Hamrah Complete Hausa Novel

 


               💞💞hamrah💞💞                                              

Hi every one am here again with anotherstory hope yhu will like it*....           *'Yar mutan Ada

Writer: fateemah Murin


Wattpad: muhdfatimagurin Page ➡1⃣


*******


Kwance take akan makeken royal bed d'inta tana latse latse a wayar ta kirar iphone 11 sanye take cikin Arabian gown me shegen kyau ta yana gyalenshi a kanta, d'an banzan hill ne a kafanta, kyakyawa ce ta karshe sossai take da kyau...... 


"Hamrah plz ki tashi kin san kin ajiye mutane kusan 20mins kenan amma ke kina kwance anan bayan kin shirya ba kyau fa wulakanci" wacce take kwancen ta d'ago idonta a hankali ta sauke akan me maganan..... 


Cikin sanyin murya tace "simra plz spare me, Ina ruwanki ni ce fa CEO na company d'in nan so duk abunda nake so shi za'ayi kuma don an jira ni a meeting ba wani abu bane" simra tayi saurin katse ta "to hell with the CEO ko ke wacece a duniyar nan baki da right d'in wulakanta d'an Adam I see no reason..... 


Wai ke kina tausayin mahaifinki kuwa? Ya d'auki ragamar company d'inshi gabad'aya ya sakar miki amma be huta ba, zan iya rantsewa kin kai 3weeks rabonki da office, baki san me ke tafiya ba......"


Katse ta hamrah tayi tana cewa "ya ishe ni plz, zaki iya zuwa mosque kiyi preaching d'inki bye" ta mike ta d'auki hand bag d'inta da wayanta a hannu ta fice tana zuba mahaukacin kamshi, tana fita ta samu mota biyu a dai dai kofan parlor d'insu da securities d'inta a tsaitsaye, da sauri suka bud'e mata mota ta shige suka fad'a d'ayan drivern yaja da gudu suka fice daga mansion d'in...... 


Fareed tower suka shiga babban building da ya amsa sunan shi me hawa 25, har gaban entrance na building d'in suka yi parking da sauri suka fito suka bud'e mata fita tayi cikin tafiyanta na kasaita ta shige building d'in..... 


********


Hamrah fareed kenan the great CEO/heir of fareed company, the only daughter to mr. Fareed Ahmad da Barr. Suhailah aryan, 'yar shekara 22 me ji da kyau da kud'i, mr. Fareed su biyu iyayensu suka haifa da sister d'inshi ummul-khiram sun taso cikin kud'i da ilimi iyayensu 'yan boko ne na karshe..... 


A Harvard university fareed yayi degree d'inshi akan business inda ya koma oxford university yayi masters d'inshi duk akan business anan oxford d'in yayi doctoring degree d'inshi tukun ya dawo nigeria ya fara juya business d'in mahaifinshi, sister d'inshi ummul-khiram ita ma a Harvard tayi karatu zuwa matakin degree...... 


Sossai suka yi daga da mahaifinta da tace karatun ya ishe ta haka ita aure zatayi, har ta tsayar da wadda zata aura da kyar mahaifinsu ya yadda akan hakan suka shirya tafiya dubai yi mata sayayyan kayan d'akintan daga chan suka wuce Saudi sukayi umura tukun suka d'auko hanyar nigeria inda suka samu mummunar plane crash da ba wadda ya tsira a cikinsu..... 


Sossai rashin ya girgiza fareed ya zamana shi kad'ai dama family d'insu ba wani yawa ne da su ba Asalinsu 'yan kano ne yayinda mahaifiyarsu shuwa Arab ce kuma family d'inta are against auren shiyasa suka yi nisa da ita ba wani sanin su fareed yayi ba......... 


Brr. Suhailah aryan ficecciyar barrister da ake ji da ita a nigeria asalin mahaifinta balarabe ne yayin da mahaifiyarta take 'yar asalin nigeria jihar kano, tun tana karama Allah yayi wa mahaifinta rasuwa mahaifiyarta hajja nana ta d'auko ta suka dawo nigeria anan tayi krt daga nursary d'inta har secondary tukun ta tafi india anan ta karanci law....... 


Sun had'u ne ta sanadin wani problem daya taso ma fareed a company d'inshi wadda yake bukatar lawyer asalin lawyer d'in mahaifinshi wadda ya zama nashi be kasa shine ya had'a shi da suhailah, anan tazo tayi iya kokarinta har suka shawo kan problem daga nan ya fara sonta be yi nauyin baki ba ya fad'a mata, dayake bata da wani wulakanci da ji da kai duk da kyaun da Allah ya mata sbd mahaifinta ta d'auko, duk da fareed d'inma ba baya ba duk kyaun mahaifiyarshi ya kwaso bata wani ja lokaci ba ta amince...... 


Ansha buki sossai duk da 'yan uwan angon kad'an kawai suka zo daga chad, zaman lafiya sukeyi kowa na aikinshi, har aurensu ya shekara 7 suhailah bata ta'ba ko 'batan wata ba, abun ya fara damunta amma se fareed ya kwantar mata da hankali da "haihuwa ai na Allah ne, in da rabon haihuwan se kiga kin haihun karki cire rai ga rahamar ubangiji"...... 


Kullum nasiharshi kenan a gareta, kwatsam se ga ciki, soyayyar duniyar nan gabad'aya suka d'aura akan cikin nan, ba karamin gata aka tanada ma babyn da be ma san sunayi ba, bayan wata tara ta santalo 'yarta kyakyawa wacce tayi karo karo na kyau se tazo tafi iyayen nata da suka tsammata kyaun, anyi shagali sossai inda yarinya taci sunan mahaifiyar fareed "HAMRAH" sam ya ki a boye mata suna........   


Anan Abuja tayi daga nursary d'inta har secondary daga nan ta wuce India tayi first degree d'inta anan ta gamu da simra 'yar india ce ba musulma bace lokacin da suka had'u ita ma ba baya ba wajen kyau haka mahaifinta ana ji da shi a india kuma yana tashen kud'i, bayan ta gama ta koma gida se simra tayi mata maganan masters da farko tace baza tayi ba se kuma ta chanza ra'ayi zama sukayi suka za'bi university da suke so..... 


Oxford suka za'ba ba'a b'ata lokaci ba aka sama musu suka wuce duk department d'insu d'aya inda suke karantar business, tana dawowa nigeria ne mahaifinta ya sakar mata ragamar company d'inshi tana son mahaifinta kaman ranta, a lokacin ne kuma kawarta simra ta musulunta, sam bata samu matsala da iyayenta ba sbd sunga takai ta zabi addinin da take so....... 


Nigeria tazo ta musulunta tana zaune gidansu hamrah d'in, dr. Fareed ya kawo mata babban malami tana d'aukar karatu a gurinshi sossai ta mai da hankali akan addini wani lokacin hamrah d'in ke daura ta kan hanya don hamrah ba baya ba wajen ilimin addini sossai take da ibada sede tana da dan banzan wulakanci mussaman akan samari ita har yanzu bata ga wadda ya dace da aurenta ba kowa low class ne in kuwa kayi gigin furta mata se ta tsiga maka abunda har ka mutu baza ka manta ba........ 


*******


Private elevator ta shige a take ranta ya baci ganin wani saurayi tsaye ciki dama kaman ta ga shigan mutum Allah ya taimake shi da ya danna kafin ta karaso da se ta jira kenan don taimakonshi zata ce sbd be isa ya sa ta jira bata wulakanta shi ba.......


tsaki taja a fili ko dago kai saurayin be yi ya kalle ta ba abunda ya kara bata mata rai kenan  dogo ne sossai ga alamun karfi sun bayyana a jikinshi daga gani ya saba daga karfe kuma kyakyawa ne a zuciyarta take maganan wani tsaki ta kara ja a ranta ta sake cewa ko me damuwa na da kyaunshi? Mtseww..........


Tabbas ranshi ya soma baci ya tsani tsaki a rayuwarshi in har kuwa ta kara ja ba abunda ze hana shi tsinka mata mari be gama tunaninshi ba elevator din yayi wani jijjiga da alamu an dan samu matsala ne bottle water dake hannunshi da ya bude da niyyar sha ya fallatsa se fuskarta a take ya jike mata fuska zuwa gyale.........


Wani irin numfashi tajaa cikin tashin hankali da matukar tsoro ta daga hannu ta tsinka mishi mari shi kuwa ya dago da niyyar bata hakuri sbd ya san be kyauta ba kuma ruwan da sanyi se Jin saukar mari yayi muryanta a sama tace "in banda hauka da dakikanci taya zaka watsa min ruwa ruwan ma me sanyi kasheni kakeson yi ne?...........


Kallonta kawai saurayin ke yi tabbas ba wadda ya san farin cikinshi haka ba wadda ya san bacin ranshi amma da ba don haka ba tsayuwa a gurin ma se ya gagare ta wani irin turiri ranshi ke yi amma baza ka taba ganewa ba a daidai lokacin da elevator din ya tsaya ta furta "bloody fool" tare da ficewa tana mamakin wa ya bashi izinin shiga private elevator............


Office dinta ta nufa seda ta shafe wasu 30mins din wurin gyara fuskanta da jikinta tukun ta nufi meeting hall d'in da zasuyi meeting d'in tana shiga ba hi ba hello kawai tace "shall we start the meeting?" A sanyaye suka amsa mata da "yes" kafin su rufe baki sukaji an ce "to hell with the meeting" kowa bayan kujeranshi ya zuba ma ido a hankali ya juyo da kujeran ya fara fiskantan ta shanyayyun idanunshi ya zuba mata na kusan 2min........ 


Bud'e baki yayi da niyyar yin magana se kuma ya fasa mikewa yayi ya fice daga company d'in cikin haddad'un motocinshi ranshi na wani irin suya kenan itace CEO na companyn kenan?lallai se tayi dana sanin marin da ta mishi a duniya baze iya tuna randa aka taba marinshi ba balle duka se ta gwammaci kida da karatu batun ta ya share ya shiga wasu harkoki don yana da tabbacin se ta neme shi shi kuma anan ne zeyi maganinta anan ne ze gasa mata aya a hannu smirk yayi tare da jan kwafa..........


a meeting hall d'in kuwa kowa shiru yayi yana jin yadda hamrah take zazzaga masifa "who the hell did he think he is? Ya ma isa duk abuja akwai wadda ya isa ja da ni, lallai se ya d'and'ana kud'ar shi se yay da na sanin wulakanta ni, se nayi sanadiyar barin shi aiki" gani tayi dukkan board of trustee d'in ba wadda ya iya magana kowa kanshi a qasa........ 


Cikin jin haushi ta fice daga hall d'in ta nufi office d'in da babanta ke yawan zama sbd ya riga ya bar aiki taimakon ta kawai yake yawan zuwa yi, tana zuwa ta banka kofan ta shiga da sauri ya mike yace "daddy's princess" ranta a 'bace tace "daddy who the heck is that? Daddy he spoiled my mood"......... 


A natse daddyn yace "where is he?" Tace "he's gone ko meeting d'in bamuyi ba" zaro ido yayi da sauri yace "kina nufin a meeting hall mutumin yake? Ya kamanninshi?" Cikin jin haushin yadda daddynta yayi sbd mutumin da kuma tunanin kyakywar fuskanshi da ya fado mata tace "I don't know" da sauri ya d'auki landline ya danna wasu numbers........ 


Yace "what happened at the meeting hall?" Bayani wadda ya kiran ya mishi da karfi ya kifa wayan tare da runtse idonshi yana bud'ewa har sun chanza kala ya kalli hamrah yace "Kin kashe ni hamrah" da sauri ta rike hannunshi hawaye na taruwa a idonta tana mugun son mahaifin ta sam bata had'a sonshi da kowa ba, sossai mamaki ya kama ta sanin mahaifin ta be ta'ba kiranta da ainihin sunanta ba se yau kafin tayi wani magana ya sake cewa........    


"Hamrah kin san kuwa waye Haisam mas'ood sa'ood? You ruined me hamrah innalillahi wa'innailaihi raji'un" tari ya fara sossai se jini ya biyo baya sossai hankalin hamrah ya tashi me ta aikata? Waye shi? Me yasa hankalin mahaifinta ya tashi haka? Hawaye ne suka gangaro mata kafin kace kobo mahaifinta ya fad'i kasa ba numfashi ihu ta kurma tana qiran "dad daddy no plz daddy" da gudu ta fita ta kira securities suka d'auke shi cikin gaggawa suka nufi "HMS specialist hospital, dake nan suke da NHIS d'insu"........... 


Da sauri aka kar'be su aka wuce dashi emergency kuka sossai hamrah ke yi da sauri ta d'aga waya ta kira mommynta tana d'agawa ta kara karfin kukanta tana cewa "mo..... mmy......... M.... om...... my" ta kasa magana cikin tashin hankali mommyn tace "baby where are yhu, what happen where is your inhaler?" Numfashin hamrah ne ya fara tafiya duk kokarin da tayi na daidaitawa abun ya ci tura tun tana jaa a tsaye har ta fad'i da sauri securities d'inta sukayi kanta kowa na tambayar inhaler d'inta amma babu......... 


Kan kace kobo ta sume a take nurses suka nufe ta suka d'aga ta zuwa wani d'aki tare da kiran doctor don yi mata allura momynta jin yadda suke hayaniya yasa cikin tashin hankali ta kashe wayan ta kira d'aya daga cikin securities d'in yana dagawa ya mata bayanin abunda ke faruwa cikin mintuna se gata a asibitin a lokacin har asthman hamrahn ya sauka se kuka takeyi......... 


Da sauri momy ta karasa d'akin ta rungume ta tana lallashi da kyar tayi shiru tare da mata bayanin abunda ya faru ba tare da damuwa ba tace "ya sunan wadda kukayi hakan?" Shiru tayi alamun tunani tukun tace "wai haisam mas'ood sa'ood ne ko wa" zaro ido momy tayi tukun tace "hamrah ya ilahi" dafe kanta tayi cikin fusata tace "momy wai ni kam waye wannan guy d'in ne da kuke ta damuwa don na wulakanta shi? Haba dan Allah"........ 


Jan hannunta momy tayi zuwa d'akin da aka kwantar da mahaifinta bayan fitowansu emergency se bacci yake yi cikin kwanciyar hankali zama sukayi kowa da abunda yake tunani................ #vote

#comment

#share


'Yar mutan Adamawa💞💞💞


                      💞💞hamrah💞💞


   

                                                     💞💞Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin 


             *'yar mutan Adamawa*


Page➡2⃣


*********


A hankali mommyn tace "baby company d'in mahaifinki is in real danger da in be samu an dafa mishi ba he will be ruin for ever, tun farkon matsalan ya sawa kanshi damuwa har hawan jini ya kama shi kuma kinsan yana da diabetes sam basa had'a hanya da hawan jini, so yayi gwagwarmaya da kyar ya samu ya gana da Haisam mas'ood sa'ood har ya aminta ze dafa mishi har company d'in ya tashi da kafafunshi........... 


Shine fa ya bawa company makudan kudi tare da sharud'a and kuma yace yana son ganawa da members d'in companyn kafin aji sharad'inshi har CEO tayi signing contract d'in, sam mahaifinki be so ki je ba na takura mishi ya barki kika za'bi time da kanki, but you end up disappointing me, duk da banji sanadiyar fad'uwar mahaifinki ba but am very sure meeting d'in da kukayi se a hankali".. .  ......   


Hawayen fuskanta ta share tana tuna marin da ta mishi a fili ta furta "innalillahi wainna ilaihi rajiuna mommy me yasa toh kuka boye min ai da na d'auki abun da muhimmanci and kuma waye haisam mas'ood sa'ood?" Mommy tace "mahaifinki ne ya hana a sanar da ke sbd kar hankalinki ya tashi, haisam mas'ood sa'ood hmmnn dan wani attajiri ne mas'ood sa'ood wadda aka kashe a shekaru 28 baya, haisam shine kad'ai d'ansu da komai nasu......... 


Medicine and surgery ya karanta har ya gama karatunshi business d'in mahaifinshi na hannun amintattun mahaifin nashi d'aya bayan d'aya suma Allah ya d'auke ransu shine haisam d'in ya ajiye aikin asibiti ya fara kula da business d'in mahaifinshi karfi da yaji ya koma business man duk da ba field d'inshi bane, he owns many company's, hospitals and orphanages duk 36 states d'in nan d'aid'ai ne be da company, hospital and orphanage"............... 


Motsi daddy yayi da sauri sukayi kanshi hamrah ta kama hannunshi tana hawaye tace "am sorry dad am really sorry, I know that I disappointed you but plz ka sake bani dama zan nemi haisam in roke shi gafara akan abunda na mishi everything will be okey in shaa Allahu".......... 


Murmushi me ciwo daddyn yayi yace cikin muryan marasa lafiya "hmmm uwata baki san waye haisam ba ai tunda ya bamu opportunity mukayi watsi dashi baze kara bamu wani ba, numfashi ya jaa tukun ya ci gaba, haisam na da tsauri sossai a cikin alamuranshi ba abunda company d'inmu zasu Kara mishi ko su rage mishi a cikin d'unbin arziki da Allah yayi mishi kiyi hkr kawai damar nan ta wuce mu"........... 


Girgiza kai hamrah tayi tace "daddy be wuce ba in shaa Allahu I will try my very best ze sake waiwayan mu da izinin Allah" a zuciyarta kuwa da na sani ne fall don ma basu san ta mare shi ba da yau mahaifinta se ya dake ta abunda ba'a taba mata ba kuma ba fata take ba..........


gyad'a mata kai kawai daddyn yayi sukayi murmushi a tare fad'a sossai iyayen nata suka mata akan wulakanta mutane jikin ta yayi sanyi tana kara tuna irin fad'an da sukayi da simra duk akan zuwa meeting da wuri da kuma wulaknci amma tayi watsi kamar bata san gaskiya ta fad'a mata ba............ 


Bayan Kwana biyu aka sallami mahaifinta tare da daura shi akan magani suka dawo gida a cikin Kwana biyun nan sam bata samu lokacin kanta ba kawai processing yadda zata had'u da haisam take yi amma abun kaman ba sauki, sossai yanzu ta mike akan company d'insu jin hatsarin da yake ciki da barazanar rufewa yasa ta kara kaimi wajen aiki da kyar take bacci simra ma ta sa mata hannu sede sun kasa samun me tallafa musu dole de se sun komawa haisam gashi ganinshi yayi wuya...   .. 


********


Kwance yake akan makeken royal bed d'inshi yayi matashi da hannayenshi ya tallafe keyarshi da su idonshi a rufe kaman me bacci amma ganin yadda yake kad'a kafanshi yasa na gane ba bacci yake ba tunanin marin da ta mishi yake lallai ta dibo ruwan dafa kanta ya riga ya tsara abunda ze mata daki daki don wlh tallahi bata mari banza ba tun randa ya bar companyn ya kira manyan companies da yake da share ya gargade su akan tallafawa fareed tower kuma sun hanu yanzu next step yake tunani........


kyakyawar fuskanshi na kura ma ido, lallai gayen nan ya had'u iyakar had'uwa kyakyawa ne na ajin karshe.......... 


Dogo ne sossai yana da siffa irin na kauraran maza kirjinshi a bud'e yake sossai yayin da ya tsuke daga kwankwaso kanshi a cike yake da gashi baki wuluk se tsantsi an mishi gyara na ban mamaki, manyan brown  oily eyes nashi  kullum suna a lumshe kamar me bacci, hancinshi dogo ne kaman pencil amma daga qasa se ya d'an karye ya lankwashe kad'an se d'an madaidaicin lips d'inshi kyawawa red sossai kaman ya shafa man baki........... 


Gashin giran shi a kwance kaman an zizara, ba fari bane kuma baza a kira shi baki ba sannan yafi wankan tarwad'a fatanshi me sheki ne sossai da taushi a gani d'aya zaka iya ce mishi fari ne sede ba farin bane, kirjinshi a cike yake da kwantattun gashi masu kyau da ban sha'awa wadda ya bi har shara'banshi na hannu da na kafa a kwance suke lufluf......... 


Sam fuskanshi ba fara'a a had'e yake tam kamar an aiko mai da sakon mutuwa, kai tun tashinshi ba takaiman man mutum da ze iya cewa ya ta'ba ganin dariyarshi abu ne wadda be yi ko da murmushi ne kuwa se wani kafurin murmushi da yakeyi in abu ya bashi dariya murmushin gefen baki wadda ko fuskanshi gabad'aya be zagaye wa shine murmushinshi kuma shine dariyarshi, Abokin shi d'aya S.A sagir Ahmad soja ne d'an jihar Adamawa........  


Iyayensu kafin su rasu aminaine sossai, shima S. A maraya ne be da uwa be da uba se de yana da 'yan uwa ta 'bangaren uwa da uba se yayyu manya mata shine karami kuma na miji sa'banin haisam da shi kad'ai se iyayenshi ya tashi ya samu kanshi da  Allah ya musu rasuwa kuma se ya koma rayuwa shi kad'ai se in sun had'u da S. A suna yawan had'uwa kasancewar aikin haisam a sati se ya zagaye states d'in nigeria......... 


Agogo ne shi sarkin aiki gashi yana wuya kaga ya yarda da mutum, magana ma in bata business bane toh be magana da kowa se S. A....... 


*******


"Hello" shiru tayi tana jin bayanin da secretary d'inta ke mata "what kana nufin ya bamu appointment amma a yola?" Daga d'ayan bangaren aka ce "sorry ma'am haka secretary d'inshi yace and he said yanzu hk yana abuja amma yace in kina son ganinshi yhu should meet him at adamawa 10am prompt".......... 


Dafe kai tayi cikin jin haushi tace "kayi min booking na available flight,  now" yace "ohk" tare da kashe wayan tana ajiye wayan ta buga tagumi tana jin takaici na kamata a haka simra ta same ta tana tambayar ta me ya faru, bayani hamrah ta mata, hakuri simra ta bata tana cewa ta daure kar ta karaya ko don mahaifinta, da karfin gwiwa ta mike ta fara shirya abunda zata bukata a karamar trolley duk da tsoron dake ranta sam taki fadawa kowa abunda ta mishi har simra kuwa gashi bata san me yake shirya mata ba da ya kira ta adamawa......... 


********


Cikin natsuwa ya mike da takun shi na qasaita ya fara cire kayan jikinshi se da ya saura daga shi se boxers tukun ya zaro towel d'inshi fari Kal ya shige toilet dake manne da d'akin se da ya shafe wajen mintuna 40 kafin ya fito ya nufi closet d'inshi kaya ne kala kala ko wanne da bangaren da aka ajiye shi a goge tsab, half jumpa ya d'auka ya saka black gezner me sheki ya sa black Zanna me adon fari a kanshi da half cover black........ 


Black Gucci wrist watch yasa a hannunshi ya fito tsab da shi se fitinnannen kamshi ke tashi a jikinshi me sanyi, a natse cikin takun isa da kasaita wayanshi kawai ya d'auka yayi gaba abunshi yana fita daga d'akin ya nufi dining area, abinci d'an kad'an ya zuba kaman wadda ze bawa baby ya hau ci a yangance a hakan ma be karasa ba ya mike, fitowa yayi da sauri me mishi hidima da kuma shugaban securities/escorts d'inshi....... 


Yaqoob ya taso ya karaso kanshi a kasa cikin husky masculine voice d'inshi yace "ka fad'awa pilot d'in nan yayi arranging jirgin nan zamu wuce yola yanzu" cikin isa da bada umarni yayi maganan a natse Yaqoob yace "ohk sir" da sauri ya juya yana waya, komawa haisam yayi ya samu cushion ya zauna yana danna waya kusan 20 mins kafin yaqoob ya dawo ya fad'a mishi an gama se da ya Kara 5mins tukun ya mike ya fice a mota aka d'auke shi aka nufi filin tashi da saukan jirgin duk a cikin gidan........ 


Suna isa aka bud'e mishi kofa ya fita ya nufi jirgin da an riga ma an kunna shi kawai suke jira basu Kara 2mins ba suka tashi daga shi se yaqoob se pilot d'in jirgin cikin 40mins suka isa yola straight gidan shi na malamre suka wuce dake jimeta se da yayi wanka ya ci abinci ya huta tukun around 2 ya nufi gidansu S. A........... 


******


Washegari karfe 8 daidai jirgin hamrah ya sauka a modibbo Adama international airport dake jimeta direct textile company d'inshi dake jimeta ta nufa a taxi ko breakfast batayi ba tana isa aka mata iso har gurin da ya kamata ta jirashi.............. 


Zaman good two hours tayi ko me Kama dashi bata gani ba se workers d'in companyn ke kai kawonsu,  wayanta ta fitar ta fara wasa da shi ta kai wani hourn zaune tana online da ta gaji ta fita ta shiga best game d'inta candy crush ta fara bugawa ta kai hour again tana bugawa nan ma gajiya tayi ranta ya sosu sossai kwanciya tayi ta jingina kanta da kujeran dake zaune ta lumshe ido..........


Chan hawaye ya gangaro mata mikewa tayi ta kalli time a kalla ta kai 5h zaune a gurin mikewa tayi tare da neman ganin secretary d'inshi aka ce mata be zo ba tare suke, kiran nata secretary d'in tayi yana d'auka murya na rawa tace "please Arham call haisam's secretary wai ya manta sun bani appointment ne, am here for at least 5hours amma har yanzu basu appearing ba"............. 


Daga chan secretary d'in yace "subhanallah sorry ma'am let me contact him" bata amsa ba ta kashe wayan ta ci gaba da share hawaye a boye.............. 


********


Kwance yake akan santalelen gadonshi yana danna waya wadda ban san me yake yi ba shirye yake tsab cikin riga fari me V neck da blue jeans me zips dayawa a jiki, ya gyara kanshi sossai se sheki yake hannunshi sanye da wani gold wrist watch na relogio masculino, d'ago watch d'in yayi ya kalli time tare da yin smirk d'in da ya mayar dariya ya mike ya zauna a daidai lokacin yaqoob yayi sallama........ 


Amsawa yayi daga bakin kofa yace "sir batun appointment d'in da ka bayar fareed company's CEO was here since 8am" ranshi a had'e yace "I know" da mamaki yaqoob yake kallonshi sbd ya san be wulakanci amma ace yau ya ajiye mutum kuma mace na kusan 5hours amma be damu ba? Tun karfe goma yake tuna mishi appointment da ya bayar da kanshi amma yayi kaman be san da shi ba......... 


Kaman a sama yaji yace "shift the appointment to HMS orphanage home 4pm prompt" da tsantsar mamaki yaqoob ke kallonshi kallon da haisam ya mishi ne yasa shi fita da sauri secretary d'inta ya kira ya fad'a mishi shi kuma ya fad'a mata hawaye ta share bayan ta kashe wayan tare da jan trolley d'inta ta fice daga companyn........ . 

#vote

#share

#comment
'Yar mutan Adamawa💞💞💞                        💞💞hamrah💞💞


     

                                                    💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin 


           *'yar mutan Adamawa*


Page➡3⃣


*********


Tana fita ta tare taxi ta shige baya ta zauna har lokacin tana share hawaye lallai se yau ta san wulakanci ba kyau kuma WULAKANCI DODO NE yakan ci me shi, adua ta ringa yi Allah yasa hukuncin ya tsaya iya nan muryan me taxi d'inne ya katse ta daga tunanin da ta fad'a "hajiya ina muka nufa?".......... 


Cikin muryanta me sanyi tace "dan Allah ka kaini restaurant me kyau in sayi abinci se ka kaini best hotel a nan" cikin girmamawa yace "ohk ma'am" Valla restaurant ya kaita ta sayi best food d'insu margi special she taste it once and she can't afford missing it now bayan ta basu kud'in suka mata packaging ta fito tare da shigewa taxin....... 


Green land hotel ya kaita gurin ya mata kyau sossai shiga ciki tayi bayan ta sallame shi ta Kama room na kwana d'aya kawai ta shiga a gajiye ta fad'a saman gado da sauri kuma ta mike ganin time toilet ta fad'a sharp sharp ta watsa ruwa tare da alwala tana fitowa ta bud'e akwatinta ta fito da doguwar riga baka me tsararren kyau ta saka tare da jefa gyalenshi kan gado ta d'auko madaidaicin hijab ta sa tare da fuskantar gabas....... 


Wadda a cikin room d'in da take aka manna green paper a jiki an rubuta 'qibla' da sallaya a shimfid'e tada sallah tayi bayan ta idar ta cire hijabin ta ninke ta ajiye a kan sallayar, ba d'ankwali a kanta gashinta ya zubo har kan kirjinta ta gaba a haka ta samu kasa ta zauna tana gyara gashin da ya rufe mata fuska abinci ta fara ci a natse....... 


Bayan ta gama ta d'auki waya ta kira simra "hello besty ya kk" daga chan tace "fyn babe ya kun had'u?" Kwafa hamrah tayi tace "ya de wulakanta ni simraa for almost 5h ina zaune ina jiran bawan Allah daga karshe wai se four in had'u dashi a gidan marayunshi" 


Cikin sanyin murya simra tace "karki tada hankalinki besty komai ze zo da sauki" murmushi kawai hamrah tayi tace "ina dad?" Shiru simra tayi na 'yan mintuna tukun tace "he's with his doctor jikin nashi har yanzu ba daad'i"  hawaye ne ya gangaroma hamrah da sauri ta share tare da sallama da simra ta kifa kanta a bakin gado ta hau kuka........


A haka bacci ya dauke ta cikin baccin ma bata samu natsuwa ba don mafarkinshi tayi wai ya mare ta a d'an tsorace ta farka tare da kallon time ganin three yasata mikewa tana dafe kanta dake tsananin ciwo a daddafe ta fad'a toilet tayi alwala tana fitowa ta bude jakanta ta fiddo powder ta shafa tare da sa lip balm da kwalli a idonta..........


Hijab ta sa tare da tada sallah tana idarwa ta daure gashinta da ribbon babba tare da yane gyalen doguwar rigar jikinta a kanta flat shoe baka ta saka me taushi sossai da tsada d'an karamin side bag shima baki tayi kyau sossai a haka ta fita da tafiya cikin natsuwa baza ka taba cewa tana da damuwa ba alhalin zuciyarta fal yake da damuwa a haka ta tari taxi ta shige........


"HMS orphanage foundation" abunda ta furta kenan ta jingine kanta da jikin kujera tare da lumshe ido, bata bude ba seda taji me taxi din yace "mun iso hajiya" tukun ta bude sauka tayi tare da sallaman shi ta taka ta isa tangamemen get din gidan marayun da sauri me gadi ya tarbe ta yana mata sannu da zuwa cikin sanyin murya ta amsa mai tare da tambayanshi inda zata ga mai gidan...........


Bude mata get yayi tare da mata kwatancen office dinshi, alheri tayi mishi tukun ta wuce se godiya yake zubawa cikin takunta na natsuwa da daukar hankali wadda naturally haka tafiyanta yake ta kutsa kai cikin gidan marayun tabbas ta jinjinawa kokarinshi gida ne tangameme tsararre gwanin kyau da burgewa wadda wasu masu iyayen ma basu samu ko kwatan shi ba..........


A hankali take wuce wurare tana haduwa da daidaikun yara maza ko mata duk kuwa wacce suka hadu zasu duka har kasa su gaida ta cikin sakin fuska take amsawa a haka ta karaso wani tangamemen fili wuri ne na wasan yaran da football field, basketball field, table tennis, da dai sauransu yaran sun kakkasu kowanne da wasan da suke duk maza ke gun...........


Cikin annashuwa da kwantaccen fara'a ta wucesu tabbas sun burgeta ba kadan ba duk da ta fara gajiya da tafiyan kallon kwantaccen kwalta 'titi' dake shimfide a tsakiyar gidan wadda bata ganin karshen shi wato kenan abun hawa na shigowa ai da tace me taxin ya shigo da ita abunda ta kiyasta kenan a ranta don ta fara gajiya da tafiyan kasancewar bata doguwar tafiya sbd yanayin asthma dinta........


Yawanci in tayi tafiya me tsai se numfashi ya sarke mata chronic asthma take da kwalla ne ya cika idonta da ta tuna bata dauko inhaler dinta ba adu'a ta fara na Allah ya tsare ta ya rufa mata asiri kar ciwonta ya tashi..........


Da kyar ta samu ta isa inda aka ce office dinshi ne numfashinta na fita da sauri sauri, zama tayi bakin kofar inda aka jera wasu kyawawan kujeru masu kyau seda ta huta sossai tukun tayi knocking seda ta shafe 5mins tukun taji an amsa mata murda kofan tayi ta shiga da sallama..........


Da kyakyawar fuskanshi tayi arba zaune a kan kujera ya kwantar da kanshi tare da lumshe ido yana juyi da kujerar be amsa sallamar ba haka be bude ido ya kalle ta ba, cikin muryarta me zaki tace "barka da warhaka" shiru ya mata be ce komai ba kaman ma be san da mutum a wurin ba..........


Rasa da wani suna zata kirashi tayi murya na rawa tace "hai.........  sir I'm here" bude lumsassun idonshi yayi ya sauke su a kanta yana mata wani irin kallo na renin wayau diriricewa tayi ta fara bari kusan two mins tukun yace "what's the time?" Kallon agogon dake daure tsintsiyar hannunta tayi a hankali tace..........


"4:40" wani kallo me kama da harara ya banka mata yana yamutsa fuska yace "lokacin da na baki kenan?" Idonta tab da hawaye tace "a'a amma tun 3:50 nake cikin nan daga bakin get aka ajiye ni seda na tako zuwa nan" hawayen datake dannewa ne ya sulale a fuskanta da sauri ta share tare da dukar da kanta bama ita yake kallo ba...........


Ya mayar da hankalinshi kan system din dake gabanshi yana danne danne cikin sauri da kwarewa seda ya shafe 10mins duk kafanta ya gaji gashi be bata izinin zama ba shi kuma bangarenshi tunani yake wato ma bata iya bada hakuri ba in tayi laifi mari, bata mishi time na about 30mins sau biyu wannan hukuncin da ya mata na zuwa adamawa da kuma ajiye ta na 5hours duk na bata mishi lokaci ne be na zo kan na marin ba gashi ta sake wani.........


Kenan ma bata ladabtu ba, kallon tantiriyar marar kunya yake mata tun daga randa ta daga hannu ta mare shi ta kuma furta banzan magana a gabanshi gaban manyan mutane da zasuyi sa'annin mahaifinta, shi haushin mahaifintan ma yake ji in ba iyayi ba ina mace irin wannan wawiya dakikiya ina CEO 'a fadarshi fa kenan' Dan tsirirn tsaki ya sake to shi ina ruwanshi tunda ba shiga shirgin wasu yake ba abunda ke gabanshi kawai yakeyi...........


Knocking akayi ya bada izinin shiga yaqoob ne a ladabce yace "sir everything is set and ready kai kawai ake jira" Hannu kawai ya daga mishi ficewa yayi yana tausayawa hamrah tabbas ya San oganshi mutum ne me jin kai da tausayi amma ya rasa dalilin hukuncin da yakewa hamrah kawai don ta bata mishi lokaci a fili yace "Ashe ba Kawai bane time fa?" (A zuciyata nace lallai yaqoob ba time bane kadai harda abunda baka taba zato ba) tabbas ba abunda haisam ke valuing irin time.............


Be kalle ta ba yace " na Baki lokaci kinyi wasa da damanki har ya wuce I have more important things to do than this" numfashi yaja tukun yaci gaba yana yatsina fuska "in kin matsu da ganina zan sake Baki dama na karshe meet me tomorrow evening at HMS beverages katsina ki kuma shirya karban hukuncin marina" ido ta zaro ranta in yayi dubu ya baci wani irin zafi kirjinta ke mata...........


Magana take son yi amma inaaa in ta bude baki sede ta jaa iska wani irin abu ta fara alamun asthma dinta ya tashi a natse ya daga ido yana kallonta tsab cikin lokaci kankani ya fahimci matsalarta amma hakan be sa ya motsa ba idanunta sun firfito sunyi jazur hannunta na kan kirjinta layi ta fara da sauri ta cire gyalen kanta ko ze dan taimaka mata taji iska amma inaaa.......


Tana kallonshi amma shi kayan gabanshi kawai ya mike yake tattarewa ko a jikin shi har numfashinta ya karasa daukewa ta sume a wurin cikin Izza da kasaita ya bud'e wani kofa dake manne a cikin office din se gashi a wani katon office amma komai na ciki da tambarin likitanci wani kofar ya kara budewa se gashi katon dakin magani..........


Abunda ya zo nema ya dauka ya fice tare da komawa office na farko a kanta yaja ya tsaya yana wani guntun tunani tsaki yaja tukun ya tsuguna yasa hannunshi duka ya ringa danna mata kirji da dan karfi wani numfashi me wuya ta fara jaa yana seizing ta kara sumewa tun kafin ya yi step na gaba hancinta ya matse tare da daura bakin shi kan nata.......


Abunda be taba yiwa wani mahaluki ba mouth to mouth iska ya dinga dan hura mata yana dagawa seda yaga ta jaa tukun yasa mata inhalern da ya dauko tare da rufe mata bakin a hankali numfashinta ya fara dawowa a hannunta ya sa inhaler tare da mikewa ya fice.......


Jet dake jiran shi cikin gidan marayun ya shige suka lula zuwa kt, se da ta shafe a kalla 15mins kafin ta gama dawowa hayyacinta kuka ne ya kwace mata hada kai da gwiwa tayi taci kukanta tanayi tana kara zukar inhaler din da ya bar mata a hankali ta mike ta fito daga office din........


Allah ya taimake ta ta samu taxi da ya sauke wasu da suka kawo ziyara gidan yana shirin fita ta tsaida shi ta shige tare da ce mishi "airport" da "yes ma'am" ya amsa mata yaja suka fice daga gidan marayun, kanta na tsananin ciwo hk idonta yayi jazur fuskanta duk a kumbure a haka suka isa airport ta sallame shi tare da shigewa............


Tabbas Abuja zata koma baza ta iya da wannan wulakancin ba gashi wani tsanar haisam dinne ya dasu a cikin zuciyarta she hates him to the extent that baza ma ta iya yarda hulda ta hada companies dinsu ba, da za'a bata bindinga a kuma bata daman kisa a ce wa take so ta kashe a duniya Allah ze yafe mata da haisam zata harbe kowa ma ya huta............


Tana cikin tunanin ne taji wayanta ya fara ringing sunan mommy ta gani se da ta seta kanta tukun ta daga sbd boye yanayin da take ciki haka ta bangaren mommyn ma kokari take na boye damuwarta "hello mommy ya kk ya gd" mommyn tace "lfy klau baby ya kin samu kun hadu kuwa?"...........


Dan shiru hamrah tayi a hankali tace "akwai matsala ne mommy?" Mommy tace "uhmm hamrah idan baku samu haduwa ba ki dawo kawai mahaifinki is in critical condition an sake admitting dinmu ya damu yana son ganinki" hawaye ne ya gangaro a idanunta ta de daure tace.......


"Karki damu mom gobe in shaa Allahu zan gama komai i will be on my way next 2morrow" fatan alkahiri mom din tayi mata har zata kashe se kuma tace "mom dad dinfa" mom tace "yana tare da doctor" hamrah tace "Allah ya bashi lfy se anjima mom" tare da yanke call din...........


Kallon me yanka tickets din tayi dake tambayanta me take so a hankali tace "any possible jirgi daze tashi zuwa kano from now on" ta ci sa'a kuwa ta samu 9pm biyan komai tayi tare da juyawa ta koma hotel din data kama don tattara kayanta...........


'Yar mutan Adamawa💞💞💞                    💞💞hamrah💞💞                                                   💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin


Wattpad: muhdfatimagurin


              *yar mutan Adamawa*


*this page is dedicated to my kawa Sadiya Muhammad Amaryar ya faisal Allah ya barku tare😌*


Page ➡4⃣


*********


Karfe 9:40 jirginsu ya sauka a aminu kano international airport driver din kakanta hajja nana ne yazo daukanta "sannu da zuwa hajiya" da yauwa kawai ta amsa mishi trolley dinta ya amsa ya saka a boot tare da bude mata baya ta shige..........


Nasarawa GRA suka nufa wani tamfatsetsen gida da ya amsa sunanshi suka shige wata kyakyawar farar mata ce tsaye daga wurin parking space taci ado da peach color lace da ya amsa sunanshi da fara'a ta tari jikan nata suna farin cikin ganin juna............


"Lale lale da zuwa baby" hamrah ta amsa da "yauwa nanaaa" shagwabe fuska tayi tace "naanaa I'm damn tired and rabona da abinci tun breakfast" naanaa ma fuskan tausayi tayi tace "Allah sarki baby me kika tsaya yi hk ya hana ki cin abinci? Yanzu muje ki watsa ruwa na dafa miki favorites dinki duka"................


Tunanin haisam ne ya fado mata yake shirin bata mata mood da sauri taja hannun kakarta suka wuce ciki, bayan tayi wanka a room dinta dake gidan ta shirya cikin cotton kayan bacci riga da short wando ta fito zuwa qasa dining ta nufa ta zuba abinci tana fara ci tunanin wulakancin da haisam ya mata ya fado mata daci ne taji ya maye taste din abincin da ta fara ci........


Hawaye ya fara gangaro mata kifa kanta tayi a kan dining din tare da fashewa da kuka hada shesheka in ta tuna kallon da take mishi tashin ciwonta na ya taimake ta shi kuwa ko a jikinshi kara kona mata rai yake "subhanallahi habibty" da sauri ta mike ta zauna tana share hawayen fuskanta guri naanaa ta nema ta zauna tana kallon jikannata cikin muryar lallashi tace..............


"Dukkan tsanani yana tare da sauki hamrah adua zakiyi ga duk abunda ya kuntatawa zuciyarki ba kuka ba" kai kawai hamrah ta daga tana jan ajiyar zuciya kallonta tayi a natse ta tambaye ta me ya same ta kin fada tayi da wayo da dabara irin na manya naanaa ta sa hamrah fada mata abunda ke damunta..............


"Ashsha subhanallahi hamrah??" Dukar da kai tayi tana forming wani hawayen fada sossai naanaa tayi mata daga baya ta koma nasiha sossai jikin hamrah yayi sanyi Dana sani fall ranta sam ta san bata kyauta ba amma aikin gama ya riga ya gama sede ta fuskanci gaba..............


Sun raba dare suna hira da naanaa kafin kowa yaje ya kwanta hamrah na Jin nishadi da farin ciki na ratsa ta har ta manta da wani haisam taji daadin hirar su da naanaa sossai a duniya ba wadda ya santa ciki da waje kaman naanaa and she love her so much.............


Washegari 


Karfe 11 na safe ta fito a shirye tsab cikin wando da riga duk bakake ta daura maroon kimono a kai ta yane kanta da black veil tasa black flat shoe da side bag baki wayanta da credit card dinta ne kawai a ciki sallama tayiwa naanaa bayan tayi breakfast ta fice dama driver ya riga ya gama shiri ya wanke motar da zasuyi tafiyan da shi cikin lokaci kankani suka kama hanya...........


Good 2hours ya kai su katsina da shike ba wani gudu drivern ke yi ba kasancewar bata son gudu direct HMS beverages suka nufa ba wani babba bane amma ya tsaru sossai don ya mata kyau ba kadan ba secretary dinshi ta kira da shike ta sa arham ya tura mata number din shi..............


Magana sukayi na 2mins yace bari ya turo a shiga da ita godiya ta mishi tare da kashewa bata kara minti daya ba aka zo aka shiga da ita bayan ta ba driver card dinta tace ya yo musu order na abinci a lady M da to ya amsa mata tare da ficewa...............


Da sallama a bakinta ta tura kofar tare da shigewa ba kowa a cikin office din katon office ne tsararren kyau ko mai na ciki maroon da black ne ya mata kyau sossai doguwar kujera ta nufa ta zauna tare da ajiye jakarta shiru tana zaune tunawa da batayi azahar ba ga la'asar ya gabato yasa ta mikewa ta fada toilet dake cikin office din a wanke yake tsab kaman ba bayi ba alwala tayi tare da fitowa..........


Ga wurin sallah nan a gefe an ware tare da shimfida darduma me laushi da quran da chasbaha a kai wurin ta nufa tare da gyara mayafin kanta ta tada sallah tana idar da azahar bata wani jima ba aka kira la'asar shima mikashi tayi ta zauna a nan tana adua Allah daura ta akan haisam har driver din da ya kawota yayi knocking mikewa tayi ta karbi abincin da card dinta ta bashi nashi........


Bayan ta gama cin abincin ta dan kishingida tana duba time 4:00 taji an tura kofar an shigo da sauri ta daga kai se sukayi ido hudu da shi yana tsaye rike da handle na kofan kau da kai yayi ya nufi kujerar shi ya zauna tare da bude system mutuwar zaune hamrah tayi gaskiya guy din nan ba de kyau ba sanye yake cikin fararen kaya da ya haska fatan shi farin jeans da farin top me v neck har yana nuna fari kal din vest da ya sa a ciki.........


Kafanshi sanye da timberlands fara hannunshi agogo ne na fata me dan Karen tsada shima fari wow ba karamin tafiya da imaninta yayi ba duk kyaunta da iya wankan ta se taji ta rena kanta gyaran murya yayi wadda ya dawo da ita hayyacinta gaishe shi tayi ba tare da ya amsa ba ya furta cikin husky masculine voice dinshi............


"Wannan shine punishment na bata min time da kikayi har sau biyu bari muga the whole lady of fareed tower wacce ba bloody fool ba me cikakkiyar hankali ba dakikiya ba......" numfashi ya ajiye sbd maganan ya mishi tsai tare da taune lips dinshi na kasa yana dan jujjuya kujeran da yake kai tare da kafe ta da lumsassun idanunshi...........


Gabadaya ya daure ta da jijiyoyin jikinta innalillahi kawai take furta wa tabbas wadancan kalaman duk da ya furta dashi tayi amfani a gareshi kwanakin baya kenan ya rike ko wani kalma be manta ba? Ya ilahi me ya kaini? Hawaye ne yake shirin gangaro mata amma se ta danne tana jin idanunshi a kanta har cikin kashinta take jin azabar kallon nan don kaman daure ta yayi da jijiyoyinta.........


Bata san lokacin da ta furta "kayi hakuri plz ka dubi girman Allah ka taimake mu" smirking yayi a zuciyarshi yace ashe ta iya bada hakuri baki ya tabe tare da dauke idanunshi ya maida kan system ya fara typing a gajiye yace "ko zaki iya daukar hukunci na gaba?" Be jira amsar ta ba ya daura da "AURE NA"..........


Wani irin zabura tayi tare da mikewa tana girgiza kai idanunta na zubar da hawaye tace "never impossible!!!" Smirking yayi yana jin wani farin ciki don ya dana mata tarko yanzu idea din ya fado mishi don har ya shigo office din tunani yake wani hukunci ya kamata ya mata na zagi da kuma marin da ta mishi tabbas ya san ko wani irin hukunci ya yanke mata baze mata ciwo na kaman ya aure ta ya wulakantata kuma ya sake ta ba.........


Hakan ne ze sa ta san shi ba abokin wasan ta bane and ya gamsu kwarai da wannan hukunci sbd ko daga ganin yadda ta firgice kawai ya ishe shi wani smirk ya sake saki tare da kallon inda take a dage yace "just 3days to think failure ta accept it then count your company down and your lovely dad....." be karasa ba se ya saki smirk ................


A kidime ta juya ba tare da ta san inda take jefa kafarta ba ta fice da mugun sauri mota ta fada tare da dakawa driver din da ke tamabayarta ko lafiya wani irin tsawa a tsorace ya shiga motar ya ja a dari suka fice daga cikin katsina kanta ta sa a tsakankanin cinyoyinta tare da fashewa da kuka.............


**


Kwance take a kan gadonta hawaye na gangara ta gefen idonta tunda ta baro katsina take kuka har zuwa wannan lokaci da ta baro kano ko sallama batayiwa naaanaa ba daga cikin mota tace driver ya karbo mata trolley dinta yazo ya kaita Airport ai kuwa a take ya cika umarnin ta ga dukkan alamu naanaa bata nan airport ya kai ta ta kuwa ci sa'a ta samu jirgi mintuna kadan ya kawo ta abj...........


Taxi ta tara zuwa gd ta kai 5hours da shigowa gidan amma ba wadda ya san da shigowarta yadda ta shigo ta fada gado hk take har yanzu ko gyale da takalmi bata cire ba zazzabi ne me zafi ya rufe ta rawar sanyi ta fara a hankali ta jawo wayarta ta kira hanne maid dinta cikin sanyin murya tace "sameni dakina"............


Ba'a wani jima ba kuwa se ga hanne ta shigo da sauri ta karasa bakin gadon tare da dukawa kasa tace "hajiya barka da dawowa" bata amsa mata ba in kuwa da sabo yan aikin sun riga da sun saba iyakacinta dasu ta basu umarni su bi bata amsa gaisuwan kowa ko da kuwa ka haife ta ne cikin sanyin murya tace "had'a min ruwan wanka me zafi"..........


Da "an gama hajiya" ta amsa mata tare da fadawa bayi 5mins ta fito tace "na hada hajiya" bata amsa ba ta fada toilet din tana layi a hanya take tube kayan daya bayan daya tana zubarwa hanne na bi tana kwashewa dama hk halinta yake wai ta tube kaya ta Adana? Se de in ba masu aiki...........


Ta kai 30mins a cikin toilet din tana kwance cikin jacuzzi ruwan zafin na ratsa ta ranta duk ba daadi ta rasa tunanin me zatayi tabbas ba tantama haisam fansa yake son dauka a kanta na marin shi da tayi, she is so confused ta rasa dalilin da ze sa baze rama marinshi ya taimake su ba gashi ya hana a taimaka musu duk kuwa yadda suke good times da sauran companies din amma sbd haisam yayi magana kowa ya janye............


Idonta a runtse tana waswasi har ruwan ya salamce cikin kasala ta wanke jikinta ta fito daure da karamin towel wardrobe ta nufa ta zaro kayan bacci nylon half gown maroon tare da sawa kanta hula net baki ba tare da ta shafa mai ba ta fesa turare tare da fitowa a hankali take gangarowa har ta sauka kasa a natse tace "hanne" da dan daga murya se ga hanne ta fito da sauri ta duka a gabanta..........


"Ki dafa min noodles da boiled egg kafin na fito daga gurin dad" tana maganan ne tana tafiya "toh hajiya" hanne ta amsa cikin girmamawa bata tsaya sauraron hanne ba ta bude wani kofa dake parlorn daga hannun damanta ta shige, shima parlor ne tangameme komai na ciki Ash and milk bata tsaya nan ba ta nufi zigzag stairs dake damanta a kasaitance take tafiya har ta gama hawa corridor ne dogo ya bayyana a gabanta haka ta mika har kusan karshen corridorn kafin ta ta bude wani kofa da sallama a bakinta.........


Arba tayi da farin cikin ta masoyanta da bata da kamarsu duniya iyayenta zaune a kan gado dad na jingine a pillow ya mike kafafuwanshi mom na zaune gefenshi tana bashi hot coffee da spoon yana sha murmushi ne ya bayyana a fuskanta kaman yadda suma murmushin ne kwance akan fuskokinsu da sassarfa ta karasa ta duka tayi hugging din baban nata tana jin duk wani damuwanta ya kau se tsantsar farin cikin ganin iyayen nata............


Breaking hug din tayi tana kallon kafan dad dinta da ya kumbura sossai fuska ta bata tare da kallon mom tace "mom mun same ku lafiya" mom na murmushi ta furta "lafiya klau Alhamdulillah" ta kara cewa "ya jikin dad?" Cikin changin yanayi tace "da sauki dai amma har yanzu yaki kwantar da hankalinshi sam jinin ya ki sauka wlh" kallon dad tayi da fuskan tausayi zatayi magana yace "ya kukayi? Ya ki ko?"..............


Cikin yake tace "a'a dad" se yace cikin tsantsan farin ciki da yaso sa hamrah kuka "ya amince? Masha Allah may god bless you daughter am very proud of you" kunya ne ya kama ta ta dukar da kai kasa tana wasa da fingers dinta Sam bata zata zataga farin ciki haka a fuskan mahaifinta ba yanzu ya zatayi? Ta amince ne ko don farin cikin mahaifinta ko kuma ta ki dad dinta ya shiga wani hali? She can't risk it she can't even imagine her life without him...........


Mom ce ta katse mata tunani da "lafiya kuwa Angel?" Yake tayi tare da mikewa tace "lafiya kalau mom bari inje" har ta juya ta sake dawowa baya tace "simra fa ban ganta ba" cikin sanyin murya dad yace "ta tafi india" da mamaki hamrah tace "lafiya? Shine ko kirana ta fadamin baza tayi ba ina ta kiranta be shiga?" Mom tace "mahaifinta ne ya rasu" "whattttt??????? Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" Dabas ta zauna a kasa ta fara hawaye tana tausayawa kawarta kenan she has to be with her dole ta tafi India rarrashinta suka tayi har tayi shiru tare da musu sai da safe ta fice..............


Noodles din da bata ci ba kenan ta haye gadonta ta dukunkune inaaaaaa waya ta jawo ta kira yaqoob cikin rawar murya tace "kace mishi na amince" tare da kashe wayar ta fashe da kuka ...................
#vote 

#share

#comment 

'Yar mutan Adamawa💞💞💞    

                      💞💞hamrah💞💞
                                                          💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin           * 'yar mutan Adamawa *Page ➡5⃣


**********

Kwance yake a kan gadonshi ya takure sossai se kace alamjirin da ya rasa makwanci idonshi a runtse me yasa be ji daadi ba da hamrah ta amince bayan shi ya bukaci hk? Sam ba haka ya so ba yaso karasa rayuwar shi ne a hk shi kadai, tabbas ya san kwanakin shi ba masu yawa bane a duniya abu daya ne ya rike shi har ya kai warhaka...............


"Fansa" yeah he's just alive bcos of that, rayuwanshi is full of miserable be san amfaninshi ba, bashi da kowa bashi da wadda ze gani ya ji daadi, wani irin shesheka ya fara ba tare da hawaye ya zubu ba shi da ze samu kukan ya zo ma da ya fi farin ciki amma abu ne me matukar wuya kirjinshi ya dafe yana murkususu a kan gadon idonshi kaman an zuba yaji tsabar jan da yayi...............


Hannunshi na rawa da kyar ya samu ya danna wani kararrawa se ga yaqoob ya shigo ganin me gidanshi a wannan hali yasa shi karasawa da gudu ya bude bedside drawer ya dauko wani farin roba karami maganin ciki ya zazzago se gasu guda biyu a hannunshi da gudu ya koma wajen fridge ya dauko ruwa me rangwamen sanyi ya haura gadon da kyar ya samu haisam ya sha maganin a take ciwonshin ya lafa ya kwanta a kan pillow tare da lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya, fita yaqoob yayi yana me tausayawa oganshi bai gushe ba kullum se yayiwa oganshi adu'ar samun farin ciki a rayuwarshi............


*********

Washegari da sassafe ta shirya ta nufi airport da kyar ta samu jirgin India amma na yamma dawowa gida tayi ta hada kaya 'yan daidai a cikin trolley dinta, bayan ta gama ta koma part din mahaifinta tana kula dashi dayake mom na da case da safen, hira sossai sukayi da dad dinta ta kara karfafa mishi gwiwa a kan maganan company dinsu a haka har mom ta dawo sallama ta mishi tare da komawa dakinta ta kwanta a kan gadonta tana kara gwada layin simra na india amma duk daya switch off...................


Kiran yaqoob tayi yana dagawa suka gaisa cikin mutunci kafin tace "ka cewa mai gidan ka idan ya gama shiri ze iya turowa gidanmu wurin dad dina don ko ya kira baze sameni ba sbd zan tafi india and I don't really know when I'm coming back" cikin mamaki yaqoob yace "ban gane ba turo me?" Cikin bacin rai tace "just tell him what I said" har zata kashe wayan tace "and batun company zasu iya signing contract din da assistant na kafin na dawo".............


Dip ta kashe wayan ta bar yaqoob da tunani wai me oganshi ke shirin yi ne? Tabe baki yayi ya karasa parlorn da sallama don isar da sakon CEO of fareed tower.............


Bayan laasar ta shirya cikin mafi soyuwar shigarta Arab gown peach color ba karamin kyau tayi ba iyayenta da kansu suka raka ta airport kasancewar dad yaji sauki sossai sallama tayi dasu kafin jirginta ya lula se New delhi, tana sauka ta tari taxi har gidan su simra ta sallame shi tare da jan trolley dinta ta nufi ciki da sallama ta tura kofar parlorn..............


Idonta ne ya sauka a kan wurin da mahaifin simra ya saba zama kullum in ta zo a wurin yake wuni komai a wurin yakeyi hawaye ne taji ya cika idonta Allah sarki bestie, ji tayi an rungumeta da sauri ta kalle wadda ya rungumetan tsugunawa tayi ta rungumeshi itama kawai se ya fashe da kuka breaking hug din tayi tana shafa kanshi cikin harshen indiyanci tace .................


"Uhmmm Arjun inace kai soja ne?" Gyada kai yayi tayi murmushi tukun tace "toh ai sojoji basa kuka ko kana so ka zama rago ne?" Sake girgiza kai yayi tace "good boy oyaa wipe the tears" sharewa yayi, ta kara cewa "where is Ammah?" Da indiyanci yace "she's in the kitchen" tace "ohk" kafin ta mika mishi trolley dinta jaa yayi ya nufi upstairs don kaiwa dakinsu ita da simra ita kuma ta nufi kitchen................


Ta baya ta rungume Ammah mahaifiyar simra juyowa tayi don ta san me mata hakan da murmushi a fuskanta ta rungume hamrah tana mata sannu da zuwa da indiyanci janta tayi zuwa parlor a take ta cika ta da kayan ciye ciye bayan sun gaisa tayi mata ta'aziyar rashin da sukayi tukun ta tambaye ta "Ammah ina simra" duk cikin harshen india suke magana fuskan tausayi Ammah tayi tukun tace............


"Hmmm simra tana saudia kanina ya tafi da ita" cikin mamaki hamrah tace "me yasa?" Tace " bayan rasuwar mahaifinta ko kwana daya be rufa ba yan uwanshi suka fara matsa mata akan musuluncin da takeyi to abun ya so yayi tsamari shine kanina yace in bashi ita su tafi saudi sbd Chan ne kadai baza su iya zuwa ba and zamu jima bamuyi waya ba"..............


"Ya salaaam" shine abunda hamrah ta furta shikenan ita kuma rayuwanta na cikin tsaka me wuya, kawartan kwara daya an raba su yanzu bata da wadda zata yi shawara dashi idan ta auri waccan mugun, innalillahi yanzu ya zatayi? Hawaye ne ya cika idonta da sauri ta mike ta nufi upstairs tana cewa Ammah "let me fresh up" da toh kawai Ammah ta bi ta............


**********

"Ta ce a turo" haka kawai ya fad'a bayan sun gama gaisawa da Alhj mudan friend din babanshi ne ba yadda ya iya ne yasa ya kira shi bashi da wadda ze tsaya mishi yayi auren se abokan babanshi wayanda be yarda dasu ba wa'yanda ya yarda da sun duk sun rigamu gidan gaskiya zuciyarshi ne ya fara zafi sms ya shiga ya tura mishi address din ya mishi transfer din 10mil....................


Alhj mudan ya kalli abokinshi Alhj halliru yace "kaji min maganan banza in banda shashashan yaro ko me ma'anan abunda yace? Mutum ne se yayi ta abu a murmurde se kace maciji?" Dariya Alhj halliru yayi tukun yace "me kuma ya ce maka?".............


Alhj mudan yace "wai ta ce a turo" da sauri Alhj halliru ya mike ya cire hulan kanshi ya fara fifita what? In hakan ya faru kenan baza su taba cika burinsu ba? Inaaa Alhj mudan ne ya katse mishi tunaninshi da "lfy kuwa hajji halliru?" Cikin takaici Alhj halliru yace "kai wai me yasa kanka be ja ne? Nufinshi wacce yake so tace a tura gidansu maganan aure"


"What? Kana nufin haisam aure ze yi? Yaushe ma ya fara soyyayya bamu........" kafin ya karasa yaji wayanshi yayi karar shigowar sako dubawa yayi ya kalli alert na kudin da ya turo mishi da kuma address din gidan su hamrah mikawa Alhj halliru wayan yayi ya duba cike da takaici yace "ba yadda zamuyi dole mu cigaba da dannewa muna nuna sonshi kenan dole mu nema mishi auren nan"............


Wayanshi ya dauka ya kira haisam kaman ba ze daga ba se kuma ya dauka "Assalamu Alaikum" da kyar haisam ya amsa sallaman maimakon ya gaishe shi se yayi shiru abinshi Alhj hallirun ne ya shaka tukun yace "masha Allah son naji abun arziki a wurin Alhj mudan ashe aure ya zo?" Da "eh" kawai ya amsa.............


Sossai hakan ya kular da Alhj halliru amma se ya ce "ai ba ma se ka turo da kudi ba muma kaman iyayenka ne zamu iya nema maka aure kuma muyi maka bada kobonka ba karka manta burin mahaifinka kenan" runtse ido haisam yayi yana jin wani abu na taso mishi sbd ambatar iyayenshi da yayi cikin gatse yace "in kudin basuyi bane in karo, and bana so ya wuce two weeks" kit ya kashe wayar................


"Kaji min dan kwal uba?" Dariya Alhj mudan yayi yace "iskancinshi ya wuce nan kai de kama Dr zubair magana se mu je gobe da yamma" Cikin kufula Alhj halliru ya tashi ya fice dama shi ya zo ya samu Alhj mudan a gidan gonanshi................


A daren Alhj mudan ya kira Dr fareed ya sanar da shi zuwansu neman auren 'yarshi a goben kuma ita ta ce a turo, da mamaki sossai Dr fareed ya amsa shi akan Allah ya kaimu yana kashewa ya danna kiran hamrah.............


*******

Kwance take a gadonsu na dakinsu ita da simra tana kallon teddy's dinsu, colorn dakin yadda papa din su ya raba kowa akwai favorite dinshi, wall sticker dinsu and rest hawaye ne ke shirin zubo mata, a yayinda karar wayanta ya fargar da ita jin special ringtone da ta sawa mahaifinta ne yasa gabanta faduwa danne komai tayi jin wayan ya kusa tsinkewa ta daga................


"Salamu Alaikum ur excellency barka da dare" a natse cikin sanyin muryanshi yace "wa'alaikissalam princess ya kk" tace "lfy dad ya jiki ya mommy?" A hade yace "Alhamdulillah ya kika same su" shiru tayi kafin ta mishi bayani kamar yadda mahaifiyar simra ta mata, fatan Alkhairi ya ma simra din tukun yace "tunda kawarkin batanan se ki shirya ki samu available flight kawai ki taho and ke kika ce maneminki ya turo?"..............


Dammm gabanta yayi wani irin faduwa, innalillahi kenan da gaske haisam yake? Waye zata nema ne ya bata shawara ita yanzu me take getting kanta into? Aure fa ba abun wasa bane tana bukatan wadda ze ce mata just call it off or go for it, don ma mahifinta ya fiye mata komai a duniyan nan she will just go for it bcos of him yes bcos of him "princess are yhu there?" Maganan dad dinta ne ya katse ta da sauri tace "yes yes daddy amm uhmm nice....... na ce ya turo".................


"Are yhu okey?" Yaaa ilahi abunda ta tsani a ce mata kenan in tana cikin wani hali yanzu se ta fashe da kuka cikin sanyin murya tace "yes ur excellency" "okey tohm kinde ji abunda nace ki dawo sbd ayi komai a gabanki" a sanyaye tace "in shaa Allahu my regards to mom" dip ta kashe wayan tare da saka kuka ta takure kanta a guri guda...........


Wani tunani ne yazo kanta da simra na nan zata ce kukan nan ba shine mafita ba bestie stand up and pray ki kai kukan ki ga mai duka shine ze miki magani crying is not a solution it will just make the matter worst, wup ta mike ta fad'a toilet ta dauro alwala ta fuskanci gabas ta fara kai kukanta ga ubangijin talikai..............


Washegari 

Nigeria


Tun safe mom ta sa a hadawa bakin abinci kala kala da drinks snacks da dai sauransu bayan sallahn la'asar kuwa se gasu iso Dr fareed da abokinshi Dr junaid suka musu har babban parlorn shi na ganawa da baki, bayan sun ci sun sha ne suka gabatar da abinda ya kawo su kamar haka...............


Alhj mudan ya nuna Alhj halliru yace "kaga wannan shine Alhj halliru shakiki ne ga marigayi Mas'ood sa'ood dan Siyasa ne yanzu hk shi ke rike da mukamin minister of Finance ka san da wannan wadda muke fata zamanshi gwamna nan ba da dadewa ba, wannan kuma ya nuna Dr zubair babban likita ne wadda aka ji dashi kuma ake kan ji dashi shima wtkl ka san shi kuma aminin mas'ood sa'ood ne se ni Alhj mudan duk wani shige da ficen kayan amfanin gona ba'a rasa nawa a ciki kuma nima aminin mas'ood sa'ood ne kuma munzo ne don nemawa dan mu haisam auren 'yarka hamrah................


Zufa Dr fareed ya share duk da Ac dake cikin parlorn shi bawai mukaminsu bane ya dameshi kasancewar duk ya san su amma haisam haisam mas'ood sa'ood fa? Dama hamrah ta sanshi ne? Dr junaid ne ya dan zunguri Dr fareed d'an firgigit yayi tukun yayi gyaran murya yace "wannan abokinane kuma aminina Dr junaid lecturer ne babba a jami'0'i dayawa na kasar nan kama daga A. B. U, BUK, nile and others se ni nine mahaifin hamrah and am the owner of fareed tower"...............


Gyada kai sukayi ya dubi Dr junaid se Dr junaid yace "tabbas ba uban da ze ki aurawa 'yarshi miji nagartacce irin haisam ba wai don kudinshi ba se don tausayi da karamci irin nashi a matsayinmu na iyaye ga Hamrah mun ba haisam aurenta" bayan biyan komai da ya kamata a biya kudinshi a neman aure inda suka so yin almubazzaraci don a san su wasu ne sam Dr junaid da Dad din hamrah sunki a yayin da suka karbi komai a tsare kaman yadda addini yace suka kuma tsaida date na d'aurin auren nan da sati biyu kaman yadda angon ya bukata..............

Tirkashi........... muje zuwa#vote 

#share

#comment


'Yar mutan Adamawa


💞💞💞    

                      💞💞hamrah💞💞
                                                          💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin           * 'yar mutan Adamawa *Page ➡6⃣


**********

"Honey kana ga ba wani mtsala? Jikina na bani auren nan ba na daadin rai bane" mom ce tayi wannan furucin don tunda dad ya fad'a mata waye 'yarsu zata aura taji sam hankalinta be kwanta ba daddy ne ya rike hannunta a cikin nashi tare da cewa "karki ringa damun kanki idan da akwai matsala ai zata sanar mana wa take dashi fiye da mu?" Cikin sanyi tace "toh shikenan Allah ya tabbatar da alkhairi" cikin dariya yace "yauwa ko ke fa hk ya kamata kice tun farko" murmushi kawai tayi tare da excusing kanta ta fice.................


Tana shiga room dinta ta kwanta a kan gado tare da fad'awa duniyar tunani abunku da uwa tana ji a jikinta something is fishy, to bata ta'ba jin Hamrah na waya da wani saurayi ba, ta kuma tuna sanda hamrah ke tambayarta waye haisam, ai in har ta riga ta sanshi suna soyayya baza ta tambaye ta waye shi ba, kwata kwata da abun be wuce two weeks ba how comes?..................


Wayanta ta jawo ta kira hamrahn ringing biyu ta daga tace "mom" "na'am Angel ya kk?" Tace "lfy klau mom ya jikin daddy" tace "jiki da sauki ya Ammahn ku?" Bata jira amsan ta ba tace "Hamrah baki samu flight din bane?" Seda gaban hamrah ya fad'i sbd yana wuya kaji mom ta kira ta hamrah idan ba serious issue bane cikin sanyin murya tace "mommy na samu in shaa Allahu gobe zan dawo"...................


"Hamrah an sa bukinki nan da two weeks" wani irin razana hamrah tayi har seda mommy tace "lfy?" Cikin in ina tace "eh....eh mom amma sati biyu beyi kusa ba?" Murmushi mommy tayi a zuciyarta tace tabbas akwai matsala amma se tace a fili "a ba hk kuka tsara da saurayin naki ba?" "Uhm amm oh ai be fad'amin two weeks za'asaka ba" mom Tace "toh de an riga an saka kuma kinga maganan aure ba wasa tunda ba gazawa mukayi gara kusan da nesa ba wani abun da zamu nema mu rasa, kinga har sadakinki na hannunmu"................


Muryanta na shirin tona asirin halin da take ciki tace "shikenan mom se munyi magana" kit ta kashe wayan ta bangaren mom shiru tayi a fili tace "zaki dawo ki sameni ne" tare da nufar dressing mirror ta kara pesawa jikinta turare dama kayan bacci ne a jikinta ta fice don zuwa wurin mijinta.........


*********

Hawaye ke gangara a idonta ai ba haka sukayi ba, be gayamata kusa za'a sa auren ba kallon ruwan da take zaune gabanshi tayi se wasa yakeyi yana zuwa yana komawa da d'an karfi ita da simra suka saba zuwa wurin amma gashi yau ita kad'ai, kallon ice cream na hannunta tayi har ya fara narkewa don be wuci spoon biyu tayi ba taga call na mommy dare ne Amma kaman rana kowa na harkoki, kuka ta fara se kuma tayi saurin daga waya ta kira yaqoob................


