga America yake samin ido akan lamurana, na gaji kice ya fita sabgata, lokacin da yayi rayuwarsa shi wane ya shiga harkarsa ya sa masa ido" cikin ɗaga murya Hafiz yake wannan tijarar wa mahaifinsa,



"kai Hafiz kana cikin hankalinka kuwa?, ko dai kaima shaye-shayen kayo?, Mahaifin naka kakewa wannan kashedin?, lallai ne Hafiz to ka tsaya iya shaye-shayen ka amma karka sake ka raina Iyaye, domin kuwa binsu shine kaɗai mafuta a gare ka sha sha sha kawai" bayan ta gama faɗa ta barshi a wajen yana huci, gashi dai gient dashi gemu maya-maya amma bashida hankali, zama yayi yana huci.




Hafiz manemin mata ne na bugawa a jarida, duk macen daya ƙyalla ya hango saiya san yadda yayi ya keta mata mutuncin ta, da yawa baya neman matan banza sai kamilallu, dan yace sunfi daɗi, kuma ko ba komai shine farkon keta su, akwai wata Yarinya Jalila daya nuna yana sonta da gaske, yasa ta fara son shi, a ƙarshe yayi amfani da son da take masa ya ratsa mutuncinta, Yarinya ƴar gidan tarbiya kowa yasan yadda mazan gidan da matan suke da tarbiya, amma saida yasan yadda yayi ya watsa mata wannan tarbiyar da Iyayenta suka jima suna ginata a kai, yanzu takai ta kawo ya maida ita karuwarsa, har bata iya jure rashinsa.





Wa'iyazubilla, Ubangiji ya tsare mana dukkan Haular mu daga faɗawa sharrin Zina, Allah ya tsare mana su, ubangiji ya kare su daga maza irin su Hafiz, Allah ya kare mana su dan nabiyyurrahmati, ameen.





A wannan tafiya Rabi tasa an tsaya yafi sau biyar, zuwa Yanzu ta hasala su Inna da Baba, Abdul, Hamma Saheeb, Kausar kuwa dama ta jima da hassala dan ita ke raka Rabi, Inna faɗa tayi mata sosai sannan ta nutsu, Baba kuwa har maketa yayi, Daddy da Mummy, da kuma Muhammad su kaɗaine basu ga laifin Rabi ba, driver ma kansa ya gaji da halinta.







Wannan kenan





*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*





*By Rumyn Royal*




*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 31-32*

>>>>>>>>>>>>>>Shuru Rabi tayi kasancewar Inna ta gargaɗeta, ga kuma tafiya data lula, kowa yayi shuru a motar, tashin karatun ƙur'ani kawai ke tashi, na Sheik Sudais, can bayan wani lokaci Rabi ta ɗago ta kalli kowa a motar, Daddy ta kalla murya a hankali ta ce "Daddy kashi nake ji wallahi, kuma ya matseni", ta faɗa masa ƙasa-ƙasa yadda babu wanda zaiji, murmushi Daddy yayi, umarnin tsayawa Daddy ya bayar, driver ya dakata ya nemi bakin hanya ya tsayar da motar, kowa na motar tambayar kansa yake meyasa Daddy ya ce a tsaya?, 



kasancewar hanya ce babu wani guri da za'a tsaya ta shiga tayi, hakan yasa Daddy fita a motar tare da Rabi da take ta riƙe ɗuwawunta dan kar kashin ya fito, cikin ikon Allah Daddy ya hango wata ƙaramar Ruga ta cikin duhuwa, kama hannun Rabi yayi suka tafi, 



Suna isa kuwa Fulanin wajen suka tarbesu da mutunci, magana yayi musu da yaren fillanci, nan take wata mata ta riƙe hannun Rabi ta raka ta inda suke larurar su ta yau da kullum, komai nasu a tsaftace gwanin sha'awa, Muhammad ne ya biyo su Daddy, dan basu faɗi inda zasu ba, yana zuwa Daddy ya ce "meya fito dakai?",



"Daddy munga ka fito ne baka yi magana ba shine Baba ya ce na biyo ka sa bo da irin wannan wajen akwai macizai" cewar Muhammad,



"babu abinda zai faru Muhammad, Ƙanwarka  na rako take bayan gida", murmushi Muhammad yayi dan yasan dama bazai wuce dalilinta ne yasa Daddy fitowa a mota ba, "Daddy daka bari ko Kausar ta rakota ai", "ni naga damar rakota, taya zan bar wani ya rakota bayan kun takura mata, da tayi abu ku hayayyaƙo mata", cewar Daddy daya ɓata rai,



Muhammad cewa yayi "Daddy wallahi ni tinda take abinta banyi magana ba, ni abinda take ma nishaɗi yake sani", Daddy ya ce "ya dai rage naku idan har da kai ma", dai-dai nan Rabi ta fito ta nufo su Daddy, Muhammad ta kalla ta ce "laaa Hamma Muhammad kaima kashin zakayi?", dariya ce  ta zowa Muhammad sai kuma ya dake ya ce "ke dai da kika yi ma falillahil hamdu", Daddy ne ya ce "Adabiyya tawo mu tafi", godiya yayiwa fulanin wajen tare da ɗakko kuɗi wanda baisan adadinsu ba ya basu, da sunƙi amsa saida Daddyn ya matsa sannan suka karɓa, hanya suka kama dan komawa mota, a hanya Rabi ta ce "Daddy nagode Allah ya saka maka da gidan Aljanna", da ameen suka amsa daga Daddyn har Muhammad, suna shiga aka hau tambayarsa inda yaje, ce musu yake naje na duba mutanen Rugar can, dan duk inda fulani suke ina son zuwa wajen,  Inna ta jishi ne kawai dan tasan wani abin Rabi ta ƙulla, tafiya ce ake yinta kamar za a bar Ƙasar dan Taraba badai nisa ba, sai wajen isha suka isa Taraba, bakin ruwan da zai tsallakar dasu Mambila suka zo, nanfa tsoro ya cika Rabi, dan cewa tayi ba zata hau Jirgin Ruwan ba, sai da Mammy ta ce "Rabi'atu kiyi haƙuri ki rufe idan ki kinji Yarinyar kirki", ruƙunƙume Mammy tayi suka shigar da Motarsu, Jirgin ruwa ya fara tafiya, duk da suna  cikin motarsu amma hakan bai hana Rabi jin tsoro ba, Kausar kanta a tsorace take, Hamma Saheeb kuwa takaicin Rabi yake tinda suka baro Bauchi, jiyai ya ƙara tsanarta fiye da da, hanyar cin Ubanta yake nema ido rufe.




Suna isa gaɓar ruwan suka sulala motarsu suka nufi cikin garin na Mambila cikin Rugar Harɗo Bello, goma sauka suka isa cikin Rugar, kasancewar ansan da zuwansu, jama'a da dama basuyi bacci ba, duk inda ka gifta mutane ne birjik suke biyo motar, rakiya sukai musu har bakin sashin gidan Harɗo, shima yana zaune shida mutanensa ciki harfa Yayyen Inna da Daddy, cikin farin ciki Harɗo ya miƙe, Inna da Daddy sai murnar ganin tsohon nasu suke, cikin azama suka fita a motar, suka nufi Mahaifin nasu, kyakykyawan tsohon mai kamala da kwarjini sai murmushi yake hakan da yayi sai naga yana min kama da Rabi sosai, haske kawai zai fita, Mammy, Muhammad, Hamma Abdul da Kausar duk sun fito, gogan naku kuwa yana ciki ya kifa p-cap ɗinsa a fuskarsa kamar me bacci, suna isa gaba ɗayansu suka tsuguna a gaban Harɗo suna mai miƙa gaisuwar su a gare shi, shi kuwa Uban sai kallon su yake yana jin rahama a zuciyarsa, bayan ya amsa duka gaisuwar su, Rabi ya hango jikin Mammy ta riƙeta idanunta har yanzu a rufe, "Matar ya da rufe ido, ko baki son ki kalli mijin naki?", cewar Harɗo, sai yanzu ta buɗe idonta, dan tsoron da take karta buɗe idonta ta ganta kusa da ruwa, ganinta kusa da tsohon da take yawan zancen sa, yasa cikin sauri ta miƙe ta nufi wajen sa, jikinsa ta faɗa tana dariya, dan ta saba sosai da tsohon, duk sanda suka zo tana tare da shi, jinin su ya haɗu sosai, cewa yayi "au dama gulma ce tasa kika rufe idon?", "waifa tsoron ruwa take shine ta rufe idon sa bo da tsoro", cewar Muhammad,



Su Inna sun gaisa da  yayunsu maza, sai farin cikin ganin juna suke, daga nan suka rankaya cikin gidan harda Harɗo da manyan Ƴayansa, 



Mahaifiyarsu dake tsaye tana kai komo tinda taji Autocinta sunzo ta kasa zaune ta kasa tsaye Allah-Allah take ta gansu, aikuwa suna shiga ta nufo su da farin ciki, Inna ce ta rumgumo ta, Daddy kuma hannunta ya riƙo suka zauna a ƙatuwar shimfiɗar da tayi musu, sauran ma duka zama sukai, bayan an gama gaisawa Mahaifiyar su Daddy ta ce "karfa ayi tuya a manta da albasa, ina maigida na ran gida, bangan shi ba, ko bai dawo daga ƙasar arnakun ba?", cewar Innawuro mahaifiyar su Inna, sai yanzu suka farga baya cikin su, Daddy ransa ne ya ɓaci dan yaƙi jinin wannan hali na Saheeb, tashi Daddy yayi ya nufi mota dan yasan yana ciki, ilai kuwa yana zuwa ya ganshi ya rufe fuska da hular hana sallah, "Son bana son shegantaka, kai koda yaushe saika nuna halinka, to idan ba zaka fito ba ka koma", yana faɗar haka ya nufi cikin gida, Hamma Saheeb kuwa baiji daɗi ba ganin ya ɓata ran mahaifinsa, fitowa yayi ya nufi gidan, hayaniyar daya guda ita ya taras dan gidan sai haya-haya ake, haɗa ido sukai da Rabi harara ya galla mata ita ma bata hana idonta ramawa ba, hakan yasa zuciyarsa ta ƙara ɓaci, tare da fatan su keɓe waje ɗaya yayi maganinta, yana zuwa ya tsuguna ya gaisar da kowa, kowa sai yaba yadda ya koma suke, Innawuro ce ta tashi ita da Inna sukaita shigo da gasassun Zabbi da na talo-talo, ga damammiyar fura mai sanyi, tasha zuma, nan aka fara habzi, kowa ci yake yana santi, driver ma har ciki aka ƙirawo shi yaci a cikinsu, kasancewar sunyi sallar isha, kowa masaukinsa aka kaishi, Hamma Saheeb, Hamma Abdul, Hamma Muhammad duk ɗaki guda aka basu, Hamma Saheeb wanka yake da muradin yi, Innawuro ya ƙira ya tambayeta inda zai kama ruwa, bayan gidansu ta nuna masa, sannan ta haɗa masa ruwan wanka mai ɗumi, ta bashi sabulu mai ƙamshi, kasancewar Daddy yana  kawo musu mai yawa, ba yadda Hamma Saheeb ya iya haka ya shiga yayi wankan, sai dai yana mamakin tsaftar tsohuwa nan, komai nasu tsaf, bayan ya fito Hamma Abdul ya shiga, Muhammad ma yayi, suna kwanciya kuwa bacci ya ɗauke su.




Washe gari da sassafe masu kiwo wato jikokin Harɗo da tattaɓa kunnensa suka kaɗa saniyoyinsu zuwa kiwo, Rabi da ta tashi da wuri ta hango ɗan gidan Baffa Adamu Yayansu Inna kenan, zai fita kiwo ta nufe shi da sauri ta ce "zan bika dan Allah Hamma Surajo", cikin hausar sa da bata fita sosai ya ce "a'a Rabi kiwo akwai wuya, ba zaki iya ba, kuma daji muke shiga", ɓata rai tayi ta ce "to nidai ina son zuwa, wallahi zan iya", babu wanda suka tambaya suka ɗau hanya, ita ma ta ɗauki kara tana bugunsu, sunyi nisa suka tsaya dan Saniyoyin suyi kiwo, aikusa Rabi ta faki idon Surajo ta nufi wani guri mai duhuwa kasancewar akwai wata bishiyar mangwaro mai Ƴaƴa shine taji tana son sha, tana zuwa tahau sa sandarta tana saƙalowa, abinda bata sani ba shine wannan nunanne da take saƙalowa wani shafcecen maciji ne a nannaɗe a jikin reshan, batai aune ba macijin nan da yaga kamar yaƙarsa Rabi take ya silalo ya bata sara a wajejen ƙwanjinta, ƙara ta saka mai amo ta yadda saida gaba ɗayan dajin ya amsa.✍️




Wannan kenan



*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*




*By Rumyn Royal*



*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 33-34*

>>>>>>>>>>>>>Rawa jikinta ya hau yi, idanuwanwa suka kakkafe nan take ta baje a wajen, Surajo da yaji ihu, baiyi tunanin na Rabi bane, saida ya dudduba yaga bata bayansa nan take ya tsorata, ya nufi inda ya jiyo ihun, 



aikuwa dubawar nan da  zaiyi sai ganin Rabi yayi a kwance kamar babu rai, a sukwane ya isa wajen yana ƙwalla ƙiran sunanta "Rabiii!!!, mai ya sameki Rabiiiii!!!!", cikin jarumta ta jinin fulani Surajo ya saɓi Rabi ya koma gida da ita a guje, dan shi baima san Maciji ne ya sare ta ba, tin kan ya isa gidan Harɗo yake ƙwalla ƙiran sunan Harɗo "Harɗo!!!!!, Harɗo!!!!!!", 




Harɗo suna zaune suna karin kumallo dasu Daddy, Baba, da sauran manyan Ƴayan Harɗo, Baffa Mahaifin Baba wato kakan Rabi, dasu Hamma Saheeb, jin ƙira suke kamar ba cikin hayyaci ake yinsa ba, saurin fitowa sukai, hakan yayi dai-dai da ƙarasowar Surajo saɓe da Rabi, yana kuka yana kuzawa Harɗo ƙira, ganin wadda ya ɗakko yana ihu, yasa hankalinsu tashi, Harɗo ne ya kamata ya kwantar akan wani ƙaton ganye, Baffa Mahaifin Baba faɗi ya ke "maiya sameta?", Daddy, Baba, Hamma Abdul, Hamma Muhammad, hankali tashe suka nufo wajen da aka kwantar da ita, Harɗo ne ya ce "wannan saran Macije ne, kuma baƙin maciji, maza a ƙira min Giɗi", ya faɗa cikin bada umarni, Baba ji yake kamar yayi ta kurma ihu, ganin Ƴarsa a kwance kamar gawa, Hamma Saheeb kuwa in banda zuciyar musulunci cewa yake a ransa "Allah ya ƙara, ga Maciji yayi maganinki, shegiya aljana", ana haka Giɗi ya zo, nan Harɗo ya  nuna masa Rabi, Giɗi ya kalla ya gyaɗa kai, wani ganye ya ciro a jakarsa ta fata, ya mitstsika saida ganyen yayi ruwa sannan ya ɗage hannun rigarta daya rufe ƙwanjinta ya murza a wajen, yana cire hannu wani jini baƙiƙƙirin ya fito, bakinta ya saita ya ɗiga mata ruwan ganyen, nan take ta fara tari, sai kuma amai, shima baƙi, saida ta gama sannan ta koma lakwaf ta kwanta sai bacci, wasu saiwoyi Giɗi ya bawa Harɗo yace a dafa da jar kanwa idan ta farka shi za'a fara bata, sallamarsa Baffa Adamu yayi, ya tafi, 



Inna ce da Mammy da Innawuro suka fito da gudu daga cikin gida, Inna kuka take Mammy tana share ƙwalla, ganin Rabi a kwance yasa Inna zatai kanta Harɗo yasa Hamma Abdul ya riƙe ta, kuka take sosai, ta rasa mai yasa bata iya juriya akan Rabi, 



Surajo aka tambaya garin yaya haka ta faru?, komai ya faɗa musu, har ihunta da yaji ya nufi wajen ya ganta a haka, faɗa Baffa Adamu yahau shi da shi, akan me zai tafi da ita bayan yasan Dajin baida kyau, haƙuri aka bawa Baffa Adamu yayi shuru, Inna kuwa hankalinta sosai ya tashi saida akai mata bayanin yanzu babu dafin macijin bacci take, sannan ta ɗan nutsu, ciki suka koma har Rabin. 




Hamma Saheeb kuwa tin sanda ta fara aman nan yabar wurin dan sosai zuciyarsa take tashi, tsaki kawai take yana faɗin "Allah wadaran naka ya lalace, haka kurum rawar kai da shaiɗanci yasa taje waje Allah ya haɗata da dai-dai ita shine duk zasu ɗaga hankalinsu, ni dama mutuwa tayi kowa ya huta da ita, haba wallahi garin duk ya ishe ni", ya faɗa yana ta auna tsaki, cewgam ya ciro ya sanya a bakinsa jin yadda zuciyarsa take tashi.







"Dear ya dace ace ka dawo haka, ka tafi shuru kamar bakada Iyalai, wallahi kana bani mamaki", cewar Yaya Talatu, daga can ɓarin aka ce "Kema dai kin san yanayin Siyasar mu, zaɓe ya matso dole sai kinai min uzuri, amma kiyi haƙuri na kusa dawowa, ina my Child?", 



Yatsina fuska tayi ta ce "suna lafiya ni jira ma nake ka dawo, ina so muyi magana akan Nawwara tasa rigima Saheeb take so, kuma ta firgice sosai akansa, dan Allah ka dawo muji da wannan matsalar",



"Ah lamari yayi, in sha Allah zan dawo a kwanakin nan, kinga ma shugaban jam'iyya ne yake ƙira na, kashe anjima zamuyi magana", yana kaiwa nan ya datse ƙiran, tsaki tayi ta aje wayar, tana takaicin mijin nata, ya bawa siyasa muhimmanci fiye da ita da Yaranta.






Nawwara ce sanye da wasu irin kaya wanda zance da su da ta bar kanta tsirarara babu maraba, ga kanta daya sha kitsan atach har gadon bayanta ya zubo, tasa eyalashesh ga taci makeup sai sheƙi take, wani takalmi tasa hils kalar komai na jikinta pink ne, tayi kyau sosai a wajen Ƴan uwnata Ƴan bariki, Mom dake falo tana kallon tashar Cnn bayan sun gama waya da mijinta, ganin shigowar Nawwara tayi "Mom zan fita ki ara min motar ki please tawa na fiffita da ita, kar guys su raina ni", Mom da take bin shigar Ƴartata da kallo ta ce "Nawwara kina nufin da wannan shigar zaki fita?", "yes Mom mai shigar tawa tayi?", 



"ko arne zaiji kunyar fita a haka Nawwara, ki koma ki saka kaya na mutunci bana son sakarci", "what caf Mom dan Allah bani key ɗin bana son gayu suyita jira na, bye", ta faɗa bayan ta zari key ɗin ta fice, "Nawwara ki dawo nace miki, karki fita a haka !", Mom ta ƙwalla dan taji, amma ina ko juyowa batayi ba, "oh Allah wannan wane irin zamani muke ciki?", Mom ta faɗa tana kallon sama, 




Hafiz ne ya shigo yana fito "ah Momcy kina lamari, kina zaune kice ke kaɗai kamar mayya", "kai mahaukaci ni kake cewa mayya, tukunna ma baka iya sallama bane?", cewar Mom




"kai Mom nayi mana kece dai baki ji ba",



"kana girma kana ƙara zama mara tunani ko?, dakai zanji koda ƙanwarka?, ka girma ka isa aure amma kana wasu abu na tantirai", "Mom kin fara ko?, dan Allah a barni a yadda nake kawai, ni bana son wani cece-kuce haba", ya faɗa tare da miƙewa ya barta da sakakken baki, kai ya gyaɗa dan lamarin na Yaran nata ya fara bata tsoro.





Hankalin Mutanen Yamadawa da Unguwar gini yayi tsananin tashi, dan yanzu a ƙalla kullum sai an samu ɓatan Yara biyar zuwa sama, duk yadda kika kai ga killace Yaranki tofa sai an sace, Yara da yawa sun dena zuwa makaranta, 






Gefe guda Tsalaha ya zama wanda yake faɗa aji a faɗin Ƙauyen Yana da kewayenta, mota yake hawa mai ɗumi, Rakiya ma kanta yanzu driver ne yake kaita duk inda zata, sai dai Tsalaha yana son yayi aure amma duk macen daya nema  sai abu ya tafi rimi-rimi sai yaji ya tsani Yarinyar, ba komai bane yasa haka illa Rakiya ta tashi tsaye akan Tsalaha dan tace ita kaɗai tasha wuyar Tsalaha dan haka ita kaɗai zata sha daɗin, shi yasa ta shiga ta fita ta hana shi aure, gata ita kuma kullum ƙara hawa take kamar farashi teɓa sai hauhawa take.





Alhaji Nura ne yake waya da Ogan su,  "Ran Oga ya daɗe", daga can aka ce "aiki yana kyau, tako ina ina samun yadda muke so, dan haka akwai kyauta mai gwaɓi Dodanya zatai mana, dan haka ranar Lahadi akwai taro, kuma da yuwuwar ka tawo da wannan Yaron naka Tsalaha", "an gama ranka ya daɗe, gaskiya nayi murna sosai, Allah ya kaimu ranar", bayan sun kashe wayar ya ƙira wayar Tsalaha ya shaida masa akwai inda zasu ranar Lahadi.





Nawwara kuwa bayan ta fito bata zame ko ina ba sai night club dake nasarawa GRA club ne wanda ya tara Ƴaƴan manya, idan kasan kai ba ɗan wani bane to karka doshi ko hanyar gurin ne, dan tabbas zaka wulaƙanta, tana isa tayi parking ta fito cikin wani irin taku ta nufi cikin club ɗin, aikuwa tana shiga aka hau ihu tare da faɗin "sai kinyi Nawwara Ƴar Sanata!!!", ko kallon inda  suke batayi ba ta doshi BAR nan take aka ɗakko mata kwalbar wisky batayi ƙasa a gwiwa ba ta ɗaga kwalbar saida ta zama saura rabi ta sauke, idanuwan nan sunyi ja sosai, Shamsu ne ya iso tare da riƙe kwalbar yana girgiza mata kai alamar ya isa haka, harara ta watsa masa tare da fizgar kwalbar ta ƙara kafa kai saida daga babu sannan ta kwantsamata da ƙasa, aikuwa nan take hankali ya dawo kanta, filin wajen ta fita ta tsaya, kallon inda Dj mai bada sauti tayi ta ɗaga ɗanyatsanta ɗaya, nan take ya sakar mata  wani daddaɗan sauti, aikuwa bata tsaya ɓata lokaci ba ta fara rawa, ihu aka sa, dan Nawwara badai iya rawa ba, rawa take kamar bada jikinta take ba, Shamsu dake tsaye kishi duk ya cika shi, ganin yadda maza suke kallon ta, dan har yanzu yana ƙaunar Nawwara a cikin zuciyarsa, can aka canza sauti akasa waƙar nan ta Rihanna da Drake wadda sukai a wani club, nanfa maza da mata aka cakuɗe, nan na hango Shamsu ya shiga ya kama ƙugun Nawwara suna rawa cike da ƙwarewa, sai wajen 1:30 na dare suka sarara bayan sun bugu da giya, Shamsu da baisha da yawa ba shiya kai Nawwara gida, saida yaga ta shiga can cikin gida sannan ya tafi. 







Mom data kasa bacci tana ta ƙiran wayar Nawwara ba a ɗagawa, har kuka tayi sa bo da baƙin ciki, duk da bayau ta saba kaiwa hakan ba, tana zaune tana gyangyaɗi taji motsi, Nawwara ce tafe sai tangaɗi take tana surutai, binta da kallo Mom tayi harta shige side ɗinta, haka ta koma ɗakinta cikin baƙin cikin halin Yaran nata.






*Mambila*




Sai wajen Magriba Rabi ta farka, maganin da Giɗi ya bayar aka bata tasha, nan take ta nemi abinci, bata akayi taci ta ƙoshi, wanka aka haɗa mata ruwan ɗumi tayi, sallolin da ake binta tayi, dan Rabi badai Ibada ba, bayan tayi sallar isha ta koma baccinta, a sannan ne hankalin su Inna ya kwanta, 






Daddy tsaraba yayo mai yawan gaske, bayan kayan Abinci, sai kaya Atamfofi dilers, haka shaddodi, lesuka, yaduka, takalma, huluna, mayafai, sabulai, mayukan shafawa, turaruka, kowanne mai yawa, dan Harɗo yana rabawa Ƴan uwa da abokan arziƙi, Inna ma da Baba ba'a barsu a baya ba suma sun taka rawar gani, sunyo nasu dai-dai gwargwado, Albarka kuwa sun shata wajen Mahaifansu. 





Inna taje gidan Surukanta, wato gidan su Baba, kasancewar Mahaifiyarsa ta rasu sai matar Babansa hakan yasa kadaran kadaham ta karɓe su, dan Baba Hari batada mutumci ko kaɗan, shima Baffa kakan Rabi haƙuri yake da ita, Rabi kuwa tinda taje take mata fitina kamar yayayyiya, Baba Hari sai bari-bari take, ƙarshe zuwa tayi ta sakar mata tumakinta da suke ɗaure ta sake su tasa Baba Hari fellawa da gudu dan taro su, Inna sai bari take amma Rabi kamar zuga ta ake, Baffa kuwa yana ƙaunar Rabi shi yasa duk abinda take yake kallonsa a Yarinta, sai da Hamma Abdul yazo gidan sannan Rabi ta saurarawa Baba Hari da ta'adi, Baba Hari sai zagin su Inna take a ranta.






Kwanan su Inna biyu suka baro gidan Baffa bayan sun cika su da kayan arziƙi, Rabi haka kurum ta tsani Baba Hari, dan kafin ta baro gidan saida ta watso mata da  kwallayenta da ta jera su a saman wata ƴar kanta, Inna bata sani ba dan saida suka fito Rabin ta ce tayi mantuwa, ashe gidan ta koma tayi wannan lamari ta fito, Baba Hari data jiyo ɓari tana bayan gida ta fito a guje, Rabi ta gani "ke meya dawo dake?" cewar Baba Hari




"Mantuwa nayi ", Rabi ta faɗa tana mai barin gidan, Inna Hari tana shiga ɗakinta taga jeranta wanda shekara da shekaru bai taɓa faɗowaba sai yau, nan take ta gane Rabi ce ta aikata, kuma wannan ɓari da Rabi tayi ta ɓaro da wani asiri da tayiwa Baffa, kuma dama Bokan yace indai wannan asiri ya faɗi ƙasa to asirin zai karye.✍️



Wannan kenan




*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*





*By Rumyn Royal*




*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*




*Allah kasa mu cika da imani, ubangiji yasa muyi kyakykyawan ƙarshe, Allah ka yafe mana dukkan kura-kuren mu, ba danmu ba badan halin mu ba ameen ya Hayyu ya Ƙayyum*





*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 35-36*

>>>>>>>>>>>>>>Taji ciwon wannan abu da Rabi tayi mata, hakan yasa ta ƙullaci Rabi akan saitayi maganinta, dan kuwa Boka yayi mata nisa sosai shi yasa kafin taje wajensa tana jimawa.





Tsakanin Rabi da Hamma Saheeb sai dai muce Allah ya sassauta, dan tsana iya tsana sun kafawa junan su, Hamma Saheeb ya tsani raini, sannan yana son a girmama shi, amma duk wannan baya samunsa daga Rabi, dan ita tsakaninta da Allah a arne take kallon sa, kasancewar yaje ƙasar arna yayi karatu, wannan kaɗai yasa Rabi sawa a ranta ba zata taɓa kula shi ba kar Allah ya kamata, wannan yasa ko a hanya suka haɗu komawa take ko kuma ta sunkuyar dakai ya wuce, babu wanda ya taɓa kula da yanayin da yake faruwa, dan su a tunaninsu Rabi tana gaida Hamma Saheeb.





Kwanansu a Rugar Harɗo bakwai suka fara shirin komawa dan Hamma Muhammad zai tafi India dan cigaban karatunsa.




Inna ce zaune gefan Harɗo suna hira cikin farin ciki da annashuwa,  cikin hirar da suke ya tambayeta ya ce "Saratu ina fatan yanzu Rabi'a bata janyo miki wata fitina ko?", murmushi tayi ta ce "To Harɗo sai dai muce Allah kyauta, dan lamarin Rabi sai Allah, sai dai fatan shiriya, dan kuwa kullum ne sai idan bata fita ba", 



"Kita binta da Addu'a, addu'ar uwa kaifiyan ce akan Yaranta, da yardar Allah komai zai wuce, kuma akwai lamarin dana hango game da Yaran nan, shiyasa nake so kafin ku tafi ayi komai anan a gama, sauran ya rage naku", cewar Harɗo



Inna da ta shiga cikin duhu ta ce "Harɗo ban fahimci zancenka ba, wasu Yara ne kake magana akai?", baƙi Harɗo yayi aka ƙira shi, shi yasa ya fita ba tare da ya sanarwa da Inna abinda zai gaya mata ba, korar zancen tayi ta koma wajen Innawuro.




Yau da yamma gidan Yayunsu suka je, da gidan Baffa Adamu suka fara, sun sha hira da matarsa Hanne, mace mai kirki mai faran-faran, Mammy taita wayar mata dakai akan yadda zata gyara kanta da tarairayar miji, irin dai zancen nan na tsakanin faccaloli, kuma alhamdulillah Hanne tana ɗaukar darasin Mammy, daga nan suka je gidan Baffa Hamisu, Hamza, Bashir, Rufa'i, gidan Adda Shatu ne ƙarshe , dan ita gidanta da nisa, sunyi farin ciki sosai da ziyarar da suka kai musu, Daddy ya cika su da abin arziƙi, har kuɗaɗe ya rabawa Yayyansa, sannan ya bawa matansu, Adda Shatu ma jari ya ƙara mata, Mammy da Inna sun cika su da kayan sawa, sai Magriba suka dawo, Hamma Saheeb Million biyar ya bawa Harɗo ya ce a rabawa family da abokan arziƙi, aikuwa yayi farin ciki sosai, Kausar data shiga dangi sai farin ciki take tana jin dama a Kano suke da kullum tana tare dasu, Rabi kuwa babu abinda yayi mata zafi, lamarinta take babu ruwanta, a daren suka koma gidan Baffa harda Daddy, shima suka juye masa kayan arziƙi, Daddy ya bashi kuɗi mai yawa, sosai yayi farin ciki, Baba Hari ma Daddy ya bata dubu hamsin, aikuwa kamar zata goya shi haka taitaji, a daren Inna tayiwa Baffa sallama, Rabi ce bisa cinyar Baffa tana cin gashashshen zabo, Baffa da yake ji kamar su bar masa Rabi ya ce "Adabiyya ko zaki zauna tare dani ne?", baki ta turo ta kalli fuskar kyakykyawan tsohon ta ce "Makarantar fa da nake zuwa?", dariya Baffa ya yi ya ce "aidama nasan saikin tsiro da wani abin da zaisa kiƙi zama dani, shi kenan nima na fasa bana auren dake", a haka akaita hira har dare ya fara, sallama Hamma Abdul yayi musu tare da Inna dan dama Baba anan zai kwana sai da sassafe ya koma rugar Harɗo su tafi, Baffa ne ya tsaida su ya ce su jira shi, ɗakinsa ya shiga ya fito, Rabi ya ƙira ya ce "zo nan Adabiyya", zuwa tayi, wata sarƙa mai kyau mai kyalli sai ɗaukar ido take ya sanya mata ita a wuyanta ya ce "ki kula sosai da wannan sarƙar Adabiyya, karki dinga fitowa da ita sarari, kidinga barinta cikin rigarki kinji", kai ta gyaɗa masa, tare da faɗin "nagode Baffa na", "yawwa Adabiyya, sai Allah ya ƙara sada mu da alkhairi, gobe zanzo naga tafiyarki", ya faɗa yana shafa kanta, Hamma Abdul ne ya ce "au wato wariyar launin fata za'a nuna min kenan, ta ita kake nikam ko oho, to nikam nayi fushi", ya faɗa yana juya baya, Baffa yana dariya ya ce "haba abokina, kasan ni dakai bata ɓaci, kai naka na musammam ne kaji", nan take Hamma Abdul ya dawo ya rumgume kakan nasa, dan yana son tsohon sosai, a haka suka tafi, dan dama tare da su Daddy da Mammy, Kausar, Muhammad da Saheeb suka zo, shine suka barsu Inna anan suka koma.







Bayan sun koma  wajen ƙarfe tara na dare Harɗo yasa aka ƙira masa Baffa, Baffa Adamu, Baba, da duk manyan Yaransa, harda Daddy a ciki, bayan kowa ya nutsu yana jitan yaji abinda ya tara su Harɗo ya fara magana kamar haka......





*Kano*


Nawwara sai ƙiran layin Hamma Saheeb take wayar tana shiga but ba a ɗauka, hakan yasa kanta ɗaukar zafi, babu ɓata lokaci ta fara bankawa kanta sigari, da taga sigari ba zata gamsar da ita ba, ta nufi friege ɗin dake ɗakinta ta buɗe, kwalaben wisky ne masu yawa a ciki, ɗaya ta ciro tin a tsaye ta fara kwankwaɗa, saida tasha yafi rabi, ta zo ta zauna, sanye take da wasu kaya pink colour masu taushi wandon ko cinyar ta bai sakko ba, rigar kuma iya cibiya, sai gashin  kitsan atach ɗinta daya sakko har bayanta, faɗawa kan gadon tayi, cikin mayen da ta fara take faɗin "kai zuciyata take so Saheeb, jikina burinsa ya mallaki jikinka Saheeb, ina son komai naka my Saheeb, dan Allah ka soni kona haukace", a haka bacci ya ɗauketa.





