Fulani 20

 


20

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*


UNCLE AA POV. 


sai da ya fita daga Masarautar gaba daya yai nisa da ita ya tabbatar da babu mai jin abun da zai fada sannan ya sake kiran line, ringing daya Nana ta dauka sai ya marairaci murya kamar zai yi kuka, a zahirin ma zai ya kukan domin ya lura msarautar ba karama bace idan kuwa har ta tabbata ba zai yi driving din ba ai ba karamar hasara yai ba, sarki guda? Sarkin ma na Yola, ga yarsa da bata san zafin kudi ba. 


“Nana na san kina son ki taimake ni ne saboda ni maraya ne, ba ni da uba ba uwa daga ni sai Yayata muka rage, kin ga wannan aikin da zaki sama min ba karamin taimako zaki yi ba, Allah kadai ne zai iya biyanki, kuma ni yanzu kin zama uwar dakina kuma uwata mai share min kukana, ban yi zaton za a hana ni aiki a gidan ku”


Nana dake zaune a falon baki tana jiran shigowarshi ta tashi daga kwancen da take.


“Miya faru”


“Ina shigowa na hadu da wata yarinya mai kama da bebin roba tace min wai ba za a dauke ni aikin ba, ba ki ji yadda na ji ba Nana, amman nasan ina da Allah, ina dake kuma zaki min gata ni kuma zan zama mai biyaya a gareki ba zan taba sabawa umarninki ba”


“Kana iya yanzu?”


“Na ma fita daga gidan na yi nisa kar ace na yi wani abun”


“Ka dawo yanzu gani nan fitowa”


Nana ta kashe wayar a fusace, wani irin dadi ne ya lullube shi. 


“Allah na gode maka da ka hada ni da yarinyar nan Allah, Allah kasa ta rika jin tausayi na tana bani kudi, Allah sani bani da komai sai burge da wankan karya Allah ka min arziki ta hanyar yarinyar nan Allah”


Ya fada yana kallon sama, ya ci wanka kam iya wanka idan ka ganshi kamar dan wani shege, bayan ko har wuni yake da yunwa wani lokacin, juyawa yai ya nufi hanyar komawa cikin masarautar. 


A fusace Nana ta isa Part din Hajiya, dan yana fadar mai kama da babin roba ta gane cewar Jurry ce dan tafi kowa rashin kiba a gida sai fari kamar zabiya, Hajiya na zaune tana tauna maganar Jarma wacce ta hanata sukuni ciki har da zancen tafiyar da babu dawowa wa zai yi tafiyar? Waye Sardauna waye Fadime balle kuma Falmata? Shigowar Nana yasa tai saurin daukar remote ta canja channel kamar da gaske kallon take.


“Hajiya kin ga Yaya Jurry ko? Wai ta kori driver na wai ba zai yi aikin ba”


Nana ta fada kamar ta fasa kuka, sai Hajiya ta mika hannu ta rikota. 


“Jurry tace za a daukar miki sabon driver ko ni?”


“Ke”


“Then why maganarta zata taba ki? Je ki kira driver”


“Ya shigo yana harabar gida”


“To kije ki bashi key din, nawa ake biyan wacan?”


“35k”


“Wannan zamu ba shi 40k, zan kira Waziri na fada masa a saka shi a list”


Da sauri Nana ta rumgume Hajiya tana murna. 


“Thank You Hajiyata I love you”


Sai da ta aje mata wayarta sannan ta fice daga dakin. Ta gate din Hajiya ta fito sai ta same shi kusa da gate din tsaye, tana kallonshi taji ya matukar burgeta saboda yayi wanka mai kyau, daman can kuma ko kallonsa tai nishadi take ji. 


“Ka zo?”


“Eh”


“Na yi ma Hajiya magana tace za a baka 50k per month” 


“Da gaske?”


Ba shiri AA ya zauna a dan simitin da aka zagaye fulawa da shi a gurin. 


“To zan maka karya ne ko na taba maka karya”


Nana ta fada da dan fada fada, sai da yai kamar ya rama sai kuma ya tuna a inda yake sai ya dariya. 


“Aa Hajiyata na gode sosai, yanzu na tabbatar da ke yar gata ce, amman sarkin ne Babanki ko kuma rikonki ake a gidan?”


“Ina ruwanka?”


Nana ta fada tana turo baki dan ita dai bata son yawan tambaya da bincike. 