Yana d'agawa cikin masifa tace "ka turomin numbern haisam" kit ta kashe wayan ta mike ta fara tafiya da kafa sbd ba nisa tsakanin inda take da gida sake kiranta yaqoob yayi cikin lumana yace "ma'am bazan iya turamiki number din oga ba seda izininshi" cikin fad'a tace "what????" Wani idea ne ya fad'o mata ta san in ba hk tace ba baze ta'ba bata numbern haisam ba se kawai tace "be gayamaka nice matar da za'a daura mana aure nan da two weeks ba?"............


Sakato yaqoob yayi irin what dinnan amma mata fa tace? Ita kanta abun taji wani banbarakwai amma se ta daure tace "se kayi maza ka turomin banda lokacinka" kit ta kashe, ba'ayi minti biyu ba se gashi ya turo mata lokacin har ta shiga gd sannu tama Ammah tukun ta haura zuwa room dinsu scarf din kanta ta cire tare da fad'awa gado tukun ta danna number dinshi...................


***********


Jingine yake da kujera daga shi se three quarter Ac na ratsa shi amma ya ki tashi sbd yana son sanyi sossai jikinshi ba riga duk wani siffa ta majiya karfi ya nuna a jikinshi gashi kwance duk kirjinshi idanunshi a runtse amma TV a kunne se ihu yake shi d'aya tsaki yaja tare da jawo remote ya kashe tvn tare da jan tsaki yanzu Alhj mudan ya gama fad'amishi abunda ya faru a gdnsu duk da har ya gama mgna be ce tak ba bayan ya gama ji kit ya kashe wayanshi................


Ya rasa dalilin da yasa yaji ya tsani hakan bayan auren daukan fansa ne ko don ya tsani yarinyar ne? Wani tsakin ya kuma ja karan wayanshi ne ya katse shi daga maganan zucin da yakeyi a kasaitance ya bud'e idon suna lumshewa da kansu tsaban be saba budewa sossai ba, kallon caller ID din yayi se yaga numbern india tsaki yaja ba tare da ya dauka ba seda aka kira sau uku tukun ya d'aga tare da yin shiru abinshi..................


"Wannan wani irin wulakanci ne? Haka mukayi da kai? Sannan in ta kira kana gani kaki dagawa?" Sarai ya gane ta amma don ya kara kular da ita se yace "excuse me?? Who is talking?" Kawai se ta sa mishi kuka sossai abun ya bashi dariya amma dake ba abun yinshi bne se kawai yayi smirk ya sake cewa "how may I help you? Fad'amin sbd na kusa fidda zakkah kar sunanki yazu be shiga ba".............


Don takaici ma kashe wayan tayi ta kife kanta ta fara risgan kuka ita ze cewa ze sata a masu karban zakkah? Allah ya isanta, ta bangaren shi kuma wani smirk din ya sake yi a ranshi yace good hk nake so yanzu kika fara kuka mtseww mikewa yayi ya shige daki.............


**********


Kallon matar shi yayi yana cewa "Aisha kina jin wai nan da sati biyu auren yallabai?" Cikin mamaki ta dubeshi tace "to ai in haka ne kai ya kamata ka riga kowa sani sbd kusancinku" murmushi yaqoob yayi yace "hmmm har yau baki san waye yallabai ba bari na kira yallabai sagir"................


Kiran sagir yayi ringing biyu sagir ya daga suka gaisa tukun yaqoob yace "officer" da yake suna wasa sossai da sagir shima ya koma kaman abokinsu duk da haisam be sakewa dashi amma yana ma haisam son Allah da Annabi kuma ya san duk fad'in duniyarnan daga sagir se shi a wadda yake wa dogon magana "what's up men" cewan sagir kenan a tare suka saka dariya...........


Bayan sun gaisa ne yaqoob yace "wani magana nake ji shine nakeso nayi confirming" sagir yace "wani magana kenan?" Yaqoob yace "wai nan da sati biyu yallabai ze yi aure?" Dariya sagir yayi tukun yace "Haba kai kuwa in ma auren zeyi ai kaine zaka fara sani ban yarda ba gaskiya amma bari na kirashi naji" sallama sukayi ya kashe wayanshi tare da danna numbern haisam...............


Se da yayi ringing har ya katse bai d'aga ba kara kira yayi se da ya kusa tsinkewa tukun aka d'aga jin yadda abokin nashi ya daga yayi shiru yasan miskilancin ne ya motsa se yace "shegen gari ya kk" a dake kaman ma shine sojan ya amsawa sagir da "lfy ya akayi zaka dameni" dariya sagir ya saka shikuma haisam yayi tsaki sarai sagir ya san karamin aikinshi ya kashe mishi waya se yayi saurin cewa..............


"Sorry man wani magana nake ji wai aurenka nan da two weeks?" Tsaki mai tsai haisam yaja yace "me kuma na tambaya na bayan uba na ya gaya maka? Dariya sagir yayi ya sake cewa "kai fa d'an air ne wlh daga tambaya se bakar magana?" Tsaki ya kuma ja tare da gyara kwanciyarshi yace "in gulmar da ka kira kaji kenan se anjima" be jira cewar sagir ba ya kashe wayanshi tare da lumshe ido yana tunanin abun duniya tsaki yaja tare da mikewa ya fad'a toilet................


Ta bangaren sagir kiran yaqoob yayi yace mishi karya ne, Sam hakan be ma yaqoob daadi ba ya so da gaske ne sbd yana so oganshi yayi farin ciki ko da kadan ne a rayuwa don sossai haisam yake bashi tausayi bawai don be da kudi ba se don rayuwar kad'aici da yakeyi ya kuma zabarwa kanshi ga masifaffen ciwon zuciya da yake dashi wadda ba wadda ya san da hakan a duniya se shi kuma haisam ya gargade shi akan kar ya fad'awa kowa, tabbas zuciyar haisam me kyau ce ba kaman yadda kowa yake mishi gani ba yana da tausayi da jin kai na talakawa baze manta randa suka fara had'uwa ba...........


A lokacin haisam na shekara goma shi kuma yaqoob na da takwas tabbas ze iya tuna tun lokacin yadda haisam ke kuka a bayan wani uncompleted building shi kuma ya fita yawon bara don sama ma kanshi abunda ze ci tabbas shima haka ya tashi ya samu kanshi a hannun kishiyar uwa dake gallaza masa azaba tare da sihirce babanshi baya iya cewa komai duk kuwa abunda zata mishi daga baya ciwo ya kwantar da baban har Allah ya karbi ranshi shine fa ta kore shi daga gidan don kar ace a raba gado har shi a suleja suke haka ya dinga bi guri guri har ya tsinci kanshi a cikin abuja a wani unguwan da ya tabbatar na masu kud'i ne ganin da yayiwa uncompleted building dinne yasa yace bari yayi fitsari kafin ya ci gaba da yawo..................


Jin ana kuka a gurin yasa shi karasawa gaban haisam kawai se shima ya kama kuka da sauri haisam ya d'go tare da share hawayen fuskanshi ya kurawa yaqoob ido, shi kuma yaqoob ya tsorata ganin kyaun haisam duk da fari bane sossai sannan kayan jikinshi ya bashi tsoro karde d'an aljanune tunanin ne ya katse jin ya ce mishi "waye kai?" Ai a take yaqoob ya fara bashi labarinshi da irin wahalan da yasha dayake yaqoob akwai surutu yana dasa aya ya kalli haisam dake share hawaye don tausayin yaqoob din yace...................


"Zaka zama kanina?" Da sauri yaqoob ya Gyad'a kai haisam ya kara cewa "ya sunanka?" Yace "yakubu Adamu" dan smirking haisam yayi don tun yana karami rabonshi da dariya yace "uhm uhm daga yau sunanka yaqoob Adam ohk?" Kai yaqoob ya gyad'a mishi ba tare da haisam ya fad'amishi sunanshi ba ya ja shi zuwa tamfatsetsen gidansu ba kowa se ma'aikata se sannu suke mishi kowa yallabai kasa yallabai sama, sama ya haura dashi ya bashi daki kusa dashi ya nuna mishi yadda ze yi komai tare da komawa dakinshi ya dauko mishi kayan sawa...........


Daga nan komai ya kankama kullum tare suke yin komai, baze manta yadda haisam yasa abokin babanshi dake kula dashi lokacin duk da fir haisam yaki komawa gidanshi sa yaqoob a makaranta daya da nashi ba tare suke lesson a gd islamic da western education, kasancewar kowa a gidan yallabai yake kiran haisam se yaqoob ma ya kama tun haisam na kwabarshi har ya gaji a haka har jami'a tare sukayi a waje amma shi yaqoob business ya karanta da suka dawo nja ba'a wani jima ba yaqoob ya samu mata Aisha haisam ne ya tsaya mishi a komai har akayi auren yanzu shekaransu uku Allah be de basu haihuwa ba shi yasa har yau be bar sawa haisam albarka ba sbd ya mishi komai a rayuwanshi kuma yana fatan randa ze ramawa haisam alkahirinshi ko da yaya ne....................


Aisha ce ta dafa shi da sauri ya dawo daga tunanin da yake yi tare da kallonta tace "dare ya tsala tashi muje mu kwanta base na tambaye ka damuwanka ba nasan duk akan haisam ne, nima ina tayaka mishi adu'a Allah ya haskaka rayuwar shi da farin ciki madawwamiya" murmushi yayi tare da amsawa da ameen ya rungume kayanshi sukayi cikin daki...................


**********


A washegari hamrah ta diro abuja ta samu mommy na ta shirye shirye da kiran waya har yan sudan tana gayyatansu, abunda ya taimake ta kenan ta tsallake tambayoyin momy akan haisam a kuma washegarin suka wuce kano a mota driver ya kaisu a Chan gurin kakanta hajja naana mom ta barta ta samu kawarta hajja naana suka cilla dubai don hado mata kayan daki, yayin da hajja ta gayyato wasu mata daya 'yar maiduguri daya kuma yar kano suka tare a gidanta tare da fara shirya hamrah.............


Duk yadda take zillewa abun sam sunki barinta a haka har suka shafe kwana bakwai sossai hamrah ke cikin damuwa amma yaya zatayi kullum se ta kira Ammah taji ko su simra sun kira amma shiru................


A Chan abuja kuwa ta bangaren ango ba abunda yayi ba ma wadda ya sani se wayanda suka nemo mishi auren kiran dad yayi yace "ammm dr fareed na kira ne in fad'a maka tun yanzu hamrah bazatayi aiki ba she will be a complete house wife, na san bawai tsufa bane yasaka ajiye aiki kayi hakan ne kawai sbd princess dinka tayi insisting so to my advice ka koma ka ci gaba da kula da company dinka it's for ur own achievement I don't think hamrah will handle it well na barka lfy" kit ya kashe is wayanshi..................


Cike da tsantsan mamaki dad ke kallon wayan Anya abun nan ze daure tun dama ya riga da ya san haka haisam yake kai tsaye yake magana ba kwana kwana to amma a hausance surkinshi ne shi be dace ya mishi magna hk ba dayake shima daddyn dan boko ne se ya share maganar ya ci gaba da hidiman bukin mamanshi uwar masu gida......................#vote

#comment 

#share'Yar mutan Adamawa💞💞💞


                        💞💞hamrah💞💞                                                            💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin                 *'yar mutan Adamawa*Page➡7⃣


************


Wasa wasa hamrah taga abu kam ya gama matsowa saura kwana uku a daura mata aure kuma a yau suka bar kano zuwa Abuja da mutane 'yan uwa da abokan arziki ba yadda mom batayi da hamrah ba tayi event ko kala daya ne amma fir taki, se mom dince ta shirya mother's eve da yini a gidanta tuni sun dawo daga Dubai, hamrah dake zaune ta jikin window tana kallon garin abuja kaman ance kalla ta hangi motocin haisam a jere suna tsuga gudu................


A zuciyarta tace dan raenin sense dama faduwa kukayi ka mutu da na fi kowa jin daadi wani tsaki taja tana kallon fatan jikinta yadda ya koma cikin abunda be wuce kwana goma ba dama gata fara sol kuma tana amfani da mayuka masu tsada da gyaran fata shi yasa gyaran jikin ya zauna sossai a jikinta tayi wani irin kyau da ka ganta kaga amarya................


A haka suka karasa gida aikuwa matan dake harabar gidan suka saka gud'a ga Amarya ga Amarya har wuya abun yazowa hamrah a dole take murmushi amma na yake da dabara ta samu ta zille zuwa dakinta tayi wanka ta shirya tare da hayewa gado don hutawa amma se akayi knocking tare da shiga a lokaci daya kallon kofan tayi se taga mom ce da d'an karamin tray a hannunta ta karaso bakin gadon ta zauna tare da ajiye tray din tana cewa...............


"Maza maza tashi ki ci abinci mutum kaman kuliya daga dawowa se kwanciya" tashi hamrah tayi tana murmushi ta jawo tray din sandwich ne da ferfesun bindin sa murmushi ta karayi tukun tayi bismillah ta fara ci a fakaice mommy ke nazartan ta ta lura yarinyar akwai abunda ke damunta amma zurfin cikinta ya hana ta fad'a musu................


Seda mommy ta bari hamrah ta gama tukun tace "hamrah" dagowa hamrah tayi ta kalleta a natse mom ta daura da "hamrah menene matsayina a gareki?" Cikin mamaki hamrah tace "uwa mana wacce bani da kamarta duk fadin duniya" mom tace "gud kenan munyi matsayin da zaki iya gayamana damuwanki hamrah me ke damunki?" Kuka hamrah ta sa tare da fadawa jikin mommy lallashinta mom ta fara da kyar ta samu tayi shiru tukun tace..............


"Mom ki dena sawa kanki damuwa plz ba abunda ke damu na kawai ina tuna yadda zan tafi in barku ne ko zuwa ganinku ne dole seda izinin wani mom ni a fasa" ta karasa hawaye na silalo mata tabbas da zata iya da ta fadawa mom damuwarta amma she can't dariya mom tayi tare da bata baki akan kowa ma haka ya fara rayuwar mace kam haka ya gada hk zatayi hakuri ba yadda ta iya sossai nasihar mom yayi tasiri don ya rage mata wasu abubuwan..................


A washegari da yamma mom tayi mother's eve kowa in ka ganshi kaman ka sace tsabar kyau wayewa da kudi don abun na manya ne shiyasa sam ba hayaniya a cikin gidan akayi an kawata gidan gabadaya da ado se kace a india ko ina na gidan kyalli yakeyi a hk aka gabatar amarya ta sha kyau sossai cikin wani dakakkiyar farin leshi an mata dinkin riga da skirt wow ko don ban taba ganin hamrah da wasu kayan bane sede Arab gowns se kuma nightwear tayi mugun kyau ga tsai ga diri masha Allah..............


A washegarin aka yi yini ranan juma'a bayan an sauko daga masallaci aka daura auren HAMRAH FAREED DA HAISAM MAS'OOD SA'OOD akan sadaki naira dubu 100 lakadan ba ajalan ba a kofar gidan su aka daura inda ya samu halarcin manya manyan kusoshin gwamnati amma duk ta bangaren dr fareed don haisam ba wadda ya turo se su Alhj mudan su ukun nan kacal abun ba karamin mamaki ya ba dad ba sede ya danne ya cigaba da amsan gaisuwa yana duba ta ina ze ga haisam din amma bashi ba alamarshi ...................


Se Chan mutane sun fara watsewa tukun haisam ya karaso shi kadai a wata arniyar benz cikin shiganshi na kullum wato kananan kaya sanye yake da dark blue Jeans tare da red shirt wadda yake da layi layi na baki a jikinshi kafanshi sanye da normal shoe na maza me kyau da tsada gashin kanshi a gyare se sheki yake zuwa kwantacciyar siririn sajenshi wadda ya hade da madaidaicin gemunshi cikin takunshi na izza da kasaita irin na zaratan maza masu ji da kansu ya qutsa cikin mutanen Dr fareed kawai ya mikawa hannu suka gaisa kowa jiki na rawa aka karaso aka zagaye shi kowa na mika mishi hannu da sunan tayashi murna................


Fuskan nan kaman an aiko mishi da sakon mutuwa hannun kawai yake mikawa ba tare da yana amsa gaisuwa da kuma albarkar aure da suke saka mishi ba kir idon dr fareed a kanshi tab Allah sarki uwata zaki wahala da wannan bawan Allahn duk da yau ranar auren shi amma fiskanshi ba digon farin ciki kallon jikinshi dad yayi yace a zuciyarshi oh Angwaye na saka shadda amma shi wannan da tsabagen iyayi shine da kananan kaya a wurin daurin aure.................


Cikin gundura da hayaniyar mutanen ya koma wurin dad yace "bana son kowa yace zai kaita gobe da dare zanzo na dauke ta" dad yace "toh Allah ya kaimu amma kayan dakinta fa?" Dafe kanshi dake sara mishi yayi don tsabar hayaniyar gurin na damunshi yace "akwai komai base an chanza min ba but in kunyi insisting se ayi hayar masu shiryawa daga company bcos I don't wanna see every woman in my house da sunan jere ko rakiya" yana kai nan ya juya ya fice cikin isa ya fad'a motarshi tare da fisga ya nufi gidanshi..............


Ba wadda ya san da fitan shi ai da baza su taba barinshi ba driver yasa ya kai mishi mota ta jikin katanga gurin karamar kofa a sace ya fice ta garden ya fita kan kwalta tare da bude wani karamin kofan se gashi a waje gabadaya karban key yayi ya wuce duk da shi kai tsaye yake abu amma be son yaqoob ya san da auren har ya gayawa sagir tunda ba wani jimawa da ita zeyi ba hankali kawai ze koya mata..................


Mom dad ya kira ya fadawa sakon haisam sam bata ji daadi ba hasali ma haushin haisam din ta fara ji a aladance ya kamata ai idan yazo daurin aure ya shigo da abokananshi suyi gaisuwa da yan uwan amarya a kuma yi photona da amarya amma ko daya haisam be yi ba shiyasa kullum se ta wa dad magana akan auren amma se yace ai haka yake ba wadda ke gane mishi tunda ba shiga mutane yakeyi ba..............


Fadawa wa'yanda suka fara shiri don kai amarya sakon ango tayi tare da kiran wani company ta basu ragamar jere ma hamrah seda suka je ma aka hana su shiga mom suka kira suka fad'a mawa cikin fusata ta nufi dakin hamrah da niyyar masife ta se ta sameta dukunkune a kan gadonta se rawar dari take tana kuka da sauri ta haura gadon tana tambayarta me ya sameta amma hamrah rungume mom din tayi ta kara karfin kukanta...............


Duk a tunanin mom sbd rabuwa da su ne da kyar ta lallasheta tace "dama fa shigowa nayi na fada miki ki kira mijinki ki fad'a mishi masu jere suna waje bari na kawo miki magani sbd zazzabin nan kuma ki rage kukan nan kin ga de yadda numfashinki ya fara sauyawa" Da toh kawai hamrah ta amsa mom ta fice ita kuma ta dauki waya ta kira shi har sau biyu tukun ya daga a zuciyarta take masifa...............


Da ba don mom ba da zan kira ka ne har ka nemi ja min aji dan rainin wayo kawai, dagawa yayi tare da shiru abinshi ba tare da ta gaishe shi ba tace "mom tace masu jere suna gate kuma an hana su shiga" tsaki yaja kaman b ze yi magana ba se kuma yace "ke a gidanku ba'a koya miki tarbiyar gaida miji bane?" Yana jin yadda numfashi ta ya sauya se ya smirking a ranshi yana cewa yes daman abunda yake bukata kenan...............


Izuwa yanzu yasan lagonta sune iyayenta dama AirPods ne a kunnenshi se be kashe wayan ba yana jin yadda take kokawa da numfashinta lumshe idanu yayi tare da zamewa ya kwanta a kan kujeran da yake, yana ji sadda mom ta shigo tare da salati tana furta "na san za'a rina mutum ya san yanayinshi amma se ya zauna yayi ta kuka kaman gidan makiyinki za'a kaiki yanzu fisabillillahi ina amfanin wannan?" Duk a zaton mom kukan da ta sha ne bata san harda bakar maganan da haisam ya fada mata ba dama kuma ciwon na kusa.............


Yana ji har mom ta shaka mata inhaler dinta numfashinta ya daidaita a lokaci daya kuma ta fashe da kuka tsaki yayi tare da kashe wayan ya kara runtse idonshi yana sauraran sassanyar karatun qurani dake tashi a AirPods din....  ta bangaren hamrah kuwa fad'a mom ta mata sossai tukun ta fice ta barta bayan ta sata shan maganin zazzabi..............


A zuciyarta take magana 'in shaa Allahu na dena kuka kenan akan haisam, zan iya daukan komai amma banda cin zarafin iyaye na kamar yadda ya fara kuma wannan ma be yi a banza ba' a haka bacci ya kwashe ta se asuba ta farka tayi sallah a lokacin mutane suka fara watsewa tana jin yadda kananan maganganu ke tashi akan wannan aure da ba ango kuma ba kai amarya...................


A ranar 'yan kano suka wuce haka da yamma jirgin 'yan sudan ya tashi aka barsu daga su se su, bayan magrib mom ta sata sake wanka da ruwan turare tana kumbura fuska tana tura baki a haka tayi wankan tana fitowa ta samu mom ta ajiye mata wata dakakkiyar leshi blue ne da touches na maroon riga da skirt ne an tsara dinkin kaman baza a mutu ba bayan ta goge jikinta ta shafa mayukanta tare da feshe jikinta da turare...............


Mom ta bata sabbin inners ta saka tare da zura kayan ba karamin amsan jikinta yayi ba hamrah akwai diri komai masha Allah mom ta sa ta gaba tare da Mika mata makeup kit dinta tace "oya fara saura inga bakiyi me kyau ba kiga yadda zanyi dake na lura duk bakya son aurannan se kace dole muka miki" dama hamrah makeup artist ce amma kanta kawai take ma se simra se kuma in mom zata buki.................


A haka tayi makeup din tayi kyau sossai kaman ka sace ta ka gudu gyale, takalmi da jaka duk fari mom ta bata ta saka a lokacin ne kuma dad ya kira mom akan haisam ya zo amma yana parlorn baki ya kuma ce tazo da hamrah parlorn shi, cikin mintuna suka isa dad be iya cewa komai ba se "Allah miki albarka ya albarkaci rayuwarki uwata kiyi biyyayya a gidan mijinki ki kuma rike sirrin aurenki" kasa ci gaba yayi don kuka ke shirin zuwa mishi mom ma tana hawaye ta kara yiwa hamrah nasiha dama ita kam tunda aka fara buki in sun kebe se ta mata nasiha daya biyu...............


Tana gama fadan abunda zata fada ta mike da sauri ta fice tana share hawaye dad ne ya kama hannunta ya mikar da ita ta zama kaman statue kukan ma ya kasa zuwar mata tana jin kaman tayi bankwana da farin ciki kenan a rayuwar ta a haka suka karasa parlorn baki haisam na hakimce a kujera se kace gidanshi hannun haisam daddy ya kama ya damka mishi na hamrah a hankali yace ..............


"Ga amana dan Allah ka kula da ita" se ya juya ya fice kallon hamrah yayi da ta bi bayan mahaifinta da kallo a take kuka ya zo mata ta fara risga mikewa haisam yayi ya ja hannunta suka fice a chan waje yayi parking motar shi so gate suka nufa direct tana ta kokarin fisge hannunta amma ko gezau har suka isa ya bude baya ya jefata da karfi har ta dan buge ya zagaya ya shiga tare da figan motan...............


Har Sunkayi nisa da tafiya bata bar kuka ba har suka shigo layin gidanshi tukun ya wani taka burki har seda ta buge goshinta a razane ta dago fararen idanunta ta zuba a cikin nashi tsawa ya daka mata "will you just shut up my friend" matsawa baya tayi kar ya mare ta seda ta tsugunar da kai tukun ta murgud'a mishi baki amma fa tsit kakeji ba kukan kallon inda suka nufa tayi a zuciyarta tace tab dama nan ne gidan haisam.............


Zata iya tuna sanda suka zo wuce nan da dad take ce mishi nan unguwan me sunanshi yace mata gidan duk na mutum daya ne ba unguwa ba, zaro ido tayi tace tab lallai to waye shi be fad'a mata sunanshi ba kawai cewa yayi na wani business tycoon ne a hk suka rufe maganan tana gani motan na zuwa gate din ya bude da kanshi a haka suka dauki wani kwalta daga damanshi seda suka zagaya gini na farko tukun yayi kwana se gasu gaban wani gate din da yafi na farko kyau da tsari shima da kanshi ya bude daga ganin plate number din.............


Kutsa kai yayi ciki a zuciyarta se wow masha Allah take cewa gidan ya tafi da imaninta bayan ya zagaya wani roundabout yayi parking a main interance na gidan a wurin ya bar motan da keyn ya fice itama fita tayi tare da bin bayanshi har cikin babban parlorn kasa be tsaya ba ya haura ita ma bayanshi ta bi zuwa saman wani rantsatsan parlor ne taci karo dashi ya hadu karshe ba wani hayaniya zama yayi ita kuma ta ja ta tsaya..................


#vote 

#share

#comment 

'Yar mutan Adamawa


💞💞💞

                      💞💞hamrah💞💞                                                             💞💞Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin               *'yar mutan Adamawa*
Page➡8⃣

************


Ta kai minti ashirin a tsaye duk kafanta sun gaji gashi tana tsoron zama ya mata rashin mutunci kallonshi tayi hankalinshi kwance yana aikin danna waya zura mishi ido tayi tana kallon hallitan Allah a zuciyarta kuma yabon kyaun shi take, ji yayi a jikinshi Ana kallonshi dago dara daran idonshi yayi ya zuba su cikin nata da sauri ta kawar da kai kasa kasa yace 'Mayya' sarai ta jishi kuma kalmar ta mata zafi amma ya zatayi..............


Rawa kafanta ya fara kaman zata fadi lura da hakan da yayi ne yasa shi nuna mata wani room da yatsa ba tare da yayi magana ba da sauri ta nufi room din tana shiga ta zube a bakin gado tana sauke numfashi "amma Allah ya isa" ta fada afili tana hararan kofan tare da murguda baki, kallon dakin tayi yayi kyau sossai cikin Ash and milk furnitures cornered bedroom ne ba wani tarkace daga gado dressing mirror se wardrobe se kuma wasu coffee table ta jikin window se one siter dake kusa kadan da gadon...................


Mikewa tayi ta bude wardrobe ba komai se akwatunanta guda uku Allah ya taimake ta mom ta aiko dashi tare da masu jera furnitures dama ta riga da ta hada kayayyakin da take son zuwa dashi se ta ajiye a dakin mom bama ta san mom ta turo ba da bata san ya zatayi ba don be mata kayan aure ba Sam...................


Toilet ta fada ta cire kayan jikinta don duk sun ishe ta wanka tayi tare da brush ta fito daure da towel Wardrobe din ta koma ta fito da akwati guda ta bude tare da zaro sabbin man shafa da ta zuba a ciki tare da turarukanta, dressing mirror ta je ta jere su ta ja kujera ta zauna tare da shafe jikinta da mayukanta ta fesa turare ta dawo ta sake bude akwatin ta cire cotton nightie fari kal dogon wando da rigarshi iya cinya me guntun hannu ta saka, zaro dogon hijab tayi ta nufi inda taga an shimfida sallaya ta tada sallah Isha tayi tare da shafa'i da wutiri tana idarwa ta mike ta linke hijab din ta ajiye kan sallayan................


Ta juya da nufin hayewa gado kenan ta ji an turo kofar ido suka had'a da sauri ta kauda kanta tare da zama a bakin gadon ta jayo jakanta ta fiddo wayanta ta fara dannawa, jinginuwa yayi da kofan tare da harde hannunshi a kirjinshi ya zuba mata lumsassun idanunshi ko a jikinta tunda be yi sallama ba me ya dame ta, a hankali ya warware hannunshi tare da zuba su a aljihu ya nufo gurinta cikin takun isa da kasaita................


Yana taku da daidai tsoro fal ya cika ta duk takunshi daya se ya kara bugun zuciyarta har ya karaso hannu ya sa ya zare wayanta dake hannunta ya d'an danna na mintuna tukun ya Mika mata komawa yayi kan one siter ya zauna abunshi ya fara danna waya, rike wayan tayi sossai don tana ji kaman ze kubuce ya fadi yadda jikinta ke rawa duba me yayi dashi tayi se taga yayi dialing number..............


Wani special number ta gani da alamun nashi ne kallonshi tayi, ya hada gabas da yamma ya mai da hankalinshi kan waya tabe baki tayi tare da kunna data ta fara chatting da friends dinta da duk turawa ne se ji tayi sako ya shigo ta sms dinta komawa tayi ta bude se taga special numbern nan kenan shi ya turo mata sakon a zuciyarta tace tsabar miskilancin ne baza a iya min magana da baki ba kenan se ta sms Allah ya kyauta..................


Budewa tayi tare da fara karantawa kaman haka "welcome to HMS prison yard kaman yadda ko wani prison suke da rules and regulations hk nima nake da and you must abide by them, firstly dole idan gari ya waye ki duka har kasa ki gaishe ni ko zan amsa ko bazan amsa ba, secondly my meals three times a day yana wuyanki kuma ba'a yimin abinci kala daya se sama da haka...................


Thirdly tsabta bana kazanta kuma na tsani me kazanta dole zaki ringa shara da mopping na sama gabadaya har dakina banda kasa, fourthly had'a min ruwan wanka da kuma fitar min da kayan sawa kafin na fito fifthly ba aiki a gidana idan har da igiyar aure na a kanki to baki ba zuwa office da sunan aiki yeah you are free zaki iya fita duk inda kike so amma ki tabbatar kin gama duk wani aiki da yake kanki.............


Last but not the least rashin kunya ko raini baya daga cikin tsari na idan kunne yaji jiki ya tsira sannan tsaki I hate it karki kuskura ki soma ban taba dukan wani ba amma kika yadda na fara a kanki baza kiji da daadi ba kuma idan ba ni na miki magna ba ko sannu bana so kice mussaman in da baki ko securities I don't know ko shi kenan but in akwai wani abu zan kara miki".................


'Dago manyan idonta da ya cika da kwalla sunyi zarazara a ciki se sheki sukeyi ta zuba mishi shima ita yake kallo idonshi a kan gashinta da suka zubo har kirjinta baki sidik ga tsantsi da laushi kau da idanunshi yayi ganin hawaye na gangara a idonta yayi smirk tare da mikewa ya nufi kofa abunshi cikin izza yake tafiya har ya fice.................


Komawa da baya tayi ta kwanta tare da lumshe idanunta he shattered each and every single of her dreams tana da burin aiki a rayuwanta sossai take da burin bunkasa company dinsu ta hutar da mahaifinta yadda ba ze yi sha'awan dama ace namiji ya Haifa ba sannan she hates to be a complete housewife kaman yadda matan arewa suke tana ga rayuwa Mara yanci sukeyi..............


Sannan shara?? Mopping? Abunda bata taba yi ba kenan a rayuwanta, gwara girki ita gwana ce don tayi catering school sossai dishes daddaya ne bata iya ba kallon time tayi dare yayi amma gobe zata kira dad ta hadashi dashi kwanciya tayi ta barwa gobe Allah ya taimake ta cikinta ba yunwa................


Washegari 


Bayan tayi sallahn asuba ta samu wani tide three quarter ta saka black color se ta dauko white shirt dogo zuwa cinyanta tayi parking kanta pony tail yana lilo ta zura silipas me taushi ta fice kallon katon parlorn tayi ba wani datti amma ta san se ta sake shara da moping nufan kitchen ta fara daura girki yam bolls tayi se tayi pepper soup na kayan ciki ta shirya su akan dining ta ajiye mishi ruwan zafi incase ze sha tea ta shirya dining din tsab tukun ta fara shara..............


In tayi kadan se ta mike tana rike baya da kyar ta gama ta fara moping se cika ruwa takeyi tana jika tiles din parlorn a haka ta jijjika da kyar ta tsaya abunda ba sabon ba hawaye ne ya cika idonta zama tayi tana hutawa se gashi ya fito da kayan bacci riga da wando light purple kallon ta kawai yayi tare da juyawa ya koma...............


Mikewa tayi ta bi bayan shi tana shiga ta same shi zaune a bakin gado dukawa tayi tace "Ina kwana" kamar yadda ta san baze amsa ba hakan kuwa be amsa ba ta mike ta fad'a toilet ta had'a mishi ruwa yadda ta saba had'awa kanta ko aka hada mata ta zuba duk turarukan wankan da ya kamata fitowa tayi tare da folding hands dinta mikewa yayi ko kallonta be yi ba ya shige toilet din................


Kallon dakin ta fara komai white kaman nata cornered room amma ya take nata kyau kayan ciki ma baza a hada da nata ba gadon ta nufa ta fara gyarawa wani tsawa ta ji a kanta "ke!!!!!" A firgice ta dago ta kafa mishi ido tana jiran jin laifin ta cikin dakakkiyar muryanshi yace "haka ake had'a ruwan wanka a garinku? How dare yhu? A dan tsorace take kallonshi tana jira taji zafi yayi ko sanyi..............


"Stop staring at me da ido kaman na owl" ya kuma daka mata tsawa tsugunar da kai tayi tana dan karkada kai yace "just go inside and change that water muguwa kawai" anan ta gane kenan ruwan yayi zafi shine baze iya kara ruwan sanyi ba se ya zage ta? Ba tare da tace komai ba ta bi ta gefenshi ta shiga toilet din ta kara ruwan sanyi ta fito shi kuma ya shiga, gyara dakin tayi tare da shara tayi moping ta fito mishi da kayan sawa kafin ta fice zuwa dakinta ta fada kan gado tare da sa kuka.................


Me yasa tayi sanyi? Me yasa take jin tsoronshi? Dama ta riga da tayi ma kanta alkawarin dena kuka amma baza ta iya ba ta san yanzu ta kulla alaka da kukan amma baza ta taba yi a gabanshi baza ta nuna mishi tana jin zafi ba daga parlor taji Ana "ke!!! Ke!!!" Ta san ita yake kira mikewa tayi tayi saurin share hawayen ta ta fita da sauri................


"What the hell is this????" Kallon abunda yake nunawa tayi jirwayi jirwayin da tiles yayi sbd yadda tayi mopping din dafe goshinshi yace "god" ita da ya kamata ya ba wahala amma shi ke jin wuyan tunda cikin awanni kadan ta sashi surutu har kanshi na sarawa zuwa yayi ya zauna tare da kallon time almost 9:30 Allah ya sa yau lahadi kira yayi ba tare da yace komai ba se ga wata budurwa ta shigo...............


Ba tare da ya kalle ta ba yace "I give you today, just today to teach her how to mop she's a maid like you" cikin ladabi ta amsa da "yes sir" mikewa yayi ya nufi dining bayan ya kalli idon hamrah ya furta "useless human being" zama yayi yana fatan ganin ba daidai ba tabbas se ya koya mata hankali............


Ai ko yana budewa wani kamshi ya ziyarci hancinshi komawa yayi ya zauna a hankali yace "ke" juyowa tayi ta nufo gurin ta ja ta tsaya kaman be so yace "serve" serving dinshi tayi kafin ta juya ta fice ba tare da ya kalle ta ba ya fara cin kayan shi ita kuma tabi bayan waccan yarinyar zuwa kasa don ba su cika aiki a sama ba in yana nan iya kacinsu su gyara su fito har kasan ma................


Tunda yarinyar ta fara koyamata take tunani a zuciyarta se nanata she's a maid take yi a zuciyarta kwabar kanta tayi ta sa hankali sau biyu yarinyar ta nuna mata amma har ta iya barin yarinyar tayi ta haura sama ko kallon bangaren da yake batayi ba ta shige daki tana rufe bakinta gadonta ta fada ta fara kuka karar sako taki a wayanta she wish she just wish it's simra............


Jawo wayan tayi se taga numbern haisam da har yanzu batayi saving ba budewa tayi se taga "u are lucky so very lucky today is not working day kika yarda kika sake delaying everything nawa se na mayar da rayuwanki a living hell, 8am nake barin gida take note of that" kife wayan tayi ta ci gaba da kukanta..............


Bata jima ba ta tashi ta shiga wanka ta shirya cikin normal gown milk ta fice ta koma parlorn bata ganshi ba ta sake moping tukun tayi breakfast ta tattara ta kai kitchen tare da wankewa ta daura abincin rana zama tayi tana tunani yanzu haka rayuwanta ze kare? Maid kowa ganin da ze mata kenan? Kiran mom tayi suka gaisa ta kira dad suka sha hira Chan de tace .................


"Dad yace bazan yi aiki ba ko zaka iya convincing dinshi?" Murmushi Dad yayi yace "lallai princess kenan baki san mijinki ba hmmm tun kafin a daura aure yace min bazakiyi aiki ba I thought kun riga kun shirya hakan shiyasa ban tambayeki ba and mijinki ne you hv to obey him tunda yace be so se ki bar maganan" dafe kai tayi a zuciyarta tana cewa 'shit shit too late to cry"..............


A aiki ranar rayuwanta ya kare se dare ta kwanta tana kwanciyar ma taji kira a wayanta kaman yadda ta gani dazu yarinyar Chan tayi mikewa tayi ta fice zuwa dakinshi a tsaye ta taraddashi bayi magana ba ya tura mata sako a waya "ruwan wanka" toilet ta wuce ta hada mishi ta fito ta fice ko tak duk yau bata ce mishi ba bayan gaisuwa........


Ita ma gasa jikinta tayi ta kwanta bacci me dadi ya kwasheta cike da gajiya..................

#vote 

#share

#comment

'Yar mutan adamawa"


Not edited💞💞💞


                💞💞hamrah💞💞
                                                         💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin             *'yar mutan Adamawa*Page➡9⃣

**************


Washegari da wuri ta gama duk abunda yake aikinta ta koma dakinta da ya tashi cin abincin ma se da ya kirata tayi serving kuma ta tsaya har ya gama ci tukun ya fice ita kuma ta tattare gurin tayi wanke wanke tukun ta daura abincin rana, bayan ta gama ne ta shirya ta fice zuwa tsakar gidan da sauri wani ya taso zuwa wurinta yace "barka da fitowa hjy, yallabai yace duk inda zakije ni zan dinga kaiki" ba tare da tace komai ba yaje ya fito da mota ta shige shikuma yaja suka bar gidan.................


Seda suka dau hanya tukun ya tambayeta inda sukayi cikin sanyin murya tace "copa cabana" shiru motan ya dauka har suka isa garden din wuri ne Mara hayaniya shiyasa ta zabi zuwa inda zata ji dadin tunaninta da kuma nazari akan sabon rayuwan da ta tsinci kanta sallamanshi tayi Tace yaje duk inda yake so in ta gama zata kira shi ficewa yayi ita kuma ta samu bakin wani ruwa ta zauna akan wasu kyawawan kujeru da aka kawata su...................


Tsam ta tsunduma duniyar tunani, tunda ya shigo gurin yake kallonta kyakyawa ne  ba laifi fari sol kaman ka taba shi jini ya fito wani munafikin murmushi ne akan fuskanshi har ya samu kujera dake facing dinta ya zauna a fili ya furta "what a beautiful damsel" lura da yayi ta fada duniyan tunani kuma fuskanta is so pale da alamun akwai abunda ke damunta ya sashi mikewa ya nufe ta.................


A kujeran gabanta ya zauna shima yayi tagumi kamar yadda tayi tare da shagwabe fuska, jin wani kamshin turare na daban yasa ta kallon wurin ganinshi a haka ya tsoratata ta zaro manyan idonta zata mike yayi saurin cewa "Amincin Allah su tabbata a gareki ya ma'abociyar kyaun fuska dana jiki" komawa tayi ta zauna tana sauke ajiyar zuciya................


Murmushi me sanyi ya mata ita ma ta mayar mishi tukun tace "god ka tsorata ni wlh" Dariya yayi tukun yace "matsoraciya kawai by the way my name is hisham nasir and yhu?" Tace "hamrah fareed" zaro ido yayi har ta dan tsorata tukun ya juya su kaman mace tare da cewa "wow what a nice name" dariya tayi tana cewa "wlh kana da ban dariya" yace "haka ake cewa, me ke damun priceless flower ne?".................


Tabe baki tayi tana cewa "you are a stranger you know?" Hada baki sukayi wurin cewa "how can I tell you my problem" a tare sukayi dariya tace "ya akayi kasan abunda zan fada kenan" yace "Kin san ko ina da super power?" Murmushi ne sossai akan fuskanta tace "hmmm I hear this" shima murmushin ya mayar mata a hankali suka fara hira sossai yake jan ta da hira har ta sake suka kwashi hira ta ma manta da wani haisam da damuwar da ya sa ta ciki......................


Hira sukayi sossai a lokaci kankani suka shaku sossai kasancewar hisham me saurin sabo da raha duk wani damuwanta ya kau kallon agogo tayi taga 5pm zaro ido tayi tare da mikewa a firgice har seda hisham ya dan ji tsoro kallonta yake da alamun tambaya kafin yayi magana ta fara magana ta waya "yi sauri kazo muje gida"...................


Katse wayan tayi ta fara Jeka ka dawo tana tunanin abunda zata girka me sauki sbd yace mata baya dinner in har 7:30 ya wuce innalillahi Allah ka tsare ni da bala'in wannan bawa a zuciyarta take maganan har drivern ya iso kallon hisham tayi tace "zan tafi hisham se munyi magana" hannu kawai ya daga mata da tarin tambayoyi a zuciyarshi amma tunda ya karbi numbernta ze samu amsan su..................


************


A rude Alhj mudan ya kira Alhj halliru "hello Alhj akwai matsala, mugu ne ya kira ni" Da karfi Alhj halliru yace "what!!!!! Me yace maka?" Alhj mudan yace "cewa yayi kudin hannunshi sun kare ko mu kara mishi ko asirin kowa ya tonu" Alhj halliru yace "me ke faruwa ne dama mugu na raye? Shekaru ashirin yayi mana aiki kuma mun sallame shi se yanzu ze ce mu bashi kudi? Aka gayamishi mun anfana da aikin ne?"...................


Ba tare da daga hankali ba Dr zubair dake zaune gefen Alhj mudan yace "Dan Allah ku dena daga hankalinku karyan iskanci yake kawai ya rasa abunyi ne barazana ce, me ya isa ya mana shima ba se mu kawar dashi ba" Alhj halliru yace "kuma haka ne fa se mu daura barde kawai a aikin donshi da zamani yake tafiya" Alhj mudan de hankalinshi be wani kwanta ba hk sukayi sallama da Alhj halliru suka ci gaba da tattauna maganan da dr zubair.................


*************

Bayan sati daya
Bayan ya fito daga sallahn magrib daga massallacin dake cikin estate na securities dinshi duk a cikin gidan ne amma gate da fence ya raba su da main house dinshi hannu ya tura gate din ya shiga tafiya yake cikin kasaita da izza irin ta zaratan maza masu ji da jini a jika kaman an ce ya kalli gefe se yaga wani mutum da bakaken kaya ya wulga ta bayan duplex dinshi me yanayi da an lankwasa cat fish da sauri ya zagaya roundabout na flowers daya zagaye compound na gidan ta cikin parking lot ya bi inda motoci sunfi kala ashirin a ciki da sauri ya boye a bayan wani mota ganin wancan mutumin ya fito yana kalle kalle............


Da yaga ba'a kallonshi se ya kutsa ta cikin garden din bayan building din a hankali haisam ke binshi har suka isa wani karamin kofa dake garden din yana gani aka bude mishi ya fita, kenan da hadin bakin securities dinshi da sauri ya koma inda yaga mutumin ya shiga ta bayan windows parlorn kasa a jiki yaga wani jaka a makale karami dauka yayi ya bud'e se yaga voice recorder ne irin na da da wasu papers anyi rubutu a jiki...............


Daukan jakan yayi ya shige cikin gida a dakinshi ya ajiye ya fito ya nufi dining zama yayi se gata ta shigo sannu be had'a su ba sede yana kallonta kasa kasa a take ya lura da a kwana daya har tayi wani iri ta tashi daga 'yar gayu ta koma wata daban bawai a jiki ba a'a yanayin tafiyanta yanayin maganan ta da kuma lura da yayi ko powder bata shafawa, ba kaman yadda aka fad'a mishi kullum tana tare da heavy makeup a fuska ba..................


Komanta ya koma a sanyaye a kaman Mara laka shi yasu ta ringa mishi rashin kunya ne yadda ze ji daadin hora ta da hujja amma se take kiyayewa ya san yanzu ko tsinke ya ajiye yace karta tsallaka baza ta tsallaka ba, kallon abincin gaban shi yayi a zuciyarshi yace 'and she's a great cooker' duk rayuwanshi ze iya tuna abincin da ya fi na hamrah daadi shine na Ammin shi.....................


Runtse ido yayi tare da saurin kawar da tunanin ya fara cin abincin da ta ajiye a natse cikin iyayi kaman be so dama ta san be wani cin abinci sossai shiyasa take yin kadan, yana gama ci Ana kiran isha goge bakinshi yayi ya mike ya fice zuwa massallaci ita kuma ta hau tattara wurin sossai take jin dama dama yanzu tunda magana be hada su in ta gaishe shi ba amsawa yakeyi ba randa in na muguntar na kusa se yayi ta sata aiki har da wadda ba nata ba amma haka take daurewa tayi in ya rasa abun masifan haka ze yi shiru.................


Dama se ya yini agidan in ba a waya ba baza ta ji muryanshi ba, basu taba haduwa da yaqoob ba se de sauran ma'aikatan gidan duk da suna mata wani irin kallo amma bata taba basu daman raina ta ba kullum fuskanta a had'e ta bangaren su da hisham kuwa sossai suka shaku kullum in ta gama aiki zata tafi copa cabana garden su sha hiransu yayi ta bata dariya............


Yana dawowa daga masjid ya haura dakinshi yayi wanka ya shirya cikin mint green kayan bacci me budedden kirji ya samu kujeran coffee dake jikin windownshi ya zauna tare da daga labulen iska se kadawa yake da alamu damina ne ke shirin shigowa kunna recorder din yayi wasu muryoyi ya fara ji kaman ya sansu ba tantama ya san muryan nan sede baze ce ga inda ya sansu ba..............


Daya daga ciki ne yace "no idea dinka be yi ba idan muka kashesu ta hanyar kunce musu birki asirinmu ze iya tonuwa se anyi binciken dalilin mutuwan" wani daga ciki yace " to Alhj mu saka musu guba mana kawai ta hannun masu aikinsu duk suci su mutu" wadda yayi magana dazu da alamu shine me fasahar cikinsu yace "Wannan ma asirin mu ze iya tonuwa" wani da tun dazu be ji yayi magana ba yaji yana cewa................


"Duk ku saurara Alhj mas'ood sa'ood na zuwa kano ko wani ranar sati kuma be zuwa da security ko daya hasalima ba wadda yake sanin tafiyanshi se drivern dake kaishi shi yasa ake cewa be ganin mutane Saturday and sunday" na farkon yayi saurin cewa "me yakeyi?" Wadda ke bayanin yace "me kake ci ne na Baka na zuba? Zuwa yakeyi ya zaga duk wani kauye da ya ji labari ko ya san suna cikin matsin rayuwa ya basu taimako kuma akwai malamai na mussam dake mishi sauka duk Sunday harda shi da danshi a ciki"................


Me magana na biyu ne yace "kai da Allah share maganan wani da plz be cikin lissafinmu" mutumi na biyu yaji yace "hmmm zamu zo kanshi ne kana tunanin in ya girma baze zame mana matsala ba" na ukun ne yace "dan Allah kuyi shiru Alhj meyasa ka bamu wannan labarin?" Murmushi yaji na hudun yayi yace "mugu zamu tura in suka isa da dare suje da yaranshi su yima matarshi mugun fyad'e to shi sa'ood ganin haka tabbas ze sa shi hadiyar zuciya ya mutu kunga shikenan"..................


Dariya suka kwashe dashi kafin kit recordern ya dauke, wani irin huci haisam ya fara numfashinshi na fisga a take duk wani memory ya fara dawo mishi muryoyin ya fara ji suna dawo mishi kaman yanzu abun ke faruwa 'haisam shiga Chan ka buya duk abunda zaka ji karka fito kaji' 'Ammi su waye ne' ' ban sani ba nima amma mugaye ne dan Allah son karka bari su kasheka duk abunda ya faru damu kai ne me bi mana hakkinmu karka manta muna sonka sossai'..............


Hawaye ne ya fara zubawa haisam yana kuma jin muryan Abba na cewa 'Aisha kema ki buya plz banson wani abu ya sameku na san duk akan dukiya ne' ' a'a Alhj bazan bari komai ya same ka ba' yana kallo a idanunshi lokacin da aka rike mahaifinshi wani kato ya hau kan Ammi tare da kokarin rapping dinta yana gani suka ta kokawa har ta cire mishi face mask dinshi, fuskan da baze taba mantawa ba kenan yana tuna yadda Abba ke magiyar wlh ze bar musu komai nashi amma dan Allah kar suyi mishi haka..................


Kunnuwan shi haisam ya toshe yana jin ihun Ammi da salatinta a kunnen shi kaman yanzu takeyi "innalillahi wainna ilaihi rajiun" ya fara yi yana tuna yadda mutumin nan be bar Ammi ba har seda yaga numfashinta ya dauke yana gani Abba ya fad'i, yana tuna yadda mutuminan ya taba zuciyar Ammi jin tana numfashi yasa aka bashi pillow ya danne fuskanta na kusan 5mins haka suka ma Abba ma.................


Zuwa yanzu haisam ya kai kasa wani irin kuka ya fashe dashi yana jin wani irin maraici tare da kadaici jikinshi har rawa yake tusa kanshi yayi a tsakan kanin ciyoyinshi a take kuma hawayen suka kafe azaban ciwon zuciyarshi ya danne su murkususu ya fara gashi yayi nisa da gado balle ya danna kiran yaqoob a haka har ya kai tsakiyar dakin numfashinshi na fita da kyar.......................


Hamrah ce ta fito don zuwa had'a mishi ruwan wankan dare don ganin 9 yayi kuma a daidai lokacin yake wanka bata da masaniyar yau tun 8 yayi wanka knocking tayi na kusa 2mins ba'a amsa ba ta tuna lokacin da tayi irin haka ta fada ba tare da taji ya amsa ba duka ne kad'ai ya rage be mata ba har zata juya taji kakari da wani irin numfashi dake sauka da karfi.................


Da sauri ta bude dakin ta shiga ganinshi tsakiyar dakin yana murkususu yasa ta karasa kanshi da gudu ta dago shi a rude take cewa "innalillahi me ya same ka? Me ke damunka? Wa zan kira maka? Dama kana da wani ciwon ne?" Duk ta rasa me zatayi se ta fashe da kuka tana jijjigashi ganin jini tayi a baki da hancinshi da kyar ya iya nuna mata bedside dinshi, da sauri ta mike ta nufi bedside din ta bude magani ta gani budewa tayi ta dibo guda biyu da sauri har jikinta na rawa ta dauko bottle water daya ajiye a wurin ta nufo shi......................

#share 

#comment 

#vote

'Yar mutan Adamawa


💞💞💞


                    💞💞hamrah💞💞
                                                           💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin                 *'yar mutan Adamawa*Page➡1⃣0⃣

************


'Dago kanshi tayi cikin tashin hankali tare da sa mishi maganin a baki da ruwan kadan sha yayi ta kara mishi ruwan kafin ta ajiye kan a kan kafanta ta jingina da kujeran, ido ta zuba mishi a yayin da yake sauke ajiyar zuciya a take bacci ya dauke shi, kallon inda yake tayi akan tattausan rug yake da a tiles ne da bata san yadda zatayi da shi ba a hankali ta sauke kan nashi ta isa gado ta dauko pillow da katon blanket dinshi ta saka mishi tare da lullube shi lub ta tofe shi da adu'ar bacci tukun ta fice tana waiwayenshi..................


Seda ta isa dakinta tukun ta fara jin haushin kanta me yasa ma ta taimake shi? Tunawa tayi da yadda ko a jikinshi randa ciwonta ya tashi a office dinshi amma ita harda kuka tsaki tayi a fili tace "don Allah nayi ba don halinka ne da sede ka mutu" a zuciyarta tace amma me ke damunshi? Tabe baki tayi irin shi yasanin nan kafin ta chanza zuwa kayan bacci tayi kwanciyarta...............


Washegari da wuri ta tashi asuban fari ta nufi dakinshi tana turawa suka hada ido yana zaune kan sallaya da qur'ani a gabanshi, da sauri ta koma shi kuma ya saki smirk ya ci gaba da azkar dinshi, dafe da kirjinta ta koma room dinta tab Allah yasa kar ya mata masifan shiga mishi daki da asuba don har ga Allah tsoronshi take kaman yadda ta saba tayi aikinta tsab kaman ba ita ba tana gamawa ta gudu room dinta.............


Kunyan haduwa dashi take ko ruwan zafin yau bata je ta had'a mishi ba da ya tashi breakfast ma bata je ba shima be neme ta ba seda ta dena jin motsinshi tukun ta fito sharp sharp tayi wanke wanke ta daura abincin rana a kitchen din ta zauna har ta gama jollof rice tayi bata iya yin biyu ba sbd yadda take jin kasusuwan jikinta ke amsawa hakan be rasa nasaba da yadda tunda ta zo gidan take kwana a high Air condition ba dama ko a gida se ta kwanta mom ke zuwa ta rage Acn ko ma ta kashe gabadaya kuma kullum ne se ta mata fadan kure Ac amma bata ji, zobo tayi mishi ta kai dinning ta shirya tukun ta koma daki tayi wanka ta samu tablets dinta tasha ta shirya cikin riga da wando duk tide se ta daura kimono me tsararren kyau a kai ta yana gyalenta wayanta kawai ta dauko tana fitowa su kuma suna haurowa su uku ta san yaqoob kam amma bata san sagir ba rabewa tayi suka wuce har zata wuce taji yace "ke!!!!"...............


Cikin dakakkiyar muryanshi juyowa tayi ta dawo su kuma suka nufi dining suka zazzauna "serve us" wayanta ta ajiye daga parlor ta shiga dining area din Allah ya taimake ta yau tayi abincin da d'an yawa kuma bata dibi nata ba serving dinsu tayi tana kallon yadda minti minti yake cije baki yana kuma sa hannu a kirjinshi da alamun dauriya kawai yake toh me ke damunshi?.................


Cikin tunaninta bata sani ba har zobon da take sawa cup din ya cika har ya fara zuba a kan dining din tsawanshi taji a kanta a firgice ta ajiye jug din " wai ke wace irin dakikiya ce marar hankali baki da ido ne!!!" Cikin in ina tace "kayi hkr dan Allah" kallon plate din gabanshi yayi duk da jallof din ba karamin kyau yayi ba yaji kifi da nama ga veggies amma se yace "au wato don kin raina ni shine zan fad'a magana ki tsallake ko? Didn't I told you ba'a min abinci daya and wannan busashen shinkafan??"................


Da mamaki yaqoob da sagir ke kallonshi sun kasa magana sam basu san haisam da wannan hali na wulakanta mai aiki ba balle wannan ma bata yi kama da mai aiki ba in kayi la'akari da yanayin kamshi dake tashi a jikinta ga yanayin dressing dinta na mata ne masu aji fatan jikinta ma kadai ka kalla se ya baka sha'awa tsabar kyalli da alamu kuma zaiyi taushi jin yayi cikin sanyin murya me dadin saurare tace................


"Dan Allah kayi hkr wlh bana jin daadi ne........" kafin ta karasa ya daka mata tsawa har seda ta kara firgita "just shut up bloody fool get out" sagir ne yace "haba man ban sanka da wannan hali ba yanzu me laifin abincin nan plz" cikin dakewa haisam yace "shut up ba da kai nake ba" wani banzan kallo ya jefe ta dashi da sauri ta fice bayan sun had'a ido har yana kallon hawayen da ya cika mata ido se kyalli yake...............


Tana ji sanda dayan da bata sanshin ba wato sagir yana cewa "who's she?" Haisam yace "Fucking maid" bata sake jin komai ba ta gangara da sauri ta bude mota ta shiga yaja kafin su bar gidan ta fashe da kukan dake cinta...............


Haisam na kai abincin baki seda ya lumshe ido tsabar dadin da yaji abincin yayi yaqoob kam duk abunda ake tunanin inda yasan fuskan yake da yaga ya kasa tunawa kawai se ya fara cin abincin wow kawai yake furtawa yace "amma abincin nan yayi daadi" sagir ma santi kawai yake se haisam ya tsinci kanshi da jin haushi ba tare da yace musu komai ba ya ci gaba da cin abinci sossai yasha zobon don yana son drinks din ji yayi sagir na cewa..................


"Ni kam na samu matar aure ga kyau ga iya girki dan Allah aboki ka shigar dani" hararar shi haisam yayi tukun ya buga tsaki tare da mikewa tsam ya nufi dakinshi dauko jakan jiyan nan yayi ya fito dashi parlor ya zauna yana jiransu yana jin yadda sagir ke ta maganganu akan hamrah se ya kunna tv tare da kaiwa tashar wrestling ya kure volume, tunaninshi kuma na ga yadda ya bata mata.............


Maimakon yaji daadi yadda ya saba amma se yaji akasin haka tunanin daren jiya ne ya fad'o mishi yadda ta taimaka mishi yadda tayi kuka sbd wadda ke zaluntarta bai da lafiya, wani irin zuciya ne da ita? To ina ma taje? Tunaninshi ne ya katse jin su sagir sun zazzauna serious kowa ya zama don musamman ya kira su yace yana da mahimmiyar magana da su............


Kallonsu ya tsaya yi yana tunanin yadda ze yi doguwar maganan da yake so dasu don ko meeting ya shiga takaita komai yake yi amma yanzu yana so ne su fahimci abunda yake so su fahimta sagir ne ya tashi ya shiga dakinshi ya bude first aid ya dauko paracetamol ya zo ya ajiye a gabanshi dariya suka saka shi da yaqoob amma gogan kam ko smirk din be yi ba sbd ranshi a jagule yake............


Sagir yace "toh na san abunda yake tunani kenan idan yayi magana dayawa kanshi ze yi ciwo to ga paracetamol" suka ci gaba da dariyansu yaqoob ne ya kalli haisam yace "dan Allah yallabai in maka tambaya baza ka damu ba?" Da kai haisam ya amsa yaqoob yace "me yasa tunda Allah ya had'ani da kai har yau baka taba dariya ba ko ciwo ne".................


Wani smirk haisam ya saki cikin takaici yace "yaqoob to ai wadda duniya tawa daadi ne yake dariya with bitterness a tongue dinshi yace me a cikin duniyan da har ze bani farin cikin rayuwa? Rayuwata haka zata kare farin ciki na na lokaci kankani ne a baya da be wuci shekaru 3 ba bana tunanin kuma sake farin ciki a nan gaba se wani iko na mai duka"..............


Numfashi ya ajiye tukun yaci gaba idanunshi sunyi jazur "yaqoob tunda Allah ya hada mu da kai kake tare dani cikin gaskiya da amana baka taba ha'intata ba baka san waye ni ba amma baka taba tambaya ba sbd ka yarda dani a yau zan fad'a maka waye ni se abu guda da zan boye maka wadda sagir ka san dalili" gyad'a kai sagir yayi tukun haisam ya ci gaba.................


"Kai sagir ka san iyayena sun nuna min so fiye da zatunku wayanda bani da kamarsu a duniyan nan baki daya su suka cire ni cikin kunci da azaba suka bani soyayya marar algus ka san an kashe su amma kaima baka san dalilin kisan ba to a yau zan baku lbr sbd Ina ganin lokaci yayi da zan dauki fansa sede Ina bukatar taimako da kwarin gwiwar ku"................


A hankali ya fara basu labarin yadda abun ya faru da yadda aka yiwa Amminshi fyade akan idanunshi aka kuma karasar da sauran numfashinsu har ya gama bada labarin sagir kallonshi kawai yake yana kiyasta yadda Dan shekara 8 ya iya daukar wannan abu ashe shi yasa lokaci daya ya tuna yadda in iyayensu sun hadu suke wasa da dariya amma rana daya haisam ya dena dariya ya kuma dena wasa da sa'anninshi...............


Yaqoob kuwa kuka yake yi yana jin tausayin me gidan nashi har bargonshi kenan bayan shekara biyu da mutuwarsu suka had'u da kyar haisam yayi controlling kanshi zuciyarshi yake ji kaman ze fito kanshi ya dauki azababben ciwo zazzabi ma gabadaya yake ji ya san ciwonshi ne ke shirin tashi kamar yadda ya san ba abunda maganinshi nan zasu mishi yana bukatar special medication amma taurin kai ya hana shi..............


Mikewa sagir yayi ya isa gefen damanshi tare da rike hannunshi idanunshi zajur fuskan nan ya koma na asalin sojoji har bari jikinshi keyi haka yaqoob ma yayi ya dawo hagunshi ya zauna yace "in shaa Allahu muna tare da kai har se munga hukunci ya tabbata akan wayannan mugaye" kai sagir ya gyada alamun tabbatarwa jakan haisam ya jayo ya bude ya fiddo voice recorder da papers din................


"Jiya na dawo daga sallah kenan naga wani da bakaken kaya ya ajiye wannan" playing yayi duk suka kuma ji papers din sagir ya dauka wasu address ne a jiki aka rubuta "ya san komai da kuma su waye" Murmushi sagir yayi me ciwo yace "abun ze zo da sauki kenan se mu nemi address din muje da hukuma" wani kallo haisam ya mishi tukun yace ................


"Bazan sa hukuma a wannan case ba da hannuna zan kashesu daya bayan daya" kallon rainin hankali sagir ya mishi yace "amma baka da hankali ka de san ba kyau daukan doka a hannu ko? Kasan hukuncin ka kuma ko?" Cikin karfin hali don jikin na son fin karfinshi yace "to se me in na mutu? Me abun daadi a duniyar da zan zauna inji?" Yaqoob yace .................


"Masu ci da sha a karkashinka fa? Ubangijinka fa me zaka ce mishi? Dukiyar da aka kashe su dansu kake son bar musu? To kenan baka dauki fansa ba kuma aikin banza kayi" shiru kawai haisam yayi ba Dan ya bar kudurinshi ba, bakinshi yake ta taunewa yana dan mimmikewa da kyar ya samu karfin halin tashi yana kuwa tashi ya zube sumamme..............


Innalillahi kawai sagir ke nanatawa yana jijjiga shi yayin da yaqoob ya zaro wayanshi ya kira doctor anwar shine ke duba shi a take yace gashinan zuwa kallonshi sagir yayi yace "me naji kake cewa?" Sadda kai yaqoob yayi yace "ba wai da gangan naki fadama ba yallabai ne yasa na dau alqawari bazan fadawa kowa ba" "me ke damunshi?" "Ciwon zuciya" dirsham sagir ya zauna se ga hawaye tausayin amininshi fal ranshi................


Adu'a yakeyi a zuciyarshi Allah ya ba haisam lafiya ya dubi marayan shi ya bashi farin ciki a rayuwa, kamashi sukayi suka mayar kan doguwar kujera har likitan ya zo duddubashi yayi tare da mishi wasu allurai ya sa mishi drip tukun ya dubi yaqoob yace "ya kamata ku dinga kiyayewa zuciyarshi ya kai matakin da ze iya bugawa a ko yaushe yana bukatan a fita dashi a mishi aiki"..............


Da toh kawai suka amsa ya musu sallama ya tafi su kuma suka sashi a gaba suna kallo..................


*************


Ta bangaren hamrah da kuka ta isa copa cabana hisham be zo ba zama tayi tayi ta kuka tana tuna cin mutuncin da haisam ya mata har taji tana son tada ciwonta tukun tayi shiru lokacin kuma hisham yazo a rude yake tambayanta me ke damunta shiru tayi kalamai ya fara mata me kwantar da hankali yace "hamrah da kin san irin son da nake miki da baki zauna kina kukan nan a gabana ba wlh kuka zanyi in baki dena zubar da hawayennan ba"....................


So? Dama ta zaci hk amma zuciyarta ba nashi bane kai bama na kowa bane ta san in har tana auren haisam to bata ba soyayya a duniya sede in ana yi lahira ko kuma ya saketa runtse ido tayi tace "Da ka zo lokacin da hamrah take hamrah tabbas da na karbi soyayyarka sbd ka cika duk wani mataki da nake so na namiji amma wannan hamrahn haisam ya nakasta rayuwarta ya saka ta yin sanyi ya sata sanin gaba da gabanta ya saka ta Rena kanta ya sata fahimtar ita ba kowa bace a duniya hisham Ina da aure".............


Kallonta kawai hisham keyi ba tare da ya yarda ba yace "waye mijin?" Cikin sanyi tace "haisam mas'ood sa'ood" a razane ya mike yace "what????? No inaaa baze yiwu ba" mikewa ita ma tayi tace "kayi hkr tun farko ya kamata na fadamaka" cewa yayi "ba komai ai aure ya wuce gaban wasa amma Dan Allah mu ajiye akan ban san kina da aure ba mu cigaba da abokantaka kamar da" ...................


Ji tayi hisham ya burgeta kai ta daga mishi tana murmushi yace "to bani labarin soyayyarku" tace "tab wani soyayya hmm bari na baka lbr" labarin komai ta bashi wadda bata taba ba ma kowa ba da ido kawai yake kallonta idonshi yayi jajazur tana dira abunda ya faru yau yace "wannan ai ba aure bane kuma ki tabbatar se na raba shi ko a dokar kasa zaki iya raba aurenan har musuluncin ma"...............


"To daddy na fa?" Murmushi yayi daga gani na mugunta ne yace "karki damu zamu samu mafita" jiki a sanyaye suka rabu she is not sure shawaranshin nan shine ya kamata tana shigowa gidan taga haisam akan kujera da drip a hannu su sagir sun tafi masallaci kafin su dawo su taimaka mishi yayi nashi ido suka had'a ba tare da ta nuna ta ganshi a halin rashin lafiya ba ta kau da kai ta wuce room dinta Sam kuma se be ji daadi ba................

#share

#vote

#comment


'Yar mutan Adamawa

💞💞💞

  


                  💞💞hamrah💞💞

                                                          💞💞


Writer: fateemah Muhammad 


Wattpad: muhdfatimagurin 
               *'yar mutan Adamawa*


Page➡1⃣1⃣

***************


Har zuciyanshi be ji daadin yadda tayin ba kofar d'akin ya tsurawa ido yana jiran ganin ko zata fito ai kuwa se gata ta chanza zuwa kamiso na kanti da d'an karamin hijab lura da tayi akwai maza a gidan, qasa qasa yake kallonta har zata wuce yace "ke!!!"................


Chak ta tsaya dama tana ta son yayi magana sbd ta tabbatar jikinshin da sauki ko babu, juyowa tayi se suka had'a ido da sauri ta dukar da kanta cikin kwa'ba fuska kaman be so yace "I thought you are sick? Ki bari za'ayi order" ba tare da tayi magana ba ta juya zata koma, haka kawai yaji yana son ta mai magana gyaran murya yayi, a hankali ta juyo kaman kuwa ta san abunda ke zuciyarshi tace..............


"Akwai abunda kake bukata ne?" Idonshi ya ware a kanta yana son ganin ko jikin yayi tsanani amma se yaganta normal d'ago ido tayi charab se a cikin lumsassun idanunshi da sauri ta shige d'akinta tana dafe kirji, me wannan? Meyasa zuciyata ke tsananta bugawa in yana magana? ( ni de nace hmmm).................


Ba tare da ta samu amsan tambayanta ba ta hau gado ta kwanta bata kara fita daga dakin ba har wuraren karfe 9 yunwa take ji amma bata son fita don tana jin muryoyinsu a parlor, ta bangarenshi kuwa tunda ta shiga hankalinshi gaba daya se ya koma kanta kar fa asthmanta ya tashi gata ita kad'ai a daki, haka kawai ya tsinci kanshi da tunanin me taci, ko tayi lunch? Yaqoob ya aika ya yo musu takeaway.................


A wani tsadadden restaurant ya saya musu, package 4 yace yayi duk da su uku yaqoob ya gani amma haka yayo, sagir ya shiga kitchen ya dauko musu plates da spoons yana mitan gidannan ya kara kyau da sheki se kace akwai mace a ciki, shiru haisam yayi ya manna mai a haka ya jujjuye musu yana tambayan "na hudun na waye?" Ba tare da haisam ya kalle shi ba yace "nawa"...............


Kallonshi sagir yayi da mamaki yace "kai kuma yaushe ka fara cinye rabin plate balle har biyu?" "Ina ruwanka?" Shiru sagir yayi ya dauki nashi ya koma gefe caccakan abincin kawai haisam ke yi ba tare da ya wani ci dayawa ba sbd yadda yaji taste din abincin Sam bai mishi ba, kuma fa kafin ya fara cin girkin hamrah abincin restaurant din was his best, Tsaki yayi tare da ture plate din ya kishingida da kujera tare da lumshe ido..................


Yaqoob na gama ci ya sheda musu private jet din haisam din is set, pilot din yace zasu iya tashi around 10am, sagir ne ya amsa, haisam kam ko bude ido be yi ba, yaqoob na kallon sagir ya dan shafa kanshi yace "madam na jira se da safenku" cikin dariya sagir yace "toh sannu me mata mu da bamu dashi sede mu rungumi pillow toh se da safe" dariya sukayi a tare banda haisam, ficewa yaqoob yayi sagir ma ya mike yana mitan................