Hafiz daya shigo falon babu kowa, sai tashin kiɗa da yake jiyowa  a ɗakin Nawwara, nufar ɗakin yayi yana sana'ar tasa wato fito, yana shiga ya tsaya a bakin ƙofa yana ƙarewa Ƴar uwartasa kallo tindaga sama har ƙasa, a ransa faɗi yake "kut gaskiya Yarinyar nan akwai kaya, jibi sura iya sura, gata kuma tazo a Ƴar uwata anya bazan cire wannan na shana da ita ba kuwa?", bai gama shawara da ɗaya zuciyar ba, ya nufi gadon gadan-gadan, hayewa yayi ya fara shafata cikin ɗaukewar imaninsa, rigar jikinta ya janye albarkatun ƙirjinta suka bayyana, take yasa hannu ya fara wasa dasu, idanunsa ya rufe ya manta da cewa Ƙanwarsa ce, kayansa ya cire ita ma ya tuɓe ta sai mutsu-mutsu take idanunta a rufe, shi kuwa ƙara ƙaimin aikata fasadi yake shi da ƙanwarsa, imani yakau shaiɗan ya shiga jininsa, ita kuma jin ana mata wasanni saita fara tayawa tunaninta abokin cin mushenta ne Shamsu, dan sai ƙiran sunansa take, tana shafashi idonta a rufe, shi kuwa hakan ƙara zautar dashi yayi, baiyi ƙasa a gwiwa ba ya afka mata, saida ya gama ya fice da sauri ya barta a haka a sheme tana baccin asara.




Wa'iyazubillah Allah ka tsare haular musulman duniya daga aikafa zina, Allah ka shirya masu yinta su dawo hanya madaidaiciya tin kafin lokaci ya ƙure musu ameen, 



Ku duba Ƙanwarsa wadda suka fito ciki ɗaya ita ya afkawa, ita kuma sanadin buguwa da tayi yasa bata san abinda ya faru ba, Allah ya tsare.







Harɗo ya kalli Baffa ya ce "kaine ɗan uwa na wanda kai kaɗai ka rage min a duk faɗin duniya, na yanke shawara ba tare dana sanar maka ba, kuma ban saba hakan ba", jinjina kai Baffa yayi alamar gamsuwa, sannan Harɗo ya cigaba da cewa "kuyi haƙuri kuma, Allah ne ya bani ikon yin hakan, kuma na hango alkhairai masu yawa akan abinda za'a ƙulla, kai Rabi'u kaine ka haifi Bello wato takwarana, sannan ubane kai ga Rabi, dan haka ayau ina so a ɗaura auren Rabi da Bello, wannan shine hukuncin da Allah ya yanke, ni nan mai sanarwa ne, dan haka a wannan dare ina son a ɗaura auren su", Daddy murmushi yayi mai sauti, haka ma Baffa, Baba, da duk wanda yake cikin wannan majalisa saida ya dara, dan haka kurum suka ji abin ya musu daɗi, babu ɓata lokaci Harɗo yasa aka amso masa kuɗi a hannun Hamma Saheeb dan ya ce da kuɗinsa za'a biya sadakin matarsa, aikuwa ba musu ya bayar dan baisan abinda ake ciki ba, dubu ɗari ya bayar, aikuwa Daddy ya kawo ba ɓata lokaci aka ɗaura auren Rabi da Hamma Saheeb akan sadaki dubu ɗari lakadan ba ajalan ba, inda Baffa Adamu ya zama wakilin ango, Baffa Hamisu ya zama wakili ga amarya, nan taro ya tashi da addu'a, sai kuma fatan zama lafiya.





Tofa kunji yadda ta kaya, ya kuke tunanin yadda wannan lamari  zai zowa kowannansu musamman HAMMA SAHEEB ɗan ƙwalisa haɗaɗɗe, maiji da nira?,




Ya RABI zata ji idan taji cewar Arne ne ya zama mijinta, ya abin zai kasance?.





Shin ya Nawwara zata yi idan ta farka ta ganta tsirara, alhalin da kaya ta kwanta, ya zata ji idan tasan abinda Hafeez yayi mata?.





Hafeez zaiyi dana sanin abinda ya aikatawa Ƙanwarsa koko ya zaiyi?.



Ina Mom take wannan ƙazamin Lamarin ya kasance?.








Duk saikun biyo ni cikin littafina mai farin jini wato RABI DANJA, zaku haɗu da amsoshin ku.





Taku har kullum mai son gani da jin nishaɗinku *RUMAISA ALIYU INUWA (Rumyn Royal)*





*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*




Comment yayi ƙaranci, gaskiya hakan baimin daɗi, ya kamata naga canji ko nima na canza akalata.



09130984617





*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 37-38*

>>>>>>>>>>>>>>Washe gari ya kama su Daddy zasu koma Kano hakan yasa Harɗo ya ƙira Hamma Saheeb dan yace da kansa zai sanar dashi, hakan yayiwa Daddy daɗi ba kuma wai dan yana jin tsoron tinkarar Saheeb ɗin bane, a'a dan saboda ta inda aka hau to tanan ne ake sauka, Saheeb dake gaban Harɗo a zaune, ƙiran sunansa Harɗo yayi "Bello", Hamma Saheeb ya amsa da "Na'am Harɗo", 


"Jiya wani babban lamari ya same mu, amma wanda yafi ruwa da tsaki a ciki kaine, nasan kai maiyi mana biyayya ne tin kana ƙaraminka har kawo i yanzu, to ni nan na yanke hukunci na ɗaura maka aure kaida Ƴar uwarka, wato Rabi'a a jiya da daddare, ku......"  


Miƙewa Hamma Saheeb yayi cikin kiɗimewa, da tashin hankali ga wani gumi daya keto mata lokaci guda, wani kallo yakewa Harɗo na kana cikin hankalinka kuwa?, 


Cikin rawar murya ya ce "Har.....Harɗo, me kake nufi daka ɗaura min aure, auren ma da wata aba Rabi, wacce Rabin kake nufi waima?", ya faɗa muryarsa ya shaking.



"Dawo ka zauna Bello" Harɗo ya faɗa murmushi kwance a fuskarsa, "babu wani zama da zanyi, idan wasa kakemin harga Allah bana son wannan wasan", "na taɓa zama nayi maka ƙarya, ban taɓa ƙarya ba ban sani ba ko lokacin ƙuruciya, amma bana taɓa yin ƙarya ga kowa  balle kai jikana, a jikokinma ƙaramin cikin su, aure ne na ɗaura maka shi kaida Ƴar uwarka Rabi, ɗiyar Gwoggonka, kuma in sha Allah sai kowa yayi farin ciki da wannan lamari",  wata iriyar ƙara Hamma Saheeb ya ƙwalla tare da faɗuwa a wajen wanwar, kansa Harɗo yayi yana ƙiran sunansa, ƙarar da mutanen cikin gidan suka jiyo shiya sanya su fitowa, su Inna gaba ɗayansu suka fito, ganin halinda Saheeb  yake ciki gaba ɗaya hankali ya tashi, Mammy da tafi kowa shiga tashin hankali bata nuna a fili ba saboda kunya da kara, amma cikin zuciyarta kamar ta kurma ihu, Kausar kuka ta sanya, Muhammad dasu Baba da Abdul ne sukai kansa, cikin gida suka saɓe shi sukai da shi, Daddy kuwa gasan maƙasudin hakan, dan dama yasan za'ai hakan, Inna sai ƙwalla take sharewa, Rabi kuwa sai taɓe baki take, tana faɗin Allah ya ƙara a cikin ranta, tare da fatan mutuwa ga wannan arne, ruwa akaita sa masa bai farfaɗo ba, saida aka ƙara kuza masa wani sannan ya farka a gigice yana faɗin "dan Allah Harɗo ka janye wannan auren, bana sonta wallahi", jin haka kowa na wajen yayi kasaƙe, kallon Harɗo kowa yake, banda Daddy, Baba, da Innawuro, dan su duk sunsan abinda ya faru, kuka sosai Hamma Saheeb yake akan baya son Rabi a warware auren da aka ƙaƙaba masa da ita, Daddy ne ya daka masa tsawa, "Ka mana shuru shashasha kawai, me kake haka a gaban ƙannenka, kana hauka ne, Aure ne wallahi babu fashi, sai dai ka mutu", Mammy kanta ya kulle, haka Inna, Kausar, Hamma Abdul da Muhammad, Mammy da tinda take bata taɓa ganin Saheeb yayi kuka ba sai yau, hankalinta ne ya tashi, tana son ta tambaya babu hali, gashi Daddynsa bai taɓa yi masa tsawa irin haka ba, Inna data kasa haƙuri ta ce "mai yake faruwa ne Rabi'u?", ta tambaya tana kallon Daddy,



Harɗo dake zaune yana kallon kowa ya ce "aure nayi masa shine yake mana tambotsai, bai san cewa koya yarda ko kada ya yarda aurensa da Rabi babu fashi, ya rage nasa idan an kai masa ita ya kashe ta", Harɗo ya faɗa ransa a ɓace tare da miƙewa yabar gidan, 


Daddy binsa yayi dan ya bashi haƙuri, Innawuro ma miƙewa tayi tana hararar Saheeb daya sunkuyar da kansa, dan shikaɗai yasan irin masifar da yake ji a zuciyarsa, Mammy da murmushi ya ƙwace mata ta ce "Saheeb dama akan haka kake wannan abin, kuma ko kunya bakayi kake ambatar baka son Rabi agaban mu (tana nufin a gaban Inna da Baba), wallahi ka bani mamaki, Ƴar uwarka ce fa", da alama ran Mammy ya ɓaci, Rabi kuwa da yake hankali bai gama cika ta ba, tunaninta wata Rabin ake nufi ba ita ba, Innawuro tabi dan ta bata furar da ta dama  mata, Inna kuwa cewa tayi "gaskiya ba aiwa Babana adalci ba, ya za'ai ba'a tambaye shi ba kawai ace za a tursasa shi, ai yanzu ba kamar da bane, yanzu zamanin da muke kowa yana da nasa ra'ayin, wallahi da anyi shawara dani ba za'ai haka ba", ta faɗa da alama har cikin ranta tana goyon bayan Saheeb, Muhammad kuwa a ransa faɗi yake "banda abin Hamma da waɗan nan wayayyun matan da basuda kunya ba gwara ka samu Ƴar karkara ba waɗanda basu san kalmar iskanci ba bare suyi", Kausar kuwa bayan Hamma Saheeb take bi, dan kamar Hamma Saheeb ace wai Rabi ce matarsa, ranta ita ma baiso ba, Hamma Abdul kuwa baiji daɗin kalaman Hamma Saheeb akan Ƙanwar tasa ba, bai kyautu dan baya sonta ya furta a gabansu ba, ficewa yayi, Muhammad ya bishi, Mammy ma tashi tayi tabar gurin tana jin ciwon abinda Saheeb yayi, Inna aka bari da shi sai Kausar, tausarsa Inna taitayi, tana bashi haƙuri, shi kuwa dukda baiji daɗin ɓata ran Iyayensa da yayi ba, sai dai idan ya tuna Rabi suka aura masa sai yaji kamar zaiyi hauka, dana sanin zuwansa Ƙasar Nigeria yake gaba ɗaya, yasan da baizo ba hakan ba zata faru ba, kansa mugun ciwo yake, ga wani bahagon zazzaɓi daya rufe shi, Inna ce kawai take kula shi, amma gaba ɗaya su Daddy sunyi fushi da shi, hakan ya haɗe masa ya sanya shi ciwo lokaci ɗaya, Mota ya shige babu wanda ya kula can baya yayi zamansa, haushin Harɗo yake ji dan ko ganinsa baya son yi, bayan sun gama sallama suka hau motarsu, suna masu jin kewa suka ɗau hanya.






*Kano*


Nawwara tana farkawa ta ganta haihuwar uwarta da ubanta, ga jikinta a jiƙe alamun kamar anyi amfani da ita, tashi tayi tana dube-dube , miƙewa tayi ta shige toilet tana ta tunanin to taya ta kwanta ba kaya, kodai tana cikin maye ta cire kayan?, to kuma maiya kawo sperm a jikinta, kore tunanin tayi wanka tayo, ko tunanin sallah bataiba, ta nufi kitchen, Lami mai musu aiki ta hango cikin gadara da rashin tarbiya ta ce "ke ki kawo min pizzer da drink", amsawa tayi cikin girmamawa, cikin sauri ta haɗa dan kar tayi laifi ta kai mata, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ta sanya earpiece a kunnenta tana jin music idanunta a lumshe, Lami tazo zata ajiye mata a center table ita kuma Nawwara ta sauke ƙafar data ɗora kan ɗaga  ƙafar kawai sai drink ɗin da Lami ta kawo ya suɓuce ya zube jikin Nawwara, sanadiyyar ƙafar Nawwara data bige hannun Lami, aikuwa ji kake tas tas Nawwara ta wanke Lami da mari, kuma Lami ta girmi Nawwara nesa ba  kusa ba, hawaye ne ya zubo a fuskar Lami "ke wace irin shashasha ce jaka mahaukaciya, ke tinkiyar ina ce, dan dabbaci kawai ki zubo min abu, ku dama talakawan nan wallahi duk abinda aka haɗa daku a ciki sai kun nuna halin ku na matsiyata, dalla matsa ki bani guri, kuma kizo ki gyare wajen", Lami jikinta na rawa idonta na zubar da hawaye ta nufi kitchen dan ɗakko abinda zata gyara wajen, Hafiz ne ya shigo ganin Nawwara tana huci ya ce "a'a big girl haw per na ganki a tsaye waya taɓa min kyakykyawar sis ɗina?", tsaki tayi ta ce "wannan Jakar housemaid ɗin ce mana, wallahi na tsane ta", "sorry ki manta da ita ai irinsu gidan zoo ne ya dace dasu, ki shiga ki canza kaya ina so mu fita mu zaga gari", cewar Hafiz



Mamaki ne ya cika Nawwara mutumin da faɗa ne tsakaninsu, ko waje ɗaya basa iya zama saboda faɗan su, amma yau shi yake cewa su fita wani guri, ɗaki ta shige ya bita da kallo yana lasar baki kamar tsohon maye.




Riga da wando ta sako, sunyi mata kyau sosai, kalar pink da ratsin blue da alama tana son kalar pink, dan komai na ɗakinta pink ne da ratsin fari, ɗan ƙaramin mayafi ta ɗakko blue ta yane kanta dashi, hils ta sanya blue tayi kyau ainun, tana fitowa ya zuba mata ido yana jin feeling yana taso masa, "wow pinky babe kinyi masifar kyau", murmushi tayi ta ce "Thanks dear", tashi yayi ya ɗau makullin motarsa suka fice, yawo yaitayi da ita, sai wajen magriba suka dawo ɗauke da shopping ɗin da yayi mata, sai mamakinsa take, amma idan ta tuna he is her brother saita cire mamakinta, sai bayan isha Yaya Talatu ta dawo, a falo ta samu Yaran nata suna game, hakan yayi mata daɗi sosai, suna ganinta suka miƙe suka rumgumeta suna mata oyoyo, "My kids naji daɗin ganinku haka, ina fatan ku kasance haka har ƙarshen rayuwarku", kiss suka bata tare da amsa mata, Nawwara ce ta nunawa Mom kayan da Hafiz ya saya mata, Mom saijin daɗi take da Yaran nata suka samu kusanci haka.



Nace hmmm Hajiya Talatu manyan ƙasa, wannan kusancin bana arziƙi bane






Matafiya wannan karon babu uhm bare uhm uhm kowa da abinda yake saƙawa a ransa, Inna sai gani take ba aiwa Saheeb adalci ba, sauran kuwa sunji daɗin haka idan ka cire Kausar, Abdul kuwa haushin Saheeb yake ji ya nuna tsanar Ƴar uwarsa a fili, Rabi kuwa babu abinda ya shalleta bata ma san me ake ciki ba, surutunta take ita kaɗai, tana tambaye-tambayen ta, Saheeb kuwa zazzaɓine ya rufe shi sosai, amma miskilanci ya hana yayi magana, Zuciyarsa  sai zafi take masa, muryar Rabi da yake jiyowa tana magana ji yake kamar ana caccaka masa mashi a ƙirjinsa, ya tsaneta tsanar da bai taɓa tunanin zaiyiwa wani ita ba balle Ƴar uwarsa ta jini, ace wai shine aka aurawa Ƴar ƙauye, Mahaukaciya, bagidajiya, ƙazama, a matsayinsa na Matan turawa suna rububinsa bai sosu ba balle wannan villeger girl ɗin, to taya ma zaiyi zaman aure da wannan abar?, "wallahi su da suka ɗaura auren sai dai su zauna da ita badai ni ba", ya faɗa a ransa.




Ana cikin wannan hararramin Rabi ta kalli fuskar Kausar ta ce "Adda Kausar dan Allah ara min wayarki nayi game, wallahi daɗi ne da game ɗin", haushi da takaici ne ya kama Kausar bata san sanda tace "wallahi bazan baki ba banida chaji", "to ki bawa kawu driver yasa miki mana, naga anan kike sawa sanda zamu zo", "eh bazan sa ba yanzu", Kausar ta bawa Rabi amsa a hassale, turo baki Rabi tayi, sannan tayi shuru.




Baba da Daddy da suke zaune kusa da juna ne suke magan iya su kaɗai babu mai ji, na kasa kunne banji komai ba, sanadiyyar haka yasa na koma boot ɗin motar na kwanta dan babu inda zan zauna.




Saida suka zo inda su Inna zasu sauka, sannan sukaiwa juna sallama, Mammy ce ta raɗawa Inna wani abu, murmushi Inna tayi, saida suka ga tafiyar su Inna sannan suka hau mota suka wuce, Saheeb baisan tafiyarsu Inna ba dan wani wahalallen baccin ne ya kama shi, za'a tashe shi Inna ta hana, Rabi sai tsallen murna take ta dawo gida, suna isa gida sallah sukai dan magrima harta wuce, isha tana yi bayan sunyi suka kwanta dan huce gajiya.





Sai bayan isha su Daddy suka isa gida, suma sallah sukai daƙyar suka tsaya suka ci abinci, suka kwanta, amma banda Saheeb dan baici komai ba, ciwan kai yake fama da shi da zazzaɓi, sallah kawai yayi, duk sanda ya tuna anɗaura masa aure sai ransa ya ɓaci, a haka bacci ya ɗauke shi.






Hafiz da gaba ɗaya ya ƙwaɗaitu da Nawwara duk sanda ya tuna da yadda ya jita sai yaji shaɗan yana ƙara ƙawata masa ita, a wannan dare yaso ya koma mata sai bacci ɓarawo ya kwashe shi.





WANNAN KENAN




*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*




*By Rumyn Royal*




09130984617





*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 39-40*

>>>>>>>>>>>>>Washe garin dawowar su Saheeb ya tashi da matsanancin ciwan kai da zazzafan zazzaɓi, daƙyar ya iya rarrafawa ya faɗa toilet yayi wanka da ruwan ɗumi, fitowa yayi jiri sai ɗibansa yake dan sai yanzu ne yaji wata muguwar yunwa na ɗawainiya da shi, ƙoƙarin shirya kansa yayi cikin riga da wando ƴan kanti masu kauri dan sanyi yake ji, fita yayi dan zuwa gaida Mammy da Daddy.







Mammy kuwa bayan ta tashi ita da Nawwara kitchen suka shiga dan haɗa breakfast, Nawwara da tin jiya magana take cinta ta kalli Mammy ta ce "Mammy yanzu da gaske Rabi aka aurawa Hamma, gaskiya ba ayi masa adalci ba, ki duba Hamma fa ki duba Rabi ni wallahi an tau....", "dalla sha sha sha yi min shuru, wato kema akwai banzan tunani a ƙwaƙwalwar ki ko, to ki kiyaye ni wallahi, karki ƙara kawo min wannan zancen, kima sa a ranki Rabi matar Saheeb ce, kuma shima dole ya haƙura ya sawa zuciyarsa cewar Rabi matarsa ce, mene ne da Rabin?, saboda ta taso a ƙauye?, ko dan kun taso cikin daula ita ta taso ba a cikin daula ba?, to duk wanda ya ce zai adawa da wannan auren wallahi zansa wando ƙafa ɗaya da shi, aikin banza kai", cewar Mammy da ranta ya ɓaci sosai, dan ita bata ga aibun Rabi ba ko kaɗan.





Nawwara da jikinta yayi sanyi ga kuma ran Mammy ya ɓaci, ta tsani abinda zaisa ta ɓayawa mahaifiyar ta rai cikin muryar da tayi nadama ta ce "Mammy kiyi haƙuri in sha Allah bazan kuma magana akan haka ba, ki yafe min Mammy dan Allah", ta faɗa muryarta na rawa, Mammy ta ce "haka nake son ji, Rabi Ƴar uwarku ce ta jini, dan haka ku sota kamar yadda zaku so junan ku, kuma Rabi in sha Allahu Alkhairi ce a tare da mu", Mammy ta faɗa, Nawwara ya jinjina kai alamun gamsuwa.






*Bauchi*


Da safe suna zaune gaba ɗayan su a tsakar gida, Rabi na gefe tana wasannin ta, Hamma Abdul ne ya kalli Baba ya ce "Baba anya kuwa kunyi duba na tsanake kuka haɗa auren Rabi da Saheeb?, nifa na hango tsanar da yayiwa Rabi a cikin idanunsa, tinda har ya rufe ido a gaban ku ya nuna baya son Rabi, ya kamata kuyi nazari sosai", Baba da ya gama jin batun Abdul ya ce "kai Abdul yanzu mu munada zarrar da Harɗo zai yanke hukunci mu kuma muce bai mana ba, bamu isa ba, wannan ba tarbiyar gidan mu bace, shi Harɗo shi yasan mai yasa ya haɗa auren Rabi da Saheeb, mudai fatan mu Allah ya dai-daita su wata rana sai labari, dan haka ka cire wani tunani a ranka, nan gaba komai zai wuce", alamar gamsuwa Abdul ya nuna, sai dai yana ganin Rabi tayi ƙanƙanta da aure, dan dai kawai ba yadda zaiyi ne amma daya hana hakan, kallon Rabi yayi yaga ita bama tasan me yake faruwa ba, murmushi yayi ganin wasan ƴartsanar  kara take sai surutunta take alamu ya nuna ma wanka zatayiwa Babyn karar, sai faɗi ta ke "kiyi shuru ina miki wanka zaki samu kiyi bacci, kuma goya ki zanyi kinji".




 Inna kuwa bata tofa tata ba shuru tayi, dan inda sabo sun saba da irin wannan auren na haɗi a Rugar su.






*Hamma Saheeb*



Yana fitowa yaga babu kowa a falon, motsi yaji a kitchen ya nufi wajen, dauriya kawai yake dan kansa kamar ya tsage, Mammy ya gani da Nawwara suna ta aiki, sallama yayi Mammy ta waigo tare da amsawa, tana kallonsa ta san baya jin daɗi, sai dai ta sa a ranta saita nuna masa ɓacin ranta akan abinda yayi na nuna baya ƙaunar Rabi a idanun Iyayenta, 


"Hamma ina kwana?", cewar Nawwara, hannu ya ɗaga mata alamar amsawa, fita tayi da wata kula, "Mammy barka da asuba", amsa masa tayi babu yabo babu fallasa taci gaba da aikinta, tsugunawa yayi a gabanta, ganin yadda ta amsa masa yasan fushi take da shi, "Mammy dan Allah ki yafe min, wallahi bansan sanda na furta hakan ba, kiyi haƙuri, Mammy wallahi bana jinta cikin raina, Yarinyar ko gaishe ni bata yi, har hararata take a matsayina na Yayanta, gashi batada nutsuwa, ga fitina da tsokanar tsiya, gashi tayi ƙanƙanta da aure Mammy, amma kawai Harɗo zai yanke hukunci ba tare da ya tintiɓeni....", "abinda kazo kacemin kenan?, idan ka gama zan wuce", cewar Mammy, hankalin Saheeb ne ya ƙara tashi, ganin Mammy bata taɓa fushi da shi ba irin haka,


 "Mammy kiyi haƙuri dan Allah wa nake da shi bayan ke da zan gayawa matsalolina, wallahi na kasa jurewa ne Mammy", ya faɗa idanunsa na kawo ruwa, abinka da uwa, nan take tausayinsa ya kamata, amma kuma ba zata ɗaure masa gindin yaƙi yiwa Mahaifansa biyayya ba, cikin taushin murya ta ɗago shi, ta dafa shoulder ɗinsa ta ce "Saheeb kowa da ƙaddararsa, wannan ƙaddarar ita Allah ya haɗaka da ita dan ka cinye ta ba tare da kayi gaddama ba, Saheeb Harɗo Uban mu ne, kuma kaima kasan biyayya ga Iyaye tana sawa a gama da duniya lafiya, yanzu kenan kana so Daddynka ya nunawa Harɗo bai isa da shi ba?, kana so yayiwa Mahifinsa gardama?, to kamar yadda kake son mu kake so ka faranta mana haka Mahaifinka yake so yayiwa nasa Mahaifin, dan haka auren Rabi da kai wani muƙaddari ne daga rabbil izzati, bamu zata ba bamu taɓa kawo hakan ba, amma sai gashi Allah ubangiji ya halatta, dan Allah Saheeb karka sake Mahaifinka yayi fushi dakai akan haka, ka daure wata rana zakai farin ciki da Rabi, kuma kace bata girmama ka, Rabi Yarinya ce ƙarama kuma tana da biyayya, ina tunanin tsoranka take ji, tinda baka fara'a Saheeb, saika ɗaure fuska taya zata iya fuskantar ka?, dan Allah kadena haka bana so, kuma kaje ka bawa Mahaifinka haƙuri kaji", Mammy ta faɗa cikin rarrashin Ɗan nata, amsa mata yayi, amma cikin zuciyarsa baya jin zai iya rayuwa da Rabi a matsayin matarsa, never.




 Nawwara ce ta dawo dan ɗaukar ragowar kulolin breakfast ɗin da suka kammala, Mammy kuwa saida taga Saheeb na murmushi sannan suka fita.





Uwa da ɗa sai Allah.



Hamma Saheeb saida ya je ya bawa Mahaifinsa haƙuri, shima Daddy ya masa nasiha sosai, amma fa zuciyarsa bata jin zai zauna da Rabi, amsa musu kawai yake dan a zauna lafiya, Ƙasar ma yake shirin bari gaba ɗaya dan Business ɗinsa na  Motoci, Enginer na wanki, da duk wani kayan wuta har da gidaje to Hamma Saheeb yana Business ɗinsa, dan dama shi Business adminstration ya karanta, sosai yake samun kuɗi da Business ɗinsa na ƙasa da ƙasa, to wannan abu daya faru sai yaji yana da buƙatar komawa Ukrain dan cigaba da harkokinsa.







Tsalaha ne da Alhaji Nura tafe a cikin motar Alhaji Nura, "yawwa idan muka je karka tsorata kuma duk abinda aka ce kayi kayi shi, banda musu", cewar Alhaji Nura,



"ai karka damu Alhaji ni nan babu abinda yake bani tsoro sai ikon Allah", cewar Tsalaha, murmushi Alhaji Nura yayi suka cigaba da tafiya, sunyi tafiya mai nisa sannan suka karyaka wata kwana, daji ne dan duhuwa ce a wajen, parka motar yayi suka fito, daga nan sukaita tafiya har suka iso wani fili, sai wani gida wanda shi kaɗai ne a wajen, kamar yadda Alhaji Nura yayi wancen karon, haka wannan karon ma, jikin Tsalaha sai rawa yake, ganin wasu shirga-shirgan mutane sanye da jan kaya, idanunsu zagaye da baƙi, hannunsa Alhaji Nura ya riƙe, suka shiga wani ɗaki, anan suka cire kayansu timbir Tsalaha sai kakkare jikinsa yake, haka dai ya sa kayan suka fito, ɗakin da suke aiwatar da shirkar su suka nufa, suna shiga idon Tsalaha ya sauka akan Tsohuwa Kalalatu aikuwa zai koma yaji an daka masa tsawa mai firgitarwa, fitsari ne ya kece masa nan take ya fara yinsa, "duk wanda ya shigo baya fita ya shigo kenan", cewar Tsohuwa Kalalatu, jin haka Tsalaha ya rushe da kuka , tsawar da tafi ta da aka kwantsama masa ba shiri ya haɗiye kukan, Tsohuwa Kalalatu ce ta ɗaga wata sanda dake hannunta ta nuna Tsalaha da ita nan take wani baƙin abu ta shige jikin Tsalaha, ba shiri ya nutsu yayi kamar dama can ya saba zuwa wajen, cikin murya mara daɗi Tsohuwa Kalalatu ta fara magana kamar haka "mun samu cigaba da yawa ta dalilin ka Autan dodanya, dan haka mun ƙara maka girma, Dodanya ta ƙara maka girma dalilin jinin daka shayar da ita", wanda aka ƙira da Autan Dodanya ne ya sunkuyar da kai alamun girmamawa, sai kuma Kalalatu ta kalli Tsalaha ta ce "kai kuma nasan komai game dakai, ka shigo ƙungiya kuma bakai ba fita, idan har kayi ƙoƙarin fita to zaka haukace kabi bola, daga ƙarshe zamu shanye jininka, da farko idan ka shigo ƙungiya zakai sadaukarwa, ba komai Dodanya take buƙata ba sai Ɗanka Adahama, dan haka muna buƙatar ka kawo mana shi a zama na gaba", hankalin Tsalaha idan yayi dubu ta tashi, yanzu ɗansa wanda shi kaɗai ya mallaka shi zai bayar, daga haka aka tashi daga meeting kowa ya fice, Autan dodanya da kullum fuskarsa take a rufe da facemask ne ya kallai Alhaji Nura ya ce "ka same ni a office", amsa masa yayi, Tsalaha kuwa tsabar ruɗewa ya kasa magana, sai da suka hau mota sun fara tafiya ya fashe da kuka, Alhaji Nura ya ce "to Tsalaha maiya kawo kuka?," "gaskiya bazan bada ɗana ba, shine kaɗai na mallaka a rayuwata amma ace shi zan bayar, a tambayi wani abu mana, amma sai ɗana", murmushi Nura yayi ya  ce "aikuwa saika bayar tinda ka amsa, dan muma nan inda zaka san abinda muka bayar to kai da gudu zaka bada Ɗanka", "ta ina na amsa zan bayar, ni bance zan basu ɗana ba", cewar Tsalaha


"aikuwa ka amsa, kuma ko ka amsa ko karka amsa tinda ka shiga ƙungiya saika bada Adahama", Alhaji Nura ya faɗa, "ni wallahi ban amsa ba shuru nayi", "ai shurin da kayi shine yake nufin ka amince", hankalin Tsalaha ya tashi sosai, a haka Alhaji Nura ya sauke shi yayi nasa guri.✍️




Wannan kenan



*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*




*By Rumyn Royal Star*



09130984617






*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 41-42*

>>>>>>>>>>>>>>>> Alhaji Nura yana sauke shi ya nufi gida kamar zautacce sai tunanin yadda zai iya kai jinin Ɗansa Adahama yake, shi  kaɗai Allah ya bashi, anya zai iya cigaba da wannan harkar kuwa?, ya tambayi kansa, (Tsalaha kenan ka manta Yaran mutane kake kaiwa yau kuma dan ance ka kawo naka shine ka shiga tashin hankali, wato su waɗanda kuka sace nasu Yaran ba Ƴaƴa bane.)



A haka ya nufi gida duk wanda ya ganshi a hanya yayi masa magana baya sani saboda ya faɗa nannauyan tunani, da wannan tunanin ya shiga gidansa, Rakiya da take wanke tsakar gida wanda yasha tyles sai sheƙi yake, dan Rakiya badai tsafta ba, ganin Tsalaha ya shigo ko sallama babu ya nufi ɗakin sa hakan ya bata tabbacin akwai abinda ke damunsa, aikuwa ba shiri  ta bishi, jin ya shiga bayan gida yasa da dakata, ƙarar saukar gudawa taji dan akwai sauti sosai kasancewar gidan yasha gyara, yana fitowa yaga Rakiya a bakin Bayan gida tana jiransa "ke lafiya kike tsaye anan?", "ba lafiya ba naga ka shigo kamar wani abu ya faru, shi yasa na biyoka", cewar Rakiya,



"shine kuma kika zo nan kikai laɓaɓa dake kamar kayan shirgi, dan Allah ki saurara min ki dene....", bai ƙarasa ba jin yadda cikinsa ya murɗa, komawa yayi cikin banɗakin sai jin saukar zawo zuuuuuuu ƙyaaaaaa, komawa tayi taci gaba da aikinta, na taƙaice muku zance saida Tsalaha ya zawaye cikinsa   tsaf, sannan ya koma falonsa wanda yaji kujeru, sai nishi yake, zama yayi yana maida numfashi, Rakiya ce ta shigo tana faɗin "sannu suwiti (sweety), ko na jiƙa maka ararraɓi?", kallon jibgegen ɗuwawunta yayi, sannan ya tuno da sunan da ta ƙira shi da shi, tsaki yayi saboda takaici a ransa ya ce "ni wallahi dama matar nan aka ce na bawa Dodanya da ba haka ba, amma zance musu matata zan bayar", ƙara tsaki yayi a fili, ya ce  "kina jina Rakiya, dan Allah dan Rasulullahi (S.A.W) karki kuma ƙirana da wani suwuty, bana so bana muradi, ji nake kamar kina cakan wuƙa idan kika ƙira ni da wannan suna, ki ƙira ni da baban Adahama na da kika saba faɗa", ya faɗa yana maida numfashi dan gudawa da yayi tasa jikinsa duk babu ƙwari, "yanzu danna ƙira ka da sunan da naji Ƴan birni suna ƙiran mazajen su shine zaka ce ina damunka baka so, to in sha Allah bazan kuma faɗa maka ba, tinda kai ba ayi maka abin arziƙi", ta faɗa tare da tashi fuuuuuu ta fice,



Murmushi Tsalaha ya yi ya ce "to ai ba irinki ce ta dace da faɗar wannan suna ba, mata ƴan shawalwalai malam, sune ya dace su faɗa, ƙwarama na bawa Dodanya ke kona huta, kuma na samu zankaɗeɗiyar mata ƴar sha biyar ma aure wallahi".