“Ba ruwana fa”


Ya amsa mata da sauri yana sosa kai. 


“To bari na je na karbo maka makullin motar, amman nan ba gidan mu bane ka biyo muje gidan mu”


“To nan gidan su waye?”


“Wai ina ruwanka?”


‘Daga gani idansu wannan bebin robar ne shiyasa ta hana a dauke ni aiki dazun, kai no kila ma wanki take musu daman wadanda ba yayan kowa ba sun fi komai falako idan sun yi abu, ni ma nan da kwana biyu zan sayi mota ana fara budawa a gari’


Ya fada a ransa a fili kuma murmushi kawai yake yana kallon Nana wacce ta wuce apartment dinsu yana binta a bayata. A bakin gate ya tsaya ita kuma ta shiga ciki. 
FALMATA POV. 


sai da ta kusan minti ashirin a tsaye sannan aka bude mata kofar, sallama ce abun da ta fara yi sannan ta shiga cikin falo cikin tsoro tsoro kamar wacce tai laifi. 


“Jekadiya tabo min yarinyar nan”


Wacce Ammy ta kira da Jekadiya ta kyafato Falmata da sauri tana nuna mata Ammy. 


“Ku zo tare zan yi magana da ita”


Jekadiyar ce ta yi saurin karasowa kusa da Ammy kasancewar tafi kusa, sannan Falmata ma ta karaso tana mikawa Ammy gaisuwa irin ta sarki da talaka duk kuwa da bata da tabbacin zata amsa. Haka Ammy ta shansu a gurin sai da suka kusa bushewa sannan tace. 


“Tambaye ta miya hana ta zuwa aiki jiya”


Jekadiyar ta rada mata a kunne, sai Falmata ta kitsa musu irin karyar da Momy tai ma Tumba. Sai da Ammy ta kare mata kallo sannan ta dauke kai tana kallon Nana wacce ta shigo falon a yanzu. 


“Ammy key din motar za a bani ga driver can ya zo”


Wani banzan kallo Ammy tai mata. 


“Ba a bincike ko waye shi ba za a bashi aiki a gida nan? Ba al'adar gidan nan ba ce”


“Hajiya ta bincike shi ta san gidansu, ni ma kuma na sanshi”


“Fine.... Amman duk yai garkuwa dakw ba zan bada ko naira ba, sai dai ya kashe ki”


Nana ta yi shiru bata ce komai ba, sai turo baki take gaba, sai da taga Ammy ta dauke kai sannan ta wuce dakin Ammy ta dauko key din ta fice. Ammy ta bita da kallon takaici sannan ta kalli Falmata tace. 


“Kin iya addu'a”


Jekadiyar ta rada mata.


“Eh na iya sosai”


Ammy na kallonta cike da burgewa tace. 


“Waya koya miki? Mamana kamun ta rasu, kuma ina da Hisnul muslim na iya addu'oin sake da yamma”


Dan murmushi kadan Ammy tai tana jin gamsuwa da natsuwar Falmata a ranta, tana jin kamar ace Nanarta ce a haka. 


“To zaki rika musu addu'ar safe, da kuma yamma, za su rika wuni a hannunki har sai sun yi bachin dare sannan ki tafi gida, da safe kuma zaki zo tun 7am, idan kuma iyayenki za su yarda su barki ki rika kwana a nan shikenan”


Sai da Jekadiyar ta rada mata sannan Falmata ta amsa. 


“To Hajiya”


“Jekadiya a karbo yaran a gurin Iya, a fada mata an samu mai reno”


Jekadiya ta tashi dan cika umarnin Ammy, Falmata na zauna a gurin har Jekadiya taje ta karbo Labib da Luma ta kawo su falon Ammy. 


“Bismillahi Rahamanin Rahim”


Falmata ta fada a lokacin da Jedakiya ta mika mata Labib. Hakan kuma ba karamin burge Ammy yai ba, sai ta ji hankalinta ya kara kwantawa da ita. Wani irin murmushi da annashuwa ne suka mamaye fuskar Falmata, daman can tana son yara sai take jin kamar ance mata dauki ga yayanki nan ki yi raino. Da hannu Ammy ta nuna mata hanyar dakinsu sannan ta kalli Jekadiya tace. 