"Matsalana da zama da kai kenan mutum ya zama kurman karfi da yaji Allah ya sa yau ne kadai da bansan yadda zanyiba gashi ba budurwa ne da ni ba balle a kashe min lokaci da Kalaman soyayya" har ya isa kofan daki ya juyo da sauri ya zauna kusa da haisam yana cewa "na tuna dan Allah haisam Ina maid din kannan, wlh Allah da gaske nake tayimin 100% a matsayin matar aure ni ko baza ka shigar da ni ba ka fadamin inda take plz".............


In dutse ya tanka toko haisam ya tanka daa fuskanshi a sake yake amma da sagir ya fara magnan hamrah se ya tamke ta sossai, da sagir yaga ba kulashi ze yi ba se ya mike ya shige daki yana me ci gaba da mitanshi, se da haisam yaga shiganshi kuma ya tabbata wanka ze yi tukun ya mike duk da jikinshi har yanzu ba wai yayi sauki sossai bane...............


A natse ya dauki one package na abincin ya nufi dakinta ba tare da wani tunani ba ya tura kofan dayake ba me kara bane Sam hankalinta be kai gurin ba, safa da marwa take sanye take cikin baby pink riga da be wuce cinyanta ba gashinta a baje har bayanta baki sidik, ba komai a fuskanta haka ba d'an kunne a kunnenta...............


Fatan jikinta se wani glowing yake gashi fari sol dashi, lumshe dara daran idanunshi yayi ya kara Ware su tar a kanta zuciyanshi na tsananta bugu jikinshi ya mutu murus, jingina yayi da jikin kofan tare da sa hannunshi daya a aljihu yyin da dayan ke rike da ledan abincin, harde kafanshi yayi tare da maida karfinshi kan kafa daya dama ba lafiya bane ya ishe shi gashi yana shirin jawa kanshi wani abun da kallonta amma baze iya dauke idanunshi daga kanta ba ba karamin kyau ta mishi ba kamar wata 'yar tsana................


A jikinta take jin ana kallonta kaman ance ta kalli kofa se kuwa suka had'a idanu kallon juna suka tsaya yi kaman kuma an mitsineta da sauri ta ja hijabin sallahnta dake kan gado ta rufa a jikinta, be ce komai ba ya warware kafanshi da ya harde ya fara takowa da d'ai d'ai da d'ai d'ai cikin izza da kasaita a hankali ta zame ta zauna bakin gado jin yadda kafanta ke rawa...............


Ya rasa dalilin da yasa yake kasa dauke ido a kanta kaman wani abu ne aka manna a jikinta yake Jan hankalinshi zuwa gareta a gabanta ya ajiye abincin ya juya ya fara takawa a hankali chak kuma ya tsaya tare da juyowa yana baza idanunshi a dakin kaman me neman wani abu a gefenta yaga abunda yake nema gurin ya nufa ko wani taku daya daidai yake da bugun zuciyarta tana jin kaman ze fado................ Har ganganta yazo ya duka sossai tare da sa hannu ta bayanta hancinshi na zukomishi kamshinta me sanyi da daadi kaman yadda itama kamshinshi da bata taba ji a jikin wani namiji ba bayan shi kai a duniya ma gabadaya duk ya buwayi hancinta, har tana tsoron kar yaji bugun zuciyanta remote na Ac ya dauka ya kashe tare da juyawa ya fice da remote din a hannunshi.......................


Baki ta tura tana kunkuni se taji ya kara tura kofar ya leko "kikace?" Zaro ido tayi da sauri tace "banfa ce komai ba" baki ya tabe yace cikin sanyin muryarshi da rashin lafiyan ya sake sanyayashi "gobe karki sake ki taka kofar dakinnan har se past 10" kai ta daga mishi a dake yace "words" tace "toh" fita yayi yaja kofan ya barta da tunani bata wani takura kanta ba ta jawo abincin ta fara ci ba tare da wani damuwa ba..................


Washegari da wuri ta tashi kaman yadda ta saba amma kuma se ta tuna abunda yace mata jiya samun guri tayi ta kira Ammah sbd taji ko sunyi magana da simra amma har yanzu shiru, wuraren takwas ta kira iyayenta a handsfree Dad ya sa duk basu riga sun fita ba tukun, hira suka sha sossai tayi sakewan da ta jima batayi dasu ba kusan 40mins suna waya kafin sukayi sallama...........


Wanka ta shiga tana fitowa ta tsinci kanta da sha'awar yin kwalliya zama tayi sossai ta tsara rantsatsen makeup Mara hayaniya sossai tayi kyau kaman ka sace ta ka gudu wardrobe ta zaro doguwar rigan atampha A shape yaji ado da stones ta zura dauri ta kafa irin na Zarah buhari ta gyara dakinta tsab ta saka turaren wuta ta koma gado ta kame ta fara danna waya..............


Yau asalin hamrahn ce a kanta, turo kofan taji anyi dago ido tayi suka kurawa juna ido ba karamin kyau yayi ba shima cikin dakakkiyar farar jumpa fara kal ya kafa hula har goshi fresh skin dinshi ya haska sossai kafanshi sanye da takalmin aldo daga gani yaji kudi, idonta ta dauke har ya shigo dakin sossai, kwalliyanta ba karamin tafiya da imaninshi yayi ba yana ji kaman duk yawon da yayi kasashe na duniya be taba ganin kyakyawa.....................


Wacce kuma shigar Hausa ya karba sossai kaman ita ba da kyar ya samu ya kau da kai jin tana gaisheshi bata sauka ba balle ta duka tace "ina kwana?" Bata zaci amsa ba se taji yace "lafiya" kaman baza su sake magana ba tace "ya jiki" yaji daadin yadda ta nuna damuwa akan ciwonshi shekaranjiya ya tuna yadda take ta kuka ya kuma tuna yadda ya mata da asthmanta ya tashi kaman baze amsa ba Chan kuma se yace "Alhamdulillah"........................


Paper ya ajiye mata a gefenta da mint na one thousand hundred thousand kenan ya juya ya fice bayanshi tabi da kallo shima se da yaje bakin kofa tukun ya juyo se suka hade ido da azama ya fice, ajiyan zuciya ta sauke ta jawo papern rubutunshi me kyau da tsari ta gani ya mata kyau sossai cewa yayi "na tafi kano ban san kwana nawa zanyi ba ga wannan in be isa ba you can contact me"....................


Kallon kudin tayi ta daga ta hada da papern ta bude bedside dinta ta zubasu mikewa tayi ta fita parlorn ta fara gyara tas ta gyara ko ina har dakinshi ta zuba turaren wuta, ta shiga kitchen ta dafa noodles ta dawo parlor ta zauna tana kallo tana ci...............


*************


Sun isa kano lafiya motocinshi ne manya guda uku suka daukoshi daga airport dayake gidanshi na kano ba filin saukan jirgi da tashinshi direct address din da aka rubuta sagir ya umarci drivern da zuwa dayake ya san kano sossai direct farawa yayi dasu can kasan unguwan ya tsaya yaqoob ne ya kira wani yaro ya tambaye shi gidan Malam isa nuna mishi akayi suka karasa................


Drivern ne yayi sallama aka amsa mishi wata mata ce ta fito bata fi shekaru 45 ba tana kallonshi, yaqoob da sagir ne suka fito uban gayyankam kallon unguwan yake cikin kyankyami da kyar ya fito ya nufe su yana jin maganan da matar ke fada ma su yaqoob cewa "ai malam isa dazun nan aka zo har gida da safen nan aka harbe shi har sau biyu yanzu haka yana aminu kano"..................


Yaqoob yace "subhanallah sun riga mu" sagir kuma cewa yake "innalillahi Allah yaja ranshi mujenku" haisam be ce komai ba ya fara taku jiki a sanyaye yana ji matar na fada musu room din da aka bashi, haisam gani yake kaman baze iya ba dafa shi sagir yayi yace " me yasa kake saurin karaya ne? Ina dakiya da jarumtarka yanzu ne ya kamata suyi aiki haisam haba mana".................


A sanyaye yace "baza ka gane raunin da zuciyata tayi ba, baza ka fahimci abunda nakeji ba sagir kenan sun rigamu wa ya fada musu? Bayan mu kadai muka san maganan zuwa kanon ma a sirrance muka tsara amma me ya faru? Kenan bibiyanmu sukeyi" kai sagir ya gyada ze yi magana kenan yaji an bangaje shi da karfi har seda ya kusa faduwa da sauri ya juyo...............


Wata mahaukaciya ce daga ka ganta zaka gane fara ce duk da dauda ya dukufar da hasken nata sanye cikin wani dogon riga da gani ya kusa shekara be ga ruwa ba gashinta dayawa amma ya dukunkune ya koma cus idanunta farare tas hannun haisam ta kama da hannu daya dayan kuma na kan kumatunshi hakoranta a washe cikin hausanta da be gama kwari ba tana yi tana hadawa da larabci tace...................


"Laaaaaaaaa ashe kana rayeeee baka mutu ba wayyo" se kuma ta sa tsalle tare da fashewa da dariya a lokaci daya kuma ta sa kuka, da sauri securities da suke tsaitsaiye su hudu suka matso da sauri zasu kai mata bugu da sauri haisam ya daga musu hannu kafin yayi magana wata buduruwa da zatayi 24 ta jaa matar tana cewa.............


"Dan Allah bawan Allah kayi hkr wlh bata hk bansan me yasa yau tayi ba" kai kawai haisam ya gyada mata yana kallonta cikin tausayawa kyakyawar yarinya amma ga yadda suke rayuwa kudi ya ciro da be san nawa ba ya ba buduruwan amsa tayi tayi mishi godiya ta juya kan matan tana cewa "mammi mu tafi"..............


Tirjewa mahaukaciyar ta fara tare da fashewa da kuka tana cewa "sake tafiya zakayi karka tafi ka barni ka dawo, dan Allah kar ka tafi" kuka sossai takeyi kaman ana zare ranta har haisam ya shiga mota yana kallonta cike da tausayawa har ranshi a haka suka fice suka barta tana rusa uban kuka............


Asibitin suka nufa suna zuwa suka samu gawan malam isa a lokacin ne ma ya tuna shi driver din da ya kawosu kano ne lokacin da aka kashe su Ammi, tuna abunda aka rubuta a papern yayi 'ya san komai' kenan da hadin bakinshi aka yi komai in ba hk ya za'ayi ya san komai kuma ya kawosu kano? Da wannan tunanin suka karasa gidanshi na kano bayan sun tsaya wani restaurant sunyo takeaway....................


Da dare suna zaune a parlor suna tattauna maganan sagir yace "amma wannan abun mamaki ne ina mu uku ne kadai muka san zancen nan se wadda ya kawo sakon?" Yaqoob yace "ko de wasa da hankalinmu suke sonyi?" Haisam yace "no I don't think so idan wasa da hankali da basuyi gangancin turo mana da voice recorder din nan ba"..............


Sagir yace "kuma haka ne fa" iskan ruwa aka fara me karfi da walkiya cikin jin daadin yanayin haisam ya lumshe ido haka kawai yake tunaninta ko me tayi duk yinin yau? Me taci tayi kukan da ta saba? Kwalliyanta na dazu kuwa na Zane fes a ranshi,  Tsintar muryan yaqoob yayi yana cewa "Allah de ya takaita mana wahala ya fiddo da gaskiya" suka ce Ameen a tare a take ruwa me karfi ya tsuge ruwan farko ne amma ya sauko da karfi da ni'ima me daadi kowa mikewa yayi ya nufi dakin da ko wannensu ya sauka dama dakin haisam kam na daban ne a kyau da tsari gabadaya gidan da dakunan ba wadda ya kai nashi kyau, sagir ma nashi daban hk yaqoob ma....................


Wanka yayi ya kwanta bayan ya bude winduna iska na daga labulayen ruwa na Dan fallatsowa favorite weather dinshi kenan, can cikin dare ya farka a firgice yana had'a zufa duk da ni'imar da ake ciki ruwan ya tsaya se iska me daadi amma shi gumi yake sharcewa "auzubillahi mina shaidanir rajeem" yake ta nanatawa a hankali ya samu natsuwa mafarkin kuma ya fara dawo mishi................

#vote

#share 

#comment
'Yar mutan Adamawa💞💞💞


                 💞💞hamrah💞💞


                                                        💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin               *'yar mutan Adamawa*


Page➡1⃣2⃣

************


Kasa tuna komai yayi a hankali ya sauko ya nufi toilet alwala yayi ya fito yayi nafila sossai ya kai kukanshi ga mahaliccinshi a natse ya mike ya koma gado ya kwanta amma se fir bacci ya ki idonshi juye juye yake cikin tunaninta da ya ki barin kwakwalwan shi ya rasa wani irin abu ne ke damunshi janyo wayanshi yayi kaman ya kirata se kuma yayi jifa da wayan a kan gadon ya ci gaba da juye juye da kyar ya samu bacci ya dauke shi.....................


Washegari wuraren 11 na safe yaqoob da haisam suka kama hanyan Abuja, sagir kuma ya nufi yola sbd aikinshi sun tattauna sossai akan zancen kisan su Ammi amma basu samu wani abun dafawa ba se recorder din nan sun tsayar akan zasu dogara da voice recorder dinnan, zasu samu ko wanne friend na Abba suyi recording voice dinshi se suxo suyi comparing............


Karfe 11:45 suka sauka a cikin gidanshi, ruwa sossai akeyi a Abuja sbd su Alhamdulillahi in ana damina suna samun ruwa sossai, motocinshi suka zo daukanshi don tazarar dake tsakanin filin tashi da saukar jirgin da kuma main house dinshi, zagaye shi securities din sukayi da lema har mota suma suka shishiga suka fara tafiya a hnkli don ba'a cika gudu dashi ba balle wannan ma da cikin gida ne....................


Kallon yadda ruwan ke sauka yake yi tare da tunanin yadda ze same ta shi kadai yake kiyasta yadda zatayi in ta ganshi, suna isa compound dinshi sukayi parking tare da fita da sauri suka baza mishi umbrella har kofan parlor yana shiga suka juya, a natse yake takawa har yakai dakinshi duk da yadda ya d'okantu da ganinta se be je dakinta ba don kawai ya jaa ajinshi a fad'arshi fa kenan...............


Yana shiga dakin ya lumshe shanyayyun idanunshi a hankali yana shakar kamshin dake tashi a cikin dakin, ya sha gyara sossai se kyalli yake, windows ya nufa yana kokarin budewa don ba ya taba rufe windows dinshi in ana ruwa ko da kuwa ruwan ze jika dakin ne yana son yaga ruwan na feshi har cikin dakin, kaman ance ya kalli kasa ganinta yayi tana wanka a cikin ruwa...............


Ido ya zaro cikin tashin hankali ya fita da sauri ya zagaya ta kofan baya, sanye take cikin short gown me siririn hannu ba dankwali a kanta ta baza gashi tana juyi a cikin ruwa sossai take son ruwa amma yanayin jikinta ba karamin wahala take sha ba in ta shiga shiyasa duk inda take in har an fara ruwa mom zata kirata ta sata a gaba har a gama ruwa, banda dare don tana tsoron ruwan dare................


Ji tayi an kira sunan ta cikin amo "haaamrahhh" a razane ta juyo se suka hade ido Sam bata zaci dawowarshi yau ba cikin tsoro ta fara ja baya bata yi taku uku ba ya cabki hannunta ya ja ta da karfi har cikin room dinta, sossai ranshi ya baci amma yanzu yana ga baze iya mata fada ba, a tsakiyar dakin ya saki hannunta ya fad'a toilet be kai 2mins ba ya fito...................


Toilet ya nuna mata da hannu jikinta har ya fara rawar sanyi da sauri ta fad'a sbd yadda rigar ya mammanne a jikinta gashi ya tsatsare ta da ido ta tabbatar magana yake jira ta mishi ya balbaleta don ta san a hasale yake, tana shiga ya saki tsaki ya nufi wardrobe dinta ya bude ya samo mata wasu sweater pink color riga da wando me taushi kaman auduga amma yana da dan nauyi ya ajiye akan gadon ya fice..................


Ta gama wankan da ruwan zaafi da ya had'a mata jikinta sossai ya dauki rawa, karamin towel ne kadai a toilet din dan haka bata da option than ta daura shi ta fito a kasalance ta fito tana jin zazzabi na nukurkusanta a natse take tafiya har zuwa gaban dressing mirror ta feshe jikinta da body's pray bayan ta goge ruwan ba tare da ta shafa mai ba har zata nufi wardrobe Dan nemo kaya se taga wadda ya ajiye mata d'auka tayi ta saka a jikinta ai kuwa tana gama sakawa se taji ya turo kofa ya shigo kai ta dukar tare da zamewa ta kwanta kan gado................


A natse ya karaso bakin gadon ya saka hannunshi a goshinta ai kuwa abunda be so din bne ya kamata zazzabi me zafi numfashinta ya sauya salon fitowa   tea ne a hannunshi da wasu magunguna da bata san inda ya samo su ba, "sit up" a hankali ta mike ta zauna mika mata cup din yayi ta dan sha tukun ya bata magani ta hadiya duk abunda take idonshi kur a kanta kaman wadda ya samu tv shi ma ta bangarenshi rasa dalilin da baya gajiya da kallonta yayi.................


Karban empty cup din yayi ya mike ita kuma ta gyara ta kwanta da kanshi ya sa mata bargo tare da ficewa daga dakin, wanka yayi ya saka kaya marasa nauyi tare da haurawa gadonshi yayi ya kwanta yana son rintsawa kafin azahar sede me? Sam bacci yaki idonshi tunani yake ko da sauki jikin nata ya san for sure se ta samu attack tsam ya sauka daga gadon ya nufi room dinta...................


Yana tura kofan dakin yaji tana Jan numfashi da karfi da mugun sauri ya karasa gadon dama ya riqo inhaler da sauri ya shaka mata tare da toshe hancinta kaman zata shide haka take yi, ajiye inhaler din yayi ya fara danna mata kirji ya danna sossai tukun ya dauki inhalern ya kara shaka mata ajiyar zuciya me karfi ta sauke se kuma ta fashe mishi da kuka kallonta ya tsaya yi da mamaki...................


Da yaga da gaske kukan zatayi tayi in be dakatar da ita ba yasa shi daka mata tsawa "will you shut up!!!!!!! Kina hauka ne dama zaki shiga ruwa? Akwai wadda ya aike ki? In kika kara budemin baki anan se na tsitsinka miki mari" tsit tayi dama tasani ba sonta yake yi ba, ko dan tausaya mata bayayi da hisham ne ta tabbatar da yanzu ya gama rudewa..........................


Tana cikin tunanin taji ya jata faffad'ar kirjinshi ya rungume ta tsam tare da kwanciya sossai ya ja musu bargo shi a ganinshi taimakonta yayi don taji dumi amma ita kuma tunani take yaushe ya zama dan iska, shiru kowa yayi yana tunani a hk bacci ya kwashesu, abunda be taba yi ba mafarki da rana, mafarki yayi mahaukaciyar nan ta jiya tana ta binshi a baya tana kuka tana kiranshi ya tsaya...............


Kin tsayawa yayi yana ta tafiya ita kuma taki dena binshi har ya isa gaban wani tafkeken rami wuta ke ci Bal bal sossai a ciki juyawa yayi yana kallonta se yaji an jashi zuwa wutan nan har a jikinshi yaji tururin wutan da azama ya farka sede tunawa da tana jikinshi yasa shi fara adu'a a hankali har ya samu natsuwa jikinta ya taba yaji zazzabin ya sauka kallon fuskanta yayi yaga yadda take bacci tayi mishi kyau ba kadan ba hancinta gabadaya ya toshe da mura bakinta is slightly open dashi take numfashi..............


Jawo wayanshi yayi yaga almost two gashi basuyi azahar ba daukarta hoto yayi kafin ya zamar da ita zuwa gadon ya mike ya fice don gabatar da sallah, bayan ya idar ya kira yaqoob ya bashi sakon yin musu ordering abinci, fitowa yayi ya koma dakinta don tashinta se yaga ta tashi tana tsaye a gaban gadon da waya a kunnenta magana takeyi cikin sanyin murya "kar ka damu ba wani worst yayi ba" be ji me aka ce ba yadega tana murmushi sossai wadda be taba gani a  fuskanta ba da wa take waya?............


Ya tambayi kanshi ji yayi ta kara cewa "Allah kuwa, muhadu gobe in Allah ya kaimu a inda muka saba haduwa" tana murmushi ta sake cewa "Allah ya kaimu" tana dago ido ya fadi cikin nashi kau da kai tayi ta nufi sallaya ta tada sallah shi kuma ya koma daga inda ya fito yana jin ranshi na suya.............


Yana zama kuma tunanin mahaukaciyar nan ya fado mishi, shi kam ya rasa dalilin wannan mafarki ko de mayya ce? Se kuma yace no batayi kama da su ba wani zuciyar yace to kasan su mayun ne? Tunaninshi ne ya katse jin sallaman yaqoob amsa mishi yayi ya shigo ya mika mishi ledan godiya yama yaqoob din kafin ya tafi daya ya kai mata shi tare da dawowa ya fara cin nashi......................

*kuyi hkr wlh na gaji ne da kyar na samu nayi wannan kuyi manage zuwa gobe In mai duka ya kaimu*
'Yar mutan Adamawa


💞💞💞


                    💞💞hamrah💞💞

                  💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin 


Page➡1⃣3⃣

**********


Yinin ranar gabadaya yayi ne a kula da ita duk da yadda wayanta ya tsaya mishi sossai a rai, magana be kara hadasu ba har dare bayan ya tabbatar tayi bacci tukun ya wuce dakinshi waya ya dauka ya kira Alhj mudan "salamu Alaikum an yini lafiya?" Da mamaki Alhj mudan ya kara duba caller Id dinshi tabbas haisam ne yau haisam ke gaisheshi?.................


Da dan rashin gaskiya yace "waslm lfy klau ya iyali" runtse ido haisam yayi tabbas akwai muryan Alhj mudan don be taba mai da hankali akan maganan shi bane yasa da yaji voice recorder din be gane ba, me Abba ya musu mai zafi hk? Akan kudi? Wani irin tsanan Alhj mudan ne ya dirar mishi fiye da baya ba tare da ya kara magana ba ya kashe wayan................


Kiran Alhj halliru yayi shima kamar yadda ya ma Alhj mudan haka ya mishi, tabbas shima akwai muryanshi tar a ciki, a zuciye ya kira Dr zubair shima akwai muryanshi d'ayan muryan ne ya kasa samu ya kira abokan baban nashi kusan biyar duk be ji dayan muryar ba daga baya hakura yayi yayi nafilfilin shi ya kwanta................


************


Ta bangaren su Alhj mudan a take suka hada meeting a daren, a rude suka hadu a wani tangamemen gida da yaji kayan duniya a wani babban parlor suka zazzauna sun kai mintuna 10 da zama kowa yayi shiru tunanin abun duniya ya ishe su suna tsoron Allah suna tsoron tonuwar asirin su..............


Wani babban mutum ne kusan sa'anninsu ya fito sanye da suit bakake ya saka hulan tabani kaji hadisi a kanshi tare da face mask a fuskanshi idonshi da girarshi kadai ake gani a tare suka mike gabadayansu seda ya zauna tukun suma suka zazzauna, "me yake faruwa ne? Bad news" Ya tambaya..............


Dr zubair ne ya fara magana kamar haka "boss yaron nan ne yake son zame mana barazana, bamu da masaniyar wa ya kai mishi voice recorder a takaice ma a lokacin da mukayi maganan ma iya mu hudu ne ya akayi recorder ya fito bamu sani ba, last two days kenan ya kira abokinshi wani soja da secretary dinshi yaron nan da suka tashi tare ya musu bayani a cikin jakan da aka kai mishi recorder din akwai paper rubuce da suna da address din drivern da ya tayamu aiki....................


Sunyi shawarar zuwa washegari a jiya kenan su ziyarci malam isa amma se muka rigasu muka tura aka kashe shi sunje sun Tarar da gawanshi" Alhj mudan ne ya daura da "se yau a dazu ya kira mu daya bayan daya da alamu so yake yaji muryar da yayi kama da na recorder din da alamu kuma ya gane"...................


Shiru wadda akewa bayanin yayi na kusan minti daya tukun yace "good news" Alhj halliru yace "yaron na dauke da ciwon zuciya bamu sani ba se shekaran jiya" wani irin dariya mutumin ya fara babbakawa har na kusan mintuna biyu tukun yayi shiru yana kallonsu se yake sukeyi............


A gadarance yace "in ya san wata be san wata ba kar ku damu I will handle him ubanshi ma yayi ya gama balle yaron da aka Haifa a gabanmu? Ku tashi kuje ku barmin komai" mikewa sukayi suna godiya kaman aljannah ya basu suka fice................


************

Washegari ta tashi jikin da sauki se mura da take yi sossai, shiryawa tayi ta fita ta fara aikinta cikin natsuwa, bata wani bata lokaci ba ta gama hada mishi yam balls da Irish potage da yaji  veggies da hanta ta shirya komai a dining ta gyara parlorn tas ta saka turaren wuta, dakinshi ta shiga yana nade akan gado yana bacci kallon fuskanshi tayi da ya fita tar a hasken rana daya taso ta windownshi............


Yayi kyau sossai kaman ba bacci yakeyi ba kafa mishi ido tayi tana morewa kallonshi gaskiya kyakyawa ne ya tserewa hisham sossai abunda kawai hisham ze nuna mishi shine hasken fata, amma fatan haisam me tsada ne don d'ai-d'ai kune masu irin fatan, tana cikin kallonshi tana kiyasta komai na fuskanshi ya bude ido tar a cikin nata.................


Zaro ido tayi ganin ya kamata tana kallonshi da sauri ta fad'a toilet dinshi, sossai yadda tayin ya bashi dariya sossai har be san sadda murmushi ya subuce mishi, hannu ya sa ya dafe bakinshi da sauri ya dira daga kan gadon ya isa gaban madubi kallon fuskanshi yayi yana dafe da baki 'did I just smile?'...................


Wani murmushin yake son sakewa amma ya kasa a haka ta fito ta same shi ba tare da ya kalle ta ba ya fad'a toilet din haka kawai ya tuna wayanta na jiya se yaji ranshi ya baci, da kallo ta bishi har ya shige jiki a sanyaye ta fara gyara dakin a natse har ta gama ta fiddo mishi suit dark blue da white shirt ta ajiye a bakin gado ta samo mishi cover me kyau da sheki baki ta ajiye a gefe ta fita................


Bayan ya fito a natse ya fara shiri yana kallon dakin, se da ya gama shafe shafe kaman mace ya gyara gashin kanshi se sheki yake ya feshe jikinshi da turaruka kala kala da baza ka tantance kamshi guda da yake yi ba karar shigowar sako yaji a wayanshi be bi takai ba seda ya sa kaya ya dauka yana budewa yana tafiya chak ya tsaya yana kara karanta saqon...............


"Yaro ya girma kenan, yaro man kaza ka kiyayeni don ko ni Karan kaina tsoron kaina nake, ka ajiye binciken da ka faran nan in ba haka ba se na tabbatar na saka a ramin da baza ka iya fitowa ba, karka ga kana da kudi ka zata kana da komai ko don ka san mutane kayi tunanin za'a taimaka maka, kayi na farko kayi na karshe shine zuwa kano, in kaki kuwa jiki magayi se na tabbatar na karasaka kaji da ciwon zuciyarka"..................


Kallon numbern yayi yaga an boye, kanshi ya dafe yana tunanin waye ne a cikinsu? Ya akayi suka san yana da ciwon zuciya? Ze iya kirga mutanen da suka sani daga sagir, yaqoob se doctor anwar se kuma hamrah ita dinma bata san ciwon dake damunshi ba, daga sagir har yaqoob ya san ko za'a kashe su baza su fada ba, dr anwar ma ya san zai iya rike mishi sirri daidai gwargwado..................


Da wannan tunani ya isa dining dama tana zaune a parlor ganin ya zauna yasa ta karasawa tayi serving dinshi tana lura da yanayin shi kaman ranshi a jagule yake a haka ta gama ta ja baya zata juya taji yace "sit" juyowa tayi tana kallonshi bata tabbatar ko haka taji ba bata son zama ya dizga ta, kallonta yayi da ido ya kara mata alama zama tayi yace "serve ur self"..............


Serving tayi ta fara cakala abincin sam bata jin daadi a takure take duk da ba kallonta yake ba amma ta kasa sakewa be wani ci dayawa ba sbd tunanin da yakeyi na wannan text da aka turo mai, mikewa yayi ya fita daga shi se wayoyinshi, yana gangarawa ya kira yaqoob ya mika mishi wayan da sms din ke ciki, da dayan wayanshi ya kira sagir ya fad'a mishi sakon magana sukayi sossai tukun sukayi sallama yaqoob yace ..................


"Kar de mu sawa kanmu zargin juna wlh bazan iya maka hk ba" hararranshi haisam yayi yace "ko zan zargi kowa a duniyan nan bazan iya zarginka ba yaqoob ka manta kaine kadai Dan uwa kuma kanina a duniyan nan?" Shiru yaqoob yayi abun ya fara bashi tsoro, sam be fatan Allah ya nuna mishi randa wani abu da ze hada su da haisam dafa shi haisam yayi suka had'a ido girgiza mishi kai haisam yayi tukun yayi Kiran Adamu..................


Yana karasowa ya duka har kasa yana mika gaisuwa hannu kawai haisam ya daga mai yace "ina da ina kake kaita?" Hade rai haisam yayi yadda ma baze iya mishi karya ba, ba tare da Adamu ya nuna wani reaction ba sbd gaskiya ze fada yace "copa cabana garden kawai muke zuwa" yace "kana tafiya ka barta" Adamu yace "a'a sau daya kawai tace naje na dawo amma tun daga nan kullum zan jirata har ta gama mu dawo".................


"Wa take gani?" Yace "wani ne ban de sanshi ba" wani numfashi haisam ya ajiye jin hakan ranshi na wani iri nufan motocinshi yayi har ze shiga yace "idan zaku ka kirani" Da "to maigida" ya amsa haisam ya shige mota aka rufe suka fice daga gidan...............


Bayan ta gama girkin rana tsab ta shirya a dining ta shiga tayi wanka ta shirya cikin borno style me kyau straight skirt ne me tsagu dan daidai da rigan ya wuce guiwa sossai atamphan ya amshi jikinta babban gyale ta dauka ta yane kanta dashi ba tare da ta daura dankwalin ba wayanta kawai ta dauka ta fice................


Suna fita taji drivern yayi waya yana cewa eh mun fita toh yallabai haka taji yace bata kawo komai a ranta ba har suka isa shiga ciki tayi inda suka saba zama ta zauna kusan 5mins bata ganshi ba waya ta fiddo ta kirashi yana dagawa taji yana wani nishi kaman wadda ze mutu a rude tace "lafiya hisham me ke damunka?" Cikin yanayi na rashin lafiya yace "ban da lafiya hamrah bana tunanin zan kara minti ashirin a duniya ki taimaka kizo".................


Tace "haba haisam ya zaayi na je gidanku" ji tayi yana cewa "mom ki tayani rokonta plz" da sauri Tace "naji zanzo base ka hadani da iyayenka ba" mikewa tayi ta fito tana tambayarshi unguwansu yana mata kwatance har ta isa mota shiga tayi tre da fadawa drivern inda ze kaita............


Ta bangaren haisam tunda drivern ya fada mishi sun fito shima ya fito daga office dinshi securities dinshi suka tattaso hannu ya daga musu ya mika hannu akan a bashi key mika mishi sukayi suna mamakin ina yallabai ze je shi kadai gashi ya aiki yaqoob, shima da gangan ya aikeshi don yasan in yana nan baze taba barinshi fita shi kadai ba.................


Yana biye da su yaga sun nufi wani sabon unguwa da ba wasu mutanen kirki a baya ya ringa binsu har suka tsaya a kofar wani gida madaidaici amma ya tsaru yana gani ta fita ta kwankwasa me gadin ne ya leko ganin macece yasa ya wangale mata get ta shige be damu ba sbd ya San yadda mata suke zuwa gidan...............


Tana shigewa haisam ya fara duba time be san ko gidan yan uwanta bane har five minutes be ga fitowanta ba fita yayi ya nufi gidan ya kwankwasa me gadin ya leko suka gaisa haisam yace "am dan Allah nan gidan na waye ne? Akwai mata ciki?" Mai gadin kaman jira yake ya fara bayani "hmmm nan gidan gidan d'an Alhj Murtala mai dala ne wlh yaron abunda yaga dama yakeyi yanzu gidan nan yadda ake zina a cikinta na tabbatar idan Allah ya tashi saukar da azabarshi baze yi kyau ba mata na safe daban na rana daban na dare daban don nima bani da yadda zanyi ne nake zaune anan...............


Cikin tashin hankali haisam yace "Wannan da ta shiga yanzu fa?" Yace "ita kam ban taba ganinta ba gata tayi shiga irin na mutunci bata ma yi kala da irin matan da suke zuwa nan ba" da sauri haisam ya ciro cati ya mika mishi yana cewa "ka sameni da wannan address din in ka isa ka kira numbern jiki" be jira me ze ce ba ya nufi ciki daga nesa ya kalli wani saurayi na rufe kofar parlorn ta waje da key..............


Labewa yayi da yake gidan akwai yalwan flowers masu tsai saurayin be ganshi ba har seda yazo kusa hannu haisam ya kai mishi take hancinshi ya fashe ze yi magna haisam ya kara mishi jiri yaron ya fara gani kafin yayi magana ya zube janshi haisam yayi zuwa bayan wani flower ya ajiye tare da lalubarshi ya dauki key..............


A ciki kuwa tana shiga taga wani saurayi tsaye a parlor gaishe shi tayi tana kalle kalle amsawa yayi ta tambaye shi "matar gidan fa" don ta fara tsorata taji unguwan shiru ga gidan kaman ba wasu mutane cewa yayi "tana ciki" dakin ya nuna mata ta sa kai zuwa ciki tana shiga ta samu hisham daga shi se gajeren wando da vest kwance akan gado...............


Zaro ido tayi ta juya zata fita se taji an datse kofar tare da saka mata key cikin tashin hankali ta juyo tana kallon hisham tace "me haka me kake yin nan" dariya yayi yana cewa "daidai kenan na san in ba haka nayi ba baza ki zo ba" mikewa yayi ya nufi fridge ya dauko five alive ya bude ya tsiyaya a cup yana mika mata .................


Girgiza kai tana hawaye har ya fara cika idanunta tace "menene dalilinka na rufe ni anan Dan Allah ka bude min in tafi ina da aure fa kark manta" dariya ya fashe dashi kafin yace "kina wasa da hisham murtala mai dala" tace "kace sunanka hisham Nasir" wani dariyr yayi yace "tun randa na fara ganinki sha'awarki ta mun mummunan kamu na so naje miki da soyayya in kin amince daga baya na yaudare ki ki bani kanki se kika zo min da mummunan magana................


Kin kuwa san waye haisam a wuri na? Kin kuwa san yadda na tsane shi balle wani abu da ya shafi nashi? Na yanke hukuncin ke ta miki haddi ne ta karfi da yaji ta yadda har se kinyi wattanni kina jinya yadda mijinkin ze kara tsanarki duk da nasan ke kina sonshi" girgiza kai ta fara hawaye na zuba take cewa "kar ka min haka na roke ka da girman Allah"............


Dariya yakeyi yana matsota tare da fizge gyalen jikinta yana cewa "a labarin da kika bani har yanzu ke virgin ce so I want to disvirgin you se in bar mishi saura na" kankame jikinta tayi tana kuka sossai tana adu'ar Allah ya kawo mata dauki da gini ya hadata ya matse tare da warware gashin kanta yasa a hancinshi yana shakar kamshin tureshi ta farayi da hannayenta.............


Had'a hannun yayi duk biyu ya lankwasa su baya ya matse har seda tayi kara a take fuskanta yayi jaa dama ga mura tanayi hannu daya ya saka yana zuje zip din riganta da karfi ta matsa har seda ta kubce ta sa gudu zuwa kofa kafin ta kai ya harde ta ta fad'i kasa daga ta yayi cak ya daura ta gado kafin ta dago ya hau ya danne ta ya sa hannu ya yage rigar har cikinta............


Harshe ya saka yana lasan daga wuyanta zuwa kan kirjinta yana ganin yadda breast dinta ya ciko brazier dinta har tunani yake yadda ze yi dasu jujjuya kai kawai take tana kuka sossai tana kuma adu'ar Allah ya kawo mata dauki ji tayi an banko kofar an shigo a zafafe hisham ya dago ze fara masifa se suka had'a ido da haisam ganin halin da suke ciki yasa haisam karasowa da hanzari ya sa hannu ya pinciko hisham daga kanta ya kai mishi wani wawan naushi a hanci kafin hisham yayi wani yunkuri ya sake kai mishi wani muryarshi na rawa yace "how dare you?" Da tsawa ya kara cewa "how dare you........." maganar ce ta makale ya kara kai mishi wani naushin..............


Hisham ya fara jin bugu a take shima ya kai hannu ze rama cikin zafin nama haisam ya kauce dambe ne ya kaure da yake hisham dinma ba laifi kirar karfi ne dashi da sauri ta mike ta jawo gyalenta ta rufe jikinta se rawa jikinta keyi kallon yadda suke fada takeyi duk da har lokacin hisham be samu haisam ko daya ba shi kuwa haisam ya mishi jini da majina duka sossai haisam ya ma hisham har seda yaga ya dena numfashi duk da haka be bar dukanshi ba seda ta taso cikin tsoro kar ya aikata kisa ta kama hannunshi cikin zafin nama ya juyo itama ya kifa Mata mari da har saida numfashin ta ya dauke na wucin gadi kafin ta dawo hankalinta y fisge ta suka nufi waje.....................

#vote

#share

#comment
'Yar mutan Adamawa


💞💞💞

                      💞💞hamrah💞💞
 

                                                    💞💞


           


Writer:fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin 
            *'yar mutan Adamawa*Page➡1⃣4⃣

**************


A zafafe yake Jan hannunta dayan hannun nata take sawa tana gyara gyalenta dake ta zamewa ga riganta a yage a haka suka isa motanshi bude gaba yayi ya jefa ta tare da buga kofan zagayawa yayi ya shiga mazaunin driver ya fada tare da fisgan motan ko takan drivern da ya kawo ta be bi ba...................


Takure kanta tayi a tsakanin cinyoyinta tana kuka sossai kuka me ta'ba zuciya tana Danasanin sanin hisham a rayuwarta wani irin tsanarshi ne ke dirar mata, a lokaci daya kuma wani irin tsoron haisam ne ya kara shigarta akan na da, fargaban irin hukuncin daze dauka akanta takeyi a lokaci daya kuma tana tuna irin dukan da yayiwa hisham.................


Bata gama tunani ba taji yayi parking motar bata dago ba balle tayi tunanin sauka ji tayi an balle marfin motar ya kara Jan hannunta daga kanta ke da wuya ta gansu a wani gida da ba wadda take ciki ba tsoronta ne ya karu ya ilahi ina ya kawo ta bata kara rudewa ba seda taga gidan ba kowa shi yasa key ya bude ya kara rufewa ta ciki suka nufi main parlor na gidan nan ma budewa yayi suka shiga ya kara rufewa...............


Cikin tsoro take cewa "ina ka kawo ni? Ina ne nan dan girman Allah kayi hkr wlh bazan kara ba" ko kulata be yi ba seda ya danganata da bedroom na gidan ya hurgata kan gadon ba ta yadda zata ji ciwo ba fuskan nan a murtuke yace cikin dakakkiyar muryarshi da ya hadu da bacin rai "abunda kike so kenan yasa kika je gidan shi? Me yasa baki tambaya na baki ba? How could you....." 


Maganan makale mishi yake image din yadda hisham ke kwance a kanta yake dawo mishi, gani yake In ya bar hisham a haka ya ga banza dole ze dauki mataki, girgiza mishi kai kawai take tana son kare kanta kafin tayi wani magana taga yana kwance belt na wandonshi, zaro ido tayi a mugun tsorace muryanta a rarrabe take cewa "dan Allah kayi hkr ka rufamin asiri kar kayi min komai plz"..............


Be kula ta ba seda ya saura daga shi se boxers a tsorace ta koma karshen gadon ta duka a kan gwiwowinta ta hada hannunta tana girgiza mishi kai, sossai ta bashi tausayi wani irin abu me daci yake ji in ya ganta haka, tuna abunda hisham ya so mata yayi da be bisu bafa? Da Allah be kaddara ze je bafa? He can't even imagine what will happen to her..............


Amma ya zama dole ya koya mata hankali ya zama dole ya tsoratata yadda gobe baza ta sake sha'awar sauraran wani namiji ba har ta kai ga kulla abota da shi, gudun zargi  ya sashi tsayawa yaji duk abunda hisham din ke gayamata anan yaji duk abunda ya faru, shiyasa ya zabi hanyar nan don hukuntata, amma da gaske tana sonshi?............,,.


Kau da zancen yayi ya haye gadon tsoron yanayin ginannen jikinshi ya kara shigarta fisgota yayi ya hau kanta ya sauke mata nauyinshi yana kallon tsakiyar kwayar idonta karara yana karantar tsoron da ke ciki hakan se ya kara mata kyau girgiza mishi kai kawai take ta bude baki da niyyar magana kenan ya hade bakinsu ya fara sarrafata da zafi zafi.................


Jikinta gabadaya ya dauki rawa ta fara mishi magiyar ya taimaka ya kyale ta wlh ba haka take so ba wlh Allah baza ma ta kara fita daga gida ba basu yi hk ba Dan Allah kar yayi a dabarance ya rabata da riga da kuma bra dake jikinta zafi zafi yake komai jin ya fincike zanin jikinta yasa ta Jan wani mugun numfashi chak ya dauke ta sume mishi..............


A hankali ya janye yana kare mata kallo sossai yanayinshi ya sauya idanunshi sun sauya kala, sossai moment din da sukayi having ya rage mishi zafin da zuciyarshi keyi, dama dan ya tsoratata yayi hakan amma kaman shi yake shirin hukunta kanshi, toilet ya fad'a ya dibo ruwa a wani bowl karami ya zo ya hau kan gadon dago kanta yayi yana karewa jikinta kallo................


Da sauri ya kuma dauke idanunshi ya fara shafa mata ruwan a hankali ta fara sauke ajiyar zuciya numfashinta yana sauka cikin sanyi tana gama dawowa hankalinta ta sa mishi kuka tare da saurin fadawa jikinshi ta kankame shi gashin kanta ya fara shafawa a hankali ta kara shigewa jikinshi sossai take a rude a kuma tsorace har hanzu a haka bacci ya kwashe ta a hankali ya kwantar da ita ya ja zaninta ya lulluba mata................


Kayanshi yasa ya fice daga gidan kusan 40mims tukun ya dawo da wani kayan daban a jikinshi shirt da wando duk farare da leda a hannunshi me tambarin gidan abinci da kuma wani daban, kallonta yayi yaga har yanzu bacci take ajiye ledojin yayi tare da fara bubbuga gefen gadon a hankali ta bude idanunta da suke cike da bacci ta zuba mishi su hade rai yayi ya kauda kai a hankali ta mike tana gyara zanin jikinta................


Da kyar yace "ki shiga ki watsa ruwa karki bata min lokaci" cikin sanyi kaman ba ita ba ta sauka ta nufi toilet din da ido ya bita idonshi na kallon kofar har ta fito be dauke ba yana kallonta ita kuma tana kallon kasa magana take son yi akan kayan da zata sa fa amma yanzu wani irin tsoron shi take...............


Da ta gaji ne ta dago a hankali ta kalleshi se suka hada ido shagwabe fuska tayi kaman yadda takewa mom in tayi laifi, ta kusa sashi murmushi amma se ya maze ya nuna mata ledan da hannu dauka tayi ta zura jallabiyan a kunyace yau ne ta fara saka kaya a gaban namiji abincin ya nuna mata ta dauka shima ta bude bata wani ci na kirki ba ta ajiye mikewa yayi itama ta mike tare da yana gyalen rigar a kanta suka fito tana binshi a baya, zaman kurame sukayi har gida ba wadda yace uffan yana parking ta sauka ta shige..................


************

Bayan sati 


Tunda abun ya faru se ya fita harkanta kwata kwata kaman fushi yake da ita, Sam abun be mata daadi yadda ko ta gaishe shi baya amsawa ba kaman kwanaki da yake gyad'a mata kai ba abincinma ba wani sossai yake ci ba, ita damuwanta kar fa ace zarginta yake yi, hk zata shiga daki taci kukanta wani lokacin yana sane hk ze ba banza ajiyarta duk kuwa da yadda zuciyarshi ke azalzalar shi gareta.............


Ta bangare daya kuma kullum se yayi mafarkin mahaukaciyar nan tana binshi tana kuka ya rasa dalilin wannan abu a haka tafiya ta kamashi zuwa kano ko fad'a mata be yi ba yadda yayi kwanaki sede kawai ta dena ganinshi, datayi abinci taga be ci ba tayi ta jiran shigowarshi be shigo ba har tayi bacci a parlorn...............


Da sassafe ta shiga dakinshi baya nan kenan be kwana a gd ba? Ta tambayi kanta don yadda ta barshi jiya hk ta ganshi yau tana son kiranshi kuma tana shakka hk ta hkr tayi breakfast kadan ta ci ta koma daki gashi hadari ya hadu alamun ruwa za'ayi kwanciya tayi bayan ta rufe ko ina ita ba bacci ba ita ba ido biyu ba..................


Yana kwance a gidanshi na kano duk tunaninta ya cika shi abunda ya zo yin ma be yi ba ya rasa dalilin wannan tunani abunda ko za'a kashe shi da be san ya zauna yayi ta tunani akan mace ba, ya rasa me yasa yake ganin kaman be kyauta mata ba har laifinshi na aurenta duk se yanzu yake gani, ga yadda ya takura rayuwarta komai dawowa mishi yake daki daki duk a abun kuma yafi ganin tsantsar wautarshi da be yi tunani me kyau ba kira ne ya shigo wayanshi..............


Kaman baze daga ba kuma se ya dauka ganin daya daga cikin securities dinshi na Abuja ne da yake ba musulmi bane cewa kawai yayi "yes??" Securityn yace "sir it's raining here at abuja" da "ohk" haisam ya amsa tare da kashe wayan da sauri yana danna number dinta dama shi yace in ana ruwa a abuja su fada mishi ..............


Tana nan kwance tana jin yadda ruwan ke saukowa amma bata motsa ba dama batayi niyyar shiga ba Karan wayanta taji a sanyaye ta dauka ta duba "Arrogant H" ta gani Zaro ido tayi ta daga ganin ya kusa tsinkewa a kunnenta ta saka cikin yanayin sanyin muryanta tace "assalamu alaikum" 

seda ya lumshe ido tsabar yadda muryan yayi tasiri a gangar jikinshi a hankali shima yace "wa'alaikissalam"..................


"Ina kwana" be amsa ba yace "hope baki shiga ruwa ba" tace "eh" kaman baze sake magna ba Chan kuma se yace "in kin ga dama ki shiga bana kusa bare na taimaka miki" bata ce komai ba sukayi shiru duk Chan kuma se ya kashe wayan yana runtse ido wai me ke damunshi ne??? Abunda har yanzu ya kasa ba kanshi amsa amma ze tambayi yaqoob..................


Ta bangarenta kuwa murmushi ta sake tana rungume pillow ko ba komai ta san ya damu da ita amma me yasa take jin daadi don ya damu da ita? Tabe baki tayi tana cewa a fili koma me nene ta san taji daadi...............


Bayan yayi wanka ya shirya cikin three pieces suit maroon da ya dan ciza se white shirt bakin sau ciki ne a kafanshi yayi kyau sossai se tashin kamshi yake yi a natse ya fito sukayi breakfast duk da shi ruwan zafi kawai ya sha suka wuce HMS orphanage foundation dake nan kano.................


Bayan ya gama duk abunda yake ya duba yanayin komai yadda ke tafiya tare da tabbatar da ba wani matsala tukun ya musu sallama ya fice a daidai bakin gate yaga wata kamar matan nan drivern ya dakatar tare da tsayawa kallonta tabbas itace se kuka takeyi 'yarta na zaune ta zuba tagumi a gabanta.................


A hankali ya bude kofar ya sauko bakinshi dauke da adu'a ai kuwa kaman ance mahaukaciyar ta daga kai tana ganinshi ta taso da gudu tana dariya fad'awa jikinshi tayi niyyar yi da sauri ya rike hannunta tare da dakatar da ita tausayin ta fal ranshi gani yake kaman taimako take bukata shi yasa take zuwa mishi ko Allah ne ya hadasu don ya taimaka mata ................


Buduruwar ce ta taso ta zo kusa dashi cikin sanyi tace "na rasa ya zanyi da ita tundaga randa ka tafi kullum se tayi ta kuka da kyar take cin abinci in na samo mana" kallon ta yayi ya kara maida kallonshi ga matar yace "ya sunanki?" Tace "qudratullah" ya lura ba laifi yarinyar na da natsuwa duk da yadda yaga suke rayuwa a titi "daga Ina kuke? Ina family dinku" tace "na tashi na ganmu a gidan wani bayarbe daga baya matarshi ta kore mu daga nan a bola muke rayuwa"..................


"Ya salaam zaku iya bina?" A tsorace take kallonshi don an sha kawo musu hari Allah na kare su daga 'yan iska manyan 'yan siyasa dake son mulki bokansu yace su yima mahaukaciya fyade, se masu satan mutane duk ba wadda basu gani ba amma Allah ya kiyaye su, amma daga gani wannan be yi kama da mugaye ba duk da be dariya...............


Fahimtar haka yasa haisam yace "ni musulmi ne dan uwanki ban taba cutar wani ba kuma bana fatan farawa a kanku bazan boye miki ba tunda na tafi nake mafarki da mahaifiyarki tana kuka ban sani ba ko ta sanadiyata ta samu lafiya" Yaqoob yace "in batason taimakon mu tafi ana jira a company" sakin hannunta haisam ke shirin yi ai kuwa ta kankame sossai ta kara sa wani kukan  a hankali qudra tace "zamu bika kaji tsoron Allah in ka cutar damu kai da mahaliccinka" gyada kai haisam yayi yaja hannunta yasata a mota yayi ma yarinyar umarnin shiga da kyar matar ta saki hannunshi ya ba drivern umurnin su kama hanyar Abuja shima daga company ze taho a jirgi..................


Ai kuwa sharp sharp yayi handling duk wani abu da aka samu tangarda ya barwa amintattunshi saura suka kama hanyar Abuja 48mins ya kaisu sun samu motocinshi a wurin In not less than 4mins suka isa cikin compound dinshi a lokacin su qudra suka iso bayan ya sallami yaqoob ya musu jagora zuwa parlonshi na kasa....................


Ta fito wanka kenan tana shiri taji wayanta na kira ko dubawa bata yi ba balle tayi tunanin dagawa tana yar wakanta tana shafa mai dago idon da zatayi sukayi ido biyu dashi a bakin kofa a razane ta mike ganin da gaske shine yasa ta sauke ajiyar zuciya se kuma ta tuna me ke jikinta ai a dari ta isa bakin gado ta jawo hijabi ta rufe har kanta murmushi ya saki a karo na biyu tun bayan rasuwan iyayenshi ba wadda ya gani kuma ba wadda ya sani se shi................


Farin cikinshi na shirin dawowa sbd da ita, tayi nasarar sashi murmushi a karo na biyu ya tabbatar da sagir da yaqoob sun gani da ba wadda ze kaisu farin ciki a hankali yake takawa gurinta ya sa hannu ya zare hijab din a tsorace ta juyo don ko tahowarshi bata ji ba, se suka hada ido ya lumshe nashi yana kallon jikinta kasa kasa da sauri ta rungume shi don kare shi daga kallonta fuskanshi a sake ya sa hannu ya rungume ta.............


Ajiyar zuciya suka sauke a tare a hankali kuma duk a boye, yace "me ke damuna ne ko kina da masaniya?" Kai ta girgiza sake ta yayi ya juya ya fara tafiya yana cewa "ki shirya ki sameni a kasa" "toh" ta furta da sauri ta nufi wardrobe ta zaro doguwar rigar material peach me manyan flowers ta saka tare da yane kanta da bakin gyale ta fice.....................


#vote

#share

#comment


Sorry🙏

'Yar mutan Adamawa💞💞💞
                💞💞hamrah💞💞


                                                     💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin Wattpad: muhdfatimagurin          *’yar mutan Adamawa*Page➡1⃣5⃣

************


A hankali take saukowa cikin yanayin tafiyarta kaman me yanga tunda ta fara saukowa idanunshi a kanta duk da baza ka taba gane hakanba sbd a kwance yake jikin kujera idanunshi a lumshe har ta karasa saukowa be motsa ba ita kuwa idanunta akan su qudra yanayin fuskanta ya nuna tausayinsu don ta lura yarinyar a matukar tsorace take se kalle kalle take.................


Kan kujerar dayake zaune ta nufa da yake three seater ce a chan karshe ta zauna tana gaida mammi amma se taga tana ta shiririta da alamu de hankali be ishe ta ba amsa gaisuwar qudra tayi taja bakinta tayi shiru, a hankali ya bude lumsassun idanunshi ya sauke a kanta gabadaya kaman baze ce komai ba kuma se yace “ki basu masauki me kyau da abinci” cikin cika umarni tace “an gama” ta mike ta nufi wani daki a kasan ta bude................ 


A gyare yake tsab kaman da mutum a ciki seda ta tabbatar da komai lafiya ta fito tana kallon qudra a hankali tace “zaku iya karasowa” mikewa qudra tayi tana rike da hannun mammi suka shige dakin har hamrah, bayi ta shige tare da kiran qudra ta nuna mata yadda zatayi komai da yake yarinyar ba laifi akwai saurin daukan abu tsab ta fahimta se cewa take “mun gode Anty” ..................


Duk da alamu sun nuna qudrar zata girme ma hamrahn murmushi kawai hamrahn ke mata ta kara jaddadda mata “ki tabbatar kin wanke mama da kyau plz kuma ki wanke kanki da kyau bari na samo muku abinci da kayan sawa” da “toh” ta amsa tana fitowa suka hada ido da shi ya kafe kofar da ido murmushi ta sakar masa da ita kanta bata san sadda ya kubce mata ba da sauri ta haura sama.................


Cikin kayan sawanta ta zakulo wani garen mata irin bubu dinnan da ake daurewa da igiya kaman belt ta san ze yima mamar sbd sam bata da kiba sossai, hk ta dubawa qudra da kusan jikinsu daya sede zata dan fita tsai doguwar riga Dubai fashio me kyau ta fito abincin da ta girka ba wani yawa ne da shi ba tana da stew a fridge se kawai ta daura shinkafa ta fice don kai musu kayan.................


Yana nan zaune yadda ta barshi fuskan nan a hade ya kurawa wayarshi ido sabanin dazu da fuskanshi ke sake duk da ba murmushi yakeyi ba be dago ba har ta shige dakin da ta sauke su qudra ta samu basu fito ba se ta ajiye kayan ta kuma komawa yanzu waya taji yanayi da sagir cikin zafi yake magana “wai ni sukewa barazana? Wlh Allah basu isa in ja musu baya ba Alkawari ne se na tabbatar da kashe su da hannnu na” zaro ido hamrah tayi tana mamakin furucin nan nashi bata san me sagir ya gayamishi ba taji yaja tsaki tare da kashe wayan da sauri ta karasa hawa...............


Tana tsaye a kitchen tana duba shinkafan hannunta a kugu tana mamaki kisa? Toh waye ze kashe? Dafe kanta tayi don har ga Allah furucin ya dake ta a haka har ta gama ta duma miyan ta jujjuye a flask ta saka a tire tare da plates, spoons da ruwa ta gangara, da sallama ta shiga a lokacin har sun gama shiri ita mamar tana kwance shiru se ka rantse me hankali ce yarinyar na zaune a gefenta ajiye abincin tayi daga kasa tace .................


“Ya sunanki?” Cikin murmushi tace “qudratullah” murmushin hamrah ta mayar mata tana cewa “masha Allah suna me daadi, yanzu taso mama ku ci abinci” Da toh qudra ta amsa tana tashin mamar nata ita kuma hamrah ta basu guri Dan su ci a natse da tunanin maganan haisam ta kwana sossai abun ya tsaya mata gashi tana tsoron yi mishi magana..............:...


Zaune suke da yaqoob a cikin garden suna tattaunawa akan companies dinsu duk da yamma ce lis don an kusa kiran magrib, duk da suna cikin gida daya amma tunaninshi be nan Sam ya rasa dalilin shigo mishi tunani bayan suna gida daya se da ya nisa ya gama hada abunda ze fada tukun yace “in tambayeka mna?” Yaqoob yace “yes boss” yamutsa fuska yayi tukun yace .......................


“Damuwa da abu, sa abun sossai a zuciya, in ka rufe ido abun kake gani ko da kuna tare da abun ka kasance cikin tunaninshi, ba ka son ganin abun cikin damuwa, yawan kallon abun....., numfashi ya ajiye don yana ga ko ze kwana baxe gama lissafa abubuwan da yake ji game da ita ba, yaqoob mene ma’anar hakan?”...............


Numfashi yaqoob ya ajiye yana kokarin danne dariyarshi don ya ma haisam farin sani ya jima da tunanin wani abu na damun yallabai din bayan abunda ke gabansu amma ya san in be yi niyyar fad’a ba ko wanene kai baka isa ya fade shi ba don son kara Jan haisam din yace “mutum ne abun? Kuma mace?” Idanunshi ya zuba ma yaqoob na mintuna kaman baze yi magana ba kuma se ya gyada kai...................


Da mamakinshi se yaga yaqoob ya gangara kasa yayi sujjada da kallo yake binshi har ya dago yana tasbihi ga mahalicci a fili yace “boss you are in love Allah kasa da mace ta gari ka fada wannan soyyayyar Allah ya sa ta zama silar farin cikinka” tsam haisam ya mike ya nufi hanyar waje what? Soyayya? Inaa be shirya ba me yasa se da rayuwarshi yazo karshe zata shiga zuciyarshi....................


Da wannan sake saken ya nufi dakinshi don yin alwalan magrib yana ga amma so bai mishi adalci ba chak ya tsaya ganinta a cikin kitchen rike da cokalin miya tana safa da marwa fuskanta ya nuna tsantsar damuwar da take ciki, tmbayar kanshi yayi shin ya cancanci soyayyar yarinyar nan? Gani yake duk duniya bata da makiyi kamarshi ya shiga cikin rayuwarta ya dakatar mata da duk wani jin daadinta yanzu yazo yace yana sonta? Har yau kullum tana fama da damuwarshi? Ido ya runtse jin ana kira yasa shi saurin fadawa dakin don dauro alwala.........................


Se bayan sallahn isha ya dawo gidan zuciyarshi se sake sake yake duk da ya hadata da Allah sossai yayi adu’ar In sonta Alkhairi ne Allah ya tabbatar masa in ba Alkhairi bane Allah ya raba su ya kuma cire mishi sonta a ranshi, a parlorn kasa ya yada zango tare da danna kiran wayanta ba bata lokaci ta gangaro ba tare da ya kalle ta ba yace “kiramin qudratullah” tace “toh” tare da shigewa dakin.................


Bata wani dade da ajiye musu abincin dare ba har sunci mammi kam ma tayi bacci ta kira qudra akan mai gidan na kira a tare suka fito har ta nufi sama for the first time a rayuwarta taji ya kira sunanta cikin sanyi har bata san ta juyo ta kafa mishi ido ba shima ita yake kallo wani irin abu ne me wuyar fassaruwa taji yana fita daga idanunshi zuwa nata da sauri ta kawar da kanta a sanyaye ta dawo ta zauna....................


Kallon qudra yayi yace “qudratullah ki dauke ni a matsayin yayanki sunana haisam ga matata sunanta hamrah ki dauke mu a matsayin yan uwanki na jini Allah ne ya turoni rayuwarku dan na taimaka muku zanyi iya kokarina ganin mahaifiyarki ta samu lafiya” dafe kanshi yayi yau yayi surutu dayawa ga yawan tunanin da yakeyi fahimtar abunda yake son sake fada yasa hamrah tace .......................


“Ki dubi Girman Allah ki fadamana gaskiya akan rayuwarki data mahaifiyarki ba yadda zamu iya taimakonku har se kin gayamana gaskiyar labarinku” kallonta yake yi fuskanshi a sake sossai yaji daadin yadda ta fahimci abunda yake son fada gyaran murya qudra tayi tare da fara magana......................


“Kamar yadda na fadamuku sunana qudratullah na tashi na ganmu a gidan wani bayarbe da matarshi yayansu uku biyun sun girme ni daya kuma na girme mata duk mata na tashi ne da tsantsar azaba da tsangwama irin ta omolara, taufiqa da oluwankemi da mahaifiyarsu da suke kira Mommy kasancewar mahaifiyata mahaukaciya yasa kowa ke guduna a yadda mommynsu taufiqa ke fada In tana zagi na.................


Cikin shege aka wa mahaifiyata a cikin bola mijinta baban inkemi ya taimakemu gashi mun zame mata karfen kafa zan koyawa ‘ya’yanta iskanci, a duk gidan magidan ne kadai ke kaunarmu haka zan yini mata aiki amma da kyar zamu samu abun sawa a baki wani lokacinma sede ni in hakura in bar ma mammi na babban abunda ya tsaya min shine ban san kowa namu ba ban san daga inda muka fito ba..............


Baban su taufiqa ya ce min shima wlh ganin mammi yayi a bola tana nakuda tausayinta yasa shi kaita gidanshi har ta haihu a hannun wata nurse dake unguwarsu shi ya min komai na suna ya radamin suna qudratullah duk da yadda matarshi ta ki jininmu shi yake min komai se kuma in ya sa matarshi dole nasha wahala sossai a wurin mammi kafin tashi na wani lokacin haka kawai ta rufe ni da duka wani lokacin cikin dare tayi kwanciyarta a kaina sede in baban taufiqa ne yazo ya taimake ni da kyar na rayu nayi wayo ya so gwada nemawa mammi magani...................


Nan ne matarshi ta tsaya tsayin daka har ya bar maganan ya ma fita harkarmu a lokacin ne mommy ta samu damar yadda taga dama dani ko a gabanshi duka kam In sha a hannun yaranta In shaa a hannun ta in kuma sha a hannun mammi shima wani lokacin In sun daura min sharri haka ze kamani ya daka da fari ya sani makaranta har zuwa primary 5 nan ma mommy ce tayi yadda zatayi na dena zuwa Inyi wankinta na mijinta da na yaranta amma da kyar zata bamu sabulun namu...................


A haka har na shekara 18 kullum mammi na fita bolar gefen unguwan ta yi zamanta tana abubuwan hauka yara suyi ta tsokanarta suna jifarta ban isa fita in dawo da ita ba in na fitan kuma bazan shigo ba se yaran sun hada mu ni da mammi sunyi mana jina jina da duwatsu tukun a haka na yanke shawarar barin gidan tunda baban taufiqa da kanshi ya gayamin wacece ni kafin ma na aiwatar da nufina mommy ta dauramin sharrin sata suka hadu suka mana duka har mammi da kyar aka kwacemu daga nan suka kore mu muka fara yawon kango da bola se abunda muka samu muke ci..................


Ba irin abunda bamu gani ba kyara, sharri, harehare da niyyar mana fyade daga ni har mammi amma Allah na kare mu, abu daya dana lura dashi shine mammi bata son karatun qurani akwai wata rana da muna wucewa ta wani shago ya saka karatun qurani anan mammi ta kuma haukace mini tana ta wani irin ihu da kyar na samu na janyeta daga wurin ba wadda ya taimaka min duk da yadda mutane suka taru suna kallo daga muka bar wurin ta samu gefen bola ta kwanta se bacci ta kusan yini tana bacci dana gane haka kullum zan zauna In karanta mata dan abunda na iya ta hanyar makalewa a islamiyar unguwanmu haka zata ta bacci a kuma yi ta tsoratani.................


Muna cikin wannan halin ne ka shigo rayuwarmu Ina me mika godiya ta ga Allah da ya turomana kai duk duniya kaine kadai ka shigo rayuwarmu da gaskiya da amana kayi niyyar taimakonmu da zuciya daya Allah ya biyaku ya baku zuria dayyaba ya baka ikon taimakonmu mu” tunda ta fara magana yake kwance a jikin kujera idonshi a lumshe yana jin zuciyarshi na kuna ji yake kaman Amminshi akawa haka sossai ranshi ya sosu hamrah kam se da tayi hawaye..............


Tuna irin rayuwar da tayi na jin daadi da uwa da uba ta wulakanta wadda taga dama son ranta Ashe akwai wadda suke shan irin wuyan nan a rayuwa? Tabbas ta tausaya musu kuma taji zata bada gudumawa wurin taimakonsu da kyar haisam ya bude idonshi be ce komai ba ya tashi ya haura sama hamrah ce ta ringa ba qudra baki har tayi shiru dama kuka takeyi tunda ta fara bada labarin...................


Ta raka ta har daki ita kuma ta dawo parlor ta kunna karatu a wayanta ta hada da home theater dinta qira’ar sudais ke tashi cikin sanyi da amo daga suratul Fatiha ya fara ta saka wayan akan wannan na karewa wannan ze shiga ta haura a parlor ta tsaya ganin dinning wayam ta Zata zata ganshi a wurin yana cin abinci don da rana ce mata yayi he’s full yanzu ma gashi be ci ba duk da ta san time din cin abincinshi ya wuce amma dole ne ma yaci.................


Dakinshi ta nufa cikin kwarin gwuiwa tayi knocking tare da turawa yana kwance kan gadonshi idanunshi a lumshe jin shigowarta be sa ya bude ido ba se ma kara shiga wani duniyar tunanin yayi kanshi ta karasa tace “baza ka ci abinci ba?” Yace a hankali “I’m full” bata san lokacin da tace “baka isa ba kana da masaniyar cewa baka ci abinci da rana ba yanzu ma kace baza ka ci ba haka kake son kwana da yunwa?” Bude idonshi yayi ya zura mata ita kuma fahimtar katobarar da tayi yasa ta dafe baki tare da zaro ido zata gudu cikin azama ya mike ya cabki hannunta ya jawota se jikinshi.................


“Lallai ma wato ban isa ba?” Ya fada yana yamutsa fuska duk da ta bashi dariya kuma yaji daadin nuna kulawarta a kanshi shiru tayi Chan kuma se tace “naga ka sawa kanka damuwa ne akan labarin su mammi kuma gashi na lura tunda safe ranka a bace yake, ba’a son musulmi ya dinga zama da fushi idan kana cikin fushi dauro alwala ka samu guri ka zauna kayi ta karatun alqurani In shaa Allahu zaka ji xuciyarka wasai ba wani damuwa” lumshe idanunshi yayi yana jin yadda take zamewa da wayo daga jikinshi be hana ta ba har ta zame................


Dan bude ido yayi yana kallonta ta langwabar da kai cikin shagwaba tace “plz in kawo maka abincin” baze iya ki ba se yace “something light plz” murmushi tayi tukun ta juya ta fice shi kuma ya shige bayi sharp sharp yayi wanka ya fito yana tsane ruwan jikinshi ta turo kofa zaro ido tayi da sauri tace “sorry” tare da juyawa zata gudu yace “come back here” cikin muryarshi na umarni juyowa tayi kanta a kasa har tsakiyar dakin ta ajiye tray din ta mike ta fice bayanta yabi da kallo yana ji kaman ya jawo ta ta bashi abincin da kanta a baki ya rungume ta suyi bacci................
#vote


#share 


#comment


‘Yar mutan Adamawa💞💞💞
                   💞💞hamrah💞💞

                                                     💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin 
                *'yar mutan Adamawa*


Page➡1⃣6⃣

************


Zaune yake akan sallaya yana karatun qur'ani wuraren karfe 2 na dare ji yayi kaman ana magana da karfi daga parlor tsam ya mike ya fita yana fita yaji daga dakin hamrah ne da sauri ya fad'a dakin tana ta fisgewa kaman wacce aka kama take shirin kubcewa se ayatulkursi take ja da karfi haurawa gadon yayi ya rike ta tsam a jikinshi yana tofe ta da adu'o'i a hankali ta fara natsuwa duk Acn dake dakin se da ta jike da gumi................


Jikinshi ta kara shigewa tana kuka a hankali shafa kanta ya ringa yi zuwa bayanta har tayi shiru Chan tace "muje mu duba su?" Yace "mafarkinsu kikayi?" Kai ta gyada tana cewa "Dan Allah ka nema mata babban malamin musulunci Ya zo gobe ya fara dubata" kai ya gyad'a mata yana rike da hannunta suka sauka karatun da ta kunna bayayi...............


Kallonshi tayi shima ita yake kallo cire hannunta tayi daga nashi ta isa wayan ta kara kunnawa tukun suka isa kofan knocking sukayi da muryan kuka suka ji qudra tace "ku shigo" shiga sukayi da sauri suka isa bakin gadon ganin yadda mammi take a murd'e wani iri ba kyan gani fuskanta yayi jajazur..................


Qudra na zaune gefenta tana tofa mata adu'a suma adu'an suka fara mata karatun parlor kuma na shigowa har dakin ido ta bude da suka koma green ta kafe hamrah dashi a tsorace ta koma bayan haisam ta boye wa idon wani irin dariya ta saki sossai kafin kuma ta fara kuka daga haka ta ringa birgima a gadon daga baya kuma tayi dip se bacci................