**********************

Bayan wata ɗaya, abubuwa da yawa sun faru, ciki harda jarrabawar fita daga Primary da su Rabi sukai, hakan kuma yayi dai-dai da shigar Rabi shekara ta  goma sha uku da haihuwa, amma har yanzu ba a sanar mata tana da aure ba, sai dai an sanya ido a kanta sosai dan bata yawo, hakan kuma shi ya sanya Rabi ganin an takura mata, Kattume sai dai tazo gidan su Rabi, Rabi tayi kukan harta gaji, Hamma Abdul duk abinda take so yanayi mata shi, duk sanda ya fita saiya siyo mata wani abin, kuma yakan zauna suyi karatu dan ya ce dukda ta gama Primary zasu cigaba da karatu ta yadda ta shiga gaba da Primary ba zata sha wahala ba, kuma Rabi akwai ƙoƙari dan sosai Hamma Abdul yake tsayawa a kanta, zuwa yanzu har turanci tana ji kuma takan iya mayarwa amma ba sosai ba, Kattume ma tana zuwa suyi karatun da ita, itama babu laifi tana ja sosai.




Daddy sun yanke shawarar Rabi zata koma Kano kuma za a sanya ta a gaba da Primary wato Secondary, Hamma Saheeb kuwa shirye-shiryen barin Ƙasar yake, dan ya rantse saiya barta, amma ya nuna cewar wani aiki ne zai kaishi ya dawo, babu wanda ya fahimci abinda ya shirya.





Hafiz kuwa yana amfani da buguwar Nawwara ya kusance ta, yawancin kullum saiya kusanceta kamar Ɗan Akuya, ita kuma dake daƙiƙiya ce bata taɓa kula ba, Mom kanta bata kula da ɓarnar da take wanzuwa ba, sai murna take ganin Hafiz yana bawa Ƙanwar  sa kulawa, shi kuwa Dad ɗinsu har yanzu baya ƙasar balle ya kula da abinda yake faruwa, yana ta yin alƙawarin dawowa amma har yanzu shuru.





Yaya Talatu ce yau tayiwa gidan su Saheeb dirar mikiya ita da Nawwara, suna zaune a ɗakin Mammy, Yaya Talatu ta kalli Mammy ta ce "wai nikam ya muka kwana da zancen Yaran nan Nawwara da Saheeb?", "Yaya wallahi ina zuci-zucin na gayawa Saheeb ɗin mukai tafiya,  to kuma sai da muka je wani al'amari ya faru, kinsan lamarin Allah, Saheeb dai an bashi mata wallahi", cewar Mammy,



"kutmar ubancan, ban gane anyiwa Saheeb mata ba, me kike so kice min Nafisa?", cewar Yaya Talatu, "subhanallahi Yaya mene na ɗura ashar , ai ba abin tashin hankali bane", "a gurin ki ne ba abin tashin hankali ba, ni a gurina tashin hankali ne, kina kallo aka bashi mata kuma mata ma ta ƙauye, bayan kinsan munyi magana dake Nafisa, ai nikam na daɗe da sanin bakya ƙaunata balle ki so jini na, wallahi kin bani mamaki Nafisa!", "Yaya ki nutsu ki fahimce ni, Harɗo ne da kansa yayi wannan haɗi, kuma babu wanda ya isa ya ja da maganar sa", "ya ci bura ubansa shi Harɗon, tsinannan tsoho, babu ruwana da ba a ja da maganarsa ai ba ubana bane kuma ba ubanki bane, ke kodai dan kece kika haifi Saheeb kike min haka, to zan sa Nawwara ta haƙura  kuma kisa a ranki babu ni babu ke", tana kaiwa nan a maganarta a fusace ta ɗauki Jakarta da mayafinta ta saɓa ta fice tana ƙwalla ƙiran "Nawwara!!!! Nawwara!!!! fito mu tafi", Nawwara da taji ƙira kamar za a tsaga gidan ta fito, Kausar ma jin ƙiran bana lafiya bane tare suka fito, ganin Yaya Talatu tana numfarfashi kamar wadda tayi dambe yasa suka fahimci ba lafiya ba, jan hannun Nawwara Yaya Talatu tayi suka fice Nawwara  tambaya ta ke "Mom wai meya faru?", banza tayi da ita suka shige mota suka nufi gida.





Mammy kuwa zagin da Yaya Talatu tayiwa tsohon arziƙin taji haushi, Kausar ce ta shiga ta kalli Mammy ita ma ranta duk a ɓace ta ce "Mammy maiya faru?",   "babu komai Kausar tsakanin mu ne", cewar Mammy, ruwan sanyi Kausar ta zubowa Mammy ta bata ta sha, tana faɗin "Mammy kiyi haƙuri dan Allah", murmushi Mammy tayi ta ce "babu komai Kausar ya wuce, muje muyi aikin Lounch kar su Hamman ki su dawo bamu kammala ba", kitchen suka nufa.





Yaya Talatu kuwa sai numfarfashi take kamar kububuwa, Nawwara sai tambayarta take tayi masa shuru, har suka isa gida, a falo suka zauna sai a lokacin Yaya Talatu ta fara sababi  da murya maɗaukakiya "ni za a kawowa rainin hankali, to wallahi duk wanda  yaci tuwo da ni miya yasha", "Mom bana son haka fa why not mun tawo ina ta tambayar ki kina min fushi, na tsani haka Mom, ki gayan maine ya faru ?", cewar Nawwara cikin rashin ladabi.



"to mara kunya wanda kike haukan a kansa shine akaiwa aure, yanzu haka da auren wata a kansa", cewar Mom da ta faɗa a fusace kamar zata daki Nawwara, cikin kaɗuwa da tashin hankali Nawwara ta ce "what Mom!, you mean Saheeb ya auri wata?", what noncense are you talking Mom?", Mom ce ta miƙe ji kake tas ta kife Nawwara da mari, "dan Ubanki nice nake miki zancen banzan, ƙwara ma da haka ta faru, rashin biyayar ki ce ta janyo miki, sha sha sha mahaukaciyar Yarinya", tana gama faɗar haka ta wuce ta a fusace tayi side ɗinta ta barta dafe da kunci, 



"Mom nice kika mara?, wallahi sai kinyi dana sanin marina, saina nuna miki banida tarbiya Mom!!!, kuma saina kashe duk wadda Saheeb ya aura, saina mata kisan wulaƙanci wanda ko iya ganeta ba zasuyi ba, saina bada mamaki, sai anyi dana sanin haifata a wannan family ɗin!!!!", da ƙarfi take magana kamar wadda ta zare, Mom tana jinta tai banza da ita, fulallikan kujerun Nawwara taita wulli da su, ta ɗaga center table ta rotsa shi da ƙasa, sai ihu take tama faɗin "baka isa ba Saheeb kai ɗin nawa ne babu wadda zaka aura bayan ni, saina kashe ta wallahi bazan taɓa bari ka kusance ta ba!!!!", tana cikin wannan hali Hafiz ya shigo, ganin yadda tayi kaca-kaca da wajen tana ihu ya san ba lafiya ba, saurin zuwa yayi ya riƙo ta yana faɗin "kina hauka ne Nawwara, so kike kijiwa kanki ciwo?", kama hannunta yayi ya shigar da ita ɗakinta, giyar da ta saba sha ya ɗakko mata ya buɗe mata murfin ya bata batayi musu ba ta kafa kai saida ta shanye gaba ɗayan kwalbar sannan ta dire, cikin maye ta ce "sai na kashe su dukan su, bazan bar kowa ba, kuma Mom sai tasan ta mare ni, Ya Hafiz zaka taya ni na kashe su ko?", ta faɗa tana kallonsa, shi kuwa dama fatansa ta bugu, dan ya kwana biyu bai kusanceta ba, fara aiwatar da abinda yake so yayi, cikin fitar hayyaci take jin yadda yake wasa da ita, harta dena gane komai, yadda ya saba yana gamawa ya fice yana jin nishaɗi.





Allah ka tsare mu da haular Musulmai baki ɗaya ameen.






"Inna dan Allah yau ɗaya ki barni na fita, na miki alƙawari bazanyi komai ba", cewar Rabi




Inna data kalle ta ta watsar ta ce "ke wallahi ki kiyaye ni, tin safe kin ishe ni, da zan barki da tuni na barki ai", baki ta turo gaba a ranta tana faɗin wallahi yau saita fita, ilai kuwa Inna na shiga wanka ta fice ko takalmi babu, tana fita ko takan Kattume bata bi ba ta shiga gari, Hayin Diga ta nufa, wani waje ne da kafatanun ƴan shaye-shaye nan suke zama, wani ƙaton kango ne a wajen, tana tafe tana waƙoƙinta wanda ita ce ta tsara kayarta dan ni dai bana ce ga mawaƙin da ya raira ba, tazo dai-dai kango ta hango su reras suka busa wiwin su, ɗaga murya ta yi ta ce "Ƴan daba me kuke yi anan wajen?", jin zazzaƙar murya yasa suka kalli wajen, wani daga cikinsu ne ya ce "kai Ƙaura dubi tsuntsuwa daga sama gashashshiya, gata Ƴar shila wallahi", wanda aka ƙira Ƙaura ya kalli inda Baushe ya nuna masa, "kai Baushe wallahi dama na daɗe banji ɗumi ba maza ku cafko ta", aikuwa cikin dabara suka zagaye Rabi bata sani ba dan bayan ta tsokano su ta cigaba da tafiya, ganin maza a gabanta sun tarfa ta yasa ta tsorata, zata juya taga wasu, a taƙaice dai sun zagaye Rabi, caraf aka damƙota ta baya, Baushe ya ce "yau zamu sanar dake abinda ya tara mu anan Ƴar tsitaka", ihu ta fara ba shiri Baushe ya toshe mata baki, wutsil-wutsil take tana ƙoƙarin ƙwace kanta amma ina, can cikin kangon sukai da ita, suna zuwa suka sauke ta gaban  Ƙaura da alama shine Ogan su, "ku toshe mata baki, kuma ku ɗaure hannunta", haka kuwa sukai, ihu take ta ciki dan muryarta bata fita, Inna take ƙira da Hamma Abdul da kuma Baba, amma ina basu kusa, tittirza ƙafarta take tana ƙoƙarin kwance hannunta da suka ɗaure ta baya amma inaa ɗaurin gagam sukai mata, rigar jikinta yake son yagawa amma ya kasa ba ƙarfi a jikinsa dalilin a buge yake, su kuwa sauran sun juya baya suna jiran oga ya kammala su suɗe ragowar, ɗaga rigarta yayi ya cire mata wando, mazagin wandon sa ya cire ya......✍️




Wayyo Rabi ki ɗakko ruwan dahuwar kanki.


Wannan kenan



*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*




*By Rumyn Royal Star*




09130984617




*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Ku yawaita faɗar HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKEEL ko sah ɗari ne a rana, yana tsare mutun daga sharrin duk wani abin ƙi, Allah ya tsare kullu muslim*



*Page 43-44*

>>>>>>>>>>>>>>>Hamma Abdul ne zaune shida Abokinsa Kamilu suna hira, haka kurum yake jin gabansa yana faɗuwa, jikinsa duk yayi sanyi, lura da hakan da Kamilu yayi ya ce "Abdul ƙalau kake kuwa?", Abdul daya nisa ya ce "babu komai kawai haka kurum naji gabana na faɗuwa bari na koma gida", Allah ya sawwaƙe Kamilu ya ce, ya tashi dan raka Abdul, tafe suke Kamilu sai hira yake masa amma daga eh sai uhm.





Rabi ta gigice ganin ƙaton gardi ya cire wando a gabanta, rintse idanuwanta tayi, ta jigata dan fizge-fizgen da take duk yasa ta jigata, ɗaga rigarta yayi zai shigeta ta ƙarfi, aikuwa cikin hukuncin ubangiji tsumman da suka ɗaure mata baki ya goce daga bakinta, cikin karaji da tashin hankali ta kurma ihun da saida ilahirin Kangon ya amsa, "wayyo Hamma na kazo ka cece ni zasu yanka ni, wayyo Inna ta bazan kuma yi miki musu ba, dan Allah kizo ki cece ni zasu yanka ni", wannan ihu da Rabi tayi na farko har cikin kunnen Hamma Abdul da suka doso Kangon shi da Kamilu, "Kamilu kaji ihun da nake ji kuwa?", Kamilu ya ce "ƙwarai kuwa kuma na mace ne", waige-waige suke, cikin ikon Allah Abdul ya kuma jin sunan Hamma a cikin kunnen sa da Rabi ta ƙira, a firgice ya ce "Kamilu kamar Rabi naji tana ƙwallan ƙira", ai bai tsaya wani jan lokaci ba ya bi inda yaji sautin a guje, Kamilu ma ya bishi.





Rabi fa ta gagari Baushe, ƙoƙarin shigarta yake sai hankaɗa shi take da ƙafafuwanta, tana ƙara kurma ihu, "ke dan me cin.... ki tsaya kona daddatsa ki wallahi, kaga ƙaramar Kucciya da Ƙarfin zaki", cewar Baushe da ya fara gajiya dan a bige yake, su Ƙaura da suke jira har sun gaji, Ƙaura ne ya ce "haba Oga Baushe wai wannan abar ce zata gagare ka, wallahi da nine da tini wani zancen ake ba wannan ba, amma ka tsaya kana wani lallaɓata, kayi mata shigar burtu kawai ko a mutu ko ayi rai", ya faɗa da muryar sa ta ƴan wiwi.




Mari Baushe ya kwaɗawa Rabi bakinta da hancinta nan take suka fara zubar jini, wani Ihun ta kurma tana ƙiran sunan Hamma Abdul a gigice, ai kuwa dama su Abdul da Kamilu sun kawo wajen, cikin zafin nama Abdul ya haura cikin Kangon, aikuwa su Ƙaura tuni suka ruga tunaninsu kwalawa ne (Police), Baushe kuwa hankalinsa ya tafi zuwa ga farka Rabi dan ko motsin gudun baiji ba, ji yayi an wurgar dashi kansa ya bugu da wani bulo, dawo wa hayyacinsa yayi ganin mutum a kansa kamar Zakin daya fito farauta, baya yayi yana shirin zaro wuƙa, Abdul ya bishi da naushi kota ina ball yake da Baushe, Baushe tin yana ƙoƙarin mayar da martani har ya haƙura,  Abdul kuwa gaba ɗaya baya cikin hayyacinsa naushi ta hannu da ƙafa yake kaiwa Baushe, ganin Baushe ya dena motsi Kamilu ya zo ya riƙe Hamma Abdul yana faɗin "karka kashe shi Abdul ka bari hukuma tayi aiki a kansa, muji da Rabi yanzu", sai sannan Abdul ya tuna Rabi a haukace ya juyo gare ta, jijjiga ta yake yana faɗin "Rabi! Rabi!!", tashi nine, ki tashi Rabi", hankalinsa gaba ɗaya ya tashi hawaye yake baisan yana zuba ba, 




Kamilu waya ya ciro ya ƙira Police dan tafiya da Baushe, aikuwa suna zuwa suka wuce da shi, shi kuwa Abdul baibi takan Police ba yayi Asibiti da ita, gaba ɗaya ya fita hayyacinsa, fatansa Allah yasa basu cutar masa da ita ba, suna zuwa aka ɗauketa, nan aka shiga nemo numfashin ta, cikin ikon Allah ta dawo dan dama firgici ne da tsoro ya sa ta suma, duba ta sukai suka ga babu abinda ya faru dan Baushe bai samu damar shigarta ba sai dai tajijji ciwo sanadiyyar bige-bigen da tayi, treatment sukai mata, 






Suna fitowa Kamilu daya biyo Abdul da shi kansa Abdul ɗin sukai kan  Likita, nan ya sanar dasu babu abinda ya faru da  ita, kawai firgici ne ya sanya ta suma, nan take suka gode Allah, ɗakin suka shiga inda aka kwantar da Rabi, aikuwa tana haɗa ido da Hamma Abdul ta rushe da kuka, rumgume ta yayi yana rarrashi, cikin dashashahiyar murya da tasha artabu ta ce "Hamma bansan me nayi musu ba zasu yankani, Hamma bazan kuma fita ba Allah kuwa, dama saida Inna tace karna fita na fito bata sani ba, Hamma kaini gida naga Inna ta", tausayi ta bashi, Kamilu ne yayi murmushi ganin cewar ita bata ma san abinda akai niyyar mata ba, tunaninta yankata za ayi,



 sallamarsu akai aka rubuta magungunan da zata sha ciwukan jikinta ya warke, suna fitowa ya sayi maganin sannan yasai mata lemo da ayaba, Kamilu kuma gida ya koma, a hanya Abdul ya kalli Rabi da tayi lamo a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya ya ce "Boɗɗo", "Uhm" ta amsa, "karki soma gayawa su Inna wannan abin daya faru kinji, sa bo da kinga ba a so a dinga ɗagawa Iyaye hankali hakan babu kyau, sannan kinga illar ƙin bin maganar Iyaye ko?", kai ta gyaɗa, ya cigaba da cewa "to yanzu basai an gaya miki ba kin gani da idonki, yanzu daba dan Allah ya kawo ni ba Rabi me kike tunanin zai faru dake?, to daga yau ko soro karna kuma ganin ƙafarki idan ba haka ba wallahi sai ranki ya ɓaci, kuma saina sa an yanka ki", aikuwa cikin sauri ta ce "wallahi Hamma bazan kuma ba, kuma bazan ƙara ƙin jin maganar Inna ba", "yawwa Boɗɗon Inna da Baba da Hamman ta, idan muka je kiyi shuru ni zanyi magana kinji", amsa mata tayi daka, da wannan suka ƙarasa gida, suna shiga Inna ta nufo Rabi da niyyar duka Hamma Abdul ya ɓoye ta a bayansa, Inna cikin fusata ta ce "wallahi ka matsa kona haɗa dakai, ace Yarinya bakya jin magana, ban isa na saki kona  hana ki ba sai kinyi,  haba wannan wane kalar zamani muke ciki", ta faɗa tana tafa hannu tare da riƙe haɓa, Hamma Abdul cikin tattausan kalami ya ce "Inna kiyi haƙuri duk abinda yayi farko zaiyi ƙarshe, har yanzu Rabi Yarinya ce, wata rana ba zatayi ba ko ance tayi, dan Allah kiyi haƙuri Allah ya huci zuciyar ki, kuma tana fita muka haɗu, muna tafe tsautsayi ya faru ta faɗi ta kurje a ƙafarta", ya faɗa yana jawo ta daga bayansa, nan take kuma hankalin Inna ya tashi ganin Rabi tayi muzu-muzu ga ido ya kumbura fuska tayi ja, "subhanallahi garin yaya haka ta faru?", ta faɗa tana ƙara  kallon Rabi, Rabi dai babu uhm babu uhm uhm, Hamma Abdul ya ce "mun tawo zamu sha kwana ashe mashin ya karyo kwana cikin tsautsayi siya bige ta", "ashasha Allah ya kiyaye gaba, sannu kinji saida nace karki fita amma dake kunnen ƙashi gare ki kika fice, Allah ma ya taƙaita, amma wannan kumburin na fuskar ki kamar an mare ki fa?", ta faɗa tana jujjuya fuskar Rabi, Hamma ji yayi ƙarya ta ƙare dan dama shi ba ma'abocin yin ƙaryar bane, ita dai Inna taji su ne kawai amma tasan tsokana Rabi tayi, danga shatin yatsu nan a fuskar ta, shuru tayi, ruwan zafi ta juye mata ta ce taje tayi wanka.





Tinda wannan abu ya faru Rabi ta dena fita, ko sha'awar fita batayi, rai da rai tana gida, tafiyar ta Kano sai ƙaratowa take, Inna da Hamma Abdul ne zasu kaita, sai murna take Inna kuwa duk ta damu dan zata yi kewar Rabi, ga shi zama ne in ta tafi ta tafi kenan, wata ran haka kurum zataita share ƙwalla tana ta so Rabi tayi aure a kusa da ita, amma Allah ba haka ya tsara ba, kullum addu'a Inna take shararawa auren nan tare da fatan alkhairi a zamansu, Hamma Abdul kuwa ya koyawa Rabi azkhar na safiya da maraice, ta haddace gaba ɗaya a kanta, Ahalari, ƙawa'idi, su kansu saida Hamma Abdul ya koyar da Rabi, Alƙur'ani kuwa Rabi ta sauke shi, izu talatin kuma ta haddace.





Akwai wasu saiwoyi da Innawuro ta bawa Inna ta ce ta yawaita dafawa da jar kanwa tana baiwa Rabi, to shine tinda suka dawo Inna take bawa Rabi tana sha, tin bata so har ta dawo tana ɗiba da kanta tana sha.






*Kano*


Saheeb zaune gaban su Daddy da Mammy ya sunkuyar da kai da alama magana suke mai muhimmanci, Daddy ne ya nisa ya ce "kana sane da cewa nan da kwana uku matarka zata dawo nan gidan da zama, kuma kasan zuwa yanzu duk wata ɗawainiyar ta akan ka take, dan haka ina so kasan cewar Rabi'a Ƴata ce kuma ina ji da ita a cikin raina, dan yadda nake son Mahaifiyar ta haka nake sonta, dan haka ruwanka ne ka riƙe ta amana ruwanka ne kayi biris da ita, idan har ka cutar da ita Saheeb ni ka cutar, dan haka ya rage naka, kuma ina so ka bada kuɗi ayi mata siyayyar kayan sawa da kayan amfaninsu na mata, basai tazo a fara tiri-tirin zuwa a siyo ba, sannan za'a sanya ta a School wannan ma nauyin a wuyanka yake dan ko babu aure Rabi'a Ƙanwarka ce, dan haka ka kula sosai", Saheeb da zuciyarsa take suya jin an danganta shi da Rabi matarsa sai yaji ina ma mafarki yake, bawai dan ance yayi mata hidima bane a'a kawai ya tsani a ƙira ta matarsa, "kayi shuru?", cewar Mammy, "In sha Allah bazai gagara ba, zan bawa Kausar ATM ɗina taje tayi mata siyayyar, kuma in sha Allah zaku same ni da yi muku biyayya", cewar Saheeb da duk abinda ya faɗa iya bakinsa ne,"masha Allahu, Allah yayi maka albarka", da ameen Mammy ta amsa, "zan iya tafiya Daddy?", "eh jeka dama shikenan, kuma dama ina so na tambaye ka ya tafiyar taka kuwa?", "yess Daddy nan da two weak zan tafi", "to masha Allah, Allah ya kaimu".


Sallama yayi musu ya fice dan zuwa wajen Abokinsa Samir.





Motarsa ya shiga ya kunna, mai gadi ya buɗe masa gate yana masa fatan dawowa lafiya, direct Sabon titin mandawari ya nufa, dai-dai unguwar Hausawa ya parka motarsa, bai fito ba ya dannawa Samir ƙira, yana ɗauka ya ce "miskili kafi mahaukaci ban haushi, ya ake ciki ne?", cewar Samir, "dalla ka fito gani a ƙofar gidan ku, ina mota bazan fito ba mutane sunyi yawa a area ga hayaniya", dariya Samir yayi ya ce "Allah ya baka mace mai shegen surutu muga yadda zakai, gani nan fitowa", kashe ƙiran yayi, daga wani madai-daicin gida Samir ya fito, shima ba laifi kyakykyawa ne da iya wanka masha Allah, motar ya gano ya nufo ta, yana zuwa ya shige, Saheeb baiyi magana ba ya kunna mota suka fita, tinda suka fara tafiya baice komai ba, Samir daya gaji ya ce "kai malam kasan dai ni bakina baya shuru, taya zaka yi min shuru, wallahi saika sauke ni nayi nawa waje babu lallai babu dole", "hmmmm kanada matsala Samir, Gusto nake so muje", cewar Saheeb, "kai kamar damuwa kake ciki Saheeb?", Samir ya faɗa cikin kulawa,




Murmushi Saheeb ya yi ya ce "damuwa kuma?, ka gani a fuskana?, badai wannan fuskar ba", ya faɗa yana murmushi wanda yake sanya dimpul ɗinsa yake lotsawa, shuru Samir yayi dan yasan ko zai ɗige Saheeb bazai gaya masa abinda yake damunsa ba, haka Allah ya yishi ba'a taɓa gane halinda yake ciki, 




Gusto suka shiga, wajen babu hayaniya, sai daddaɗan sauti ke tashi wanda babu tashin hankali a ciki, manyan Yara sai shiga suke da Babies ɗin su, anan suka samu waje suka zauna, Samir ne kawai ya buƙaci Abinci, Saheeb kuwa ruwa kawai aka kawo masa, Samir yana kai loma ya hango wasu tsala-tsalan Ƴan mata ya ce "kai guy ana bura uba a Kano, wato idan kana so kaga mace iya mace saika koyi zuwa nan", tsaki Saheeb ya yi ya ce "kace dai idan kana son ganin tsagerun mata mara sa aji kazo nan, macen arziƙi indai bada mijinta zata zoba ba amfanin a ganta a wannan wajen, mace mai kunga tana gida tana taya Maman ta aiki", ya faɗa ya basar kamar bashi yayi magana ba, jinjina kai Samir yayi dan ya gamsuwa da zancen Abokin nasa, sun jima a nan saida magriba ta kawo kai suka bar wajen.





***********************

Kwanci tashi aka ce asarar mai rai, yau ne su Rabi za'ai bankwana da garin Bauchi, gidan su Kattume kawai ta shiga dan sanar mata ta tafi birni, "Sallamu alaikum", Rabi fa ƙwalla da ƙarfi, Kattume dake wankewa Kaka kwanika ta amsawa ƙawar tata " ke dalla birni zan tafi ni dasu Inna da Hamma, kuma zamu daɗe a can", nan take idin Kattume ya fara tara ƙwalla, Kaka dake jinsu ta ce "kice zamuyi kewa Rabi, Allah ya tsare kinji ya dawo daku lafiya", "Ameen Kaka", cewar Rabi tana  ta zumuɗi ko kula da ƙwallar idon ƙawarta bata yi ba, Kattume ta share hawayen daya zubo mata ta ce "yanzu shikenan mun dena ganin juna Rabi, ke kaɗai nake wasa da ita, kinga idan kika tafi shikenan", tana kaiwa nan ta fashe da kuka, dan sosai suka shaƙu da juna, jikin Rabi ne yayi sanyi nan take ita ma ta fara hawayen cikin kuka ta ce "ke ki dena kuka zan dawo kuma zan siyo miki kayan birni na tawo miki da shi kinji, amma sai kin min alƙawarin ba zaki ƙara kuka ba", cikin sauri Kattume ta share hawayenta ta ce "kinga na share bazan kuma yi ba", Rabi ma nata hawayen ta share ta ce "yawwa nima na dena zo ki raka ni kiga tafiya ta", hannunta taja suka fice, Kaka dake tsaye tana ganin abinda yake faruwa ita ma saida ta share hawaye dan Yaran sun bata tausayi.






Suna fita sukai gidan su Rabi, Inna da Hamma Abdul sun kimtsa ga mai mota a waje waje yana jiran su, Baba ne yake ta musu Addu'ar sauka lafiya, jiya dama ya daɗe shi da Rabi yana mata nasiha, daga haka suka fita suka shiga Motar Kattume sai share hawaye take, Rabi kuwa sai murna take, Baba kansa saida ya share ƙwalla, saida suka bar ganin ƙurar motar su Baba ya rarrashi Kattume ta koma gida cike da kewar Aminiyar ta.






*Kuyi haƙuri da wannan banjin daɗi ne 👏*




Wannan kenan




*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*




*By Rumyn Royal Star*




09130984617





*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*one time the day will come unexpected, so we better to think before it come because this our life is not permanent, great day to u all ya Allah  keep us together me, peaple and also friends and families, ameen*







*Page 45-46*

>>>>>>>>>>>>>>Mutanen  Kano sai hada-hada suke na tarbar baƙin Bauchi wato su Inna, dake yau Lahadi hatta Daddy yana gida, shi kuma Hamma Saheeb yau da ƙunci ya  tashi, kasancewar zuwan wannan ƙazamar Yarinyar gidan su a matsayin matarsa, haka ya tsallake yabar gidan babu wanda ya kula, dan ƙarfe takwas kowa yana baccin bayan Asuba ya fice, sai da suka ji shuru suka duba side ɗinsa baya nan, tunani sukai ko wani abinne na ujila ya taso ya fita da wuri.





Girke-girke na musammam Mammy da Kausar suka haɗawa su Inna, sunyi wanka sun shirya jiran su kawai suke, Muhammad ma yana gida.





Matafiya kuwa sun sha hanya duk da babu nisa tsakanin Kano da Bauchi,  Hamma Abdul dake yasan gidan direct can aka nufa da su, har cikim gidan aka kaisu, jin alamun tsaiwar abin hawa su Daddy suka ji, cikin hanzari Mammy ta miƙe ita da Kausar, leƙawa Kausar tayi cikin nuna zallar farin cikinta ta ce "Daddy, Mammy su Inna sun iso, aikuwa Daddy da Muhammad tini suka miƙe suka fice har Mammy da Kausar dan tarar su, driver kuwa kayansu ya ciro musu, Kausar da ta rugo da ɗan gudunta ta rumgume Inna tana faɗin "oyoyo Innar mu, Hamma Abdul barka da zuwa Kano", murmushi yayi mata, tare da kanne mata ido ɗaya, saurin kawar da kanta tayi tana masa hararar wasa, Inna kuwa tsabar farin ciki ta kasa magana, dan rabonta da Kano ta manta, Daddy, Mammy da Muhammad da suka ƙaraso cikin farin ciki Mammy ta ce "barkan ku da zuwa, kun shawo hanya", Rabi da kuwa tini ta shige cikin gidan ba wanda ya kula, Muhammad wajen Abdul ya nufa sukai hugging juna cikin farin ciki, Daddy banda fara'a babu abinda yake, dan yana ta so Yayar tasa tazo taƙi sai yanzu, "ku ƙaraso daga ciki sai kuyu ta rumgumar junan a can", cewar Daddy da sai yanzu yayi magana, dariya suka sa, Shitu ma'aikacin gidan ne ya shigar musu da kayansu falo, Daddy ne ya bawa drivern daya kawo su Inna kuɗi masu yawa, aikuwa driver ji yayi kamar ya goya Daddy, haka yabar cikin gidan farin ciki kamar ya kashe shi.




Suna shiga aka baje a falo, sai lokacin su Daddy suke tambayar Rabi, Inna da sai yanzu ta kula babu Rabi babu dalilinta hankalinta yaɗan tashi, Hamma Abdul ne ya ce "ita ce farkon fitowa a mota fa, to ina tayi kuma?", "kodai Lambu ta nufa, dan zuwanku na ƙarshe kunsan nan ne wajen zuwanta, taita kaɗo Goba tana ci", sai a lokacin suka ɗan nutsu, Muhammad ne ya tashi dan zuwa ya duba, Inna ce ta ce "oh Rabi kenan, to ki fara hutawa mana, shine zata nufi can ita ko gajiya batayi", 



"Banda abin Adda ai jikinku ke gajiya yanzu, amma Rabi kam ƙarfi take ji", cewar Daddy,




"aikuwa dai ki barta tasha bidirinta", Mammy ta faɗa, Mai aikinsu ce ta zo ɗauke da kayan motsa baki, drinks gasu nan kala-kala.





Abinda basu sani ba shine Rabi tin a mota kashi ya matse ta, Allah-Allah take azo taje ta juye shi a mazubinshi, cikin ikon Allah tana zuwa idanta ya rufe ta nufi side ɗin da ita kanta bata san na waye ba, bata tsaya ɓata lokaci ba, ta shige toilet dama masan nasu yawanci na zama ne, tana shiga ta zauna ta fara nishi, idanunta sunyi bulu-bulu, sai gumi take dan da alama kashin irin mai taurin nan ne, dan harda daddafa gefe da gefen masan, ta jima sannan tayi wawiyar ajiyar zuciya, sai kuma a lokacin ta fara kaɗe ɗoyin, dan ita kanta yayi mata ɗoyi balle ni dana tsaya ina lissafo muku halin da  ta shiga, tsarki tayi, sannan tayi duban duniyar nan na inda  zata murɗa tayi floshing ɗinsa, ta kasa, sai dube-dube take bata gani ba, kawai saita wanke hannunta da fuskara ta fuce tare da addu'ar fita daga toilet ɗin,(Gufra nak), sai kuma ta ce "wannan masan bansan ta ina zan murɗa kashin ya tafi ba, ba irinna su Adda Kausar bane, nasu ina murɗa shi kashin yake yafiya, shi kuma wannan bansan ya ake ba", ta faɗa tana ƙarewa ɗakin kallo, bed ɗin ne ya burgeta ta faɗa kai tana birgima, kamar an tsikare ta ta miƙe, ta nufi wajen da taga kayan sawa dake glass ne ana  ganin kayan ciki, yasa ta tsaya tana ƙirga kayan, "mtseww na gaji wallahi, wannan uban kaya kamar na mutum dubu", ta faɗa cikin gajiyawa da ƙirga kayan, sai da ta je har kan madubin ɗakin ta ɗau wannan ta duba ta ajiye ta ɗauki wani, har ta gaji, ta fice a falo ma saida ta kalli komai sannan ta fara ƙwalla ƙiran Inna "ina kuma wai suka tsaya basu shigo ba?", fita tayi tare da barin mayafin doguwar rigar da ta saka, ta fice dan ganin maiya hana su shigowa ciki.




 cikin gida kuwa sai duba Rabi ake dan hankali kowa ya tashi, dan Muhammad da bai ganta a gerden ba ya koma ya gaya musu, tini aka fara dube-dube, mai gadi suka tambaya ko ya ganta ta fita, ya ce baiga kowa ba, bayan fitar driver, hankalin Inna ya tashi har tana cewa "ko dai a motar muka barta ni Saratu, Allah dai yasa ba bacci tayi na barta a motar ba", Abdul kuwa ya san tabbas Rabi ta fito a mota, sai haƙuri ake bawa Inna, hankalin kowa a tashe yake, Mammy da Kausar har ɗakunan su suka duba basu ganta ba, hatta ɗakin Daddy da Muhammad saida aka duba, babu ita babu dalilinta, Mammy ce ta ce "bari dai na ƙara dubawa Lambun nan.






