Najma 17-18

 


πŸ‘„πŸ«¦πŸ‘„πŸ«¦πŸ‘„πŸ«¦

    *_NAJMA_*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

By maman noorul 

Hudah Wanan littafin na kudine regular 300 vip 600 via 

2378022567

Aisha Mohammed

Zeinith bank,for more information please contact me via my watsaap number 09090112846


πŸ…Ώ️1️⃣7️⃣🫦1️⃣8️⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim 


        Dan mikewa yayi yace"husnah   bani 5minit bari inje toilet 


    Jinjina Kai tayi ya shiga,ta bisa da kallon ganin ya d'au waya ya Dan Jima kafin ya fito ya Fara abinda yafi so a rayuwarsa,sai da ya samu natsuwa da yake so,ya koma gefe Yana maida numfashi 


Husnah ta rungumeshi  tana sake shiga jikinsa tana me Jin sonsa 


         Yace"ya kamata ki tashi ki tafi gida  kafin dare yayi Miki"


Tace"anan Zan kwana mummy Bata Nan ai na fada maka 


        Yace"still ki tafi dan Nima a gun aiki Zan kwana"d'agowa tayi tana kallonshi cikin wani irin expression tace korata kake ne captain "


    Mikewa yayi yace"duk inda Kika d'auka hakane"


      Mikewa itama tayi tace"nasan halinka so kake in tafi ko ka dauko wata tunda ba ka da aiki sai Hawa yaran mutane toh iam not going anywhere anan Zan kwana 

"


Bebi ta kantaba ya shiga yayi wanka ya fito d'aure da towel yasan husnah da naci bazata tafi ba sai ya jawo wayarsa ya Fara rubuta text wani kallo ta masa tace"i know you are texting her toh ba inda zani kai wani irin womanizer ne mace daya bata isarka 


        Bayan ya gama text din ya ajiye wayar a saman mirrow ya cigaba da shafe shafensa.kaya ya saka black jeans da dark blue polo yayi mishi kyau sosai ya dau wayar zai fita ta sha gabanshi 


Wani mugun mari ya sauke mata da yasa ta durkusa kasa ta  saki kara ya ratsata ya fita 


       Just as she insinuated gun mace ya tafi hotel 


___________


       Minna 


      Zaune take a falo cikin isa da takama sai order take baes mami, jikin mami na rawa wajen bin umurninta 


         Ajiye kofin shayin tayi a gabanta tace"hajiya ga shayin 


      Wani kallo tayiwa mami tace"salon in sha ki kasheni ko wai shin nikam fatima meyasa baki da hankaline yanzu sai nace ki d'aga min shayin zaki d'aga min  haba 


Jiki na rawa mami ta dauka tace"dan jiya kince yayi sanyi  dayawa shiyasa ban daga ba yau yi hakuri Bari in dauko Kofi in daga Miki shi "


    Saukowa da imran yayi daga sama ne yasa mami ta kalli sama ya daure fuska hakan yasa hajiya kau da kai tana tabe baki shiko sake daure fuska yayi dan beso ta kawo me wani wargi 


Mami tace"wai daman baka tafi ba? "


         Yace"yanzu dai zan tafi mami zan samu abinda zan karya dashi kuwa? "


     Ta girgiza kanta tace"eh imran gashi can dining"karasawa yayi ba tare da ya gaida hajiya ba ta bishi da harara tace"sai ya dameni? Ai uwarka ma bata samu gaisuwar arziki ba 


      Ajiye mata shayi mami tayi ta dauka ta kai baki ta kurba cikin fada tace"daga ki daga kadan sai ki maidata ruwa  sanyi 


   Mami ta tsaya tana kallonta sai kuma tace yi hakuri kawo toh a jiko miki wani"


       Cikin yatsina da kallon banza tace"tunda baki san zafinsa ba a kauye babu irinta an zo an samu waje ana albuzaranci"


           Mami bata kuma cewa komai ba ta juya sama dakin autar ta jannaht tayi ta tasheta tace"7 fah ya wuce  zaki makara school"


Da kyar jannaht ta mike ta shiga bayi, mami ta fita ta shiga dakin haroon shima baccin yake ta tashesa da kyar tace"karka manta fah abbanka yace ka wakilceshi a meeting ai dirowa yayi a gado a gurguje ya shirya ya sauko ko breakfast beyi ba ya bar gidan shi da imran 