Ajiyar zuciya suka sauke juyawa yayi ya kalli hamrah tare da sake kallon qudra be yi magana ba ya juya rike da hannun hamrah suka fice har kofan dakinta ya sake ta ze juya da sauri ta matsa ta rike hannunshi tare da langwabar da kai tace "Ina tsoro Allah bazan iya kwana ni kadai ba" kallonta yayi ba tare da yace komai ba ya kuma Jan hannunta zuwa dakinshi har bakin gadonshi ya kaita tare da nuna mata gadon................


Hawa tayi ta kwanta abunta shi kuma ya koma kan sallaya ya ci gaba na nafila da adu'o'i har seda tayi bacci tukun ya mike ya hau gadon ya kwanta tare da kurawa fuskarta ido ya jima yana kallonta tukun ya gyara mata kwanciya zuwa jikinshi tare da lumshe ido a haka shima bacci ya dauke shi...................


Ita ta fara tashi da asuba ganinta a jikinshi ya sata komawa tayi lub kamshin jikinshi na shiga hancinta lumshe ido tayi idonta biyu har aka shiga massallaci se a sannan ya mike yana furta adu'ar tashi daga bacci jin ana sallah yasa ya ce "subhanallah" Da Dan hanzari ya kwantar da ita ya mike ya fad'a toilet seda ta ga shiganshi tukun ta mike ta fice..................


Bayan tayi sallah tayi azkar dinka har wurin 6 tukun ta mike ta shige kitchen ta fara ayukanta bakinta na rera karatun qurani sbd ba karamin tsorata tayi ba da mafarkinta da kuma kallon da mammi ta mata, a haka ta gama doya da kwai da pepper soup ta zuba ruwan zafi a flask tattare komai tayi ta dauki nashi ta shirya mishi a dining, ta share parlorn ta goge abunda ya kamata dakinta ta koma...............


Bayan tayi wanka ta shirya tare da duba wasu kayan da zata ba su qudra su saka kafin ajima ta samo musu wasu kayan, da kayan ta fita a hannunta ta shiga kitchen ta sungumi tray din abincinsu ta fita da shi tana sauka ta samu qudra na aikin goge tiles yayin da mai aiki ke goge jikin stand da sauransu zaro ido tayi tana cewa "kai kai kai qudra bar aikin nan maza kije ki ci gaba da kula da mammi"................


Murmushi qudra tayi tare da nufar hamrah ta karbi trayn hannunta tana cewa "Anty ai mammin ma bacci take" a tare suka nufi dakin hamrah na lura da maid din tana hararta amma bata ce komai ba bayan sun shiga ta ajiye kayan hannunta ta bawa qudra umarnin wanka ta shirya kafin ta sauko tana son suje su samu kayayyakin anfaninsu...............  


Godiya sossai qudra tayi mata ba tare da tace komai ba ta koma sama a dining ta ganshi yana karyawa kusa da shi taje tukun ta gaida shi, amsawa yayi yana kallon shiganta riga ne off-shoulder a jikinta da high west skirt da akayi shi da yadi mai taushi kaman material ya budu sossai akwai adon pink da baki a jikinshi rigan ma pink ne ta daura turban black a kanta fuskanta ba komai................


Dakinshi ta fada ta gyara tsab ta wanke toilet dinshi ta fito a tsaye ta ganshi yana waya a tsakiyar dakin ya juyawa toilet din baya a sanyaye yake wayan kaman baya so sanye yake cikin wani dakkakiyar shadda sea green me guntun hannu gaban rigan ya sha aiki zubi na yan gayu me tafiya da zamani aka mishi kanshi ba hula se gashinshi da ya sha gyara se kyalli yake hannunshi sanye da Rolex wristwatch silver color ta shagala sossai da kallon ginannen jikinshi da ya amshi shaddan don ba shaddan bane ya amshe shi................


Har bata san ya juyo ba suna hada ido tayi saurin sa kai zata fice yace "hey" tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba kunya sossai ya kamata kaman ta nitse take ji se da yazo dab bayanta tukun yace "zuwa karfe biyu malam Mohd ze zo" Kai ta daga ba tare da tsawa ko fada ba yace "words" tace "toh amma yanzu zamu je sahad store da qudra Ina son sama musu kayan anfani kafin 2 din in shaa Allahu zamu dawo".................


Be yi magana ba ya juya safe dinshi dake cikin dakin ya sa ma password a take ya budu kudi ne a ciki dollars sun fi yawa se naira a cikin naira din ya debo kudi a kalla ze yi dubu dari biyar, ya mayar ya rufe tare da dawowa bayanta bata yi tsammani ba taji faffadan kirjinshi a bayanta lumshe ido duka sukayi yana jin kamshinta na rikita mishi lissafi ta baya ya zagayo da hannunshi tare da kama hannunta ya daura mata kudin................


A hankali tace "sunyi yawa fa" be tanka ta ba se kanshi da ya daura a wuyanta yana shakar kamshin ganin In be yi da gaske ba ze iya sake layi yasashi saurin sakinta ita ma da sassarfa ta fice ajiyar zuciya ya sauke tare da kwanciya rigingine akan gadonshi yana tunanin rayuwa be san dalilin shigowanta rayuwanshi ba, be san me yasa ya kamu da matsanancin sonta ba amma ya bar wa Allah komai kuma kullum se yayi musu adu'a be fatan sake bakanta mata a rayuwa bayan wadda yayi mata a baya...............


Shiyasa yake so kafin wa'adin da ya dibar wa su Alhj mudan ya cika ya sake ta tun be daura mata idda ba, be jin ze iya tafiya da alhakinta a kanshi ba tare da ya nemi gafararta ba sbd be san me ze cewa ubangijinshi ba akan wannan aure na fansa da yayi, tana fita ta dafe kirjinta da ke duka tara tara tana mamakin me wannan ta sha jin labaran soyayya tana karantawa tana kuma gani a films kala kala................


Ta kuma lura duk alamun da akace sun bayyana a kanta, kenan ta fara sonshi tsintar kanta tayi da adu'ar Allah yasa ya sota ko da kadan ne kuma taji daadi sossai da yanzu baya hantararta sam se ma kaman lallaba ta yakeyi a ganinta fa kenan, har ta dauki gyale se ta fasa ganin off-shoulder ce jikinta hijab ta samu daidai cinyarta pink color ta saka kwalliyan turban din ya fito ta gaban hijab din sossai tayi kyau a bakin jaka ta saka wayanta tare da kudin da ya bata ta kara da ATM card dinta duk cikin hakan ta zura black flat shoe ta fice ...................


Ta samu qudra ma ta gama shiri cikin material da ta bata me hade da gyale brown color ita ma ba lefi kyakyawa ce kuma fara ce zata iya kama hamrah a fari duk da farin ya disashe tsabar wuya, bata kai hamrah kyau ba amma itama tana da nata kyaun na daban, har yanzu mama bacci take da kyar qudra ta taimaka mata Tayo wanka ta kuma dura mata abinci duk mammin nata tayi sanyi kaman ba ita ba duk suratan da takeyi na hauka daga jiya zuwa yau sam bata yi ba...............


Bayan sun fito hamrah ta tsaya ta kunna karatu a tashar saudi sunna ta hada receiver din da home theater ta sa volume da dan yawa tukun suka fice drivernta ne ya taso ya fiddo musu mota yana jira su shiga tace "a'a malam Adamu bani keyn yau Ina sha'awar driving" a dan tsorace yace "yallabai baze yi fada ba?" Murmushi tayi mishi tukun ta girgiza kai fita yayi ya bata keyn ta shiga qudra ma ta shiga gefen................


Hamrah ke magana da zuciyarta oh lallai duniya wai yau ita hamrah ke ma driver magana kaman abokinta ba tsawa da isan nan, ita kuwa qudra duk da kauyanci sossai ya bayyana a yanayinta amma baza ka wani gane ba sbd natsuwarta kuma bata da yawan hayaniya magana kadan kadan ke hadasu ta fadar hamrah zama da haisam ya shafa mata miskilancinshi da tana da surutu ba kadan ba, sossai maganan ya ba qudra dariya se tayi murmushi tana cewa "ana shafar da miskilanci ne?" Itama hamrah dariya tayi ..................


Da hiran suka karasa sahad store, store ne da ba abunda be hada ba na komai da komai na kuma manyan mutane ne masu ji da kudi ganin qudra ta rikice ne yasa hamrah rike hannunta tana cewa "ki natsu plz ba abunda ze sameki in har muna tare da yardan Allah" kai qudra ta gyad'a a haka ta jata wurin atampopi ta fara zaba musu ita da mammi sossai take jidar musu kaya don Allah ya mugun sa mata kaunarsu da tausayinsu har ranta laceses ne, atampopi ne, dogayen riguna masu kyau kayan shafa da ta tabbatar ze karbi fatanta, kayan kwalliya, turaruka, gyalulluka, side bags masu kyau da shoes tas ta karar da kudin da haisam ya bata.................


Aka had'a musu komai aka kai musu mota suna shiga mota qudra ta fashe da kuka da mamaki hamrah ke kallonta tace "qudra lafiya? Wani abun ne ya sameki" cikin kuka tace "farin ciki ne Anty yanzu duk kudin nan da kika kashe akan ni da mahaifiyata? Bani da bakin gode muku ke da yaya haisam Allah ya biyaku da gidan Aljannah, ya kara hade kanku ya rabaku da sharrin makiya"..................


Murmushi hamrah tayi tana cewa "qudra yanzu fa kika ce mini Anty kika kuma cewa mijina yaya toh in har mu Antynki da yayanki ne me yasa don mun miki abu ke da mammi zakiyi kuka? Uhm? Adu'ar de ya dace kuma Ameen Allah ya karba" shiru qudra tayi tana yabon kirki na mutanen nan ashe akwai irin masu halinsu har yanzu a duniya?................


Ita kuma hamrah kalmar da ta furta guda daya ne ya tsaya mata a rai 'mijina' shi ta rinka maimaitawa a zuciyarta tuna aduar qudra na Allah ya kara hade kansu yasa ta sake cewa Ameen a zuciyarta tana fata mala'iku su amsa, a haka suka karasa shagon telan ta da sauri ya fito ya tare ta yana mata sannu da zuwa kaman ze zube murmushi tayi................


Ta ciro atampopi da laces ta mika mishi shagon suka shige ta mishi bayanin na qudra da na mammi duk ya rubuta sbd kar ya manta wata mace ce a shagon ta gwada qudra nan ma ya rubuta fasalta mishi yadda ze yi na mammi dinkin ba na yan mata ba, kuma manyan size yadda iyaye mata suke so, a take ta mishi transfer rabin kudinshi yana ta godiya suka fice............  


Kallon time tayi tana kiyasta ko ze ishe su zuwa saloon? 12:10 ta gani ze ishe su sbd saloon da zasu akwai ma'aikata dayawa da za'a musu komai cikin time, wani katafaren saloon da kap abuja za'a iya kiranshi na daya 'dr FishSpa' dake nan maitama 'unguwarsu hamrah' suka shiga tun daga waje se qudra ta rena kanta tana ganinta kaman almajira, a haka suka shiga ciki aka musu tarba me kyau a take suka tambayeta me za'ayi?..............


Nuna musu qudra tayi tana musu bayani da turanci akan ayi mata gyaran jiki me kyau a kuma wanke mata kai har da pedicure da toh matar ta amsa tare da yin gaba qudra ta bita ita kuma hamrah wash and set ta bada umarnin a mata dayake bata sa relaxer asalin gashinta me tsantsi ne sossai ga baki ana gama mata ta duba ba'a gama ma qudra ba tace zata je ta zo tare da ficewa.................


Ta kofar gidansu ta wuce tana jin kewar gidan gabadayanshi da mutanen ciki ta san ko ta shiga yanzu baza ta samu iyayen nata ba suna gurin aiki tunda haisam ya tafi da ita ko ta kofar gidan bata kara wucewa ba sede suyi waya, a gidan makwabtansu tayi horn get man din ya wangala ta shige knocking tayi a kofar parlorn gidan wata mata ce ta bude zata yi sa'a da hamrah In yayi wuta ta bata watanni cikin farin cikin ganin hamrah tace "manyan baki yau hamrah ce a gidan?"...............


Murmushi hamrah tayi tace "nice Maman arfat" bismillah ta mata har cikin parlor ta kawo mata drink da snacks tare da kwance babyn dake bayanta tana ajiye wa hamrah a cinya, Maman arfat itama yar wani ce sossai ta kware a iya lalle aure ne ya kawota unguwan su hamrah dayake gidansu ana aure da wuri yanzu ne take degree dinta na farko.............


Jininsu ya hadu sossai da hamrah duk da ba wai za'a kira su kawaye bane sede zumunci sukeyi sossai duk da tunda akayi auren hamrahn ko waya basu sake ba, hamrah na murmushi jin tambayar da Maman arfat ke mata na Ina maigida bata amsa ba tace "kinga kuwa lalle nake so ja shiyasa da nazo saloon na ratso hannuna fari sol" Maman arfat tace "kin kuwa taki sa'a jiya na siyo lallen" dibowa tayi ta kwaba ta Karbe arfat ta kwantar suka fara ba wasu masu yawa bane sam ba hayaniya ja ne se ya kwanta yayi kyau a farin fatarta.................


Se duba time take lura da tana sauri yasa maman arfat ta yi mata sharp sharp ta sa mata Leda one hour ta cire mata ta kaita toilet ta wanke hannun ya kuwa yi kyau ya fita ras kaman ka kwace hannun kiran wayarta ne yasata barin toilet din da sauri zaro ido tayi ganin haisam..................#vote

#comment

#share


'Yar mutan Adamawa💞💞💞                  💞💞hamrah💞💞

                                                        💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin           *'yar mutan Adamawa*


Page➡1⃣7⃣

************


Seda call din ya kusa tsinkewa kan ta daga zuciyarta na dukan tara tara sabanin abunda tayi tunani taji ta zata ze hau ta da masifa ne amma se taji sanyayyen muryanshi me cike da amo yana cewa "wai Ina kuka tsaya ne?" Se ta tsinci kanta da kara sanyaya murya tace "sorry ga munan tahowa" kashe wayan yayi ba tare da yace komai ba, godiya tayiwa Maman arfat ita kuma ta raka ta har motan taja ta fice daga gidan....................


Ta samu an gama ma qudra duk abunda tace sallaman su tayi ta ATM card dinta taja hannun qudra suka fice tana yaba kyaun da jikinta yayi ita kanta qudra kallon jikinta take kaman ba nata ba se godiya take kara yiwa hamrah a haka suka karasa gida.............


Ta bangarenshi kuma tana fita daga dakinshi yaji zuciyanshi yayi mugun bugu tunawa da yayi da rigan jikinta off-shoulder ne Allah ya sa ba gyale ta sa ba don wani masifaffen abu ne yaji ya tokare mishi kirji da sauri ya fita se yaga har sun wuce ganin driver dinta yasa ya gane ba tare suka fita ba sama ya koma a balcony din dake daura da dakinshi ya zauna gurin na facing tsakar gidan sossai ba abunda be gani amma in kana kasa da kyar ka iya fuskantan ko akwai mutum a wurin.......................


Ya jima a wurin yana aiki a system tare da kurban coffee kadan kadan har aka kira azahar yaje yayi sallah ya dawo a lokacin ne ya kirata bayan sun gama waya ya jingina da kujeran tare da lumshe ido hade da daura kafa daya akan daya be yi good 30mins ba yaji horn get din ya budu da kanshi...............


A hankali ya bude idanunshi ya zuba wa motar yana fatan kar ya ganta da gyale ai kuwa tana saukowa ya sauke wani nannauyen ajiyar zuciya tare da lumshe ido ya kara budesu akanta ba karamin kyau ta mishi ba be ma lura da qudra ba duk hankalinshi na kanta, yamutsa fuska yayi ganin tana mikawa malam adamu key da hannunta, hannun ya bi da kallo ganin Jan lalle daga nesa yana kyalli se ya tsinci kanshi da jin haushin mikawa adamu key da tayi da hannunta..................


Mayar da idanunshi yayi ya lumshe su, be tashi a wurin ba har yaga shigowar malam Muhammad babban malami ne yana dealing da irin abubuwan asiri, jinnu da sauransu tsam ya mike ya fita daga wurin a hanya ya hadu da ita har ta dan gota shi taji an rike hannunta kallonshi tayi shi kuwa idanunshi na kan lallen sossai ya mishi kyau amma baze iya furtawa ba dago ido yayi se cikin nata da ido ya mata alaman su koma kasa.................


Juyawa tayi suka fara saukowa a tare bayan ya sakar mata hannu a parlor ta tsaya shi kuma ya fita tare da shigowa da malamin bayan ya zauna suka gaisa itama gaishe shi tayi ya amsa, da ido ya nuna mata dakin su mammi ta fahimci me yake nufi se ta shige dakin ta kira su rike da hannun mammi suka fito ai kuwa mammi na had'a ido da malamin ta juya zata gudu tsawa ya daka mata "dawo" dawowa tayi suka kaita har gabanshi ta zauna daga kasa..................


Sossai malamin ya tsaya kallonta a take ya fahimci matsalanta sede yana wuyan karyewa wannan asiri don kaman ma ya tashi daga asiri ya koma tsafi me karfin tsiya ya tabbatar zasu sha wuya kafin karyewan komai kallon haisam yayi yace "shekarunta nawa a haka?" Kallon qudra haisam yayi se tace "zatayi ashirin da shidda zuwa da takwas a haka".................


Jinjina kai malam Mohd yayi yana furta "ya subhanallah, Allah ka tsare mu da son zuciya" Da Amin su hamrah suka amsa a take yayi bismillah ya fara karatun ayoyin ruqya tunda ya fara take wani irin gurnani kaman zakanya daga baya ta kwanta a kasa tana wani irin birgima zuwa Chan ta fara magana "ka bari ka bari zamuyi magana" be saurare ta ba ya ci gaba dayi har ta fara fidda wani irin hayaki daga bakinta daga baya kuma tayi dib Chan ta bude idanunta a hankali tana kallonsu daya bayan daya.................


Kur idonta ya tsaya akan haisam se kuma ta tabe baki tare da saukar dashi kan qudra malamin ne ya ce "ya sunanta" qudra tace "ban sani ba wlh mammi kawai nake ce mata" da mamaki yake kallon haisam shi kuma ya kasa cewa komai se hamrah ce ta fara ba malam labarin su qudra kaman yadda ta basu ta kara da taimakonsu da haisam yayi niyya...............


Tunda ta fara malamin ke girgiza kai yana mamakin son kai irin na mutane a fili yace "Allah yasa karshen wahalan ki kenan kai kuma Alhj Allah ya saka maka da Alkhairi ya biya ka" suka ce Ameen Gabadaya kallonta malam mohd yayi tare da cewa "baiwar Allah ya sunanki?" Juya mishi hannu tayi alamun bata sani ba, girgiza kai ya sake yi yana cewa "wato har yanzu basu rabu da ita ba, zan bada magunguna na sha, na wanka, na fesawa kaman turare se na hayaki duk za'a dinga mata safe, rana da kuma dare"....................


Kai su hamrah suka gyada ya mike yana cewa ze aiko haisam ya bi bayanshi a waje ne ya ciro kudi sossai ya ba malamin amma se yaki karba seda yayi da gaske tukun ya karba suka yi sallama................


*************


Bayan sati uku


"Akwai meeting da zasuyi a top ten hotel ranar 12/7/2019 zasu hadu da mugu da duk wani me sa hannu a kisan mahaifanka" sake maimaita karanta sakon haisam yayi ya kai sau shidda kallon hamrah dake zaune gefenshi tana breakfast yayi ganin hankalinta be kanshi ma yasa ya mayar da wayan ya ajiye yana tuna date din yau, saura sati daya................


A take yaji abincin da yake ci ya fita kanshi ajiye spoon din yayi, tare da fad'awa duniyan tunani, ya dauki matakin da yayi niyya ne ko ya bari? Kai gaskiya alkawarin da ya dauka se ya cika shi tabbas a ranar kawai ze je ya kashe su ya amsa laifinshi In yaso shima a kashe shi, sake kallon hamrah yayi yana tunanin toh In ya mutu zatayi farin ciki? A ranshi ya ce tabbas zatayi farin ciki makiyinta ya mutu, kenan se ta kara aure.................


Ruf ya runtse idanunshi don tunaninta da wani namijin ma kadai ya sa yaji wani irin zafi a zuciyarshi kaman an ajiye mishi dalma, kau da tunanin yayi tare da kara dauko wayanshi ya duba numbern da aka turo mishi sakon se yaga no number, tsam ya mike ya nufi dakinshi, da kallo ta bishi don tunda ya fara tunanin hankalinta ya koma kanshi.................


Yanzu zaman su de baza a kira shi dana daadi ba kuma baza a ce mishi na wuya ba, a duk sanda ze ci abinci toh tare suke zama su ci, aiyukanta de bata bata fasa ba, amma yanzu baya mata tsawa ko yayane zata iya tuna rabonshi da mata fada tun randa ya taimake ta daga hannun hisham kullum sede ya mata magana cikin sanyin muryarshi da kaman wani abu na damun shi sossai haka nan in ta mishi rashin kunya ko kallo bata isanshi balle tayi tunanin ze kula ta har suyi fad'a......................


Bata san ya akayi ba ba kuma ta san yaushe ta kamu da soyayyarshi me tsanani ba, ta fi sonshi a haisam din da ba na yanzu da yayi sanyi ba, ta fi son in ta mishi abu ya kula ta ya kuma yi mata masifan shin nan, amma ta rasa dalilin chanzawarshi tana fatan Allah ya yaye mishi duk wani abunda ke damunshi tana son sanin waye haisam amma bata isa ba sbd kullum In tayi niyyar tambayanshi ko shi ko 'yan uwanshi se ta tuna wtkl rabuwa zasuyi tunda auren fansa yayi da ita so tana ganin bata da hurumin sanin kowa nashi....................


Ta bangaren mammi kuwa jikinta yayi sauki sossai amma tun daga randa aka mata ruqya bata kara magana ba har yau, in ka ganta yanzu baza ka taba zaton cewa tayi hauka ba ko bata da hankali, kullum tana zaune shiru ba uhm da uhm uhm amma zata ci abinci in hamrah suna hira da qudra zata sa musu ido tayi ta kallonsu, in haisam na nan kuwa ta ringa hararanshi kenan tabe baki kawai yake yayi wucewarshi har wa yau ba'a dena mata amfani da magungunan da malam mohd ya bayar ba.............


Kuma har wa yau basu dena kwana da karatun qurani a home theater ba, qudra kuwa zama da hamrah ya sata ta fara kilewa sossai ta waye ta kuma koyi iya wanka da kwalliya a wurin hamrah ga girki da kullum tare sukeyi hannunta har ya d'an fad'a, in basu da aiki se su zauna hamrah tayi ta koya mata 'yan kananan word na turanci wani lokacin kuma suyi kallo.................

***********


Tsaye take a kitchen da misalin karfe 9 na dare coffee take had'a mishi ganin tunda ya dawo daga office yaki yaci komai ko dawowa cin abincin rana be yi ba gashi ta lura kaman be jin daadi, bayan ta gama ta nufi dakinshi da sallama ta shiga, yana zaune a bakin gado yana ta aiki a system a kan labbanshi ya amsa be daga ido ya kalle ta ba har ta karaso gefenshi...................


Lumshe ido yayi jin yadda kamshinta ya buge shi a hankali ya bude jin hannunta a goshinshi kallonta yayi ita kuma tayi raurau da ido tana cewa "subhanallah you are burning jikin ne? In kawo maka maganinka?" A take ta rikice ido kawai ya zuba mata yana lumshewa yana budewa, hannunta dake kan goshinshi ya kama tare da sawa a cikin nashi ya matse, shi kadai ya San me ke damunshi...............


Bam suka ji an bude kofa a tare suka kalli kofan yaqoob ne tsaye ganinsu a haka yasashi saurin komawa yana cewa sorry, kanshi a mugun daure ya juya zuwa kasa mace? A dakin haisam da wannan dare? Shi yasan yadda haisam ya tsani harka da mata ko mai aiki ce ze iya rantsewa bata taba shiga dakin haisam ba se namiji, Sam be so ya sawa zuciyarshi zargin haisam din amma me takeyi a dakinshi da half gown?................


Tsiririn tsaki yaja tare da sake lumshe ido yasa dayan hannunshi ya dafe kirjinshi dake tsananin ciwo a hankali ta zame ta nufi drower dinshi ta samo maganinshi balla tayi tare da dawowa gefenshi ta mika mishi amsa yayi ya harba a baki tare da daukan coffee din ya kurba, dan danna wayanshi yayi yana mikewa ya fita a parlorn kasa ya samu yaqoob yana zama yace "ya akayi?"...................


Yaqoob yace "dama na lura kaman jikinka na shirin tashine tunda rana shiyasa nazo na dubaka" ba tare da ya zauna ba yace "I'm fine don't worry" mikewa yaqoob yayi yanacewa "seda safe Allah ya sawwaka" a labbanshi ya amsa tare da juyawa ganin yaqoob din har ya fice ya haura shima tana zaune inda ya barta kusa da ita yaje ya zauna.................


Kusan mintuna biyar suka kashe a hk kafin taji ya ce "hamrah" tace "na'am" yayi shiru kaman abunda yake son fad'an yana mishi nauyi bayan ya nisa yace "kina son na sakeki yanzu ne ko in bari in na mutu kawai......... kiyi .... wani au..ren tunda baki da idda" runtse ido tayi ta san irin wannan rana na nan zuwa sede bata kawoshi nan kusa ba .................,


Kuka ne yake shirin kubce mata amma se ta danne me zata cewa iyayenta? Wani irin hali mahaifinta ze shiga? Wani irin kallo mutane zasu mata? Da sauri ta mike zata fita yayi azamar chabke hannunta kukan da take dannewa ne ya kubce mata da dan sauri ya jawota jikinshi tare da lumshe ido yana jin zafin kukan nata fiye da ciwon da yake ji a kirjinshi................


Be iya cewa komai ba se shafa gashinta zuwa bayanta da yakeyi ciwon jikinshi na karuwa a hankali kuma tayi shiru seda tayi tsit tana sauke ajiyar zuciya a hankali cikin sanyin muryarshi yace "I'm sorry hamrah, am really sorry I didn't..........." kasa karasawa yayi sbd kakarewa da maganan yayi se kara matseta yayi...............


Tace "me yasa kace ko se ka mutu? Bawa ya san ran mutuwarshi ne?" Har ta cire ran amsa taji yace "tabbas idan har ya san abunda yake shirin yi" "me kake shirin yi?" Shiru ya mata daga ji kuma be da niyyar yin mgna, a hankali take zamewa har ta raba jikinta da nashi se ji tayi yana cewa "kiyi hkr I can't tell you, ni Haisam mas'ood sa'ood na sa......"........................
😂😅 kar zuciyarku ta buga plz, kowa ya fito ya fad'i ra'ayinshi se naga comment dayawa zan ci gaba🥰🥰


#vote

#share

#comment'Yar mutan Adamawa💞💞💞            💞💞hamrah💞💞
                                                       💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin             *'yar mutan Adamawa*


Page➡1⃣8⃣

*******


Da sauri ta sa hannu ta danne bakinshi idanunta da suka cika da hawaye ta saka cikin nashi da sukayi wani irin ja tana girgiza mishi kai a hankali, tabbas a lokacin da zai iya da yayi kukan shima ko zai ji saukin abunda ya danne mishi zuciya, jikinshi ya jawo ta shi kuma yayi baya suka kwanta a kan gadon jikinshi ya sanyata tare da matse ta tsam, duk sukayi shiru a haka bacci ya kwashe shi daga jin yanayin saukan numfashin shi ma ta san baccin ba na daadi bane...................


Ita kuwa kasa baccin tayi sossai ta san ta kamu da sonshi duk da har yanzu duk abunda ya mata na nan kasan zuciyarta, son ne ya danne fushinta a kan shi, Sam bata son rabuwa dashi babban damuwanta kuma shine ambatar mutuwan da yake yawan yi tuna maganan rannan tayi na 'ze kashe su da hannunshi' kenan in har ya kashe sun ya san shima hukuncinshi kisa ne, kenan ya kusa kashe su? Toh ma su waye ne? Me suka mishi da baze yi anfani da kudinshi ya sa a hukuntasu ta hanyar da ta dace ba?...................


Abunda baza ta taba yarda dashi ba kenan, zatayi iya kokarin ta na ganin bata bari ya aikata mummunan abu ba ko ba komai har yanzu mijinta ne shi ba zata yarda ya yi wani abu na ashsha ba In shaa Allahu, shirin mikewa take ganin kaman baccin shi yayi nisa amma se yaki sakinta se ma kara kankameta da yayi................


Ba ta da wani option se na komawa faffadan kirjinshi tayi lub a haka bacci ya kwashe ta tana ta faman tunanin yadda zata sama musu mafita..............


Washegari 


Kasancewar bata sallah yasa yana fita massallaci itama ta fita ta fad'a kitchen yau abincin gargajiya take sha'awar musu wakenta ta gyara tsab ta saka a roba me kyau tare da rufeshi da murfi ta fice bayan ta zumbula hijab babba har kasa, in ba kuskure ba kaman tana yawan jin Karan injin markade a cikin quarters da ta tabbatar na ma'aikatan gidan ne idan zasu fita ta kofan baya lokacin da take zuwa copa cabana......................


Me bawa flowers din tsakar compound din ta yiwa sallama tare da cewa "bawan Allah taimaka ka mika mana markaden nan plz" tare da mika mishi robar karba yayi duk da be Santa ba amma yana yawan ganinta akai akai duk tunaninshi ya karkata ne akan me girkin ogansu ce ita shiyasa tana bashi ya washe baki a dole yaga kyakyawar mai aiki ko xata yarda da ya aureta wlh.................


Kara hade rai tayi tana mika mishi dari biyar da sauri ta sake kudin ganin yana shirin had'awa da hannunta, bata tanka ba ta juya ta shige gida ranta na suya wai ita yau wannan wawan ke shirin tabawa jiki? Ko da shike laifin haisam ne tunda har ya budi baki ya fadawa abokanshi ita maid ce to waye baze fad'awa ba...............


Duk abunda ya faru a kan idonshi ya faru sossai ranshi ya baci tabbas laifinshi ne be nuna wa kowa value dinta ba sema kaskantar da ita da yayi, da sauri ya fito daga corridor din ya tsaya daga karahenshi ta parlor a daidai lokacin kuma ta shigo parlorn da shi ta fara hada ido da sauri ta kawar da kanta tare da nufar kitchen.................


Jikinshi ne ya kara sanyi ganin hawayen da take ta kokarin boyewa da karfe ya runtse idonshi tare da dunkule hannunshi ya jima tsaye a wurin ya rasa wani mataki zai dauka a hankali ya bi bayanta zuwa kitchen daga bakin kofan ya tsaya a hankali ta juyo ganin shine yasa ta ci gaba da aikinta na dama kunun tsamiya tana yi tana goge hawaye nan ma seda ya dan jima har seda yaji shigowar qudra..................


A parlor suka gamu ta durkasa tana cewa "ya haisam Ina kwana?" Da "lfy" kawai ya amsa ya wuce ta ya nufi dakinshi dama kasa yayi niyyan sauka amma ganin roban markaden a hannun qudra da alamu karbowa tayi se ya shige dakinshi kiran yaqoob yayi ya bashi umurnin ya had'a meeting yana bukatar ganin duk wani ma'aikaci dake karkashinshi.................


Ta bangaren su qudra kuwa yau kwata kwata bata gane kan hamrah ba daga gani ranta a bace yake amma a haka ta gama aikinta na kosai da kunun tsamiya ta harhad'a na su qudra ta bata ita kuma ta shirya nasu, tana bude kofan dakinta ta ganshi tsaye a tsakiyar dakin daga ganin alamunshi ta san ranshi a bace yake amma se ta kara hade rai ta karasa..............:


Hannunta ya rike ya jata zuwa toilet towel ya mika mata tare da nuna mata ruwan wankan da ya had'a mata ba tare da musu ba ta karba a gabanshi ta fara shirin tube kayan jikinta da sauri ya juya ya fice, bayan ta fito daga ita se towel iya cinya se sunne kai takeyi a haka ta karasa gaban mirror shi ya mika mata mai ta shafa ya bata roll on da body's spray dun ta fesa.............


Da kanshi ya bude wardrobe ya dauko mata inner wears ya mika mata a kunyace ta saka ta rasa me yasa yake mata haka yau amma lura da tayi be kura mata ido kaman yadda ya saba ba yasa ta d'an sake, dakakkiyar lace ya dauko orange me adon light blue dinkin doguwar riga ne bubu yaji zubi me kyau irin na inji ya mika mata tana dan yamutsa fuska ta karba don bata son kaya me nauyi sam..................


Sawa tayi ya zauna mata d'as a jiki sossai ya mata kyau kallonshi tayi tana jiran ganin me a gaba murmushi ne ya so kubce mishi ganin yadda ta shagwabe alamun ta gaji amma se ya danne da kanshi ya zakulo gyale light blue me adon orange kad'an kad'an a jiki takalmi baki ya bata ta saka sossai yaji daadin yadda bata mishi musu a duk abunda ya saka ta, ba tare da ya barta ta shafa ko powder a fuskanta ba ya ja hannunta suka nufi kasa.............


A hankali tace "baka yi breakfast ba zamu fita?" Kallonta yayi itama shi take kallo for the first time a rayuwanta taga ya sake sassanyan murmushi da mugun mamaki take kallonshi har tayi tuntube bata sani ba da sauri ya taro ta yana cewa "kula mana" bata damu ba ta ci gaba da kallonshi amma ganin fuskanshi ya koma normal kaman da ya sa tayi zaton ko hasashe ne...............


Da kanshi ya bude mata mota ta shiga gidan gaba shima ya zagaya ya shiga mazaunin driver tayi mamakin ganin get a wangale ba kowa a tsakiyar gidan shi ya ja su har wani wuri ta bayan gidan da bata ta'ba zuwa ta wuraren ba wani katon kofa ta ga yayi parking da kanshi ya zagayo ya bude mata ta fito ya rike hannunta suka nufi kofan suna shiga taga duk mutanen wurin sun mike sossai mamaki ya kama ta ganin duk wani m'aikacin gidan a wurin har securities, masu aiki mata da maza kai duk wani wadda yake aiki a under shi..................


Kujeru ne guda biyu masu kyau asaman hall din amma daya yafi daya kyau da tsaruwa a kan karamin yaqoob ne zaune amma shima ganin shigowan haisam ya sashi mikewa hannunta cikin nashi ya kaita har gaban kujeran ya mata nuni da ta zauna mamaki ne kadai ke kasheta bata gama mutuwa da mamaki ba har seda taji hannunshi a kwankwasonta ya taya ta ta karasa zaman.................


Komawa gefe yayi ya tsaya a gefen kanta yana kallon yadda duk ma'aikatan suka cika da mamaki har yaqoob ba tare da wani damuwa ba ya fara magana "Assalamu Alaikum" suka amsa har wayanda b musulman ba "Ina son presenting muku something so special, so amazing, my happiness, my one and only, my everlasting, the only woman i cherish and value in my whole life after my mom" numfashi ya sauke ba tare da ya kalli inda take ba...............


Ita kuwa zuciyanta tsinkewa ya ringa yi a zuciyarta take ta adu'ar Allah yasa ba wulakantata zeyi ba kaman yadda ya saba amma da ya gama da ita har lahira a idon wayannan mutane a tsorace take kallonshi tare da mai da hankali akan abinda yake cewa...............


Kaman daga sama taji yace "Mrs Haisam mas'ood sa'ood" dago ido tayi don ganin wacece haka se taga ita yake kallo da mamaki ta kalli mutanen duk suma ido suka kura mata wasu na jin haushin toh me yasa don yana sonta se ya gaya musu, sake kallonshi tayi se taga ya tsuguna da gwiwa d'aya a gabanta dayan kuma ya tsayar da shi akan tafin kafan ya daura guiwan hannunshi kan kafan dake lankwashen a hankali cikin ra'da da kankan da murya yace ..............


" I LOVE YOU HAMRAH" zaro ido tayi sossai se ya kara mata kyau shima idanunshi cikin nata ya kara tabbatar mata a lokaci daya kuma ya sake mata murmushi da har hakoranshi fararen tas da kuma dasorinshi suka bayyana mutuwan zaune yaqoob da hamrah dake fuskantanshi sukayi a haka da murmushin ya mike ya juya yana fuskantan mutanen wurin suma duk mamaki kaman ya kashesu haisam ne ke dariya????..............


Akwai mutanen da suka shekara ashirin da saninshi amma basu ta'ba ganin murmushin shi ba se yau ciki harda yaqoob tsintar muryanshi sukayi yana cewa "my lost but found smile, as you can all see she brings back my smiles" se ya gimtse fuska yana ci gaba da cewa "she is my wife" ya kara nanatawa "my wife I married her months ago mutane dayawa sun Shaida na biya sadakinta...............


And as from today itace komai na cikin gidan nan kar wani ko wata su tare ni da complain na komai duk me complain ya sameta, ba se na fad'a ba but in mutum ya isa yayi disrespecting min mata I will make sure he end the rest of his or her life in prison" ya fad'a da bacin rai with bitterness in his tongue tuna rike hannun matarshi da me bawa flowers dinshi ruwa yaso yi d'azu tsit kake jin wurin ko numfashi me kyau ba wadda ke fitarwa barin ma hamrah da ta daskare a wurin...................


Sun kai minti biyar a haka yana tsaye kyam kaman wani soja se taji yana cewa "shall we?" Kallonshi tayi se taga ya mika mata hannu a hankali ta kama ta mike ya ja hannunta suka fice suka bar masu aiki da baki a sake sossai kunya ta kama me ba flowers ruwa se yake ga kaman kowa ya san abunda yayi shirin yi dazu kenan haisam ya gani? Allah ya so shi be furta mata abunda ke ranshi ba alokacin...............


Har kowa ya fita yaqoob ya kasa motsi ya rasa ma tunanin me kwakwalwan shi ze yi kiran sagir yayi ya zayyane mishi duk abunda ya faru sossai yaji zafi ganin haisam be dauke shi a bakin komai ba tunda har ze yi aure ba tare da saninshi ba su da kullum suke tare, hakuri sagir ya bashi tare da bashi tabbacin shigowanshi a washegari su tattauna don ko shi wlh be sani ba a hk suka yi sallama.................


Ta bangaren su hamrah kuwa suna shiga mota ya ja ya fice da hankali har cikin compound dinshi hannunta ya kama ya jata zuwa garden na cikin gidanshi da shi kad'ai ke shiga se masu gyarawa ita kanta bata taba sanin wurin ba a grass carpet ya zaunar da ita shima ya zauna a gabanta tare da sa hannayenshi cikin nata yace cikin rad'a.................


"I'm sorry for all the things I did to you, if I hv ever wrong you knowingly or unknowingly plz find a place in your heart to forgive me" Da sauri ta tari numfashin shi tana cewa "ya isa hk plz wlh na yafe maka ban ma rike ka a raina ba" idonta yake son kallo amma sam ta ki cikin stammering tace "do you meant it?" Da sauri yace "I do, I really do"...............


A hankali ta daga kai tare da kallon kwayar idonshi kaman me son gano karya ko gaskiyar da ke zuciyanshi da wannan dama ya samu ya rike kwayar idonta cikin nashi sun kai five minutes a haka da kyar ta samu ta kwace idanunta tana sauke Ajiyar zuciya taji ya ce "ban taba tunanin fad'awa soyayya ba a rayuwa na, ban kuma so in fad'a ba" Da sauri ta saci kallonshi yace ...................


"Yes sbd na san bazanyi tsawon rai ba a wannan shafin da rayuwa ya budemin ma bazan so ki shigo ciki ba, na fad'a miki ina sonki ne kawai sbd ki sani ko ba komai kya tayani adu'a bayan raina, ban kuma son se lokaci ya kure na furta miki Kalaman nan ki zata sbd banda yadda zanyi ne".............


Numfashi ya ajiye yana ganin kokarin kanshi yau ya zama aku tsabar magana da yaga yayi ci gaba yayi "ban fata ki fad'a cikin soyayyata kaman yadda na fad'a cikin naki, zanyi tafiya zan je na had'a kan duk wani abu da nasan mallaki na ne in baki sbd ko na mutu kar wani matsala ya tinkaro ki a kan wannan amma zan roke ki abu daya ki rike yaqoob yadda na rike shi zaki iya canza duk wadda kika ga bai miki ba amma plz banda yaqoob"............


"Wai me ke damunka ne? Wai baka da magana ne se na mutuwa?" Yake yayi yace "Ina da shi mana ba gashi nayi na sonki ba?" Murmushi ne ya kubce mata shima yayi a hankali tace "waye haisam mas'ood sa'ood I want to know" shiru yayi tare da zamewa ya kwanta akan kafanta ya lumshe ido ita kuma ta sa hannu cikin suman kanshi tana sosawa a hankali.................

Sorry😐🙏🙏


#vote

#share 

#comment

'Yar mutan Adamawa💞💞💞


                  💞💞hamrah💞💞

                                                         💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin


Wattpad: muhdfatimagurin             *'yar mutan Adamawa*


Page➡1⃣9⃣

************


"Bazan iya baki labarin haisam ba hamrah" ba tare da damuwa ya nuna sossai a fuskanta ba tace "sbd me? Ban kai ba Koh? Na san ni ba kowan kowa bac........." da sauri ya mike ya sa hannu a bakinta yace "kinfi kowa, kin kai har kin wuce" yayi shiru kaman baze yi magana ba se kuma yace "you owe me my story but not today" bata ce komai ba ya koma ya kwanta..................


A natse ta ci gaba da mishi wasa da gashi wani abu ta tuna da sauri tace "d'an d'aga In je In zo" a hankali ya zame tare da had'a yatsotsinshi ya sasu kasan keyanshi ya kwanta a kai ita kuma ta fice daga garden din a hanya se haduwa take da ma'aikatan gidan kowa dukawa har kasa yake ya gaishe ta suna neman gindin zama a haka har ta shiga cikin parlorn kasa bata had'u da qudra ba se mammi dake zaune tana kallon tashar saudi sunnah...............


Duk da ba magana take ba amma se da hamrah tayi mata sannu kan ta wuce sama a basket ta had'a breakfast dinsu tare da daukan food mat ta fito ta koma garden din, a gefenshi ta shimfid'a mat din tare da shirya abincin ta zuzzuba a plate kan tace "bismillah" a hankali ya bude ido tare da mikewa ya zauna kallon plate da cup din yakeyi ze iya tuna favorite din Abban shine Ammi na mishi akallah sau uku a sati mayar da idonshi yayi ya lumshe mood dinshi na chanzawa...................


Lura da hakan da tayi ne yasa tace "baka so ne in sama maka wani abun?" Kai ya girgiza mata tare da sa fork ya fara ci yaci sossai kafin ya lura bata sa nata ba dauka yayi a fork din ya kai bakinta a hankali ta bude ya saka mata shi ya ringa bata har ta koshi ta tattara kayan ta mayar kan ta dawo har yayi magana da pilot dinshi akan yana son su fita waje is the weather stable or not, pilot din ya bashi assurance na zasu iya tafiya nan da one hour.................


A hanya suka had'u se ta juya dama wurinshi zata koma a jere suke tafiya duk da ba uhm ba uhm uhm amma akwai tsantsar kulawarshi a kanta duk wani motsinta yana sane da shi har suka haura kowa ya wuce dakinshi wanka ya sake tare da shiryawa cikin suit bakake sossai yayi kyau ba tare da ya neme ta ba ya fice rike da briefcase dinshi ba tare da ya nemi yaqoob ba ya wuce abunshi daga shi se pilot din..................

**********


Bayan kwana uku


Zaune suke a parlorn sama su hudu hamrah, sagir, yaqoob da Aisha matar yaqoob suna tattaunawa akan matsalar haisam kwanan sagir biyu kenan da zuwa se da ya zo ne yaqoob yayi noticing haisam baya qasa abunda be taba faruwa ba kenan ko da baza su je tare ba ze fad'a mishi yayi tafiya, sagir ya kawo idean samun hamrah da maganan a tare suka shiga wurinta lafiya lau ta tarbe su suka gaisa tukun sagir yace "matarmu ko kinsan inda mijinki yaje?"..................


Da mamaki tace "kuna nufin kuma baku san inda yaje ba? Tare muka yi breakfast jiya daga In shiga daki In fito se ban same shi ba be ajiye min note kaman yadda ya saba ba kuma be turomin msg ba" Yaqoob ne yace "subhanallah Allah ya sa kar ya aikata wani abu de, duk na lura kwanakin nan akwai abunda yake boyewa" sagir ne yace "yanzu ba wannan ba Dan Allah ko zaki bamu labarin yadda aurenku ya kasance?".................


Ba tare da gardama ba hamrah ta basu labarin duk abunda ya faru dafe kai yaqoob yayi yana cewa "yanzu duk abunnan ya faru da yallabai Ina tare da shi ban sani ba? Anya na mishi Adalci kuwa ?" Sagir yace "kar ka damu ka san zurfin cikin haisam amma In shaa Allahu Alkhairi ce a gareshi" Yaqoob yayi saurin cewa "ai Alkhairin ce ma tunda har naga murmushin yallabai a jiya"..................


Da mugun mamaki sagir yace "kana nufin haisam smiled yesterday?" With assurance yaqoob yace "kwarai kuwa har da wani cewa I love you hamrah" cikin zare ido sagir yace "god Alhamdulillah zanso na sake ganin lost but found smiles and laughs na haisam I truly miss it" kunya duk ya cika hamrah, amma jin suna zancen haisam yasa ta daure ta tambaye su labarin haisam me yasa kowa ke mamakin ganin murmushin shi? Ita ta dauka yanayi ai a idonta ne be taba yi ba.....................


Gyara zama sagir yayi yana cewa "ba abunda zamu boye miki yanzu mun riga da mun zama friends kuma tunda haisam ya soki toh na tabbatar sbd kyawawan halayenki ne hamrah wlh akwai babban matsala Ina zargin ana turowa haisam duk wani informations da muke bukata amma yana boye mana yau kusan wata kenan Ina ta faman bincike amma ba abunda na iya ganowa su suspects din sun boye mana shi kuma haisam dake samu ya ki bari mu sani sbd wani burinshi na banza".......................


Tace cikin daurewar kai "ban fa gane ba" yace "yanzu kuwa zaki gane" a natse ya bata labarin haisam tunda ya fara hankalinta ya karkata kanshi da ya iso inda aka kashe su Ammi bata san sadda kuka ya kwace mata ba innalillahi kawai take maimaitawa a zuciyarta dama haka haisam yayi rayuwa? Ashe kawai gani zakayi a zahiri yana jin daadi ga arziki amma abunda ya fuskanta a badini yafi karfin tunanin mutum?.................


Wani irin so da tausayinshi taji ya ninku a zuciyarta abunda kuma ya daga mata hankali shine alwashinshi girgiza kai takeyi kaman wacce ta samu tabin hankali a fili take furta "I will never allow him to do such thing, bazan taba bari yayi wannan aika aikan ba innalillahi wainna ilaihi rajiu'n" su yaqoob ne sukayi ta bata baki har ta natsu..................


Shine take kuma gayamusu a lissafin da takeyi cikin satinnan ne ze aikata abunda yayi alwashi, a nan suka yanke shawaran yini tare a parlorn saman har randa ze dawo, Aisha de nata Adu'a anan don itama se lokacin take sanin wasu abubuwan don ba komai yaqoob ke gaya mata ba.............


Back to exact moment 


Hira sukeyi na rayuwa da yanayin siyasar wannan lokaci, yadda hukuma suke shan wahala da dai sauransu sunayi tana duba girkinta a haka qudra ta hauro ta samesu duk da tana jin kunyasu da nauyin ganin duk taron masu ilimi ne duk se su kashe minti talatin suna exchanging words da turanci mussamman In musu ya kaure amma ita ko daddaya take fahimta a cikin maganansu, sagir ke yawan tilasta mata zama suyi hiran tare bayan yaqoob ya bashi labarinsu hamrah kuma ta basu na taimakon da ya sama musu wadda har yaqoob be da masaniya..................


Duk da hamrah na biye musu ne kawai sbd wani lokacin suna yi ne in suna son cheering mood dinta mussaman in tunanin haisam ya mata yawa kullum kafin tayi bacci zata saka waya a gaba tayi ta kallo ko ze kirata ko kuma ya turo mata msg amma shiru wani lokacin tayi kuka ta kuma roki ubangijinta kar ya ba mijinta daman aikata wannan mummunan aika aikan tana fatan asirinsu ya tonu kafin lokacin da ya dibar musu yayi................


Da wuraren 12:40 ta shiryawa su yaqoob abinci a dining su kuma ta shirya musu a parlor, sagir se santi yake yana had'awa da zagin haisam In ya tuna lokacin da yake ta rokon haisam ya shigar da shi wurin hamrah yake wani cin rai yana wani ciccin magani ashe kishi ne, a zuciyarshi kuwa farin ciki yake taya abokinshi na samun mata ta gari................


Tsabta, kwalliya, ilimi both western and Islamic, iya girki ga haiba da son mutane, Allah Allah yake haisam ya dawo yaga wannan murmushin nashi da ya shekara ashirin rabon da ya gani, bayan sun gama lunch ne qudra ta sauka don taimakawa mammi tayi sallah ita ma tayi ta kuma bata abinci, su sagir ma massallaci suka wuce yayin da Aisha ta shiga dakin hamrah don gabatar da sallah kasancewar hamrah bata sallah se tayi zamanta parlorn tana kallo amma hankalinta na kan mijinta......................


Kaman daga sama taji kamshi kaman nashi da sauri ta daga kai se ta ganshi tsaye a kanta shima ita yake kallo sanye yake da fari sol din tshirt da dark blue jeans kafanshi sanye da timberlands farare gashin kanshi a gyare kaman kullum tsintsiyar hannunshi na sanye da Rolex watch golden color, suna had'a ido ya kawar da kanshi tare da nufar dakinshi da mugun sauri da gudu tabi bayanshi kafin ta karasa ya datse dakin da karfi take bugawa tana cewa................


"Haisam plz ka bude akwai maganan da nake so muyi plz if you truly love me" runtse idanunshi yayi yana jin kalamanta amma baya Jin ze fasa abinda yayi niyya yau da sauri ya bude wardrobe dinshi ya ja wani abu kaman box ya danna password se ga abu ya bude bindinga kwance a cikinshi da bullets a gefe bullets din ya durawa gun din dama tun Chan yana da license na rike bindinga sbd tsaro................


A ta bayan wandonshi yasaka rigan be gama sauka ya rufe bindingan ba ya bude kofan tana kokarin rike hannunshi yayi saurin fisgewa ya juya zaro ido tayi a hankali Tace "Gun haisam no karkayi plz haisam listen to me" kokarin Shan gabanshi takeyi amma Ina da gudu ya ganagara kan ta gangaro har ya shiga mota ba tare da ya kalle ta ba ya ja a gate ya tsaya na 2seconds kan ya fice da mugun gudu....................


Da sauri itama ta karasa ta fisge key tare da fad'awa mota tana isa get ta danna musu horn akan su bude amma se suka ki kuka ta fashe dashi ta fita ta nufi get din da kafa amma nan ma sunki barinta fita oga yace suka barta ta fita wlh a bakin ransu, hannu ta daura a kai, Aisha ce ta fito tana sallah take jin maganganun hamrah kuma kaman ita kadai don bata ji muryan haisam ba tana sallama ta fito bata ganta ba shine ta sauko anan suka had'u da qudra sukayi waje gabadaya ganinta cikin wannan yanayi yasa su saurin karasawa gareta daidai nan su yaqoob suka shigo..................


Da sauri hamrah ta nufesu tana kokarin rike hannunayensu a tare suka ja baya se ta sulale ta zauna dabas tana fashewa da kuka su sagir a rude suke tambayan me ya faru su qudra suka ce suma basu sani ba a haka suka fito suka ganta, nasiha suka fara mata amma innaa kukan ya ki tsayuwa da kyar suka samu tayi musu bayanin haisam ya fita da bindinga..................


Suma sun rude amma basu san me abin yi ba basu san ina yayi ba lallaba ta sukayi zuwa ciki duk da hankalinsu a mugun tashe jugum jugum suka zauna numfashin hamrah ne ya fara seizing kaman zata shide sagir ne ya tuna a labarinta tana da asthma kuma yaqoob ma asthmatic ne da sauri ya tambayi yaqoob inhaler se gashi ya fito dashi Aisha ce tayi ta shaka mata har ta dan dawo normal ta kuma ci gaba da kukan qudra ma kuka takeyi duk da bata san me yake faruwa ba.....................


Kusan 30mins sun rasa abunyi kowa na zaune ya zuba tagumi hamrah de har yanzu tana hawaye taku suka ji ana nufowa saman bakin stairs suka zubawa ido suna kallo a hankali figure dinshi ya bayyana farin rigan jikinshi ya dawo ja da jini hannunshi ma duk jini idanunshi na zubar da kwallah ba tare da ya kalli kowa ba ya nufi dakin shi yana shiga ya sa lock duk sun daskare a wurin ba wadda ya iya motsi kowa ya sadakar haisam yayi kisa..................


Ba wadda ya iya motsi a cikinsu ba'ayi five minutes ba suka ji siren, motocin polisawa guda hud'u a cike da police suka shigo gidan suka ba kansu position manyan suka shigo direct suka yo saman ganin mutane zaune a parlorn yasa babban yin sallama amsawa sagir yayi babban yace "we are here to arrest haisam mas'ood sa'ood" cikin karfin hali yaqoob yace "for??" Yace "an kira mu a five star akan anyi kisa so kan mu fara bincike ma aka ce an ga haisam ya fito daga room din jiki duk jini kuma ta gaban dunbin mutane ya wuce bayan sunji Karan bullets daga shiganshi.................


Mutanen da ya kashe manya ne da kudi baze iya resolving case din nan ba, na muku bayanin nan ne sbd girmanku kuma musamman kai sir" yayi maganan yana kallon sagir dakinshi sagir ya nuna musu suka karasa tare da knocking ba bata lokaci ya bude ya fito har yanzu hawaye be bar zuba a idanunshi ba suka sa mishi ankwa sbd hannunshi da ya mika musu har sunzo tsakiyar parlorn sagir ya tsayar dasu tare da zuwa gaban haisam murya na rawa yace................


"Did....... yhu?" Idanun haisam na kan hamrah da itama shi take kallo ido cikin ido idanunta sun kumbura suntum ga hopes dayawa yana gani a ciki she hopes yace no amma se taji yace "I killed them" wani irin mari sagir ya sauke mishi tare da fashewa da kuka yana cewa "why haisam why??????" Da tsawa yaqoob ne ya janye shi ko gezau haisam be yi ba idanunshi har yanzu yana kan hamrah da ya gama lura numfashinta na tafiya, a hankali ta mike ta nufo shi amma taku biyu ta zube a kasa numfashinta ya tsaya chak a lokaci daya suka jashi zuwa waje har ya fita idanunshi be bar kanta ba.............................


#vote

#share 

#comment'Yar mutan Adamawa
💞💞💞                    

              💞💞hamrah💞💞


                                                        💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin          *'yar mutan Adamawa*


Page2⃣0⃣

**********


A rud'e sukayi asibiti da ita ga tashin hankalin abunda haisam yayi gashi ya riga yayi confessing to laifinshi, Sam yaqoob yaki yardarwa zuciyarshi cewa haisam yayi kisa zugum suke zaune suna jira doctor ya fito daga dakin da aka kwantar da hamrah, sagir se safa da marwa yake tare da naushin dayan hannunshi da d'aya lokaci zuwa lokaci....................


Akallah 30mins doctorn ya fito kanshi duk sukayi suna tambayan ta farfad'o kai ya daga musu tare da cewa "Alhamdulillah ta farfad'o bacci takeyi yanzu sede gaskiya ya kamata ku guji fad'a mata abunda ze d'aga mata hankali jininta ya hau sossai kaman ma tundama tana da hawan jinin yanzu zan rubuta muku magunguna In ta farka muka ga komai normal zamu sallame ku"....................


Yaqoob ne ya amsa da "in shaa Allahu za'a kiyaye mun gode doctor" wucewa doctorn yayi yayinda yaqoob ya bishi don amso prescriptions din, su kuma su sagir suka shige dakin a kan plastic chair ya zauna yana dafe kai duk tunaninshi ya tafi akan ta Ina ze fara, abunda baze ta'ba bari ba kenan a yanke wa abokinshi hukuncin kisa yana wurin? Kuma yana ji yana gani??? Girgiza kai yayi yana kallon innocent face na hamrah tana bacci peacefully Aisha da qudra na zaune gefenta.....................


Yanzu duk wani responsibilities da komai na hamrah ya kamata ya koma kanshi In yaso yaqoob se ya ci gaba da running companies da orphanages na haisam din, ba'a wani jima ba yaqoob ya shigo da magunguna a leda ya ajiye a drawern gefen gadon asibitin kallon qudra yayi yace "ya kamata ki koma gida hk ko don mammi"..................


Da "toh" qudra ta amsa sagir ya kara da "ku tafi har matarka ma ta hadowa hamrahn abunda zata bukata In ta tashi" ba tare da yaqoob yace komai ba ya juya suka bi bayanshi duk tausayin bayin Allahn ya cika qudra dama masu kudi ma suna shiga kuncin rayuwa kaman wannan? Ita ta dauka talaka ne kad'ai ya san wannan fad'i tashin, ita kuwa Aisha taji daadin bin mijinta da aka ce tayi sbd tana lura dashi gabadaya be cikin natsuwanshi karfin hali ne kawai irin na maza.................


Sossai kuma ta tausayawa hamrah da haisam ajiye kanta da mijinta tayi a matsayinsu ta san baza ta taba iya d'auka ba ita kokarin hamrahn ma take gani, yaqoob kuwa tunaninshi gabadaya ya tafi ne akan wani irin mataki ze d'auka In ya tuna wayanda haisam ya kashe ba karamin fad'uwa gabanshi ke yi ba haisam ba d'an siyasa ba su kuwa sossai ake damawa da su a gwamnati duk da fuska biyu garesu amma jama'ar gari suna son su duk da haisam na taimakon alumma sossai shi ma kuma ana sonshi amma yana tsoron sharrin mutane ya san zuwa yanzu maganan ya gama yad'e ko ina.........................


Wayanshi da ya bari a motan ne ya katse mishi tunani d'agawa yayi yana kallon me kira chief judge ne na high court ya san tabbatar da zancen yake son yi don haka be daga ba, bayan kiran ya katse yaga calls sossai na manyan mutane gabadaya ya kashe wayan yana jan tsaki tare da jan motan suka fice daga asibitin..............


**********


Bayan tafiyan su yaqoob da akallah mintuna ashirin hamrah ta farka a hankali take bude idanunta har suka budu tar kallon inda take takeyi tana tunanin me ya kawota nan? A hankali duk wani abinda ya faru ya fara dawo mata, sagir dake zaune be san ma ta farka ba sede yaji kuka da sauri ya dubi inda take zaune akan gadon ta had'a kai da gwiwa kanta ba dankwali gashinta sun zubo har kan kafafuwanta da sauri ya kawar da kanshi..................


Barinta yayi tayi kuka sossai seda ya tabbatar zuciyarta ya danyi sanyi tukun ya ja kujeranshi zuwa kusa da gadon dankwalinta ya dauka daga kan pillow a natse yace "Hamrah" dago kai tayi tana kallonshi mika mata dankwalin yayi ta karba ta d'aura a kanta ya kara ciro hanky ya mika mata ta karba ta fara goge hawayen fuskanta seda ta gama tsab tukun yace..................


"Hamrah kuka a gareki ba shine solution ba yanzu me amfanin kukan me ya rage miki? Na tabbatar se abinda ya kara miki, in har da gaske kina son haisam be kamata a ganmu a nan ba, dan Allah ki sawa zuciyarki salama kar wani abun bayan hawan jini ya kamaki".............


Hawan jini? Ita? Runtse ido tayi tana kara jin kanta na Sarawa kuma tana kallon gaskiyan sagir in har tana son haisam ya kamata daga yanzu ta fara fighting don ganin ya fita, karasa goge fuskanta tayi tana mika mishi hanky din tace "in shaa Allahu na gode" gyad'a kai yayi duk suka yi shiru ta bude baki da niyyan magana kenan aka turo kofan yaqoob ne da Aisha..............


Aisha na riqe da basket a hannunta da kayan tea a ciki da ruwan zafi se fruits d'ayan hannunta kuma Leda ne me d'an girma tazo ta ajiye a gefen gadon tana ma hamrah sannu ita ma ta amsa yaqoob ma sannu ya mata tare da jan d'ayan plastic chair ya zauna, Aisha kuma ta zauna gefen hamrahn duk shiru sukayi kowa na sake sake a zuciyarshi.................


"Amma kun san ba haisam bane yayi kisan nan?" Maganan hamrah ne ya katse musu tunani kowa ya maida hankali kanta yaqoob ne yace "sbd me kika ce haka?" Tace "wlh ban yarda ba, duk da daurewar shi a fuska haisam na da zuciya me kyau yana da tausayi baze iya sa harsashe ya kashe mutum ba" sagir ne ya katse yaqoob daga maganan da yake shirin yi da cewa................


"Tabbas haisam be yi kisa ba na sanshi na san waye shi tun ba yau ba, in har haisam na wuri ko Kiyashi baze yadda ka kashe ba" Yaqoob yace "duk mun yarda haisam baze yi kisa ba amma maganan bakinmu bashine ze sa alkali ya yarda ya fasa yanke mishi hukunci ba we need proof" sagir yace "hkne first of all lawyer, wa kuke ga ya kamata mu dauka a aikin nan?".............


Hamrah tayi carab tace "Barr. Suhailah aryan" kallonta sukayi Aisha tace "mace?? Kina tunanin zata iya wannan aiki?" Sossai hamrah ta kalli Aisha tana cewa "kin kuwa Santa?" Girgiza kai Aisha tayi hamrah tace "she's my mom, amma ba don tana mahaifiyata bace nayi suggesting tayi wannan aiki ba, nayi hakan ne sbd a tarihi ban taba ji ko gani mom tayi shari'a ta fad'i ba, se ta tabbatar da gaskiyan mutum take karban shari'anshi kuma har a gama shari'a tana kwana kan sallaya"....................


Shiru duk sukayi tabbas yaqoob ya sha jin labarinta hk sagir ma ya Santa amma be ta'ba tunani tana da 'ya kaman hamrah ba maganan hamrah ne ya sasu kallonta "amma se munyi da gaske zata karbi shar'ian haisam In bamu ci sa'a bama baza ta karba" Aisha tace "sbd me bayan surkinta ne?"..................


"Yanzu fa na gama cewa bata karban case din mara gaskiya bare wannan da mutane dayawa suka ga shiga da fitan shi dakin kuma suka shaida karan bindinga and kuma ba mutum d'aya ba har hud'u the worst thing kuma ya riga ya amsa laifinshi" ta karasa hawaye na zuba mata duk shiru sukayi suna tunani Chan sagir ya sauke ajiyan zuciya yana kallon hamrah yace..............


"We have to find a way kenan da zamu sata karban shari'an?" Kai hamrah ta gyad'a tare da cewa "I hv already find the solution to this" Yaqoob yace "menene?" Dan karamin murmushi tayi tare da sauka daga kan gadon tana yafa dankwalin dogon rigar jikinta a kanta zuwa wuyanta tayi taku daya biyu tukun tace "just inform them Ina asibiti and please inhaler"...................


Sagir yayi saurin cewa "bade da rayuwarki zakiyi wasa ba???" Ta shagwaba fuska tana cewa "we don't hv any way out than that" Yaqoob yace "but...." ta katse shi da "plz" Shiru yayi tare da sa hannu a aljihu ya dauko mata inhaler din sagir kuma ya ciro wayanshi ya kira mom ringing uku ta d'aga suka gaisa a mutunce tukun ya sanar mata hamrah na HMS hospital ba lafiya cikin tashin hankali take tambayar me ya sameta, ce mata yayi kawai se tazo tare da kashewa...............


Ba'ayi mintuna sha biyar ba se ga call din mom tana tambayar shi room ya fad'a mata ta kashe da murmushi ya kalli hamrah yana cewa "ke fa 'yar gata ce har ta iso" karamin murmushi hamrah tayi tare da narkewa akan pillow ta lumshe ido ba'a jima ba mom da dad suka turo kofar da sallama basu ma bi ta kan 'yan d'akin ba sukayi bakin gadon kowa ya kama hannunta suna kiran sunanta...................


Sagir ne yace "Ina yininmu" dad ya juyo yana cewa "opps sorry sannunku" suka gaggaisa mom ta tambayi me aka ce yana damunta yaqoob yace "hawan jini" zaro ido iyayen nata sukayi dad yace "subhanallah how comes me ke damunta haka?" Shiru 'yan dakin sukayi mom kam har da hawayenta 'yarta karama da ita da hawan jini hamrah ce ta motsa suka juya suna kallonta................


A hankali ta bude idanunta tana ganin dad ta fashe da kuka sossai harda shesheka, cikin damuwa dad yake cewa "daddy's princess ya akayi me ya sameki?" Bata amsa ba se kukanta da ta karawa volume jin mom na tambayan sagir Ina mijinta yasa ta dago ta rungume mom tana ci gaba da kukan, a tsorace sagir ke kallonta da mugun mamaki Ina ta samo wannan kukan? Be san a wuya take ba daman kukanta ta ci gaba dayi har se da asthma dinta ya tashi da kyar aka shawo kanshi seda doctor yazo ya mata allurai na asthman yana ta masifan me yasa baza a kwantar mata da hankali a mata abunda take so ba haba ya zasu had'a mata zafi biyu...........


Mom da dad ne suka bashi hkr su sagir kam kasa ko motsi sukayi wani irin plan ne wannan har da wasa da rayuwanta duk sbd haisam yanzu in da likitan ya kasa shawo kan asthman fa sagir kam harda dana sanin barinta da yayi yake yi bayan 30mins ta dawo normal se ta nemi zantawa da iyayenta kawai su sagir suka fice...........


Bayan sun fita ne ta dubi su mom a hankali ta fara basu labarin waye haisam tun farko har karshe abunda bata fad'a bade yadda akayi aurensu wannan sirrinta ne tunda tun lokacin bata fad'a ba mom har seda tayi hawaye wannan kisan wulakanci? Kenan koda shi ya kashesu doka kawai ya dauka a hannunshi amma sun chanchanci mutuwa................


Maganan hamrah ne ya dawo da ita tunaninta "mom don Allah ki taimaka ma.............." kan ta karasa dad ya rufe mata baki mom kam dama tana hararanta dad yace "baki da hankali ne mamana?? Da labarin da kika bamun nan, da hawan jinin da kika samawa kankin nan kike kuma rokanmu mu taimaka muku? Mamana In mun taimaka mishi ba ke muka taimakawa ba? In kuma mun taimaka miki ai kanmu muka taimaka"...........


Rungume dad tayi hawaye na gangara mata mom ce tace "ki kwantar da hankalinki zanyi iya kokarina sai mu barwa Allah saura yanzu da voice recordern nan zamu fara anfani se ki karbomin, na san kuma ba zama d'aya za'ayi ba, se ki san yadda zakiyi da mijinkin kar ya amsa laifin a zaman farko don in ya amsa to komai ya baci" kai hamrah ta gyad'a tana tunanin ya zatayi da haisam ya musa ................


Tare suka kai dare da su mom ta matsa aka sallame ta da tayi niyyan bin su gida dad yaki Sam yace ta koma gidanta, dasu sagir suka koma gida ta kuma basu labarin yadda sukayi da mom, nan yaqoob yace akwai wani tape din a hannunshi, batun sa haisam ya fad'i gaskiyar me ya faru kuma duk zasu gwada wadda yayi dacen sashi toh, a haka suka karasa gida...................
*A gaskiya bana jin daadin yadda ake tafiyan nan, reaction dinku ke sa nake typing kullum ko akasin haka, idan da ana voting kad'ai bama sai an had'a da comment ba I will manage, amma ace mutum sama da hamsin zasu karanta a nan wattpad amma vote din be fi shidda ba fisabilillahi kuma kuke tunanin in muku kullum???.......


Wallahi Allah ba don wasu mutane kalilan da suke son novel dinnan suke bada shawara kuma suke nuna jin daadinsu ba da na dade da dena rubutawa ba'a dole ban sa wani ya karantaba amma In kaga kana so ka karanta kasa hannu kawai kayi voting shine aiki??? Allah ya kyauta.....


Godiya ta musamman a gareku:-


Maman Heedaya 

Eshat sadaukin karaye 

Zainab Ads 

~🌹🌹

Hassana Abdullahi fagge 

Suwaiba Ibrahim Yusuf 

Pretty pinky💞💞

Arfah2425

Zainabsamba

OuachoAboubzeinabDa duk wayanda ban ambata ba na group din  "Mu karu da juna" da kuma 

"Hamrah fans group" ba don ku ba da wannan littafin ya dade da zama tarihi na gode kwarai*...........
#vote

#share

#comment


'Yar mutan Adamawa
💞💞💞   


                💞💞Hamrah💞💞

                                                      💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin   *'yar mutan Adamawa*


Page➡2⃣1⃣

*******


Bayan kwana uku


Duk yadda suka so ganin haisam abun ya ci tura seda sukayi da gaske tukun a kwananshi na uku a cell aka ba hamrah daman zantawa dashi na 30mins kuma saura kwana biyu a shiga court daga sama aka bada umarnin tura case din court tunda ya amsa laifinshi duk mom ta gama shirinta na zaman farko In yaso kan zama na biyu se su san abunyi daga yanayin zaman farko...............