Rabi ta fito kanta ko hula babu dan dama ta wurgar da Mayafin kayan jikin ta a falo, tana fitowa ta hango bishiyar Goba ata baya, acan nesa da inda ta fito, nan ta nufa, tana zuwa Mammy tana kawo kai, sai ganin Rabi tayi kai ko ɗankwali babu zata hau bishiyar, "Rabi'a!  me kike anan ana ta neman ki?", washe baki tayi tana faɗin "laaa Mammy ina su Innar?", hannunta Mammy ta kamo tana sauke ajiyar zuciya ta ce "banda abinki Rabi'a kin tayarwa kowa hankali sai neman ki ake, ashe ke kina nan", Rabi ta ce "ai ni kuma jira nake su tawo nan ɗin", Mammy ta kalle ta ta ce "suzo lambun suyi me?", shuru Rabi tayi, Mammy suka hango riƙe da Rabi kai babu mayafi, ajiyar zuciya suka sauke, Abdul ne cikin hassala ya ce "ke! ina kika je dan iskanci ana ta neman ki?", Daddy ne ya katse shi da faɗin "kaga Abdul ƙyale ta, ku mai yasa bakwa iya tafiyar da Yara ne, ayi mata a hankal", Inna kam takaici ne yasa ta shiga cikin gidan ta barsu a nan, Daddy ne ya kamo hannun Rabi sukai ciki, suma sauran suka mara musu baya, bayan sun ci abinci, Inna ta tambayi Saheeb sai lokacin Daddy ya ciro waya ya ƙira shi, bugu biyu ya ɗauka "Saheeb duk abinda kake ka baro shi kazo gida yanzun nan", cewar Daddy, yana faɗar haka ya katse ƙiran, Inna ta ce "haba Rabi'u kace duk abinda yake ya bari, idan yana abu mai muhimmanci fa?", Daddy yayi murmushu ya ce "ai nasan bazai wuce gidan su Abokinsa yake ba", "amma daka bari ya dawo duk sanda ya kammala abinda yake, zai dawo gida", cewar Inna.





Rabi da tinda suka ci Abinci ta shige ɗakin Kausar sai sata magana take, daga ƙarshe tasa ta taje tayo wanka, ta bata ɗaya daga cikin kayan da Daddy yasa  Hamma Saheeb ya bada kuɗin suka siyo tasa, riga da wando ne masu kyau, kamar Pakistan suke dan rigar har ƙasan gwiwar Rabi, gashin ta Kausar ta tufke mata wanda Inna ta wanke mata shi tas da shampoo irin nanan gida Nigeria, wanda mata suke koya su iya su samu abin siyarsa su rufawa kansu asiri, gashin kuwa mai tsawo da yawa, ga santsi da laushi, har gaban goshinta yake, Kausar ta ce "Rabi gashin ki abin sha'awa dama nayo gashin Inna dana caɓa", "Adda Kausar ciri nawa ki sa a naki, wallahi bana son sa zafi idan Inna tana taje min, kuma taita cewa saina je kitso", ta faɗa tsakaninta da Allah, dariya ta bawa Kausar ita kuma ganin Kausar tana dariya ta cuno baki wai taji haushi.






Bayan Magriba Hamma Saheeb ya shigo lokacin gaba ɗayan familyn suna falo, da sallama ya shiga, cikin nuna farin cikin ganinsa Inna ta amsa cikin fara'a tare da cewa "sannunka da dawowa Yaron kirki, Allah yayi wa rayuwa albarka", da ameen ya amsa tare da zuwa kusa da ita ya zauna, hannun ya bawa Abdul suka cafke suna jin daɗin haɗuwa da juna,  cikin ladabi ya gaida Inna, ta amsa cikin kulawa, su Daddy da Mammy ya gaisar, Kausar da Muhammad suka gaida shi ya amsa, Rabi dake kusa da Mammy tana game a wayar Muhammad ko kallonsa batayi ba, kuma taga shigowarsa, shima baibi ta kanta ba, amma yaji haushin rashin gaisuwar da batayi masa ba alhalin tana gani ƙannansa suka gaida shi, kamar Inna tasan abinda yake tunani, cikin tsawa Inna ta ce "kee! Rabi baki ga Yayanki bane, kowa ya gaishe shi kina ji, kinsa sailula a gaba kina son lalata musu", jin abinda Inna tace yasa Rabi ɗagowa, karaf suka haɗa ido da Saheeb wanda kallon tsana yake auna mata, ita ma bata son sanda ta galla masa harara ba, aikuwa ji yayi dama ya kashe ta dan takaicin hararar da tayi masa, "ba magana nake miki ba Rabi?", cewar Inna da taga tanaiwa Rabi magana tayi shuru, ita kuwa ji take data gaishe shi ƙwara ta mutu, dan kuwa ba zata aikatawa Ubangijinta laifi ba, bata da zaɓi sai ji kawai akai ta fashe da kuka, kallo aka bita da shi, Daddy ne ya ce "dan Allah Adda ki barta haka nan, kinga kin sata kuka, indai gaisuwa ce ai suna tare zata dinga gaishe shi, yi shuru Ƴar lelen Daddynta", Mammy ce ta ce "tsakani ga Allah Adda taya zata iya gaishe shi ya haɗe girar sama data ƙasa, ko nice nayi shayin masa magana ai bare ita, yi shuru abinki", wannan abu daya faru Saheeb ji yayi zuciyarsa na masa zafi, wai akan wannan Yarinyar su Mammy suka masa haka, har ɗaurin gindi ta samu, da zasu kura idanunsa har ja sukai, Hamma Abdul ma ransa ya ɓaci, kuma ya lashi takobin saiya ci ƙaniyarta, saida sukai Dinner sannan suka koma falo aka cigaba da hira, Rabi kuwa ɗakin Kausar ta tafi ta  kwanta dan bata son ganin Arne.






Nawwara kuwa gaba take da Mom ko kallon ta bata yi, wai tayi fushi da ita, Mom ma bata ƙara bi ta kanta ba, Hafiz kuwa yanzu ya maida Nawwara kamar matarsa, zai taimaka mata ta bugu ta fice a hayyacinta shi kuma yayi amfani da ita, wannan lamari ko kaɗan baya damun Hafiz illa ma ƙara jin daɗin hakan da yake, budurwarsa wadda suke sheƙe ayarsu tare ya fara jan baya da ita, hakan kuma ba ƙaramin tashin hankali bane a gare ta, dan alƙawarin aure yayi mata, hakan ne ma yasa ta ƙara sakin jiki da shi, (hattara dai Ƴan mata, akwai samari masu amfani da wata dama jdan ya fahimci kina son sa kuma kina mugun son aurensa, to zaiyi amfani da wannan dama ya dinga hillatar ki da daɗin baki akan zai aureki akwai abinda yake jira ne, da haka yana kawo hannu jikin ki kina barinsa saboda wannan kalma ta aure daya ratsa a sharrinsa, to wallahil azeem duk sanda ya raba ki da mutumcin ki, ya kwanta dake to ki fitar da rai akan zai aure ki, dan kuwa ya rigada ya gama dake, dan wallahi bazai aure ki ba, mata mu hankalta, mu riƙe mutumcin mu, sai munfi kowa alfahari da hakan, Allah yasa mufu ƙarfin zuciyar mu ameen).




Kullum Hafeez a wulaƙanta budurwarsa yake, ƙarshe data dame shi cemata yayi "kinga Jalila kidena ɓatawa kanki lokaci, ni nan ba yanzu zanyi aure ba, idan Iyayenki auraddake suke da niyyar yi to kije su baki wani, ninan banga ranar aure ba, dan Allah ki sama min lafiya ki dena bibiyata haba", kallon mamaki ta bishi da shi idanunta suka ciko ta ce "kana nufin Hafiz dama ba aure na zakai ba, kasa na zama kamar matarka, duk sanda ka neme ni sai nazo gareka, naƙi kowa naƙi jin maganar Iyayena a kanka Hafeez shine zaka saka min da haka, dan Allah Hafeez idan wasa kake min ka dena", cewar kyakykyawar budurwar ƴar choculate colour da ita, cikin haɗe fuska da zallar rashin mutumci ya ce "ke kinga bari na fito miki a mutum, ni Hafeez Zubairu Garba Yakasai daga yau na rabu da Jalila rabuwa ta har abada, bana buƙatar ta a gaba ɗayan rayuwata, jikinki nake so kuma na samu, kinga babu yiwuwar mu cigaba da  ɓatawa juna lokaci, dan haka ga wannan kije zasuyi miki amfani", ya faɗa yana wurga mata rafar ƴan dubu-dubu wajen guda goma, one million kenan, a gigice ta bishi tana ihu tana ya rufa mata asiri ya dawo, "Hafiz dan Allah ka dawo kar ka tafi ka barni, saida ka bari dudiya ta gama sanin me muke aikatawa shine zaka guje ni, Hafeez ka cuce ni, Allah bazai barka ba, Allah ya wulaƙanta ka Hafeez kamar yadda ka wulaƙanta min rayuwata, Allah ya tarwatsa maka farin ciki kamar yadda ka tarwatsa min nawa Hafeez, Allah ya saka min", wani irin kuka take wanda duk wanda ya ji saiya taya ta, kukan, ta durƙushe  a wajen sai gunjin kuka take, daga ƙarshe ta tashi ta tattare kuɗin ta tafi, tasha alwashin kuɗin nan zata ajiye shi domin ramako.






Yau Nawwara take shirin komawa gidansu Saheeb  dan akwai plan ɗin da ta haɗa tare da shawarar wata Ƙawarta Kareena, haɗa kayan take kamar zata bar Ƙasar dan akwatuna guda bakwai ta cika da kaya, ko Mom bata sanarwa ba, tana gama haɗawa ta sa aka fitar mata dasu aka sa mata a mota ta shiga ta bata wuta ta  nufi Rijiyar Zaki gidan su Saheeb.





Saheeb bayan sun gama hirar yayi musu sallama ya nufi side ɗinsa domin hutawa dan yau kam ya gaji da yawa, tin daga farkon falo ya fara jin canjin iska, dan kuwa alamu ya nuna an shigo, a falo yaci karo da ɗan ƙaramin mayafi ga remote ɗinsa inda ya ajiye ba anan ya dawo ya taradda shi ba, tunani ya fara akan wanda ya shigo, dan yasan babu mai shigo masa ɓangarensa, ko kausar saita nemi izini yake barinta ta shigo, Muhammad kuma dama babu abinda yake kawo shi sai idan zasu tattauna magana mai muhimmanci, to shin waye ya shigo masa? ga dai Mayafi a hannunsa alamu sun nuna mace ce, bedroom ɗinsa ya nufa ai yana shiga wani mugun wari wanda bai taɓa ji ba yayi masa sallama a hanci, saurin toshe hanci yayi, bed ɗinsa ne yaga stil ya hargitse, hannunsa nane da hancinsa ya nufi gadon ƙurawa bedsheet ɗin ido yayi can ya hango kamar yari wari ɗaya, " ko wace wannan mai shigo min ɗinnan koda kuwa Aljana ce saina hukunta ki", tunawa da warin yayi ya durfafi toilet ai yana buɗe murfin dow ɗin ya mayar ya rufe ya fice zuwa falo yana kakarin amai wani ɗan sink ne a falon inda ake ɗan wanke hannu nan yaje yayi ta kwara amai har ya fara galabaita, dan tinda uwarsa ta kawo shi duniya bai taɓa shaƙar wannan ɗoyi ba,(inji shi fa lolz), saurin fitowa yayi yayi side ɗin masu aiki dan yanzu yasan su Mammy sun kwanta dan tambayoyi ne a cikin sa, ga idanunsa sunyi jajir saboda yadda ransa yake a ɓace, aikuwa yana zuwa ya taso mai bawa fulawa ruwa ya ce ya shiga ya gyara masa komai na side ɗinsa, ya tabbatar ya tsaftace ko ina, garden ya koma ya zauna ransa na suya, dan ya rantse saiya hukunta wanda ya shigar masa side har ya masa mafi girman ƙazanta.





Wannan kenan





*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*



*By Rumyn Royar Star*



09130984617




*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 47-48*

>>>>>>>>>>>>>>Shi kansa Mai aikin yana shiga ya toshe hanci yana faɗin "Oga kuma yau me ya ci, wannan bayan gida haka kamar mushen ɓera", (kunsan shi kashi duk rashin ɗoyin sa idan ya jima ba ayi floshing nasa ba to yana ƙara bugawa fiye da lokacin da akayi shi), to kamar haka kashin Rabi ya kasance, saida mai aikin ya  tabbatar komai yayi clean ko ina sai ƙamshi ke tashi, hatta bedshit saida ya canza masa yasa wancen a  washing machine sannan ya fito, lokacin daya same shi ya jingina jikinsa da kujera idanunsa a rufe, "Yallaɓai na kammala aikin", ɗagowa yayi da rinannun idanunsa wanda suke cike da bacci sannan da tarin ɓacin rai da masifa da suke cinsa, hannun ya ɗaga masa, tashi yayi ya shige ciki, duk da haka sai yaji ƙyanƙyamin gaba ɗaya side ɗin yake ji, amma ba yadda ya iya haka ya nufi bedroom ɗin, ganin ko ina fes ga ƙamshi na tashi, yasa ya nufi toilet, wanka yayi ya fito, bayan ya goge jikinsa, turare ya saka kamar mai aure, shortnicker ya sanya, yayi Addu'ar kwanciya bacci, ya kashe lamp light ya rufe jikinsa da lallausan bargonsa ya kwanta, saida ya gama saƙe-saƙensa bacci ya ɗauke shi.







Nawwara bayan ta fito a daren ta nufo gidan Daddy, horn tayi gateman ya buɗe ta ƙaramar ƙofa ganin wadda take horn ɗin yasa shi buɗe gate, turo hancin motar ta tayi, ta parka ta fito, ko kayanta dake bayan boot bata sa an ɗakko mata ba ta nufi ciki, babu kowa a falon, ɗakin Kausar ta nufa.





Kausar ce kwance tana aikin chat, Rabi dake kwance a gefan ta tana bacci, Nawwara ce ta shigo ko sallama babu, Kausar da taga shigowar ta saida ta tsorata, cikin dakiya ta ce "Nawwara at this time?, what happen ?,



"Kausar all is well, kawai na dawo nan ne, Mom naga alama bata son abinda nake so, ina son Ya Saheeb Kausar, shine cikon numfashi na, ina son na rayu dashi rayuwa ta har abada Kausar, Ya Saheeb shi ne zaɓina, amma an kasa gane hakan, ina so ki taimake ni na samu Ya Saheeb", kuka take tinda ta fara maganar, har shiɗewa take saboda kuka, Kausar gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, ta matuƙar jin tausayin Nawwara, kukan da take idan kagani dole kaji tausayinta, tasowa Kausar tayi tazo inda Nawwara take ta ɗago ta ta rumgume tana bubbuga bayanta alamun rarrashi dan tama rasa ta ina zata fara, can dai ta nisa ta ce "Nawwara kibar kukan haka nan, komai yana da ƙarshe, idan Hamma Saheeb mijinki ne wallahi zaki aure shi, kiyi addu'a, nima zan taya ki, amma tinkarar Hamma Saheeb yanzu ba abu bane mai sauƙi, nasan kin san an masa aure zuwan mu Taraba....", "ya isa Kausar, bana so ki ƙara maimaita min kalmar auren Ya Saheeb, dan Allah, ina jin zafi a zuciyata, zan tinkare shi tinda ku naga tsoronsa kuke ji, zani da kaina na furta masa ina son shi, idan kashe ni zaiyi saidai ya kashe ni", Nawwara ta faɗa da tsawa, hakan shi ya tayar da Rabi dan tsawara da ƙarfi Nawwara tayi, cikin muryar bacci Rabi ta ce "Adda Kausar mene ya faru?", sai a lokacin Nawwara ta kula da Rabi, sanye take cikin kayan bacci na masu irin shekarunta, piech ne da adon blue black, riga da wando sunyi mata kyau matuƙa, ga gashin kanta daya kwanta a bayanta, sai da  gaban Nawwara ya faɗi, galala tayi tana kallon Rabi dake murza ido, Kausar ce ta ce "babu komai koma baccin ki", Rabi kuwa ganin yadda Nawwara take kallonta yasa ta tura baki gaba ta galla mata harara, sannan ta koma ta kwanta, Nawwara da taga Yarinyar kamar hararta tayi ta ce "Kausar wannan Yarinyar waye?, batada kunya harara ta naga tana yi", murmushi Kausar ta yi ta ce "haba taya zata harare ki, kawai dan bacci ta farka ne, kije ki kwanta dan Allah, ki dena damuwar nan", ɗaya gadon Nawwara ta hau ta kwanta dan ko tunanin cire kayan jikinta batai ba, ba jimawa bacci ya kwashe ta wanda ke cike da mafarkin abin sonta Saheeb.






Sai washe gari Mammy da Daddy suka ga Nawwara, nan take sanar dasu da daddare tazo, Daddy saida yayi mata faɗan futowar daren da tayi.




Hamma Saheeb bai fito da wuri ba, hakan yasa sukai break basu jira shi ba, Nawwara kuwa sai da safen taga baƙin da aka yi, haka ta gaisar da Inna a wulaƙance kamar taga kashi, Hamma Abdul kuwa a yanayin shigar ta ya fahimci wannan batada tarbiyya, dan ko ƙara kallon ta baiyi ba, Rabi taga irin kallon da Nawwara  taiwa Innarta, hakan yasa taji bata son Nawwara, a haka akai break kowa ya tashi aka koma falo, Daddy kuma ya fice sai a lokacin Mammy ta ce "Nawwara wannan Yayar Daddyn su Kausar ce, wannan Abdul  shine babban Ɗanta, sai Rabi ita ce autar ta, nasan baki san su ba, dan duk sanda zasu zo baku haɗuwa", cikin wani irin yanayi da zai nuna muku cewar yaƙe ta ke ta ce "ayya sannun ku", Inna da tin ganin Yarinyar ta fahimci ƴar wulaƙanci ce yasa bata bata fuska ba, yanzu ma da tace sannun ku ko kallon inda take batai ba, dan Inna bata ƙaunar wulaƙanci, haka Hamma Abdul wayarsa yake dannawa, Mammy, Kausar, Muhammad kuwa babu wanda yaji daɗin abinda tayi, dan duk sunga a yadda tace sannun ku ɗin, banza kowa yayi da ita, suna zaune ƙamshin turaren Hamma Saheeb yayi musu dafifi a hancinansu, idanuwan Nawwara kamar zasu fito saboda kallon maitar data bishi da shi, 



Yayi masifar kyau cikin tattausan yadin kufta mai ɗankaren uban tsada, kai da gani basai an faɗa maka ba, naira tayi kuka a yadin, brown ne ɗinkin ya zauna a kyakykyawan jikinsa, babu hula a kansa, sai gashin sa daya sha gyara sai shining yake, sajensa daya ƙawata cute face ɗinsa sai kyallin gyara yake, glass ɗin dake idonsa ya zare ya shigo da sallama, kusa da Inna ya zauna, gaishe ta yayi cikin ladabi, ta amsa cikin so da ƙaunar ɗan ɗan uwannata, Mammy ya gaisa, sannan sukai hannu da Hamma Abdul, Muhammad dasu Kausar suka gaishe shi, Nawwara data manta cikin mutane take ta zuba masa mayatattun idanunta, wanda kowa na wajen saida ya kula da kallon da Nawwara take bin Hamma Saheeb da shi, shima ya gani basarwa yayi, Kausar dake kusa da ita ce ta zungure ta, nan take tayi firgigit ta dawo daga duniyar data lula, ganin kowa ita yake kallo yasa taji wani iri, "ina kwana Ya Saheeb", cewar Nawwara, bai amsa ba, dan ta bashi haushi, ganin haka ita kuma taji duk babu daɗi, ƙwalla ce ta ciko idanunta, ba shiri ta miƙe ta nufi ciki.






Hira sukai sosai, Rabi sai game take zuwa yanzu ta ƙware da game ɗin, Hamma Saheeb ma ko ta kanta baibi ba dan ko ganinta baya son yi kawai ba yadda ya iya ne,  sai da kowa ya tashi a falon ya zama daga Mammy dai Rabi, Hamma Saheeb ya kalli Mammy ya ce "Mammy jiya waye ya shiga side ɗina?", cikin mamaki Mammy ta ce "waye kuwa zai shiga, babu mai shigar maka indai ba kai ka buƙaci aje a gyara maka ba", aljihunsa  yasa hannu ya ciro mayafi ya ce "wannan me abin ita ta shiga, sannan ga wani shaidar ma", ya faɗa yana ciro warin yarin Rabi, Mammy ce ta ƙurawa kayan ido, sannan ta kalli inda Rabi take, sai alokacin ta tuna lokacin da suka zo, a lambum kusa da side ɗin Saheeb ɗin ta ganta, hakan na nufin ta shiga wajensa a tunanin nan ne wajen su, kallon Saheeb tayi ta ce "to mene Ƴar uwarka ce ta shiga tunaninta nanne side ɗin mu", ta faɗa tana karɓar mayafin a hannunsa, shi kuwa zuciyarsa nan take tahau lugude a ransa faɗi yake "wato ita ce ta shigarmin har toilet tayi min ƙazanta, wai wannan ce aka aura masa, nikam na shiga uku, taya zan iya zama da wannan inaaa bazai taɓa yuwuwa ba wallahi", a fili kuwa baice komai ba, tashi yayi  yaiwa Mammy sallama akan zaije an kawo kayansa daga Mali zai duba, fatan nasara tayi masa ya fice, duk abin nan Rabi bata san sunayi ba dan tayi nisa a game ɗinta cikin kwanciyar hankali.







A fusace ya shiga mota ya fice bayan gate man ya buɗe masa gate, a fili ya ce "wallahi sai na hukunta ki, sai kin gwammaci ba a haife ki ba, wallahi na tsane ki tsana mafi munin tsana, wannan warin ace duk na kashin ki ne?, anya mutum ce wannan, dole ne ki girbi abinda kika shuka", yana masifa shi kaɗai yana dukan sitiyarin mota.







Nawwara kuwa tana  shiga ta ɗakko wisky ɗinta dake cikin kayanta tasha dan rage raɗaɗi, ta rantse yau saita tinkari Saheeb da batun soyayyarta.






Mom kuwa lokacin da Nawwara ta fice tana kallonta da window, ta kuma san duk inda zata bazai wuce gidan Nafisa ba, Hafiz kuwa daya dawo ya shiga ɗakin Nawwara yaga bata nan, ga ɗakin kaca-kaca da alama ba hankali kwance ta fita ba, side ɗin Mom ya shiga "Mom! Mom!, ina Nawwara ne?", "tayi zuciya ta bar gidan, ban san me Nawwara ta zama ba, wallahi na gaji da halin ta", cewar Mom.





"Mom akan dai wancen ɗan iskan ne ko?", Hafiz ya faɗa cikin ɓacin rai.




"Ɗan iska kuma Hafiz?, ɗan uwanka ne fa, why zaka ƙira shi haka?, bana son haka", 





"To Mom idan ba ɗan iska ba me kike so na ƙira shi, duk ya haukata min Ƙanwa, ta zama wani iri, wallahi Mom dole ma ya sota saiya aureta dan uwatas", yana faɗa ya fice dan zuwa club dan shi a tunaninsa can ta nufa.






Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah, yau satin su Inna guda a Kano, da tini sun tafi Daddy da Mammy sai jansu suke sai da sukai sati, dan tin kwana biyu da zuwansu Inna take cewa zasu tafi amma saida su Mammy suka hana tafiyar, yau dai Inna ta dage saita tafi, Rabi sai haɗa kaya take a tunaninta tare zasu koma, suna falo gaba ɗayansu idan ka cire Nawwara, "To Adda Saratu wallahi naso kin ƙara koda sati ne, amma kin dage sai kin koma", cewar Daddy, Mammy dake gefan Inna a zaune ta ce "Yaya Saratu kamar ma gudun mu kike yau fara'arki tafi ta kullum saboda zaki mana murabus", dariya akai, Rabi Daddy  ya kalla wadda taci doguwar rigar Atamfa ta sanya mayafi jiran tafiya kawai ta ke ya ce "Rabi'a banfa gane miki ba, keda kika ce zaki zo ki zauna mana amma naga kinyi shiri kamar wadda zaki tafi", "Kawu ai zan dawo ne", cewar Rabi, Inna ce ta ce "babu inda zaki bini, keda kika ce kina so a sanya ki a Makaranta ki zama malamar Asibiti shine zaki wani ce zaki bini", ai kamar an tinawa Rabi ido ta zaro ta ce "ai kuwa na tina Inna, wallahi na manta ne shi yasa", kowa na wajen saida ta sashi dariya, inka cire Saheeb wanda ko inda take bai kalla ba, "yawwa Ƴata ki zamanki ki zama likita kinji maza dawo nan kusa dani", cewar Mammy.






A ranar su Inna suka ɗau hanya, bayan ansha tataɓirza da Rabi dan cewa tayi saita bisu saida Hamma Abdul yayi mata jan ido sannan suka tafi, haka ta yini tana fushi da kuka, sai rarrashi ake.






Inna kuwa saida ta share hawaye dan tasan shikenan Rabi ta dawo Kano kenan ita da ita sai ziyara, shi kansa Abdul yaƙe yake dan yasan zaiyi kewar Rabi.









********************

Tsalaha lokacin da aka ɗiba masa yayi harya wuce amma bai kai Ɗansa ba, ya nemi da a canza masa ya kawo matarsa Tsohuwa Kalalatu ta ce Dodanya ba jinin matarsa take so ba na Ɗansa take so, idan ba haka ba zaiga masifar da bai taɓa gani ba, haka yana ji yana gani, yai wakilci har Makarantar su Adahama aka ɗauke shi, Tsalaha kasa binsu yayi saboda kukan da yake, haka ya koma gida yana mai jin tashin hankalin rashin Ɗansa.






Lokacin dawowar Adahama gida yayi shuru, hakan yasa Rakiya fita dan zuwa Makarantar dan haka kurum taji gabanta yana faɗuwa, Tsalaha baya nan shi yasa ta kulle gidan ta nufi Makaranta, tana zuwa taga maigadi ta tambaye shi, nan yake sanar da ita ai awa wajen biyu da tsahin Yara kowa ya tafi, babu kowa cikin Makarantar, nanfa hankalin Rakiya ya daɗa tashi ƙaramar wayarta ta ciro a jaka ta ƙira Tsalaha,



Tsalaha dake zaune a kasuwa kai kana ganinsa kaga wanda kwanciyar hankali bata wadace shi ba, yana zaune yaji ƙira firgigit yayi kamar mara gaskiya, ganin mai ƙiran yasa shi jin kuka ya taso masa, dan Rakiya ce ke ƙiransa, saida ya aro nutsuwa ya ɗaga "Halo (hello) Baban Adahama, kana jina kuwa?, halo", "ina jinki Rakiya meya faru", cewar Tsalaha da shi yasan kwanan zancen,




"Yawwa ashe kana jina, kaga naji shuru Adahama bai dawo ba shine na je makarantar, maigadi yake cemin awa biyu kenan da tashin su, ko kuna tare da shi ne a kasuwa?", "awa biyu bai dawo ba kuma?, ninan bama tare nayi tunanin ya dawo tin ɗazu, to kodai bayan kin baro gida shima ya koma", cewar Tsalaha.




Katse ƙiran tayi ta nufi gidan cikin sauri dan sosai gabanta ke faɗuwa, hankali tashe ta koma gida, nan ma bai koma ba, gidan su Tsalaha ta nufa, nan ma suka ce baizo ba, suma hankali tashe suka fita nema, ƙarshe harda Tsalaha aka shiga gari neman Adahama har dare babu shi babu labarinsa, Rakiya sanin yanzu garin satar Yara ake yasa  hankalinta ƙara tashi, in banda kuka babu abinda take, Abinci kuwa babu batun ci, dan duk cin Rakiya yau saida ta saduda, Mahaifan Tsalaha ma sun saddaƙar masu sace Yara sun sace Adahama, Tsalaha kuwa kamar gaske duk ya daɗa figewa ya zama abin tausayi, sai jaje ake masa, Rakiya sai tsinuwa take aunawa masu sace Yara, haka Iyayen Tsalaha sai tsininuwa suke aunawa baji ba gani, Tsalaha kuwa duk wata nitsuwa da ake yasan harda shi a ciki, hakan yasa shi zirga-zirgar banɗaki, nan take ya ƙara ramewa ya zama abin tausayi, kowa ya ganshi sai yayi tunanin ɓatan ɗansa ne ya sashi komawa hakan, kai tafi-tafi har sati babu batun Adahama, Rakiya ta susuce, jikinta ya kuma saki ta zama abin tausayi.




Sai bayan ɓatan Adahama da sati guda, Tsohuwa Kalala ta cewa Tsalaha ya nemi inda zai ajiye gawar Adahama dan ita ce zata dingai masa aman kuɗi, amma karya sake agani ko a shiga inda ya aje gawar idan haka ta faru, zai haukace kuma wanda ya gani ma zai haukace, sannan masifu zasuyita samunsa, aikuwa Tsalaha nan take ya maida ɗakinsa ma'ajiyar gawar Adahama mai amon kuɗi, yana shiga da daddare yaga gawar Adahama, cikin tsoro ya ambaci sunansa, aikuwa saiga kuɗi na fitowa ta bakin Adahama, ƙara ƙiran sunan yayi kuɗin dai ya cigaba da amayowa, ganin kuɗaɗe yasa Tsalaha manta halinda yake ciki, farin ciki ne ya mamaye shi, wannan yasa tin daga ranar yake garƙame ɗakinsa idan zai fita.






Nawwara ce taci kwalliya sai walwali take, compound ɗin gidan ta nufa dan can ta hango Saheeb zaune hakan yasa taje  ta ɗau wanka dan zuwa ta sanar masa sirrin zuciyarta, tafe take tana yauƙi tana rangaji, yana  zaune yana danna waya sai ganin mace yayi taja ɗaya daga cikin kujerun ta zauna "barka da hutawa Ya Saheeb, hala kana shan iska ne?", kallonta yake  da mamaki, yana nazarinta, "yawwa" kawai ya ce,  ganin haka yasa ta ƙara gyara zama cike da kwarkwasa ta ce "ina son zamuyi magana Ya Saheeb", kawai mamaki yake na yaushe har yayi arahar da wannan Yarinyar zata zo inda yake, shi dai yasan baya musu wasa tsakaninsu gaisuwa ce amma ace wannan abar tazo gabansa tana wannan abin, so yake yaga ƙarshen iskancin ta ya ce "ina jinki", cikin farin cikin karenta zai kama kurciya ta ce "Ya Saheeb a cikin duniya ta babu wanda nake so da gani sai kai, wallahi ina masifar ƙaunarka, na jima ina son gaya maka amma na kasa ganin fuska sai yau dana kasa jurewa nace saina zo na gaya maka, ko da zuciyata zata huta, ina mahaukacin sonka wallahi na rasa ka zan iya mutuwa, dan Allah ka aure ni Ya Saheeb", mamaki, haushi haɗe da takaici ne sukaiwa Hamma Saheeb dirar mikiya, zata cigaba da magana ya katse ta da "keee! ashe bakida hankali ban sani ba, ashe mahaukaciya ce ke?, koda yake bazanyi mamaki ba idan na tuna cewa kina shaye-shaye hakan ba abin mamaki bane, har ni kike cewa kina so har gabana kizo ki gayan haka, ashe bakida kunya?, nayi tunani muna cikin ƙabila wanda akafi sani da kunya ashe ke ba cikinsu kike ba, har zaki iya zuwa kicewa Namiji kina son shi ya aure ki, lallai kin cika ƴar giya, bari na gaya miki idan kika kuma fuskantata kamar haka da wannan haukan naki wallahi saina ci ubanki a wajen nan sha sha sha tashi anan konai ball dake", ya faɗa tare da miƙewa, saurin tashi tayi, kuka ne ya kufce mata cikin jin haushin abinda yayi mata ta ce "ni ka wulaƙanta saboda nace ina sonka Saheeb, to ka rubuta ka ajiye ni Nawwara saika soni kuma saika aure ni, sai kazo da kanka ka tsuguna ka nemi da in soka, wallahi tallahi sai ka soni", tana kaiwa anan ta shige cikin gida da gudu, shi kuwa wani shu'umin murmushi yayi dan ya tabbata Yarinyar nan Ƴar giya ce kuma sai yayi maganinta.




Rabi da duk abinda ya faru akan idanunta ne, hakan yasa ta ƙara tsanar Saheeb ganin ya sa Nawwara kuka, duk da ba shiga harkar Nawwara take ba amma bata son taga babba yana kuka, tsaki tayi mai ƙarfi, karaf a kunnen Saheeb da yake shirin barin wajen, waigowa yayi suka haɗa ido da Rabi, ganin haka yasa ta ƙara galla masa harara haɗi da murguɗa masa baki, motsa bakinta tayi sai yaga kamar Arne tace masa, aikuwa cikin hanzari ya nufe ta dan damƙarta yaci ubanta dan dama ciki yake da ita, aikuwa a guje ta shige falon gidan, haka ya koma yana cizon yatsa, yana ganin sake suka samu suka raina shi, duk da ya kwana da sanin Rabi ta jima da raina shi, amma dama yake so ya samu ya kakkarya ta kafin yabar Ƙasar ƙila ta dena ganinsa abokin wasanta, side ɗinsa ya shige ransa duk a ɓace.