        Fitar ba jimawa sai ga jannaht ta fito sanye da uniform riga da wando farar riga sai dark blue wando uniform din ta sha guga sai karaman hijabi tea da bread da kwai ta ci sanan ta bar gidan driver ya kaita school 


      Ajiyar zuciya mami ta sauke bayan ta gama aiyunkanta ta dau waya yau tana son magana da iya tayi kewarsu gashi alhaji ya ki bari ta lekasu bisa umurnin hajiya 


       Kiran umma tayi bugu biyu ta dauka sun dade suna hira ta tambayi lafiyar uwani yariya da take Jin kaunarta  a zuciyarta  allah ya gani tana kaunar uwani kauna na ban mamaki yar d'an uwanta tilo ta kuma ji dadi da aka ce mata uwani ta tafi makaranta yau da alhaji zai yarda da ta dauko uwani nan tayi karatu amma hajiya bazata yarda ba 


       Tsawar hajiya ne ya katse mata tunani data ce ke fatima zo ga wayana ki hadani da  Afan tun jiya be kirani ba 


     Mami ta mike ta karasa falon dan dama tana zaune ne a dining   ta karaso ta duka ta dauki wayar tana kokarin dialling numbersa call dinshi ya shigo 


       Tace"gashi ma yana kira, hajiya ta washe hakura tana balain kaunar Afan duk jikokinta kusan guda talatin tafi kaunarsa shima yana sonta fiye da komai a zuciyarsa sai yayi wata be kira mami ba amma ita so biyu so uku sai ya kirata a rana 


Zubawa hajiya ido mami tayi tana jin kewar danta da ya mata nisa saboda dabiarsu daya da hajiya,Bata kiranta in ba ita ta kirashi ba Kuma in tana magana sai ya yanke wayar yace zai kirata bazai Kira ba  


      Maganar hajiya yasa ta sake kallonta da tace"oh tafiya zakuyi toh allah ya kiyaye hanya soja mazan fama muna daga nan muna muku addu'a da ka dawo wanan karon sai aure kana ganin dai d'an uwanka ya ajiye iyali harda d'an na gaji da ganinka haka? "


           Ko me yace sai taji hajiya ta kyalkyale da dariya sun dau lokaci suna waya mami ta tsaya ko zaice a bata waya shiru sai kawai ta mike tayi ciki ranta ba dadi ta shige dakinta ta zauna bakin gado ta danna numbersa 


     Saida ta kira kusan so biyar ya d'aga kiran saidai beyi magana ba 


Tace"salamu alaikum"


     Yace"mami ina kwana"


Tace"lafiya lau ka tashi lafiya"sai kuma ta jiyo muryar mace na cewa mamin mu ne bani ita mu gaisa pleasa


      Gabanta ne ya fadi ta kalli agogo ta gan tara batayi ba kuma kamar ba a gun aiki yake ba karfa zarginta ya zama gaskiya Afan mata yake bi Dan tun dawowarsa na karshe ta Fara ganin canji a gunsa,ta rasa ya zatayi da lamarin afan ga dai Deen ya natsu Kamar shine babba Amma shine sanadin kukanta kullum dai tana me addu'a samun shiriya 


Amsar daya bata ne yasa ta dawo daga duniyar tunani da yace"lafiya lau mami"


Tace"kai dawa a wajen "


    Shiru yayi bece komai ba, sai ta fara me nasiha tace"afan ka ji tsoron allah a duk inda ka samu kanka ka tsare mutunci mu dan girman allah karka aikata zina domin alfasha  bashi ne, zina bashi ne domin sai ka manta zasu dawo maka kar wata rana sai ka zo kana son wani abu ya fara dawo maka 


            Ganin zata b'ata me lokaci yace"zan kira ki anjima"be jira cewarta ba ya katse wayar 


      Mami tayi shiru cikin yanayi na rashin jin dadi ta kwanta sai ta kira alhaji            _________


     Tunda ya tashi ya so zuwa gidansu amma ya daure sai kai kawo yake tsakanin waje da tsakar gidan 


Kallon agogo yayi ya gan goma ta wuce sai kawai ya yanke shawaran zuwa  gidin bishiya inda abbu ke zama 


    Ya koyi sa'a shi kadai ne zaune ya karasa ya zauna gaidashi yayi abbu nata amsashi cikin jin dadi bayan sun gaisa yace"


Maman nur

No comments

Powered by Blogger.