Zaune take a kan sit me karamin table tana facing wani empty sit din ta d'anyi duhu ta rame kad'an hannunta take ta murd'awa feeling nervous tana ga kaman baxe saurareta ba, a hankali kofan ya bud'u se ga haisam ya bayyana daga shi se dogon wando jeans na tun rannan da kuma vest baki bayanshi police ne guda d'aya se da ya tabbatar da zamanshi tukun ya fice don basu wuri.............


Tunda ya shigo wurin idanunshi ke kanta duk ya lura da yanayinta Sam bata cikin natsuwarta runtse ido yayi abunda yake gudar mata kenan yasa ya nemi sakinta a hankali ta saci kallonshi bata san sadda ta zare ido ba tare da isa gabanshi within a blink tare da rike hannunshi tayi rau rau da ido zatayi kuka yace "shiiiii karkimin kuka nikam".............


Yana rufe baki hawayen na gangarowa runtse idanunshi yayi yana jin hawayen nata har ranshi tsintar muryarta yayi tana cewa "Me ya sameka haka? Basa baka abinci ne?" Ba tare da ya amsa ta ba ya jawo ta kan kafanshi ta zauna bawai basa bashi abinci bane abinci me kyau suke bashi amma rashin sabo yasa be iya cin abincin kirki ga zafin wurin da yake ji kaman ana gasa fatanshi ga sauro duk da suna sa mishi magani amma wuri a bude dole ne wasu na mutuwa wasu na shiga, and ya kasa wanka a toilet din wurin kai ko fitsari da kyar yakeyi mutumin dake wanka akai akai, fatanshi har ya dishe kuma ramanshi ya nuna sossai rashin walwalanshi kuma ya karu..................


"Me yasa kika zo?" Da mamaki take kallonshi wani irin tambaya ne wannan ya ma za'ayi ya mata irin wannan tambayan ranta a d'an bace wadda be boyu a muryanta ba tace "how on earth will you ask such question?" Shiru ya mata ranta ne ya kara baci taji tana son karaya da halin shi, tuna musabbabin zuwan yasa tace "jibi za'a shiga court" ta'be baki yayi ko a jikinshi ganin ba magana ze yi ba yasa ta kara da................


"Plz and plz haisam kar ka amsa laifin da ba kai ka aikata ba, I know you didn't killed them bcos you can't" Da mamaki yake kallonta me yasa ta kasa yarda shi yayi kisan? Juya kanshi yayi tare da sauke ajiyan zuciya he feel hurt idan yaga yana karya mata zuciya don ba yadda ya iya ne yasa yace "waennan words din hamrah su zan fad'a a ko ina a kuma gaban ko waye, I killed them, period idan abunda ya kawo ki kenan you can leave plz".............


Mikewa tayi daga kafanshi ranta a bace hawaye na zuba daga idanunta tace cikin d'an tsawa "why????? Haisam why on earth will you admit to something da ba kai ka aikata ba I know that and you clearly knows too, why plz???" Shima mikewa yayi don kukanta na shirin karya mishi zuciya baya ya juya mata tukun yace "sbd ba wadda yake sona, sbd banga amfanin zamana a duniyar da ban ta'ba jin daadin ta ba, sbd nobody cares da mutuwana ko rayuwana"...............


Cikin d'aga murya tayi saurin katse shi "who says so? Wa ya gayamaka baka da masoya a duniya? Wa ya gaya maka mutuwarka baze kassara rayuwar marayun da ka jima kana tallafawa ba? Haisam baka yiwa yaqoob da sagir Adalci ba In har kace basa sonka" sanyaya murya tayi tace "and I, I truly loved you, I love you and I will continue loving you to the square of infinity" ta duka kasa kan gwiwowinta ta ci gaba, "for my sake haisam, for the love I had for you, for Allah's sake karka amsa abunda ba kai ka aikata ba tell the truth you know and Allah will show a way to set you free"..................


Daskarewa yayi a wurin zuciyarshi na tsananta bugawa, Sam be zaci jin words dinnan daga bakin hamrah ba, ji yake kaman ya gudu ya bita tayi proving words dinta a gareshi a cikin gidansu suyi rayuwa cikin farin ciki be gama tunanin ba police daya kawo shi ya shigo yace "time's up" mikewa hamrah tayi daga kasa tana share hawayen face dinta ta nufi kan desk jakanta da aka gama bincika kafin da kyar aka barta tashigo dashi ta bude ta d'auko paper ta nufi wurinshi................


A hannunshi ta saka papern tana kallon kwayar idonshi tace "wannan shi ze tabbatar maka da ina sonka haisam na samu hypertension just bcos of you, a ranar da aka kama ka asthma na ya tashi sau ba adadi yininmu guda a asibiti nan ma don na ki ne aka sallame ni amma doctorn yaso na kwana biyu, haisam In har ka bari aka kashe ka to tabbas zan bi ka amma bazan ta'ba yafe maka ba sbd na san iyayena ma zasu iya bina and you will hold responsible for our death" d'age tayi tayi kissing kumatun shi kan ta juya ta fice with so much hope a ranta na maganganunta sun shige shi...................


Yana sonyin magana amma ya kasa uttering word sbd miyaun bakinshi sun kafe yana kallonta har ta fice without given him a second glance, a sanyaye ya juya shima ya wuce don komawa room dinshi hannunshi rike da papern da ta bashi..................


**********

Federal high court Abuja


Mutane ne makil ciki da wajen court din 'yan jarida kuwa sunfi a kirga kowa na son ya san me su Alhj mudan sukayiwa haisam ya kashesu duk iyalan mamatan sun hallarta masu tsinewa haisam nayi masu cewa a bari de aji me suka mishi nayi, masu cewa kawai kudinshi ne ya rud'e shi nayi, masu daidai kenan nayi...............


Hamrah, sagir, dad, yaqoob, Aisha, qudra har mammi data nace se tazo tun asuba tayi wanka ta shirya ta zauna a parlor sun so mata wayau su gudu amma ta kasa ta tsare, Qudra ce ta bata labarin abunda ke faruwa don ta saba komai taji ko ta gani zata zo tayi ma mammi bayani tun lokacin da take hauka ma balle yanzu da natsuwa da kamala ya nuna sossai a fuskanta duk da har yau bata magana................


Duk suna zaune a gaban gaban court din hankalinsu ya tattaru gaban court din dukda Alkalin be shigo ba haka ba'a shigo da haisam ba, su mom ne de ke zazzaune, kaman daga sama hamrah ta kalli wadda bata ta'ba zato ba a gaban court din mamaki ne ya kusa kasheta ganinshi sanye da kayan lawyoyi suna had'a ido da ita ya kashe mata ido tare da d'age gira da sauri ta kawar da kanta sagir yaga abunda ya faru yana kuma mamakin Ina hamrah ta san wannan..................


Tunaninshi ne ya katse ganin judge din ya shigo yana shiga suka mike suka tsatsaya seda ya zauna tukun suma suka zazzauna, tambaya yayi akan shari'ar da za a gabatar yau, aka gabatar mishi ya nemi a kawo me laifi tukun aka fito da haisam yau kam bakar jallabiya ce a jikinshi duhunshi ya kara fita idanunshi sun kara girma ga rama nan har wuyanshi be saba da zama a wahala ba sam...............


Duk waenda suka sanshi sossai seda abun ya ta'ba su be kalli kowa ba har aka karasa dashi cikin inda masu laifi ke tsayuwa, judge ya bukaci lawyoyi su gabatar da kansu mom ce ta mike "My lord sunana barr Suhailah Aryan lawyer me kare wadda ake kara" lumshe ido haisam yayi yana tunanin wacce irin mata Allah ya bashi ne, bayan duk abubuwan da ya mata mahaifiyarta ce ke kare shi? Tunaninshi ne ya katse jin anacewa................


"Sunana Barr Hisham Murtala Mai dala, ya mai shari'a nine lawyern daze tsayawa mamatan da haisam ya kashe" runtse ido hamrah tayi tana jin zuciyarta na tsananta bugawa a take idanunta sukayi ja tana budewa se cikin na haisam da shima ita yake kallo hawayen idanunta ne suka sauka a kan kumatunta girgiza mata kai haisam yayi na ta dena kuka ita kuma se ta langwa'be kai tana make kafad'a...................


Juya kanshi yayi zuwa kan alkali da ya bada umarnin fara shariah Hisham ne ya taso ya fito zuwa inda haisam yake yace "malam muna son sanin cikakken sunanka" haisam yace "sunana haisam mas'ood sa'ood" murmushi hisham yayi tukun yace "kai asalin d'ansu ne ko kuwa?" Da sauri mom ta mike tana cewa "objection my lord lawyern wadda suke kara be kamata ya shiga cikin rayuwar wadda nake karewa ba sbd wancan personal life dinshi ne" judge din ya gyara glass tukun yace "korafi be karbu ba Barr ci gaba" zama mom tayi tana mamakin tambayar da hisham yayi kenan ya san wani abu....................


Kallon hisham haisam yayi sossai sai yanzu ya tuna inda ya sanshi don memory din haisam na wuya ya manta abu, haka Allah ya hallice shi ze iya tuna abunda ya faru a rayuwarshi daga shekararshi ta hud'u zuwa yau, ajiyar zuciya ya sauke tukun yace "Kamar yadda na fad'a a baya sunana haisam ban san sunan asalin iyayena ba, na tashi na ga kaina a wani gidan marayu Alheri orphanage foundation dake nan kano, a lokacin ni yaro ne Mara hayaniya kuma mara magana sossai se de baiwar ilimin da Allah ya min yasa ba wadda be sanni ba..........


Bana fad'a, bana dukan na kasa dani haka bana shiga hurumin da ba nawa ba, aboki na d'aya handball dina karami da kullum Ina tare da shi, in har anga Ina magana to da ball din nake har wasu suke zaton ko ina da matsala na Aljanu ko tabin kwakwalwa, akwai wani yaro a tare dani a lokacin da yake tsananin jin haushina sbd buge shi da nakeyi a komai...............


Yana matukar son ganin an damu dashi se kuma akayi rashin dace duk manyan gidan In sunzo haisam ne, masu aiki da yara duk haisam haisam ashe abun na ba yaron haushi, kasancewar makarantanmu, wurin wasanmu, makwancinmu, ajinmu a takaice komanmu daya abunda kenan yasa ba'a ganin kokarin yaron a komai se an kira haisam kan a kira shi duk da a lokacin shekaruna basu wuci hudu zuwa biyar ba na kasance me tsabta sabanin yaron, shi kuwa yana da cin zali, karya da iya magana, dayake ba fita ake a gidan ba se wani abu babba ya tashi, yaronnan yasha dukana bawai don banda karfin ramawar bane a'a kawai don banson magana ne nake kyale shi..............


Ba irin azaba da wulakanci da basu nuna min ba amma ko d'aga kai na kallesu bana yi, yasha sace littatafai na a lokacin exams don na fad'i amma ban ta'ba fad'uwa ba, ana haka Alhj mas'ood sa'ood yazo neman yaro ze yi adopting daga ganin motocin da ya shigo dasu ma yaran gidan suka rude kowa na son ace shi aka d'auka a lokacin ko kallon wuraren motocin banyi ba, yaron Chan na ta murna se kai kawo suke daga inda aka sauke Alhj mas'ood da hajiya Aisha..............


Yara aka fitar musu dasu maza da mata akan su zabi wadda suke so kasancewar sunce yaro karami suke so   Ni a lokacin banje ba Ina daga gefen motansu Ina ta hira da ball dina ashe har sun zaba suka zabi yaron sun fito kenan hajiya Aisha ta ganni Ina dariya da wasa da ball dina a take ta chanza ra'ayi duk da yaron fari ne tas amma na fi shi kyau sossai nesa ba kusa ba kuma rawar kanshi da yadda taga yake wa yara don ta zabeshi yasa ya fara fitar mata a rai tana kyalla ido ta ganni tace ta fasa yaron atafir se ni duk yadda mijinta yaso lallashinta amma ta ki sam suka koma suka bada hakuri tare da cike wasu takardu na adopting da sunana ban sani ba ma se aka zo aka ce in zo mu tafi................


Da tausayi nake kallon sauran yaran ina musu adu'ar Allah ya kawo musu dauki suma duk da rayuwarmu na gidan ba takura bare tsangwama, Ina shirin shiga mota kenan naji yaron ya rungume ni a kunne yadda ba wadda ze ji ya rad'a min "ko ba dade ko ba jima se na kaskantar da kai haisam, it's a game I promise".............


A lokacin ban dauki maganan da wani mahimmanci ba na watsar, daga lokacin na bude sabon rayuwa me yanci, jin daadi da farin ciki na lokaci kankani zuwa shekara biyu, Ba irin gatan da ban samu ba ta uwa ta uba har na manta da cewa ni maraya ne bansan mahaifiyata ba bansan mahaifina ba, Ammi ta sa nayi alkawari bazan fad'awa kowa cewa a gidan marayu suka dauke ko bayan ransu amma yanzu uzuri ya sa na fad'a..........


Muna cikin rayuwa ta farin ciki har tafiya ta kama mu zuwa kano anan ne aka aikata abunda har abada bazan manta ba kuma ban yafe musu ba har bayan ransu" a nan ya bada labarin kisan su Ammi yadda yaci gaba da rayuwa har zuwa yau banda yadda ya auri hamrah, anan ya fad'i yadda yake fama da ciwon zuciya tun daga lokacin har yanzu da se gaba yake karawa, ya kuma bada lbr yadda aka ajiye mishi recorder yaji tsab ya kuma tabbatar muryan Alhj mudan, Alhj halliru da kuma Dr zubair amma be san dayan ba. Da sauri hisham ya katse shi anan yana cewa "shine dalilin da yasa ka kashe su" kallon hamrah yayi tana ta kuka zuciyarshi a karye ga tuna mutuwar su Ammi ga kuma kukan hamrah a sanyaye yace "..............

#vote 

#comment

#share 'Yar mutan Adamawa💞💞💞

                     💞💞hamrah💞💞

                                                   💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin                *'yar mutan Adamawa*Page➡2⃣2⃣

************


"Ba ni na kashe su ba" Wani wawan ajiyar zuciya hamrah ta sauke tana share hawayen fuskanta, mom ma murmushi ta saki yayin da hisham ya tsaya speechless court din gabad'aya ya d'auki surutu har seda alkali ya tsawatar ta hanyar bubbuga desk dinshi aka natsu..................


Hisham ne ya juya ga judge tare da cewa "ya mai girma mai shari'ah Ina da mutane sama da ashirin da suka shedi lokacin da haisam ke fitowa daga d'akin bayan an ji Karan bindiga bada jimawa ba, sannan a ranar da police suka kama shi ya furta da bakinshi cewa shi yayi kuma akwai mutane sama da 10 a wurin, da wannan nake so koto tayi gaggawar Yankewa wannan azzalumi hukuncin da ya dace dashi"....................


Gyad'a kai alkali yayi tare da 'yan rubuce rubuce tukun ya d'ago "lawyer me kare wadda ake kara ko kina da tambayoyi da zakiyiwa me laifi?" "Akwai ya mai shariah" mikewa tayi ta isa gaban haisam tana murmushi don haisam ya saukaka mata shari'ar sossai, shi kuwa kanshi a kasa kunyar surukar tashi yake ji kaman me "malam haisam ka bamu labarin yaro a baya amma baka fad'a mana sunanshi da kuma wanene shi ba? Ya sake bibiyarka ko kuwa?"...................


Haisam yace "ai yaron ba kowa bane fashe hisham murtala maidala, Ina ga bayan bari na wurin ne Alhj murtala maidala yayi adopting dinshi" da sauri hisham yace "objection my lord, me laifi na kokarin alakanta kanshi dani sbd wata manufa tashi ta daban ni ban sanshi ba, kuma asalin mahaifina shine murtala maidala" baki sake haisam ke kallon hisham alkali be ce komai ba, ba karamin d'aure mishi kai sukayi ba.....................


Barr suhailat ce tace "haisam kace ba kai ka kashe su ba ya akayi ka fito daga d'akin jikinka duk jini?" Shi wlh har magana ya kare mishi ga kirjinshi dake zafi sossai kaman baze ce komai ba se kuma yace "bayan an turo min recorder din anyi ta turo min text msg na barazana akan kar In yadda In binciki abinda ya wuce shekaru dayawa amma naki ji...................


Sati d'aya kafin ayi kisan aka turomin sakon hotel da zasuyi meeting da su mugu da numbern room din da suka kama dama na riga da nayi alkawarin d'aukan fansa akan kisan ba tare da na sa hukuma ba, ranan na zagayowa na d'auki bindiga na dayake ina da licenses na nufi hotel din, Ina stepping kafa na cikin room d'in naji karan bindiga dayake babban floor ne kuma a ta waje suke da sauri na karasa inda suke na samu gawawwakin su I was shock sbd ban san wadda ya kashe su ba hausahin da naji na kashe sun ne yasa na rufe gawawwakin da duka ban samu na cika burin da na tashi dashi ba..............


Bayan na dakesu ne se na fito ganin mutane a tsatsaye cikin tashin hankali yasa at that moment nayi deciding daukan laifin da ba ni na aikata ba, proof d'ina kuwa shine bindiga na ba'a ta'ba har'bi dashi ba and kuma bullet na ko d'aya be 'bata ba" murmushi mom tayi tare da d'aukan bindigan ta mika don a isar dashi ga alkali, tace "ya mai shar'ah muna neman a d'aga wannan shari'ar zuwa sati ko sati biyu sbd mu kamallah had'a shedunmu" ta karasa da bowing head dinta..............


Bayan judge din ya gama rubuce rubucenshi ya d'ago tare da cewa "an d'aga wannan shariah se sati na sama, Court na bukatan ku gama harhard'a duk wasu shedunku zuwa sati na gaba rana e ta yau, court ta bada umarnin a ci gaba da tsare mai laifi har ranan da za'a sake zama, bum bum bum" courrrrrrrrt aka mike seda alkali ya fita tukun kowa ya fara fita bakin mutane cike da maganganu kowa na fad'in albarkacin bakinshi, idanunsu na cikin na juna har aka fice da haisam................. 


Cike da karfin hali suka fice kowa ya sawa ranshi In shaa Allahu haisam ze fita, haisam be iya karya ba duk wadda ya sanshi ya san wannan halinnashi na fad'an gaskiya ko da ze kasheka kuwa, bayan sun isa gidansu hamrah ne aka baje musu abinci kowa yaci ya koshi tukun suka fara shawaran me abu na gaba da za'ayi, neman proof suke ido rufe kaman daga sama sukaji mammi tace..............


"Hotel d'in akwai CCTV camera so you hv to bring it before them don suna shirin zuwa cirewa I know" cikin sanyin murya take maganan, kowa kallonta yake da mamaki ya akayi ta fara magana? Tukuna ma ya akayi ta san hotel d'in akwai cctv kuma har da suna shirin zuwa cira? Bata kara magana ba duk tambayoyin da suka mata ko pim bata ce ba, sagir ne ya mike yana cewa "bari naje muga abinyi dole su shigar dani security room dinsu and mom kema ya kamata muje dake sbd ba yadda za'ayi su hana ki bincike".....................


Charab hamrah tace "nima zani" har kaman ze ki se kuma yace "muje to" suka mike suka fice a mota d'aya suka fita sagir ke driving hamrah na gefenshi mom a baya ba'a wani jima ba suka isa hotel din direct security room suka nufa mom ta nuna musu ID card d'inta a take suka barsu suka shige sagir ya fara binciken date d'in da time d'in se kuwa gashi, ba tare da ya tsaya dubawa ba ya fitar da wani flash ya tura a ciki, hamrah ma ta bashi wani ya kara copying, ya Adana nashi itama ya bata nata ta Adana tukun ya goge footstep d'in................


Sharp sharp suka fito suka shiga mota, a hanyarsu ta komawa ne sagir yayiwa hamrah tambayar dake ranshi "ni kam kin san hisham din nan ne naga ya d'aga miki gira tare da kashe miki ido da ya shigo court" Shiru tayi kaman baza ta ce komai ba tukun tace "i was almost raped by him" wani irin birki sagir ya ciza mom ta sa salati da ihu hamrah tace "sagir sagir bayanmu" Da sauri sagir ya kalli mirror motoci uku bakake na gaban ya kusa isowa kansu da alamu buge su yake shirin yi da azama sagir ya taka motan suka fara tsere akan hanyan...................


A tsorace hamrah ke kallon mirror itama a take ta haddace plate number din motan gaban ganin sun ciro bindigu ta mirror sun fara harbinsu yasa ta kara tsurewa ga sagir se mahaukacin gudu yake kaman ze tashi sama a takaici sun d'an d'auki lokaci suna wannan hali motansu kuwa ya fara gajiya ga bullet da ake ta musu ruwanshi, sagir da ya rasa mafita se kawai ya nausa embassy dinsu na abuja...................


Hanyar ba yawaitar motoci ba mutane anan mutanen dake binsun suka kara bud'e musu wuta, da wani irin speed motan gaban ya zo ya bugi nasu gaba sukayi hamrah ta buga kanta da gaban motar har seda ya fashe ta dafe wurin tana juyawa don ganin ko mom ta samu matsala amma ganin ba abinda ya sameta yasa ta dubi sagir "why not mu kirasu incase bamu karasa ba su se su zo" da sauri sagir ya fidda wayanshi ya mika mata gashi ko bindiga be fita da ita ba kar'ba tayi ta fara lalubo sunan da ya gayamata................


Ta danna kira ring biyu aka d'aga tayi saurin sawa sagir a kunne magana yayi na mintuna biyu yace ta kashe kan ma ta kashe aka sake Dakar su se ji kake kummmmmmm motar ta kwacewa sagir ta bugi wani itace dake gefe tare da yin tumble ta fad'i kasa....................


Da gudu motocin suka juya ganin haka suka ranta a d'ari dai dai lokacin sojoji suka iso wurin kan kace me sun bisu wasu kuma suka tsaya kan motar su sagir tare da kiran ambulance, sojojin da suka bi bayan waencan sun samu sun cimma mota d'aya da kyar suka sha kanta suka samu suka kama mutum biyu dake ciki tare da juyawa suka kyale sauran don waenda suka kaman ma sun ishe su hujja...........


Ta bangaren su hamrah kuwa ba'a jima ba ambulance ya karaso da kyar aka samu aka 'balla motar tare da fito dasu kaman gawawwaki................


😰😰 bazan iya gani ba😰😰


#vote 

#share

Comment

'Yar mutan adamawa


💞💞💞

               💞💞hamrah💞💞

                                                    💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin          *'yar mutan Adamawa*


Page➡2⃣3⃣

************


Cikin tashin hankali dad da yaqoob ke zirga zirga a gaban rooms din da aka shigar da ko wannensu a cikin asibitin embassy d'in su sagir d'in yayinda Aisha, qudra da mammi ke zaune zugum kowa da abinda yake sakawa a ranshi doctors d'in sunyi at least one one hour kan suka fito na mom ne ta fara bayani "Alhamdulillah she is stable now ba abinda ya sameta se buguwa da tayi nayi mata alluran bacci nan da two hours zata farka In shaa Allahu se drugs da zaku samo mata, wani ya biyoni ya kar'bi prescriptions d'in".................


Gaba tayi abunta, har yaqoob ze juya ya bita se doctorn da ke kan sagir ya fito "ya samu kariya a kafa se jikinshi da ya bugu sossai, an gyara kariyar we pray ya gyaru da kyau" shima ya wuce kai yaqoob ya dafe yana salati dad yace "kenan wadda ya kashe su Alhj mudan ne ya kawo wa su hamrah hari don kar su kai flash din court" yaqoob yace "exactly, wannan hk yake Allah yasa basu salwantar da flash dinba am afraid" Aisha ce tace "yanzu kam they are safe here ba abunda ze same su, and in shaa Allahu flash din na nan" tana rufe baki doctor d'in wurin hamrah na fitowa..................


"Ta gurd'e a hannun hagunta sannan ta bugu sossai a kai an gyara hannun, zata jima tana bacci In ta tashi munga ba wani matsala to but kuyi adu'a Allah ya sa ba abinda ya samu kanta, se ta tashi zamuga" godiya sukawa doctorn ta wuce dad ya wuce straight d'akin da aka kwantar da hamrah ya kama hannunta me lafiyan tare da lumshe idanunshi yana adu'ar Allah sa kar ta samu wani matsala da kan Allah ya bata lfy...............


Aisha da mammi wurin mom sukayi yayin da qudra ta shiga wurin sagir zama tayi akan plastic chair tana kallon fuskanshi a cikin zuciyarta kuwa tasbihi take ga ubangiji da ya halicci wannan bawa kyakyawa haka, Yaqoob ne ya je ya sassayo magungunan kowannensu ya kai kowanne d'akin marar lafiyan tare da yad'a zango a d'akin sagir suka zauna tare da qudra kowanne yayi shiru yana tunanin duniya.....................


Bayan kwana biyar


Mom ta warke garau ba abunda ke damunta yayin da hamrah har yanzu jikin se a hankali tana yawan fama da ciwon kai kuma har yanzu ana mata dressing ciwon dake goshinta kullum wurin da bandage yayinda sagir jikinshi yayi sauki sossai kariyan ne kad'ai da har yanzu be fara takawa ba...............


Yaqoob yayi magana da chief security d'in haisam aka raba securities d'in biyu aka zuba rabi gidansu hamrah duk da suma ba laifi suna da securities kad'an, yayinda rabi suke gidan haisam d'in, An riga da an sallami mom taci gaba da harhad'a duk wani proof daze taimake su, yaqoob yaje har sau biyu yaga haisam amma be fad'a mishi abunda ya faru ba..................


***********

Court


Tunda aka shigo dashi idanunshi ke kan goshinta dake zagaye da bandage da kuma hannunta shima da bandage me ya sameta? Ya tambayi kanshi, sanye take da doguwar rigan atampha me adon stones daga sama har kasa rigan flay ne be kamata ba sam se gyale baki data yafa a kanta ba tare da ta sa d'ankwali ba, itama shi take kallo yayi rama sossai se manyan ido da karan hanci da hannu ya mata alama ya dafe goshinshi tare da juya hannun yana nufin me ya sameta.................


Murmushi ta mishi me sanyi tare da girgiza kai 'bata fuska yayi ta kara sakan murmushi kallon wurin yayi yana mamakin Ina sagir hankalinshi ne ya koma kan shari'ar da aka fara mom ce ta fara magana "ya mai girma mai shari'ia Kamar yadda muka roka aka d'aga case d'innan don samo sheda toh Alhamdulillah ga shedunmu zamu gabatar in an bamu dama" hannu alkalin ya mata alamun bismillah....................


Massive Panasonic aka fitar babban tv da ya kai 152 inch d'aya daga cikin ma'aikatan court din bangaren technology ya fito ya harhad'a mom ta bada flash drive d'in hamrah me kaman ring aka saka a take komai na d'akin ya fara haskawa, d'aya bayan d'aya suka fara shigowa duk wadda yazo cikin dariya da murna za'a bawa Juna hannu a gaisa a kuma zuba mishi abunda yake so in wine ne ko juice.................


Mugu ne ya shigo karshe kato ne me ingarman jiki daga ka ganshi zaka san rikekken d'an daba ne daga shi se vest da wando jikinshi duk tattoo ko ta Ina kanshi akwai kitso manya dukawa yayi da gwiwa d'aya yayi musu alamu na jinjina tukun ya zube kan kujera tare da fidda taba ya fara busawa, magana suka fara suna tuna baya inda yake ta zuzuta ni'imar Ammi wai har yau be samu irin ta ba ai sunyi missing suka ci gaba da magana suna ta izgilanci har lokacin basu fara maganan abunda ya kawosu ba.................


Haisam runtse ido yayi yana ciza baki inama mutumin be mutu ba ya same shi, lokaci lokaci suna duba time Dr zubair ne yace "wai ni me ya ajiye boss ne har fa yanzu be karaso ba" waya Alhj mudan ya d'auka da nufin kiranshi tussss suka ji karan bindiga mugu aka fara harba a goshi without any hesitation mutumin ya har'be Alhj halliru da dr zubair Alhj mudan ne karshe se roko yake kar ya kasheshi wlh ko nawa yake so ze bashi seda mutumin yayi dariya sossai tukun ya d'auke Alhj mudan da bindiga................


Sanye yake da bakaken kaya fuskanshi sanye da mask amma daga dantsenshi zuwa yatsunshi duk a waje suke tsalle yayi yabi ta window yana gilamawa haisam na shigowa da bindiga a hannunshi yana sand'a har ya isa inda suke tabbas gaskiya ya fad'a don yana ganin gawawwakinsu ya hau duka yana kuka sossai, 'yan court d'in wasu seda sukayi hawaye ganin yadda yake kuka kaman mace sun tausaya mishi sossai Lallai koda shi ya kashe su wlh bai yi laifi ba, "a wajensu fa kenan"....................


Ajiyar zuciya hamrah ta sauke tana d'auke hawayen idonta, mom ce ta katse sad moment d'in court d'in don har alkalin jikinshi ba karamin mutuwa yayi ba, tace "A ranar da muka je d'auko flash d'in ya mai girma mai shari'a an kawo mana hari", ta bada labarin abunda ya faru tsab ta kara da "yanzu hk an samu an kama biyu kuma sunce zasu fad'i gaskiyar wadda ya aiko su" kallon wani security daga cikin nasu tayi se ya fita suka shigo tare da sojoji da samarin biyu a d'aure irin mugun d'aurin sojojin nan sun jiggatu sossai tsabar wuyan da suka sha har canza kammani sukayi.................


Rantsuwa aka sasu suyi akan zasu fad'i gaskiya tukun mom ta tambaye su "ko zaku iya sanar mana da sunayenku?" D'aya yace "hamisu" d'ayan yace "Audu" mom tace "zamu iya sanin wa ya sanya ku aikin nan na kashe mu?" Seda suka had'iyi nyau tukun Audu yace "Alhj murtala maidala" hisham ne yace "what????? Wannan sharrine ba gaskiya bane" alkali yace "ka gyara zancen ka court kake" sa hannu hisham yayi a goshi yana sharce gumi carab a idanun hamrah zaro ido tayi zatayi magana taji hamisu na rantsuwa yace "in karya nake Allah ya karbi numfashi na anan Alhj murtala maidala ne kuma a lokacin suna tare da d'anshi wannan" ya nuna hisham................


Ran haisam a bace yake kallon hisham wato be ji magananshi ba shine ya tura a kashe mishi hamrah!!!! What sagir na asibiti a karye?? Duk sbd shi??? Bai chanchanci wannan sadaukarwa daga garesu ba kallon hamrah yayi se yaga tana kallon hisham ya rasa gane expression dake fuskanta irritation look ne ko hate one ne tsulum yaga ta mike tace.................


"Ya mai shari'ah na san wadda yayi kisan nan" kowa ita yake kallo da mamaki har mom jan glass dinshi alkali yayi ya bata umarnin fitowa ta kuwa fito ta tsaya aka bata qur'ani tace "ba se na rantse ba kowa ma anan ya sanshi" duk hankali ya koma kanta tv ta nufa ta kunna tare da mayar da slide din baya har inda mutumin yake tsaye da bindiga yana saitin mugu hannun mutumin ta nuna tana cewa.................


"Kunga wannan" ta nuna agogo da zobe tare da wani ciwo babba kaman kunan wuta a bayan hannun makashin ta d'aura da "exactly shine a hannun barrister hisham murtala maidala" ta fad'a tana kallonshi cikin ido, a take idanun kowa ya koma kanshi se sharce gumi yake ai kuwa tsab gashinan a take ya juya da niyyan guduwa ya cire riganshi da hulanshi na lawyers ya hurgar se tusssss kake ji wani police ya har'be kafanshi a take ya fad'i a wurin yana Ihun azaba..............


A yayinda haisam da hamrah suka had'a idanu tare da sakarwa juna murmushi a tare ya d'aga mata babban yatsa girgiza kai tayi tare da komawa kujeranta ta zauna handcuff aka sawa hisham aka shigar dashi bayan kanta polisawa suka tsatsaya a bayanshi, alkali ne ya bada umarnin a zo mishi da Alhj murtala maidala a take yayi waya kan ko wani offishin 'yan sanda akan a fita a tare shi da wuri In ba hk ba ze iya guduwa sbd live ake nuna shari'an, hutun rabin awa alkali ya bayar don yana da tabbacin In Allah ya yarda kan lokacin an kamo murtala maidala................


A take court ya dauki hayaniya dayake wannan karon an cika fiye da zaman farko kowa se tsinewa su Alhj mudan sukeyi yana musu fatan dawwama a wuta (subhanallah Allah ya tsare mu yasa mu cika da imani, tabbas idan mutum ya bar duniya mala'iku suna zagawa don jin me za'a fad'a akan wannan mamaci In alkhairinka yafi yawa toh tun daga nan zasu fara roka maka gafarar ubangiji In kuma sharri ne azabar Allah se ya tabbata akanka, ya Allah kasa mu bar alkahiri a bayanmu mu mutu kowa na fad'ar halin kirkinmu a gareshi, Ameen thumma Ameen).............................
#vote

#comment

#share


'Yar mutan Adamawa💞💞💞

                  💞💞hamrah💞💞


                                                   💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin               *'yar mutan Adamawa*


Page➡2⃣4⃣

************Bayan mintuna 30 an samu an kamo Alhj murtala da kyar don shirin guduwa yayi amma se Allah ya ba polisawan nasara kan ya bar Abuja sukayi ram dashi, a gaban Alkali aka gurfanar dashi Aka sa shi rantsuwa kuma ya fad'i gaskiyar abunda ya sani, fir yaki yace shi be san komai ba, ba yadda ba'ayi dashi ba yaki ga hisham dake ta aikin ihu sbd azabar zogin da kafanshi ke mishi shima aka tambaye shi ya fad'i gsky yaki sam..................


Umarni Alkali ya bayar akan a tafi dasu a tambayesu a ajiyesu a gidan horo na sati biyu a horasu har se sun fad'i gaskiya and court ta sallami haisam sbd he is not guilty he's also a victim, amma duk da haka court na bukatar shi ranar da za'ayi shari'ar karshe bum bum bum, ya buga aka mike tsaye, ya fice abinshi, murna a wurin hamrah, dad, mom, qudra, yaqoob, Aisha da mammi kaman su zuba ruwa a kasa su sha..................


Mutane se tayashi murna suke suna tsinewa su Alhj mudan iyalansu duk da sukazo kunya kaman suyi yaya a haka aka watse, kishingid'e yake a bayan mota tana zaune gefenshi yaqoob ke tukawa yayinda Aisha ke zaune a gefenshi, idonshi a lumshe ya rasa wani irin yanayi yake ciki sam ga yana jin ciwon zuciyar nan na kara damunshi hannunta yaji cikin nashi a hankali ya bud'e idanunshi se suka sauka cikin nata murmushi me sanyi ya sakar mata itama ta mayar mishi tare da kwanciya kan kafad'arshi..................


Da sauri ya zame tare da matsawa kallon tambaya ta mishi da sauri kuma ta dafe kanta tana cije baki a hankali yace "menene?"  Seda ta nyamutsa fuska tukun tace "headache amma ba sossai bane" yace "ko zamuje asibiti ne?" Kai ta girgiza mishi tare da murmushi shiru yayi sbd shi be san ance zata iya samun matsala a kai ba sbd hatsarin, har suka isa gida ba wadda ya kara magana se massaging hannunta da yakeyi.................


Direct d'akinshi ta wuce dashi dayake itama ba gidan take kwana ba da safennan ma aka bata sallama a asibiti yasa d'akinshin ba a gyare ba duk da tsab yake se d'an kura a bakin gado ta ajiyeshi ta shige toilet dinshi, gyalen kanta ta maidashi d'ankwali ta wanke bayin tsab tukun ta had'a mishi ruwan wanka me d'umi da kamshi tanayi tana tuna sanda ta had'a mishi ruwa me zafi zagin duniyan nan tana ga ba wadda be mata ba da sauri ta kau da tunanin tare da fitowa ta mika mishi towel dinshi.......................


Kar'ba yayi tare da mikewa a gabanta ya fara cire kayan jikinshi zaro ido tayi ta juya da sauri zata gudu cikin azama ya jawota ta dawo kan kirjinshi hannunshi yasa ya zagaye cikinta dashi tukun ya kwantar da kanshi kan wuyanta yana shinshuna ta cikin shagwa'ba da bata ta'ba ganin wani namiji ko jinshi dashi ba taji yace "Ina kuma zaki??? Ni ni fa ke zakimin wankan" zaro ido tayi tana jin yadda maganan yayi mata tasiri har zuciyarta a take tsikar jikinta suka fara tashi gyaran murya tayi tama rasa me zata ce..................


Murmushi me sauti yayi tare da sakinta yana cewa "tunda baza amin ba shikenan" satar kallonshi tayi ya tura lip dinshi na kasa gaba kad'an ba karamin kyau ya mata ba, juyowa yayi se suka had'a ido right eye d'inshi ya kashe mata tare da d'age gira yana tambayar yaya dai, girgiza kai tayi tare da ficewa tana murmushi shima murmushi yayi kan ya gama cire abunda ze cire ya fad'a toilet...................


Seda ta tabbatar ya shiga wankan tukun ta dawo d'akin sauri sauri ta gyara tana jin ciwon kanta na karuwa bayan ta gama ta nufi kitchen ta fara had'a mishi abunda ze ci jollof na cous cous tayi yaji veggies masha Allah ta had'a mishi zobo ta tattara ta kai dining ta dawo ta gyara kitchen d'in tana stepping foot d'inta out yana fitowa daga room d'inshi kallonta ya tsaya yi se yaga kaman tana layi a hankali ya nufe ta kan ya karasa ta tafi luu zata fad'i da sauri ya tare ta tare da rungume ta a jikinshi yana bin fuskanta da kallo a hankali ta bud'e idonta da sukayi jaa tana kallonshi ta kara mayar wa ta lumshe....................


Muryanshi a d'an birkice yake cewa "Hey Noory Are you alright?" Bata amsa ba ji tayi yasa hannu ya d'aga ta chak zuwa d'akinta a kan gad'o ya shimfid'e ta shima ya hau ya zauna kusa da ita Yana feeling temperature d'inta jikinta yayi zafi sedai ba sossai ba tamabayarta ya karayi a hnkli tace "kaina" se kuma ta fashe mishi da kuka rudewa ya so yi ya rasa ma me ze mata Chan kuma se yace "tashi lets go hospital" kai ta girgiza mishi a hankali tace "in nayi wanka na sha magunguna ze dena In shaa Allah" da kanshi ya shiga bayin ya had'a ruwa ya taimaka mata tayi wanka se nonnokewa takeyi shiko ko a jikinshi ba tare da ya shafa mata mai ba ya fesa mata turarukanta ya samo mata simple riga ta saka chak taji ya d'aga ta suka nufi dining tana dariya tace "nafa ji sauki ni ka sauke ni zan iya tafiya" be tanka ta ba har sukaje ya ajiye ta a kan kujera ya koma d'akinta ya d'auko magugunanta da mamaki take kallonshi haisam ke mata duk abubuwan nan? Allah sarki duniya tana cikin tunanin rayuwa taji yace "haaaaa"..................


Bud'e baki tayi ya zuba mata abinci da kanshi ya d'inga feeding d'inta har ta koshi ya bata zobo tasha seda tasha sossai tukun ya bata magani da ruwa ta had'iya kallonshi tayi tace "baka ci ba kai" kallon abincin yayi ya kuma kallonta se yayi murmushi yace "zanci you know you are a great cooker, I really missed your cooking" se ga hamrah ta fara blushing bata ta'ba jin ya yabi girkinta ba se yau kai ko a fuska bata ta'ba gani ba tana nan zaune har ya gama ci tukun ya taso ya d'aga ta waro ido tayi tana cewa "ikon Allah yau kam bazan yi tafiya bane a gidan nan?"......................


Yana murmushi yace "yeah baki jin daadi don hk shut up kar ki sake cewa komai" Shiru tayi tana kara jin kaunarshi har ranta d'an kulawan da ya bata nan ya kara tabbatar mata da Lallai yana sonta yadda ya fad'a a kan gado ya kwantar da ita tare da d'an kara Acn d'akin ya sa mata borgo yace "Ina ga stress ne ya miki yawa ya kuma had'u da ciwon dake kanki you have to get enough sleep and rest in kika tashi in shaa Allah you will be ohk" kai ta gyad'a tare da lumshe idonta a goshinta ya mata peck tare da fara bubbuga bayanta kaman baby har bacci yayi awon gaba da ita................


Fita yayi ya koma d'akinshi ya kwaso wayoyinshi ya kunna duk da be son kunnawan yasan damunshi za'ayi da call Ai kuwa yana kunnawa calls suka fara shigowa yana amsa call din har ya fita yana kashe wannan wannan ze shigo da hannu ya nuna ma securities dinshi motocin da zasu fita dashi suka d'auko ya shige ba tare da ya nemi yaqoob ba yasan shima yana bukatar hutu a haka yana wayan ya fad'a musu inda zasu har suka isa yana waya seda ze shiga d'akin da sagir yake ne tukun ya kashe.....................


Da sallama ya shiga suna had'a ido sagir ya sakar mishi murmushi to his greatest surprise se yaga haisam ma ya mayar mishi ya manta kafin abubuwan nan su faru ance haisam ya fara murmushi a hankali haisam ya tako cikin takunshi na isa da izza ya karaso bakin gadon yayi hugging sagir suka bubbuga bayan juna a tare tukun suka saki juna sagir yace "congrats friend amma nayi farin cikin ganin ka free ba laifin komai a kanka indeed your wife is a blessing".................


Kai haisam ya gyad'a yana murmushi shima yasan yayi dacen mata Akwai yin Allah amma da ba don hamrah ba da ze iya cewa da yanzu baya duniya kallon kafan sagir yayi tukun yace "sorry friend duk sbd ni ne hakan ya........" katse shi sagir yayi da "haba haba haisam don wannan abu ya sameni se kace sbd kai? Gsky banji daadi ba me abun bani hkr anan" Shiru haisam yayi yana tuna lokacin da yake cewa hamrah ba me sonshi a duniya da sagir yaji kam da ya yanka shi d'anye....................


Sun jima sossai suna hira har mai aikin mom ta kawo abinci ba yadda sagir be yi dashi ba yaki ci, ganin yana ta kiran hamrah bata d'aga bane yasa yayi tunanin baccin ne har yanzu amma duk hankalinshi ya koma kanta sagir ne ya lura dashi yake tambayanshi lafiya don be ta'ba ganin haisam ya damu da kiran wani ba In ya kira sau d'aya baka d'aga ba shikenan tambayarshi yayi amma se yace "babu" shiru sagir yayi yana cin abincinshi hknli kwance..................


Bayan ya bar wurin sagir gidansu hamrah yaje don yiwa mom godiya sossai suka mishi nasiha for the first time bayan girmanshi ya zauna yaji nasihan na gaba dashi kuma sossai ya shige shi bayan ya bar wurinsu ne ya nufo gida da sallama ya shiga parlorn kasa qudra ce tsaye yayinda mammi ke zaune kan kujera kaman lalla'bata takeyi amma be san akan me ba..................


Qudra ce ta gaishe shi ya kuwa amsa da murmushi ta mishi jaje nan ma murmushi kawai yayi yana cewa "ya akayi ne?" Tace "wlh mammi ce tun da muka dawo daga court taki taci abinci muje ma tayi wanka taki d'an sallahn da takeyi ma yau taki" yana kallon mammi yace "dama tana haka ne?" Tace "eh in har ta d'auki sarkan kafan nan ta rike toh ranan gabad'aya duk abunda takeyi baza tayi ba kuma ta ringa kuka kenan yau ne ma naga batayi kukan ba"..................


A hankali ya kai idonshi kan sarkan gabanshi na fad'uwa wani abu na dawo mishi a rai kaman ya ta'ba ganin abun nan sede ya manta a ina kuma yaushe ganin kallon da yakewa zobben yasa ta boye kayanta ajiyar zuciya ya sauke tukun ya nufi kujeran ya zauna gefenta dayake three siter ne ya kalli qudra tare da cewa "kawo abincin" d'aukowa tayi ta kawo mishi ya amsa da kanshi ya fara bata ga mamakinsu kuwa se suka ga kar'ba seda ta koshi tukun ta kau da kai...................


A hankali yasa hannu ya riqe nata ya mike se itama ta mike murmushi yayi tukun ya mikawa qudra hannun ta sa cikin nata ta ja ta zuwa daki shi kuma ya nufi hawa sama a bakin step na karshe ya kalleta seda ya lumshe ido ya sauke ajiyar zuciya tukun ya kara budewa a fili yace "masha Allah" tare da sakar mata murmushi itama ta mayar mai tana baya baya seda ta isa tsakiyar parlon tukun ta tsaya a dai dai lokacin shima ya gama haurowa wurinta ya nufa tare da rungumeta a kunne ya rad'a mata "you are my happiness" murmushi tayi hannun shi yasa a goshinta jin temperature d'inta normal yasa yace "ciwon kan yayi sauki ko?" Kai ta gyad'a ya d'an bata fuska yana cewa "rowan muryan Akemin" murmushi tayi tana cewa "ni na isa? Me abu da abunshi" murmushi ya kuma yi yana cewa "I'm tired lemme fresh up yau zaki bani labari" murmushi kawai tayi ya wuce ta bi bayanshi ta had'a mishi ruwan wanka ta fice....................


Yana shiga toilet d'in yaji kanshi ya fara sarawa wani abu na dawo mishi hazo hazo a ido kai ya dafe yana ambaton sunan Allah ya rasa menene yake son tunawa da yake sa shi jin fargaba da fad'uwar gaba da kyar yayi wanka ya fito ya saka three quarter da bakin vest ya hau gado tare da lullubewa da bargo yana jin tsoron kar abunda yake son tunowa ya kara jefa shi a wani matsalan abunda kenan ya haddasa mishi zazzafan zazzabi na lokaci d'aya.......................


•kuyi hakuri plz abubuwan ne se a hankali se kun kara hkr dani•

#vote


#share 


#comment
'Yar mutan Adamawa 💞💞💞


                 💞💞Hamrah💞💞
                                                  💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin          *'yar mutan Adamawa*


Page➡2⃣5⃣

******


Bayan wasu kwanaki 


Gabad'aya haisam ya rasa natsuwar shi da hankalinshi, ba yadda be yi ba don ganin ya kawar da gizo da kwakwalwarshi ke mishi amma ya kasa, ya sakli kanshi gabad'aya duk abunda da yakeyi yanzu be yi, tun ranar da suka dawo court be sake fita ko parlorn saman ba yana kwance a d'aki ko yaushe..............


Sossai kuma abun ke damun hamrah adu'a take Allah yasa ko me ze sake zuwar musu ya zo da sauki kwanan shi biyar kenan a wannan hali yaqoob yazo yayi iya abunda ze iya amma inaa haisam be saurare shi ba haka ma an sallami sagir sede har yau be samu daman zuwa wurin haisam d'in ba amma kullum ze kirashi ya fad'i me ke damunshi ma ya kasa............


Abun ya ishi hamrah yau kam tayi niyyan In shaa Allahu se ya fad'a mata damuwarshi ko zata iya taimakonshi ya warware, da tray d'in abincinshi ta shiga tare da sallama a can kasan makoshi ya amsa mata ta shigo a kan stool d'in dake gefen gadonshi ta ajiye tare da hayewa gadon ta janye bargon da yake ciki sanye yake cikin Armani wears sky blue da fari yayi kyau sossai d'an zaman da yayi a wuri d'aya sede yayi wanka yaci ya kwanta yasa fatanshi yin wani fresh amma raman nan na nan sede karuwa ma da yayi ko morning training da yake yi da yanzu sam be yi...................


Yana dafe da kanshi da yake ji kaman ze fashe tsabar ciwon da yake mishi abun na mishi kaman wadda yayi losing memory d'inshi yana tuna wasu abubuwan, seda ta zauna da kyau a kan gadon tukun ta had'a kai da gwiwa ta fashe mishi da kuka bilhakki sbd abun ya Ishe ta, a hankali ya bud'e jajayen idanunshi ya zuba mata sun kara girma se wani lumshe su yake yi tausayin ta ne fal a ranshi kaman yadda tausayinshi ke cike da ranta..............


Gani yake bata dace dashi ba she needs someone that will make her happy and feel special shi gashi ya gaza, hannu yasa ya janyo ta jikinshi ya rungume ta tsam yana shafa daga kanta zuwa gadon bayanta seda tayi kukanta ma'ishi tukun tayi shiru tana sauke ajiyan zuciya sossai kukan ya ta'ba shi be ta'ba sata farin ciki ba a rayuwa kullum shine dalilin kukanta ji yake kaman shima yayi kukan tsabar yadda ranshi ke kuna...............


Muryanta yaji tana cewa "during the journey of life, everyone goes through times of failure, pain and suffering, only those who have the gots to get up and continue with their journey emerge victory" matse ta ya karayi a jikinshi yana jin maganganunta har ranshi jikinshi ya fara mutuwa ta kara cewa "haisam plz for goodness sake let all your troubles and pain motivate you to move on, it's only then, will you be able to get up and carry on with your journey of life more stronger than before, you know you are the most strong man I've ever known..............


My love, the harder you fall the more intense should be your passion to succeed, opportunity ze iya zuwar maka amma In ka kuskura kayi accepting defeat you might not get to see what life has in store for you, man up your mind, body and life you will be happy in shaa Allah" be ce komai ba amma ta tabbatar maganganunta sun shige shi ganin yadda jikinshi yayi sanyi sossai zamewa tayi ta mike ta zauna tana cewa "sit up and eat kafin abincin ya huce"...................


Mikewa yayi ya zauna ta sauka tayi serving d'inshi meatballs ne da kidney sauce se kuma lemon mix drink da ta had'a mishi da kanta ta ringa bashi har ya koshi ta mika mishi cup din ya karba ya sha sossai duk idanunshi na kanta har zata mike ya jawo ta ta dawo inda take bata yi tsammani ba taji well tender fingers d'inshi a fatar cikinta seda taji wani mugun shock ta zaro ido tana kallonshi se yadda tayin ya bashi dariya har be san sadda ya murmusa ba yace "hey matsoraciya ni ba wani abu zanyi ba I want to know ko kinci abinci ko baki ci ba"................


Ta bata fuska tare da turo lips tace "shine zaka tsorata ni, ni na koshi" with so much adoration yake kallonta kaman wata baby doll don ya ja maganan yace "lies ji cikin ki fa kaman ze had'u da baya Anya ma kina cin abinci!!"  Kara turo lips din tayi tana jin daadin ganin kaman ya d'auki maganganunta don gashi yana kokarin sakewa da ita sossai, ganin ta tafi duniyar tunani yasa ya tafi da hannunshi kaman ze haura kirjinta se kuma ya dawar ya cakwali cibiyar ta zillo tayi tare da fad'awa kanshi tana dariya......................


Shima murmushi yayi kan ya gyara ta a jikinshi ya matsa yayi serving abincin ya fara bata tana karba daga kwance a kan kirjinshi abunta se shagwa'ba take zuba mishi son ranta, inda bata san 'barnan da take mishi ba   Da ta sani da bata makalkaleshi haka ba a hk har ya gama feeding dinta suka ci gaba da hira kad'an kad'an tana tambayarshi rayuwarshi na baya abunda ya shige mata duhu se ya mata dalla dalla................


Wani tambaya ta mishi da ya bashi dariya sossai ganin yadda tayi da fuska yasa ya gimtse dariyan yayi shirin tsokananta tambayar da ta mishi ya kara maimaitawa "kayi 'yan mata dayawa?" Yace "yap Ina da 'yan mata goma shabiyu, how can you see a handsome and hot guy like me ki tambayeni Ina da 'yanmata!!" a take ta had'iye duk wani annurin dake fuskanta tana jin zafin maganan sossai a zuciyarta tana kuma da na sanin tambayarshi da tayi don kara kular da ita se yace "biyu Christians ne, uku fulani, biyu hausawa, uku" to his greatest surprise se yaga ta fashe da kuka tsakaninta da Allah tana murza ido tana turo baki...................


A zuciye ta mike ya jawo ta ta dawo kan jikinshi yace "subhanallah hamrah, I'm sorry I was just kidding, I didn't meant to hurt you am sorry" ko kulashi batayi ba se ma fisgewa da take ta kokarin yi ya rike ta tsam se ta koma kan kirjinshin ta ci gaba da kukanta don sossai taji haushi a zuciyarshi yace cewa "na shigesu, hamrah bade kishi ba" ganin bazatayi shiru ba yasa ya juyata kasan shi ya haura samanta tare da sa babban yatsan shi yana share mata hawayen a lokaci d'aya ya Kure bakinta data turo gaba tana zuba ruwan shagwaba Da ido.................


He feel like kissing her ba tare da ya gama tunanin ba kawai yayi jumping into conclusion, a natse ya had'e bakinsu ya fara kissing d'inta slowly and passionately runtse idanunta tayi tana jin yadda soft and fresh tongue d'inshi dake kamshin u fresh mint daya jefa a bakinshi bayan ta gama bashi abinci yake yawo cikin bakinta with passion, butterflies taji suna yawo a cikinta har bata san sadda ta kara kankameshi ba tana manna shi da jikinta...............


Ganin ya fara sake layi yasa a tsorace ta zame jikinta tana sauke numfashi ga kunyar shi da ya dirar mata, ta sake jiki tayi ta amsan sakonshi murmushi yayi tare da maidata kan kirjinshi shi kuma yasa kanshi a pillow cikin kasa da murya yace "you have always stood by me in my most difficult time, I will like to thank you for your gratitude and time, thanks noory you are the most happiest thing that ever happened to me in my life I love you"...................


Tana murmushi ta kara shigewa jikinshi ya sa hannu ya rage musu hasken d'akin yana cewa "oya lets sleep" a shagwa'be tace "ban iya baccin rana bafa" yace "ki koya" a cikinshi ta ringa yawo da hannunta duk wai don ta tsokane shi yana jinta ta kuma mishi babban tsokana amma se yayi shiru kaman be ji, da kanta ta gaji tayi bacci yana murmushi ya gyara mata kwanciya tare da kurawa fuskanta ido yana tuna duk wani moment din rayuwansu a haka bacci yayi awon gaba dashi..................Wata mata ce zaune a cikin wani bola babba rike da wani yaro d'an shekara be wuce biyu ba, dukanshi take iya karfinta daga gani mahaukaciya ce tana dukan tana masifan ze sake cinye mata abincin da ta ajiye, se tsala kuka yake yana kokarin fisgewa ya gudu se Ammah, Ammah yake ta maimaitawa d'ayan hannunshi kuma ball dinshi ne karami green me grasses a jiki wasu mutane ne suka wuce a mota da wani uniform a jikinsu da alamu forces ne har sun wuce suka dawo suka diddiro................


Kan matar nan sukayi suka sa hannu don fisge yaron nan, rungume shi tayi tana kuka tana girgiza kai da karfi suka fisgo shi kafan mamarshi ya rike shima yana kuka yana kiran Ammah, Ammah a kan kafan akwai wani sarkar kafa gold ne me shegen kyau da sheki, shi ya rike gam yana ta kuka har sarkar ya tsinke anan suka samu daman d'auke shi a wurin ya jefar da sarkar yana ta kuka amma ball d'inshi na kirjinshi a manne suna ji suna gani aka rabasu, mutanen suka kaishe bakin Alheri orphanage suka jefar dashi sukayi gaba me gadi ne yazo ya d'auke shi ya shige dashi ciki ya sha kuka se ajiyar zuciya yake saukewa yana kiran Ammah..................


A mugun firgice haisam ya farka daga mafarkinshi har seda hamrah ma ta tsorata ta farka jikinshi se rawa yake rikeshi tayi tana cewa "innalillahi wainna ilaihi rajiun, Auzibillahi minashaid'anir rajeem, hasbunallahu wa ni'imal wakeel" sau uku ta maimaita tukun shima ya kar'ba yana maimaitawa har seda ya samu natsuwa tukun ya zame ya kwanta a kan kafanta yana had'a puzzles na mafarkin shinnan, Ammah ya maimaita, ball d'inshi, sarkar da ya gani a hannun mammi five days back, Alheri orphanage home................


Da azama ya mike ya dira daga kan gadon tare da jan hannun hamrah itama saukowa tayi tana tambayarshi lfy be amsa ba se waje da ya nufa bayan ya sake mata hannu bayanshi ta bi suka nufi kasa da sassarfa yake sauka yana karasa sauka suka had'a ido da ita sun kai two mins suna kallon juna kafin murya na rawa yace ".........................#vote

#share

#comment

'Yar mutan Adamawa💞💞💞
                  💞💞Hamrah💞💞                                                   💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin              *'Yar mutan Adamawa*


Page➡2⃣6⃣

***********


"Am.......maah" kai ta gyad'a mishi tana zubda hawaye da mugun gudu ya karasa gabanta tare da sa gwiwowinshi a kasa ya kwantar da kanshi kan cinyarta se kawai ya fashe da kuka sossai, itama kukan takeyi da sauri qudra ta fito da mugun mamaki take kallon namiji kaman haisam na kuka haka kuma akan kafan mamminta? Kodai wani abu ne ya samu hamrah jin shesheka a gefenta yasa ta juya Ai kuwa hamrah lafiyanta bata gama tunani aka shigo parlorn yaqoob ne da sagir suka shigo sagir na dogara sandarshi a hankali...............


Turus suka tsaya suna kallon yadda haisam ke kuka sossai duk jijiyoyin jikinshi sun tashi ya kankame kafan mammi kaman his life depends on it, itama se shafa kanshi take tana hawaye da kyar ta tsayar da kukanta tace "haisam my son" da mamaki 'yan parlorn duk suke kallonta ta kara da "calm down it's okey you got me" kalamai masu sanyi ta ringa fad'amishi cikin harshen turanci har yayi shiru ya kuma d'ago tasa hannu ta share mishi hawayen fuskanshi tana murmushi shima murmushin ya mayar mata.....................


Zuciyarshi fal farin ciki "he got his mom" amma abunda ya bashi mamaki jin yadda take turanci ascent d'inta ma ba na nigeria bane qudra ce ta matso tana cewa "subhanallah kar de an koma gidan jiya" tana nufin haukan mammi ya dawo sbd abun akwai d'aure kai rana tsaka kawai mammi ta kira haisam d'anta it's unbelievable......................


Batayi mamakin turancin mammin ba sbd ko a haukanta In ta fara zuba turanci da larabci ko mutane masu wucewa se sun tsaya kallonsu da mamaki mammi ce ta kalli qudra tare da cewa "ko d'aya habibty Ina cikin hankali da tunani na" qudra tace "amma mammi taya yaya haisam ze zama d'anki?" Kallon mammi yaqoob, sagir da hamrah suka yi don tambayar da ke ransu kenan kuma taya haisam ya ganeta................


Tana murmushi tace "son" ya d'ago tace "oya man up hawayen ya isa kuje kuyi sallah ku dawo I will give you guys my complete story" gyad'a kai sukayi yaqoob yazo ya taimakawa haisam ya mike suka fice jin ana kokarin tada sallah murmushi mammi ta sakar Wa hamrah har zuciyarta tana son daughter-in-law d'inta sbd duk wani abunda ya faru na court tana sane tana kuma cikin hankalinta taga irin gwagwarmayan da hamrah tayi akan d'anta don zama na farko da akayi a wurin ne ta gama gane haisam d'anta ne...................


Hamrah ma murmushi ta sakar mata tare da juyawa don gabatar da la'asar itama se taji mammi tace "daughter-in-law" juyowa hamrah tayi tana cewa "na'am" a rarrabe sbd taji sunan wani banbarakwai mammi tace "ya kamata ki kira su mom d'inki sbd suma su san waye asalin surkinsu" hausan ta wani iri daga ji bata wani kware sossai ba murmushi hamrah tayi tana cewa "tohm" ta juya ta haura seda ta kira su mom ta gayamusu abunda ya faru In brief suka ce zasu zo yanzu tukun ta shige toilet don gabatar da alwala....................


A parlorn kasa kuma baki sake qudra ke kallon mammi bata ankara ba taji mammin ta rike mata hannu tare da janta suka shige room d'insu a bakin gado ta zaunar da ita tare da shigewa bayi don gabatar da alwala seda tayi ta fito tukun qudra ma ta shiga.................


**************

Bayan kowa yayi sallah su mom ma sun hallara kowa yana zaune a parlorn kasa a natse haisam na daga kasa ya mayar da kanshi kan kafan mammin ta ci gaba da shafa kanshi yayinda qudra ke zaune dab da haisam d'in hamrah na kusa da mom da dad dinta rike da hannun dad bayan ta kawo musu d'an abun ta'bawa da ruwa da drinks, sagir da yaqoob suna zaune daga gefe suna kallon mammi magana ta fara kamar haka:-


"Sunana Queen Noor el-Hussein of Hashemite kingdom of jordan, jordan qasa ne na larabawa da mafi rinjayen Addini shine musulunci is located at western Asian Jordan is bordered by Saudi Arabia to the south and east, iraq to the north-east, Syria to the north and Palestinian West Bank to the west, the Dead Sea is located at the western borders of the country and Red Sea In extreme south-west ...................


An haife ni a babban birnin Jordan me suna Amman mahaifina is hand to the king na lokacin wato Abdallah I, na tashi a cikin kingdom hannun Anty na wadda nake nieces a gareta da ita da mahaifiyata ya da kanwa uwarsu d'aya ubansu d'aya, mu hud'u ne a gidanmu duk mata nice ta biyu, tunda aka haifeni Queen Raiyah ta d'auki son duniya ta d'aura min har ya zamana iyaye na sun bata ni tun Ina shekara uku...................


Tana da d'a kwaya d'aya d'an shekara bakwai Abdallah A Abdallah wadda shine crown prince a lokacin, Abdallah na matukar sona soyayya irin ta 'yan uwantaka duk wadda ya ta'bani to se ya rama min, inde ka ganni to dole Abdallah na wurin nima sossai nake kaunarshi a matsayinshi na d'an uwana ya shagwa'ba ni sossai wadda hakan ke ma Queen Raiyah daad'i sossai, asalin iyayena kuma basu so hakan ba amma ba yadda suka iya tunda sun riga sun bada ni.................


A haka har na shekara 19 yayinda Abdallah II wato crown prince yana da 23, ya gama degree d'inshi a yayinda lokacin ne ni kuma nake kokarin had'a nawa daga lokacin ne rayuwa na ya fara shiga matsala da damuwa wadda da ban sanshi ba sanadiyar soyayya da Abdallah ya zo min dashi ni kuwa har ga Allah bana sonshi irin so na aure sede na 'yan uwantaka...................


Ina da saurayi na da muke matukar son juna lecturer d'inmu ne zeyi 30 a shekaru d'an kasan nigeria ne yace min shi fulani ne daga garin Adamawa ta nigeria, duk da ban san wuraren ba amma na yarda dashi sossai kaman yadda fatanka yake haisam haka fatar mahaifinka, shi ba fari ba yafi chocolate haske sossai baza ka ta'ba banbance fatanshi ba kyakyawa ne sossai na karshe kuma yana da zafi, yana kuma da riko da wuyar manta abu a rayuwanshi..............


Sossai nake sonshi shima haka asalin sunan shi Dr. Umar faruk, soyyayar da  Abdallah ya zo min dashi shine cikas na farko a soyyayata da Umar faruk duk da bana boyewa Abdallah komai na rayuwa amma na boye mishi soyayyata da Umar sbd Ina tsoron su ce basa sonshi kasancewar shi bakin fata ai kuwa hankalin kowa seda ya tashi sbd yadda Abdallah ya birkice yake neman kashe kanshi sbd soyyayata ni kuwa na kekashe kasa nace ni bana sonshi, mamaki kuwa mutane sun sha shi har sun gaji..................


Babban abun mamakin shine yadda mahaifiyarshi wacce muke cewa Ummi tace sede Abdallah ya mutu In ze mutu don baza tayiwa 'yarta dole ba kaman yadda yake d'anta haka nima nake 'yarta kowa na jinjina karfin halinta da karamcinta duk da yadda take son Abdallah amma tayi biris kaman abun be damunta, ana haka iyaye na suka aiko na je bayan naje suka sani a gaba da nasiha da fad'a akan kar na ma umminmu butulci ko bana son Abdallah na yarda na aureshi daga baya ai zan soshi..............


Suma ce musu nayi ni inada da wadda nake so anan suka tambayeni waye nace musu Umar d'an nigeria ne tun kafin na karasa Amminmu ta d'auke ni da mari ta fara fad'a kina hauka ne? Yanzu da ki auri d'an uwanki kin gwammace ki auri bare? Barenma ba balarabe ba bakin fata? To baki isa ba bada nyau na ba, Abbun mu ma fad'a sossai ya min, da kuka sossai na dawo kingdom..................


Inda na fad'i akan cinyar ummi nayi ta kuka kaman raina ze fita itace ta ringa rarrashina tana bani baki akan ba wadda ya isa hanani auren wadda nake so ko da kuwa a bangon duniya yake inde musulmi ne da haka hankalina ya kwanta na mike Ina share hawaye na carab muka had'a ido da Abdallah dake kwance akan doguwar kujera yana jin mu da kallonmu.................


Ya ban tausayi yadda ya rame amma se na basar sbd soyyaya gaskiya ce, Abdallah kyakyawa ne na karshe fari tas bazan ce yafi Umar ba sbd kowanne a cikinsu na da baiwar kyanshi na daban, mahaifina ne ya samu King Abdallah I wato Abbi da shawaran kar a wani kula da lamarina duk yaranta ce da rashin sanin ciwon kaina shi gaba yake hangowa gwara a aura mata wadda ke sonta akan wadda take so shine kad'ai gatan da zamu mata...................


Da shawarwarin Abbu Abbi ya amince da aurenmu da Abdallah, duk wani bidiri da akeyi Umar faruq be sani ba, ba yadda na iya hk Ummi ma taso a auramin wadda nake so amma an fi karfinta a hk aka d'aura aure na da Abdallah kaman zan had'yi rai na mutu auren was so silent da mutane kad'an ne kawai suka sani, an kaimin hadimai amma na koresu suka koma part d'insu kuma naki nayi komai...................


Abdallah shi ke mana komai har girki sbd ya iya tare ummi ta koya mana duk wani aikin gida, Ina kame akan kujera ze zo yayi shara yayi mopping ya girkamin inci In kaya na yayi datti ya had'a da nashi ya bada a wanke mana a kuma goge ya dawo ya shiryamana a haka har mukayi wata uku sharrin zuciya yasa na fara tausayawa Abdallah ganin da gaske yake sona duk da fa soyayyarmu da Umar ko girgiza be yi ba to be san an aurar dani ba na tabbatar da ya sani da wlh se ya rabu dani................#vote

#share 

#comment'Yar mutan Adamawa
💞💞💞


                 💞💞Hamrah💞💞

                                                  💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin        *'yar mutan Adamawa**It's my day, Alhamdulillah Am +1, pray for me🙏*Page➡2⃣7⃣

************

Da kyawawan hali irin na Abdallah aka ce zuciya tana son me kyautata mata har Abdallah ya karbi hakkinsa a gareni for the first time bayan wata uku da aurenmu nayi kuka sossai inda hakan me makon ya sa min soyayyar Abdallah se ya dasa min tsanar shi sossai wadda ko kafin aurenmu ban yi mishi tsanar nan ba.............


Na dauke mishi wuta ko kallonshi banayi, kullum In na tafi school daga safe toh se yamma sossai zan dawo ko da banda lectures haka zamu yini muna shan soyayya da Umar ba wai ban san haramcin hakan ba A'a sharrin shaidan dana zuciya, Akwai 'yar wani daga cikin fada dake mutuwar son Abdallah sunanta Raina ta tsaneni sossai In mun had'u toh se habaici da zagi duk da bana kula sbd na tashi da jinin sarauta da mulki irin na Queen Raiyah wadda ko Abdallah baze nuna min ba ga miskilanci wadda mutane dayawa suna d'auka iyayi ne da girman kai tunda Abdallah da yake namiji ma be yi miskilanci ba se ni mace.................


Raina level d'inmu d'aya school d'inmu d'aya haka department dinmu 

Ganin yadda muke Shan soyayya a school da Umar yasa ta fara neman hanyan da zata raba mu da Abdallah dan ta samu aurenshi tana cikin shirinta ciki ya bayyana a jikina inda nayi bakin ciki sossai yayinda su Ummi da Abdallah farin ciki kaman suyi yaya cikina nada wata hud'u amma sam be fita ba in ba ka sani ba ko fad'a maka akayi ba zaka yarda ba..................


A lokacin tafiya ta kama Umar ze je Amsterdam wani course na wata 6 ina kuka da komai ya lallabani ya tafi, tafiyanshi da wata biyar na haihu 'yan biyu bayan wahalan da nasha kaman bazan rayu ba Hassan d'in yazo ba rai inda akayi naming d'ayan el-hussein yana da wata biyu Umar ya dawo zaku sha mamaki idan nace muku tun randa Abdallah ya fara sanina mace ban kara yadda wani abu ya had'a mu ba har Abdallah yayi watanni hud'u.................