Nawwara kuwa bedroom ɗinsu ta shige ta faɗa gado tahau kuka, Kausar tana Makaranta shi yasa bata san abinda ya faru ba, Rabi ce ta shiga ɗakin ganin Nawwara haka yasa ta harareta ta zauna a ɗaya gadon tana waƙe-waƙen ta wanda suke yi a ƙauyensu, jin murya na waƙa yasa Nawwara ɗagowa, cikin dashashshiyar murya ta ce "ke dan Kutumar ubanki yi shuru kona daddatsaki, shegiya ƴar ƙauye", sosai Rabi taji zagin har tsakar kanta, cikin tsiwa ta kalli Nawwara zuciyarta na ƙuna ta ce "sai dai naki, kuma batun Ƙauye ina yanzu kika gama yiwa wani wanda asalinsa ƙauyen ne magiya akan ya soki ya ci miki mutunci, kuma daddatsawa da kike magana akan zaki mafashi ga fili nan zoki gwada datsa ni", ta faɗa tana tsayawa ta tsare Nawwara da ido, takaicin maganar da Rabi ta gaya mata take, wato taga lokacin da suke magana da Saheeb kenan, cikin hargagi Nawwara ta taso zata kaiwa Rabi duka Mammy ta shigo dan neman Rabi ganin Nawwara zata daki Rabi yasa Mammy cikin sauri ta zo ta janye Rabi, ganin haka Rabi ta fashe da kuka tana faɗin "Mammy sai zagarmin Iyaye take, tana ƙiransu ƴan ƙauye, kuma har Kawu ta ƙira ta zaga dan kawai na shigo ɗakin nan zan kwanta, jiya ma har shaƙe min wuya tayi dan na gaishe ta", sosai Mammy ta yarda, kuma ranta ya ɓaci sosai, Nawwara kuwa suman tsaye tayi, jin ƙaramar Yarinya da kaidi, "wallahi Mammy ƙarya take min..", "ya isa Nawwara", Mammy ta faɗa tare da jan hannun Rabi tana rarrashinta, Mammy bata kula da lokacin da Rabi ta juyo ta kalli Nawwara da ita ma kallon Rabin take ta sakar mata gwalo, "Kai lallai wannan shu'umar Yarinya ce, lakaci ɗaya ya haɗan sharri, haka haka Ƴan Ƙauyen suke?".✍️








Wannan kenan




*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*









*By Rumyn Royal Star*





09130984617




*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 49-50*

>>>>>>>>>>>>>>Zama dai tsakanin Nawwara da Rabi babu daɗi dan tinda Nawwara ta zagi uban Rabi take gamuwa da iftila'o'in Rabi, tako ina ta hana Nawwara sakat, yauma hakance ta faru, Kausar ce da Nawwara zaune a falo kowacce tana aikin latsa waya, Rabi ce ta shigo da sallama a bakinta kamar gaske, zama tayi kusa da Kausar ta ce "Adda Kausar hutawa kike?", Kausar data saba da manyance irinna Rabi ta ce "eh Adabiyya, hutawa muke", "kuke ko kike, nidai ke kaɗai na gani anan, ko keda wayar ki kuka zama ku ɗin", cewar Rabi, Kausar sanin hali yasa ta ce "eh nida wayata nake nufi, wai bakyajin baccin rana ne kije kiyi?", 



"bacci kuma Adda Kausar, ni bana jin bacci, Adda Kausar dan Allah ki bani wayarki nayi game, kinga kwana biyu baki aramin nayi ba, kuma Hamma Muhammad baya nan", kallonta Kausar tayi ta ce "wallahi bazan baki wayata ba, kina ganin aiki nake da ita zaki ce na baki, dan Allah ni kin takura min", Rabi ranta a ɓace ta koma kujera me zaman mutum ɗaya ta haɗe fuska tana kumbure-kumbure, Nawwara da ta kalle ta ta ƙasan ido ta ja tsaki tare da faɗin "Kausar kina bani mamaki ta yadda kika bari wannan banzar Yarinyar ta raina ki wallahi, wai har wayarki kike bata, mtseww", ta ƙare faɗa da jan tsaki.



Rabi da ko ɗaga kanta  ta kalli inda Nawwara take batayi ba ta ce "ai a duniya ba a taɓa yin banza guda sai banzaye da yawa, ba ɗaya ba ba biyu ba kuma ba uku ba, dan haka kisa minjaye", ta faɗa tare da barin wajen, Nawwara data kalli Kausar alamu ya nuna neman ƙarin bayani take akan abinda Rabi ta faɗa, Kausar ɗin ma kallon Nawwaran tayi, "Kausar me Yarinyar nan take nufi da maganarta?", Kausar data fahimci duk abinda Rabi ta faɗa ta ce "no shirmanta ne kawai, ki dena shiga sabgarta kema dan Allah".




Nawwara kuwa ta fahimci Rabi kaɗan, "lallai zan koyawa Yarinyar nan hankali, zata san na birni ya girmi na ƙauye, duk iskancin dake kanta saina sauke mata shi", Kausar murmushi tayi a ranta ta ce "ko kuma ta koya miki ba, bakisan wace Rabi ba shi yasa kika shan alwashi a kanta", a fili kuma ta ce "Allah ya kyauta.





Rabi kuwa ɗakin Mammy taje taga tana  gyara wardrop ɗinta ta taya ta.





An kammala komai na komawar Rabi Makaranta, Uniform, Books, Sandal, Safa, da duk wani nau'i na kayan makaranta an gama kuma Saheeb da kansa yayi wannan fafutukar, dan Daddy ne da kansa ya sashi dan dole yayi, zo kuga murna wajen Rabi lokacin da tayi arba da kayan makarantar, sai gwadawa take tana cirewa, inta raya mata saita sa taita gwada yadda zatai tafiya dasu idan ta saka,  sai da Mammy ta ƙwace suka samu lafiya, ranar Momday zata fara zuwa hakan yasa take ta ƙirga ranaku.





*QUEEN ELIZABETH* sunan makarantar, makaranta ce wadda ƴaƴan manya ne a ciki, dan duk Kano ansan wannan Makaranta, hatta Ƴaƴan Sanaters akwai a ciki, to nan ne Daddy yasa Saheeb ya sanya Rabi dan ya ce dole makatanta mai kyau zai sanya ta, Saheeb kuwa mita yayi tayi a lokacin "Wannan Yarinyar mai toshashshiyar ƙwaƙwalwa ita aka sa a wannan makarantar dan dai kawai a sani asarar kuɗi, dan na tabbatar babu abinda zata iya ƙarshe ma idan taga ƙwarin makarantar ta ce a cire ta, banda Daddy daya bari na sata a ko Kuntau Acadamy ne dukda suma ba daga nan ba wajen karatu ai da yafi", haka dai yayi ta mitarsa shi kaɗai ya haƙura.






Ranar Monday tinda Rabi tayi sallar Asuba bata koma ba, Allah-Allah take lokaci yayi a tafi, wanka kuwa tuni tayi, dama  kuwa sunje gyaran gashi jiya ita da Kausar kanta yasha gyara hakan yasa fuskarta ƙara kyau, tayi raɗau da ita, hancin nan ya ƙara fitowa, ƙaramin bakinta yayi cas abinsa, bakwai dai-dai Rabi ta kammala shirinta cikin Uniform ɗinta riga da sikat kalar ruwan sama ne siket ɗin sai farar riga mai kwala, sai neaktie ɗin shima kalar sky blue, ɗan ƙaramin hijabin da iyakarsa ƙirginta, shima sky blue mai hula, farar safa da comboth ɗinta fari yayi mata ɗas, gaba ɗayanta tayi kyau, saita fito ƴar baby da ita, bakin nan yaƙi rufuwa dan daɗi, ta riga kowa fitowa kan dinning, mai aiki kuwa ita da Mammy sai aiki suke a kitchen kasancewar su Daddy ma da wuri zasu fita har Saheeb, Muhammad ne ya fito falo, nan yayi arba da Rabi ta hakimce a kujerar dinning, dariya ce ta ƙwace masa, ganin yadda haƙoranta suke a buɗe gashi ita kaɗai ba kowa, jin dariya yasa ta ɗago, ganin Hamma Muhammad yasa ta cuno ƙaramin bakinta ta ce "dan Allah Hamma kazo ka kaini karna makara kaga fa lokaci sai tafiya yake", Muhammad inda take ya nufo ya zauna ya ce "haba ƴar ƙanwata ki bari kiyi break, ko malaman yanzu suna gida basu fitoba ai, kinga yadda kayan nan sukai miki kyau kuwa?", washe baki tayi tabi kanta da kallo, suna zaune Mammy ta fito ita da mai aiki "a'a Doughter har kinyi me?", cewar Mammy, "na shirya Mammy", Rabi ta faɗa.





"Masha Allah kinga yadda kikai kyau kuwa", cewar Mammy, dariya Rabi tayi cikin farin ciki take kallon kowa na wajen, Daddy ne ya sakko, Kausar ma da Nawwara suka fito dan karyawa dan kowa yau yanada wajen zuwa, Nawwara da Kausar sunada lucture, Daddy zai leƙa Campanynsa, Muhammad zaije amso wasu takardu na tafiyarsa India, Hamma Saheeb ma yanada wajen zuwa hakan yasa kowa tashi da wuri, nan dining ya cika saura Saheeb kawai, kamar yasan shi ake jira ya iso yana sanya agogon rolex a hannunsa, bayan ya gaida su Mammy, su Kausar suka gaida shi, Nawwara ma data ruɗe dan yayi mata kyau yau shigar ƙananun kaya yayi sun amshi jikinsa, baƙar riga yasa anyi adon rubutu da golden *you are the best* aka saka, sai wando shima baƙi haka takalminsa sau ciki shima black da ratshin golden, idanunsa sanye cikin glass, gashinsa yasha gyara kamar koyaushe, sai ƙamshi yake, zama yayi Kausar ce tayi saving nasu, Mammy tayi na Daddy, bayan sunyi bismillah suka rufarwa abincin, Rabi kuwa da ba gaishe da Saheeb take ba abincinta take ci hankali kwance, ita ta fara gamawa ta goya jakar goyanta kalar sky blue & white, Daddy ne ya ce "Ƴar Daddy har kin gama?", amsawa tayi, ya ce "masha Allah, ayi karatu banda wasa, ki kula sosai banda faɗa", amsawa take cikin nutsuwa, Mammy ma tayi mata  tata nasihar, Hamma Saheeb ya kammala zai tashi Daddy ya ce "to gata nan saika miƙa ta makarantar", Saheeb ji yayi kamar an buga masa guduma aka, ransa ya ɓaci sosai "Daddy ina sauri Muhammad ya kaita dan Allah", "nasan da Muhammad ɗin ai nace ka kaita", ganin ran Daddyn ya ɓaci yasa shi   cewa "tom Daddy" waje ya nufa ita kuwa Rabi kamar tace ba zata bishi ba sai kuma ta bishi, sallama Rabi taiwa su Daddy, Muhammad sai tsokanarta yake shi da Kausar, Nawwara kuwa haushi taji jin wai Saheeb ne zai kaita, jitai abincin ya fita a ranta ta miƙe ta koma ɗaki.




Tana fitowa taga mota babu Saheeb a  wajen, guri ta samu ta zauna tana jiransa, shi kuwa ashe yana cikin motar ita  yake jira, ganin ta nemi guri ta zauna ransa yakai ƙoƙoluwar ɓaci, horn yayi mai ƙarfi, kallon motar tayi ta kauda kai, wani horn ɗin yayi still dai bata taso ba a fusace ya fito cikin zafin zuciya ya ce "ke wace iriyar wawiya ce, ke nake jira kin zauna anan kina ji ina miki horn,  dallah taso konai tafiyata", banza tayi dashi kuma bata kalli inda yake ba, hakan ya ƙara hassala Saheeb, hannunta ya damƙa ya fige ta, ƙara ta saka saboda ya riƙe mata hannun da ƙarfi, cikin tsiwa ta fuzge hannun ta ruga da gudu zata koma ciki, cikin zafin nama ya damƙo ƙaramin hijabinta ta dawo wanka mata mari yayi har sau biyu, ƙara zatai ya make bakin ya buɗe gidan baya ya cillata ya rufe ya zago ya zauna ya tada motar, ihu take tana kuka, "ka buɗemin mugu Allah ya isa ban yafe maka ba, azzalumi, in sha Allah sai kaga sakayya, kuma wallahi saina gayawa Kawu", ransa a ɓace yayi parking dan ba'a taɓai masa zagin da taimasa ba, idanunsa sunyi jajur kamar gauta, sai huci yake, gefan hanya ya tsaida motar ya fito ya zagayo, ya figota titi ya daddage ya ƙara kifa mata mari, wannan karon sai da jinta da ganinta ya tafi hutun wucin gadi, hakan bai ishe shi ba saida ya ɗakko wayar usb ya ninkata yahau dukanta, ihu take tana zaginsa shi kuma zagin da take masa ne yake ƙara masa ɓacin rai, ita kuma bakinta yaƙi mutuwa, wajen hanya ce da babu kowa, hakan yasa yai mata duka har saida ya gaji ya ƙyale ta, dan dama ya daɗe yana son wannan damar, Rabi ta daku iya dakuwa dukan da ko Inna bata taɓai mata shi ba, ta jibgu, tana zaune a ƙasa gefan motar, tana maida numfashi tana kuka sosai, "shigo mu tafi ko na ƙara miki wallahi, kuma wallahi daga yau ko wani naga kin zaga sai naci Ubanki, nida ba wasa nake miki ba har kin samu damar raina ni, nida ba shiga sabgarki nake ba, dalla shigo kona sabauta ki wallahi", bata kalle shi ba kuma bata tashi ba balle ta shigo motar, zuwa yayi ya  ɗagata  ya jefa bayan motar ya rufe ya zaga suka tafi, kuka take a ranta tana tunanin yadda zata rama wannan dukan da zagin da yayi mata, "bazaki min shuru ba, saina ɓalla ki wawiya kawai", banza tayi dashi kuma bata dena ba, a wannan yanayin suka shiga makarantar, Office ɗin Principal suka nufa, anan akai mata interview kuma sosai sukai mamakin yadda ta san komai, shi kansa Saheeb yayi mamakin ƙoƙarinta, wata Malama aka sa takaita ajin da zata zauna, Saheeb kuwa da zai tafi ya yiwa Principal kyauta mai tsoka ya tafi ya barshi yana zabga godiy.







A  class 1A aka kaita dan sune masu ƙoƙarin makarantar, kasancewar Rabi zuciyar ba daɗi can wani layi inda ba kowa ta koma ta zauna tana tunanin da abinda zata rama wannan duka da Hamma Saheeb yayi mata, Ajin maza da mata ne kowa sabgarsa yake wasu suna karatu wasu kuma wasanninsu suke, Rabi kuwa sai bin kowa da ido take, wani malami ne ya shigo da ganinsa ba bahaushe bane kuma ba musulmi bane dan ga cross nan a wuyansa, ganinsa yasa kowa tashi tare da faɗin "good morning sir", ya ce "morning how are you", suka ce  "fine sir", "ok sit properly", zama kowa yayi tare da ƙoƙarin ciro littafinsu, duk wannan abu daya faru babu Rabi a ciki, dan tana zaune tana kallonsu, da suka tashi bata miƙe ba, kuma Sir Samual yana lura da ita, ƙyaleta yayi kasancewar ya ganta she is new commer, Saddiƙa wadda tin zuwan Rabi take so ta kula ta batayi ba saboda kar sauran ƙawaye suce ta fiye shishshigi ita ce ta matsa kusa da Rabi ta ce "sister ki ciro book ɗinki mana", Rabi kamar doluwa yau haka ta zama, littafin ta ciro English text book ne dan topic ɗin English yake ɗaukarsu, har yayi ya gama Rabi bata fahimce shi ba dan tunanin ɗaukar fansa take, yana fita Malamar Economic ta shigo tayi ta fita, daga nan kuma aka kaɗa ƙararrawar break, Rabi nan ma babu inda taje har sukai suka dawo, Saddiƙa ce ta kawo mata ruwan Faro ta ce "sis ga ruwa naga baki fita break ba, ko bakida lafiya ne?", "lafiya ƙalau nake, bana sha", ta faɗa tana kawar da kanta gefe, Saddiƙa duk saita damu, yau ɗaya ta ganta amma ta shiga ranta, sai dai kamar bata son mutane, haka Saddiƙa ta faɗa a ranta, ƙyaleta tayi, har aka tashi Rabi a haka take, bakin gate suka fito, Rabi tunani take wane zaizo ya ɗauke ta?, tana tsaye Drivern Daddy yazo shiga tayi suka nufi gida.






******************


Su Inna kewar Rabi ta kewaye su, Kattume kullum sai tazo ta tambayi Inna Rabi yaushe zata dawo?, Inna sai dai tace "zata zo Kattume na tabbata ita ma kina ranta, nasan idan tayi hutu zata zo kinji Kattume", da haka take lallaɓa Kattume.





Hamma Abdul fa soyayya suke shi da Kausar babu wanda ya sani sai su saii kuma ni dana ƙware fagen iya bin ƙwaƙwƙwafi, kullum suna manne da waya, soyayya ce mai tsafta da iya taku, shi yasa babu wanda ya sani, (kwaji dashi ja'iran kaya Lolz).






Rakiya ta rame wannan ƙiba ta tafi, kullum tana jiran taga Adahama yayi sallama ya shigo, amma har yau shuru, Tsalaha kuwa ya saduda, dan kuwa dole ma ya saduda dan yasan inda Adahama yake, kuɗi yanzu yafi nada dan sosai Tsalaha ya zama gawurtaccen mai kuɗi a wannan gari, yasa an ƙara rushe gidansa anyi masa na zamani, irinna manyan masu kuɗin birni, gidan Iyayensa  ma ya rushe an ƙawata musu, Alhaji Nura ya bashi shawara akan ya shiga birnin Bauchi ya samu ƙaton shago ya zuba kaya, tanan ne zai wanke idon masu gulma, idan ba haka ba za'a gano shi da wuri, da wannan shawara Tsalaha yayi amfani, hakan yasa mutane suke tunannin kasuwancin sa ne yake bashi kuɗi.






"Baban Adahama ka bani makullin ɗakin ka na share maka, yau wajen wata ɗaya ka hana in shiga, nasan yayi ƙura", cewar Rakiya.





"Ke Rakiya wace irin shara, ni na share ɗakina da kaina", Tsalaha ya faɗa, shuru tayi, dan yanzu batada hayaniya sosai.





Nawwara ce zaune ita da Kausar suna cin Abinci, "Kausar wai nikam ina matar da Saheeb ya aura ne?, ko tana ƙauyen ba yanzu za'a kawota ba?",




"Wace kuma matar Hamma bayan da ita muke kwana muke tashi a cikin gidan nan",



"ban gane ba, ban gane a gidan nan muke kwana da ita muke tashi ba, wace?", Nawwara ta faɗa tana neman ƙarin bayani.




"Rabi'a ita ce matar Hamma Saheeb", "what?, ban fahimceki ba, wace Rabi kuma, nasan dai Rabi yarinyar nan kuma nasan babu abinda Ya Saheeb zaiyi da ita", cewar Nawwara.





"Hmmm Rabi dai Yarinya ita nake nufi, ita ce matar Hamma Saheeb ta aure", Kausar ta faɗa.




"kutmar lallai ma, ita aka aura masa ashe, amma wannan hauka ne da gidadanci, wannan wane mai ƙaramar ƙwaƙwalwar ne yayi haka?", 




"dakata malama, karki nemi kici mutumcin tsohon arziƙi, Kakana wanda ya haifi Mahaifina abin sona, shine ya haɗa kuma hakan dai-dai ne a wajen mu, ki iya bakin ki", Kausar ta faɗa tare da bar mata wajen,  wani irin murmushi Nawwara tayi ta ce "ta kwana gidan sauƙi, dama na tsane ki kuma gashi tsanarki ta ƙaru a yanzu, sanadiyyar auran wanda nake so, dole na kawar dake, amma zanyi shawara da Kareena nasan bata bani shawara banza, muje zuwa lokaci yayi", ta faɗa tare da sheƙewa da dariya.







Lokacin da Hafeez yaje Club baiga Nawwara ba ya ƙira wayarta nan take gaya masa tama gidan Mommy, yaso zuwa sai kuma ya fasa, a kwanakin nan burinsa kawai ya keɓe shida Nawwara, amma ya rasa yadda zaiyi, gashi Jalila sun ɓaɓe, yanzu so yake ya samu wata sabuwar ya farka ta, gani yayi kamar an share matan, baya ganin kowa sai Nawwara ita ce yake jinta yadda yake so, Mom kuwa ta shiga sabgogin business ɗinta, dan har Dubai take zuwa, Dad kuwa kullum a ƙaryar zai dawo yake amma yaƙi.





Tinda Mom tabar gidan Mammy bata kuma nemanta ba, tayi fushi sosai da  ita, Mammy kuwa taƙira ta yafi a ƙirga taƙi ɗagawa ƙarshe ta sata a user busy, haka ta haƙura.






Rabi  tinda abin nan ya faru bata gayawa kowa ba, ranar data dawo da Mammy ta tambayeta ya taga idanunta sunyi ja, ta ce mata ƴan ajinsu ne suna wasa suka tsokane mata ido, a haka aka tafi, washe gari Driver ne ya kaita, ranar dai ta gane karatun da akayi, duk da da turanci ne amma ta gane wani abinne dai sai imani, dan dama kunsan Hamma Abdul yana mata lesson a gida kafin ta dawo Kano.




Nawwara ta tattara kayanta yau zata koma gida dan shirya manaƙisa, dan ta rantse saita kashe Rabi ta yadda babu mai gane ita ce, kuma ko zatai yawo timɓir sai Saheeb ya aure ta, da wannan ta haɗa kayanta tayiwa su Mammy sallama, ta tafi bayan Mammy ta haɗa mata sha tara ta arziƙi, dan Mammy ba daga nan ba akwai hannun kyauta✍️.






Wannan kenan




*Ina miƙo gaisuwa ta gare ku ma'abota bibiyar Littafin RABI DANJA, ina alfahari daku, ina jim daɗin comment ɗinku, Allah ya barni daku, yaja zamani, ya ƙarawa Iyayenmu lafiya da zaman lafiya da tsawan kwana mai amfani, waɗanda suka rasa nasu Iyayen Ubangiji ya jiƙansu yasa aljanna makoma ameen*





*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*






*By Rumyn Royar Star*



*09130984617*




*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*






*Paradise is a home of honor dignity rest, satisfaction beauty, joy may Allah make it to be your parmanent home, Jumma'at Kareem*







*Page 51-52*

>>>>>>>>>>>>>>Yau Satin Rabi huɗu da fara zuwa Makaranta, hakan yayi dai-dai da tafiyar Hamma Saheeb da sati uku, Rabi tana fahimtar karatu sosai, amma har yanzu ta kasa manta abinda Saheeb yayi mata, kuma taci alwashin ramawa, kuma har yanzu bata san yayi tafiya ba, tunanninta ko basa haɗuwa ne kawai, Saddiƙa tana son Rabi sosai a ranta, hakan yasa suka ƙulla abota, akwai wata ɗaliba wadda koda yaushe a takalar Rabi faɗa take, amma har yanzu Rabi bata kula ta ba a tunanin wannan Ɗaliba mai suna Hanan Rabi tsoranta rake ji kamar yadda sauran Ɗalibai suke tsoranta, bata san Rabi tara ta take ba, Mazan Ajin kansu tsoran Hanan suke saboda batada mutumci ko kaɗan ko malamai ba raga musu take ba, saboda Mahaifinta Defuty Governor ne shi yasa take wanga rashin ɗa'a, kamar kullum Rabi da Saddiƙa ne zaune suna bitar karatun da akai musu, saiga Hanan da ƴan koran ta, wato tawagarta, kansu Rabi suka tsaya basuyi aune ba suka ga anyi wuf an zare littafin da suke dubawa a fusace Saddiƙa ta ɗago kai ganin Hanan yasa ta yin shuru dan ita ma ta kwana da sanin wace Hanan, Rabi kuwa bata ɗago ba sai dai ranta ya mugun ɓaci,





"Ku banzaye kuzo na aike ku", cewar Hanan, da sauri Saddiƙa ta miƙe, Rabi kuwa ko motsi batai ba, Hanan ce ta ƙara fusata ta ce "ke dalla dake nake naga bakida niyyar tashi", nan ma Rabi tayi burus da ita, ganin haka Hanan ta damƙo hijabinta da niyyar janyo ta, Rabi kuwa tasowar nan da zatai sai ji kake tas tatas ta wanke fuskar Hanan da maruka har biyu gefan dama da hagu, cikin huci da tafarfasar zuciya Rabi ta nuna Hanan da hannu ta ce "ba'a min tsawa aka, tinda nazo naga take-taken ki ke karya ce baki san abinda kike ba, nayi miki bakan ne ko zaki dena amma naga kamar ƙara ingizaki ake, to ni dai nafi ƙarfin ki, da kinsan wace Rabi Danja da baki nemi tashin hankali dani ba, dan haka wallahi daga yau kika ƙara shiga sabgata kota Ƙawata wallahi ba Ƴar Defuty ba  ko Ƴar shugaban Ƙasa ce ke saina yi maganin ki wannan marin so mun taɓi ne, ki ja dani kiga yadda zan jaki a ƙasa, mtsewww", tana gama faɗa ta ja hannun Saddiƙa  da tayi mutuwar tsaye tana ganin Rabi ta janyo musu masifa, Hanan kuwa tinda ta riƙe kumatukan ta biyu, bata ko motsa ba, ƴan koranta kuwa sai faɗi suke "cafɗi gaskiya Hanan wannan ta raina ki, marin ki tayi fa, haka zaki barta", mazan ajin kuwa babu wanda Rabi bata birge shi ba, dan dama fatan su a samu wadda zata tankawa Hanan, Hanan zama tayi inda su Rabi suka tashi  masu zuga suna ƙara ingiza Hanan.







Rabi kuwa wani waje suka samu suka zauna Saddiƙa cikin nuna tsoro ta ce "Rabi'a kinsan kuwa wa kika mara?, kinsan me zai faru idan shugaban Makaranta yaji, wallahi zai iya korar ki, nidai kije ki bata haƙuri dan Allah", wani bahagon kallo Rabi tabi Saddiƙa da shi ba shiri tayi gum da bakinta, 



Rai ɓace Rabi ta ce "na bata haƙuri fa kika ce, kinsan kuwa tinda nake ban taɓa bawa kowa haƙuri ba, bayan Inna ta da Baba na, sai Hamma na, bayan su sai Kawu da Mammy, su kaɗai nake jin zanwa laifi na bawa haƙuri, sai wata banza can da yadda Iyayensu suke biyan kuɗi haka nata suke biya, har zaki ce naje na bata haƙuri, wallahi karki hasalani kisa naje nai mata ɗan iskan duka, kuma da kike cewa zata sa a koreni ta daɗe bata sa an kore ni ba, kuma wallahi idan baki bar tsoranta ba zamu raba hanya, dan na tsani matsoraci ni", tana kaiwa nan a zancen tabar wajen, Aji ta koma fuskar nan tata a murtuke, har lokacin Hanan na zaune inda suka barta, Kujerar zaman ta Rabi ta nufa ta yadda dole sai Hanan ta matsa zata wuce "zaki iya bani waje na wuce?", cewar Rabi fuskar nan babu annuri, Hanan bata kula ta ba kuma bata matsa  ba, hannu Rabi tasa ta jata ta wurgar ta shige wajen zamanta ta zauna, Hanan kuwa saida ta ƙume a goshi wannan sanadi yasa Hanan kurma uban ihu ganin jini a goshin ta, ita kuwa Rabi ko gezau saima zubutun ta take hankali kwance, Ƙawayen Hanan kuwa sun ruɗe sun rikice, suna zuzuta jinin daya fito a goshin Hanan, kuma fa ƴar kurjewa ce babu yawa, wannan lamari Saddiƙa ta dawo ta gani, nan tabi Rabi da kallo, ganin kamar ma bata san abinda ya faru ba, ta hau faɗin "Rabi'a kin fasa mata goshi, na shiga uku, kinga fa jini a goshin ta", saita nufi wajen su Hanan ɗin tana faɗin "dan Allah sis Hanan kiyi haƙuri wallahi baƙuwa ce ita ki ya.....", hankaɗa ta taji anyi, cikin masifa Rabi ta hau Saddiƙa da faɗa "ke kina ganin ke wace da har zanyi abu ki bada  haƙuri nina  saki, ko kece kikai to ahir ɗinki Saddiƙa Iyayena ne kawai zanyi abu su bada haƙuri na ƙyalesu, amma bake ba, ki kiyaye wannan, kuma fiye da haka zan mata idan bata fita sabgata ba", ihu mazan ajin da wasu daga cikin matan suke suna cewa "sai kinyi Rabi'a, wallahi muna yinki, kin haɗu", komawa wajen zamanta tayi, su kuma ƙawayen Hanan suka jata zuwa clinic, 





Suna shiga kasancewar ansan wace Hanan duk sai aka ruɗe ana faɗin "garin yaya meya same ta?", ɗaya daga cikin Ƙawayen ta ne ta faɗi ƙarya da gaskiya, nanfa labari ya karaɗe makaranta wata ta kusa kashe Hanan, shugaban Makaranta hankali in yayi dubu ya tashi, har Clinic  ɗin ya nufa, ya tambayi abin da ya faru, nan ma aka maimaita masa, ba shiri yasa aka ƙira masa Rabi, hankalin ƴan aji duk ya tashi dan sun san kora ce za'aiwa Rabi, ita kuwa ko gezau haka ta nufi Ofice ɗin Principal, gaba ɗaya malamai suna ciki, yawancin suna cikin tashin hankali, dan suna tsoron Defuty yasan da wannan ya cire tallafin da yake basu, "Kece Rabi'a Umar ko?", cewar Principal, cikin dakiya da rashin tsoro ta ce "yes sir  i am", "meya sa kikayi duka  ga Hanan Abdussalam?", 



"Sir tsokana ta tayi ban kula ta ba, tinda nazo take talakata", Rabi ta faɗa, "shine kikai niyyar kashe ta saboda bakya son ganinta ƙyashi da hassada sun rufe miki ido, kina neman kashe Ƴar mutane?", cikin mamaki ta furta "kisa kuma?", cikin tsawa ya furta "yes kisa", kai ta fara girgizawa ƙwalla na taruwa a idanunta, hankalinta ya tashi ita tunaninta ma Hanan ɗin ta mutu sanadiyyar fashewar goshin ta, cikin kuka ta fara musu bayanin abinda ya faru, basu bari ta gama ba, suka hau zaginta da cin mutumci a gareta, cikin su idan ka cire English teacher ɗinsu Samual, Malama Khadija da Malam Mubarak, su kaɗai ne basu ce komai ba dan sun san Hanan batada kunya, kuma dole ita ce ta tsokani Rabi'a, amma kowane malami zagin Rabi yake sa bo da kuɗin da ubanta yake cika musu aljihu da shi, Rabi kam tasha kuka, nan take Principal ya ƙira Daddy akan yazo suna son ganinsa yanzu.





Hanan kuwa tana Clinic ana ta riritata har kayan ciye-ciye aka tulo mata, sai faɗi take ita a ƙira mata Dad ɗinta, sai haƙuri ake bata kamar za'a goya ta, dan jinsu suke kamar su mayar da ciwan kansu.






Daddy da yake zaune cikin katafaren Ofice ɗinsa tabkeke da yaji kayan alatu kai kace Ofishin shugaban ƙasa ne, ya tsaru iya tsaruwa, Muhammad ne a zaune yanai masa bayani akan takardun da yasa shi ya amso masa gurin wani abokin cinikayyarsa, "Daddy yanzu fa Campanoninka sunkai guda goma, biyar a nan Nigeria biyar a mabanbantan ƙasashe, kai da Hamma Saheeb na rasa wanda yafi wani kuɗi a cikin ku", Daddy ne yayi murmushi ya ce "to ko zamu tattaro maka Dukiyar ka ƙirga mana ne, kaga sai ka bambamce", ya faɗa cikin zolaya, ɗan zaro ido Muhammad ya yi ya ce "wa ni Daddy, ai saina shekara ban ida gamawa ba, nikam barni da karatun dana ɗakkowa kaina, na fannin lafiya ma ya ishe ni, ku dai kuji da wannan", dariya Daddy ya hau yi, ƙira ne ya shigo wayar Daddy ganin daga Principal ne ya sa shi ɗauka, bayan sun gaisa "yawwa Alhaji Rabi'u muna gayyatar ta zuwa Makaranta yanzu dan Allah idan babu damuwa", "ok babu damuwa yanzu zan shigo in sha Allah", katse wa yayi ya kalli Muhammad tare da miƙewa ya ce "Makarantar su Rabi'a ne ake nema na, Allah dai yasa lafiya?", Muhammad ma miƙewa  yayi ya ce "muje Daddy, in sha Allah lafiya ƙalau", fita sukai driver ya jasu zuwa  Queen Elizabeth.






Spain


Hamma Saheeb cikin fararen ƙananun kaya masu kauri kasancewar ana cikin cool weather, rigar da yasa mai hula ce, kayan sun amshi jikinsa, zaune yake farfajiyar gidan sa dake nan Spain ɗin, waya ya ciro dan ƙiran Mammy dan kusan kullum saiya ƙira ta, tana shiga ya shagwaɓe kamar yana gaban ta ya ce "Mammy bakya kewa ta ko, naga ma kamar kin dena sona yanzu keda Daddy", murmushi mai ƙawa Mammy tayi ta ce "Son baka ga dai-dai ba, muna sonka da gaba ɗayan zuciyar mu, kaine root of our family fa, kaga kuwa idan bakai babu mu Son, fatan kana cikin ƙoshin lafiya?", cikin jin daɗin kalaman Mammyn nasa ya ce "Mammy ina lafiya sai dai kewar ku, ina Auta ne kwana biyu ban ji ɗuriyarta ba, idan na ƙira bana samun ta", 




"Kausar kam Exam ta ɓoye ta, dan wayar na ƙwace dan tayi karatu sosai, tana lafiya yanzu ma ta tafi School ɗin", Mammy ta faɗa.




