Auren Fari Complete Hausa Novel


💑 *AUREN FARI*💑                  

                 0⃣0⃣1⃣

*NA SADAUKAR DA LABARIN GA AUNTY RABI TAH ( HAJIA RABI BADAWI MAMAN IBRAHIM )*Sauri takeyi kamar zata tashi sama, hannun ta rike da kwanon miyar manja, tun dazun aka aketa asibiti kai abinci amma don shiriri ta miyar ta baro gida shine ta dawo dauka.

Fakam fakam fakam tafiya takeyi ba ko jinkirtawa saboda tsoron kada Yaya Abba ya dawo masallaci a fada mishi yau kuma ga abinda tayi. Ji kakeyi rikichaaaa,!! Karam karam....... Ta antaya jikin mai tahowa da miyar da ita duk suka afka mishi yayi baya da karfi tare da riketa gamm bayansa ya bigi bango da karfi miyar ta karasa wanke mishi gaban farar gizna din sa, ya runtse ido da karfi lokacin da yajin miyar ya watsa mishi a ido yaji wani irin azaba ya ingije ta silbin miyar ya kwashe ta ta fadi duk ta nade miyar a hijabinta.

   Ta mike a harzuke malam wannan wane irin wulakanci ne baka gani zaka jefani cikin miya in bata sabuwar hijab dita ta islamiya? Bayan asarar da ka janyo mun kai baka iya tafiya kana duban gaban ka? 

Bala'i take zazzagawa yana kokarin goge yajin da ke idon sa. Sam bata lura da mutanen dake bin bayan sa ba, sai da wani ya finciko ta karfi zai kwada mata mari yayi saurin daga mishi hannu alamar ya kyaleta. Ta ja baya tare da rike kugu iyyyeee cewa zakayi tafe kake da masu tare ma fada to wallahi yau sai kun biyani miyata da hijabi na..... Sai lokacin ne ya kalleta idanun sa jawur ga bacin rai ga radadin yaji ya da ka mata tsawa ke gidan ku ba a koya miki tarbiyya ba? Wannan tsummar hijabin da banzar miyar manjar ki kike wa mutane rashin kunya akai? Kin San darajar kayan da kika bata? Ya zaro ido ya na nuna jikinsa.

Kai ka sani ni kasan miyar nawa aka kashe akayi ta? Ko kuwa kasan kudin wannan hijabin.....shut up!!!  Ya daka mata tsawa tare da damko ta. Lokacin ne hankalin mutane ya dawo kan su. Wani yayi saurin dafa kafadar sa yallabai ba girman ka bane don Allah ka kar ka biye mata.

Ya hakade ta ya gitta zai wuce sai ta chafko hannun sa da karfi kamar wani zaki ya dubeta da karfi ya kalli siririn hannun ta sannan ya kalleta ita din dukan ta zai iya hadiyewa. 

Wallahi duk mazuran ka sai ka biyani zaka bar wurin nan yama rasa me zai mata ya chafki hannun ya kudundune ta ya jefar suka wuce yabarta kwance tana ihu duk ta tara mutane kanta asibitin.

Abba da ya fito masallaci ya hango mutane taruru ya tukaro wurin yaga lafiya sai kawai yaga *umaimah* wani takaici ya turnuke shi ya figeta da karfi sukayi dakin jinyar, tunda tagan shi jikin ta ya fara kyarma. Suna shiga ya fara wanka mata mari biyu sannan ya tambayi ba asi, tana gama fada mishi kuwa yasa mata charger ya bata kashi sai da goggo ta karbeta.

 Abincin sai dai aka siyo mai da yaji.

  Umaimah marainiya ce, gaba da baya tana hannun wan babanta gidan banda gallaza mata babu abinda akeyi ko karatu sun hana a sanyata da tsiya sun kangarar da ita. Matar marikin nata ce aka kwantar duk da nisan da ke tsakanin su da asibitin kullum itace ke kai abincin safe, rana da kuma dare. 

 Kamar mahaukaciya haka ta fito kacha kacha ta nufi gida tana takaicin wulakancewar hijabin islamiyar data samu da kyar aka yi mata. Haka ta koma gida ta shiga wanke kayan da manjan ya kasa fita abinda ya kara harzukata tana addu'ar Allah ya kara hada ta wannan dan rainin wayon. 

  Sati daya, sati biyu....har an share kusan sati biyar basu kara haduwa ba gashi an sallamo goggo sai ta fita batun sa.

 Umaima bata da kiwa ko Kadan shi yasa take cin gajiyar mutane da yawa cikin unguwar ana yawan kiranta gidaje mai shara, wanke wanke dan wankin yara haka dai idan ta gama abinci, sabulai mai da tsumma. Gidan su Sam babu Wanda ya damu domin sun dauki hakan kaskanci da bayar dakai wani lokacin ma sai suyi ta mata dariya tare da habaici. Ita kuwa tafi jin dadin bautar da takeyi wa mutanen gari suna godewa ba nan da kullum wulakncin safe da rana daban ba.