“Ki karasa mata bayani”


“To ranki ya dade Allah kara miki lafiya”


Jekadiya ta bi bayan Falmata rike da Luma. Sai da suka shiga cikin dakin sannan Jekadiya tace. 


“Duk inda kike so za ki iya shiga a cikin gidan nan dan raino, ana fita da su waje amman ba sosai ba, idan kuma zaki gyara dakin sai kin kai su dayan dakinsu tukuna, a yanzu dai duk sun iya zama suna koyon tsayi ne, sai ki kula da su sosai, ana ba su madara da kunun waken soya da nake hada musu, Ni ko Iya ne muke musu wanka da safe mu shirya su haka ma yamma, aikinki canja musu pampers”


Falmata ta gyada kai tana kallon jekadiyar wacce ta ke mata bayani cikin hikima da natsuwa, bata taba ganin ta ba sai hau haka zalika Jekadiyar ma bata taba ganin Falmata ba sai yau domin a lokacin da aka kawo ta gidan Jekadiya ta tafi mahaifarta ganin family. 


HAJIYA BABBA POV. 


After like 10 minutes da fitar Nana a falon Sirleem ya shigo, har ya zauna saman kujera be yarda ya daga kai ya kalli Hajiya ba, saboda ya san fushi take da shi. 


“Ka kyauta, ka bar nan ka je Kaduna gurin Karuwa ko? Yarinyar da Mahaifiyarka bata son mu'alamar ka da ita”


Sai a lokacin ya dago ya kalleta amman ya kasa furta komai. 


“Wai Sirleem yaushe zaka yi hankali ne? Mansurar nan fa ina jin ma ta tsufe ka ko ku zo wari miye riba a auren irin wannan kuma yarinyar da ba kabilarka ba? Me Mansura take da shi da Nana ta rasa?”


Wayarsa dake silent yake kallo kiran Mansura ne yake shigowa kamar tasan maganarta ake. Ba tare da ya dago ba tace. 


“Zan auri Nana ne kawai Hajiya saboda kina son aurena da ita, amman ba dan Nana tana cikin irin matan da nake so ba”


“Ko kaso ta ko karka sota duk uwarsu daya, kai bari ka ji na fada maka, ko da Nana zatai cikin shege ta haihu sai ka aureta, kai da za a ce Nana tana ta Hiv dole ne ka aureta, dan dole ne burina ya cika, dole ka yi min abun da nake so”


Kallon Hajiya kawai yake, zuciyarsa na raya masa da kamar akwai manufa a auren da Momy take son hada tsakaninsa da Nana, baya son yai wani mummunan tunani akan mahaifiyarsa kuma baya son zatonsa ya zama gaskiya, why ma Hajiya zatai haka? Mikewa yai tsaye.


“Zanje na kwanta”


Bata ce masa komai ba, ta dauke kai.


‘Waya sani ma ko kaine zaka lalata abun da aka fada’


Ta ayyana a ranta, can kuma ta sauke ajiyar zuciya. 


“Kuma wani lokacin fa bokayen nan suna karya, waya sani ko karya suke dan su ci kudi? Kai ni ban ma yarda ba gaskiya”


Ta fada a fili bayan ta tabbatar da cewar Sirleem ya fice daga falon. FADIME POV. 


“Koni abu dai be yi kyau ba”


Bappa ya fada cikin rashin jindadin abun da ya faru, muryarta ta dawo daidai bayan sun riga sun tafi, a yanzu kam kowa ya yarda Fadime tana da aljanu, domin su kadai ne zasu iya saka mutum haka. Daker da sudin goshi aka saka Fadime cikin gida, wani irin bakin haushin Wasim take ji tana jin kamar ta dauki wuka taje ta kasheshi, ba a taba zuwa ance ana sonta ba sai yanzu, kuma daga birni amman yasa muryarta ta zama abun tsoro sun gudu.


“Inna Hajjo ki ce musu muryata ta dawo su dawo dan Allah”


Amo dai bata ce komai ba sai hadiyar yawu take, domin ita ma a yanzu tana dan tsoron Fadime. Haka Fadime ta wuni a gidan tana kuka kamar an mata mutuwa data tuna sai ta ji kamar ma ba zata iya shan ruwa ba, ga wani uban haushin Wasim da take ji, har alwashin ta ci cewar indai ta samu sa'ar fita taje dajin nan sai ta samu dutse ko kuma ta je da wuka ta caka masa. 