"Allah ya bada sa'a, Muhammmad ya ce min satin gaba zai wuce India, Mammy ya zancen Abdul ne, Daddy ya ce da tare zai haɗa su su tafi shi da Muhammad, ya kuma naji zai tafi shi kaɗai?", "Eh tare zasu tafi suprise zaiyiwa Abdul ɗin, an gama komai na tafiyar tasu", "Masha Allah, Allah ya taimaka ya basu sa'a", cewar Saheeb.




"Saheeb", Mammy ta ƙira sunansa, yana jin haka yasan akwai abu mai muhimmanci da zata faɗa, dan bata fiye ambatar sunansa sai zasuyi magana mai muhimmanci, amsawa yayi tare da tattara hankalinsa wajen ta.




"Saheeb kana tambayar kowa amma baka tambayar amanar ka", cewar Mammy.




"Mammy wace Amana ta kuma?", "ok ka manta, to matarka nake nufi, Saheeb kana wasa da wannan auren naka, nasan shine dalilin tafiyarka, ƙyaleka kawai nayi, amma ka sani Rabi'a amana take a gurinka idan har baka kula da ita wallahi sai Ubangiji ya kama ka, dan kawai ba zaɓin ka bace ba a ce kayi buris da lamuranta ba, dole Ƴar uwarka ce ko babu aure, balle akwai aure tsakanin ku, ka nutsu Saheeb dan Allah ka kula da Rabi kamar yadda zaka kula da Kausar",





 "Mammy Yarinyar nan fa bata ganin mutunci na, ko gaishe ni batai, kuma ko tsawatar mata bakwa yi, wallahi Mammy ko zancen ta bana so anai min, na tsani mara kunya a rayuwata", 




"Saheeb taya zata gaishe ka bata ganin fuska, haɗe face kake fa idan tana guri, kuma hakan ba yana nufin ba zata rainaka bane, saboda Rabi hakan baya tsorata ta sai dai ka janyo ta raina ka, kana ganin yadda suke da Muhammad tana girmama shi sosai, saboda baya haɗe face ɗin shi, ya kamata ka jata a jikinka Saheeb, dan Allah na roƙe ka", "Mammy duk naji kuma indai fannin kulawa ce zan mata duk abinda take so aimin magana zan turo kuɗi a siya mata, amma Mammy bana jin zanyi zaman aure da wannan Yarinyar, zan nemo matar aure nayi aure na, ita kuma zan cigaba da ɗaukar ɗawainiyar ta, amma gaskiya Mammy bazan zauna zaman aure da ita ba, dan har yanzu zuciyata ta kasa yarda da hakan, wallahi da zaku ce na sake ta sakin ta zanyi sai a aurawa Muhammad ɗin ita", 


"kai Saheeb ni kake gaya wa haka, kasan me kake faɗa kuwa, kana hauka ne, to wallahi karka sake Mahaifinka yaji wannan, ka bani mamaki wallahi", tana faɗar haka ta kashe wayar, hankalin Saheeb ya tashi dan baya son saɓawa Mahaifansa, ji yayi ya ƙara tsanar Rabi haka kurum tazo tana haɗa shi da Iyayensa, ƙara ƙiran wayar Mammyn yayi harta katse bata ɗauka ba, haka ya haƙura, amma zuciyarsa babu abinda take sai aunawa Rabi zagi.







Nawwara da Kareena wadda fuskarta tasha bleaching ga ƙuraje duk sun feso mata kana ganin shigarta da kuma yanayin ta zaka san ƙwanƙwararriyar ƴar bariki ce, dan a girme ta girmi Nawwara nesa ba kusa ba, "ki kwantar da hankalin ki Nawwara kamar kin samu Saheeb kin gama, zamu je wani guri anjima dake na tabbata daga yau komai zai zama ke kike juyawa", cewar Kareena, rumgume ta Nawwara tayi tana farin ciki "kai amma nagode Aminiya ta shi yasa duk wani abu daya dame ni na gaya miki yake zama tarihi", murmushi Kareena tayi irin na an yabe ta ɗin nan, saida yamma suka fita a motar Nawwara Ƙauyen Tsakuwa suka nufa, suna isa wani daji tace "tsaida motar anan, kinga wancen dutsen?", Kareena ta faɗa tana nunawa Nawwara, "eh na ganshi", "yawwa to nan zamu hau", zaro ido Nawwara ta yi ta ce "mu hau kuma kinga fa yadda yake taya zamu hau?", "ok to mu koma saiki zauna da damuwarki, amma ki ajiye damuwarki ke kaɗai karki kuma gaya min", Kareena ta faɗa ranta a ɓace.



"haba ƙawata kiyi haƙuri",  Nawwara ta faɗa tana kashe motar suka fito, sunci uwar tafiya sannan suka nufi ƙaton dutsen, haurawa suka fara Nawwara ta gaji iya gajiya, bata taɓa tafiya haka ba, ita kuwa Kareena da gani ta saba, saida suka isa tsakiyar dutsen Kareena ta ce su dakata, tsayawa sukai Kareena ta taƙarƙare ta zunduma ihu har sau uku, Nawwara zata keta a guje Kareena ta damƙota, cikin ɗaga murya Kareena ta ce "Ɗan ƙundun uba, tsinanne uban tsinannu, la'ananne uban la'anannu gamu gare ka, Boka uban Bokaye, kafisu kafi waninsu, kaike sa ɗan wuta bin hanyarsa, babu maija da kai ya Boka Sarmadan", tana rufe bakinta, wani hayaƙi ya turnuƙe wajen, tare da ƙwantsama wata ƙara mai firgitarwa, Nawwara kuwa ta jiƙa wandonta da fitsari yafi sau biyar, jikinta kuwa sai karkarwa yake, idanunta sunyi wiƙi-wiƙi,




Wannan hayaƙinne ya dishashe saiga wani mutum ɗan ƙarami a gaban su, kamar jariri amma fuskarsa ta manya ƙatuwa ga ido mici-mici jajawur, kannan sol kamar ba a halicci gashi a jiki ba, kunnensa kamar funkaso, hancinsa botarere kamar tukunya, bakinsa kuwa kamar da wuƙa aka yanka shafcece, dariya ya kece da  ita ya ce "yaku la'anannu nasan me yake tafe daku, akan Saurayin ki ne da baya kula ki baya sonki ke kuma kina son shi, sannan yayi aure yana da mata yanzu haka, sai dai ki sani ko kaɗan baya son matar da aka aura masa, hasalima bata gabansa, Iyayensa ne suke son auren, yanzu dai ki faɗa me kike so ayi akai?", cewar Boka Sarmadan.




Mamaki ne ya cika Nawwara jin ya jero abinda suka zo su faɗa masa, "Allah gafar....", "keeee la'ananniya ba a ƙiran sunan Allah anan, dan ba hanyarsa kika biyo ba, dan haka ki kiyaye!!!", ya faɗa cikin tsawa.



"zan kiyaye Boka, ina so ne asa shi ya soni, kuma ya aure ni",  cewar Nawwara, "an gama tsinanniya aikinki zai tabbata, zan baki wani ruwa ki bashi yasha a abin sha, karki sake ki kuskure dan idan wani yasha akwai matsala", "tom boka amma baya ƙasar nan, taya zan bashi ya sha?", eh zamu sa shi ya dawo, sai kiyi amfani da wannan dama ki bashi ya sha", Kuɗi mai yawa ta  ɗakko zata bashi nan ma tsawa ya daka mata "ba'a biyanmu sai abu ya tabbata, ku tashi ku bar nan dan Ƙundin ubanku", saurin miƙewa sukai, kafin su farga ya ɓace ɓat.




"Kai amma wannan Bokan ya iya aiki, ki duba fa cewa yayi ba'a biyansa sai aiki yayi", cewar Nawwara, murmushi Kareena tayi ta ce "bana gaya miki ba, yanzu dai ba wannan ba, naji bakiyi masa zancen Yarinyar ba", "kina ji ya ce Yarinyar bata gabansa, kinga kuwa banida damuwa da ita yanzu", kai Kareena ta jinjina, da haka suka baro Ƙauyen Tsakuwa.







Su Daddy suna isa Ofice ɗin Principal suka nufa, nan suna ga malamai fal a Ofice ɗin, Rabi na ganin Daddy ta nufo shi a guje ta faɗa jikinsa tana kuka mai cin rai, Daddy da Muhammad nan take hankalinsu ya tashi, Muhammad faɗi ya ce "Rabi'a mene meya faru?", kuka ya hana ta magana, wajen zama aka bawa Daddy da Muhammda suka zauna, sosai Daddy yayiwa su Principal kwarjini, Daddy ne  ya ce "lafiya Principal meya faru?", Rabi na jikinsa tana kuka, duk jikinta da ɗau zafi sanadiyyar zazzaɓin daya rufe ta, Principal ne ya ce "wato Alhaji Yarinyarka ce tayi yunƙurin kisa, da badan Allah ya taƙaita ba da tuni wani zancrn ake ba wannan ba", "what kisa?", Daddy da Muhammad suka haɗa baki wajen faɗa.




"Eh wallahi Yallaɓai, Yarinyar Defuty ta lakaɗawa shegen duka yanzu haka tana Cilinic bata san wanda yake kanta ba", cewar wani tsamurmurin malami.




Rabi kuwa kai kawai take girgizawa, Muhammad kuwa cewa yayi "kai inaa Rabi ba zatayi haka ba, ku dai canza wani rahotan", Daddy ne ya ɗaga masa hannu, Rabi kuwa a gigice ta ce "wallahi Daddy ban kashe kowa ba, ita ce ta tsokane ni, tinda nazo take takala ta kullum idan nazo, shine yau.....", nan ta labartawa Daddy komai, nan take ya fahimci saboda an taɓo Ƴar Defuty ake so a nuna shi ba komai bane, Ransa a ɓace ya ce "a rakani Clinic ɗin naga Yarinyar, Principal zai hana Daddy yayi saurin fita a Ofice ɗin, Muhammad ya bi bayansa, da kwatance aka kaisu, suna shiga Nurses ɗin suka miƙe daga gaban Hanan da duk ta ishe su da abata kaza a bata kaza, Daddy ne ya ce "ina Yarinyar da aka kawo?", wata Nurse ce ta nuna masa Hanan da take danna waya hankali kwance, "wannan ce Yarinyar da akai yunƙurin kashewar?", Muhammad ya tambaya rai ɓace, shuru sukai, Hanan kuwa ganin mutane a kanta yasa ta ɗago ta kalle su tayi wuri-wuri, Daddy ne ya ce "sannu kinji, meya haɗa ku da Rabi'a?", ganin kwarjinin Mutumin yasa Hanan nutsuwa, nan ta gaya masa komai bata yi ƙarya ko ɗaya ba, ta sanar dashi ita ce take tsokanar Rabi, Daddy bayan ya saurare ta ya ce "Yarinyata  ku dena faɗa a makaranta kinga karatu ne ya kawo ku, bai kamata ace haka tana faruwa da ku ba, karna sake jin kunyi faɗa daga yanzu, kuyi abinda ya kawo ku", amsawa Hanan take da to, Rabi kuwa jikinta duk yayi wick dan sosai jikinta ya zige da zazzaɓi, Daddy ne ya ce "daga yau ku zama Abokai, kuma ku bawa juna haƙuri", Hanan ce ta taso ta miƙawa Rabi hannu ta ce "kiyi haƙuri Rabi'a", hannu Rabi ta miƙa mata sukai musabiha, amma bata bata haƙuri ba, Muhammad dama yasan za'a rina dan yasan Rabi dai ba zata bada haƙuri ba, Hanan kuwa jin hannun Rabi da zafi nan take ta ƙwalalo ido ta ce "fever sis, bakida lafiya dama?", ta faɗa cikin kulawa, sai lokacin Daddy ya farga da yadda take komai a slow, hankalin Daddy da Muhammad ne ya tashi, Nurse ne zasu riƙe ta dan bata magani Daddy ya ce "No ku ƙyale ta Asibiti zan kaita", duk Hanan ta shiga damuwa dan tasan ita ce silar hakan, kuka ta saka sosai saita bisu, Daddy ne ya bata haƙuri ta zauna, wannan lamari Principal da muƙarrabansa suka zo suka taras, Daddy ko inda suke bai kalla ba, sai rarrashin Hanan yake ganin duk ta ɗaga hankalinta akan Rabi, kunya dosai Principal da Malamai suka ji, haka Daddy suka tafi da Rabi Asibiti ko takan Shugaban Makarantar bai bi ba, dan ransa ya ɓaci sosai.







Asibitin MDS suka nufa private ne suna zuwa aka karɓe ta dan sun san DADDY sosai, saida likitan ya tabbatar ta samu bacci ya fito, ruwa ya sa mata tare da allurar kashe fever, yana fitowa ya sanar dasu Daddy tana farkawa za'a dawo dai-dai, saida tasha Baccinta tana farkawa ta ce ita Mammy, Likita ne ya sallame su, dan jikin nata yanzu babu zazazzaɓin, gida suka tafi bayan an haɗa su da magunguna.






Wannan kenan





*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*







*By Rumyn Royal Star*





A taya ni sharing fisabilillah👏






*09130984617*



*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 53-54*

>>>>>>>>>>>>>>Suna komawa Mammy da tayi mamakin ganin su tare da Rabi, tambayar Daddy tayi shi yayi mata bayanin abinda ya faru, ita ma ranta ya ɓaci sosai, har tana ikirarin a canza mata makaranta, Daddy ne ya ce "ai Nafisa babu batun canza Makaranta, su kansu yanzu a cikin jin kunya na baro su, wannan kaɗai ya ishe su, sannan saina nunawa Principal kuskurensa wallahi", da alama ran Daddy ya ɓaci, Rabi kuwa Mammy da kanta ta taya ta ta cire kayanta, ruwa mai ɗumi ta haɗa mata ta taimaka mata tayi wanka, kunun gyaɗa da yaji madara Mammy ta bawa Rabi tasha da yawa sannan ta kwantar da ita, sai da taga ta fara bacci ta baro ta, Kausar tana Makaranta saida ta dawo ta tarar da Rabi ba lafiya, Mammy ce ta bata labarin abinda ya faru, Kausar ma buɗar bakinta cewa tayi a sauya mata Makaranta tinda abin nasu haka yake.




Sai can wajen la'asar Rabi ta farka, yanzu jikin sosai taji sauƙin sa, fitowa tayi, a falo ta tarad da su, jikin Mammy taje ta kwanta sai sannu suke mata, suna tambayar ta ya jikin ta, rau-rau tayi da ido ta ce "Inna nake so naje Mammy, dan Allah a kaini naga Inna da Baba", Mammy ce ta hau rarrashi, Daddy ya ce "haba Rabi'atu na, ki bari idan akai hutu za'a kaiki kinji ko, ki bar kuka, idan ma ni kike so na kaiki da kaina zan kaiki", cikin rarrashi yake mata magana, daƙyar tayi shuru, sai da Muhammad da Kausar suka ce zasu fita da ita gobe su kaita *Roxy* ɓangaren wasanni, sannan tayi shuru, haka dai sukai ta janta harta saki ta fara dariya, sannan hankulansu ya kwanta.





A Makaranta kuwa rigima Hanan tasa sai tabi su Daddy taga halin da Rabi take ciki, sai haƙuri ake bata ana rirriƙeta, Principal kuwa haushin ta yake ji, da sauran malamai, dan ƙaryar da suka shuka a kanta tasa su jin kunya matuƙa, dan Principal a ransa faɗi yake "ban san taya zan ƙara kallon idon Alhaji Rabi'u ba dan gaskiya na kwafsa da yawa", wannan tunanin yake ta yi.




Hanan kasa zaman Makarantar tayi drivern ta aka ƙira  yazo ya tafi da ita sai kuka take.




Duk wannan abu da ake Saddiƙa bata sani ba, hankalinta a tashe yake jin Rabi shuru, ga shi ba damar zuwa, sai da aka kusa tashi ƙawayen Hanan suka shigo Class ɗin anan Ƴan aji suka san meya faru, Saddiƙa jin Rabi ba lafiya nan hankalinta ya ƙara tashi, sai dai tayi farin cikin jin ba'a kori Rabi ba, haka dai aka tashi kowa ya nufi gida, Saddiƙa kamar zatai kuka, sanin cewa bata san gidan su Rabi ba da taje ta duba ta, School bag ɗin Rabi tana gurin Saddiƙa da ita ta tafi.






Cikin farin ciki Nawwara ta koma gida, bayan ta sauke Kareena a gidan su, Mom dake falo tana waya da wata abokiyar business ɗinta ce ta ɗago jin Nawwara na rafka sallama, katse wayar tayi bayan sun ƙare, duban Nawwara tayi ganin farin ciki fal fuskarta ta ce "wata sabon gani, yau kece da wannan farin cikin, me muka samu?", jikin Mom Nawwara ta faɗa ta ce "Mom ina cikin farin ciki yau, na kusa samun abinda zuciyata ke muradi, ina daf da yin aure Mom",



Mom dake mata kallon mamaki ta ce "to ikon Allah, kice nayi Suriki ban sani ba, wane ɗan sa'ar ne wannan?", 



"kai Mom kinsan fa wanda nake nufi, ni kuwa wa zanso bayan shi, Ya Saheeb Mom, ina daf da mallakarsa, zai dawo tafin hannu na sai yadda bayi dashi, zan juya shi kamar waina a tanda",



"Ban gane ba, kina nufin kice ya amince ya amshi soyayyarki?", cewar Mom




"Hmmm Mom abin sirri ne, ke dai ki fara shirin aurar da Nawwaranki",



"To aishikenan, zan kuwa fara shiri, auren Auta ai ba'a magana", Mom ta faɗa cikin annashuwar ganin Ƴarta ta cikin farin ciki.




A wannan Ranar ne NAWWARA tayiwa Club dirar mikiya, tasha giya tayi tatul, tayi ɓarin kuɗi kamar a bola ta samo, Shamsuddeen kuwa ranar ya more ta son ransa, ya samu yadda yake so da  ita, ranar tare suka kwana, Mom kuwa ta jira dawowarta shuru, ta ƙira wayarta tana ringing amma ba a ɗauka, Hafeez ma baya gida bai dawo ba, haka Mom ta kwana ko rintsawa batai ba, sai bayan sallar Asuba bacci ya kwashe ta tana kan sallaya.





Sai wajen 11:45 Am ta tashi babu sallah babu salati, babu komai a jikinta sai blenket ɗin da ya rufe ta da shi, hasken ranar daya ratso daga window ne ya haske mata fuskarta, buɗe idanuwanta tayi ganin da tayi ba'a bed ɗinta take ba hakan yasa ta ware idanunta, waige-waige take idanunta ne ya sauka akan fuskar sa, gane abinda ya faru tayi ta ja tsaki, tashi tayi babu komai a jikinta ta nufi toilet wanka tayo ta fito da towel ɗaure a jikinta, yana kwance har yanzu bai farka ba, kayanta ta saka babu batun yin sallah ta ɗauki jakarta, da wayarta, duba wayar tayi taga miss call wajen saba'in da ɗoriya, mafi yawa na Mom ne, tsaki tayi ta ɗauki key ɗin motar Shamsu ta fice, a ranta ta ce "kasan yadda zakai ka koma gida".





Tana komawa gida bedroom ɗinta ta nufa ta ƙara yin wani wankan ta saka mini sket da ƴar riga iya cibiya, kalbar gashin dokin kanta ya sakko har mazaunanta, ƙaton bluetooth ta saka a kunnenta ta fito ta nufi kitchen, ƴar aikinsu dake aikin haɗa breakfast ce a tsaye tana fere dankalin turawa, cikin isa da garada Nawwara ta ce  "ke ki haɗa min coffee da pizza ki kawo min yanzu" tan faɗa ta juya tabar wurin, cikin sauri ta haɗa mata komai dan dama akwai pizza ɗin, kai mata tayi tana hakimce a falo da shigarta ta arna.





Mammy dake bacci kan Sallaya ce ta farka, saurin tashi tayi, ta ɗauki wayarta ta ƙara ƙiran Nawwara aikuwa bugu uku ana huɗu ta ɗaga, "Kina ina Nawwara tin jiya baki kwana a gida ba, ina kuma ƙiran ki baki respond, ina kika je?", dariya Nawwara ta kece da ita kafin tayi shuru, Mom kuwa mamakin dariyar take, Nawwara ce ta ce "haba Mom wannan tambayoyi birjik haka ki tsaya ko numfashi ki shaƙa mana, kuma ni babu inda na kwana ina cikin gidan nan, tin jiya, hala baki duba Room ɗina bane?" abinda yasa Nawwara tace haka saboda tasan Mom bata shiga ɗakinta, 



"Kina nufin kice kina gida a gida kika kwana?", "yes Ma yanzu ma haka ina falo banganki ba", Nawwara ta bata amsa, ajiyar zuciya Mom ta sauke kana ta katse ƙiran, wanka ta shiga ta shiryo cikin Atamfarta super tayi kyau cikin riga da zani, sai baɗa ƙamshi take, a falo ta taradda NAWWARA, kuma sosai ta yarda da ƙaryar da Nawwara ta shuka mata.







Hanan a hargitse ta je gida, yau ko bari escort ɗinta ya buɗe mata motar batai ba, ta buɗe ta nufi gida a guje tana ƙwala ƙiran "Aunty!!! Aunty!!!", wata mata ce zaune a katafaren haɗaɗɗen falonta da yasha kayan more rayuwa masu tsada a zaune kana ganinta zaka ga kamar da suke da Hanan kamar an tsaga kara, sai dai ita wannan ta manyanta, ganin Ƴarta na gurzar kuka, ga kanta da plasta, hankali tashe ta miƙe tare da taro Hanan, "Ya salam Hanan meya same ki, ya akai kika ji ciwo haka, kukan me kike?", lokaci guda ta jero mata wannan tambayar, cikin sakalci daya zame mata jiki ta ce "Aunty muje mu duba ta dan Allah, nice na sata zazzaɓi wallahi, Aunty bakiji jikinta ba zafi sosai, Aunty muje gidan su dan Allah kinji", sosai take kuka har muryarta ta dashe, Aunty kuwa hankaki a tashe ta ce "Hanan wace wannan?, meya faru? ki gaya min", ruwan sanyin kusa da ita ta tsiyayo ta bata tasha ta ce "yawwa ki nutsu my baby, ki sanar dani meya faru?", ajiyar zuciya Hanan ta shiga saukewa bayan ta shanye ruwan  ta ce "Aunty batai min komai ba, nice nake yawan tsokanarta da faɗa amma bata taɓa kulani ba, shine yau..........", nan ta labartawa Aunty komai.



"Hanan na sha gaya miki takalar rigima babu daɗi wataran zaka tsokano wanda ya fika ƙarfi, jibi yadda taji miki ciwo, sannan ke kuma kin haɗa rigima a school, gashi kin janyowa ƴar mutane fever, wannan duk bashida amfani, ki nutsu kiyi abinda yakai ki makaranta ba neman faɗa da mutane ba", cewar Aunty.



"Aunty to nidai muje gidan su na bata haƙuri", 



"taya zamu gidan su bamu san gidan ba", kuka Hanan tasa harda ihun ta, ganin haka Aunty ta ce "to idan kukan ki ne zai kaimu gidan kita yi",



"Aunty ni kisa a gano gidansu muje", haka tasa Aunty a gaba saida ta ƙira Principal, ta tambaye shi akan Rabi da inda take, nan ya gaya mata Mahaifinta ma fitacce ne, Alhaji Rabi'u, ta sanshi sosai, dan duk wani sha'anin su idan ya tashi a companynsa ake musu Atamfofi, sai bayan magriba suka shirya tare da escort ɗinsu suka nufi gidan Alhaji Rabi'u.






Kafatanin Iyalen gidan Alhaji Rabi'u suna zaune a falo suna hira, Rabi tana kwance kan cinyar Mammy, zancen tafiyarsu Muhammmad ake shi da Abdul zuwa India, sai lokacin Kausar da Rabi suka san tare da Abdul za'ai tafiyar, Rabi sai jin daɗi take Hammanta zashi India karatu, dan shi kuma  ɓangaren Engeneer yake zon zama, suna a haka Maigadi yayi sallama, izinin shugowa Daddy yayi masa "Yallaɓai kunyi baƙi daga gidan Defuty, Matarsa ce da Ƴarsa", mamaki gaba ɗayansu sukai, ita kam Rabi bama tasan me ake nufi ba tana ta murnarta na labarin da taji na zuwan Hamma Abdul India, Daddy ne ya ce "ok kace su shigo", amsawa yayi gamida fita, suna zaune Aunty tayi sallama hannunta cikin na Hanan, amsa mata akai cikin sakin fuska, bayan sun zauna Mammy ta ƙira mai aiki ta kawo musu drinks haɗi da kayan motsa baki, bayan sun gaisa Aunty ta ce "kuyi haƙuri kunga baƙi babu sanarwa kuma da daddare", Daddy ne ya ce "a haba babu komai, ai nikam ku ba baƙi bane dan ga Ƴata nan a gefanki ita ai na shaida ta, ya ciwan naki?", ya faɗa yana kallon Hanan,



Haka kurum Hanan ta tsinci kanta cikin jin kunyar mutanen wajen, Mammy ta ce "au kardai ita ce suka samu hatsaniya tsakaninta da Rabi'a?", Aunty ce ta ce "wallahi kuwa Mammyn Rabi'a, munzo ne mu bada haƙuri, tinda ta dawo hankalinta a tashe ta ce sai tazo taga jikin Ƙawar tata, dan Allah ayi haƙuri sha'anin Yara sai su, tayi min bayanin komai kan cewa ita ce da laifi", Mammy ce ta ce "haba baiwar Allah, ai kowa yasan Yaro, shi yasa ma ba'a shiga faɗan su, wallahi komai ya wuce, Allah ya shirya mana su", da ameen suka amsa, Hanan ce ta taso ta matso inda Rabi take ta kama hannuwanta ta marairaice ta ce "am so sorry dear, bazan kuma yin abinda nayi ba, ki yafe min", Rabi ganin yadda Hanan tayi yasa taji tausayinta "na haƙura, ya ciwanki?", ta faɗa yana kallon goshin Hanan, "da sauƙi ya jikin ki kema?", Hanan ita ma ta tambaya tana taɓa wuyan Rabi, "da sauƙi na warke", cewar Rabi.



Hannu Hanan ta miƙawa Rabi alamun su gaisa ita ma miƙa mata tayi Hanan ce ta ce "Now we are friend, no fight no hostility", kai Rabi ta girgiza alamun amincewa, su Muhammad da Kausar ne suka hau tafi, su Daddy ma suka ɗauka, abin ya birge su, basu jima ba, suka tafi su Mammy sukai musu rakiya har bakin mota sannan suka dawo, Aunty da kanta ta amshi number ɗin Mammy dan su dinga gaisawa, bayan sun dawo ciki mai gadi ya shigo musu da ledoji niƙi-niƙi da kayan dubiyar Rabi, Rabi kuwa ko takan kayan bata bi ba ta nufi dining dan cika timbinta da tuwon semo da miyar kuɓewa ɗanya da taji nawan ƙaramar dabba.







SPAIN



Saheeb daga jiya zuwa yau jiyai hankalinsa gaba ɗaya yayi gida, babu abinda yake so illa yaji shi ya sauka a ƙasarsa ta haihuwa, nan take yayi booking flight ɗin ƙarfe sha biyu, a gurguje ya kammala shirinsa ko gida bai sanarwa ba ya hau jirgi sai Nigeria.





Kasancewar yau lahadi kowa yana gida har Daddy, Rabi kuwa yau sha'awar goba take ammaa Mammy ta hana ta zuwa wajen bishiyar, ta ce ta bari zata sa a tsinko mata, ga ƙafar Rabi ƙaiƙayi take mata.







Saheeb ƙarfe uku da rabi ya sauka a filin jirgi na Abuja, wani jirgin ya hau wanda zai tashi ƙarfe huɗu zuwa Kano, aikuwa bai jima ba jirgi ya cika suka nufo Kano, taxy ya hau sai gida, biyar ce tayi masa a ƙofar gidan su, bayan ya sallami mai taxy ya ƙwanƙwasa ƙofa, maigadi ya leƙo ganin ƙaramin mai gida ya sashi saurin buɗe ƙofa, yana masa  barka da zuwa, amsa masa yayi ya nufi side ɗinsa dan ya gaji so yake ya watsa ruwa yaji daɗi sannan ya nufi side ɗin su Mammy, dai-dai wannan lokaci kuwa Rabi tana kan bishiya ta ɗare abarta sai tsinko Goba take tana sha, idan ta tsinko wata taga ba'a nune take ba saita jefo ta ƙasa, Hamma Saheeb daya nufi side ɗinsa wanda dole saiya dangana  ta jikin bishiyar gobar zai wuce dai-dai ya zo zai gibta bishiyar dai-dai nan Rabi ta jefo wata ƙatuwar goba wadda ta gatsa taji babu zaƙi shine ta wullo, aikuwa sai a dokin wuyan Hamma Saheeb, sosai yaji zafin wannan jifa, ya sunkuya dan ganin abinda ya faɗo ya ƙara jin saukar wata a gadon bayansa, bishiyar ya ɗaga kai ya kalla, dai-dai nan ita ma taji motsi ta kallo ƙasa, aikuwa karaf idanunsu suka shiga na juna, zaro idon tayi shima cikin kaɗuwa ya zaro nasa, hakan yasa dukansu suka bawa juna tsoro, ihu tasa shima ihu yasa dan dole ma ya tsorata, dan ya manta da Rabi da kamarta, sannan yanzu daga zuwansa yaga mutum akan bishiya, ga duhun magriba ya kawo kai, ga ido manya-manya an zaro masa, ga bakinta duk abin goba, wannan yasa shi tunanin gamo yayi, ita ma kam bilhaƙƙi ta firgita, wannan dalili ya sasu ihu lokaci guda.✍️







Wannan kenan





*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*





*By Rumyn Royal Star*




*09130984617*



*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 55-56*

>>>>>>>>>>>>>>Ruƙumƙume reshan da take kai tayi ta rintse ido tana rusa ihu, Hamma Saheeb side ɗinsa ya nufa a guje ya shiga ya rufe ƙofa, ita kuwa saurin buɗe idonta tayi ganin ba kowa a wajen ta tsorata ta sakko ta nufi side ɗinsu, ta kusa yin karo da Mammy data fito nemanta, sai hakki Rabi take, Mammy ce ta dube ta ta ce "daga ina kike? bana hana ki guje- guje ba Rabi'a", "Mammy aljani na gani a lambuncan wajen bishiyar nan", 


"ok bayan na hana ki saida kika je ko?,  saboda kar nayi miki faɗa shine zaki ce  kinga Aljani", "Mammy Allah Aljani ne, yana gani na ya fara ihu, kuma suna kama da wannan babban na nan gidan wallahi", Mammy ganin shirmen na Rabi ne yau ya motsa ta ce "maza jeki lokacin sallah ya gabato kiyi alwala, tafiya tayi tana tunanin aljani mai kama da Hamma arne, alwalar tayi ta fito daga toilet ɗin a guje dan kar Aljanin ya bayyana.





Shi kuwa yana shiga ya sauke ajiyar zuciya, yana tunanin gamon da yayi, ransa yaji duk ya ɓaci, tsoron side ɗin nasa yaji yana ji, da hanzari ya kunna karatun alƙur'ani a wayarsa nan take yaji nutsuwa ta shige shi, wanka yayi ya canza kaya, wankan da ya tsaya yi ne ya ɓata masa lokaci har aka idar da sallar magribar, a ɗakinsa yayi sallar, bayan ya idar ya miƙe ya nufi ɓangaren su Daddy, lokacin daya hango bishiyar nan a guje ya wuce wajen yana a'uziyya.