  Duk satin nan bata zama gida tana gidan Alhaji yakuba tana taya su aikin biki, musamman gyaran daki domin sun yarda da ita matuka.Har yau ransa a 6ace yake, yarinya karama talaka kuchaka ta dizgashi, zuwansa asibitin biyu bai ganta ba inama lokacin ya kakkaryata lallai da ya huce bai zauna cikin bacin rai irin haka ba, ya ringa hasko ta cikin kuchakan kayanta da shegen yadin da take ikirari da sabuwar hijabi Wanda ko kyallen goge takalman sa yafishi daraja.

 Ya buga tsaki ina jiye wayarinyar nan haduwar mu nan gaba....... Au wai baka shirya ba? Don Allah malam hanzarta kowa ya hallara kai kadai muke jira.

 Ya kara hade rai ya mike okay ina zuwa.

 Yauma cikin rantsattsiyar gizna yake fara tasha aiki na alfarma tafe yake yana kasaita ran nan nasa a 6ace. Yanda yake saukowa a benen yasa abokan duk bushewa da dariya baibi ta Kansu ba kawai yayi gaba abinsa. Mustapha ya yi nuni da baki ji yanda yake hura hanci kamar shine angon duk suka kara kwashewa da dariya.

Hajia ta kira umaima lokacin da ake ta faman tafiya party tace ke bazaki je bane? Murmushi tayi ta ce eh hajia. Dalili? Maza zo nan ta kama hannun ta tayi ciki da ita wata durowa ta bude kinga duk wadannan kayan Asma'u cewa tayi a bayar don haka ki zabi Wanda zaki zaka yanzu kije ayi dake idan kin dawo ko zuwa gobe sai ki zo ki kwashe sauran don ke na ajiye wa....ta zaro ido ni hajia. 

Eh ke fa..

Maza shirya kada motocin su kare, wani paper lace ne milk dinkin riga da skirt ta dauka. Har zata fita taga hajiyar ta shigo da sauri ta miko mata takalma ungo wurin amarya na roko miki wannan kuma gyale ne sanya maza ki wuce.

Ko hoda bata shafa ba. 

 Tana zuwa ta fada mota. Ko da a ka sauke su. Fiddausi kanwar amarya na ganin ta tace yauwa umaima zo Ku shiga da kayan nan. Ta ce to ta shiga aiki. Dai dai lokacin da sukayi tsaya da mota kamar ance ya daga kai kawai ya hango ta rungume da lemuka. 

 Da sauri ya fito sai kuma ya yi turus daya tuna inda yazo. 

Muje ko? 

Ya rungume hannu a kirji tare da jingina da mota ya ce kuje ina zuwa ...duk suka kalleshi sai kawai yayi sauri ya fiddo waya yasa a kunne hakan yasa suka fahimci waya zaiyi. Suna wucewa ya mayar da ita aljihu, ta fito tana ta faman kakkabe kakkaben kaya yayi murmushi watau yau bata son abinda ka taba kayan jikin ta. 

Sam bata lura dashi ba ta zo zata wuce sai kawai taji an fizgeta anyi bayan motoci, ta dago da karfi sai kawai ta ganshi. Ta fizge hannun ta tare da ingijeshi kana hauka ne zaka kama ni? Zai yi magana ta juya abinta kayan data fasa dauka kenan ta shiga ciki duk an zazzauna ta hango kujera can tsakiya ta isa ta janyo zata zauna ashe biye yake da ita kawai ya harbar da kujerar ji kakeyi *timmm* ya wuce abinsa duk aka juyo hankalin kowa ya dawo kanta ta wunkura da karfi zata isa gunsa fiddausi ta gani gaban ta. Sannu umaima ke nake nema zo muje ki taya my serving wani takaici ya turnuke ta ta bishi da kallo dai dai lokacin da ya hau gun anguna ya zauna ya juyo yana hararar ta.

 Kunya duk ta baibaiye ta. Shine ya bude tàro da addu'a ya bada tarihin ango don haka bata nan suna can suna shirya abinci.

Fiddausi tace kamata yayi mu fara kaiwa haka .

Umaimah tayi karaf Anty fiddausi kawo in faro daga sama wurin angwaye.

Yawwa Allah ya yi miki albarka umaimah dama kowa baison zuwa saman cen, ta dauki ture ta fara shiryawa. Zuwa na uku da zatayi ta debi cocktail juice da farfesun kayan ciki ta tafi tana isa kamar zata ajiye bisa yanda ta faro daga farko kawai sai ta antaya mishi duka ajiki har turen jikake rikichaaaa ...... Duk Wanda ke high table din tsaye ya mike hankali tashe........ DOWNLOAD HERE

No comments

Powered by Blogger.