Ranar da bazan ta'ba mantawa ba a rayuwa na da abubuwa suka had'e min a lokaci d'aya farin ciki da kuma bakin ciki, ranar ne na rubuta last paper na a school na gama jami'a bayan na fito daga paper muka samu restaurant ni da Umar muka zauna yayi mana ordering abinci muna ci muna zuba soyyayya har lokacin Umar be san nayi aure ba balle haihuwa zan iya kirga sau nawa na ba el-hussein nono duk da irin son da nake mishi amma laifin ubanshi ya shafe shi...................


Ashe bayan fitana an turawa Abdallah hotunanmu da Umar a wurare daban daban na shakatawa da cin abinci cikin soyayya da farin ciki wadda hakan ya so buga zuciyarshi a take ya mike ya fita da keyn mota a hannunshi be ta'ba jin bacin rai a kaina ba a rayuwarshi irin ranan Address d'in inda muke yanzu da aka turamishi ya nufa to his greatest surprise muna zaune muna zuba soyayya har a baki Umar ke ban smoothie Ina sha muna dariya................


Yana zaune kaman zuciyarshi ze buga har muka gama muka mike Umar ke tambayana se Ina? Ina tura baki nace mishi se park Ina son kallon wasan yara da Animals kallon jikinshi yayi yace gaskiya bazan je park haka ba da suit se kace nina kawo boko duniya muje ki rakani apartment dina na sauya kaya, hararan wasa na sakar mishi ina cewa ko sauka daga mota bazan yi ba a haka muka nufi apartment dinshi a wani building me hawa 12 yana hawa na 8..................


Abdallah na bin bayan mu har Chan Umar na murmushi ya sauka a motar yana cewa 15 mins ya min kad'an Allah ki karamin nace naki ina ta kokarin ganin wacece ta tsaya daga kofan da nake zaune In baka lura ba zaka ce daga motar ta fito hk Abdallah ma da be lura ba duk ya d'auka ni ce ya fiddo wayanshi ya d'auka a hoto, Umar na zagayawa yarinyar ma ta zagaya suka had'a tafiya kaman tafiyansu d'aya dayake daga bayanmu Abdallah yake sam be ga fuskar ba..................


Seda Umar ya shafe 25mins kafin ya fito yana dariyan wayan da ya gama yanzu a elevator da babanshi Abdallah na ganinshi da wani kaya na daban kuma yana dariya be jira yaga fitowana ba a zatonshi fa kenan yaja motar da mahaukacin gudu ya wuce yana kuka kaman mace, tsab na gane motar amma ko a kwalan riga na muka wuce da Umar se yamma likis na dawo gida.................Ina shiga na samu Abdallah kwance a kan kujera zazzabi ya rufe shi se rawan d'ari yake da sauri na isa gareshi na d'aga el-hussein dake kuka akan kirjinshi na sa hannu zan ta'ba goshinshi da wani irin tsawa da ban ta'ba jin Abdallah yayi ba yace karki kuskura kar ki soma ta'ba ni da wannan kazantaccen hannun naki, da mamaki nake kallonshi zanyi magana ya dauke ni da mari for the first time a rayuwarmu gabad'aya da Abdallah...............


A lokacin ya fisge d'anshi ya jefe ni da bakaken maganganu da ni sam ban fahimci me yake nufi ba tare da min saki d'aya, duk da wlh naji daadin sakin amma se jikina yayi sanyi da na gane Abdallah zargi na yake da zina da aurena, kuka sossai nayi ban tsaya d'aukan komai ba na fice zuwa part d'in Ummi Ina kuka na fad'a mata Abdallah ya sakeni a rude ta kira Abbi dasu Abbu na aka tambayi Abdallah me yasa ya sakeni amma fir yaki magana har marinshi Ummi tayi amma yaki cewa komai se hawaye ni kuma nace ban san me na mishi ba.................


Iyayena sun bashi goyon baya sossai suka kuma bani laifi duk da basu san me ya faru ba inda iyayenshi suke bayana a take a wurin Abbi ya ba shi umarnin mayar dani amma ya kekashe yace sam wlh baze maidani ba ya rabu dani kenan da mamaki suke kallonshi amma bud'an baki na nace dama ba sonka nake ba na dubi Abbi nace Dan Allah Abbi wannan karon ku auramin wadda nake so, Abbi yace haka za'ayi daughter ki ce mishi ya turo..................


Iyayena basu ce min ci kanki ba amma fushinsu ya nuna sossai a fuskokinsu a haka aka tashi taro rikon el-hussein ya dawo wurin Ummi a tsakan kanin ne na shayar da el-hessein sossai anan ne yasan soyayyar mahaifiya sossai na kula dashi na watanni uku zuwa na gama idda anan na samu Umar na bashi labarin duk abunda ya faru da fushin da iyayena da 'yan uwana sukeyi dani.................


Sossai Umar ya nuna min bacin ranshi da ban ta'ba gani ba na boye mishi da nayi daga baya ya sauko ya tafi gida ya turo iyayen shi basu koma ba seda aka d'aura mana aure da Umar faruq inda Abdallah ya tarkata ya bar kasar tun daga randa ya sakeni ya shiga shock sossai jin an d'aura aurena abunda be taba zata ba seda yayi kuka sossai sbd har lokacin soyayyata na cikin ranshi ba abunda ya ragu.............


Na zata a nan Amman zamu ci gaba da rayuwa kwatsam se Umar ya ajiye aiki ya d'auke ni zuwa nigeria garin Adamawa, tafiya ta nigeria wani babban experience ne a rayuwata ta zaman duniya duk yadda muke larabawa da kin jinin bakin fata se naga fulani sun dama mu sun shanye akan kin jinin kad'o da suke cewa a da kenan ban san yanzu ba................


Na zauna cikin matsi da takurar 'yan uwan Umar da ban ta'ba cin karo da irinshi ba ko a labari duk In zasuyi toh sede a bayan Umar kasancewar shine babba a gidan gabad'aya Hamma suke ce mishi a wurin mijina Ina samun soyayya da ko wacce mace take fatan samu amma a wurin 'yan uwanshi zan iya cewa rayuwa na a jimeta cikin karewa kaman prison yake..............


Kasancewar Umar me tafiye tafiye abubuwa dayawa dake faruwa ba sani yayi ba a hk a daddafe har na shekara da auren Umar 'yan uwana basu ta'ba zuwa nigeria ba sede muyi waya zuwa lokacin kuma iyayena sun riga da sun sauko daga fushin da sukeyi da ni, kwatsam Umar yaje wani seminar Abuja a mota suna dawowa sukayi accident ban ta'ba fuskantar tashin hankali irin wancan ba a rayuwa na sbd ina tsananin son mijina ya bani soyayya da tsantsan kulawa da ban ta'ba zaton 'yan Africa sun iya ba...............


Nayi jinyar mijina na watanni biyu inda a lokacin Ina da cikin wata hud'u nayi kuka sossai a ranarda Umar ya bar duniya ya mutu da Kalmar shahada kafin nan last words dinshi shine he loves me in kula mishi da duk abunda na Haifa In namiji ne in sa sunanshi In macece In sa sunana"..................


Kuka ne ya katse ta kana jin d'acin abunda take fad'an a cikin kukanta daga ji ba karamin so takewa Umar ba a lokacin haisam karan kanshi hawaye yake, kai kowa ma a parlorn In ka cire sagir da dad suma karfin hali ne ya hana su kukan, bayan ta tsagaita da kukan ta ci gaba, "na shiga shock da seda aka fidda tsammani da cikin jikina tsabar kad'uwa da mutuwar Umar a d'akina na zauna har seda Umar yayi arba'in tukun na tattara bada sanin kowa ba daga cikin familynshi ba Ina tsoron kar suce In zauna se na haihu In basu kai abunda bazan ta'ba iyayi ba kenan sbd duk soyayyar da nakewa Umar kan abin cikina ya dawo..................


Ina isa Hashemite kingdom wurin ummina naje da cikin wata biyar a jikina fad'uwa nayi a jikinta na fashe da matsanancin kuka Ina jin mutuwar Umar na dawo min sabo sbd a Chan nigeria ban samu wadda zan sa a gaba nayi kukan da zasu gane d'aci da rad'ad'in rashin Umar a gareni ba, a lokacin ana family meeting ne hall d'in a cike da mutane ko ta Ina 'yan uwa ne, Abdallah na zaune a kujeran mulki a lokacin Abbi yayi murabus ya d'aura shi kan mulki shi kuma ya koma gida sbd a wurinmu idan crown prince ya cika 25 kuma yana da d'a namiji ake bashi sarautanshi, ido ya kura mini a lokacin wani sabon soyayyata ne ya dira a zuciyarshi cike da tausayi na duk da be san me ya sameni ba soyayyar da yayi ta dannewa ya taso mishi sossai................


Duk da a lokacin yayi wani aure ya Auri Raina, duk wurin shiru sukayi kowa ya zuba ido yana kallo na yayin da kowa ke sake sake a zuciyarshi wasu na tunanin ko har bakin fata ya nuna min halinsu ya sako ni, wasu na tunanin wulakanta ni yake sbd ganin yadda na rame se katon ciki gashi nayi duhu.................


A rude Ummi ke tambayata In fad'a musu abinda ya sameni amma na kasa magana, Abdallah ne ya taso ya zo ya rike hannayena Ina kallonshi na fad'a jikinshi na ci gaba da kuka na fitar hankali numfashi na na d'aukewa na furta Umar ya rasu ya tafi ya barni............


Dip kowa a parlorn ya dauke wuta Shi kanshi Abdallah yaji mutuwan ya mugun shiganshi, suna na ya fara kira ganin kaman na sake Ai kuwa yana dubawa yaga na sume, a rud'e sukayi asibitin cikin kingdom d'in dani, da kyar likitoci suka samu na farfad'o gashi jini na ya hau sossai kun san hawan jinin masu ciki, Abdallah ne ya ci gaba da kula dani kaman da kaman bamu ta'ba aure ba kaman wani abu be ta'ba had'a mu ba.................


El-hussein da ke da shekaru biyu kullum a wurina yake yini yana makale dani Ammah yake cemin yayin da yake kiran Abdallah Abbah, wata rana Ina kwance akan gadona na asibiti nake tamabayr Abdallah matarka ta haihu ne? Tunda na dawo bamu had'u ba yace eh tana da 'ya princess Iman murmushi nayi na furta Iman bint Abdallah shima murmushin yayi................,


A lokacin ne nayi deciding tambayar shi me yasa ya zarge ni da zina da aurena?...................

#vote

#share 

#comment
'Yar mutan Adamawa💞💞💞
                  💞💞Hamrah💞💞


                                                     💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin


Wattpad: muhdfatimagurin          *'yar mutan Adamawa*


Page➡2⃣8⃣

************


Shiru yayi kaman baze ce komai ba se kuma yace me yasa kike son sani? Nace sbd zargi ba daad'i bawai don ina sha'awar komawa aurenka bne, Shiru yayi yana kallona har ga Allah ni abunda ke zuciyata ne na fad'a don ban da sha'awar yin wani auren In nayi kaman banyiwa Umar adalci ba ko shekara ba'a rufa da rasuwarshi ba ace nayi aure...................


Wayanshi ya d'auko ya nuna min abunda aka turomishi da videonmu a restaurant din da muka ci abinci kan zuwanmu apartment dinshi da picture din da ya d'auka lokacin Umar ze shiga ciki da wata a gefenshi, murmushi nayi hawaye na gangara a ido na Ina tuna moment d'inmu na lokacin dashi da murmushi na kalli Abdallah nace................


Lallai Abdallah kishi ya riga ya rufe maka ido kallon cikina nayi na cigaba Ina shafawa nace tabbas wani baya haifan d'an wani kenan rabon wannan cikin ne yasa ka sakeni, da mamaki yake kallona yace ban gane ba, nace ka manta ni renonka ce Abdallah ko da duniyan nan gabad'aya zasu ce nayi zina na san kai ba me yadda bane sbd kasan abunda zan iya ka kuma san wadda bazan iya ba.................


Ya sake cewa ban gane ba, nace toh me yasa baka ci gaba da tsanata da kuma fushi da ni ba har yanzu? Yace Wlh na rasa wannan dalilin, nace sbd ka yarda dani kenan, Abdallah ka kalli videon mu na restaurant ka kalle ni da kyau ka koma ka kalli hoton da ka d'auka da hannun ka na wata dake kokarin shiga building nasu Umar....................


Kallon videon yayi tare da kuramin ido a cikin wayan yana son gane abunda nake son nuna mishi ya koma ya kalli hoton ya kurawa buduruwan ido, da karfi yace shiiiiiiiiiit Wtf!!!!!!  Kau da kai nayi Ina murmushi haushin kanshi ne ya kamashi ganin banbanci karara da be kula dashi ba se yau, kayan dake jikina a cikin restaurant da kayan jikin wancan ba d'aya bane kuma structure na jikinmu ma ba d'aya ba na fita cika da hips sossai ita kuma tsiririya ce kaman zata karye.................


Hawayene ya fara zuba a idonshi yana cewa I'm sorry noor am so sorry na mareki na kuma yi miki fad'a a kan abunda baki aikata ba, nace Abdallah bakayi komai ba abunda kayimin nan ma shine daidai a matsayinka na yayana na cancanci duka fiye da marin da kamin sbd haramcin soyayya da wani bayan akwai aure a kaina wadda na san hakan na take Abdallah ka yafemin danne maka hakki da nayi na dibi fushin Allah da mala'iku Allah baze kama Umar da laifi ba sbd wallahi shima bai sani ba....................


Ina tsoron fad'a mishi ya rabu dani, ajiyar zuciya Abdallah ya sauke yace na yafemiki ukhty Allah yaji kan Umar ya gafarta masa, zan amsa kenan naji ance In kina son yafiyar Allah se ki koma d'akinki ki gyara duk wani abunda kika bata tunda har yanzu d'an uwanki na sonki, kallon kofa nayi Ammi, Abbu, Abbi da Ummi ne a tsaye ashe tunda muka fara magana akan abunda ya raba mu suke tsaye sossai sukayi mamakin boyemusu abu irin haka da mukayi ya kamasu..............


Ko da shike lokacin bazan ji zafin zargi ba sbd murnan zan auri Umar sun yarda da kaddara sun kuma yarda rabon d'an cikina ne ya kashe auren, kowa ido ya zuba min yana jiran jin me zance Abdallah yayi karfin halin cewa ba wadda ze miki dole 'yar uwata In baki so, a hankali nace Allah ya bamu zaman lafiya hawaye na gangaromin, murna sossai iyayenmu sukayi har mamakin murnan Ummi nake ashe tana sona da d'anta amma take kauda kai.....................


A lokacin suka tsayar da Auren bayan na haife abunda ke cikina, wata hud'u da nayi a tsakankanin nayishi ne cikin farin ciki da soyayyar 'yan uwa da iyaye na sossai Abdallah ke nuna min kulawa har nima na fara sonshi duk da har ga Allah be kai son da nayiwa umar ba na yarda kuma so d'aya ne na riga na ba umar ya tafi dashi kabarinshi ban ta'ba mantawa da shi cikin adu'o'i na ba, ranar wani Juma'a na tashi da nakuda.................


Inda akayi asibiti dani ban wani jima ba na sauka yarona namiji sak Umar ba abunda ya raba su be d'auki komai nawa ko d'aya ba ban san hali ba, haisam kaga gata sossai lokacin haihuwanka don ko el-hussein dake d'an cikin masaurata kuma balarabe gaba da baya be kai ka samun gata ba kuma Allah ya d'aurawa kowa nawa sonka musamman Abdallah ran suna kaci suna Faruq Umar faruq...............


Bayan arba'in d'inka aka d'aura aurenmu da Abdallah muna cikin masarauta d'aya amma bamu ta'ba haduwa da Queen Raina ko sau d'aya ba se bayan aurenmu da muka koma bangaren mu kowa da part dinshi In ba mijinmu bane ya nemi ganin mu gabad'aya ba toh bama had'uwa.............


Sossai nake kula da Abdallah na mallaka mishi komai nawa na kuma bashi gabadaya lokaci na Ina fatan Allah ya yafemin zunuban da na kwasa a aurenmu na farko bayan shekara d'aya da wata takwas a lokacin shekarunka kenan yayin da el-hussein keda shekaru hud'u a wurin ummi yake sbd kar mu barta ita kad'ai na nemi Abdallah ya barshi a wurinta........................


Ranar da safe Abdallah na shirin tafiya fada nake ce mishi zanje asibiti bana jin daadin jikina da kulawa ya dubeni yana cewa ko zamu je tare, nace mutanenka fa? Kawai ka tafi zan je ni kad'ai ba ga faruq ba ze rakani, dariya yayi kan yayi pecking forehead dina yace se kin dawo Allah yasa azo da kyakyawar news ina murmushi na rakashi har bakin kofa ya tafi na dawo na kimtsa na fice asibiti bayan an gwada ni aka tabbatar min Ina da ciki wata biyu nayi murna nasan Abdallah ma zeyi murna sossai..................


Muna isa gida Ina bud'e part d'ina na fara jin jiri Ina kallon hayakin dake tashi a parlorn da sauri na shiga d'akina ko zan dena jin warin hayakin da kuma jirin dake d'iba na da kyar na samu na ajiye handbag d'ina akan bedside Ina rike gam da hannun faruq dishi dishi nake kallon Raina dake dariya har na dena ganinta daga nan ban san me ya faru ba se ganinmu nayi nigeria..................


Zan iya tuna duk wani abu da ya faru dani a shekaru 26 da nayi a hali na hauka" kuka ne ya kwace mata sossai qudra ma sossai take kuka tana tsinewa Raina da ta zama sanadiyar tashinta a bola bayan mahaifinta sarki ne guda haisam ma hawayen tausayin mahaifiyarshi yake ya mike ya koma kan kujera kusa da ita tare da kwanto da ita gefen kafad'anshi ta ci gaba da kuka a natse qudra ta mike ta kwanta a d'aya kafad'anshi se abun ya ba 'yan parlorn tausayi....................


Se ji sukayi qudra ta fara wani irin abu tana jan numfashi da karfi tana saukewa da sauri haisam ya saki Ammah ya riqe ta yana jijjigata Ammahn nan kanta tayi tana kiran sunanta se ji sukayi ta fara cewa cikin murya irin na maza, "ku natsu ban shiga jikinta da niyyar cutar da ita ba sede na shiga ne dan in isar muku da sako" haisam yace "wani irin sako ne ze sa aljani irinka shiga jikin 'yar uwata?" Murmushi tayi tukun ta fara cewa:-


"Ni sunana Bishwaaz mu 'yan biyu ne ina da d'an uwa me suna Bishaam ni na kasance me bin addinin mahaifiyata wato musulunci, ni babban malami ne a duniyarmu ina yawo kasashe kasashe da'awah da sauransu yayin da mahaifi na da d'an uwana suka kasance mushirikai masu sa'ba ma Allah, a yawona na da'awah nasha gamuwa dake da 'yarki cikin yanayi na hauka na kuma shaa gamuwa da haisam cikin yanayin damuwa da son sanin waye iyayenshi...................::Tun lokacin na sa a raina zan taimaka muku sbd bincikena ya nuna min kece magaifiyarshi se tafiya ya kamani na kwanaki a wurinmu ku kuma shekaru kusan ashirin a duniyarku, bayan na dawo ne na fara binciken inda kike amma na rasa se na tafi wurin mahaifina naje zan shiga d'akinshi kenan naji Bishaam na bashi labarin wata mahaukaciya da aka bashi aikin dawwamar da ita a hauka gashi yanzu be da lafiya kuma yayiwa shugabanshi alkawari ko mahaifinmu zai iya taimakawa ya d'aura ni akan aikin?...............


Ina ji mahaifinmu yace bani labarinta, sak labarinki dana bincika ya bayar dariya mahaifinmu yyi tukun yace wani kasungumin matsafin ne ya baka aikin? Bishaam yace Ashik Arwahun ya mahaifina, ya karbi aikin ne sbd son da yakewa sarauniya Raina duk sanda aikin ya karye zai mutu ita kuma zata haukace, kai na gyad'a Ina dariya sbd idan waccan babban matsafin Ashik arwahun ya mutu toh har abada baza'a sake samun matsafin marar tausayi ba irinshi.................


Kafin mahaifinmu yayi magana na shigo Ina murmushi nace ya mahaifina zan karbi wannan aiki har zuwa sadda d'an uwana ze mike daga wannan rashin lafiyar da yakeyi, murmushin jin daadi yayi sede d'an uwana na shakka sbd murmushin da ya gani a fuskana yafi kowa sanin halina yana tsoron abunda ze sami ubangidanshi...................


Toh bayan ya tattara 'yan gidanshi da suke saki hauka tuburan se na shiga jikinki nayi yadda zanyi na had'aku da d'anki na sa mishi tunani da mafarkinki randa yake kano na saki kika je har bakin gidan marayunshi ni na dinga kuka har ya tausaya ya d'auke ki da matar shi ta fara saka karatu a gidan ranar Bishaam ne yazo duba me kike ciki tsorona kar ya gane haisam sbd ya San shi amma da kuka sa karatun ko kwana be yi ba ya gudu dama bashi da lafiya gashi kina shirin kona shi yaranshi ya turo akan su duba mishi don be yadda dani ba...................


Da suka zo se suka tarar da malamin da matar haisam ta bashi shawaran kawowa ya kona su tare da fattatakan su nayi farin ciki sossai sbd baza su kaara dawowa ba daga lokacin ni kuma na dawo na yi ajiya a harshenki nayi tafiyata yadda baza ki iya magana ba, da aka zo batun haisam yayi kisa ni nasan be yi ba amma ba yadda zan yi In fad'a randa akayi zama na farko kika gane d'anki sbd.................


Ta'bon cokali da Raina ta mishi kin tuna?" Ammah tace "kwarai kuwa a lokacin yana tafiya ko ina shekaranshi d'aya da wata biyu suka fita da yayanshi garin yawonshi ya tsinci kanshi a part d'in Raina tsabar mugunta irin nata ta san bata isa ta tare ni tamin rashin kunya ko ta neme ni da fad'a ba sbd bazan d'auka ba, ta sa cokali a wuta yayi zafi sossai ta nanawa faruq a dantse a gigice ya saki ihu da gudu na isa dayake na fito Ina nemanshi a ranar seda nayi darun da ban ta'ba yi ba a masarautar seda na ga Abdallah ya tsitsinka mata mari Ummi da Abbi sunyi mata fad'a sossai kan na hakura bayan spoon d'inne ya zauna a hannun faruq ya zama sheda da har yanzu be goge ba wadda dashi na ganeshi"....................


Kai duk 'yan d'akin suka gyad'a hamrah, sagir da yaqoob duk sun san shedar, Aljani Bishwaaz ne ya ci gaba da magana "bayan kin gane d'anki ne gashi ba bakin magana se kika dukufa da mishi adu'a bayan an dawo ana neman sheda ne nima na dawo na tuna musu da abunda hankalin kowa be je kai ba wato CCTV camera, bayan an gama shari'ah an wanke haisam kafin nan nayi niyya idan hankalinku be kai kan agogo da zobe da na shiga jikin hisham na sashi sawa ba se in shiga jikin d'aya inyi magana amma se matarshi ta gane....................


Da gayya rannan na shiga jikinki na saki fitowa parlor da sarkan kafanki kina kuka na kuma hana ki cin abinci da sallah har seda haisam yazo tukun na fita, dayaga chain d'in se ya kasa tunawa, na dinga mishi gizo da abunda ya faru a kwakwalwanshi amma ya kasa tunawa sbd a lokacin yana yaro sossai da naga in na ci gaba a haka zan iya sama mishi matsala a kwakwalwanshi shine yau nazo mishi a mafarki na bashi duk wani labari na abunda ya faru na san me ilimi ne ze iya ganewa se kuma gashi ya gane...................


Ina nan zaune har kika gama bada labarinki shine nayi tunanin fad'a muku wannan zan iya sake zuwa In kun koma fada sbd sheda, ku ci gaba da adu'a Allah ya kare ku" ya kalli haisam yace "kayi dacen mata ta gari wadda annabi yake mana mu maza fatan samu ka riqe ta amana Allah ya ci gaba da kare ku se anjima" kafin su mishi godiya ya tafi ta hanyar wani atishawa da qudra tayi har sau uku........................
#vote

#share

#comment
'Yar mutan Adamawa💞💞💞

             💞💞Hamrah💞💞                                                   💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin          *'yar mutan Adamawa*


Page➡2⃣9⃣

************


Bacci ne ya d'auke qudra bayan fitan Aljanin daga jikinta chak haisam ya d'auke ta yaje ya kwantar da ita a kan gadon d'akinsu, bayan ya fito ya koma mazauninshi na farko kusa da Ammah kanshi a kasa yayi shiru sagir ne ya fara magana ya taya shi murnan samun mahaifiyarshi da kuma ta'aziyar mahaifinshi amsawa yayi tare da godiya...................


Haka yaqoob ma, mom da dad ma ta'aziya suka mishi tare da nasiha sossai yayi musu godiya Ammah ma tayi musu godiyan bama d'anta auren hamrah da sukayi da kuma d'awainiyar da sukayi dasu lokacin a court, murmushi mom tayi tana cewa "haba ai ba komai an riga an zama d'aya" har mota suka rakasu suka wuce, sagir ma sallama ya musu yana cewa................


"Man zan wuce da daren nan zan wuce sisters suna ta fad'an rashin fad'amusu da banyi ba, ga wurin aiki da ban d'auki permission ba nayi xuwana Dan ma sun san na samu kariya zanje nayi clearing, se munyi waya" murmushi haisam ya mishi tare da hugging dinshi suka bugawa juna baya a tare suka saki juna haisam yace "Bani da bakin gode maka, zan so Dan Allah in zamu Jordan muje tare sbd kune kaman 'yan uwana da kai da yaqoob kunyi min komai bani da Abin ce muku se Allah ya biyaku da mafificin alkahiri, muje mana in raka ka airport d'in"..................


Sagir yace "waa tab na san baka gama Shan nono ba wuce kaje In ka karasa ka sameni a airport din amma ni yanzu driver ze tafi dani" dariya sukayi a tare haisam na girgiza kai wai Shan nono se kace wani baby, sallama sukayi da yaqoob da Ammah da hamrah ya shige mota drivern haisam ya ja shi don kaishi airport, yaqoob ma daga nan be koma ciki ba ya wuce part d'inshi...................


Hamrah, haisam da Ammah ne suka koma ciki, hamrah se sussune kai take wai ita kunya suna shiga ma bata zauna ba tayi wup ta haura da sauri, murmushi Ammah tayi tana cewa "daughter-in-law ba de kunya ba" haisam yace "zaku saba ne a hankali" Kai ta gyad'a ta samu kujera ta zauna shima ya zauna daga kasa ya fara bata labarin su Abba da Ammi d'inshi da irin dukiyar da ya bar mishi, da yadda ya ringa juyasu har suka ninka na da....................


Sossai yayi ta mata zuba abunda be ta'ba zama yayi labarin da wani ba duk wani ci gabanshi seda ta sani, Ad'ua ta ringa yiwa su Ammi tare da musu fatan dacewa lahira sbd rike maraya da sukayi ba tare da sun sanshi ba suka kuma mallaka mishi duk wani dukiyar da suka tara da guminsu, ita me tsakaninta da mutanen nan in ba adu'a ba? Zata ci gaba da musu adu'a har itama ta koma ga mahallicin ta..................


Suna cikin hira aka kira sallah rakata har room d'inta yayi tayi alwala ya shimfid'a mata sallaya seda yaga ta tada sallah tukun ya shiga toilet d'inta yayi alwalan shima ya fice, Ta bangaren hamrah kuwa tana hawa ta shige kitchen tana tunanin abun da zata girka musu, duba fridge d'inta tayi a hankali ta sauke ajiyar zuciya ganin akwai stew d'in da tayi fiddo shi tayi tana dubawa yaji kaji kam ba laifi akan gas cooker ta d'aura tana dudduba abunda zata karamishi.................


Nan da nan ta gama had'awa ta kunna d'ayan cooker d'in ta d'aura white rice, a d'ayan kuma ta d'aura zobo, ficewa tayi ta nufi d'akinshi ta gyara gadon da suka bata da sukayi baccin rana, ta fiddo tray d'in d'azu ta kai kitchen ta duba abincinta ganin duk sunayi normal ta rarrage gases d'in sbd wanka da take son shiga ta fice.............


Bayan tayi wanka tayi alwala tana fitowa ta shafa mai sama sama ta fesa spray bayan ta shafa roll on ta bincika kayanta ta samo wani dogon riga kaman na bacci me yauki irin na saudiyan nan ta saka ta koma ta fesa perform ta d'auki hijab ta saka ta koma kitchen din, ta sauke miyanta ta kuma wanke shinkafanta ta kara mayarwa tare da zuba veggies a ciki, ta tace zobon ta yanka mishi cucumber dama a dafawan ta saka 'bawon pineapple ta ajiyeshi don ya huce kan ta zo tayi had'i cooler me kyau da tsada ta d'auko ta zuba stew d'in a ciki se tashin kamshi yake ta ajiye.....................


Jin kiran sallah yasa ta koma d'akinta tayi sallahn magrib tana idarwa ta fito ta samu har shinkafanta ya tsotse ta kwashe a cooler, ta had'a zobonta ta sa kankara bayan ta zuba shi a babban jug ta had'asu a babban tray ta sa spoons, cups da plates ta d'auka tazo ta ajiye akan dining na parlor,  tare da komawa d'akinta ta gabatar da isha da ake ta kira bayan ta idar ta fito trayn ta d'auka ta nufi kasa tana karasa sauka yana shigowa murmushi suka sakarwa juna ya karaso gabanta yayi pecking kumatun ta tare da kar'ban tray din hannunta.................


Zaro ido tayi tana leka bayanshi murmushi ya karayi me sauti yana cewa "Ammah bata fito ba sarkin kunya" dariya ta saki tana binshi a baya suka nufi dining d'in parlorn kasan ya ajiye, yana ajiyewa ya juyo tare da janyowata jikinshi tana kokarin fisgewa ya matse ta kaman zatayi kuka tace "Dan Allah ka rufamin asiri kar Ammah ta fito ta ganmu haka" yana dariyar ganin yadda tayin suka ji motsin kofa, da azama ya sake ta yana Sosa kai suka kurawa kofar ido se kace wa'yanda sukayiwa sarki karya.................


Ganin ba wadda ya fito ne yasa suka kalli juna tare da fashewa da dariya a tare, kofar ya nufa yayi sallama aka amsa mishi ya shige ganin qudra na zaune akan sallaya lafiyanta klau yasa ya saki ajiyar zuciya ya kalli 'bangaren Ammah yace "Ammah food is ready" tace "Ohk" ya kalli qudra yace "ya jikin, ba abunda ke miki ciwo ko?" Kai ta girgiza dukda tana jin nauyin jikinta da ciwo kaman an mata duka sbd ko ya aljani ya shiga jikin mutum kuma ya tashi toh se ya bar masa ciwon jikinnan...................


Mikewa tayi ta zare hijab d'in jikinta ta bi bayansu don har sun fice akan dining ya samesu Ammah nayiwa hamrah sannu da aiki a kunyace ta amsa, qudra ma tayi mata sannu da aiki tana mata dariya kasa kasa harara ta sakar mata tana murmushi shi kam idonshi na kanta ta mishi kyau sossai don be ta'ba gani tayi harara ba, mikewa tayi don serving da sauri qudra ta riga ta d'aukan serving spoon d'in tana cewa "Ammah kijimin matar yayan nan zata kwashe ladan gabad'aya" murmushi duk sukayi Qudra tayi serving d'insu suka fara ci cikin natsuwa da farin ciki...................


Bayan sun gama ci hamrah ta fara tattara kayan qudra ta sa hannu suka tattare suka haura sama suka bar su haisam da Amman akan dining d'in suna isa kitchen suka fara wanke wanke suna hira abinsu, bayan sun gama qudra ta mata sai da safe ta fice ita kuma ta koma room d'inta ta cire gown d'in jikinta ta zakulo wani nightwear d'inta hot red Nylon me tsiririn hannu d'an guntu ta saka ya bi jikinta sossai ta kara fesa turare ta kashe wutan d'akin ta gyagyara labulaye ta haye gado tare da janyo system d'inta na kanfanin Apple ta kunna wani horo film mai suna 'The nun" ta fara kallo....................


Chan bangaren su haisam kuma Ammah na ganin 9:30 yayi tace "hiran ya isa hk ka barmin daughter-in-law ita kad'ai, kuma ka koremin 'ya wai karta ji yarantanka ta rainaka itama tana Chan ita kad'ai" murmushi yayi dama tunda ta gama basu labarin 'yan uwansu na bangarenta sunayensu da matansu da 'ya'yansu da ta sani, tana gamawa ya kora qudra, Ammah na murmushi ta fara bashi labarin yarantanshi da yayanshi yana jin son ganin yayan nan nashi, soyayyar yayan nashi ya shiga ranshi sossai so irin na 'yan uwantaka.............


Yace "toh Ammah, yaushe zamu wuce jordan d'in?" Shiru tayi tana kallon yatsun hannunta, tsoro take ji tana shakkar kar wayanda ta sani Sossai kuma suka shaku ace sun mutu, tana kuma tsoron kar de suna zaton ta gudu ne da kanta sbd bata son Abdallah, ganin yanayinta ya sauya yasa shi cewa "no Ammah, in baki shirya ba karki takura kanki duk sanda kika so se mu tafi" murmushin yake tayi tace "kaima ai se ka shirya ka nema mana visa da sauransu kaga kenan kana bukatar lokaci" murmushi yayi tukun yace "Ammah Kin manta Ina da private jet? And sits dinshi har guda 8 ze dauke mu tsab ko yanzu kika ce mu tafi pilot a shirye yake"......................


Kad'a kai tayi tace "toh se mu tafi ko jibi ne" yace "Ohk ma, and gud nyt" ta amsa da "Allah yayi albarka ya kuma tashemu lafiya" ya amsa da Ameen yana haurawa, d'akinshi ya shiga ya watsa ruwa ya shirya cikin sky blue nightwear wando da riga me bud'add'en kirji, har ya hau gado ya kwanta se kuma ya mike he just want to see her, yau ya kasance mishi rana mafi mahimmacin da baze ta'ba mantawa ba he wants to add to this memory tsam ya mike ya nufi room d'inta....................


A hankali ya tura kofan ya shiga tare da mayarwa ya rufe idonshi ne ya sauka a kanta hasken system d'in ya haska d'akin ba laifi tana kankame da pillow tayi rub da ciki daga gani a tsorace take, dama haka take tana matukar son horror film amma In tana kallon ko curtains ne yayi motsi se ta tsorata In ta gama kuma ko fitsari ya matse ta haka take kwana a takure tsabar tsoro.................


A natse ya kai idanunshi kan screen na system din daidai lokacin aka haska wani wurin tsoro da ya sata kara kankame pillow da blanket d'inta a sad'ad'e kaman 'barawo ya isa bakin gadon a hankali ya sa hannu a kafanta yayi mata tafiyar tsutsa, a mugun firgice ta mike tsaye zata kurma ihu ya jawota cikin zafin nama ya rungumeta jikinta ne ya d'auki mugun rawa ta fashe da kuka tana karkarwa, ganin da gaske ta rud'e yasa ya raba ta da jikinshi yana jijjigata a hankali yana cewa "hey hey!!! It's me, mijinki ne" a hankali ta fara dawowa daidai tsoron ya fara saketa "hamrahhh" ya ambaci sunanta a kasalance cikin muryanshi me Amo da shiga zuciya, bata amsa ba sbd yadda jikinta ya mutu ga kamshinshi daya cikata..............


Cikin duhun ya had'a fuskansu a hankali yana brushing karan hancinshi da nata lumshe ido tayi tana jin tsikar jikinta na tashi, lumsassun idanun nata ya manna wa peck, a hankali kaman be so ya gangaro bakinta In a stylish way ya had'e bakinsu bata san sadda ta bud'e mishi lips d'inta ba inda ya samu daman capke harshenta ya fara tsotsa cikin yanayinshi me sanyi da cikar kamala...................


A hankali ba tare da saninta ba ta matsoshi sossai tare da manna tudun kirjinta da bata saka mishi bra ba da bare chest dinshi a lokaci d'aya ya rud'e yaso bircikewa tsayuwa taso gagararsu gabad'aya a hankali ya yi baya da ita ta fad'a kan gado ya bi bayanta, da hannu d'aya ya matsar da system d'inta ya d'aura akan bedside tare da rufewa, dip hasken d'akin ya d'auke gabad'aya. Dan gulma da kusasu naki matsawa ko ina duk da ba abinda nake gani chan naji haisam ya fara adu'ar saduwa da iyali a lokaci d'aya kuma naji hamrah na magana cikin rawar murya, hkr take bashi akan ya barta amma alamu sun nuna haisam yayi nisa kuma baze ji kira ba, da sauri na fice sbd karsu lalatani🙈🙈🚶‍♀🚶‍♀...........................


#vote

#share

#comment'Yar mutan Adamawa💞💞💞

                  💞💞Hamrah💞💞

                                                  💞💞


Writer: fateemah Muhammad gureen 


Wattpad: muhdfatimagurin           *'yar mutan Adamawa**this page is dedicated to all my readers a duk inda suke, Ana mugun tare and thanks for your prayers am totally fine now Alhamdulillah*Page➡️3️⃣0️⃣

*************
Bayan kaman mintuna 30 zuwa 40 naja Amadun kafana na koma d'akin da lalu'be na samu na isa bakin gadon na la'be, kukan hamrah ke tashi a hankali cikin yanayi na tsantsan shagwa'ba da sakalta kwance take akan faffad'an kirjinshi ya rungume ta tsam kaman his life depends on her idanunshi a runtse fuskanshi cike da wani annuri da farin ciki me wuyan fassaruwa..................


Shafa daga kanta yakeyi zuwa bayanta he's speechless or can he say out of words a hankali ya d'agota ya d'aura kanta akan pillown da yake ya had'e fuskansu tare da sa hannu ya kunna bedside lamp ido yake so su had'a amma taki sam ta runtse idonta hawaye kuma be bar gangara ba, ita kanta bata san dalilin kukan nata ba kawai ta kasa controlling hawayen ne bata Ankara ba taji harshenshi akan fuskanta In a romantic and inspiring way yake lashe hawayen nata dip kukan ya d'auke hawayen ya kafe zuciyarta ya fara bugawa da karfi karfi kankame idanunta ta kara yi tana jin tsikar jikinta na tashi kaman wadda ake mata tafiyar tsutsa a jiki................


Seda ya tabbatar kukan ya tafi gabad'aya tukun ya kara jawo ta kusanshi ya fara rad'a mata wasu kalamai da ya sata barin duniyar mutane, kalamai ne masu ratsa jini da jijiyar wadda ake gayawa me cike da tsantsar soyayya da kulawa a tare suke tafiya kuma da ban hakuri, kasa kunne nayi sossai duk da wasu words d'in sun wuce ni tsintar wasu nayi inda yake furta...................


"The day you stepped into my life you changed it into something so beautiful and meaningful, you are just so amazing to have around I cannot stop myself from telling you everyday how much you mean to me, you are the first and the only person to touch my heart with your passionate and never ending love..............." 


Jikinta na d'an tsuma da rawa kad'an kad'an baza ta iya ci gaba da sauraran rad'ar da yake matan nan ba zuciyarta ze iya bugawa da soyayyarshi zamewa tayi ta koma kan kirjinshi tayi lub numfashi ya sauke tukun ya ci gaba In a whisper "you came into my life and totally changed my world I have lost total control of myself, I'm a changed person believe me my heart does not belong anymore to me it's given away to you hamrahhhh" kara shigewa jikinshi tayi a hankali ya zameta ya mike toilet d'inta ya shiga ya had'a mata ruwa me d'umi sossai, ya dawo ya d'auke ta chak kaman 'yar baby ta cukwikuye blanket a jikinta a haka suka isa toilet d'in ya tsunbulata cikin ruwan tare da zame blanket d'in runtse ido tayi tare da kankame shi se kuma ta sa mishi kuka....................


Cike da shaukinta da tausayinta yake kallonta a lokaci d'aya kuma yana shafa bayanta da alamun lallashi yana ta son su had'a ido amma taki sam ta runtse ido gam gam da kanshi ya wanke ta tas ya barta tayi wankan tsarki ya kuma d'auke kaynshi zuwa kan kujeran dake d'akin,da kanshi ya cire bedsheets d'in kai ya d'auko wani a wardrobe d'inta ya shimfid'a, nightwear d'inta ya dauka ya mayar mata tare da kwantar da ita duk idonta a rufe dukawa kanta yayi a hankali yace "Hamrahhhh".....................


Bata amsa ba sam se kara shigewa blanket da tayi kara kiran sunan yayi nan ma shiru tayi dukawa yayi sossai kanta yayi pecking goshinta tare da furta "I'm deeply and madly in love with yhu, Allah yayi miki Albarka and thank yhu so very much for this" ya karasa yana shafa maranta, numfashinta ne ya nemi d'aukewa murmushi ya sake ganin yadda take fisgan numfashin da karfi juyawa yayi da kallo ta bi bayanshi har ya fice tukun ta saki murmushi tare da cije lip d'inta na kasa ta kara lumewa a kan pillownta tare da lumshe ido tana tuno moments d'insu na d'azu..................


He was extra gentle, so loving and caring, he fills her with his love wani irin sonshi taji yana fusganta tabbas ta yadda haisam daban ne ko a cikin maza ya iya tafiyar da mace yadda ya kamata da sauri ta mayar da idonta ta rufe jin an turo kofa shine ya shigo sanye da farar jallabiya da alamu wanka yayi sallayanta ya d'auka ya shimfid'a ya fara nafilfili yana godiya ga Allah akan haskaka mishi rayuwa da yayi be ta'ba tunanin his life will turns out to be this happy ba se yau wani irin annashuwa da farin ciki yakeji da tunda ya san kanshi be ta'ba tsintar kanshi ciki ba...............


Tana kwance tana jinshi tana kuma kallonshi cikin kamala yake sallahn da tsantsar natsuwa da bata ta'ba kawowa yana da ibada haka ba, Raka'a takwas yayi sallama hud'u tukun ya zauna cikin muryanshi me daad'in gaske da har ta zata sheik Abdulrahman Sudais ne ke rera karatu sbd yadda muryansu ta zama iri d'aya sossai taji ya fara karatun suratul Anbiya'i ba tare da qur'ani ba duk da baccin da ya cika idonta amma sam taki yarda tayi she can't miss this, haisam is an angel to her................


Suran tas ya karance tukun ya d'aga hannu ya fara yiwa Allah kirari da sunayenshi kyawawa 99 ya d'aura da godiya ga ni'imarshi (Allah) a gareshi bayan ya shafa ya mike ya ninke sallayan tare da cire jallabiyan ya saura daga shi se boxer tukun ya hauro gadon tare da janyota jikinshi bayan yayi brushing lips d'inta da nashi a haka bacci ya kwashe su gabad'aya cikin yanayin marar misaltuwa a garesu.......................


*************


Da asuba shi ya fara tashi zame ta yayi ya shiga toilet d'inta sharp sharp yayi alwala jin an shiga sallah yana fitowa ya nufi gadon damshin ruwan alwalan dake hannunshi ya fara shafa mata a fuska yana hura mata iska a hankali ta bud'e idonta kasancewar wutan d'akin a kashe yasa be gani ba ya ci gaba da shafa fuskan a hankali cikin sanyin murya tace "na tashi" be ce komai ba ya juya ya fice da sassarfa.................


A hankali ta mike ta zauna tana jin jikinta kaman an mata duka a natse ta sauke kafanta tana jin tsoron takawa a hankali kuma ta fara tafiya jin ciwon ba sossai ba kad'an ne yasa ta ci gaba da tafiya duk da ba normal tafiyanta ba, sit-bath ta sakeyi da ruwan da yafi wadda ya mata jiya da sauri sauri tayi ta d'auraye jikinta tayi alwala ta fito ta chanza rigan jikinta ta zunbula hijabinta babba ta tada sallah.........................


Tana idarwa a wurin ta 'bingire se bacci don wani gajiya takeji kaman duka aka mata, shi kuwa haisam bayan ya idar da sallah suka tsaya da yaqoob, yaqoob d'inne ke gaya mishi ma'aikatan gidan suna son ganawa dashi suna son mishi jajen abunda ya faru yace suna ta son mishi amma be samu zama ba, nan ya ce su taru a meeting hall na gidan by 11 anan haisam d'in ke gayamishi zasu wuce jordan gobe kuma harda shi yake son su tafi..................


Yaqoob yace "wai ka manta akwai zuwa court next week kuma ana bukatar ka a wurin?" Zaro ido haisam yayi yana furta "opps Wlh na manta, kenan dole tafiyan ze koma after zaman ba komai Allah ya kaimu" sun kara tattaunawa akan maganan companies d'insu anan inda aka samu matsala da bayanan anan yaqoob ya sanar mishi komai normal amma ya kamata ya zazzaga ya ga komai da kanshi, sun tattauna sossai har se da gari ya fara haske tukun kowa ya nufi gidanshi a ta wajen fence d'in ginin haisam yaqoob  yake amma duk gida d'aya ne........................


A qasa ya tsaya suka gaisa da Ammah ya ba Maids d'inshi na tun da kafin hamrah tazo umarnin had'a breakfast su kuma shirya duk dining biyu na sama da kasa tukun ya haura sama d'akinta ya fara lekawa ganinta kan sallaya yasa shi karasawa ya d'agata zuwa kan gado ya koma d'akinshi yayi wanka ya shirya cikin kananan kaya, ya kwanta a kan gadonshi duk tunanin hamrah kuma se ya cika shi a hankali ya mike ya nufi d'akinta.....................


Ita kuma tunda ya d'aga ta ta farka yana fita ta tashi ta zauna tana dafe kai "ya ilahi banyi breakfast ba" abunda ta furta kenan tana sauka a hankali toilet ta shiga ta kara yin wanka da ruwan dumi ta fito d'aure da karamin farin towel iya cinyanta se wadda ke kanta zama tayi akan dressing mirror ta warware towel na kantan ta ja drawer ta fiddo hand dryer ta jona ta fara gyara gashinta...................A razane ta juyo jin an turo kofan d'akinta se suka had'a ido da sauri ta komar da kanta ta dukar tana jajjan towel d'in jikinta kaman me shirin kara mishi tsawo, kunya duk ya cika ta, murmushi ya saki ya taka a hankali cikin natsuwa ya karasa bayanta a hankali ya duka tare da janye gashinta ya manna mata peck a kumatu ya kurawa fuskanta ido ta jikin madubi kanta a kasa tana wasa da yatsun hannunta...................


Tsintar muryarshi tayi cikin rad'a yana cewa "Good morning sweetheart" zaro ido tayi da ta tuna bata gaisheshi ba se idon ya fad'a cikin nashi da sauri ya kashe mata ido d'aya runtse ido tayi murmushi na kubce mata a lokaci d'aya tasa tafin hannunta ta rufe fuskanta, yana murmushi yake cewa "nop nop nop baby karki hanani kallon kyakyawar fuskan kinnan ki cuceni" a lokaci d'aya ya sa hannunshi ya zame hannun nata a kunyace ta kara gaisheshi amsawa yayi yana tambayarta ya jikinta.................


Tace "ni lafiyata klau" karkata kai yayi cikin yanayi na zolaya yace "ko??" Hannu yasa ya d'auke ta yana ci gaba da cewa "toh mu koma dama ban gaji ba" wutsil wutsil ta fara da kafa a tsorace tana cewa "no no wlh banda lafiya, Ban yiwa su Ammah breakfast ba dan Allah Kayi hkr" ta karasa a shagwa'be for the first time a rayuwanta da ta fara ganin dariyanshi ya yi mata kyau sossai har bata san sadda ta shagala da kallonshi ba tare da sa hannu ta zagaye wuyanshi yadda zata ji dadin ganinshi faffad'an murmushi shimfid'e a fuskanta idonta ya hure suka saki wani dariyan a tare.......................*Alhamdulillah readers na ji daadi kuma na gode sossai da adu'o'inku gareni, Amma yanzu sbd Ramadan da ya karato ga cutar nan da ta addabi mutane am sorry to say baza ku ringa ji na kullum ba sede lokaci zuwa lokaci zan ringayi In Allah ya bani dama na gode sossai*.............
#vote

#comment

#share


'Yar mutan Adamawa💞💞💞

                    💞💞Hamrah💞💞

                                                    💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin


Wattpad:  muhdfatimagurin            *'yar mutan Adamawa*


Page➡3⃣1⃣

*******


A lokaci d'aya haisam ya cirewa hamrah masifaffen kunyanshi da ta tashi dashi, suna hira irin ta masoya har ya taimaka mata ta shirya cikin doguwar riga Arab gown black me stones gold dayawa a jiki sossai ya mata kyau kuma ya amshi fatanta kasancewarta fara, cikin tsantsan so yake kallonta kanta a kasa a hankali ya furta "kinyi kyau noory" murmushinta me kyau ta sakar mai tare da cewa "thanks" yace "our breakfast is ready" girgiza kai kawai tayi yaja hannunta suka fice da kanshi ya taimaka mata ta zauna a dining taja plate zata serving ya kar'be yana mata hararan wasa, da kanshi yayi serving plate d'aya ya matso dashi ya sa spoon da fork yana bata yana ci har suka gama, duban time yayi yaga har lokacin meeting d'inshi da ma'aikatanshi yayi dama ya fad'awa Ammah da qudra akan su shirya zeyi presenting d'insu ga ma'aikatan gidan gabad'aya................


Hannunshi a nata suka gangara suna isa step na karshe ta zame hannunta ganin Ammah zaune a parlorn se lokacin ta kula da yanayin Ammah a zuciyarta take cewa tab lallai Ammah irin manyan matan nan ne masu ji da kyau, mulki da kudi se yanzu yanayinta ya nuna sanye take da atampha cikin wadda hamrah ta d'inka mata holland ne maroon da adon sea green sossai d'inkin ya mata kyau bata d'aura d'ankwali ba amma ta yana babban mayafi sea green akan tulin gashin kanta da Yasha gyara da kayan gyaran kai da hamrah ta saya musu dama wani kam qudra bata san anfaninshi ba, ta d'aura kafa d'aya kan d'aya remote a hannunta tana chanza tasha suna had'a ido ta sakar musu murmushi me sanyi............


Cikin muryanta irin na haisam me cike da kasaita da isa take cewa "masha Allah, yarana kunyi kyau" ta karasa tana mikawa haisam da ya karaso gabanta hannunta dukawa yayi yayi pecking hannun, abunda ya lura tana matukar so kenan abunka da larabawa cikin sanyin murya yace "thanks Ammah"...........


Har kasa Hamrah ta duka ta gaishe ta cikin fara'a da tsantsar kulawa ta amsa mata kallon parlon yayi yana cewa "Ammah Ina yarinyarnan nifa bana son African time" murmushi tayi tace "Tana shiryawa but ina ga ta gama zuwa yanzu kam" tana rufe baki se ga qudra cikin milk and black gown tayi kyau sossai mayafin rigan ne akanta kaman yadda hamrah tayi cikin burgewa Ammah ke kallonsu a rayuwanta tana matukar so da daraja shigar larabawa amma kuma Allah ya gani soyayyar shigar hausa fulani shima sossai ya shiga ranta maganar haisam ne ya katseta yana cewa "Shall we?".........


Tace "yeah sure" ta mike suka fice ita dashi a gaba yayinda qudra suka jera da hamrah suna magana kasa kasa a haka suka karasa mota ya bud'ewa Ammah baya ta shiga qudra ma ta zagaya ta shiga yayinda hamrah ta shiga gaba don ta san in za'ayi irin wannan meeting d'in shi ke driving motan shiru ya d'auka Ammah na kallon wannan daular da d'anta ke ciki tana tasbihi ga ubangiji..........


A haka suka isa meeting hall d'in ya cika makil da ma'aikatanshi na gidan yana shiga suka mike yau yaqoob yasa an kara kujeru a high table, mic aka ba haisam yayi musu godiya ya kara da yadda yaji daadin nuna kulawarsu a gareshi kuma ko basu mishi jaje ba ba matsala tunda everything is fine and okey now ya kara da gabatar musu da mahaifiyarshi da sister d'inshi.............


A takaice ya basu asalin labarinshi na asali don a ganinshi basu da hurumin sanin gabad'aya tarihinshi tunda ba shi ke kasansu ba su ke kasanshi wannan ma shawaran yaqoob ne don ba yadda ya iya ne ya basu labarin a takaice..........


Anan suka tayashi murna d'aya bayan d'aya suka ringa zuwa suna gabatar da kansu a wurin Ammah a mutunce suka gaisa da musulman da kuma arnan bayan kowa ya watse ne suma suka kama hanyan compound d'insu haisam be shiga ciki ba se ma komawa owners corner da yayi yaqoob ya shiga gaba driver ya shiga securities d'inshi suka zagaye shi da motocinsu suka ja suka bar gidan..............


Suna shiga ciki Ammah ta shige d'aki ta barsu nan hamrah ta sake don in Ammah na wuri se tabi ta rasa natsuwarta tsabar kwarjinin matar, jan qudra tayi suka haura suna hira ta taya ta gyara part d'in gabad'aya duk da har lokacin bata dena jin yadda kasusuwanta ke ciwo ba amma ta d'aure sukayi sanitation sossai suna gamawa ana kiran azabar nan suka d'aura abinci spinach rice, pepper chicken and pasta salad se zobo sanin yadda haisam ke so dayake bibbiyu suke aikin duk da qudra bata wani iya ba amma tana taimakon hamrah sossai da kananan abubuwa kuma anan take koya, and ga enough hotplate da gas se suka yi saurin gamawa a tray gabad'aya suka shirya qudra ta sauka dashi qasa yayinda hamrah ta shige d'akinta don watsa ruwa.............


A gajiye tayi wankan ta fito ta shirya cikin palazzo trouser da karamin shirt black tayi tock-In ta saka turban cap a kanta tare da fesawa kanta turaruka masu sanyin kamshi don da ouds take anfani se haramain elmadina kallon kanta tayi a madubi taga yadda tayi kyau sossai powder ta d'auka ta shafa tare da shafa wet lipstick a bakinta, wayanta kawai ta d'auka ta fice a parlor ta tsaya tana gyara zaman curtains d'in parlorn se ji tayi an rungumeta ta baya kamshin turarenshi ya sanar da ita waye, da fara'a sossai tajuyo tana cewa "welcome home" 'bata fuska yayi yace "welcome home who?" Murmushi me sanyi tayi tace "welcome home honey"...........


Murmushi yayi a lokaci d'aya yana juya idonshi yace "really??? So I'm your honey?" A kunyace ta boye fuskanta a kirjinshi yace "by the way you look so breathtaking baby" ya karasa yana pecking goshinta tace "thanks" yace "and gaskiya ni ban son kunyan nan gaskiya yana cuta na" ya karasa yana tura lip d'inshi na kasa d'ago kanta tayi daga kirjinshi tana murmushi tace "muje Ammah na jiranmu" yace "for??" Tace "lunch" yace "okey baby let's go, I just can't wait to eat ur delicious meal, I missed it" girgiza kai kawai tayi tana mamakin haisam yau ne fa kawai da safe fa be ci abincinta ba kuma tana lura be wani ci na safen ba bata san me yasa ba.............


Duk da haisam ya zama mata me fara'a da wasa amma ga sauran mutane bayan Ammah, qudra and yaqoob se sagir duk a yadda suka sanshi da yake Mara fara'a sam izza, isa da kasaitar da ya d'auko a gun mahaifiyarshi har ma ya zarce ta, rashin wasa da time d'inshi duk sunanan a yadda suka sani daa.........


Bayan sunyi lunch suka d'an zauna sukayi hira sossai hamrah tayi kokarin sakewa da Ammah don nuna mata take ita bata d'auke ta surkuwa ba su a wurinsu Ina suka san wani surkuntaka shiyasa da ta zo nan tayi ta samun matsala da surukanta don iyayen miji 'ya'ya suke d'aukar surkuwa a wurinsu ayi hira da wasa har kwanciya akan kafa girki tare da sauransu...........


Nan Ammah ta kara fad'ad'a musu labarinta zamanta a yola da challenges data fuskanta da kuma yadda ta d'auki Africa, Nigeria in particular se la'asar duk suka mike haisam yayi waje Bayan yayi alwala a toilet d'in Ammah hamrah ta haura samanta..............


Bayan ta idar da sallah tana ninke sallaya taji shigowarshi amma be shigo d'akinta ba se ta zare hijab d'in jikinta ta kara gyara jikinta, ta jawo waya ta hau online suka fara chatting da friends d'inta kusan 30mins tana zaune se gashi ya shigo kashe data tayi tana kallonshi sanye yake da black vest da ya fito da duk wani kirar karfi na jikinshi se milk color three quarter murmushi suka sakarwa juna.............


Ya karaso ya warware farin kyallen dake hannunshi me kamshi yana nuna mata yace "mind if I close ur eyes?" Girgiza kai tayi tace "for??" Yace "it's a surprise baby, guess" yamutsa fuska tayi tukun ta kalleshi tana murmushi tace "you know, Am not good at guessing" yace "Ohk then let's go" rufe idonta yayi da kyallen yaja hannunta suka fice............


Daga saman balcony suka tsaya ya koma baynta ya rungume ta a hankali ya warware kyallen hannunshi d'aya rike da keyn mota yana karkad'a mata a fuska kallon keyn tayi tukun ta leka kasa zaro ido tayi she just can't believe what her eyes is showing her...........


'Bugatti La voiture Noire' most expensive/latest car in the world of the year 2020, juyowa tayi tana kallonshi cike da neman karin bayani zatayi magana kenan ya sa mata car key d'in a tafin hannunta yana gyad'a kai, hannu tasa a baki hawaye na cika idonta haisam just gift her with a car of 19million wani irin ihu ta sake da ya tsorata shi amma ganin tana tsalle da rawa a lokci d'aya yasa ya saki murmushi yana girgiza kai...........


Dama d'abi'ar su kenan ita da simra In har aka basu kyauta daya burgesu sun dinga ihu kenan suna tsalle da rawa, cike da so da burgewa yake kallonta yadda take rawan ne kuma ya bashi mamaki dama hamrah can dance? Ya tambayi kanshi...........


Be gama tunaninshi ba yaji ta rungumeshi tana cewa "thank yhu, thank yhu so much Ahhhhhhhh" ta kara yin wani ihun tana tsalle a jikinshi be zaci zatayi murna haka ba sam, nace Lallai haisam baka san yadda hamrah da simra ke hauka ba In sabon mota ya fito wannan ma kullum tana bibiye da shi kawai bata son cewa dad d'inta ya saya mata ne In ta duba yanayin da company d'insu ke ciki ba kaman da ba..............


Hannunta yaja suka koma parlor ya jawo wasu papers ya mika mata karba tayi ya bata biro ya nuna mata kasa yace tayi signing tayi tayi har ta gama tukun yace ta duba, dubawa tayi se kawai ta fashe mishi da kuka jawota yayi jikinshi yana shafa bayanta kyauta ce na companies d'inshi guda biyu 'iron industry dinshi dake kaduna' se 'textile company d'inshi na yola" kuka takeyi tana girgiza kai murya na rawa tace...........


"I can't collet this haisam, I can't it's too much ya kakeso nayi dasu ni bana so" a hankali yace "dole ki kar'ba sbd you deserve it hamrah ba abunda zanyi miki kyauta dashi a duniyan nan daze nuna miki how much you mean to me haskena, hamrah Ina sonki sossai and I want to apologize for what I did to yhu, I'm truly sorry and at same time just wanted to thank you for whatever you did for me, you don't know what I was going through..........


There was a time when I gave up on everything coz there was not a single reason to do anything, I was really stressed and hassled at that time but your timing in my life was more than perfect I think you entered my life as sunshine, you did so much for me that I really can't thank yhu enough, I just want to let you know that you are the best person I have ever met, I sincerely appreciate everything you did for me, thanks once Again, I Love yhu"..............Cikin muryan kuka ta furta "I Love yhu more" d'ago fuskanta yayi yana share mata hawaye da babban yatsanshi bata hankara ba se jin bakinshi tayi cikin nata ................


*hey readers!!! Ramadan mubarak fatan Allah ya amshi ibadunmu a wannan wata me albarka ya kuma sa muna daga cikin 'yan tattun bayi, Ameen thumma Ameen*.....

#vote 

#share

#comment

'Yar mutan Adamawa💞💞💞


             💞💞Hamrah💞💞


                                                     💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurinWattpad: muhdfatimagurin 
           *'yar mutan Adamawa*


"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!! May the mercy and blessings of Allah SWT be with u and ur family now And always, Happy Eid Mubarak Allah ya maimaita mana Ameen summa Ameen.Page➡3⃣2⃣

*************Bayan sunyi dinner ne haisam ke shedawa Ammah tafiyarsu baze yiwu gobe ba sbd shiga court da za'ayi cikin next week sede washegari Bayan zaman In Allah ya kaimu, tace "Ba komai Allah ya kaimu" ya kara da "Am ina son gobe in Allah ya kaimu zan tafi lagos bazan dawo ba se ana gobe za'a koma court sbd zan shiga kd, kano da yola Ina ga daga Chan ma zamu dawo da sagir"................


Ammah tace "Ohk Allah ya kaimu" ya kuma cewa "Ammah gobe zaku je shopping da yamma se ku saya duk abunda kuke bukata har trolleys sbd shirin tafiya" zatayi magana yayi saurin cewa "Adu'a Ammah" murmushi tayi kaman ya san ki zatayi se kawai tace "Allah ya kaimu yayi albarka" cikin farin ciki yace "Ameen" ya mike tare da mata se da safe ya haura yana satan kallon hamrah da suke hira qasa qasa da qudra............


Bayan ya shige ne qudra ta fara tsalle tana jin daadi zasu shopping girgiza kai kawai Ammah tayi tana murmushi kallon hamrah tayi tace "habibty tashi maza ba'a barin miji shi kad'ai se da safe" a kunyace hamrah ta mike tana amsawa ta haura, a parlor ta same shi yana zaune gabanshi ATM cards ne kusan guda biyar na first bank ya d'auka ya mika mata ta kar'ba tana tambayarshi "me za'ayi dashi" yace "in kunje shopping se kuyi anfani dashi" girgiza kai tayi tana cewa "A'a be dace ba gaskiya, Ammah baza taji dad'i ba mahaifiyarka ce fa be kamata komai zaka bata ya dinga fita daga hannun matarka ba, ka bata da kanka ka fad'a mata pin d'in hakan ze fi".....................


Gyad'a kai yayi se yanzu yake ganin kuskurenshi hakan ze iya sawa Ammah taji ba daadi murmushi yayi yace "na gode da tunatarwa, yauwa noory dama ina tunani me kike ganin zanyiwa Ammah da ze sa taji daad'i sossai" Shiru tayi tana tunani Chan kuma se tace "ka bari muje jordan d'in tukun" Kai ya gyad'a ita kuma tunani ta fara In har Ammah ta fito daga Hashemite kingdom to ba abunda zata bukata mijinta me kud'i ne sossai haka babanta ba abunda zata nema ta rasa toh me zata ba haisam shawara ya mata? Zata tambayi mom d'inta In shaa Allah....................:


"Ina so inyi having words da qudra" tace "Ohk lemme let her know" ta mike ta gangara bayan ta kirata ta shige d'akinshi don had'a mishi kaya ta barsu a parlor, shiru duk sukayi se kuma yace "hey sis" Kai ta d'ago tana murmushi tace "hello bro" shima murmushi yayi yace "wow ashe kina jin turanci" tace "Eh Ina d'an ji nayi primary a class, secondary ne de sede kullum naje na tsaya a window Ina kallon me akeyi wani lokacin har duka akemin amma hakan baze hana gobe na koma na makale a window ba, dukda government ne amma ba lefi na tsinci abubuwa dayawa"...................


Kai ya gyad'a Allah sarki rayuwa In ba kaddara ba kanwarshi? 'Yar sarkin jordan fa amma suka sha wannan wuya a duniya, don son kau da yanayin da ta shiga yasa shi cewa"me burinki?" Tace "Ina so inyi karatu amma na san yanzu kam ya wuce sbd na girma" yace "and wa ya gaya miki ana girma da karatu" kallonshi tayi da alamun tambaya yace "eh zaki iya yin karatunki Amma aure fa?".................


A sanyaye tace "wa ze iya aurena yanzu yaya? Neman 25 fa nake kuma banda ilimi" idonta ya ciko da hawaye, shiru yayi kaman baze ce komai ba se kuma yace "na miki miji In har kina so fa kenan ze rike ki da gaskiya da amana" tace "shi yace yana sona?" Girgiza kai yayi yace "sam sede nasan ko yanzu na bashi shawaran aurenki ze aureki sbd yadda ya yarda dani ya kuma yarda bazan cuceshi ba, ya kuma san bazan mishi za'bin banza ba".......................


Anan hamrah ta fito daga room d'inshi ta shige nata, kan qudra na qasa tana sake sake toh In har wani ya mugun yarda da yayan ta hk to me yasa ita baza ta yarda dashi ba? Ta tabbatar baze za'ba mata wadda ze cutar da ita ba, a hankali tace "Allah ya tabbatar da alkhairi yaya, duk abunda kace hk za'ayi" murmushi yayi yana yaba mata a zuciyarshi ganin kaman ta d'an damu yasa yace "karki damu zan bashi shawara bayan auren ya sama miki teacher ta kowar dake na 'yan wattani se kiyi waec ki shiga university".................


Murmushi me kyau ne ya subuce mata tace "na gode sossai yayana" shima murmushi yayi ta mike tana cewa "good night bro" yace "Allah ya tashemu lafiya" ta fice shi kuma ya mike ya shige room d'inshi direct toilet ya wuce bayan ya cire kaya ruwa me dumi da kamshi ya samu yana jiranshi murmushi yayi yana yabawa matarshi a zuciyarshi ganin yadda ya dawo ya samu gidan ya zama bayan yasan bata wani jin daadi sossai, bayan yayi wanka ya fito ne ya nufi wardrobe din shi don d'aukar nightwear se yaga trolley d'inshi madaidaici a jingine da jikin wardrobe   d'in.......................


Dukawa yayi ya kwantar tare da bud'ewa kayanshi ne a shirye tsab tsab a ciki duk wani abunda yasan ze bukata toh akwaishi a ciki lumshe ido yayi yana godiya ga Allah tabbas mata ni'ima ne a garesu maza, Ada In ze yi tafiya ba ruwanshi da wani shirya kaya sbd ba iyawa yayi ba sede duk garin da yaje In har be da gida toh sayan kaya yake, In kuma akwai gidanshi a garin toh yana da kayayyakinshi intact toiletries kuma sabbi ko yaushe akan kashe kud'i, amma ji yanzu ta mugun rage mishi adadin kud'in da ya kamata ya kashe a tafiyannan...................


Rufe trolley d'in yayi ya bud'e wardrobe ya d'auki nighties ya shirya ya hau gadonshi ya kwanta tare da jawo wayanshi ya danna mata kira tana d'agawa ya nemi ta kawo mishi coffee da to ta amsa shi, bata fi 20mins ba ta shigo rike da karamin tray a hannunta a bedside d'inshi ta ajiye tana kallon jikinta ganin yadda yake kallonta da lumsassun idanunshi, sanye take da black silk half gown me tsiririn hannu yabi jikinta sossai iyakarshi cinyanta ba d'ankwali a kanta gashinta dake gyare sossai se kamshi yake tayi parking d'inshi pony tail da ribbon babba d'aya fuskanta ba komai...............


Tayi mishi kyau sossai dakuna fuska tayi tana mishi alamun kallon na me, murmushi ya sakar mata tare da miko mata hannu yana mata alamun ta kama ze nuna mata tana rikewa ya jawo ta se jikinshi shagwa'bewa tayi cikin wani irin murya tace "Auuu ka tashi ka sha coffee d'inka ni bacci zanje nayi" cikin murmushi yace "zan sha ne, amma bari na gama aikin lada" zatayi magana taji ya had'e bakinsu ya fara sarrafa ta cikin yanayi me wuyar mantawa a garesu gabad'aya wani irin soyayya yake gwada mata da bata ta'ba zaton akwai shi a duniyarnan ba, a hankali na fice tare da ja musu kofa................


********


Kallon rigimammen fuskanta yayi a lokaci d'aya yana dafe kai, tsaye suke a bakin stairs dayake zigzag one ne ba ta yadda za'ayi na kasa yaga na sama idan ba haurawa yayi ba, sanye yake da three pieces suit milk da baki yayi kyau sossai gashinshin nan yasha gyara kaman ba gobe, hannunshi rike da brief case d'inshi an riga an fita da trolley d'inshi, ita kuwa tide ne a jikinta black color me kaman three quarter don be sauka kasa ba se crop top pink, pony tail hair packing nan de shine a kanta da pink ribbon babba lips d'inta akwai pink lipstick se kwalli da ta sakawa idanunta.................


Ya lura Tunda sukayi breakfast take fama da rigima duk sbd tafiyarshi toh Yanzu ma wai sallama suke, a shagwa'be ta langwa'bar da wuya tana taro hawaye a idanunta, puppy face yayi cikin sanyin murya yace "dan Allah noory kar ki bar hawayennan su zubo" kan ya rufe baki ma sun zubo dafe kai yayi a hankali yace "ya Allah, ya kike so inyi In na tafi na barki a wannan hali?" zafin hawayenta yakeji Sossai wlh shiyasa sam be son ganinsu, a hankali ya ajiye briefcase d'in hannunshi a jikin staircase ya matso sossai gabanta tare da sa hannu a kugunta cikin yanayi na rarrashi yace "haba mana noory, in ba kya so in tafi ne se na zauna, Allah ba zanyi abunda bakya so ba"...................