Suna falo suna jiran a gama haɗa abincin dare, Rabi ce ta shigo falon da shigarta ta ɗazu, siket da riga ya kanti, gaishe da su Daddy tayi dasu Hamma Muhammad da Kausar, dan ɗabi'ar gidan ce duk sanda sukai salla sai sun gaisa, wannan ma nau'in tarbiyya ne, ta zauna kenan sai ga Hamma Saheeb, babu wanda bai masa kallon mamaki ba, Rabi da tayi suman zaune ganin kamar da suke da aljaninta na ɗazu, shi kuwa bai kula da ita ba, Daddy ne ya ce "kai saukar yaushe haka babu sanarwa?", dariya Hamma Saheeb yayi ya ce "Daddy mamaki nake so na baku kuma gashi na bayar", Muhammad ne ya matso gefansa yai hugging ɗinsa, Kausar ma cikin farin ciki ta ce "sannu da zuwa Hamma", amsa mata yayi cikin sakin fuska, Daddy kuwa cewa yayi "aikuwa ka bamu mamaki sosai", dai-dai nan Mammy ta shigo falon ganin Saheeb ya sata sakin baki da ido "Son kaine?", ta tambata da mamaki "yes Ma nayi kewar ku shine na dawo dan na ganku, fatan na same ku lafiya", "lafiya ƙalau ya hanya kuma", cewar su Daddy, amsa musu yayi cikin farin ciki, "Doughter bakiga Hamman ki ba ne babu sannu da zuwa?", cewar Daddy, bata kalle shi ba ta ce "sannu da zuwa Hamma", sai a lokacin ya kula da ita, sai yaga ta ƙara girma sai dai yaga kayan nan ɗazu daya dawo, tunanin kayan yake inda ya gansu, jin yayi shuru Daddy ya ce "kana ji tana maka sannu fa Son", "yawwa na same ku lafiya", ya amsa ba tare da ya ƙara kallonta ba, ita ma bata amsa ba, Mammy ce ta ce kuzo komai ya haɗu kan dinning", tashi sukai suka nufi dinning eria, Hamma Saheeb sai kallon kayan jikin Rabi yake yana son ya tuna, can Allah ya nufe shi da tuna gamon da yayi da aljana a kan bishiya, nan take ya gane ita ce wato ta tsorata shi, shin ubanme ya kaita kan bishiya?, kuma taya ta hau?, wannan tambayar yakewa kansa, ransa ne ya ɓaci tuna ihun da tasa shi harda gudu, "lallai wannan yarinyar sai na koya miki hankali, wato ni ta tsorata", a ransa yake ta wannan maganar, saida ya suka kammala suka nufi Masallaci, bayan sunyi sallah suka dawo, Hamma Saheeb ne ya ce "Mammy zani na kwanta dan Allah ki aiko min da black tea", sallama yayi musu ya fice, Mammy da  kanta ta haɗa masa tea ɗin ta ƙira Rabi ta ce "maza jeki ki kaiwa Hamman ki yana side ɗinsa", amsa tayi dan bata musu da Mammy amma da babu yadda za'ai ta je inda yake, bayan tana cike da shi, akan dukan da yayi mata,  haka ta nufi wajensa ƙofar a buɗe take tana zuwa ta shiga, baya falo hakan yasa ta ajiyewa a kan center table ɗin falon, ta juya zata fita taji ance "ke haka ake a garin ku idan an aiko ki ki ajiye abin aiken ki fice ba tare da kin sanar ba", ya faɗa fuska a murtuke, ƙoƙarin fita take bata bashi amsa ba, ya ƙara daka mata tsawa "keeee ba dake nake ba zaki fita baki bani amsa ba, sa'anki ne ni?", juyowa tayi ta harba masa harara ta ce "badai na kawo maka saƙon ka ba kuma ka gani", mamakin rashin kunyarta yake, taku uku yayi a fusace ya figi hannunta ta matse mata hannu sosai saida ta rintse ido kallon fuskarta yayi cikin hassala ya ce "ke kina jin ke wace da ina magana kina mayarmin da martani, wace iriyar mara kunya ce ke, to yau zaki gane kuranki wallahi, waima ɗazu kece akan bishiyar wajen cen?", idonta da sukai ja saboda azabar da hannunta ke mata saboda riƙon da yayi mata ta ce "ni wallahi ba mara kunya bace, kuma mai nayi maka da zaka min mugunta, wallahi saina gaya ka da Mammy", haushi da takaici ne ya rufe shi ganin ƙaramar Yarinya ta raina shi da girmansa da komai, "zan ɓalla ki wallahi, ki gaya musu mana, ki bani amsa wace a kan bishiya ɗazu?", ya ƙara tambayarta a fusace kamar zai mare ta "nice na hau zan ciro Goba", ta faɗa cikin azabar da take ji a hannunta, gashi ta hana kanta kuka, "ke ce kika hau saboda shaiɗanci, wato har hawa bishiyu kike saboda rashin sanin ciwan kai, wai kuma a haka wancen tsohon ya aura min ke a matsayin mata, na rasa mena tsarewa tsohon nan wallahi, ya rasa wadda zai haɗa ni da ita sai ke, jibe ki fa, wallahi na tsane ki tsana mara adadi bazan taɓa sanki ba ni na sani, kije kisa a raba auren da aka mamuƙa min da ke ", ya faɗa tare da wurgar da ita a wajen, kuka ne ya ƙwace mata, babu abinda yake mata ciwo illa hannunta daya riƙe, kalamansa sunyi mata girma, ta daiji kalmar aure, tsoho ya  haɗa aure, da  kuma kalmar na tsane ki, wannan su tafi riƙewa, but bata fahimci batun auren sosai ba, dan a lokacin batada buri sai na ya cika mata hannu, bata bar gurin ba sai da ta ɗaga murya ta ce "wallahi nima na tsane ka mugu azzalumi, wallahi saina rama arne kawai", a fusace ya tinkaro ta ta fice a guje,  komawa yayi yana jin haushin ta ce ta tsane shi "kai harni wannan tatsitsiyar zata ce ta tsane ni, harni zata ce ta tsana, mtsewww", ya ja tsaki ransa duk ya ɓaci.



(Ku jimin ƙarfin hali, wai tace ta tsane shi yake jin haushin kalmar a bakinta, wato ita da ka faɗa mata fa tayi yaya kenan,).





Mammy dake zaune tana jiran shugowar Rabi ta ganta a guje tana kuka riƙe da hannu, gurin Mammy ta nufo Mammy ce ta ce "subhanallah Rabi meya faru?", "Mammy shine fa ya murɗe min hannu saboda kawai na kai masa shayinsa na ajiye wai me yasa na ajiye, shine ya kwaɗamin mari kuma ya murɗe min hannu, ya ce ya tsane ni", ran Mammy ya ɓaci sosai, mammatsa hannun Rabi tayi tasa mata wani cream mai sanyi a wajen, ta rarrrashe ta ta je ta kwanta, Mammy kuwa ta rantse sai tayi maganin Saheeb.







Nawwara kuwa lokacin da taji Saheeb ya dawo kamar ta  zuba ruwa a ƙasa  ta sha, ba shiri ta nufi gidan su Saheeb da kwalbar ruwan da Boka ya bata, kwananta ɗaya a gidan ranar ta fito sai taji motsin su Mammy a kitchen shiga tayi "sannun ku Mammy", "yawwa Nawwara kin fito ne?", "eh Mammy", lemon abarba taga Mammy na haɗawa, sai zuba ƙamshi yake ta ce "kai Mammy wallahi daga ji drinks ɗin nan dole yayi daɗi", murmushi Mammy tayi ta ce "na Saheeb ne yana son wannan lemon, shine nake haɗa masa", farin ciki ne ya ɗarsu a wajen Nawwara jin faɗuwa tazo dai-dai da zama, zama tayi a kitchen ɗin,





Mammy ce ta fice Nawwara ganin ga dama ta samu yasa ta nufi bedroom ɗin Kausar ta ciro kwalbar ta nufi kitchen ɗin, tana zuwa ta buɗe kwalbar ta tsiyaya ruwan ciki ta rufe, tana gamawa ta fice, Rabi da take jin ƙishirwa ta nufo kitchen nan ta taras da Nawwara tana zuba abu cikin lemo, tana ganin lokacin datai sauri ta gama zubawa ta rufe ta mayar da kwalbar cikin zaninta, ganin zata fito yasa Rabi barin wajen a guje, tana tunanin abinda Nawwara ta zuba a cikin lemon, ruwan da  bata sha ba kenan, ta koma falo ta zauna, ganin babu kowa kuma bata yarda da Nawwara ba yasa ta koma kitchen ɗin ta ɗauki jug ɗin lemon ta fita dashi harabar gidan, zata zubar kenan driver ya ganta ya ce "a'a Rabi me zaki zubar haka kamar lemo, ai bani shi nan na shanye ba'ayi almubazzaranci ba, kafin tayi magana driver ya amshi jug ya ɗaga kai ya moɗa iya son ransa, magana take so tayi masa amma kamar an rufe bakinta, saida yasha sosai, ya ɗago kai ya ce "ke Ƴar nan yanzu wannan lagwadar zaki zubar, kinji masifar daɗin lemon nan kuwa?", ya faɗa yana shanye ragowar, tare da danƙawa Rabi jug ɗin, Rabi kuwa ƙurawa driver ido tayi taga yadda zai fara kakarin mutuwa, taga babu alamun wani abin, dan ita a tunaninta guba ce Nawwara da zuba a ciki, aikuwa da gudu ta mayar da jug ɗin, inda Allah ya taimaketa babu wanda ya ganta.




Mammy ce ta dawo kitchen ɗin tana dubawa taga babu lemo cikin jug, ƙara dubawa tayi kodai ba a jug ɗin ta zuba ba, "to wane ya shigo ya shanye lemon nan?", kai ta gyaɗa a ranta tana faɗin "ƙila Yaran nan ne suka shanye bari na haɗa masa wani", nan ta tsaya ta haɗa wani, ta ƙira Rabi ta ce "maza kaiwa Hamman ku yana side ɗinsa yana jira", karɓa tayi ranta baiso ba ta tafi, tana shiga ta taradda shi a falo yana kallo, sallama tayi a ciki, wannan ma dan sanin muhimmancinta ne yasa tayi, bai ji ba, yadai ga shugowarta, ajiye masa tayi ta nufi hanyar fita "ke zo", bata waiwayo ba kuma bata tsaya ba, "keee! ba dake nake magana ba?", ficewarta tayi a cewarta ai ba sunanta ke ba, hakan da tayi ba ƙaramin baƙanta zuciyar Saheeb yayi ba, cikin hanzari yabi bayanta, aikuwa cimmata yayi, ya danƙo ɗankwalin kanta ya sharara mata mari bata gama shanyewa ba ya ƙara mata wani, sannan ya hankaɗa ta, "har sau nawa zan gaya miki na tsani raini, kina ji ina ƙiranki zaki min banza, ko ni ɗin sa'an ki ne?", kuka take sosai dan marin ya shigeta over, bakinta harya fashe, dan marin na gawurtaccen namiji ne, hannunta ta duba taga jini  ihu ta saka "wallahi bazan yarda ba, wayyo Inna ta kizo za'a kashe ni, Babana kazo dan Allah ka tafi dani Hamma Abdul kazo ka taimake ni jini a bakina", bilhaƙƙi ihu take tana tumami, shi kuwa ganin zatai masa hauka yasa shi barin wajen, aguje ta bishi da wani dutsen kwangila da aka ƙawata wani waje da shi, inda Allah ya taimake shi ya shige ciki da babu abinda zai hana ta same shi, glass ɗin tagarsa ta kwantsame, ta ƙara ɗakko wani ta jefa saida ta fasa masa window har guda  biyu, ihu take bata dena ba tana faɗin "azzalumi mugu, arne kawai, in sha Allah sai Allah ya ƙona ka a wuta, Allah ya isa na", dai-dai nan Mammy, Nawwara da Kausar suka nufo wajen hankali tashe, Mammy ganin Rabi tana ihu a ranta tasan Saheeb ya zalumceta, kamo Rabi tayi ta rumgume tana faɗin "meya faru? ya isa kukan haka", sai a lokacin taga bakin Rabi a fashe, "kai meya same ki a baki?", "Mammy ni gida zani gurin Innata bazan zauna ba, kullum saiya dake ni ya zage ni bansan me nayi masa ba", kuka take sosai harda shan majina, Mammy ranta yau ya ɓaci matuƙa, inda yake ta nufa tana shiga ta taradda shi yana shan lemon data haɗa masa cikin kakkausar murya wadda bai taɓa jinta tattare da Mammyn ba ta ce "Ka kyauta Saheeb wallahi ka kyauta, nagode da nunamin da kake ban isa ba, basai ka huce abinda akai maka akan Yarinyar nan ba, ka sake ta tinda sakin a hannunka yake, kuma zan sanarwa Daddynka bazai yuwu a haɗa Yarinya da azzalumin mutum kamarka ba, dole zansa a raba auren nan kar a cutar da Yarinya ƙarama", tasowa yayi ya nufo inda Mammyn take tini tabar gurin ta barshi tsaye duk ya rasa yadda zaiyi, "kai wannan Yarinyar tinda kika shigo rayuwata kike haɗa ni faɗa da Iyayena, taya zan soki?, taya zan iya rayuwa dake duk sun gaza ganewa, na rasa me yasa idanunsu suka rufe", zama yayi dan yasan yanzu koda yabi Mammy to ba zata saurare shi ba.






Mammy tana fitowa ta kama hannun Rabi dake jikin Kausar suka bar wajen, Nawwara kuwa farin ciki ne fal a ranta, na farko Saheeb yasha lemon data zuba asiri, na biyu ya daki Rabi ga tsanar ta sosai daya nuna, wannan dalili yasa take ganin maganin da tasa ya fara aiki, bin bayansu tayi.







Drivet kuwa tinda yasha lemon nan yake jinsa wani iri, shauƙi kawai yake ji na zuciyarsa nasan wani abu, amma ya rasa mene wannan abin, bai taɓa tsintar kansa a wannan halin ba sai yau, har wani fara'a yake yana rumgume hannunsa a ƙirjinsa, Jazuli driver kenan da tsumin soyayyar wanda bai san wace ba yake ɗawainiya da shi, Malam Halilu maigadi ne yazo ya ganshi  haka zungurinsa yayi ya ce Jazuli meye haka ne sai wani murmushi kake kamar an biya maka makka", still Jazuli murmushin yake ya ce "ai wallahi wani irin yanayi nake ciki Halilu, ban taɓa samun kaina cikin wannan hali ba irin yau, farin ciki nake kuma ina jin soyayya a raina", 




"Soyayya Jazuli?, to wa kake so?", cewar Halilu




"wallahi ban sani ba Halilu kawai ina jin hakan ne", "ikon Allah", shine abinda Halilu ya ce ya bar wajen, dan lamarin sai zuba idon.






Rabi tasha rarrashi wajen Mammy, sannan tayi shuru, amma harga Allah ta tsani Saheeb, ko ganinsa bata son yi, kuma tayi rantsuwa saita rama duk abinda yayi mata.







Kwalliya Nawwara ta ɗauka cikin shigar material tayi kyau sosai sai ƙamshi take, riga da sket ne sun matseta tsam, babu ko mayafi ta nufi side ɗin Hamma Saheeb, da sallama ta shiga, yana falo abin duniya duk ya ishe shi, ganinta yayi kamar wadda aka jefo cikin kwarkwasa da yauƙi ta nemi waje ta zauna, mamaki yake ta yadda ta shigo masa waje babu neman izini "barka da hutawa ranka ya daɗe kyakykyawana",



 Nawwara ta faɗa tana kashe ido ɗaya, mamaki ne da takaici suka dirar masa, sai yake gani kamar a mafarki, dariya ce ta ƙwace masa ta takaici, wannan dariya da yayi sai tayi tunanin aikin Boka ne yake aiki a jikinsa, "dariya na baka ne masoyi?", harga Allah dariya abin ya bashi, wai kamar shi wannan Yarinyar tazo tanaiwa wannan haukan, to wai taya aka raina shi haka?, wannan tunanin yake a ransa, ganin fuska yasa Nawwara miƙewa ta nufi inda yake zaune, kujerar da yake kai ta sakaya zata zauna tare da kai hannu jikinsa, bata sauke  hannunta jikinsa ba, ya tashi a fusace ya sharara mata mari, ya ƙara mata wani a saitin kunnenta hakan ya bawa komai nata tafiya hutun rabin lokaci, bai bari ta dawo ba yahau jibgarta yana huce haushin yau a kanta, ihu take tana bashi haƙuri amma ina an kaishi bango yau, saida ya tabbatar ya jibgeta sannan ya nuna ta ya ce "idan kina haukan ki, da bibiyar mazanki, da shaye-shayen ki karki sake ki sako ni a ciki, idan ba haka ba, zan karairaya ki wallahi, taya har nayi lalacewar da zaki raina ni haka, kizo har ɗakina kimin karuwanci, koda yake ba laifinki bane, giyar da kike sha babu abinda ba zata saki yi ba, da kuma rashin tarbiya, na rasa abinda Mom take har ta barki kika zama karya mara aji haka, ta barki kin lalace kin zama abinda kika zama, wannan laifinta ne dana Dad, to amma bari na gaya miki daga  yau karna sake ganin wannan fuskar taki a cikin gidan nan, ki bar gidan nan karmu sake haɗa ido idan ba haka ba wallahi saina kusa kashe ki, tashi ki fice kona aikata abinda nace!!",





 a guje tabar falonsa cike da tsoro, ga mamakin da take na aikinda Boka yayi musu baiyi ba, tana isa wajen shiga side ɗin Mammy dan haɗa kayanta ta gudu nan taci karo da Jazuli ya sha gabanta kamar an wullo shi "wallahi kece, kece wallahi tallahi, Alhamdulillah", ya faɗa yana riƙe da saitin zuciyarsa, ita kuwa cikin masifa ga bakinta a kumbure sanadiyyar dukan da tasha wajen abin sonta ta ce "Kai jaki dalla matsa kona ci bura ubanka wallahi", ko gezau baiyi ba sai yaji kamar kalaman soyayya ta sanar da shi, zata wuce ya ƙara shan gabanta ya ce "wallahi babu inda zaki ki barni masoyiyata sai dai muje tare", mamaki ne ya gume Nawwara taya wannan mutumun yake mata haka, kodai baigane ta bane?, "kai kakuwa san dawa kake magana driver?", "da Nawwara nake magana, sanyin idaniya ta, mai sanyaya zuciyata, wallahi  duk duniya banida wadda nake so da ƙauna irinki",  yana aje kalamansa ta zabga masa mari har sau biyu, abin mamaki hannunsa yasa ya shafi fuskar tasa ya sumbata, "na shiga uku ko haukacewa kayi ne kai?", "a kanki ba dole na haukace Nawwara", a guje ta nufi cikin gidan tana ƙiran sunan Mammy shima kuwa tuni ya rufa mata baya yana ƙiran sunan Mammyn kamar yadda tayi.✍️








Tofa ƙaƙa-ƙara-ƙaƙa😂



Ana zaton wuta a maƙera sai aka ganota a masaƙa.






Wannan kenan





*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*









*By Rumyn Royal Star🌟*



*09130984617*



*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 57-58*

>>>>>>>>>>>>>>Mammy dake side ɗinta taji muryoyi siririya da garjejiya suna auna mata ƙira, da sauri ta fito, tana fitowa taga Jazuli driver da Nawwara suna tsaye sunyi wurjanjan, ga bakin Nawwara ya haye kamar mumbari, Nawwara na ganin Mammy ta faɗa jikinta ta saka kuka dan lamarin ya fara bata tsoro, Mammy kuwa kallon Driver tayi ta ce "lafiya driver?", ai bata kammala jawabinta ba shima ya saka kuka, yana nuna Nawwara, kukan Nawwara ne ya ƙaru ganin  driver yana kuka kuma yana nunata cikin tsawa Mammy ta ce "haba da Allah mene haka ne wane ya mutu, ku gaya min kun sani a gaba kuna kuka, kaima da girmanka da komai kake kuka sai kace ƙaramin Yaro", "Mammy wallahi haukacewa yayi, nidai gida zan tafi Mammy", "wallahi ba zaki tafi ki barni ba ƙafata ƙafarki a gidan nan, Hajiya wallahi ina son Nawwara banida mata a duniyar nan sai ita, idan kuma kuka hana ni ita zan kashe kaina wallahi", Mammy da ta saki baki da hanci tana kallon abin mamaki ta ce "ita Nawwaran kake so Jazuli?", kai ya waina da sauri, 



Su Kausar da Rabi da suke tsaye duk mamaki ya mamaye su, "Mammy wallahi idan bai dena cewa yana sona ba sai nayi ƙararsa, saina masa rashin mutunci, nida ba shiga sabgarsa nake ba, ya kalle ni ya ce ni yake so, to wallahi idan ma hauka ne a kansa saina sauke masa shi", yana kaiwa nan a zancen ta ta nufi ɗaki, shi kuwa  ganin tabar gurin ya yunƙura da nufin ya bita Mammy ta ce "wai driver me kasha yau kazo kana mana wannan abin, ko da gaske ka haukace ɗin?", ta faɗa ranta a ɓace, cikin gursheƙen kuka da Jazuli yake wanda ya kasa dena shi ya ce "wallahi Hajiya da gaske sonta nake kuma wallahi bazan iya bari ko nan da can ta taka ba tare dani ba, wallahi Hajiya zan mutu idan ta ce bata sona", ya kai ƙarshen maganarsa yana dafe saitin zuciyarsa,




Muhammad ne ya shigo gidan ganin Driver yana kuka ya sa shi tambayar lafiya?, Mammy data sauke gwauron numfashi ta ce "iko sai Allah", Nawwara ce ta fito da ƙatuwar troly ɗinta ta nufi hanyar fita Mammy ce ta riƙo ta ta ce "Nawwara ina zaki haka?", "Mammy zan tafi ne", 


"Saboda me zaki tafi?, kuma meya same ki a fuska haka?", "Mammy faɗuwa nayi", ta faɗi haka dan bata so su san dalilin kumburin fuskar tata, driver ne ya miƙe ya share hawayen sa ya ce "zo muje na kaiki gidan", "sai dai kakai uwarka dan kaza-kazan ka", ta auna masa ashar, hakan bai dame shi ba, Mammy ta ce "kinga karki ce zaki tafi indai wannan ne zansan yadda zanyi, amma bana jin lafiya ƙalau", "Mammy ina son na tafi ne wallahi", Mammy ƙyaleta tayi ta sakai zata wuce driver Jazuli ya fizgi trolyn ya fashe da kuka ya ce "wallahi sai dai mu tafi tare, idan kika tafi bansan ya rayuwata zata ƙare ba", Muhammad dake tsaye yana ganin ikon Allah ya tintsire da dariya, dan sosai abin ya bashi dariya, Nawwara kuwa tsoro taji ta koma bayan Mammy ganin yadda Jazuli ya zazzaro ido yana mata magana, Mammy ma ta tsorata, Rabi kuwa dariya harda riƙe ciki, Kausar kuwa ciki-ciki take dariyar, tsawa Mammy ta dakawa driver amma duk da haka bai nutsu ba, Nawwara da sauri ta ƙira Mom ɗinta ta fashe da kuka ta ce tazo gidan Mammy yanzu, 




Aikuwa hankali tashe ta fito ta nufo gidan Mammy, ko shigowa da motar ta batayi ba ta ƙwanƙwasa aka buɗe mata ta shigo, a falo ta same su Nawwara na jikin Mammy ta ruƙunƙumeta, driver ya sasu a gaba ya kafa musu ido yana murmushi, Muhammad da Rabi kuwa sai dariya suke dan sun kasa hana kansu denawa, Mammy ta tsawatar musu amma abu yaci tura,




Mom ce ta shigo a ruɗe Nawwara na ganinta ta sheƙo a guje ta faɗa jikinta ta fashe da kuka, driver Jazuli ma miƙewa yayi ya nufo Mom, Mom tana shirin tambaya abinda ya faru kawai taga mutum a gabanta yana share hawaye tare da ƙirƙirar murmushi, saurin natsawa tayi ta ce "kai lafiya?", sai cewa yayi "kuka take tayi kuma bana so", Mom da take son ta gane waye sai a lokacin ta fahimci drivern gidan ne, ai nan take ta ce "to ina ruwanka, maima kake a cikin mutanen gidan?", "wallahi Hajiya sonta nake kuma ina son ku bani aurenta", hannu Mom ta ɗaga ta yarfawa Jazuli, "kai amma mahaukaci ne kai ko?, Nawwaran kake so, koda yake banga laifinka ba, laifin mutanen gidan na gani, sa bo da basa ƙaunata bare su so jinina, dole akwai kitumurmurar da aka haɗa dan a ƙasƙantar dani", tana kaiwa nan a zancenta ta ja hannun Nawwara, Mammy na magana ko waigowa Mom batayi ba suka fita, aikuwa a 360 Jazuli ya bisu, ganin haka yasa suma suka ruga a guje dan ya tsorata su ainun, da sauri Mom ta cewa maigadi ya rufe ƙofar kar yabar driver ya fito aikuwa suna fita ya sawa ƙofar mukulli, ihu Jazuli yake yana kokawa da Halilu, ganin haka Halilu ya cika da mamaki, yana tunanin anya lafiya kuwa?, Muhammad ne  ya fito ya riƙo driver da ƙarfi, "ka cika ni maigida, dan Allah karku rabani da rayuwata, ta tafi fa, kuma gani ta tafi ta barni dan Allah ku buɗe min naje gare ta", kuka yake sosai abin tausayi, Mammy kuwa ɗakinta ta koma ta ƙira Daddy ta shaida masa dukkan abinda yake faruwa, dama kuma bai jima da fita ba, ya ce gashinan zuwa.




Mom da Nawwara suna fitowa motar ta suka shige suka bata wuta, saida suka je gida Nawwara ta sauke ajiyar zuciya, Mom ce ta tambayeta abinda ya faru, nan ta bata labarin abinda ta sani, amma bata gaya mata komai akam asirin da tayiwa Saheeb ba, Mom kuwa sai alhakin Mammy take ɗauka akan ita ce tayi wani abin danta wukaƙanta ta, kuma sai Saheeb yasan ya dakar mata Ƴa.





Nawwara kuwa ɗakinta ta shiga ta ciro kwalbar veer ta kwankwaɗe ta, tana ta haukanta har bacci ya kwashe ta.





Driver kuwa kuka yake kamar ƙaramin Yaro ya dawo wani iri idan kuka ganshi saiya baku tausayi wallahi, zuwa yanzu Muhammad da Rabi, Kausar sun dena dariya tausayin Driver ne ya dame su, a haka Daddy ya dawo ya taras ganin Daddy yasa driver maimaita abinda yake ta faɗa na son Nawwara, Daddy rarrashin sa yayi "kana ji Jazuli kayi haƙuri abi abinnan a hankali, kuma ka zama namiji ka dena kuka akan soyayya, idan kana haka ba zata soka ba, ko kana so ta ƙika?", da sauri Jazuli ya ce "a'a Alhaji", "to ka nutsu zata dawo da kanta, amma ka dena cewa zaka fita ka bita, bana so, jibi duk ka zama wani iri lokaci guda", haka yayi ta bashi baki harya nutsu, amma soyayyarta duk bayan minti saita daɗu, haka aka lallaɓa shi ya koma ɗakinsa.





(Hoɗijam da tuni Saheeb ne a wannan lamari, Allah ya soka Yaro. ) 



Saheeb kuwa bayan ya jibgi Nawwara ya je yayi wanka ya kwanta, duk wannan hayaniya bai san anyita ba.






*******************


Inna ce da Baba suke ta farin ciki akan tafiyar su Abdul India, dan jiya  Daddy ya ƙira su ya sanar musu Abdul ya je Kano daga  nan zasu wuce, sosai Abdul yayi farin ciki dan dama yana son faɗaɗa iliminsa, yana son sarrafa Injina, wannan shine mafarkinsa, ga shi Kawunsa zai sa mafarkinsa ya zamo gaske, wannan dalili ne ya sanya su cikin farin ciki, sai addu'a sukewa Daddy, tafiyar nan da kwana uku ne hakan yasa zai shiga Kano gobe.





Tsalaha ne shi da Alhaji Nura wanda yanzu ya kasance babban Abokinsa mai bashi shawara mai kyau da mara kyau, kuma baya musu haka yake amfani da ita, yanzu ma shawara yake bashi akan ya koma Kano da zama nan ne harka tafi buɗewa, kuma zai auri duk wadda yake so a Kanon ba tare da Matarsa ta gida ta sani ba, "kana da kuɗin ka Tsalaha sai yadda kaso haka zakai, idan aure kake so zaka ƙara haka zalika idan Karuwan ne gasu nan sai wacce kake so zaka zaɓa, iya kuɗinka iya shagalinka, ga zaɓe ya zo kuma za'a bamu aiki fiye da baya, kaga saura baifi wata biyar ba, to na tabbata za'a samu mu kawo jini, dan haka ka shirya", 




Tsalaha da yanzu babu sauran imani a zuciyarsa, dan ya rantse ko Iyayensa aka ce ya kawo zai kawo su, ya ce "naji duk batunka, kuma zamu  Kanon kaga sai na siyi gida acan kome nake so sai nayi, kuma batun jini a shirye nake da bada koma waye Alhaji Nura", hannu Alhaji Nura ya bashi suka tafa.







"Hmmmm kedai bari Kareena komai ya  ɓaci, wallahi bakiga wulaƙancin da Saheeb yayi min ba, kuma kamar yadda Boka ya ce haka nayi, ya sha lemon kuma, amma kamar bai sha ba, sai kuma takaicin wannan labarin dana baki akan drivern gidan, naso Saheeb ne yake bina yana kukan nan da wallahi nayi farin ciki, amma sai wani ajawon ƙazami ne ya mutu a kaina, ni bansan ma taya haka ta faru ba mamaki nake, da fa ko haɗa ido dani drivern nan baya yi", cewar Nawwara kenan da take waya da Ƙawarta Kareena.




"kika ce yasha, gaskiya bana jin yasha wannan abu, dan ni nafi tunanin driver ne ya sha", Kareena ta faɗa.





"kai haba Kareena, da hannuna na zuba maganin fa, kuma Mammy ta ce na Saheeb ne, kuma naje na taradda shi yana  sha wallahi".



"Shikenan ki fito mu komawa Boka yau, dan abin nan da mamaki", cewar Kareena, amsa mata tayi da gata nan zuwa.





Mom ce zaune ita da wata mata da gani irin kilallun ƴan bokon nan ne, suna bedroom ɗin Mom a zaune kallonta Mom tayi ta ce "wato Hajiya Sa'a nayi mamakin abinda Ƴar uwata Nafisa tayi min, ta zaɓi dangin mijinta a kaina, kuma jiya....." nan ta bawa Hajiya Sa'a labarin komai daya faru har dukan da Saheeb yayiwa Nawwara, tana kammalawa Hajiya Sa'a ta kece da dariya ta ce "amma kin bani mamaki Talatu, da iliminki da wayewarki ki tsaya sai da amincewar wani zaki yi abinda ranki yake so, aini kin ganni nan wallahi duk abinda na gani ina so samunsa nake ba tare da yardar me abin ba", cikin mamaki Mom ta ce "kamar yaya sata fa kenan", murmushi Hajiya Sa'a tayi ta ce "ke kanki kinsan bana sata, sai dai na karɓa da ƙarfi", "taya kenan?", Mom ta tambaya.






"kinsan banida Uwa banida Uba", Mom ta ce "hakane", to Allah ya bani Uwa da Uba yanzu, ita ce komai nawa, duk abinda nake so a faɗin duniyar nan ita ce kemin shi, ko mene ne saina same shi wallahi, ciki kuwa har da Mijina da nake aure yanzu, ita ce tayi yadda tayi ya aure ni kuma ya fifitani fiye da matansa, idan kina so na kaiki gurinta ki gaya  mata duk abinda kike so ya kasance zaki sha mamaki", shuru Mom tayi dan ita bata saba bin malamai ba, balle Bokaye, ita barta da sabgar gabanta, sai dai taji ta yarda da abinda Hajiya Sa'a ta ce, nan take ta ce ta amince, Hajiya Sa'a ta ce "to ki shirya zuwa gobe muje", amsa mata tayi, nan sukaita hira har lokacin tafiyar Hajiya Sa'a tayi ta tafi.






Nawwara da Kareena ne gurfane gaban Boka, dariya yake ta ɓaɓɓakawa kamar zai haɗiye su sa bo da girman bakinsa, lokaci guda ya gimtse dariyar "dama na gargaɗe ki da kar kiyi kuskure, sai gashi kinyi, na farko kin bari an ganki lokacin da kike zubawa, na biyu ba wanda muke so yasha bane ya sha, wadda ta ganki ce ta bawa wanda bashi muka so ya sha ba yasha, kuma tana zarginki ne shi yasa tayi hakan", tsoro Nawwara taji jin an ganta "Boka wane ya ganni?", "bamu sani ba dan duk iya bincikena na kasa ganinta amma mace ce", hankalin Nawwara ya ƙara tashi, a ranta faɗi take Mammy ko Kausar a cikinsu ne wani ya ganta, dariyar da yake ɓaɓɓakawa ce ta dawo da ita "ki dena wani tunani ba wannan ne a gabanki ba, dole zamu canza sabon shiri, zan baki laya ki binne a inda babu wanda zai ganki, sannan bayan kin binne saiki ƙira ni a waya ki sanar dani, Kareena zata baki number ta", "to Boka shi ku....", ki kwantar  da hankalin ki zamu  cire masa asirin da yasha, zai dawo dai-dai ya dena bibiyarki", sai lokacin hankalinta ya kwanta, Layar ya bata suka baro wajen, "dama  na gaya miki kin kuskure kika ce a'a", cewar Kareena, "ƙwarai kuwa ni wallahi bama wannan ba,  ance wata ta ganni, wallahi tsoro nake ji", "dalla kibar tsoro koma wace nasan Boka zai rufe bakinta babu abinda zatayi", da wannan hankalin Nawwara ya kwanta, aikuwa tana komawa gida ta binne layar acan bayan gidan su.







Washe gari da wuri Hajiya Sa'a ta zo suka nufi gidan Uwa da Uban Sa'a, abin mamaki gida ne ƙerarre mai hawa biyu, gidan ya  haɗu sosai, suna shiga masu aiki ne kowa da abinda take sai gaida Hajiya Sa'a suke, kaitsaye wani falo suka shiga ya haɗu iya haɗuwa komai ja da baƙi kamar gidan tsafi, zama sukai, Hajiya Sa'a ce ta ƙira waya, jinai kawai ta ce "gamu muna Falo", daga haka ta katse ƙiran, basu jima ba aka cika gabansu da kayan ciye-ciye, saida suka ci sukai nak dan dama ba suyi breakfast ba, da Mom ba zata ci ba saida Hajiya Sa'a ta ce "idan baki ci ba ba zata saureki ba", sannan Mom ta ci, sai bayan sunci suka jiyo taku daga saman bene, ɗaga kai sukai saurin kawar da kai Mom tayi, ganin mace doguwa  siririya gata Zabiya idanunta jajajur, gargasa a jikinta kamar ba mace ba, duk gashin jikinta fari ne, hannayenta kamar na fatalwa, ga tsawo kamar na fatalwa, fararen kaya ne a jikinta hakan ya ƙara sawa duk wanda ya kalle ta saiya firgita, wata kujera ta zauna ta kafe Mom da ido, fuskarta ko ɗigon fara'a babu "kina son Ƴarki ta auri ɗan Ƙanwarki, gashi kuma duk basa so, kina so ya sota ya aure ta", cikin muryarta da take fita da sauri da sauri ta faɗa, Mamaki Mom ta shiga yi jin ta faɗi abinda yake ranta "tabbas hakane", cewar Mom, "to ku tashi kuje an gama, zaki bada ɗari uku", buɗe jaka tayi tana  ciro rafar ƴan dubu-dubu har guda uku ta miƙe cikin ɓacin rai ta ce "ɗari uku nace", Hajiya Sa'a Mom ta kalla tana neman ƙarin bayani "naira ɗari uku take nufi", cewar Hajiya Sa'a, cikin mamaki Mom take kallon   Boka Uwa, taga basu take kallo ba, ɗari ukun ta ciro ƴan ɗari-ɗari sababbi ta ajiye ta ɗauki damin kuɗinta ta mayar mamaki da tambayoyi fal ran Mom,




Saida suka fito Mom ta ce "Hajiya ɗari uku fa ta ce ", "ƙwarai duk girman aikinki haka zata karɓa", "to mai yasa hakan?", Mom ta tambaya, "sa bo da haka tsarinta yake, karki yawaita tambaya akan wani abin kiyi shuru zaifi miki amfani", shurun tayi ganin ran Hajiya Sa'a ya ɓaci, haka suka dawo gida sai can yamma Hajiya Sa'a ta tafi bayan Mom ta cikata da kayan arziƙi.✍️





Wannan kenan






*Alƙalamim mu Ƴancin mu✍️*







*By Rumyn Royar Star🌟*





09130984617



*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 59-60*

>>>>>>>>>>>>>>Nawwara lokacin data binne wannan layar ta ƙira Boka ta sanar da shi, cewa yayi "kin tabbata babu wanda ya ganki?", "babu wanda ya ganni ranka shi daɗe", "to madallah, sharaɗin da zan gaya miki shine ki tabbatar kun haɗu kunyi ido da ido da shi nan da kwanani uku, idan kwana uku tayi baki haɗu dashi ba a wannan lokacin duk wanda kika haɗu dashi a kansa sihirin zai faɗa, koda Ubanki ne dan haka ki kiyaye wannan sharaɗin", amsawa tayi cikin compdence.