Daker ta yi bachin dare kamin safiya ta waye duk ta matsu, so take kawai ta samu sa'ar fita taje dajin tai masa kacakaca domin dai yanzu ta gane shi din makiyinta ne, sai yanzu ta gano dalilin mafarkinsa da take ashe dan ya cutar da ita ne, yanzu ga miji ya zo amman yayi sanadin guduwarsa. 


Kokon da Inna ta dama mata kadan ta sha tace mata zata je gidansu Ma'u. 


“Ba fitarki ba ki dawo da hitina, ni tsoron hitarki nake”


“Inna daga gidansu ba zanje ko'ina ba, kawai labari zan bata”


“To Allah ya tsare amman ki kiyaye Malam yace kar na barki ki fita fa”


“Yanzu zan dawo”


Ta fice daga gidan cikin sauri kamar zata tashi sama, a maimakon ta nufi gidansu Ma'un kamar yadda ta fada sai ta dauki hanyar dajin, tana tafe tana matsifa har ta isa, da yake yau da masifa ta zo sai ta haye saman dutsen ma ta zauna tana jiransa, zuciyarta ta cika har ta kusa fashewa, ga kuka da take jin kamar zai subuce mata, data tuna abunda ya faru sai ta ji kamar ta fashe kuka. 


“Ba zan yi kuka a nan ba amman Wallahi yau ba zan kyale ba”


Maganar take kuka na subuce mata, kuma har ga Allah tsoro take ji, dan mutumen da zai iya dabon maciji kuma ya mayarda muryarta abun tsoro tasan ba karamin shu'umi bane. Kasa ta hango shi tsaye yana dago mata hannu, duk irin kaurin guiwarta da masifar da ta zo ta so sai fa ji kamar basa tare da ita saboda tsoron ganinsa da tai. Mikewa tai tsaye ta sauko saman dutsin ta tsaya a kasa. Kallonta yake cike da burgewa yana murmushi. 


“Me nai?”


Kallonsa tai kamar ta daka masa tsawa tai masa masifa kuma tana jin tsoro waya sani ko ya maida ta bera yanzu kuma. 


“Mutanen sun zo?”


“Miyasa ka karesu?”


“Ni na koresu?”


Ta fashe da kuka. 


“Sun gudu sun ji muryarta abun tsoro, yanzu ba za su sake zuwa ba, kuma gashi nan babu mai zuwa hadda birni suke ma kuma suna da mota, kuma ni ina son shi ya min, yanzu shikenan ba za su sake zuwa ba”


Kuka take da gasken gaske tana hawaye shar har idonta sun fara ja. Shi kam kallonta kawai yake yana murmushi kukan da take ma burgeshi take, a rayuwarsa be tana haduwa da macen da komai nata yake burge shi ba kamar Fadime. 


“Zauna”


Ta ki zama sai kuka take, kafadunta ya dafa ya zaunar da ita sannan shi ma ya zauna yana kallonta kamar zai cinyeta. 


“Ai wasu za su zo ko?”


“Babu wanda zai zo ni ba'a so na, Kuma fa yan boko ne”


Ta kara fashewa da kuka, sai yai dariya. 


“Ni ma nasan boko?”


Kyaleshi tai sai da ta gama kukanta sannan ta kalleshi tace. 


“To what is a now?”


At first murmushi ya fara kamin ya tintsire da dariya, daya bayyana fararen hakoransa, ya shafa kansa sannan ya kai hannunsa ya cafko wutar bayanta. 


“An sake saka miki wutar nan fa”


Wani uban zabura Fadime tai ganin hannunsa na ci da wutar. 


“Kai ne kake saka min ita”


“Ni ai ba zan cutar da ke ba, kuma idan aka sake saka miki wutar nan to zata kona mai ita ne”


Ya fada da fuska dake nuna babu alamar wasa a maganarsa. Ita dai kallon tsoro kawai take masa kamin ta fara tafiya a hankali tana yi tana waigensa har ta samu ta daina hangosa sannan ta lafta da gudu kamar an korota. SHATTIMA POV.


8pm yana zaune dakin karatunsa yana operating system dinsa Ra'ess ya shigo gidan. Mikewa yai tsaye ya kashe wutar dakin ya fito ya hanyo kofar, silently ya shiga kitchen ta hada ma kansa coffee yana fitowa Ra'ess na kawowa kofar kitchen din. 