Yana rufe baki tana had'e bakinsu da farko tsayawa yayi da mugun mamaki ba tare da yayi responding ba daga baya kuma se ya bata had'in kai sossai sukayi kissing na juna kafin a hankali ta zame ta d'aura goshinta a kan kirjinshi tace "I'm gonna miss yhu" shima cikin kasa da murya yace "same here, ni tun jiya ma na fara missing naki" murmushi tayi ya kalli time yace "bari na wuce time na tafiya" se da ta d'ago tukun tace "Allah ya kiyaye ya tsare, Allah yaba da sa'an abunda aka je nema, a guji haram plz komai kankantarshi ruguza duk wani halal da aikin kirki yake, ka kula min da kanka" lumshe ido yayi murmushi na subuce mishi a hankali ya furta "Alhamdulillah, Ameen haskena"........................


Dukawa yayi ya d'auki briefcase d'inshi kafin yayi pecking cheeks d'inta da forehead dinta yace "thanks, pls take good care of yourself for me, I love you" tace "love you too" ya juya ya gangara ya san in yace ze biyewa hamrah se ya fasa tafiyan gabad'aya, a parlor ya samu Ammah da qudra suna hira Ammah ke tambayar har ya fito ya amsa da eh ya zaro ATM card ya mika mata yana fad'a mata pin d'in, godiya zata mishi ya 'bata fuska se kawai tayi mishi adu'o'i masu kyau suka raka shi har mota qudra na fad'a mishi tsarabar da ze kawo mata don ya tambayeta, seda suka ga ficewar motocin tukun suka koma..................


Wani irin farin cikin da nishad'in da be ta'ba tsintar kanshi a ciki ba yakeji yau wai shine zeyi tafiya har ya samu masu mishi adu'o'i da mishi hani da haram abunda be ta'ba samu ba tsawon fara aikinshi tabbas uwa ta daban ce haka mata ta gari rahama ce, Kula da yaqoob yayi boss d'inshi na good mood yasa shi fara janshi da hira Ai kuwa suna hira har sukayi departing......................


Yana isa kafin ya su isa masaukinsu ma seda ya kira ta ya tabbatar mata da saukarsu lafiya ya kuma bata umarnin In sunje shopping d'innan ta sama ma su Ammah waya sun d'an yi hira tukun sukayi sallama da niyyar In ya huta yyi refreshing zasu ci gaba, da yamma Ammah da qudra suka fito sanye da abayoyi bakake masu kyau sossai da hamrah ta ta'ba sayamusu ya amshi farin fatarsu sossai sunyi rapping gyalen a kansu dayake a wurin Ammah yawancin shiganta ita ma kenan tun tana buduruwa sbd yanayin dressing d'insu ne na larabawa.....................


Haurawa qudra tayi don duba hamrah ko ta shirya tana sa kai parlorn tace "wowwww, matar yaya wlh yayana yayi sa'a kinga wani irin kyaun da kikayi?" Cikin murmushi hamrah tace "koh kanwarmu" ta karasa tana kashe mata ido cikin zolaya, yamutsa fuska qudra tayi tana cewa "Lallai ma sister-in-law nafa girme miki kawai don kina auren yayana ne" a tare sukayi dariya tana sa shade me kyau a idonta sanye take cikin abaya baka itama me tsananin kyau da tsada don akallah ze yi 25k gyalen yane a kanta bayan tayi parking gashinta a tsakiya sossai tayi kyau kafanta sanye da Vinci flat shoe me kyau baki haka handbag d'inta ma................


Hannunta rike da sabon car key d'inta ganin irin kallon da qudra ta kafe ta dashi ne yasa ta wara ido tana cewa "ko kin zama yayanki ne? In kina son shade d'in akwai a kan mirror guda uku ki zabi wadda ya miki kyau ai da gudu qudra ta shige d'akin kafin ma hamrahn ta gama magana dariya tayi kawai, bata fi two minutes ba ta fito da wani kwame a fuskanta itama ba karamin kyau tayi ba.....................

#share 

#vote

#comment

'Yar mutan Adamawa💞💞💞

                   💞💞Hamrah💞💞
                                                   💞💞Writer: fateemah Muhammad gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin 


        *'yar mutan Adamawa*Page3⃣3⃣

***********


Suna sauka suka samu Ammah ta shiga toilet aikuwa hamrah taja hannunta tana cewa "kanwata come and save a soul zo kiyimin photo in samu na turawa hubby na" qudra ta fashe da dariya tace "Ai kam ya samu na kallo kar matan Lagos ko Adamawa su sace miki shi" ta'be baki hamrah tayi a lokacin suka isa jikin motanta ta shiga Snapchat ta mikawa qudra tana nuna mata yadda take so hoton ya fita complete her and her car se background na gidanta me cike da flowers da akayi roundabout a tsakiyar compund d'in..................


Sunyi kala uku kafin sukaji motsin Ammah da sauri hamrah ta juya tana dukar da kai murmushi Ammah tayi tana cewa "wow daughters kunga yadda kukayi kyau" murmushi hamrah tayi sanin kusan da ita Ammah takeyi sbd ai tare qudra suka shirya da Ammahn, da sauri qudra tace "mun gode Ammah" rolling eyes Ammah tayi tana ta'be baki tace "Uhmmm su o'o ba'a kasa da ita ba ta kwashe" shagwa'be fuska qudra tayi hamrah ta saci idon Ammah ta mata gwalo bubbuga kafa ta fara tana tafiya har ta zagaya ta bud'e gidan gaba ta shiga..................


Hamrah tayi murmushi tace "thanks Ammah" murmushi Ammah ta mayar mata tana son tambayarta haisam ya sauka lafiya Amma bata son hamrah tayi tunanin wani abu se kawai ta share, gidan baya hamrah ta bud'e mata ta shige ta bud'e driver sit ta shige ta tayar bakinta da adu'ar fita taja ta fice a natse....................


Duk inda motar hamrah ya wulga se an bishi da kallo tsabar kyaunshi da d'aukar ido da yakeyi suna isa sahad kallo ya koma kansu kowa na son sanin wane mammallakin motarnan a nigeria a tare suka bud'e kofofin suka fito they look so breathtaking just imagine farare kyawawa su fito cikin expensive car wearing expensive abayas 'yan matan sanye da glasses yayinda suka sa middle aged woman a tsakiyarsu, da kallo aka bi su har suka shige wasu kam zata sukayi ba sa jin ko zo da hausa, kowa 🛒 yaja suka fara zagayawa a waye da yake Ammah ba bakon abu bne a gareta qudra kuma tana da yanayi na wayayyu, zuwanta da hamrah sau d'aya ta d'auke komai da taga hamrahn tayi...................


Hamrah ma hanya daban tayi dukda bata da intension na d'aukar abubuwa dayawa a wurin perfumes ta tsaya tana duba designs d'inta taji phone d'inta na ringing d'agawa tayi tana murmushin sunan da tayi saving don har ranan bata chanza ba cikin muryanshin nan me gard'i da Amo yace "hey noory" tace "hey ya kake" yace "fyn but am tired tunda na sauka ban zauna ba" a shagwa'be tace "and you don't care to put anything in my stomach?"...................


Kara shigewa cikin kujeran da yake kai yayi yana jujjuyata a hankali yana jin muryanta na sa mishi wani affection da be san daga Ina ba be kuma ta'ba ji a muryan kowa ba se noorynshi, a kasalance yace "I've no appetite of every's woman cooking except for you and Ammah" murmushi tayi wadda yake jinshi har cikin ranshi tace "duk da hka de plz find something and eat I don't want yhu sitting with empty stomach"...............


Cikin zolaya yace "Ohk ma" sounding ya amshi umarni dariya sukayi a tare, ya kara cewa "are yhu at the shopping?" Tace "yes tun d'azu" yace "baby who drive?" Cikin ko In kula tace "me, why asking?" Yace "da wani mota kuka fita, kun fita da securities?" Kwa'be fuska tayi wannan irin questions d'in se kace d'an jarida, a kasalance yace "are yhu there?"...............


Tace "yes hubby, da new brand car na muka fita, with no security" da sauri ya mike ya zauna da kyau yana cewa "noory have u  think of what I'm thinking? What if god forbid something bad happens to yhu? You are not safe out there plz kuyi rushing ku koma gida" murmushi tayi tana jin yadda yake magana with tensed se kace ance wani abu ya samesu...............


Cikin ko In kula tace "nothing will happen in sha Allah just be positive ohk?" Yace "Ohk, but I have to deal with ko wani security dake gidannan they left you out without any protection knowing motar nan ba wadda ke da ita a nigeria a yadda kidnappers nan sukayi yawa and for sure you know who you are marrying to", jin da gaske kaman ranshi ya baci yasa tace "no plz ba fault d'insu bane ni na hana su" ita dama tun asali tana mugun son fita da securities sbd suna kara mata class but yanzu da tayi hankali se take ga kaman they will be a burden to her but tunda hubby d'inta na so ta fita dasu his wishes is her command.................."Ohkey fine" jin tayi shiru se ya zata ya d'an takura mata shi mutum ne da in yana son abu he so much cherish and overprotect that thing sbd if something happens be san kuma ya ze yi rayuwa ba, tace cikin excitement da ta tuna yadda hoton ta na d'azun yayi kyau "hubby hau watsapp ka ga wani abu it's a gift" murmushi yayi jin bama ta d'auki maganan da wani abu ba yace "ohkey noorie" ya offing phone d'in tare da kunna data abunda be ta'ba valuing ba kenan In ba akwai important abunda ze yi ba he's not the type of buying data to dawa zeyi chat, in ma browsing ne he prefer modems yayi a system hankalinshi kwance.................


Yana hawa yaga "QOMH" ta tura mishi sako shiga yayi ya danna kan sunnanta tare da downloading photon da ta tura mishi "masha Allah" yayi murmuring a chan kasan makoshi she's so so beautiful tana da wani irin abu a gareshi da ba ze iya fassarawa ba a hankali ya fita tare da danna kiran video call, ta bangarenta ganin video call yasata murmushi sossai AirPods ta ciro a jakanta ta makala a kunnenta suna ganin fuskan juna suka sakarwa juna murmushi me sanyi da kayatarwa a hankali yace...............


"Norrie am coming back I can't withstand it here I so much miss you" tace cikin zolaya "uhmm you are not welcome bcos I'm not missing u up here" shagwa'be fuska yyi ya tura lips yana wani kifkifta ido kaman yaro na shirin yin kuka, dariya me kyau ta fashe dashi har tana yin baya shagala yayi da kallonta she's so cute when she's laughing, in ta kalli yadda yake yi d'in kasa controlling dariyanta take, shi kuma tsakani da Allah ya ki maida fuskanshi normal se kara shagwa'bewa yakeyi..............


Gefenta taga yake kallo a lokaci d'aya ya had'e rai tun d'azun ya lura da gayen yana ta zirga zirga duk idanunshi kan hamrah wani irin abu ne yaji ya toshe mishi makoshi kishin maza ya motsa sounding so commanding yace "leave, ki samu su Ammah kila sun gama ke suke jira" ganin yadda yayin ta gane abunda yake nufi ta wuce dama ta gama d'ban perfumes d'in se ta kama tafiya a hankali zatayi offing yace "no plz don't off the call" hira ta fara janshi dashi don ya sake take tambayarshi tana son zuwa gida gobe plz zata nunawa su dad kyautar da ya mata be Musa mata ba sam yace Allah ya kaisu kallon background d'in yayi da sauri yace "baby koma baya plz" komawa tayi tana tambayar menene yace "just turn around" tana juyawa taga wani abaya me kyau sossai da ya tafi da ita............


Sea green ne da flowers red gaba da baya ba masu yawa ba kaman bubu yake daga wurin kirji har wrist d'in a sake yake se daga wrist d'in ne aka d'an kama anyi patterns ja a jiki yayi kyau sossai tace "should I take it?" Da sauri yace "yes baby ze miki kyau sossai" kallon kud'in tayi taga 30k cirowa tayi ta jefa a chart d'inta da ba wani abu se perfumes ihun qudra taji ba yadda ze ja hankalin mutane ba tana cewa "matar yaayaa" dafe goshi hamrah tayi tare da 'bata fuska tana kallon haisam tace "ba kaga qudra ba kooo?" Murmushinshi me class ya sake mata har hakwaranshi na bayyana yce "toh karya take? Ke ba matata bace" bata samu bashi amsa ba qudra ta iso tana leka fuskan wayan taga yayanta da sauri ta kar'be AirPods na hamrah ta saka tare da kar'ban wayan suka fara magana.............


Ciro kayan cikin chart d'inta tayi ta zuba a na qudra tana kallon trolleys da ta za'ba masu kyau dasu brown color ta fara tura musu, kayan da qudra ta jida kam wane, hango Ammah da sukayi yasa su karasawa gareta suka turawa masu packaging kaya aka fara had'awa qudra ce ta karasa da wayan tana mikawa Ammah da AirPod d'aya sawa Ammah tayi a kunne tana kallon fuskan favorite d'anta murmushi tayi suka fara gaisawa take tambayarshi yadda ya sauka da aiki har aka gama had'a musu suna waya ATM Ammah  ta bayar suka bata POS ta saka pin suka zare kud'insu tare da d'aukar musu kayan suka fice zuwa car, boot hamrah ta bud'e suka saka a ciki tayi wa yaran alheri suka fad'a mota anan layin sahad d'in suka tsaya wani shagon waya ta za'bar ma Ammah qudra ta zabi nata sukayi registering sim ana gab magrib suka isa wurin telanta suka bashi atampopi da laces d'inki yayi musu bill suka bashi advance suka wuce gida ana kiran magrib suna shiga gida a gajiye...............


Hamrah taso tsayawa ta musu takeaway sbd bata tunanin zata iya yin girki amma nauyin Ammah ya hanata

Allah ya taimake ta tana d'aura ido akan dining taga coolers farare manya masu kyau sossai a jere fes kusan hud'u direct taje ta bud'e ganin abinci yasa ta sauke ajiyan zuciya ta san aikin haisam ne sawa yayi akayi murmushi tayi a fili tace "thanks hubby" ta taka ta shige room d'inta seda tayi wanka tukun tayi sallah a gaggauce sbd lokacinshi dake tafiya se bayan isha tukun ta fito ta tattari coolers d'in tayi kasa dasu a dining na kasa ta shirya musu komai da zasu bukata................


Bayan sun gama ci kowa ya tafi ya kwanta yau ba hira sbd duk a gajiye suke, sun raba dare da haisam suna waya kan suka kwanta, washegari bayan sun gama abincin rana da qudra ta musu sallama ta tafi gidansu, cikin farin ciki iyayenta suka kar'beta bayan sun gama gaisawa ta jasu waje ta nuna musu motar ta securities da suka zo da ita a motarsu daban suna tsatsaye sallamansu tayi akan In ta tashi tafiya she will give them a call, sossai su dad sukayi mata murna suka koma parlor nan ta nuna musu takkaddun companies da haisam ya bata............


Ta kuma roki mafinta ya kar'ba ta bashi kyauta, yana girgiza kai yace "Aa'aa mamana, bazan kar'ba ba na nan Abuja ma kad'ai ya isheni bazan iya yawace yawace ba ki kula da kayanki da kanki tunda field d'inki ne, na gode sossai Allah ya miki albarka" a hankali tace "Ameen but" dad yayi saurin cewa "no but's princess" kallon mom tayi mom ta girgiza kai alamun baza ta sa baki ba ..................


Kallon dad tayi tace "dad gsky I want to be a complete house wife bazan iya handling companies d'innan ba and haisam be so I know ya bani ne kawai with no intention na bari na nayi aiki" mom tace "toh Yanzu ya za'ayi?" Dad yace "shawarannan ya kamata da mijinki zakiyi but ni a ganina ki bar companies d'in a hannunshi I'm very sure zai kula dasu kaman yana hannunshi ke se ki dinga samun profits d'inki daga gida"..................


Murmushi ta saki tana cewa "thanks dad you the best" a nan suka tsayar da shawaran zasuyi anfani, yininta cur da iyayenta ta se da tayi magrib ta kira securities d'inta suka zo da manyan baskets na abinci ta fita wadda tana isowa ta bawa maids d'insu umarnin girgikawa har mota suka rakata da kanta taja motarta securities suka bita a baya tana isa gida ana isha a parlorn kasa ta ajiye baskets d'in leka d'akinsu Ammah ta samu suna sallah...............


Fitowa tayi ta haura ta watsa ruwa sharp sharp ta fito tayi isha ta shirya cikin guntun gown fari wadda ya kai mata kaurinta me kauri ta sa hula a kanta ta fito kitchen ta shiga ta d'ibi plates da spoons da cups ta sa kan tray ta nufi fridge ta d'iba musu drinks da ruwa duk da akwai a kasan amma gwara ta d'iba daga nan, qasa ta gangara tana dafe kai kwanan nan ta rasa wani irin ciwon kai take me tsanani hk take kwana dashi kuma bata fad'awa haisam ba, a parlor ta samu su Ammah suka mata sannu da dawowa inda suke tambayarta lafiyansu mom d'inta tace suna gaidasu bismillah ta musu zuwa dining qudra tayi serving d'insu suka ci a parlor suka zauna suka d'an ta'ba hira tukun suka watse yau bata wani Jima tana waya da hubbyntan ba tace mishi ta gaji se da safe sukayi sallama ya kashe...................#vote

#share 

#comment'Yar mutan adamawa💞💞💞


                💞💞hamrah💞💞


                                                      💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin


Wattpad: muhdfatimagurin      *'yar mutan Adamawa*Page➡3⃣4⃣

***********


Bayan kwana uku 


Tsaye yake a parlorn part d'in sagir dake gidan bappanshi a nan cikin yola shagari phase 2 sanye yake da kananan kaya Jean da red polo shirt, hannunshi dake sanye da Rolex wristwatch d'aure kan Tv d'ayan hannun a kwankwasonshi kallon sagir da yake ta rawa a tsakiyar parlorn yayi fuskanshi d'auke da murmushi............


Yace "are yhu dancing?" Juyowa sagir yayi yana kallonshi a lokaci d'aya kuma yana ci gaba da rawanshi yace "I have no idea of what am doing, did you see me dancing?" Ya karasa da sigar tambaya, karkata kai haisam yayi tare da d'age gira yace "yeah I saw u dancing" a tare sukayi dariya...........


Cike da farin ciki da mamaki sagir ke kallon haisam ya manta when last yaga dariyar haisam baze iya tunawa ba, ko da haisam ya fara fara'a be ta'ba ganinshi yana dariya haka ba se yau sede murmushi, shi kuwa Haisam mamakin sagir yakeyi wani irin amini ne wannan me wuyar samu a duniya? Wani irin yarda sagir yayi dashi hk? Daga yace mishi ya mishi mata tun kan ya karasa sagir ya tashi ya kama rawa, be san wacce iri bace, mummuna ce ko kyakyawa, gurguwa ce ko makauniya duk be sani ba kuma da alamu tsakaninshi da Allah yayi accepting be gama tunanin da yakeyi ba yaji sagir yaja hannunshi zuwa kan cushion ya zaunar dashi tare da zama gefenshi yace.............


"Uhm Ina jinka yaushe zan tura?" Haisam yace "Da gaske nake yi maka fa sagir" ta'be baki sagir yayi tare da cewa "dama cewa nayi da wasa, haisam na sanka na san yadda kake sona baza ka ta'ba za'ba min abunda zanyi kuka dashi ba duk wacce ka za'ba min na san kyan d'abi'u da halinta ne ya sa ta sameni by the way bari na kira Anty Aimana (babbar yayarshi)na sanar da ita ta fi kowa matsamin akan aure, tukun na ma wani gari Amaryar tawa take".............


Lumshe ido haisam yayi yana hamdala a zuciyarshi tabbas qudra baza tayi dana sanin yarda da zabinshi ba sbd ya san sagir me rufa mata asiri ne duniya da Lahira dukan da sagir ya mishi a cinya ne yasa shi bud'e ido yana 'bata fuska yace "wani irin muguntar ce kuma wannan?" Sagir yace "ba'a sani ba ya za'ayi ka manna min hauka ina ta magana ka min shiru"............


"Sorry in-law" juya kai sagir yayi yana kallon haisam yace "pardon plz?" Haisam na murmushi kaman baze ce komai ba se kuma yace "in-law, qudra ce matar da na baka" lumshe ido sagir yayi murmushi kwance a fuskanshi yana tuna kyaunta da d'abi'unta ya rasa yadda akayi be yi wannan tunanin ba se da haisam ya zo mishi da maganan yaji sonta na shiganshi a hankali, dafashi da haisam yayi ne yasa shi dawowa daga tunanin da ya tafi ya dafe zuciyarshi tare da karkata kai yace "uhmm sonta ze fasa min zuciya".................


A tare suka saki dariya haisam na girgiza kai ya rasa yadda akayi duk shiriritar sagir daa be bashi dariya ko yayi niyyan yi se ya kasa, kallon time yayi tare da maida hankalinshi kan sagir yace "I'm leaving, you should be ready gobe 12 za mu tashi" mikewa sagir yayi yana amsawa da "toh ba matsala yauwa haisam" tsayuwa haisam yayi yana kallon sagir ganin he is so serious yasa shi ma maida hankali kan maganar da sagir ke shirin yi..............


"I thought gabad'aya 'yan uwan mahaifinka na nan yola? Amma bakayi maganar nemansu ba har kuma ka gama shiryawa tafiya wata kasa" Shiru haisam yayi yanayin fuskanshi na sauyawa yace "kana tunanin suna bukatana? After all wahalan da Ammah ta sha a hannunsu ta tafi sun kuma san ta tafi da jininsu did they care to follow her? Sun kuma san garinsu da kuma gidansu tunda iyayenta suka ba babana aurenta they don't care so I also don't, nayi rayuwa na ni kad'ai na ma I'm okey balle yanzu da nake da dangin Ammah da Ammah kanta"....................


Be jira amsan sagir ba ya fice ranshi 'bace, dafe kai sagir yayi yana mamakin wani irin mutum ne haisam shi da ya kamata yayi farin cikin saninsu amma ya d'auko wani abu ya d'aurawa kanshi? Gsky ya kamata suyi magana da hamrah ko zata iya tankwara shi a haisam d'in da yayiwa farin sani he meant what he said, tunawa da yayi be kar'bi numbern qudra ba yasa yabi bayan haisam da gudu a kusa da motarshi ya sameshi yana bud'ewa dayake be zo da securities ba ya barsu da yaqoob a company, sagir na isa ya sa hannu ya zare wayar dake hannun haisam.................


Wacce samsung S20 ultra ce kai tsaye ya shiga contact dayake ba security yake sawa wayan ba, cikin sauki ya samu lambar qudra an rubuta 'lil sis' d'auka yayi yasa a wayanshi tare da mikawa haisam wayanshi sukayi sallama haisam ya wuce.................


*********


Ta bangaren hamrah kuwa yau taje saloon da qudra suka biya gidan Maman arfat ta musu jan lalle me kyau sun d'an jima tukun suka sallameta suka ratse gidansu hamrah nan ma sun d'an jima tukun suka wuce tana driving motar securities na bayanta duk tunanin haisam takeyi yau throughout sau d'aya suka yi waya sun saba suyi waya akallah sau biyar ga text messages da suke exchanging se take jin wani iri ta san aiki ne ya mishi yawa ga itama tana cikin Jama'a. Da tunaninshi ta karasa gida suka gaisa da Ammah ta haura zuwa sama tana neman layinshi baya shiga a haka ta karasa tayi wanka ta fito ta shirya a gajiye take dadin abun  kwananan nan ba ita ke girki ba maid d'insu grace ke yi a kitchen na kasa tare da umarnin haisam, tana gama shiryawa ta fad'a gado a gajiye bata jima ba bacci yayi awon gaba da ita bayan ta turawa haisam texts guda biyu ta kuma turawa qudra text akan baza ta sauko ba gsky tayiwa Ammah se da safe...................


Washegari 


Tana tashi baccinta ta fara gyaran part d'inta kal kal ta gyare ta saka turarukan wutanta masu tsananin kamshi da tsada wuraren 10 ta gama a lokacin har sunyi waya da haisam sau biyu, tana gamawa ta fad'a kitchen ta fara girki, girki tayi musu me rai da lafiya tana gamawa ta fad'a wanka sharp sharp tayi ta fito ganin time ya gudu ta feshe jikinta ta ko ta Ina ta zauna tayi d'an nude makeup ba tarkace sam ta samo atamphar ta me kyau sossai ta saka riga da skirt ne da yaji ado da patterns d'in zanin d'aurin zarah buhari tayi me kyau gashinta dayasha kananan chuku ya sauka har bayanta yatsunta da style na jan lalle se sheki yakeyi ta gama 12 ta sauka wurin Ammah.............


A parlor ta samesu suna hiransu gaida Ammah tayi dayake basu had'u ba se lokacin Ammah ma ta shirya cikin material me kyau doguwar riga yayin da qudra ta saka atamphar super was da suka saya a shopping d'insu na kwanaki an mata d'inkin borno style tayi kyau ita ma zaman hira sukayi sunfi 50mins da zama tukun sukaji karan shigowan motoci ba wani bata lokaci haisam, sagir da yaqoob suka shigo..............


Da fara'a Ammah ta tarbe su suka samu wuri suka zazzauna idon haisam na kan matarshi ita kuma ta sunne kai kasa yayinda ta d'ayan 'bangaren Sagir ya kafe tashi gimbiyar da ido da yake har ya kirata sun fara ta'ba soyayyan dukda rabin akalan maganganun shike zuba mata, mikewa tayi taje ta shiryo musu ruwa da drinks gaigaisawa sukayi da juna haisam ya mike tare da wani karamin akwati ya ajiye gaban Ammah a rayuwanshi be ta'ba tafiya ya riko tsaraba ba se wannan kuma daadinshi yakeji har ranshi da wani karami ya haura a hannunshi, mikewa hamrah tayi ta nufi kan dining na parlorn da ba jimawan nan ta sa grace shirya abinci a wurin na su Ammah har sagir ta dudduba komai normal tukun ta musu bismillah da yake sagir me saurin sabo ne har ya sake da Ammah kaman mahaifiyarshi suna ta hira yna mata fulatanci jefi jefi kasancewar ta koyi kad'an zamanta da su, mikewa sukayi suka karaso qudra ta fara serving yayin da Hamrah ta juya ta haura samanta................


Tana shiga taji an jawota an rungume kamshin turarenshi ya sanar da ita wayene a tare suka sauke ajiyar zuciya a bayyane a kunnenta ya rad'a mata "I miss yhu noory" murmushi me sauti tayi tana tashi daga jikinshi kallon cikin idonshi tayi tare dayin wani far da ido tace "same dear" lumshe ido yayi cike da kaunarta yace "wlh sonki ze kasheni, noory kinyi kyau sossai kina da kyau ko bakiyi wanka ba" dariya ta fashe dashi tana girgiza kai kwa'be fuska yayi yace "tunda kin maida ni laughingstock bari na je inda akeyi dani" zaro wayanshi yayi cike da tsokana yana kallon yadda ta zazzare ido juya mata baya yayi yana murmushi ya nufi balcony yana makala waya a kunne seda ya kashe murya yace "hello baby"...............


A matukar hasale hamrah tayi kanshi tare da fisge wayan daga kunnenshi tana shirin ganin wacce me kararren kwanance ke soyayya da mijinta to her surprise se taga fuskan wayan ba komai se kyakyawar hotonta da ta d'auka randa zasu shopping yayi kyau sossai a fuskan wayan kallonshi tayi taga yana dariyarshi me kyau dinnan har wushiryanshi na nunawa kanshi tayi da gudu ya juya yayi d'aki a waje tabi bayanshi kaman wata yarinyar da aka kwacewa sweet za tabi ta kar'bi kayanta yana isa d'akinshi ya fad'a gado............


Itama tana shigowa ta yi kanshi ta hau ruwan cikinshi ta fara dukan kirjinshi dukan wasa hannunta duk biyu ya rike tare da juyata ta koma kasanshi a lokaci d'aya ya kurawa fuskanta ido tabbas ita ce farin cikinshi yana sonta har be san iya adadi ba kallon kitson kanta yayi da d'ankwalin ya zame ya bayyanashi a hankali ya shafa kan yace "I love this" a hankali ya dawo da hannunshi kan Hannunta ya gangara zuwa hannunta ya kamo yatsunta ya kurawa ido yana shafawa a hankali yace..................


"Ina son wannan ma noory ki dingayi yana ma hannunki kyau sossai" a kasalance ta d'aga mishi kai dawowa yayi da hannun da wani irin salo ya fara shafa fuskanta lumshe ido tayi tana jin yadda tsikar jikinta ke tashi a hankali yayi leaning sossai ya had'e bakinsu cikin wani irin salo ya fara sarrafata yana nuna mata yadda yayi missing d'inta nan ta bashi had'in kai tana nuna mishi tafi missing d'inshi, salun alun naja amadun kafana nayi waje............
#vote 

#share 

#comment
'Yar mutan Adamawa


💞💞💞


                      💞💞Hamrah💞💞
                                                          💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin


Wattpad: muhdfatimagurin 


               *'yar mutan Adamawa*


Page➡3⃣5⃣

***********


Kwance take akan kirjinshi a tsakiyar parlorn shi kuma yana jingine da jikin kujera remote a hannunshi yana chanza channels da misalin karfe 8 na safe ne dayake tafiya court d'in se 10 sunyi wanka de amma ba wadda ya shirya daga shi se three quarter ita ma wani d'an vest ne a jikinta me kaiwa cinya, gama breakfast d'insu kenan fita ma yayi niyyan yi amma sam ta ki barinshi.............


A tashar wrestling ya yada zango tana kallon tvn ta shagwa'be ita sam bata so murmushi yayi kan ya mika mata remote d'in zee world ta kai yana gani ya ta'be baki hannunshi dake jikinta ya fara yawo dashi yana abunda yaga dama dariya ta fara tana zillewa yace "ni gaskiya ki kyaleni inyi abunda raina yake so tunda kin hanani kallona".........


Tana dariya ta mika mishi remote d'in cikin dariya tace "gashi ga kayanka kalli abinda ranka ke so" yace "inaa ai kallon kuma ya fita raina" ci gaba yayi da yawo da hannunshi a jikinta tana zillewa tana dariya har seda yaga ta gaji tukun ya kama kwankwasonta ya d'agota suka kurawa juna ido.........


hure idonta yayi ta lumshe cikin rad'a yace "Every time I look into ur eyes, I remind myself how wonderful my life is. To the most beautiful wife in the whole world, I love you and I will always do" murmushi mai sanyi ta sakar mishi tasa yatsun hannunta tana shafa fuskanshi a hankali tace "you are the most amazing person I have ever met, you make the world a better place to live in. I feel so lucky to be loved by someone like you"...............


Murmushi suka sakarwa juna tayi pecking lips dinshi juya idanu yayi yana girgiza kai yace "it's not enough" dariya tayi tana mikewa da azama ya jawota ya dawo da ita within a blink ya hade bakinsu ya fara kissing in a most romantic way.........


Sun jima a haka kan suka mike ya d'auke ta in a bridal style suka shige d'aki, daga parlor nayi zamana Ina kallon zee world abina........


Bayan one hour suka fito a shirye cikin shiga ta kamala sanye yake da dakakkiyar blue black kashmiya an mishi d'inkin half jumpha da ya zauna a jikinshi sossai adon kayan kawai abun kallo ne takalmin kafanshi half cover black agogon hannunshi silver color basaj da ya d'an mishi ruwa se hula ta asalin bahaushe fari me blue zare yayi kyau irin sossai d'innan, ita kuma tana sanye da lace dark blue da pink flowers da kud'inshi ya kai kimanin dubu tamanin da biyar d'inkin doguwar riga ne me kyau akayi mata, peach gyale me d'an girma ta yafa da wani Gucci bag peach hk takalminta ma peach color ne tayi kyau sossai suka fito perfect...........


Kallon time haisam yayi yace "mun 'bata lokaci fa" tace "toh duk ba kai bane na san zuwa yanzu su Ammah sun wuce" murmushi yayi ya sa hannunshi na dama cikin nata ya fiddo wayanshi ya musu hoto ya fita yayi kyau sossai kuwa gangarawa sukayi suna hirar su a hankali har suka fito harabar gidan tabbas su Ammah sun tafi kallon sauran securities d'inshi yayi ya kira babban cikinsu ya tambaye shi yaqoob ya wuce, amsawa yayi da "yes sir, sun jima da fita da oga sagir da su mama" Kai haisam ya gyad'a tare da pointing wata black Bentley da yaji kud'i ya wanku se kyalli yake yi keyn securityn ya mika mishi ya san in yayi hakan yana nufin shi zeyi driven motar jan hannun hamrah yayi suka nufi motar da kanshi ya bud'e mata gaba ta shiga ya gyara mata gyalenta ya rufe mata kofar ya zagaya ya shiga ya tayar da adu'an shiga abin hawa ya ja suka fito tsakiyar compound d'in kan ma su gama fitowa securities mota biyu sun tsaya daga gefe seda ya jira d'aya ya shiga gaba tukun ya shiga tsakiya d'ayar motar ta bi bayansu suka fice...........


Sun isa court d'in a little bit late an d'an fara nisa a case din suna shiga ido gabad'aya ya dawo kansu kowa na furta 'tabarakallah masha Allah' sun had'u kuma sun dace da junansu wasu har pics suka musu, se da suka samu wuri suka zauna tukun aka ci gaba da fafatawa sunyi hiring wani lawyer yana iya kokarinshi ganin yayi defending d'insu sede mom ta toshe ko ina da shedodinta jefawa hisham tamabaya mom tayi tace "me yasa kayi kokarin raping matar haisam?" Ranshi a bace ga kafarshi da be samu wani kulawa ba ya fara wani irin ruwa da wari yayi baki sossai ya rame kaman ba hisham ba abun ya isheshi hk ya san ko ya ci gaba da boyewa ba abunda ze chanza tunda shedu sun riga da sun tabbata ya kuma san asalin hukuncinshi yanaga gwara ya fad'i gaskiya kawai kuma ya d'auki mataki akan hamrah don itace maccen da ya fara so a rayuwanshi har yanzu kuma yana sonta amma hassada da jin haushin haisam yasa ya danne son, ganin shigowansu yanzu kuma yayi shattering duk wani dream dinshi na rayuwa da ita ya tabbatar yanzu suna tsananin son junansu, runtse ido yayi tukun ya fara magana..............


"Tabbas ni maraya ne a gidan marayu na tashi kaman yadda haisam ya fad'a tunda na d'aura idona akan haisam naji duk duniya ba wadda na tsana irinshi duk da na san ba mugun abu irin hassada amma se zugan shed'an yayi tasiri a kaina tun bana nuna mishi 

Har ya kai na fara nuna mishi karara tabbas na tsangwame shi sossai duk da ya kasance Mara magana mara kuma son hayaniya duk abinda nke mishi be ta'ba kula ni ba, abunda ya dad'amin tsana da kinshi shine da su Alhj mas'ood da matarshi suka zo adopting d'a nayi murna sossai nayi ta bazawa friends d'ina a lokacin irin daular da zan tsinci kaina kwatsam se matarshi ta chanza ra'ayi suka ban hakuri tare da danka min kud'ade suka d'auki haisam suka tafi...........


Na shiga kunci sossai da damuwa tsanar haisam ya kara karfi a kaina duk da bani da wani wayo amma na kudiri abubuwa dayawa akan haisam na ko ba jima ko ba dad'e se na kuntata mishi ko ta wani irin hali ana haka Alhj murtala maidala yazo d'aukan yaro duk da yana da yara amma duk mata yana bukatar namiji da ze d'aurashi kan hanya irin tashi yazo an kawo mishi yara yana dubawa ni kuma nazo akwai yaron da ya ta'bamin kayana a cikinsu a lokacin kai har zuwa yanzu duk wadda yayi gigin ta'ba abuna ya shiga uku duk da yadda ake bamu kulawa ake kuma nuna mana illar fad'a da juna da kuma hukunci masu fad'a amma sam bana ji yaron takalmina da nake ji dashi yaje ya tsinka,da compass irin na cikin maths set d'innan nazo Ina juyoshi na chaka mishi a goshi ihu ya sake a take akayi kanmu ana rirrike ni Ina fisgewa don hakan be isheni ba, cewa akayi naje nayi kneel-down da murmushi Alhj murtala yazo ya rike hannuna yana cewa "na samu irin yaron da nake so" nan sukayi cike cike ya tafi dani.........


Ya bani kulawa sossai sede ya d'aurani kan gurbatacciyar hanya tun Ina karami na san komai nashi na kuma san yadda ya tsani Alhj mas'ood to the extend kawai don ya fishi arziki da d'aukaka kuma ba d'an nigeria ba, Alhj murtala yayi enrolling dina a best law school a duniya nayi karatu sossai akan harkan law duk sbd irin hk se da na gama jami'a na san da Alhj mas'ood wadda Alhj murtala ya d'auki kin duniya ya d'aura mishi duk da Alhj mas'ood d'in da zuciya d'aya yake hulda dashi kuma yana sane da irin makircin da yake kulla mishi amma Allah na kareshi shine yayi adopting haisam kuma yafi Alhj murtala kud'i...........


Nan na had'a buri na da burin Dad d'ina duk akan mutanen da basu san munayi ba, tun Ina school na san yadda Dad d'ina ya kashe Alhj mas'ood da abokan Alhj mas'ood kuma Abokan Alhj murtala a 'boye wato su Alhj mudan, bayan gama karatu na ne kuma na san irin dukiyar da aka barwa Haisam nan na fara nawa takun amma ban ta'ba nasara ba har dawowar wadda yayi wa su dad aiki da kuma had'uwana da matar haisam Ina ganinta Allah ya d'aura min sonta a lokacin ban san matarshi bace"...........


Matse hannun hamrah haisam yayi yanajin ranshi na kuna, cigaba da bada labari hisham yayi yadda ya gane matarshi ce hassadar shi ta danne son da yake mata yadda har yaso raping d'inta Allah ya kawo haisam da kuma ta gefe d'aya yadda Alhj murtala yayi ta makarkashiya ta hanyar turawa haisam recording din da yayi tun randa suka tattauna yadda zasu kashe Alhj mas'ood.............


Ya kara da "munyi playing game d'in sossai har kashe su Alhj mudan da nayi duk don mu d'aurawa haisam laifin a kasheshi kowa ya huta se kuma asirinmu ya tonu, tabbas hassada mugun ciwoce don har yanzu banji nadaman abunda na aikata ba kuma ko yanzu aka ban bindiga haisam zan kashe idan kuma na fita rayuwarshi zan cigaba da hari(innalillahi wainna ilaihi rajiun Allah ka rabamu da hassada da kyashi ka raba duk wani musulmi dashi don ruguza duk wani aikin lada yake ya kuma kashe zuciya yayi sanadiyar zefaka wuta, Ameen).............


Ya kara da "Ina son hamrah kuma Ina so ki sani har abada bazan dena sonki ba" Shiru court d'in ya d'auka tabbas In kaga ana magana akan abu toh abun be kai bane duk mamaki ya kashe mutanen wurin yayinda zuciyar haisam kuwa ke bugawa da tsananin karfi kara rike hannun hamrah yayi, da kyar Alkalin ya nitsar da kanshi yana kallon Alhj murtala da hisham da suke tsaye ko alamun da na sani babu a idanunsu, yaranshi da matarshi kuwa se kuka sukeyi gyaran murya alkalin yayi tukun ya fara magana kai tsaye ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya be saurari komai ba ya sallami kowa aka fara tafiya iyalansu na ta kuka............


Mom da haisam suka tsaya daga bakin kofar court d'in suna magana yayinda yaqoob, qudra, da Ammah ke tsaye wurin motocinsu sagir yana daga bayansu yana waya yayinda hamrah ke tsaye wurin wani bishiya tana danna waya dad dinta take son kira ganin be zo court d'in ba yau, inda taken kan hanya ne dole in anxo wucewa abi ta wurin In har daga cikin court din ka fito kuma duk wadda ke harabar wurin ze iya ganin komai dake faruwa a daidai wurin, polisawa ne suka fito dasu hisham da alhaj murtala suka nufi motan prison don kaisu a zartar musu da hukuncinsu sun iso daidai wurin da hamrah take ya tsaya yana kallonta itama tsayar da wayan da takeyi da dad d'inta tayi tana kallonshi da tausayawa ganin da gaske kallonta yake yasata ta'be baki ta juya mishi keya ta ci gaba da waya bata ankara ba taji an buga kanta da tsananin karfi da bishiyar da take fuskanta wani irin kara ta saki da yaja hankalin duk wadda ke haraban kanta da wani irin zafin nama yaqoob, haisam da sagir sukayi kansu suna isa haisam ya duka a matukar tsorace ya d'agota Inaaaa hannunta ya kama yaji pulse d'inta ya dena bugawa girgiza kai ya fara hawaye na cika idonshi.........


Yaqoob da sagir suna isowa a tare suka sauke wa hisham naushin da ya zubar mishi da hakora biyu to their greatest surprise yace "gara ta mutu kowa ma ya rasa da inyi uku babu" ya karasa yana fashewa da dariya wani irin duka suka rufeshi dashi polisawan basu hana ba securities d'in haisam na suka sa hannu Ammah da qudra da mom suka rirrike hannun hamrah qudra kam ta jima da fara kuka............


Mom ce tayi karfin halin cewa "hospital haisam" inaaa shima ya daskare a wurin ya rasa me zeyi hankalinshi kwata kwata baya jikinshi seda Ammah ta girgiza shi da karfi tana cewa "haisam tashi muje asibiti" tukun ya mike da ita a hannu da gudu yayi wurin mota, seda polisawan nan suka ga su sagir sun kusa kashe hisham tukun suka kwace shi suka shige mota rai a hannun Allah don ba karamin buguwa yayi ba, bin bayansu su haisam sagir sukayi zuwa HMS, A ICU suka same su suna tsatsaye haisam ya kasa shiga se zirga zirga yake yasan ko ya shiga ba abunda ze iya yi jijiyoyin kanshi duk sun mimmike idanunshi sunyi jaa kaman an zuba mishi borkono kirjinshi kuwa se a hankali he can't inaa baze iya rasata ba, dafashin da dr Anwar yayi ne yasa shi dago kai da sauri yana kallonshi idanunshi sun kara girma girgiza kai dr Anwar yayi, lumshe ido haisam yayi a hankali yake ja baya idanunshi a runtse Ammah ce tayi saurin rike hannunshi a hankali ya bud'e ido suna had'a ido ya fashe da kuka har jikinshi na rawa duk a rude suke amma kaman sunfi tausaywa haisam zama Ammah tayi ya duka kan gwiwowinshi ya d'aura kai a cinyanta yana kuka...............


Toh Jama'a..........

#share 

#comment 

#vote

'Yar mutan Adamawa
💞💞💞


                    💞💞Hamrah💞💞

                                                      💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin


Wattpad: muhdfatimagurin          *'yar mutan Adamawa*


Page➡3⃣6⃣

*************


Sossai ya birkice musu har ciwonshi ya kusa tashi doctor Anwar ne ya ce "sir ka kwantar da hankalinka plz ka san yanayin jikinka ba wai mutuwa tayi ba she will be ok in shaa Allah" da karfi haisam yace "In kwantar da hankali? My wife is there laying helplessly cikin mutuwa ko rayuwa and you are telling me in kwantar da hankali??" Cije hakwaranshi yayi tare da wargaza gashin kanshi, Ammah ce tace "Eh ka kwantar da hankalinka faruq shine magana, you have to be strong for her in ta kwanta ka kwanta kenan kai ba namiji bane man up kayi abunda ya dace Ohk?"....................


Sagir yace "yes plz man up my friend" Kai ya gyad'a yana share fuskanshi kallon mom yayi da take zaune shiru a gefe tabbas ita ma kwarin gwiwa take bukata she's her only daughter kuma duk sbd shi suke fuskantan hk a rayuwa yanayin jikin babanta ya tuna a hankali ya mike ya isa gabanta ya tsuguna yace "mom she will be ohhk In shaa Allah" Kai mom ta gyad'a tace "yeah In shaa Allah but before then, ya zanyi da mahaifinta haisam? You know how he loves her right? Kuma ka san yanayin jikinshi ba lafiya ne gareshi ba ko?" Haisam yace "mom zamu wuce yanzu with hamrah to Akila hospital of Amman, Jordan. I know main problem d'in be wuci brain bane kuma my good friend dr Isma'il Akilah is there he will take care of that, why not ki boyewa dad maganan kawai akan mun tafi jordan da su Ammah In yaso kya dinga kira a boye kina jin yanayin jikin in tayi sauki I will let you know yadda ko an fad'a mishi zuwa lokacin hankalinshi baze tashi ba"......................


Gyad'a kai mom tayi ta yarda da shawaranshi it's the best to her don she can't withstand it in aka ce ga mijinta ga kuma 'yarta a hankali tace "haisam brain kaman kace?" Yace "I'm not sure tunda ban duba abubuwan da sukayi ba" tace "ze iya yiwuwa haisam I'm afraid ka san accident da mukayi kwanaki sun ce there is high rate of samun matsala a brain d'inta so a dinga kula banda yawan tunani da kuma kiyaye buga kan".....................


A tsananin rud'e haisam yace "mom???? Subhanallah and nobody cares to let me know?" Tuna irin  ciwon kan da hamrah takeyi kwanaki yayi tunda shi doctor ne he know little about brain problems "innalillahi wa inna ilaihi rajiun, mom we are leaving right now" kallon su Ammah yayi suka gyad'a mishi kai yace "sagir plz ka tafi da su Ammah gida su shirya kafin na gama da hospital d'innan zamu sameku da su yaqoob a gidan" yaqoob yace "and shiryawana fa?" Haisam yace "you don't have to a gida zamu barka you should take care of everything here"....................


Yana maganan yana lalatsa waya su sagir suka nufi waje a dai dai lokacin ya fara waya "hello dr" ta d'aya bangaren dr Isma'il yace "hmmm manyan gaari kana duniya?" Da harshen turanci suke maganan haisam yayi guntun murmushi yace "many has happened dogon labari" dr Isma'il yace "wait haisam kai ne me dogon magana hk? And kaman I heard you smiling?" Wani murmushin haisam ya sake a dame yace "yeah duk zaka gani we are on our way with my wife she's seriously sick and she's behind of all the smiles and talks abunda kuka jima kuna nema da jira".......................


Dr Isma'il yace "subhanallah Ohk se kun iso zan tanadi komai kan zuwanku I know it's all about brain shi yasa ka neme ni" godiya haisam ya mishi sukayi sallama kallon dr Anwar yayi dr Anwar ya gyad'a mishi kai suka nufi d'akin dr Anwar da sauran doctors da suka duba ta suka hahhad'a duk wani abu da suke da tabbacin za'a bukata suka ba yaqoob, haisam na tsaye a kanta ya kurawa fuskanta ido duk kanta na'urori ne tayi wani fayau da ita kallon kayan jikinta yayi Allah kenan kaman ba da safen nan take sanye da tsadadden lace ba amma yanzu ita ce cikin cheap and plain yadi na marasa lafiya ...............


Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke ya juya yana kallon nurses mata da suke kokarin gyara gadon da zasu d'aurata zuwa mota ajiyar zuciya ya sauke zuciyarshi duk a chunkushe ya bi bayansu zuwa motan suka ja suka fice daga asibitin bayan doctors d'in sun mishi fatan alkahiri ya musu godiya tare da barin amanar asibitin a hannun dr Anwar suna isa gida suka nufi filin tashi da saukar jirginshi seda sukayi parking aka saka ta a jirgin ya gyara mata drip da ke hannunta fitowa yayi yana son komawa part d'insu don had'o musu 'yan kayayyakin da zasu bukata ya bar kula da hamrahn wurin nurse guda d'aya daya d'auko daga hospital dinshi sharp sharp ya nufi gida da yaqoob da sauran securities dinshi da gudu ya haura upstairs be tsaya magana da sagir dake zaune parlorn kasan ba d'akinshi ya shiga ya za'ba kaya kad'an abunda ze bukata kawai ya d'auka ya shiga d'akinta ya had'a wasu abubuwan idonshi ne ya kai kan vest d'inta da ta sa da safe kan shiryawansu a hnkli ya d'auka ya kai fuskanshi ya shaki kamshinta tare da lumshe ido a take idon ya cika da hawaye da sauri kuma ya mayar yana tuna maganan Mom kafin ta wuce gida daga asibiti "be strong ga 'yata a hannuka I know you zaka iya sbd na yarda da kai take care of her plz".................


Saka sauran abubuwan da ya d'auka yayi yaja trolley d'in ya fice a kasa ya samu su Ammah a tsatsaye da trolleys d'insu be son kallon da suke mishin nan sam hakan ya sa ya kwakwulo murmushi ya sa a fuskanshi yana cewa "shall we???" A tare sukace "yes sure" suka fice suka shishiga mota zuwa airport na gidan basu kara good 20mins ba suka d'aga yaqoob da Aisha suka bi su da adu'o'i...................**************


Babban Birnin Amman ta kasar JordanSun sauka lafiya dr Isma'il da kanshi ya zo taran su ya zo da motoci guda biyu da Ambulance tunda suka sauka Ammah ke kallon mahaifarta duk da abubuwa dayawa sun Chanza amma that feelings of being home na nan hawaye taji yana cika mata ido kaman batayi rayuwa a nan ba ko ina ya chanza abubuwa dayawa da babu su amma yanzu komai masha Allah daga ta ga inda suka nufa ta gane Abdul-monem Riad street kuma a nan Akilah hospital yake a wurin ake kawo jinyar duk wani d'an masarautarsu idan ciwon yafi karfin asibitinsu..................


Suna isa aka sauketa aka shige da ita ICU ko yatsa bata motsawa Dr. Ismail ya basu tabbacin zasu iya tafiya yanzu aiki zasu shiga da ita kuma gsky basa son wuri ya kasance da hayaniya sbd wargi kad'an ze iya sawa kwakwalwan ya ta'bu se bayan four hours zasu fito daga aikinsu na farko kuma za'a mata alluran bacci na about week in ta farka komai normal shi kenan In kuma aka samu Akasi za'a sake aikin abunda ba'a fata, sossai haisam yayiwa dr Ismail godiya, baza a Kirasu abokai ba sede course mate suna yawanyin assignment da sauransu tare suna gaisawa kasancewarsu musulmai duk da shi yaki sakin jiki da su amma normal zasu gaisa har su ringa tsokanan shi da d'an kurma bayan sun gama karatu sun jima basu had'u ba  seda aka kawowa dr Isma'il wani aiki akan transplant na kidney me tsananin hatsari ya san haisam ze iya taimakawa amma yana tsoron kiranshi yaki zuwa sanin halinshi se kawai ya had'a mahaifin mutumin wato tsohon sarkin jordan da haisam din ya roki alfarma har haisam ya yarda ya zo ya musu aiki ya taimaki sarkinsu wato Abdallah II.................


Bayan sun bar Asibitin suka nufi Hashemite kingdom dr Ismail ne yasa drivers dinshi da suka d'auko su daga Airport kaisu masarautar, kusa da Ammah yake zaune a sit d'in baya yayinda qudra da sagir ke motar baya dukda haisam na ciki damuwan rashin lafiyar matarshi amma sam fuskanshi be nuna hakan yanzu ganin Ammah a yanayi na curiosity yasa shi ajiye nashi damuwar a gefe ya fara comforting d'inta kallonshi tayi ta sakar mishi murmushin yake shima murmushin ya mayar mata....................


Sun isa get d'in masarautar aka hana su shiga tunda basu fad'i wadda suka zo gani ba tunani Ammah tayi na waye zata ce toh ta san ko ya zatayi baza'a barta ganin sarki haka kawai ba se kawai tace "wurin Ummi tazo daga wata kasa 'yar friend d'inta ce tayi missing phone d'inta ne yasa bata kirata ba" kira wani daga cikin masu gadin yayi a waya, Ammah bata damu ba ta san Ummi ko bata Santa ba ba kuma ta san da zuwanta ba zata ce a barta ta shigo ai kuwa bata gama tunanin ba yace "zaku iya shiga" drivers d'in suka ja zuwa ciki da kwatancen bayin da suke tsakar gidan suka isa part d'in Ummi komai an chanza shi a masarautar bata ga abunda ta sani ko guda ba, sallaman drivers din sukayi haisam ya musu alheri..................


A hankali Ammah ta sa kai parlorn bayan bayin sun masu iso su haisam suna bayanta wata tsohuwar mata da zatayi shekara saba'in fara ce sol kyakyawa tsufanta be wani nuna ba sossai sbd yadda take cikin kud'i ga wayewa da take dashi glass ne fari a idonta hannunta rike da wani qur'ani da be wuci izu goma ba, Ammah na cewa "salamu Alaikum" matar ta d'aga kai da sauri tana kallon bakin kofar ajiye qur'anin hannunta tayi tana qyara zaman glass d'in idonta..................


Cikin harshen larabci ta ce "wayene?" Ammah tace cikin rawan murya "Ummiiii" cikin rawan jiki matar ta fara lalu'ba sandar ta me tsada tana kamawa ta dafa tana cewa "muryan wa nake ji hk kaman habeebty?" Ammah tace "ni ce Ummi nice" da sauri ta karasa ta fad'a kan ummin har seda ta koma da baya ta zauna Ammah ta kwanta akan cinyarta ta fara kuka me ta'ba zuciya..................


Sossai sukayi kuka da kyar ummi ta tsayar da kukan da takeyi ta fara rarrashin Ammah har ta samu tayi shiru Ammah ta kama hannun Haisam da qudra suma suka duka gabanta kallon Ammah tayi da alamun tambaya Ammah tace "faruq" tana nuna haisam se kuma ta kalli qudra tace "ban san ko kuna da masaniyar na tafi da ciki ba" Ummi tace "kwarai ma kuwa abunda yafi d'aga mana hankali kenan gaki ga ciki ga kuma faruq sossai muka shiga damuwa Ina kika shiga habeebty?".......................


Ammah tace "dogon labari ne Ummi Ina su hussain da babanshi ya su Ammi na?" Wani kukan Ummi tasa hakan ya sa Ammah cikin rud'u a rud'e tace "me ya faru waye ya rasu a cikinsu?" Ummi tace cikin Kuka "Allah yayiwa Ammi da Abbunki rasuwa sanadiyar gobara da ya tashi musu cikin dare Abbi d'inku kuma last year ya rasu" innalillahi wainna ilaihi rajiun duk 'yan parlorn suka maimaita  qudra da Ammah a tare suka fashe da kuka Ammah na had'awa da kiran sunan Allah duk sun gane iyayen Ammah ne suka rasu tunda nan d'in cikin masarautar ne..............,..


Sun kai 10mins suna kuka da kyar haisam yayi karfin halin basu baki da turanci don harda Ummi yake kuma bata jin hausa har ya samu sukayi shiru, Ummi ta d'auki wayanta tayi kira da larabci tayi magana na mintuna be wuci biyu ba ta kashe ba'ayi 5mins ba wani dattijo ya shigo ze yi 50 daga ka ganshi zaka san ya jiqu da mulki don yadda yake tafiya ma kad'ai abun kallo ne sam tsufa be bayyana mishi ba suna tsananin kama da qudra hankalinshi na kan mahaifiyarshi yace cikin harshen larabci "lafiya kuwa Ummi? Me ya faru wannan kiran gagawa?" Bata bashi amsa ba se ga Matashin saurayi ya shigo da wasu yara mata biyu zasuyi 16 suna zama se ga wata zatayi sa'a da haisam itama ta shigo a yangance ta samu wuri ta zauna..................


Kallon Abdallah Ummi tayi tare da nuna mishi Ammah a hankali ya juyo ya kalleta lokaci d'aya ya mike kaman wadda aka tsikarawa allura ya iso gabanta tare da kama hannunta hawaye se gangara yake a idonshi sam ya kasa magana hugging d'inshi Ammah tayi tana cewa "yaya" zuwa yanzu duk hawayenta sun bushe ba karamin kuka tayi ba d'azu sunkai 5mins a hk tukun tayi breaking hug d'in ta sa tafin hannunta ta share mishi hawayenshi cikin rawan murya yace "noor Ina kika shiga? Ina ne ban nemeki ba amma ban sameki ba Ina d'ana faruq? Ina cikin da kika tafi dashi?".......................


Kallon el-Hussein Ammah tayi se taga ya juya kanshi gefe maida kallonta tayi kan Abdallah Da alamun tambaya se ya dukar da kai shima ba yadda beyi da El-Hussein ya yarda Ammanshi wani abu ne ya sameta ba amma yaki yana bin maganar Queen Raina da yanzu take garkame tsabar haukan da takeyi gashi harshenta ya murd'e ta kasa magana ballantana su san me ya sameta, Ammah ce ta katse shirun da fara basu labarin abunda ya faru da ita daga farko har karshe zuwa labarin haisam wadda ya bayar a court daga rabuwansu har I zuwa yanzu, duk 'yan parlorn seda kowa ya zubda hawaye da sauri el-Hussein ya rarrafo ya dawo gabanta tare da had'e hannunshi yana cewa "Ammah ki yafemin ashe Maami 'Queen raina' karya tayi ta fad'amin a kanki har ya kai na kullace ki a zuciya I'm sorry ki yafemin" kanshi ta fara shafawa a hnkli tace "na yafema hussein" kallon qudra Abba yayi tare da bud'e mata hannu yace "daughter" da sauri ta karasa ta fad'a jikinshi, Ummi kuwa faruq ta bud'ewa hannu ya karasa yayi hugging d'inta, wani irin ihu sukaji da sauri suka mike Abba wato Abdallah shine a gaba suka nufi wani part me tsananin kyau da sauri.........................#vote

#share 

#comment'Yar mutan Adamawa💞💞💞


                   💞💞Hamrah💞💞
                                                       💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin


Wattpad: muhdfatimagurin               *'yar mutan Adamawa*


Page➡3⃣7⃣

************


Tsaye take a wani d'aki da kofanshi kaman na cell an d'aure da sarka ta waje na waje ze iya hangan duk abinda na ciki keyi, part d'in mai tsananin kyau ne amma nan wurin warin da yakeyi Allah ne kad'ai ya sani  kasan inda take duk abinci ne ru'babbu irin cimansu jikin ta duk kuraje masu tsananin wari gashin kanta wasu ta fisfisgesu wasu kuma Na nan jikinta fari ne amma fuskanta baki kirin idonta a zazzare tana ihu harshenta ya zazzago idonta na sauka kan Ammah ta kara saka ihu tana nuna ta kaman abun asiri harshen dake lilo ya koma ta fara maganganu tana tona duk wani asirin kanta..................


Duk abunda tayi seda ta amoyo shi tana gamawa ta fara wani abu kaman me sharafan mutuwa kaman kuma wacce ake saduwa da ita ta muguwar hanya a haka tana zunduma ihu ta mutu fuskanta baki Kirin kaman gawayi, innalillahi wainna ilaihi rajiun waenda suke wurin sukayi ta nanatawa yaranta dake wurin mata su uku se kuka sukeyi Qudra ma seda ta mata hawaye sbd ya fahimci Itace kishiyar mamanta da tayi sanadiyar haukacewanta da tashinsu a titi..........................


Ammah ma kuka takeyi had'e da salati tana godiya ga Allah, Abbah kam hannun kananan 'yan matan nan ya kama ya juya a hankali suka fice, Ammah ce ta kalli d'ayan buduruwan da zatayi sa'an Haisam tace "Iman??" Kai buduruwan ta gyad'a hannunta Ammah ta kama suka nufi waje el Hussein, haisam da Ummi ke rike da hannunshi se sagir suka bi bayanta, duk tunanin duniya ya addabe su rayuwa kenan duk kudinka duk mulkinka In baka aikata me kyau ba bazaka ga da kyau ba musamman ga waenda suka santa suka san irin izza da isarta gashi ta mutu a wulakance.....................


Part d'in Ummi suka koma anan suka sami Abba da 'yan matan alamun 'yan biyu ne zaune suna ta kuka yana basu baki d'ayarce tace "yanzu duk wannan mugun abun Maami ce ta aikata?" Shiru yayi d'ayar tace "Wannan itace Maman ya el-hussein da Maami tace muguwa ce bata da hali mai kyau" Ummi tace "ba wani halin 'yata me wuyar samu ne bata da mugunta sam In tana dashi kuma toh tare da ubanku sbd nono ne kad'ai ban shayar da ita ba".................


Ammah ce tace "Ummi mna, yarane duk abunda aka fad'amusu dashi zasuyi anfani, ya sunansu?" Ta maida tambayan kan Abbah, yace "Yasmin da Jasmin, ga yarsu Chan itakam kin Santa ai?" Kai Ammah ta gyad'a tare da dafa kan Iman dake kwance kan kafanta tana kuka tace "sannu Iman Allah ya baku hakurin rashi ya kyautata makwancinta".....................


Cikin kuka buduruwan tace "I'm so sorry Ammah, Dan Allah ki yafemata on our behalf" Ammah tace "na yafemata Allah ya yafemana gabad'aya" suka amsa da Amin iman tace "ban san da wani baki zan gode miki ba, kin kasance me kyakyawar zuciya bayan duk irin wahalan da kikasha ta sanadiyarta gashi kin yafe mata, ban san me yasa kullum take addressing d'inki da bakar munafuka ba dama kece kika haifeni" ta karasa da fashewa da wani irin kuka after all muggan labaran da taji yau batayi tsammanin mahaifiyarta zata samu rahaman ubangiji ba yadda mutuwarta kad'ai ya kasance ya isheka ishara da alama, mikewa zaune iman tayi ta sauka kasa inda qudra take ta kama hannunta tace "sis????" Se kuma ta fashe da kuka................


Rungumanta qudra tayi sauran ma suka sauko suka rungumeta, el-Hussein ma karasowa yayi tare da hugging dinsu gabad'aya Abbah da Ammah suka zubawa haisam ido karamin tsaki yaja tare da mikewa ya karaso ya shiga family hug d'in for minutes suka saki juna Abbah yace "Faruq dr. Haisam" yayi maganar kaman akwai sanayar juna tsakaninsu murmushi haisam yayi ummi tace "ka sanshi ne?" Yace "Ummi kin manta shine Abbi ya roka yazo yamin transplant?" Kallon Haisam Ummi tayi da turanci tace "shine kuwa, ashe na gida ne rashin sani fa kenan" kiran bayi Ummi tayi ta bada umarnin kaisu masauki da sauri 'yan biyu sukace "zamu zauna da Anty qudra" iman tayi saurin cewa "laa la la la ku 'yan biyu muma 'yan biyu so a dakina zata zauna" a tare suka ce "Deedi last time we check bakya son kowa ya shiga room dinki why now?" Tace "bcos she's my favorite sis" shagwa'bewa sukayi suna kallon Abbah yace "korafi be karbu ba ku biyu su biyu final".....................


Dariya gabad'aya 'yan parlorn suka sa cikin fusata suka mike suna bubbuga kafa suka fice duk da qudra ba jin turanci take ba ta fahimci akanta ne, El-hussein yace "bro faruq or dr haisam da friend dinshi kuma part dina right?" Ya karasa yana kallon Ummi kwa'be fuska ummi tayi tace "Aka gayamaka shi tuzuru ne irinka? Toh da matarshi part daban za'a ware musu a gyare ba me shiga se shi, bayinsu da matarshi baze iya zama da tuzurai ba" dariya 'yan parlorn suka saka ya mike da gudu yayi kan Iman da gudu tayi waje tana kiran qudra tabi bayanta.....................


Shafa Kai haisam yayi yace "godiya nake ummi" tace "karka damu u my favorite jika" murmushi Ammah tayi ta san yadda Ummi ke son haisam tun da, Abbah yace "Ummi inaga In akayi asr se a maida auren mu da noor a kuma sallaci raina, ko ya kika gani" tace "hakan ma yayi Allah yaji kanta" suka amsa da Ameen banda haisam da ya ta'be baki, A tare matasan suka fita, inda aka ware mishi yana facing na el-hussein suna isa suka rabu Bayan el-Hussein ya nuna mishi, bayi na rike da trolleys dinsu seda ya tabbatar musu yana zuwa wanka kawai zeyi ya shigo part din Hussein kan suka barshi Hussein dinma halinsu d'aya da sagir...................


************


Bayan sallahn asr kuwa aka maida auren su Ammah aka sallaci Raina dukda kowa ya shede ta da bakin hali da kin talakawa amma yau gashi talakawan ke sallatanta kuma su zasu kaita cikin kasa su binne (Allah ya mna kyakyawar karshe Amin), kafin asr din duk 'yan uwan Ammah sun zo da 'yayansu suka kara yin wani kukan na tunawa da iyayensu seda Ummi tayi musu fad'a sun gaisa da su haisam da qudra, haisam ya sake dasu sossai duk da halinshin nan na nan yayi introducing sagir a matsayin me neman auren qudra kuma abokinshi duk da suma seda suka ji labarinsu kaf...................


Ammah ma bata san sagir da qudra na soyayya ba seda haisam ya fad'a and she's happy for her daughter sagir is a good person, har kwarya kwaryan walima Sarki Abdallah II yasa aka had'a na dawowar matarshi da 'ya'yanshi duk Amman sun san da farin cikin mai martaba kasancewar kyautar da yayi ba na wasa bane sun tayashi murna sbd dayawa sun san matsalan da ya shiga sanadiyar 'batar ta, ana cikin ribibin haisam ya kar'bi keyn mota daga hannun Hussein ya zame se asibiti ya samu sun fito ita kuma tana bacci, kasancewar shi babba kuma sananne don yana jerin matasa masu ji da kud'i yasa suka barshi ya shiga kai tsaye sbd basu san da zuwanshi ba kuma dr Isma'il na cikin theatre, shiru ya zauna a d'akin hannunshi na cikin nata ya kurawa fuskan ta ido........................


***********


Be san iya adadin da ya d'auka zaune a wurin ba se ji yayi an dafa kafad'anshi d'agowa yayi se yaga Ammah da Abbah se Ummi da sagir da Hussein mikewa yayi ya fito Ummi da Abba da Hussein suka tsaya kallon hamrah yayinda Ammah da sagir suka bi bayanshi tsaye suka sameshi ya had'a kai da gini duk yanayinshi ya chanza Ammah tace "haisam wai damuwan nan na menene?" Kallon Ammah yayi kaman zeyi magana se kuma ya fasa hannunshi sagir yaja suka zauna a sits din dake wurin yace "Haisam be kamata ba sam ka san illar wannan tunanin ga lafiyanka ko? In ita hamrahn ta tashi ta sameka cikin wani hali sbd da ita zataji daadi? Dan Allah ka daure ko don alkawarin da ka d'aukarwa mahaifiyarta"....................


Hawayen da ya cika idonshi ya mayar yace "I'm trying sagir, I'm trying" Ammah tace "we know but ka kara Allah ze bata lafiya" Kai ya d'aga Ummi da su Abba suka fito daga d'akin Ummi tace "ragon namiji a hk kakeso na aurekan?" Cikin yanayin magananshi na kaman baya so yace "dama nace Ina sonki?"dakune fuska tayi ta wani 'bata baki, Dariya suka saka har shi murmushi yayi, Abbah ya kara mishi nasiha suka ce suje gida tunda asibitin ba'a kwana kuma se gobe da safe kuma ake tunanin farkawanta, yace "a'a zan kwana da ita a matsayin doctor tunda Ina aiki dasu ai" Ba yadda basuyi dashiba akan ya bisu yaki sam hk suka barshi da niyyan za'a  turo mishi abinci kuma ya fad'i abinda yake bukata yace babu In ma akwai akwai mota a hannunshi kuma Atm dinshi na jikinshi, sallama suka mishi sagir kam yace yana nan se Chan dare ze dawo Hussein ma yace nan ze zauna........................


An aiko bayi da dogarai suka kawo musu abinci da darduma kato me taushi har da pillo da wani extra borgo aka kuma zuba dogarai kusan takwas a bakin kofan ya san duk aikin Ummi ne matar tana sonshi, sun jima sossai dasu sagir har 11 tukun ya korasu suka tafi ya dawo ya zauna ya ci gaba da aikin kallonta wayanta ya d'auko dayasaka a aljihunshi yayi sliding ba key pictures ya shiga ya fara gani d'aya bayan d'aya duk nata yawanci na tun da ne kafin ya shigo rayuwanta komai takeyi se tayi pic lokacin in tana cin abinci ne, kafin bacci, kallon film, in taje cinema, a beaches kala kala na wurare daban daban a school ne, wasu har wadda take brush, ya kasa gajiya da kallon hotunan ta wasu yayi dariya wasu yayi tsaki sbd da maza wasu ya kwaikwayi yadda tayi da fuska shi kad'ai kuma sai yayi murmushi....................


Har wuraren 2 tukun ya mike ya shiga toilet yayi alwala ya zo ya hau kan sallaya ya fara jera nafilfili yakai 3:30 kan ya kwanta bacci kad'an yayi aka kira assalatu ya mike ya gabatar da sallah ya koma ya kishingid'a yana azkar d'inshi wuraren 6 masu shara da mopping suka shigo ya basu wuri sukayi suka gama suna gamawa doctors suka fara round kafin a iso d'akinsu har masu kawo abinci daga masaurauta sun kawo musu breakfast be ta'ba bama har doctor Isma'il ya shigo suka gaisa yake tambayanshi me jiki, ya amsa da da sauki ya duba ta ba wani matsala farkawanta kawai suke bukata..........................