Yau ne Hamma Abdul ya dira a Kano, Rabi bata san da zuwansa ba tana zaune tana homework da aka basu a makaranta ta duƙufa tana yi, sai jin sallama tayi kamar muryar Hamman ta, ɗagowa tayi aikuwa idanta ya faɗa ana Hamma Abdul tuni tayi jifa da biro ɗin hannunta ta kwasa a guje taje ta ɗafe shi kamar yadda ta saba "oyoyo Hamma na, ina Inna da Baba na ba tare kuka zo ba ?", ta faɗa tana duba bayan sa,  sauke ta yayi yana nishi cikin farin cikin ganin Ƙanwar tasa cikin walwala da kuma yadda ta ƙara girma tayi kyau abinta ya ce "kai Boɗɗo me kike ci kikai wannan girman haka, kinji yadda kikai nauyi kuwa?", shagwaɓe fuska tayi ta ce "kai Hamma nifa banida nauyi", "Inna suna gaishe ki ba tare muka zo ba", rau-rau tayi da ido zatai kuka ya ce "karki sake kimin kuka yanzu saina koma abina", "a'a Hamma yi haƙuri", ta faɗa cikin fara'a mai ƙarawa cute face ɗinta kyau, suna a haka Kausar ta fito suna haɗa ido suka sakarwa junansu murmushi mai ma'anoni da yawa, "Oyoyo Hamma Abdul, ka ƙaraso mana wannan Ƴar rigimar ta barka a tsaye", baki Rabi ta cuna ta ce "kai Adda Kausar ni ɗin?", "eh mana ke ɗin muna da wata ƴar rigimar ne bayan ke", Mammy ce ta shigo itama tana ganinsa ta yalwatu da farin ciki, gaisawa sukai cikin mutunci ta tambaye shi su Inna, ya gaya musu suna gaishe su, nan Kausar ta cika shi da kayan cima, ruwa kawai yasha ya ce yana so ya watsa ruwa, masaukinsa da ya saba sauka aka kaishi, bedroom ne mai kyau an tanade shi ne sa bo da zuwan Abdul, yana shiga ya shiga wanka, bayan ya fito ya canza kaya ya  fesa turarensa ya fito, kai Hamma Abdul ma ba baya ba wajen kyau da tsafta, sai nace Kausar kin iya zaɓe.






Saheeb kwana biyu Mammy bata sakar masa hakan yana damunsa sosai, hankalinsa duk a tashe yake, ga Daddy ma lokacin da yaji dukan da Saheeb yayi wa Rabi sosai ya nuna  masa ɓacin ransa, kuma ya ce aure ne babu fashi, wallahi saidai ya haɗiyi zuciya ya mutu, wannan lamari yayiwa Saheeb zafi.





Ɓangaren Jazuli kuwa kullum kuka ya rasa ta yadda zaiyi yaga zaɓin zuciyarsa, Daddy ya sanarwa da Halilu maigadi karya sake yabar Jazuli fita, yanzu ko driving ɗin bayayi Daddy ya bashi hutu, Mammy harga Allah tana tausayin Jazuli, sai dai tasan Yaya Talatu ko ƙaruna Jazuli zai zama ba zata bashi Nawwara aure ba, dan ita Mammy bata san asirin da aka so yiwa ɗanta ne ya koma kan Jazy ba, ta zaci soyayyar tsakani ga  Allah ne, kullum Jazy yana ɗaki yana jinyar zuciyarsa, har fakar ido yake ya fita sai dai Halilu yana ankare da shi, Halilu irin kafcecen mutanan nan ne masu ƙirar samudawa, shi yasa Jazy ya kasa da Halilu, shi kuwa Jazy irin tsamurarun nan ne Allah ya wadata shi da rafkeken kai, ga idanuwansa ƙili-ƙili, ga aukin hanci dan ya kusa mamaye tsakiyar fuskarsa, bakinsa shi ba ƙato ba kuma ba ƙarami ba, kuma albirinku fari ne  shi, dan harga Allah yana da haske sosai, goshinsa irin me tattarewan nan ne, ba shida aski saina baratalli, wato baya barin ko silin gashi sol ake masa, sai kuma ƙafa wadatacciya da yake da ita, dan irin wafceciyar ƙafar nan ce dashi bai fiya samun takalmi dai-dai shi ba, sai dai ya samu ƙarshen number, wannan shine Jazuli driver.






Yanzu Rabi da Hanan an zama Ƙawaye na ƙut da ƙut, ba faɗa babu hayaniya, sun duƙufa karatu, Saddiƙa tayi farin ciki da hakan, sauran Ƙawayen Hanan ta watsar da su dan sune masu zugata lokacin tana kan tsininta, sosai ake ji da su a Makarantar, dan babu mai taddo su, karatun kawai suke na tsakani da Allah, kuma ba kowa bace tayi silar jajurcewar su sai Rabi, dan cewa tayi "karatu ne ya kawo mu kuma shi zamu yi, ni duk mai son karatu ita ce ƙawata wadda bata son karatu taja baya", wannan shine dalilin dagewar wasu dan da yawa suna son hulɗa da Rabi hakan yasa duk wadda ba tada ƙoƙari indai tana tare da Rabi to ko dan ta birge Rabi saita dage, Auntyn Hanan kanta tasan haɗuwar Hanan da Rabi alkhairi ne, dan Hanan ta gyaru har a gida yanzu bata rashin ji, komai a zancen ta saita sako Rabi, wannan soyayya babu wanda bai santa ba a ahalin Hanan, hatta Defuty da kansa yasan labarin Rabi kuma yaji Yarinyar ta shiga ransa, dan duk abinda Hanan take so to kuwa suna son abin koda kare ne.



Duk wannan sabbin Ƙawaye da tayi Rabi bata manta da Aminiyarta Kattume ba, dan ita ɗin ta daban ce a zuciyarta, kuma tana son zuwa ta ganta bayan hutu, tana ta siyan abu tana ajiye mata, dan bata manta alƙawarin da tayi mata ba lokacin da zasu baro Ƙauyen, shi yasa duk sanda Kausar ko Muhammad suka fita da ita siyayya saita siyowa Kattume nata, idan an tambaye ta na waye sai tace na Kattumenta ne.





A wannan kwanakin Saheeb bashida aiki saina jin karatun ƙur'ani da yawaita addu'a, dan dama azkhar baya wuce shi, dan kwana biyu wasu irin mafarkai yake masu abin tsoro, ana kawo masa hari amma abin harin baya cin galaba a kansa, hakan yasa ya gane addu'a ce sila, Allah yake kare shi.






Wannan lamari ba ƙaramin ɓata rayuka da yawa yake ba, ciki harda Boka Uwa data kasa da Saheeb tayi masa ture tayi duk wani surkullenta ta kasa da shi, Aljanun data tura da yawa sun dawo wasu sassa na jikinsu ya ƙone a sanadiyyar shiga jikin Saheeb da suka so suyi, dan kawai su sashi ya dena duk wata ibada dan asirin ya shige shi, 




Haka ɓangaren Nawwara  yau anci kwana biyu gobe ne zuwa ta haɗu da Saheeb tayi idanta idansa.





Shin zata samu nasara kuwa?.






Zuwan Abdul gidan ya ƙara sa shaƙuwa da soyayya tsakanin sa da Kausar, sannan ya ƙara wayarwa da Ƙanwarsa kai akan rayuwa, yayi mata akan duk wani abu da yakamata ta sani kafin lokacin sa "Rabi'a ke ɗin Yarinya ce har yanzu amma ina son na sanar miki da wani abu da baki sani ba sa bo da kinga zan bar ƙasar nan bansan ranar dawowa ba har sai mun kammala  abinda ya kaimu, abu na farko da zan gaya miki shine haƙuri, zaman rayuwar gaba ɗayanta haƙuri ake, a duk inda kika tsinci kanki ko damu ko babu mu ki kasance mai haƙuri da kuma riƙe sirri, karki bari kowa yasan sirrin ki akan zaman da zaki da mijinki nan gaba, ya zamto duk abinda ya faru ki barshi iya ke da shi banda kai ƙara anyhow, ke bama iya ke da miji ba akan kowa sai kin koyi haƙuri Boɗɗo, abu na biyu tsoron Allah, a duk abinda zakiyi kiji tsoron ubangijin daya halicce ki, kinsan dai me ake nufi da tsoron Allah,  to ko bama ganin ki to shi gana ganinki, ki guji saɓa masa, wala a fili ko baɗini, ki zama nutsatstsiya kuma mar'atussaliha, mai bin mijinta ya hana ta ta hanu kuma ya sata tayi abu tayi, mai kwantar masa da hankali, ki zamo mai tsafta da riƙo da addinin ki, ki yawaita addu'a Azkhar kar yabar bakinki, karki yawaita surutu idan bakya yin komai ki yawaita tasbihi ga Allah swt, Allah ya tsare min ke ya kare minke a duk inda kike Boɗɗo na", wannan shine nasihar sa gare ta, kuma ta riƙe duk abinda ya gaya mata, washe gari Asabar suka lula sararin samaniya zuwa Ƙasar su sharukhan da kajol agarwal dan yin abinda ya kaisu wato karatu.






Sun tafi sunbar mutane da kewar su, su Inna kuwa a waya sukai musu fatan alkhairi, Rabi tayi waya da Inna da Baba, sai shirme take musu baji ba gani, ta tambayi Kattume sunce tana nan ƙalau, wai amma dole sai sun kai mata wayar, daga ƙarshe dai katse ƙiran sukai.








Hafeez fa  lamarin neman matansa ya fara yawa yanzu wata hajar ya samo sai sheƙe ayarsu suke babu ƙaƙƙautawa, dan yanzu baya kwana a gida a Hotel yake kwana shida Zee baby, Mom tayi ƙiran duniyar nan ya dawo ya ce mata shi fa baya ma gari, haka ta haƙura ta ƙyale shi.







Saheeb ne zaune ya riƙo hannun Mammy ya marairaice kamar zaiyi kuka ita kuma ta haɗe fuska "Mammy kimin duk hukuncin da zaki min amma bana son fushin ki wallahi, ki sassauta min Ma walllahi ko baccin kirki bana iyawa ki gafarce ni Ma", kallon sa tayi taga tabbas ya faɗa kwana biyu, haɗe fuska ta kuma yi ta ce "Idan har bazan gaya maka magana kaji ba Son wallahi zakaita ganin ɓacin raina ne, dan bazai yuwu ka maidamu sakarkaru ba", "Ma wallahi na tuba bazan kuma ba Mammy, zanbi yadda kuke so amma bana son fushin ku", murmushi Mammy tayi ta ce "tinda zakayi abinda muke so falillahil hamdu, da farko ina son kaja Rabi jikinka, ya zamto kana bata kulawa ta yadda zata saki jiki dakai, kudinga walwala tare ka dena takura mata Son, ka jiɓanci lamuranta wannan shine kawai abinda muke so",  jin tsaurin lamarin yayi dan baisan taya zai iya hakan ba sai dai dole ya iya sa bo da farin cikin su, "Mammy an gama zaki same ni maiyi miki biyayya", shafa fuskarsa tayi ta ce "Allah yayi maka Albarka ya baka masu yi maka biyayya kamar yadda kake manaa", da amin ya amsa, hira suka shiga yi dan bakowa Kausar tana da lucture Rabi ma tana Makaranta.






Bayan sun gama  ya shirya ya fita.





"Ina so ne  na rama wani abu da akaimin, amma duk muguntata na kasa samo wadda ta dace da wanda yayi min muguntar", Rabi ta faɗa tana cin magani, Saddiƙa ce ta ce "waye yayi miki muguntar", "babu ruwanki nidai ku kawo min ire-iren mugunta dan Allah", Hanan ce ta riƙe haɓa alamun tunani ta tafi, Saddiƙa ce ta ce "ɓawon Ayaba ki ci ki ajiye ɓawon inda zai wuce ya taka ya suɓale", "no besty wannan yayi kaɗan", Hanan ce ta zaro ido ta ƙyasta ƴan yatsu ta ce "yess ga idea", "which idea? please tell us", cewar Rabi da sauri




"Zamu haɗa Nitroxite wato iskar dariya ta yadda duk wanda ya shaƙa zaita tintsira dariya, gejinta mintuna goma", "wow dear wannan yayi wallahi", Rabi ta faɗa tana sheƙa dariya dan harta hango Hamma Saheeb yana dariya babu kama hannun yaro, can kuma ta haɗe face ta ce "taya zamu samu besty?", lab zamu shiga mu haɗa da kanmu, wai ku harkun manta chemistry teacher ne ya koya mana", tunawa sukai suka ce "yess muje yanzu tinda yau babu practical", tashi sukai suka shiga suka haɗa nau'ikan abinda zai samar da Nitroxite ɗin, sun jima suna haɗawa, dan da book ɗin chemistry ɗin suka shiga Saddiƙa tana karantowa su kuma suna haɗawa har suka kammala babu wanda ya shigo ya gansu, a wata ƴar ƙwalba suka juye suka fito, "taya to zaki bashi ya shaƙa?", cewar Hanan, tunani Rabi ta  tsaya yi can ta ce "turare turarensa zan je na gauraya da shi", harda tsallen su ta samo bakin zaren, aji suka koma suna ayyana yadda za'ai suna dariya.







Wayyo Saheeb ka shiga rukunin basawa, Rabi ta waiwayo kanka saita Allah, ga kuma Nawwara tafe, shin iskar dariya ko idanka idanta wanne ne zai faru?.✍️






Burinsu zai cika kuwa?.






Ba zaku san komai ba sai kun biyo ni tiryen-tiryan.




Comment ɗinsu yayi sanyi ababen ƙauna, kar kusa ni nima nayi sanyin, dan ina daf da ajiye typing, dan naga kamar baku so.






Wannan kenan








*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*







*By Rumyn Royal Star🌟*





09130984617




*💫RABI DANJA💫*






            

                *✨NA✨*

        *RUMAISA ALIYU INUWA*




              *Marubiciyar*

*1-RAUDHA*

*2-ZAZZAFAR ƘAUNA*

*3-BAƘAR ƘADDARA*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

        {R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 61-62*

>>>>>>>>>>>>>>Saheeb yana fita Nawwara ta zo, hira suke da su Mammy amma hankalinta nakan ta yadda zata haɗu da Saheeb, cikin dabara ta ce "Mammy nikam ina Ya Saheeb Mom sai cigiyarsa take tinda ya dawo bai je ba", murmushi Mammy tayi ta ce "wallahi na rasa gane kan Son baya son ziyara, sau ɗaya tin dawowarsa yaje Daneji gaida su Mama suma suna yawan tambayarsa, Muhammad ya fishi son jama'a wallahi, kuma ɗazu muna tare da shi ya fita bansan ina ya nufa ba".




Nawwara kuwa gabanta ne ya faɗi dan Boka ya ce idan har duhu ya kawo kai bata haɗa ido da shi ba to tabbas akwai matsala, Mammy ce ta kalle ta ganin ta tsaya tunani ta ce "kina lafiya kuwa Nawwara", saurin amsa mata tayi da "eh Mammy", Kausar ce ta ce "Nawwara ni kuwa ina ya Hafeez tin taron familyn Daneji rabo na da shi, ince ko baya ƙasar?", "wallahi nima kaina sis na kwana biyu bana ganinsa ban sani ba ko ya koma", cewar Nawwara.



Hira suke amma hankalinta yana kan Saheeb, sannan tana tsoron sake haɗuwarta da Jazuli driver, suna zaune Rabi ta shigo gidan da sallama, Mammy ce ta fara cewa "oyoyo my dear, an kwaso gajiyar makaranta ko?", "eh wallahi Mammy na gaji", Kausar ce ta ce "to me aka zo min da shi yau?", "kai Adda Kausar rannan ɗin mafa dana kawo miki dairy milk Saddiƙa ce ta kawo min, yau kam haka na dawo", ta faɗa tana kallon Nawwara dake danna wayarta, dariya ce ta ƙwacewa Rabi aka rasa dalilinta, Nawwara data ɗago taga ita take kallo tana dariyar, ranta ne ya ɓaci ta miƙe a fusace ta ce "ke dan uwarki dawa kike wannan dariyar?", Rabi da taji an zago mata uwa ta haɗe rai kamar ba ita ce mai dariyarba ta ce "da ke nake wallahi, dan abar dariyar ce ke", aikuwa Rabi batai aune ta Nawwara takai mata duka a kumatu kuma sa bo da mugunta dunƙule hannun tayi, Mammy ce tayo wajen ta ce "haba Nawwara saurin kai hannu haka?", 


Kausar ce ta ce "haba Mammy kina ganin fa haka kurum ta kamai mata dariya, meta gani na dariyar, sannan ma sa'arta ce ita", Nawwara da taji haushin Mammy sa bo da ta ɗaure gindin Rabi, a ranta ta ce "wallahi duk sanda ɗanki ya shigo hannu na kun shiga uku, saina yi wasan katantanwa daku", a fili kuma cewa tayi "Yarinyar nan ta jima tana min irin wannan na rasa mena  tsare mata a rayuwa", ta faɗa tana komawa ta zauna tare da ɓata rai,




Rabi kuwa tana tsaye tana aunawa Nawwara harara na dukan da tayi mata, Mammy ce ta ce "Rabi ki dena irin haka, dole ne mutum ya fusata, ke kanki kika ga anai miki dariya ba zaki so ba, babu kyau karki sake, kuma Nawwara kamar Kausar take yadda ba zaki raina Kausar  ba bai dace ki raina Nawwara ba, karki kuma kinji Ƴar albarka", kai Rabi ta gyaɗa, "to maza je ki cire Uniform ɗin kiyi wanka ki zubo abinci kici", amsa mata tayi ta ɗau jakarta ta nufi ɗakinta da yanzu take ciki, bedroom ne da madai-daicin gado mai kyau kalar pink da blue, komai na ciki haka kalarsa yake, ga teddies nan masu kyau an jere mata su a saman gadon, sai wata sofa a gefe mai kyau, ga kan madubinta shaƙe da kayan kwalliya da turaruka da mayuka, wardrop ɗinta mai huɗu shaƙe da kayan sawarta, toilet ta shiga tayo wanka ta fito, sai cin magani take kamar ta tina da wani abu tuni ta sa dariya gami da zuwa inda ta ajiye jakar makarantarta ta daƙƙo ta ciro wata kwalba wadda  ta adana sinadarin dariya, kan madubi ta ajiye ta ce "wallahi zanso naga yadda zakaita sheƙa dariya, wannan kaɗai ne zaisa na huce abinda kaimin Yaro", ita kaɗai take ta maganganunta harta shirya ta fice ta nufi kitchen.





Saheeb kuwa yana fita ya nufi Unguwar su Abokinsa Sameer,  daga nan suka nufi gidan ball na Ahmad musa dake Nasarawa.






Nawwara ta gaji, ga la'asar tayi har ta wuce babu batun Saheeb, ganin Magriba ta kawo kai ta shiga ɗaki ta ƙira Boka yana ɗagawa ya kece da mahaukaciyar dariya "ya ce kin ƙara rasa shi Yarinya bakida sa'a, sai dai ina miki tsoron wanda zaki haɗu da shi, ya rage naki ki ɓoye kanki kije gida ba tare da  kin kalli kowa ba, ko wani ya ganki hakan ya zarce har wayewar gari, hakan shine masalahar ki", "Boka dan Allah ba yadda za'ai a ƙara min lokaci baya....", ƙit Boka ya kashe waya yana sheƙa dariya, ranta a ɓace ta fito, ko takan tayiwa su Mammy sallama batayi ba  ta fice, tana fitowa sa bo da ranta a ɓace ya ke ko takan abinda Boka ya ce mata batayi ba ta fito tana ɗurawa Bokan ashar a ranta, 







Jazuli daya fito dan ɗaura alwalar magriba, dan yanzu ko fita bayayi, daga ɗaki sai masallaci shima shida Halilu suke zuwa su dawo dan sosai ya rame ya lalace, kamar ance masa ɗago ita ma jin motsi ya sata kallon wajen aikuwa sai idon Jazy a cikin na Nawwara



ji yayi kamar yaga Mahaifiyarsa daya jima bai gani ba, tasowa yayi a guje ya janyota jikinsa ya rumgume yana faɗin "ina kika shiga kika barni, nasha wahala wallahi, kullum jira nake naji Alhaji ya ce nazo muje gidan ku mu gana da Mahaifinki amma naji shuru, wallahi ayau dai bazaki tafi ki barni ba", ihu Nawwara take tana ture shi amma inaa Jazuli ba riƙon sakainar kashi yayiwa Nawwara ba, "Mammy na shiga Uku na, kuzo ku taimake ni dan girman Allah!!!!", da ƙarfi take ihun hankalinta a tashe ga tsantsar baƙin ciki na wannan runguma, dan taso ace Saheeb ne yake mata wannan abin.




A guje Mammy, Kausar da Rabi suka fito, dai-dai nan Saheeb ya yi horn, Maigadi yana shirin zuwa ya ƙwaci Nawwara daga rumgumar Jazuli yaji horn ganin su Mammy yasa ya koma ya buɗe gate ɗin, Saheeb ganin ana ta tirka-tirka ga ihun Nawwara daya cika wajen yasa ko gama parking baiyi ba ya fito, Mammy faɗi ta ke "Jazuli ka cika ta mana wannan wane irin hauka kake da jahilci, wallahi dole ne Alhaji ya kore ka yau ba zai yuwu kadingai mana ɗiban albarka a gida ba", sosai Mammy take kumfar baki, suna jan Nawwara ita da Kausar, Rabi kuwa dariya harda riƙe ciki dan ita harga Allah abin dariya ya bata bata ji tausayin Nawwara ba, zuwa yanzu Nawwara ta jiƙe da gumi hawaye ya wanke mata fuska, ga hammatar Jazuli banda bugawa babu abinda take, dan baya samun wanka sosai, ga bakinsa in banda bugawa babu abinda  yake, dan duk sanda yayi magana to a saitin hancin Nawwara yake yi, Saheeb daya tawo a fusace jin abinda Mammy take faɗa, aikuwa hannu yasa ya saita fuskar Jazuli ya zafga masa mari wanda bai san sanda ya cika Nawwara ba, aikuwa Nawwara na jinta free ta yi kan Mammy ta rumgume tana kuka, Mammy ma hawayen take ita da Kausar, dan basu taɓa ganin tashin hankali haka ba, ita kuwa Rabi hawayen dariyar da tayi take sharewa sai su Mammy sukai zaton kuka tayi, duka Saheeb yake ta kaiwa Jazuli yana take shi da ƙafa, babu abinda Jazuli yake faɗa irin "wallahi saidai ku kashe ni amma babu mai raba ni da ita, wallahi saikun aura min ita kona kashe ta na kashe kaina, dan baku san yadda nake jin zuciyata ba ne, amma da baku dake ni ba, wayyo Allah na ka dena dukana haka ina jin zafi", (Allah sarki Jazuli wallahi ya bani tausayi).



Rigar Jazuli duk ta yage sa bo da yadda Saheeb yake jan shi, dan shi Saheeb tunaninsa Jazuli iskanci ne ya sashi rumgume Nawwara, jin kalaman da Jazy yake faɗa saiya ƙara fusata Saheeb, saida Mammy taga dukan yayi yawa bakinsa da hancinsa sai zubar da jini yake, kan nan nasa daya sha aski duk ya kukkurje, Mammy ce ta dakatar da shi, dan ya tabbata Jazuli ya haukace, Saheeb faɗi ya ke "bai dace ana barin irin waɗan nan a gidan nan ba, dole ya bar gidan nan yanzu", ya faɗa yana ciro kuɗi wanda baisan adadinsu ba ya wurga a fuskar Jazuli ya ce "ka tattara kayanka ka fice a gidan nan, karna sake kallon fuskar ka", rarrafowa yayi ya kama ƙafar Saheeb ya ce "dan girman Allah Ƙaramin maigida karka raba ni da gidan nan, dan bansan ina zan nufa ba, kuma wallahi bazan iya barin Nawwara ba, dan Allah ko zaku kore ni ku aura min ita na tafi da ita", yana kuka yana faɗa, zuciyarsa sai suya take masa, Saheeb kuwa zancen sa na ƙarshe da ya ce a aura masa Nawwara ne ya ƙara fusata shi ya hankaɗa shi ya ce "ka fice nace, da na baka damar ka ɗibi kayanka amma yanzu daga nan ka fice wallahi idan na kuma ganinka saina illata ka", idan kuka ga yadda Jazuli yake kuka saikun taya shi dan ya gigice ya zama abin tausayi, sai dube-dube yake hango Mammy yayi ya nufe ta, ganin haka yasa Mammy barin wajen ita da su Kausar, Rabi ce tayi saura a wajen wadda zuwa yanzu kuka take wiwi sa bo da tausayin Jazuli, tinda take bata taɓaiwa Saheeb magana dan kankin kanta  ba sai yau cikin shashsheƙa ta ce "dan Allah Hamma karka kore shi wallahi bashida lefi, kaga fa kuka yake a tsaya a fahimce shi", wani bahagon kallo Saheeb yabi Rabi da shi ya ce "ok ba shida laifi ko, sa bo da bake aka rumgume ba, shine kike wannan maganar, wato nufin ki nabar marungumi a gida duk sanda kika so ya rumgume ki sai kizo wajen sa, sa bo da bakisan ciwan kanki ba har kina cewa na barshi, bar nan kona ɓalla ki, ashe kina iya magana haka kamar ta Allah, na sake jin kin tsoman baki a lamarina har takai ga kin bani shawara, wallahi mai raba ni dake sai Allah sha sha sha kawai", murguɗa baki tayi ta ce "ai shawara ba ruwanta da babba ne zai baka ko yaro, kuma sai kayi dana sanin abinda kai masa", a guje ya bita zai kamo ta ta ruga, ƙwafa yayi yana  takaicin rashin kamota da yayi.




Juyawa yayi ya kalli Jazuli yaga har yanzu bai tashi ba, rigarsa ya janyo yayi hanyar  waje dashi, sai haƙuri yake bashi amma yaƙi saurararsa, ƙwalla ƙiran sunan Nawwara yake yana ihu amma sai da Saheeb ya futar da shi, ya ce da Halilu maigadi ya datse ƙofar karya soma barinsa ya shigo, sosai Halilu yake jin tausayin Jazuli, dan da gani ba lafiya yake ba.





Nawwara sai kuka take, ba komai ne ya sata kuka ba illa rashin nasara data samu, kuma ta raya a ranta wannan rumguma da Jazuli yayi mata saiya zamo ajalinsa, dan burin ta tabar gidan, Mammy sai rarrashi take, anan dai Nawwara ta kwana.






Daddy baya gari yana Canada shi yasa duk abinda ya faru bai sani ba.





Washe gari bayan dawowar Rabi daga Makaranta tayi wanka taci abinci sai da ta tabbatar Saheeb ya tafi sallar la'asar ta saɗaɗa ɗakinsa, wata robar turare ce wadda ita kaɗai ce za'a iya kwancewa, ita ta buɗe ta tsiyaye sinadarin shaƙa na dariya sannan ta mayar ta kulle ta fice a guje tana dariya, a ranta tana faɗin ko baka fesa yau ba gobe zaka fesa.





Yana dawowa side ɗinsa ya nufa, dan yana son ya fita, kaya ya sauya tinda dama yayi wanka kafin ya tafi masallaci, gaban mudubi ya je ya fesa turare wajen kala huɗu, wannan na robar shine ƙarshe a dai-dai wuyansa ya fesa shi, ya juya kenan zai ɗau key ɗin motarsa yaji dariya tazo masa ɓakatatan ba tare da anyi abin dariya ba, nan fa ya fara dariya babu gaira babu dalilin yinta, abu takai ga harda riƙe ciki, yana yi yana faɗin "kai wai me yake faruwa ne hahahhahahaahaha, dariya haka kurum hahahahaha",  gefan gado ya zauna yana tayi ƙarshe dai fito ya nufi side ɗin Mammy dariya taƙi ci taƙi cinyewa, har waje yake samu idan yayi dariyar saiya miƙe, so yake ya dena amma abu yaci tira, da wannan dariya ya shiga falo, Mammy da Kausar auna zaune Kausar na tsefewa Mammy kitso sai ganin Saheeb sukai yana ta sheƙa dariya harda ƙwalla, fara'a suka saki Mammy ta ce "Son hala wani abin farin cikin ne ya same mu haka?", gani tai ya dafe ciki yana dariyar tare da nuna su da hannu "wallahi Mammy ba ɗaya hahahahhahaha, kawai na tsinci kaina ina dariyar ne hahahahahhaha, bansan taya haka ta faru ba Mammy hahahahhahahah", dariya suka sa dan da alama yau barkwanci Saheeb yake ji Mammy ta faɗa a ranta "Hamma dan Allah ka bamu labarin nan muma mu dara", cewar Kausar tana dariya "ke ni sa'anki ne hahahaahahhahahaa, nace muku wallahi babu abin dariyar da akai hhhhhhhhhh nima tsintar ta nayi ina yi hahahhahahha", dariya suka hau yi, Rabi ce ta fito ganin abinda ke faruwa ta murmusa tare da zama, Mammy ce ta ce "Son kana dai yi mana baƙin ciki ne dan karka bamu labarin", zuwa yanzu ya hassala amma dariyar da yake ba zata bari su gane ransa ya ɓaci ba, "hahhahahhhhhhhhh Mammy wai ba zaku fahimci halin da nake ciki bane hahahhahahhahaah, wallahi babu wani abin dariya hahahhahahhaha bana son ina yi amma saita zo hahahahhahah", Rabi dariya kawai take harda hawaye burin ta ya cika, Saheeb kuwa cikinsa har ƙullewa yake sa bo da dariya, Mammy ganin mintuna sun tafi amma bai dena dariyar ba, ga shi kamar faɗa-faɗa yake a dariyar tasa yasa hankalinta ya fara tashi, Kausar ma ta fara gane ba lafiya ba dan duk abin dariyar da za'ai Saheeb baya taɓa dariya irin haka sai dai yayi murmushi, amma yau shine da dariya harda hawaye ga ciki yana ƙullewa.





"Son da alama ba lafiya ba, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un", Mammy ta faɗa hankali a tashe, tashi tayi ta ɗago shi, still dai dariyar yake, amma kana ganinsa kasan ya jigata, Mammy ta rasa me zatai, duk ta gigice, wannan damuwa da Mammy ta shiga sai duk hankalin Rabi ya tashi dan batasan abin zaiyi tsamari haka ba, ga Saheeb duk ya wahala ga shi dariyar taki tsayawa, kuka Rabi tasa Mammy ma kukan take haka Kausar, kwantar da shi Mammy tayi tasa Kausar ta kawo mata ruwa, tofi tayi ta bashi yasha, yana gama sha ya cigaba da dariyar, zuwa yanzu kowa na falon kuka yake, "ku dena kuka mana Mammy hahahhahahhaha  zan dena hahahhahahhah, amma nayi mamakin dariyar nan da nake lokaci ɗaya fa hahhahahhahah", "kayi shuru haka Saheeb " Mammy ta faɗa tana share hawaye, Rabi da kukanta yafi na kowa ƙarfi a wajen yasa ya kalle ta cikin dariya ya ce "kin cikan kunne malama ya isa kukan haka kiyi min addu'a hahahhahahhahahhaha", mugun tausayinsa taji, da nasani take sosai a ranta, da gudu ta matso inda yake duk ta gigice ta kamo hannunsa tana so tayi magana ta kasa sa bo da yadda kuka yaci ƙarfinta, hannunsa yasa a fuskarta yana share mata hawayen ta, tare da girgiza mata kai alamun ya isa haka, Mammy  kuwa gaba ɗaya taji tausayin su ya cika ta, Kausar sai kuka take ta rasa wa zata ƙira ta  gayawa duk ta gigice, can zuwa wani lokaci sai bacci ya ɗauke shi hannunsa na cikin na Rabi, ita ma baccin ne ya ɗebe ta, ya zamto kanta na gefansa hannunsu sarƙe dana juna, ajiyar zuciya Mammy ta sauke haka Kausar, Mammy taso tashin Rabi sai kuma ta fasa, sasu a gaba sukai suna kallo, Mammy sai mamakin abinda ya kawo masa wannan dariyar take.✍️




Wannan kenan



*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*







*By Rumyn Royal Star🌟*





*09130984617*


No comments

Powered by Blogger.