“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”


Ra'ess ya fada da karfi yana kallon Shattima dan be san da akwai mutun a cikin kitchen din ba, tun abun da ya faru a kauyensu Fadime ya kasa dawowa daidai ga shi ya kasa daina jin muryar a kunnensa. 


“Are you okay?”


Shattima ya fada yana kallonsa, sai ya shafa fuskarsa yana jin kamar gumi na sauko masa. 


“I'm not, Wallahi i'm not....... kai......!”


Ya fada sannan ya karasa cikin kitchen din ya bude fridge ya dauko ruwa mai sanyi ya sha sannan ya firo falon ya zauna, Shattima dai a tsaye jikin kofar yana kallonshi. Can ya dago ya kalli Shattima.


“Neman aure na je wani kauye, amman na rasa ganewa, amman garin ai akwaishi, sai dai idan su wadanda muka je gurinsu ne aljanu, malam kaji wata murya?”


Ra'ees be karasa ba Shattima ya tintsire da dariya kamar ba shi ba, daman can ya san Ra'ees da tsoro, amman a yanayinsa na yau ya tabbatar da abun da ya gani babba ne ba karami ba, but the funniest part is neman aure fa suka je kamar yadda ya fada, be fada masa komai ba a matsayinsa na babban abokinshi gashi yanzu sun dawo da wahala. 


“It's not funny Man ba abun dariya ba ne”


Shattima ya gintse dariyar da murmushi. 


“Then kuka kake son nai? Imagine ka je neman aure ba tare da sanin best friend dinka ba?”


Sai da Shattima yai maganar sannan Ra'ess ya tuna cewar Ammy tace kar ya bari ya san komai sai magana ta yi karfi. 


“Kai ba fa aure zan kara ba, wani na raka”


Ya fada yana kokarin kawarda tunanin Shattima daya kasa daina murmushi ganin yadda gumi yake ta karyoma abokin nasa. 


ZAINAB POV. 


Sai da suka gaisa sannan ta shigo da shi falon baki a inda ta saba shigowa da shi idan za su fira, sannan ta tashi ta shigo cikin gida ta saka mai aikin gidan ta jera masa abinci da lemu. 

Be ci komai ba, dan babu abun da yake bako a cikin abun da aka shirya masa, ruwa kawai ya sha ya cigana da danna wayarsa. 

Ba a dauki dogon lokaci ba ta dawo fuskarta dauke da murmushi zuciyarta kuma cike da kaunarsa ta zauna a kujerar dake kusa da tashi. 


“Zata fito yanzu ku gaisa, idan ka gaisa da ita sai na kira Ammy ku gaisa”


Ya gyada mata kai yana kara kallon kyakkyawar fuskarta wacce ke dauke kamar masa hankali a ko yaushe, ba ma shi kadai ba most mazan da suke sonta kyauta ne yake daukar hankalinsu.


“Allah yasa dai kar sai magana ta yi karfi matarka tace na ci amanarta”


Gyara zama yana cigaba da kallonta fuskarsa dauke da murmushi.


“Ai ba haram mu kai ba, kuma ko da baki nemi ni ba, ni zan kawo kaina da kaina gurinki, idan na fada miki cewar na dade da kaunarki cikin raina ba za ki yarda ba”


Ta yi murmushi. 


“Zan yarda ma ganin yadda kai saurin amincewa da ni”


Lokaci daya suka daga kai suna kallon Iya wacce ta shigo falon cikin shiga ta alfarma kamar ba ita ba. Ba laifi ta sake masa fuska kamar da gaske tana na'am da shi din, har kasa ya kai ya gasheta Zainab kuma tana ta kallon Iya cikim jindadi, a iya tunaninta irin wannan ranar Iya take jira na ganin surukunta. Halshe Iya ta fitar kadan ta laso kurwarsa dake yawo a bayan kansa tasa hannu ta jimke ba tare da ita Zainab din ta kura ba balle kuma shi da ya ki yarda su hada ido. 

Cikin mutunci da girmamawa suka gaisa sannan ta mike tsaye tana Allah shi masa albarka ta fice. Sai ya ciro bandir din yan dubu ya mikawa Zainab. 


“Baby gashi ki bata ta siye goro”


Zainab ta karba tana murmushi ta bi bayan Iya ciki farincikin yau uwarta da mijin da zata aura sun gaisa da juna. 

No comments

Powered by Blogger.