Around 9 su Ammah suka zo basu jima da zuwaba ya tafi akan ze je yayi wanka ya dawo se wuraren 10 yana shigowa hamrah na motsawa da sauri ya karasa jikin gadon yana kallon fuskanta a hankali ta bud'e ido ta zubawa haisam d'an 'bata fuska tayi tare da juya idonta zuwa kan Ammah kallonta tayi sossai tukun ta kara juya fuska zuwa kan sagir da el-hussein duk kallon fishaaa tayi musu ta dawo da idonta kan haisam yace "hamrah" a hnkali tace "who are you" wani irin numfashi haisam yaja da ya kusa tafiya gabad'aya da kyar ya samu numfashin ya dawo baya baya ya farayi yana girgiza kai da sauri sagir ya kamashi ya aijiye a kan kujera ya fita da sauri ya kira dr Isma'il da sauri suka dawo da sauran doctors d'in suka ce su haisam su fita hannunshi Ammah ta kama suka fita suka zauna a sits din kofan d'akin a daidai lokacin Ummi ta shigo sarki kam be samu zuwa ba sbd mutanenshi sun kai 20mins kan doctors d'in suka fito dr Ismail yace musu kai tsaye "an samu matsala tayi losing memory dinta but zamu kara aiki if we are lucky na biyun nan kam everything will be ohk in kuma bamu ci nasara ba hk zamu hkr har Allah ya dawo mata dashi......" be karasa ba suka ji fad'uwar abu a rud'e suka juya cikin tashin hankali sukayi kanshi da sauri dr ya ta'ba pulse dinshi yaji yana bugawa a hankali da karfi ya kwala kiran nurses maza a yanayin ciwon zuciya da yasan haisam dash akwai risk sossai a irin wannan fad'uwan wasu scholars din ma sukace In sunyi irinshi sau uku there is high rate of paralyzing a na ukun................


Doctors da suka shafi ciwon zuciya ya kira suka shige d'akin shima ya shiga don taimaka musu.................


#vote

#comment

#share 


'Yar mutan Adamawa💞💞💞


    💞💞Hamrah💞💞

            💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin


Wattpad: muhdfatimagurin 


  *'yar mutan Adamawa*


Page➡️3️⃣8️⃣

*************


Likitocin sun shafe akallah awanni biyu a kanshi da kyar suka samu suka shawo kan ciwon zuciyarshin sbd yadda be kula da tsarin ciwon sam, su Ammah suna tsaye daga waje se adu'a sukeyi zuwa lokacin ta kira mai martaba har ya iso Ummi tafi kowa d'aga hankali har da d'an kwallanta 'yan uwan Ammah ma duk sunzo sunzone da niyyar duba matar d'ansu se suka samu abunda ya faru duk suka zazzauna, babban likitan zuciyarne ya fito tare da Dr Isma'il suna sharce gumi duban su Ammah dr Ismail yayi ya furta "Alhamdulillah mun samu shawo kan komai"..................


Gabad'aya wurin ajiyan zuciya suka sauke wasu na mika godiya ga Allah doctor Aiman wato babban doctorn da ya karanci zallan ciwon zuciya da warakarta ya kalli su Ammah yace "taya akayi yana babban doctor yake wasa da lafiyarshi hk? Kun kuwa san stage da zuciyarshi yake? Be ta'ba sha mishi magani ba idan ba tashi yayi kaman ze kasheshi ba what a carelessness?"....................


Me martaba ne yace "yanzu muna sone a mishi special treatment akan wannan ciwon In Allah yayi ze rabu da  ita" ya karasa ignoring tambayoyin da dr Aiman ya mishi, shiru dr Aiman yayi na wani lokaci sanin da wadda ze yi magana gwara tun wuri ya kiyayi harshenshi se yanzu ma yake ganin wautarshi a maganganunshi na farko, cikin girmamawa yace "Ranka ya dade yanzu akwai wasu X-ray da zamuyi za kuma mu d'aurashi akan magunguna zuwa sati biyu se muyi aiki"...............


Mai martaba yace "Ohk Allah ya bada sa'a I want All the bills" dr Aiman yace "In shaa Allahu" Ammah tace "zamu iya shiga mu ganshi?" Dr Isma'il yace "yes sure" suka shige gabad'aya sun jima a kanshi kan suka fice da kyar Ummi ta bisu wai ita zata zauna dashi qudra, Iman, sagir da elhussein suka bari a asibitin, bayan azahar Haisam ya farka a hankali ya bud'e idonshi ya fara kallon inda yake yana tunanin me ya kawo shi nan da sauri ya mike ya zauna yana zare ruwan hannunshi sagir ne ya rike hannunshi yana cewa "calm down buddy me kakeyinnan?" A kasalance haisam yace "I wanna see her" elhussein yace cikin harshen turanci "haba bro baka ganin condition d'inka? Karka damu itama bata kuma farkawa ba kuma qudra da Iman na tare da ita"....................


Zamewa yayi ya koma yana dafe kirji shi karan kanshi ya san ya ma kanshi illa sossai da rashin kula da ciwonshi kuma ya san in ya tashi tambayarshi baze mishi da daadi ba yanzu ma ji yake kaman ana zuba mishi ruwan dalma a zuciyar runtse ido yayi dr Aiman ne ya shigo ya mishi sannu ya dudduba yanayin komai na wurin yaga komai normal base ya kara 'bata bakinshi wurin yiwa haisam bayanan abunda zeyi da wadda baze yiba ya san ya san komai juyawa yayi ze fita haisam yace....................


"Ina bukatar sallama" kan Dr Aiman yayi magana Dr Isma'il ya shigo sagir yace "a yadda kaken nan kakewa mutane wani maganan sallama dan Allah ka bari ka kara jin karfi" Da hausa yayi maganan yasa sauran duk basu ji ba haisam yace "discharge me" ya fad'a yana kallon Dr Aiman da yayi kasake yana ganin ikon Allah dama dr Isma'il ya fad'amishi se yayi ta hkr da haisam halinshi se shi ji yadda yake bashi umarni kaman wani d'anshi girgiza kai Dr Aiman yayi ze yi magana dr Ismail yace "Ohk za'ayi discharging dinka na san da ayi da kar ayi duk d'aya in muna bukatar ka zamu ganka tunda matar ka na nan" karamin murmushi haisam yayi juyawa dr Aiman yayi ya fice ba tare da yace komai ba...................


Anyi discharging dinshi bayan ruwan hannunshi ya kare d'akin da Hamrah take suka koma gabad'aya sagir yaja qudra suka koma wani wuri ta cikin hospital din kaman wurin shatawa suka zauna suna hirar su ta masoya, a d'akin kuma elhussein na rike da waya yana aikin dannawa yayin da haisam ke zaune ya kurawa hamrah ido Iman kuwa tana kwance akan darduman da ta idar da sallahn la'asar wayanta ne ya fara ringing ta mike da sauri ta nufi waje kassncewar an musu warning na karsuyi hayaniya ko motsi me karfi a kanta....................


Business partners dinta ne kasancewarta fashion designer sun kira ne akan design d'in kayan dake hannunta amaryar zata sa nan da two days har ta manta ma sbd yadda abubuwa sukayi ta faruwa sam hankalinta be kan hanya tafiya kawai takeyi tana basu hkr da fad'a musu rashi akayimusu shiyasa bata samu tayi ba but she assures them zatayi iya kokarinta bata hankara ba taji tayi karo da mutum duk abubuwan hannunsu sun zube wayanta har screen din ya tsage a tare suka duka suna cewa "sorry......." se kuma sukayi shiru a tare shi wayanta ya d'aga itakuma takkadun da ya zube daga hannunshi ta tattare suka mike a tare ido suka zubawa juna da sauri ta kawar da nata tana cewa "sorry" tare da mika mishi takardun kar'ba yayi har yanzu kallonta yake yace "I'm the one to apologize na fasa miki fuskan waya" kar'ba tayi tana cewa "mind not" ta juya ta nufi komawa d'akin nan taga yana bin bayanta tambayan kanta tayi wannan kuma lafiya, shima tunani yake me zataje yi Chan tana shiga ta koma kan darduman tayi kwanciyarta da sallama Dr aiman ya shigo ya mikawa su elhussein hannu suka gaisa ba tare da ya cewa haisam komai ba bayan musabaha ya mika mishi prescription na magungunan da ya d'aurashi akai kar'ba yayi ya ajiye a gefen gadon hamrah juyawa dr Aiman yayi ya fita yana satan kallon iman...................


Bayan one week


Komai na tafiya yadda suka saba har wa yau hamrah bata farka ba abunda yayi mugun damun haisam amma su Dr Ismail suna kwantar mishi da hnkli sossai zuwa yanzu sun saba da dr Aiman abunda yasa farko kaman bazasuyi shiri ba halinsu ya zo d'aya kowa naji da kanshi amma daga baya komai ya koma normal sitting room na asibitin suke samu su baje su biyar suyi ta hira dukda haisam be cika magana ba amma yana sakewa sossai a wurin zasu ci abinci idan ba aiki bane ya tada drs d'in a hk ma Haisam yayi wa wani aiki sau d'aya amma da kyar suka rokeshi yayin.................


Soyayya me karfi ya shiga tsakanin Aiman da Iman inda soyayyar sagir da qudra ta kara karfi sbd lokacin da suke samu tare suma asibitin suke yini wani lokacin har Ummi In taga suna abubuwansu na soyayya tayi ta zagin elhussein da ko buduruwa be da wai shi har yanzu be ga wacce tayi mishi ba seda Ammah tasa haisam a gaba tayi mishi kuka tukun ya yadda da shan magungunan shi har yanzu saura na week ya gama, Mom tana kiran haisam kullum tana jin yadda jikin hamrah yake be ta'ba boye mata komai ba ta fad'amishi dad ya d'aga hnkalinshi sossai yana tambayar Anya lafiya ko waya bata mishi ba tunda suka tafi, ta kan ce lafiya ai shi ke buya idan kaji shiru toh lafiya ne da hk take samu ta kashe maganan, but she prays and hope hamrah taji sauki nan kusa ko don kwanciyar hankalinsu....................,.


Kaman yau zaune suke a sitting room su biyar suna hira qudra, iman, jas da yas yadda suke kiran twins suna cikin d'akin da hamrah take kowa harka yake da waya qudra ta kara haske da wayewa turanci yanzu sossai ya fara zama mata kasancewar yadda kowa ke magana dashi a gidansu dukda larabawa ne amma jefi jefi zakaji sunyi larabcin yawanci da bayi ko don su qudran kar suji wani iri ne oho...............


Na'urorin jikin hamrah ne suka fara kara a hankali hankali duk d'aga kai sukayi suna kallon gadon jin karan ya kara karfi ne yasa jas tashi da gudu ta nufi sitting room d'in dr Ismail tana shiga ta furta "hamrah....." tana haki tana nuna musu waje da sauri suka mike suka nufi d'akin suna shiga suka samu har ta farka tana ta kallon d'akin suna had'a ido da haisam ta sakar mishi karamin murmushi lumshe ido yayi tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya murmushi na subuce mishi dr Ismail ya karasa yana furta mata sannu Kai ta gyad'a ya nuna mata haisam yace "kin san shi?".................


Lumshe ido tayi ta kuma bud'e, haisam ya nuna mata sagir yace "noory wannan fah?" Gyad'a kai tayi ya kuma nuna mata qudra seda tayi mata murmushi kan ta gyad'a kai zubewa haisam yayi a kasa yayi sujada yana mika godiyarshi ga Allah duk murmushi kwance akan fuskokinsu fita duk sukayi suka koma sitting room suka bar mata da mijin bayan dr Isma'il ya d'an duba ta ya cire mata duk wasu na'urori dake jikinta, chak haisam ya d'auke ta zuwa toilet ya taimaka mata tayi wanka da brush suka fito ya taimaka mata ta shirya dama akwai kayanta a d'akin, abinci ya bata da kanshi ya 'balla mata magungunanta ta sha ta koma ta kwanta hannunta ya rike yace "I missed you noory"................


Tace "hmmm, mom fah?" Yace "bata zo ba" ya bata labarin duk yadda sukayi ya kara da "let me call her" kira yayi suka gaisa tukun ya mika mata cikin tsantsan farin ciki Mom suka gaisa da hamrah tana ta furta Alhamdulillah bayan sun gama gaisawa ne take tambayarta dad fah tace yana office ta kirashi ta toh ta amsa mata suka kuma yin hira kad'an sukayi sallama.................


Kiran dad tayi suka gaisa yace "nayi fushi princess tun tafiyarki se after week tukun kike neman daddy? I'm here duk hnkali na a tashe" tace "am sorry dad banda lafiya ne" ta kwashe komai ya fad'amishi sossai ya nuna bacin ranshi na kin gayamishi da mom da haisam suka ki yi daga baya kuma ya hkr bayan hkrn da tayi ta bashi ta nuna mishi hakan da akayi shine daidai sbd yanayin shi ya tabbatar mata suna hanya zasu bi next available flight su zo ko don ganawa da 'yan uwan haisam ma, fatan alkahiri tayi musu tare sa sallama nan familyn haisam suka fara shigowa d'aya bayan d'aya duk wadda ya shigo In ya fita haisam ze mata bayanin yadda suke Ammah da Ummi suka shigo last suka mata sannu a kunyace ta amsa Tana dariyar yadda Ummi ke tsokanar haisam shima yana ramawa bata ta'ba ganinshi cikin farin ciki haka ba se yau and wai haisam ne ke wasan kaka da kakarshi Lallai.................


Su qudra ne suka shigo nan sabon hira ta 'barke kasancewar hamrah me saurin sakewa har ta sake dasu Iman kaman sun jima da sanin juna twins sunbi Ammah, sun jima suna hira kan sukayi shirin tafiya duk suka tafi suka bar haisam kad'ai se dogaraye suma zasu taho daga baya zuwa yamma in sunga yanayin jikintan ba matsalan komai, tunda aka barsu su kad'ai ta kwanta ta lumshe ido kaman me bacci shima kyaleta yayi yana tunanin gajiya tayi, waya ma ya fara da yaqoob yana jin lafiyar dukiyanshi sun jima sossai suna waya bayan sun gama ya kalleta tana kwance yadda take lura yayi da kaman ba bacci take yi ba yasa yace "noory?" Shiru tayi seda ya kara kira tukun ta bud'e idonta a hnkli ta zuba mishi.........................


Da mamaki yace "dama ba bacci kikeyi ba?" Kai ta daga mishi ya kara cewa "lafiya dai?" Ta lumshe mishi ido a hankali tace "na gaji da asibitin ai na warke" yace "Ohk lemme check dr Ismail yazo yayi discharging dinki in da wani matsala ma se mu dawo balle bama fata" Kai ta gyad'a mishi ya duka yayi pecking goshinta ya juya ya fice yana fita ta ja tsaki tana goge goshinta ranta a had'e rubuce rubuce dr Isma'il yayi ya tabbatar musu da samun lafiyanta In taji ko ciwon kai tayi suyi saurin zuwa asibiti godiya sossai yayiwa dr yace "se munzo aikina na san dole za'a tusani gaba kaman yaro😏" dariya dr Ismail yayi yana cewa "toh yaro na san dole ma dr Aiman ya sa muzo masarautar sbd sarauniyar tashi" murmushi kawai haisam yayi dama an riga an tafi da komai nasu so keyn motan elhussein dake hannunshi ya d'auka yana niyar riketa ta ja baya tace "zan iya fa" be damu ba ya shiga gaba suka fice dogarai suka bi bayansu motarsu daban na dogaran daban suka fice se kingdom.......................
#vote

#share 

#comment

'Yar mutan Adamawa
💞💞💞


                    💞💞Hamrah💞💞

                                                     💞💞Writer: fateemah Muhammad Gurin


Wattpad: muhdfatimagurin         *'yar mutan Adamawa*


*Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! I dedicated this page to "Mu Karu da Juna" group thanks for your prayers na ji sauki sossai and in shaa Allahu hamrah yazo karshe two pages to go........ Page➡️3️⃣9️⃣

*************


Yau kwana uku kenan da aka sallamota daga asibiti sossai ta saba da duk 'yan uwansu haisam ta bangaren mahaifiyarshi zasu fita dasu Iman su zaga tana nuna musu gari, shopping ne gidan kawayenta ne, wurin aikinta ne da dai sauransu duk kuma a fitan da sukeyin nan bata ta'ba tambayar haisam ba hasali ma se sun fitan yake sani wani kam sede yaga shigowarsu sossai abun ke damun haisam tunda hamrah tayi sauki ko hannunta taki yarda ya rike se ya yini be ganta ba iyakacinta kwana a bangarensu kwanan ma d'aki daban daban tun yana tambayarta matsalanta har yazo ya fita harkanta shima gudun ruwan ta yake son gani tunda ya san shi be mata wani laifi ba but weird halintan hurts him a lot................


Kwance yake kan doguwar cushion dake a parlorn part d'insu ya dulmiya cikin duniyar tunani sagir ya tafi jiya da yamma sbd nemanshi da akeyi a office, kaman daga sama yaji sallamanta a hnkali ya amsa kallon bakin kofar yayi se yaga itama shi take kallo abu tazo d'auka sam batayi zaton samunshi a part d'in ba da bata shigo ba, 'bata fuska tayi ba tare da ta ce mishi komai ba ta nufi d'akinta tana shiga taji an turo kofar da sauri ta juyo tana kallonshi shima ita yake kallo he missed old her so very much sam be san lefinshi gareta ba....................


Matsowa ya farayi jikinta ita kuma ta fara matsawa baya a haka a haka har suka isa jikin gini hannunshi yasa ya dafe ginin gefe da gefenta ya rankwafo sossai kanta da d'an fusata tace "wai me haka ne dan Allah?" A hankali yace "tambaya kike? Wai hamrah me ke damunki ne? Laifinme na miki da na chanchanci shariya daga gareki?" Da sauri ya matsa ganin ta rufe hanci tana kuma kokarin amai don sossai take kakari da mugun mamaki yake kallon hannunta da ta rufe hanci dashi he just can't believe this ba de shi ke wari ba, runtse ido yayi yana fatan kar tunaninshi ya zama gaskiya don baze iya ba wlh, da gudu tayi bayi tana kwarara amai jin amantan yayi yawa yasa ya nufi bayin don ya taimaka mata yana shiga ya riko ta jikinshi ganin yadda take layi da sauri ta fisge jikinta tace "bana so haisam Dan Allah ka dena zuwa kusa dani" cikin sanyin murya yace "meyasa?" Shiru tayi seda ya kara matsota tukun tace da karfi "wari kakeyi sossai wlh" zaro idonshi yayi yana kallonta maganan ya dake shi, shi ke wari? Jikinshi ya shunshuna kamshin fitinannun turarukanshi ke tashi maida kallonshi yayi zuwa kanta se kawai ya juya ya fice da sauri kuka ta fashe dashi tana zamewa a kasan bayin ta had'a kai da gwiwa......................


Sossai tayi kuka tana sonshi ba wai bata sonshi ba amma ta rasa me yasa in yazo ganganta se take jin wari da tsananin tashin zuciya ga wani haushinshi da ta rasa dalilin da yasa take jin hakan a ranta kuka ta ringayi na kusan mintuna 40 tukun tayi wanka jiki a sanyeye ta fito ta shirya cikin wando da riga da ya sauka mata har gwiwa rigan yellow wandon kuma black color se ta samu veil black tayi wrapping kanta dashi yellow flat Vincci shoe ta saka tayi wanka da turarukanta ta d'auki wayanta ta fito a parlor ta sameshi yanzu ma yayi wanka sanye yake da maroon Armani shirt se dark blue Jean da ya haska shi sossai gashin kanshinnan a gyare se sheki yakeyi kallon kallo suka tsaya yi, ya bata tausayi sossai ta san yadda yake sonta hk itama tana sonshi amma ta kasa zama dashi suyi solving matsalansu yanzu ma ba yadda ta iya ne ta furta mishi d'auke kai tayi ta nufi kofa ji tayi yace "hamrah!!!" Muryanshi a matukar sanyaye.................


Dauriya kawai yakeyi ga jikinshi da yake ji yana damunshi matuka donma yana kan drugs dinshi kuma aikinshi nan da two days kuma har yanzu hamrah bata sani ba, ganin ta juyo tana kallonshi yasa shi kau da kanshi yace "we re going to Akilah hospital now za'a duba lafiyanki and akwai test da zanyi" Kai ta gyad'a mishi ya mike rike da keyn sabuwar Ferrari da King Abdallah II ya ba shi daa da kud'inshi ze saya Abban ya mishi fad'a kuma yasashi dole yaje company dinshi ya d'auka itace ta shige gaba shi kuma yabi bayanta tafiya sukeyi kaman waenda basu san juna ba sbd ratar da ke tsakaninsu har suka fita parking space ta waya ya fad'awa Ammah sun tafi Akilah hospital Adu'a tayi musu sukayi sallama duk gidan ba wadda ya lura da halin da suke ciki, suna isa jikin motar ta bud'e back seat daga hannun damanshi ta shiga ta takure jikin motar tana d'auke numfashi don duk motar kamshinshi yakeyi kuma shine bata so sbd sam bata son kamshinshi....................


Be ce mata kala ba ya shiga ya tayar suka fice daga masarautar har suka isa asibiti magana be had'a su ba bata ma jira ya gama  parking ba tayi saurin fita tana sauke numfashi da mugun mamaki yake kallonta rannan a matukar had'e asalin haisam da ta fara had'uwa dashi ya koma be kalli ko inda take ba ya shige gaba ta bi bayanshi tana tsirtar da nyau har kofan office d'in doctor Isma'il ya kaita se da yaga shiganta ya juya zuwa office din doctor Aiman..............


Yana shiga ya zube a kan kujera yana dafe kai a lokaci d'aya hawaye na cika idonshi da sauri doctor Aiman ya taso ya dawo kujeran da haisam din ke zaune kasancewarta doguwa, Hannu yasa ya dafa kafad'ar haisam kasancewar su abokai sossai yanzu don sbd halin hamrahnnan kullum wurinsu yake yini har gidansu Aiman yake zuwa yayi bacci a d'akinshi sun kuma saba da mamanshi, cikin sanyin murya Aiman yace "wai me ke damunka ne haisam? Ka san yanayin jikinka be kamata ka ringa sa damuwa a ranka ba"...............


Da turanci haisam yace "baza ka gane ba" hawayen idonshi suka gangaro zaro ido Aiman yayi yana cewa "subhanallah!!! Haisam ka fitar da damuwanka plz wtkl kaji sauki a zuciyarka" haisam yace "hmm baka san ni ba har yanzu Aiman baka san waye haisam mas'ood sa'ood ba na rike damuwar da ta fi wannan so wannan ba komai bane" cikin kausasa murya Aiman yace "komai ne duk da ban sanka ba amma na tabbatar lokacin da ka rike wancar damuwar zuciyarka tafi haka karfi yanzu baza ka iya rike kwatankwacin waccan ba tukuna ma wani irin damuwa ne?"...................


A hankali haisam ya kwashe labarinshi In brief ya ba Aiman har zuwa wannan damuwar da yake ciki yanzu, seda Aiman yayi hawaye yana mamakin irin wannan rayuwa me mutane suka d'auki rai akan dukiya? magana ma kasawa yayi da kyar ya samu ya fara kwantar mishi da hankali shiru sukayi chan kuma se Aiman yace "Anya ba ciki ne da matar ka ba?" Kallonshi haisam yayi da jajayen idanunshi yace "ciki ne ze sata tsanata? Har ni zata ce Ina mata wari?" Aiman yace "is possible sbd mun ta'ba fuskantan irin wannan case din amma yana jimawa baka ji anyi case irin haka ba" (Ban ta'ba yarda ciki na sawa mace tsananin tsana da kyamar miji ba seda ya faru a unguwarmu, sossai ya girgiza aurensu sbd kin yarda da mijin yayi daga karshe tafiyarshi yayi se bayan wata tara ya dawo a lokacin ta haihu suka ci gaba da rayuwa normal).................


ba tare da haisam ya yarda ba ya share maganan sukayi abunda ya kawoshi suna gamawa ya mishi sallama ya fice a office din Dr Isma'il ya sameta suka gaisa da dr Ismail din nan ya tabbatar mishi komai normal godiya ya mishi tare da sallama yana fad'amishi be mishi hira ba be jin daadi ne sam har waje dr Isma'il ya rakosu tana daga Chan baya tana zuwa ta bud'e inda tazo ta zauna abunta suka gama magana da dr Ismail ya shiga ya jaa ....................


A hanyan Akilah hospital akwai wani had'add'en park daga bakinshi akwai wani coffee shop mutane suna d'an harkokinsu duk da ba wasu masu yawa bane, suna isowa nan yaji hamrah tayi wani irin ihu da sauri ya taka birki tare da juyawa don ganin ko lafiya se ganin saukarta yayi ta nufi wasu matasa 'yan mata biyu da samari biyu suma suna ganinta suka sa ihu har hankalin Wasu jama'a ya koma kansu 'yan matan suka rungumeta suna tsalle 'yan mazan kuma suka rirrike hannunta, wani irin bugawa gaban haisam yayi yana kallon yadda samarin nan suka rike mata hannaye a take yaji ciwonshi dake kusa na shirin tashi tsananin yadda zuciyarshi ke bugawa..................


A matukar harzuke yaja motar da mugun gudu ya bar wurin dukda sanin yadda kasar waje basa d'ukan wannan gudun, da sauri hamrah ta juya tana kallon motar tashi zuciyanta na bugawa maida idonta tayi kan hannunta dasu Aslam suka rike se kuma ta runtse ido tana adu'ar Allah ya kaishi gida lafiya maganar Aisha ne ya dawo da ita daga tunaninta tana tambayarta wayene da harshen turanci karamin murmushi tayi tace "mijina ne" da turancin ta mayar mata kasancewar basa jin hausa janta sukayi zuwa cikin park d'in a chan karshe inda aka shimfid'a musu darduma mai taushi da kayan abinci kala kala suka zauna..............


Friends d'inta ne ko ince squad mates dinta lokacin da suke school kowa ya sansu 6stars Aslam,Asad,farha, Aisha,Simra se ita suna cikin best students anaji dasu a ilimi da kuma kud'i a department d'insu komai nasu tare sukeyi dukda 'yan kasashe ne daban daban ba wadda kasarsu ya zama d'aya suna da groups dayawa a yanar gizo na hiransu, kallonsu tayi tace "wai me ya had'aku anan ne?" Aslam yace "we just catching up an jima ba'a had'u ba we called you layinki na nja baya shiga haka simra ma".............


Cikin murmushi tace "I was sick shiyasa ko online ban hau ba balle na ga hirarrakinku kwana uku kenan da aka sallamo ni na hau whatsapp kuma chats sunmin yawa ban samu bud'e namu ba" Aisha tace "ba wani abu" suka kuma tambayarta simra nan ta fad'amusu yadda itama tai ta nemanta bata sameta ba, sun jajanta rasuwar mahaifinta inda hamrah ta tambayesu daga nan wani kasa sukayi suka amsa mata da se gida sbd kwanansu 10 kenan da barin gida sunje kasashe a kalla 4, Ai kuwa hamrah ta ringa mitar sunyi yawo banda ita suna tayi mata dariya duk da turanci suka sha hirar sbd babban cin yarurruka duk turancin sukeji..............


Basu rabu dasu Aslam ba se karfe goman dare nan ma guduwa tayi ta barsu sun sha yawo kam sunyi ciye ciye kaman me, seda ta nufi gida tukun zuciyarta ya fara bugawa fargaba fal ranta tuna yadda haisam ya fice dazu gashi tayi dare sossai tana matar aure tana ta tunane tunane har me taxi ya iso kofan masarauta ganin itace yasa suka barshi ya shiga da ita sanin nisan dake tsakanin gate da parts din gidan har ciki sossai ya ajiyeta ta sallame shi tare da nufar part dinsu............


A hankali ta tura kofan parlorn ta shiga duhu ne dulum a parlorn kasancewar duk wani abu da ze iya bada haske a parlorn a kashe suke hasken wayanta ta haska tare da kunna bulbs din parlorn kwance ta ganshi kan doguwar kujera idonshi lumshe kaman me bacci ganin haka yasa ta nufi d'akinta se ji tayi an kira sunanta cikin kakkausar murya da sauri ta juya ta ganshi zaune idanunshi sun rine tsabar 'bacin rai a raunane cikin yanayin 'bacin rai yace "hamrah wanene ni gareki?" Kallonshi tayi a d'an tsorace tace "miji" yace "ashe kinsan ni mijinki ne amma kika kasa d'auka na da daraja hamrah na gaji bazan iya irin wannan wulakancin ba, zuciyata bazata iya d'auka ba for goodness sake da aurena a kanki amma wasu mazan da basu san daraja da kimarki ba suke rike miki hannu da saninki ba tare da kin hanasu ba...........


Kin ban mamaki in zama da nine kika gajidashi ki fad'amin zan fahimce ki but plz banda sabawa Allah ta hanyar wulakancin da kika fara min, Wai ni haisam mas'ood sa'ood, ni d'innan zaki bud'e baki kice Ina miki wari ni? Dumeni a kwana hud'u kacal hamrah ji yadda na zama ha......" maganarshi ne ya katse sbd numfashinshi dake seizing kallonshi tayi hawaye na gangarowa a idonta ganin da gaske numfashi ya fara nema yasa tayi kanshi da gudu rirrikeshi tayi a take ya fara wani irin tari me karfi se ga jini ya fara gangara ta hancinshi kuka sossai hamrah keyi tana kiran sunanshi "haisam haisam no plz Wlh inasonka iansonka sossai In ka mutu nima binka zanyi karka mutu ka barni Dan Allah, bazan sake ba bazan kara maka duk wani abunda baka so ba da karfi tace help!!!! Somebody help me!!! Haisam haisam" jijjigashi take iya karfinta inaa shi kuwa har jikinshi ya sake dogaran da suke gadin kofan part dinsu ne suka shigo da gudu ganin halin da yake ciki yasa su d'aukarshi da azama zuwa mota d'aya daga cikinsu ne ya je part din Ummi ya sanar dasu ksancewar Ammah na Chan sarki baya gari da gudu suma suka fito a lokacin har an saka haisam a mota hamrah dake kuka kaman ranta ze fita itama ta shiga tana dakawa drivern tsawar Akila hospital kuma yayi sauri in bazeyi ba ya bata keyn a d'ari ya fita daga gidan motar su Ammah biyu ta bi bayansu...........


Suna isa aka kar'beshi da gudu dayake tun kan su iso Elhussein ya kira dr Aiman ya sanar da shi theatre direct suka shige dashi suna shiga suka rufe kofar jinginuwa hamrah tayi da kofan tana sakin wani kuka me ratsa zuciya tabbas In haisam ya mutu baza ta ta'ba yafewa kanta ba dafa ta da taji anyi ne yasata juyowa ganin Ummi da sauransu yasa ta fad'awa jikin ummin ta kuma kara karfin kukanta numfashinta ya fara hawa da sauka alamun asthmanta kara ta saki tana dafe mararta Ammah ta kara riketa tana cewa "hamrah calm down plz me ya Faru ne? Mu da yace mana tunda kukaje aibiti baku dawo ba kuna zaga gari se kuma gashi daga cikin gida aka fito dashi" girgixa kai hamrah tayi tama kasa magana tsabar azabar da takeji a maranta ga asthma d'inta da ya tashi ga tambayoyin su Ammah don kowa tambaya yake jefa mata anan ta gane kenan tunda ya dawo ko abinci be ci ba yana kwance anan inda ta sameshi har shigowanta...............


Jin wani abu na gangarawa a kafanta yasata kallon wurin da sauri se ganin jini tayi yana zuba dayawa kara ta saki tare da sulalewa ta zube a wurin da gudu nurses sukayi kanta aka d'auketa se wani d'akin inda wasu doctors suka rufu akanta..............
#vote

#share

#comment'Yar mutan Adamawa💞💞💞


   💞💞Hamrah💞💞


            💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin


Wattpad: muhdfatimagurin 


 'Yar mutan AdamawaPage➡️4️⃣0️⃣

********


Seda su dr Aiman suka shafe good four hours kan suka fito suna sharce gumi a rud'e Ammah tayi kansu tana tambayar ya aikin dr Ismail ne ya amsa mata da "Alhamdulillah it was successful" duk ajiyan zuciya suka sauke suna mika godiyarsu ga Allah, dr Aiman yayi karfin halin tambayar "Ina hamrah?" Nan Ummi ta fad'a mishi abunda ya faru sun jajanta abun sossai inda suka nemi ganin doctorn da ya duba ta wata nurse ce taje ta kirashi yana zuwa ya mikawa su dr Aiman hannu yana musu murnan fitowa aiki lafiya kuma cikin nasara nan doctor Isma'il ya tambayeshi condition din hamrah, shiru yayi na 'yan mintuna tukun yace "am sorry to say tayi miscarriage na cikin wata d'aya da sati biyu" "innalillahi wainna ilaihi rajiun" suka furta a tare cikin jimami su qudra harda hawaye elhussein ne yayi karfin halin tambayar jikintan, doctorn yace "she's stable now, asthma dinma ya sauka se rashin karfin jiki da take fama dashi shima ruwan jikinta na karewa za ta samu karfin jikin in shaa Allah" godiya sossai suka mishi ya juya ya fice................


Nan suka ci gaba da jajanta abun inda su doctor Aiman suka tabbatar musu da tashin haisam se nan da 24 hours duk d'akin da hamrah take suka yada zango kasancewar hana shiga d'akin da haisam yake da sukayi su dr Anwar suka wuce office d'insu don parking zuwa gida, Ummi da kanta ta kira amintacciyar baiwarta ta bata umarnin yiwa hamrah girki, cikin awa d'aya aka kawo abincin pepper soup ne na kayan ciki da yaji had'i se wani abincinsu na larabawa da Ummi taga hamrahn na so se ruwan zafi da kayan tea, nan suka fara shawaran wadda ze kwana daga karshe aka yanke Ammah ce zata kwana don Ummi tace bata yarda da yaran nan ba rashin hankali zasuyi mata In ta farka cikin jimamin rashin d'anta, duk tattarawa sukayi zuwa gida, Ammah da kanta ta kirasu Mom ta sanar dasu suma ashe suna kano har sunyi booking flight zuwa jordan din da karfe 8 na safe a lokacin kasar zasu sauka, nan ta kira mijinta shima ya tabbatar mata da safe ze dawo, Chan wuraren asuba hamrah ta farka da kuka, da kyar Ammah ta lalla'bata tayi shiru inda ta tabbatar mata da 'barin cikin da tayi anan ne na ta san irin halin da haisam ya shiga lokacin ciwonta da d'aurashi akan magani da akayi aikinshi dama saura 2days ga abunda ta jawo tayi kuka sossai na rashin babynsu inda ta d'aurawa kanta laifin gabad'aya da bata tsawwalawa haisam da sabbin halinta ba da be kwanta ba har ta shiga tashin hankalin hakan da yayi sanadiyar d'an cikinta, da tun farko ta zauna dashi sunyi shwara da duk hakan bata faru ba, amma hausawa sunce da na sani keyace...............


Ta samu taci abinci ta watsa ruwan zafi a jikinta tare da alwala tazo ta hau sallaya ta fara nafilfili tare da nemawa haisam sauki a wurin mai duka, Ammah ma jonata tayi har seda aka kira assalatu kan sukayi raka'atanil fajir suka gabatar da sallar asuba, gado hamrah ta koma inda ta roki Ammah akan ta koma gida ta huta itama bacci zatayi ta tabbatar kan ta farka su Iman sun zo, da kyar Ammah ta yarda ta'bi guard d'aya ya maidata gida dayake sun bar mota d'aya suka tafi da sauran...........


Ta jima kan bacci yayi awon gaba da ita se around 9 ta tashi, da ciwon ciki da sauri su mom dake d'akin suka aiki Iman kiran likita daya dubata jiya, in less than five minutes ya shigo ya dubata ya tabbatar musu da se an yi mata wankin ciki, daa ya d'auka base anyi ba ficewa duk sukayi Mom harda kukanta wai 'yarta na shan jarabawa a cikin wata d'aya tayi ciwuwwuka kala kala, hajja nana ce tayi ta bata baki inda ta mata tuni akan ciwo abu ne me kankare zunubi In ma bawa ya jima beyi ciwo ba toh ya kamata ya binciki kanshi, dad ma lalla'bata yayi suna cikin haka Ammah, Abbah, Ummi da qudra suka shigo dama Iman da elhussein kam sun tsufa a asibitin su Mom ma daga airport seda suka sauka a hotel da suka kama sukayi refreshing kan suka wuto asibitin, Yas fa Jas suna school............


Mintuna 30 doctor Amir yayi ya fito da nurses din da suka tayashi aiki inda ya tabbatar musu da komai normal, duk hamdala sukayi tare da shigewa room din, katon darduma dasu suka shigo dashi suka shimfid'a kowa ya zauna suka gaggaisa tare da yiwa su Mom sannu da zuwa suka ci gaba da hira jefi jefi, har wuraren 11 tukun hamrah ta farka wanka tayi taci abinci se shagwa'ba take zubawa mom da dad da hajja nana suna lalla'bata yayin da qudra da iman suke tsokananta Ummi na musu jaraba, kusan one hour da tashinta dr Aiman da dr Ismail suka shigo a kunyace dr Aiman ya gaisa dasu Abba inda dr Ismail yayi musu albishir din tashin haisam komai lafiya sauki kuma ze zo se a hankali kuma gaskiya yayi a kalla 2weeks kan su bashi sallama godiya sossai sukayi musu su Iman nata murna hamrah kam harda kukanta duk da tana mugun son ganinshi amma tana matukar tsoron abinda ze biyo baya, inta ta tuna yadda sukayi dashi kwanakin nan mussaman ma jiya haka tana ji tana gani suka fice gabad'aya suka barta daga ita se hajja nana..............


Sun samu idonshi biyu sannu suka ringa mishi yana amsawa da kai, duddubawa yake yi ta inda zata fito duk da sun 'bata amma yana son ganinta, yana kuma son ganin damuwar ciwonshi a idanunta ko ze fitar dashi daga kokonton da yake ciki.............


Ammah ce ta taimaka mishi ita da elhussein ya samu ya jingina da jikin pillow, qudra ta kawo silver da ruwa yayi brush Iman ta sa mishi abinci me ruwa ruwa kad'an yaci yace ya koshi inda yake tambayar su dad yaushe a gari suka sanar dashi yau da safennan, san da zuwa ya musu tare da yiwa Abba San da dawowa, ya Amsa da fara'a yana tambayar shi jiki, da Alhamdulillah ya amsa sun d'an jima suna hira tukun Ammah tace Abba da elhussein suje gida sbd mutanen fadaa, itama imaan ta wuce office d'inta ta tabbatar tana da aikin yi, Ummi ma taje gida ta huta sbd duk gwiwowinta ciwo sukeyi da kyar suka yarda suka tafi, dad ya raka su ya dawo, inda ya sanar musu yana wurin hamrah Incase suna nemanshi yayi juyawarshi, nan zuciyar haisam ya buga me ya samu hamrah? Yana son tambaya amma bakinshi yayi nauyi har su dr Isma'il suka shigo suka taimaka mishi ya kwanta suka kara dubashi suna mishi d'an hira anan ne ya dubi dr Aiman yace "Hamrah ta dena sona da gske ko?" A hankali yayi maganan ganin Mom na d'akin, dr Aiman yace "waya gayamaka? Ka kuwa san irin tashin hankalin da ta shiga?" Haisam yace "toh Ina take da ta damu dani, da tana nan zaune kusa dani amma tunda na farka ko mai kama da ita ban gani ba" Dr Aiman yace "In har na fad'a maka zaka d'aga hankalinka last abunda muke kuma so kenan" haisam yace "In baku gayamin ba wlh se hankali na yafi tashi gwara ku gayamin did something bad happened to her?" Kallon juna doctors din sukayi dr Aiman ya juya ya fice, dr ismail ne yayi karfin halin sanar dashi duk abunda ya faru da sauri shima ya juya ya fita ganin hawaye na gangarowa a idanun haisam...............


Ammah ce ta taso ta zauna ganganshi tare da fara bashi baki Mom da qudra ma ficewa sukayi hawaye sossai yayi Ammah na mishi nasihar Allahn da ya basu yana sane dasu, ya kar'bi kayanshine a lokacin da ya so kuma ze iya basu wani sadda yaso da kyar ya yi shiru ya dena hawayen ya rasa wa ze d'aurawa laifin shi a matsayinshi na doctor ne ko kuwa ita da cikin ke jikinta Amma ta kasa ganewa daa sun zauna sunyi settling komai da hakan be faru ba but duk da haka se ya hukuntata duk da ta matukar bashi tausayi...............


   Two weeks latter


An jima da sallaman hamrah yayinda suke saka ran sallaman haisam yau ko gobe yayi sauki sossai Alhamdulillah, su mom ma sun koma tun last week tunda aka sallameta ko A be shiga tsakaninsu da haisam ba tana cikin tsananin damuwa duk da irin kulawar da take samu daga familyn da farko tana zama ta yini a asibitin duk da ko ta mishi magana ba amsawa yakeyi ba daga baya kuma se ta dena zuwa, haka kawai se ta kwanta a d'akinshi ta ci kuka, tana ganin laifinta a gabad'aya abunda ya faru yau ma kaman kullum ta samu tabaa Ammah excuses din da ta saba bayarwa take dogging zuwa asibiti, duk da ta lura Ammah da ummi sun gane sun samu matsala da juna amma se suka barsu suyi sorting issues d'insu out da kansu, hakan ya mata daadi sossai ta kuma gode Allah da ya bata surukai marasa jefa kai a abunda be shafe su ba............


Ta san yau za'a sallame shi hakan yasa ta mike da kanta ta gyara part d'inta tsab tare da saka turarukan wuta irin nasu na larabawa masu tsananin kamshi tana gamawa ta fad'a bayi tare da wanke jikinta tsab da sabulanta masu kamshi tana fitowa ta shafa mai tare da shiryawa cikin wata arniyar bomshot dark blue da red crop top me tsiririn hannu bayan igiyoyi ne da akayi crossing har tsakiyar bayanta da kad'an ya wuce bra d'inta ta gaba ma ya d'an sauka kad'an duk da bai kai cibiyar taba daga sama ana iya hangan red sexy bra da ta sanya se ta d'auko fari kal din riga kaman jacket da kad'an ya wuce cinyarta shara shara ne ana kallon duk abinda ke jikinta ta sanya, yana da igiya se ta d'aurashi daga kasan cibiyarta kad'an gefe da gefenshi tsagu ne har kan kwankwasonta sun fito d'as dasu, fashion d'an kunne ta makala a kunnenta red babba, se babban ribbon da ta d'aure kanta shima red, dashike jiya aka zo har gida aka wanke mata kai wato home service se kan ya kwanta yayi kyau se sheki yake............


Red luffers me taushi ta zura a kanfanta tare da fara feshe kanta da turarukanta seda ta shafa haramain madina a fatanta bayan kunne kasan boobs d'inta da wuyanta zuwa bayan gwiwanta tukun ta d'auko oud wood intense da golden oud body spray ta feshe fatan ta dashi tukun ta pesa oud 24 hours perform a kan kayanta kamshi ya bule ko ta Ina na jikinta, powder ta shafa tare da zizara kwalli a idanunta bata ta'ba giranta ba se lips d'inta da ta shafawa hot sexy red lipstick tayi kyau sossai kaman me..........


A parlor ta kwanta kan doguwar kujera bata damu da d'aura girki ba sbd an kawo musu daga part d'in Ammah ta kuma duba komai normal, AirPods ta makala a kunnenta tayi connecting da wayanta tare da playing wani hausa song na Umar M Sharrif shine first hausa song da ta fara so a rayuwanta, a wayan hajja nana taji shine ta tura sunan wakan "Fadli falala" lumshe ido tayi tana jin yadda beat din wakan ke tafiya tana bi a hankali, ta d'an jima kwance a wurin har qudra ta turo mata da text message akan sun dawo daga asibiti gabad'aya, bata amsa ba sema ignoring da tayi kaman bata gani ba, Chan kaman after five minutes taji an turo kofan parlorn kamshin turarenshi ne ya fara sanar da ita wadda yake wurin dukda daga gadon asibiti yake hakan be hana kamshinshi sallama kan ya iso ba, bata tanka ba kasancewar sallaman da yayi yayita ne akasan makoshinshi seda ya iso tsakiyar parlorn cikin tafiyanshin nan na isa da kasaita tukun ta mike tsaye cikin sanyin murya ta furta "haisam" chak ya tsaya ba tare da ya juya ba, seda ta kara kiran sunan nashi tukun ya juyo tare da kafe ta da lumsassun idanunshin nan, daburcewa tasoyi ya koma mata kaman yau ta fara had'uwa dashi hakan kuwa sam be mata daadi ba, cikin rawan murya ta fara magana "kayi hakuri ka yafemin plz tabbas ni mai tsananin laifice a gareka, I don't even know what goes over me da har na aikata abubuwan da nayi maka sam banyi zaton da d'a a mahaifata ba, har nayi saken da na rasashi... our chilld.... my ba...by"........


Kuka ne ya sarketa ta kasa karasa maganan hannunta dafe da flat tummy d'inta ta sulale ta zauna a kasa ta fara rerawa bata kula da zuwanshi ba se full tender hands dinshi da taji a kafad'unta tare da d'aga ta ya rungume a kirjinshi sossai yayi cuddling d'inta yana shafa bayanta kuka tayi sossai a jikinshi duk tausayinta ya cika shi, shima yasan yayi laifi uwa ce fa ta rasa d'anta ya san ciwon da takeji ya ninka wadda shi yaji, ashe duk abubuwan da tayi ta mishi sam ba laifinta bane? Tabbas bashi da right din fushi da ita, Allah ya maida musu mai albarka..........


D'agota yayi daga kirjinshi tare da d'aura hannayenshi kan kunnuwanshi ya d'an duko kad'an yana kare mata kallo kasa kasa a tausashe yace "Seeking for forgiveness of the worlds best wife....... yours sincerely the worlds dumbest husbanddddd....." ya karasa da jan maganan, bata san sadda murmushi ya subuce mata ba harda giirgiza kai don maganan shi ya mugun bata dariya shagwa'be fuska yayi yace "what's funny wifey!!! By the way you look sooo breathtaking sweetheart" a kunyace ta boye fuskanta a kirjinshi ya kara rungumeta yana shafa bayanta yace "mistakes do happen in life and you learn from the same, whatever happened was because of me, I was fool for not realizing it, I really repent from heart, let's make a brand new start, Am so sorry love" kan ta amsa mishi ya had'e bakinsu ya fara nuna mata yadda yayi missing dinta na kusan wata d'aya da baya baya suka shige d'aki tare da rufo kofa a fuskata😏

#vote

#share 

#comment

'Yar mutan Adamawa


💞💞💞

                    💞💞Hamrah💞💞

                                                   💞💞


Writer: fateemah Muhammad Gurin 


Wattpad: muhdfatimagurin             'Yar mutan Adamawa


Page➡️4️⃣1️⃣

************


Bayan sati d'aya


Soyayya sossai suke sha ko waje basa fita daga sun je sun gaida mutanen gidan zasu dawo su mule a part d'insu se washegari za'a sake ganin idonsu Ummi tayi ta musu jaraba kenan wai soyayyar banza soyayyar wofi har su za'a nunawa soyayya su da tun soyayya na soyayya suke yinta, su qudra de iyakarsu dariya don basu ga fuskan wasa haka da haisam ba gwara elhussein ma na iya tsokanarshi, a tsakanin ne sagir ya kira haisam suka zartar da zuwan iyayenshi neman auren qudra yayi magana da Abbah inda yace ya sanar dashi zasu iya zuwa nan da two days ma is okey, cikin farin ciki sagir ya amsa, a yau kuma suke hanya, dr Aiman ma ta haisam yabi inda Abbah yace suma suzo a had'u ayi komai lokaci d'aya murna sossai shima yayi...................


Masarautar ko ta Ina hada hada akeyi kaman bikin sallah ko wani gagarumin aure alhali tambaya ce kawai kasancewar yanzu ne Abba ze aurar da 'ya tun hawanshi mulki se abun ya zama kaman wani babban bidiri ne ze wakana anyi abinci kala kala, an gyare duk wani lungu da sako dake cikin masarautar duk da bakin nigeria ba kwana zasuyi ba, jirginsu ya sauka karfe 8 na safe a Babban filin tashi da saukar jirgi na kasar jordan babban birnin Amman tundaga nan suka san gidan girma zasu nemi aure yadda motoci da dogarai suka cika airport din cikin mintuna suka gama abunda zasuyi suka shige motocin se kingdom a part mai kyau aka sauke su aka cika musu gaba da abinci seda suka huta suka ci suka sha tukun 'yan uwan dr Aiman suka iso suma an baza musu kayan alfarma sunci sunsha kan sarki da tawagarsh suka karaso suka gaiggaisa tukun suka gabatar daabinda ya tarasu kasancewar 'yan nigeria zasu juya 4 na yamma................


An gabatar da komai cikin karamci inda aka bada har sadaki ko wanne 2000k banda sauran kud'aden al'ada inda aka tsayar da bukin nan da 3months, da yamma 'yan Adamawa suka wuce da sha tara na arziki cike kuma da farin cikin karamci irin na Hashemite kingdom of jordan, a Daren Abbah ya kira haisam Ammah na hakimce a gefenshi a kasa ya zube ya mika gaisuwa tare da ban gajiyar baki bayan duk gaishe gaishe Abbah yayi gyaran murya yace "haisam ya maganan 'yan uwan mahaifinka su ya kamata ku fara nema amma se kuka yo wata kasan kuka bar na waenda kuke wuri d'aya" haisam yace "Abbah ai kaine mahaifina 'yan uwana kuma duk suna nan anan" murmushi Abbah yayi cikin farin cikin d'aukar shi mahaifi da haisam yayi yace "bance ni ba mahaifinka bane amma Ina magana ne akan asalin mahaifinka Dr Umar faruq ya kamata 'yan uwanshi su san da bayyanarku" kasa da Kai haisam yayi yace "Abba ka gafarce ni amma Ina da ku kuma kun isheni rayuwa da sun damu dani da tunda Ammah ta bar gabansu da sun bita sun san halin da take ciki kuma su san me ta haifa amma basuyi haka ba, after all wahalan da mahaifiyata tasha a hannunsu da banzantar da rayuwata da sukayi suke zaton zan iya nemansu In na zama wani abun?"...............


Abbah yayi murmushinsu ta manya yace "ba wadda yazo amma kuma ai yan uwanka ne, hannunka baze ta'ba ru'bewa ka yanke ka yar ba ka neme su ba don halinsu ba ka neme su na tabbatar ko mahaifinka na da rai abunda ze ce kenan" haisam yace "Ammaa....." katseshi Ammah tayi ta hanyar kiran sunanshi shiru yayi na 'yan mintuna tukun yace "duk abunda kukace Abba" murmushi Abbah yyi yana furta "masha Allah tunda jirginka na nan gobe se mu wuce da yamma zamu bar su qudra gabad'ayansu anan se mu tafi da Ummi, Ammanhnku, elhussein, matarka se ni da kai" gyad'a kai haisam yayi ba don ya so ba daga fuskanshi ma zaka gane be ji daadin hakan ba, da haka ya karasa part dinsu inda hamrah ta mantar dashi damuwarshi da soyyayarta me wuyar mantawa....................


Adamawa Nigeria


Sun sauka lafiya a modibbo Adama international airport dake cikin jimeta inda motocin haisam guda hud'u suka zo tararsu manyan Jeep's ne masu rai da numfashi, guda biyu securities ne a ciki yayinda biyun ba kowa se drivers Ammah, Ummi da hamrah suka shiga d'aya yayinda haisam, Abbah da elhussein suka shiga d'aya motar securities d'in d'aya a gaba d'aya a bayansu, lelawaji suka nufa da kwatancen Ammah har kofar wani madaidaicin gida me kyau ba laifi suka fiffito bayan drivers sunyi parking yara se kallonsu sukeyi kasancewar Layin da suka shigan bana masu kud'i har chan bane se de baza a kirasu talakawa ba gashi sunga larabawa, cikin yaran Ammah ta kira tare da turashi ya fad'awa daada tayi baki da tsallenshi ya shige mintuna kad'an ya fito yace "tace ku karasa" har ciki ya rakasu Abbah ya mishi alheri a madaidaicin parlorn suka sami wata tsohuwar bafulatana kwance daga kasa akan katifa an mata shimfid'a daga gani bata da lafiya sossai wata buduruwa zaune gefenta tana dama mata nono a kwarya sannu da zuwa buduruwan tayi musu suka zazzauna Daada ta mike da kyar ta zauna tana gyara glass din idonta tace cikin harshen hausa "sede fa ban gane ku ba bayin Allah"................


Murmushi Ammah tayi tukun tace "Noor ce daada tsohuwar matar marigayi Hamma umar" hamdala da hailala matar ta fara hawaye na gangara a idonta a take tafara neman gafarar Ammah akan abubuwan da suka mata ta umarci yarinyar da kiran babanta da gwagwanninta guda uku tace maza su bar duk abinda suke su zo Ai kuwa cikin minti 10 kowa ya iso Ammah sam bata manta fuskokin su hajara ba sbd sun mata abunda baza ta ta'ba mantawa ba seda ta fad'a musu sunanta kan suka ganeta gafarar ta suka ta nema suka kuma sanar mata da farko basu bada kai a nemanta ba har seda suka cinye kud'in Umar tukun nadama ta shige su sbd ibtila'in da Allah yayi ta saukar musu a lokacin kuma basu da kud'in jirgin zuwa jordan nemanta, ta nunamusu haisam inda ta basu takaitaccen tarihin abunda ya faru dasu sossai suka tausayamusu suka nemi gafarar Haisam d'in ya yafe musu inda suka gabatar mishi da kansu bappanshi d'aya daya saura marwan se goggoninshi Hajara, Raihana da zaliha duk suna da family sossai yayi musu 'barin naira inda suka tattara suka wuce gidanshi na malamre don hutawa, be fad'awa kowa ba ya shirya wa Daada tafiya umura don a duba jikinta ya tabbatar rashin kwarrarrun likitoti ne da ta fi haka lafiya inda pilot dinshi ze koma dasu Ammah washegari a washegarin suka wuce haisam ya d'auki hamrah zuwa gidan daada inda akayi ta zuwa gaisawa dashi duk kuwa wadda yayi ido hud'u dashi se ya samu kyautar kud'i me tsoka anan sagir yazo ya sameshi suka yi mata yini cur washegari bayan sallahn isha suka kuma zuwa gidan daada inda ya fad'a mata gobe jirginsu zai tashi zuwa Saudi don ayi mata aiki sossai matar tayi ta murna inda 'ya'yanta sukayi ta godiya....................


Sunje Saudi an mata aiki cikin sa'a inda likitocin suka tabbatar musu se nan da kwanaki Akallah goma za'a sallameta hakan yasa su haisam bazama yawo a lokaci d'aya kuma suka bud'e sabon baabin soyyayya kaman zasu cinye junansu, tsaye take a gaban ka'aba tana adu'a cikin natsuwa a lokaci d'aya kuma tana zubar da hawaye haisam baya nan a hotel din da suka sauka ta baroshi, kaman daga sama taji an dafa kafad'arta, a hankali ta juya wa zata gani, Simraaaa. A hankali ta furta sunan a lokaci d'aya suka rungume juna hawaye na gangara a idanunsu cikin farin ciki nan suka bar harami suka samu wani coffee shop suka zauna tare da fara hiran yaushe gamo, har simra tayi aure da 'yarta d'aya hamrah sossai hamrah taji daadin takwaran da simra tayi mata inda suka wuce school d'insu hamrah karama don hamrah babba ta ganta kuma su d'auko ta, yarinya karama me tsananin wayo a play class take sun d'auke ta suka wuce gidan simra ta jima a chan tukun haisam ya kirata yana tambayanta inda take kwatance ta mishi da taimakon simra har ya iso mijinta yaje ya shigo dashi cikin karamci suka gaisa, inda simra ta cika mishi gaba da kayan ciye ciye suka kuma kulewa d'aki da bestyn ta seda hamrah ta bata labarin duk abinda ya faru bayan rabuwarsu tukun simra ta barta tasha iska se cikin dare sukayi musu sallama tare da exchanging numbers suka wuce a daren suka koma asibiti kasancewar kwanakinsu sun cika washegari da safe suka wuce har airport simra da mijinta suka rakosu kaman karsu rabu, a Abuja suka sauka inda haisam yasa aka gyarawa Daada part a cikin gidanshi ya zuba mata ma'aikata ta tare a chan, aiyukan da ya taru mishi ya maida hankali a kai shida yaqoob......................

***********


Bayan wata uku


Tsaye nake a gaban hashemite kingdom Ina kokonton Anya kuwa shine? Ko ba shine ba ganin yadda akayi renovating masarautar ya koma sabo gal, Ina cikin dube dube na don tabbatar wa shine ko yaya se naga wasu manyan motoci sun doshi gate din tare da danna horn da gudu na bisu don tabbatarwa ai kuwa shi dinne mutane dinke da gidan ko ta Ina hidima akeyi su hamrah kirjin buki satinsu d'aya da zuwa dukda yadda take jin jiki kwana biyun kullum hk zata yini da jiri, ciwon kai se ciwon jiki amma taki sam haisam ya dubata ko suje asibiti, kaman kullum tsaye take dafe da kanta idonta ya rine sede tayi fresh sossai tayi kyau cikin doguwar rigar lace ash da white dukda bubu ne d'inkin hakan be hana uban hips da boobs da ta tara ba fitowa kanta yane da tsiririn bakin gyale, so take ta shiga cikin gida wurin amaren nan amma jiri ya tsayar da ita bata Ankara ba taji an rungume ta ta baya kamshin turarenshi da take matukar so ne ya sanar da ita wayene hakan yasa ta juya ta shige jikinshi gabad'aya ya kara rumgumeta...................


A kasalance tace "babban abokin angwaye, babban wan amare" murmushi yayi yace "babbar kawar amare kuma antynsu" murmushi tayi tana zamewa tace "zauji cikin gida nake son shiga In na biye maka baza na tafi ba" pecking goshinta yayi yana mayar da ita jikinshi yace "ba inda zaki je babynah na wahalar dake ki huta haka plz" kara d'agowa zatayi se taji ya d'auke ta gabad'aya ya nufi bedroom dinshi, a shagwa'be tace "ni ni ni ba wani baby" murmushi me sanyi yayi yace "au baki gane ba don wannan babyn me tsani Appah d'inshi ba?" Dariya suka yi a tare tuna wancan cikin, a kan gado ya kwantar da ita shima ya kwanta gefenta jikinshi ta hawo tana kara kankameshi tace "surprise dinner da ka had'awa su  sagir a yola na nan ko?" 'Bata fuska yayi yana cewa "Ina tunanin canceling ma ga fa yadda akayi events kusan kala 6 a nan be isa ba?"....................


Tace "a'a ayin kawai ka ga friends d'inku ko ince friends dinshi da family da basu samu daman zuwa ba zasu ji daadi sunyi attending wani abin suma" seda ya sauke mata light kiss a baki tukun yace "ur wishes is my command ur highness" murmushi tayi tace "gobe da yamma zamu wuce ko?" Yace "nop immediately after the nikkah tunda muna da abunyi kan amarya da ango su iso" Kai ta gyad'a ba tare da ya kalleta ba yaci gaba da mata hira be kula ba kawai se jin saukar numfashinta yayi a hankali dubawa yayi se yaga har tayi bacci murmushi kawai yayi yana kara cuddling d'inta.....................


Tun kan ta tashi zafin jikinta ya sanar dashi zazzabin dake jikinta Ai kuwa be gama tunani ba yaji ta mike da sauri tayi hanyar bayi amai ta fara ba ji ba gani dukda ba wani abincin kirki bane cikinta hakan yasa aman wahalar da ita sossai ga jiri dake dibarta cikin tausayawa ya sata jikinshi a tsanake ya wanke mata jiki tare da fitowa da ita ya shirya ta cikin simple gown jallabiya ya sa ya d'auki kayanshi zuwa mota guards da bayi tare da jama'ar gidan In sun gansu sede su kau da kai don ko a jikinshi shikam cikin kankanin lokaci suka isa Akilah hospital Dr mace ya samu ta dubata akayi mata test basu wani jima ba results ya fito tana d'auke da cikin wata uku da sati d'aya..................


Murna wurin haisam harda hawaye dukda ya jima da zargin hakan amma tabbatarwan yafi ko wani irin labari daadi a gareshi kyauta kam doctorn ta sha shi drip ta sawa hamrah sbd jiri da kuma aman da tayi, cikin mintuna d'akin da hamrah take ya cika harda amare seda haisam yayi da na sanin sanarwa Ummi da yayi da wannan gayyar da ta taramishi, anan suka yini da dare aka bata sallama taji sauki sossai kowa se tarairayarta yake........................


#vote

#share 

#comment'Yar mutan Adamawa💞💞💞                   💞💞Hamrah💞💞

                                                   💞💞


Writer: fateemah Muhammad gurin


Wattpad: muhdfatimagurin             'Yar mutan AdamawaPage➡️4️⃣2️⃣ to 🔚🔚🔚🔚

**************


Sanye yake cikin dakakkiyar farar shadda gezna da yaji kud'i se sheki yakeyi, 'yar ciki da babbar riga anyiwa gaban rigan zubi me d'aukar hankali dark blue zare mixed with white, 

kallon trouble wife din shi yakeyi ta d'auko wannan hula ta mayar ta d'auko waccan har daga karshe ta za'bo wata dark blue zanna shima akwai designs da farin zare jikinshi ta saka mishi ya kuwa zauna das yadda take so ya fitar da shi sossai, a cikin watches ta za'bo wata na bakar fata da ta tabbatar da tsadarshi sbd kyaun fatan bayan ta d'aura mishi ta koma wajen shoes black polished covered one ta d'auko tazo ta sa mishi akan bakin socks dake kafan ta d'auko collections na performs dinshi ta fara bulbule shi har seda ya fisge kwalaben shagwa'be fuska tayi kan tayi magana ya jawota jikinshi yace "sorry wifey kamshin ya isa haka na tabbatar wadda be san angwaye ba In ya ganni ze ce Ina cikinsu"............


Baki ta turo zatayi mishi kuka ya lura cikin nan d'an rigima ne abu kad'an se ta fara kuka bilhakki hakan yasashi saurin had'e bakinsu ya bata kiss of her life, seda ya tabbatar ya mantar da ita rigiman da ta fara tukun ya ra'bata ya fice yana d'aukan wayanshi daga kan dressing mirror har ya isa kofa tukun yace "baby ki tabbatar kin shirya fa nan da 40mins jirginmu ze tashi plz karki kwanta balle bacci yayi gaba dake" Kai ta gyad'a mishi tana blowing mishi kiss..............   


Bayan an d'aura auren sagir Ahmad da amaryarshi Qudra Abdallah se na Dr Aiman Da amaryarshi Iman Abdallah, ana gama d'aurin auren ya sulale zuwa cikin gida inda ya samu Hamrah ta shirya cikin farin dakakken lace itama, gown ne ya mata kyau sossai komai nata fari kaman ka d'auke ta tsabar kyau don light make up tayi, tun daga wurin d'aurin auren ya cire babban rigan a parlor ya yasar tare da karasawa ciki seda ya lumshe ido yana mika godiyarshi ga Allah ganin irin kyaun da hamrah tayi sossai cikin ya sata yin wani irin kyau na fitar hankali ai kuwa ganin ze shiririce yasa ta d'aukan bag d'inta ta nufo shi tana cewa "muje ba time yayi" murmushi me sanyi ya sakar mata tare da cewa "kina da kyau" bata tankashi ba har suka fice sukayi wa 'yan gidan sallama Ammah na mata bayanin abunda zata kiyaye basu wani jima ba jirginsu ya d'aga zuwa nigeria..................


Sun sauka lafiya inda suka fara shirye shiryen dinnern da zasuyi a green land sossai suka tsara abubuwan a gajiye suka koma malamre don shiryawa a lokacin tuni su sagir sun iso a family house na su sagir suka sauka har da 'yan uwansu haisam din don sagir yaki su sauka gidan haisam sbd irin karamcin da akayiwa 'yan uwanshi a Hashemite kingdom, suma shiryawa sukeyi ana idar da isha za'a wuce daga Chan ango ze wuce da amaryarshi gidansu dake Dogirei nan cikin jimeta................


Tunda suka shigo gidan tayi connecting woofers na gidan da wayanta tare da playing wakarta na fadli falala duk da sanin ba son wakar haisam keyi ba shi na turanci ma yaushe yaji balle wani hausa, Ai kuwa be so dinba dukda bai mata magana ba a haka sukayi wanka suka shirya suka fito zama yayi a parlorn yana jiran ta gama make up ta fito a lokaci d'aya kuma yana sauraren wakar duk da ba yau ya fara ji a wurin gimbiyar tashi ba, wankan half jumpha yayi blue black kashmiya ce da taji kud'i ta gogu tsab yayi kyau sossai da black wristwatch different company da wadda ya sa d'azu haka half cover shoe dinshi ma baki ne se sheki yakeyi zallar dark blue zannanshi kafe a kanshi so masha Allah kamshi kam kaman gidan 'yan borno............


Waya yakeyi da yaqoob da shima tawagar angwaye ya biyo daga jordan din akan suyi maza su karasa event center din be so su kai 12 a wurin, da toh yaqoob ya amsa shi dama sune masu d'auko amarya da angonta yana sauke wayan idonshi ya sauka akan tauraruwarshi, haskenshi a hankali yace 'fa tabarakallahu ahsanul khalki' kyau ma karamin word ne da za'a danganta ta dashi sanye take da sea green lace rigan me d'an fad'i ba wani ado a jikinshi me dogon hannu se zani da ta d'auroshi har kan cikinta lace din daga ka ganshi zaka gane ba me karamin kud'i bane fuskanta tayi asalin heavy makeup da ya zauna mata kaman baby doll ta kafa d'auri da d'an kwalin kayan ta d'aura black silk d'ankwali a saman d'an kwalin kayan shima d'auri ne me zaman kanshi, kafanta sanye da black hill shoe hannunta rike da black pose me d'an girma d'an kunnen kunnenta ma black ne fashion mara sarka tayi kyau har ta gaji, hure idonshi tayi ganin yadda yake kallonta ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe ido yace "Anya zan iya barinki fita haka?" Shagwabe fuska tayi tace "plz mana not today ka manta bikin best friend dinmu akeyi?" A be so ba a ya so hk ta lalla'bashi suka fice a sabuwar Bentley d'inshi baka se kyalli take............


Sun isa sun samu an fara event d'in suna shiga idanun suka dawo kansu sunyi kyau iya kyau kuma sun mugun dacewa da juna wasu har hotuna suka taso suka musu nan MC yayi tambaya akansu aka fad'a mishi su waye su nan ya fara zuba musu kirari har suka isa wurin zamansu shi gefen ango ita kuma gefen amarya duk kishi ya cikashi har da dana sanin barinta da yayi ta taho ganin yadda maza ke kallonta, anyi shagali sossai rawa kam kala kala inda aka kira babban abokin ango, yayan amarya da babbar kawar amarya Kuma antynta, best couples of the event suzo su d'an taka mana seda aka maimaita sau kusan uku kan haisam ya mike ya nufi hamrah tare da mika mata hannu ta kama a hankali ta mike inda aka saki wakan breathless na shayne ward da tafiyar burgewa suka karasa tsakiyar filin inda sukayi tsaye wakan na ta'ba zuciyarsu sbd yadda yake tashi a hankali, da hannu sagir da suka gama magana da qudra ya kira M.C yazo kuwa da saurinshi inda sagir ya fad'a mishi wakar da zai sa musu Ai kuwa ya wuce yaje ya sa aka saka a hankali muryan M Shariff ta fara tashi cikin wakar shi ta 'fadli falala' nan hamrah ta fara juyawa kad'an kad'an cikin aji, tana bin wakar da d'an lips dinta da ya sha pink janbaki.............


Har akayi baitin farko na namiji akayi na biyu na macen tukun aka d'an yi kid'a kanta na kasa take d'an takawa se jin muryan haisam tayi yana bin wakar yana kallon cikin idonta ya fara cewa.........


*lallai kaunace da soooo kin nuna gareni*🎵

*ko anki ni soo kece mai kulani*🎶🎵

*nai dace a sooo abokaina ku jini*🎵🎶

*ke nafi so a so in an tambayeni*🎼🎼

*bana kallon ko wace 'ya cikin yanayi na soooo*

*in ba ke ba banda abokiyar yin rayuwaaa*🎼🎶🎵


Hannu hamrah ta d'aura a bakinta tana kallonshi with so much love and surprise yadda yake bin wakar kamar shi yayi Zata iya rantsuwan muryanshi yafi na M sharrif daadi da wakar tana nan tana murna har aka maimaita *fadli falala anyiwa d'an Adam se godiya ciki nassamoka nai nasara a so ba damuwaaa*............


Se da tayi gyaran murya tukun ta fara bin baitin karshen tana juyi a gabanshi shi kuma ya zaro sabbin one one thousand ya fara zuba mata inda take cewa.........


*Aaaaa so na d'and'anaaaa daad'i ya rufeni..*🎶🎶

*in na russunaa masoyina d'agani..*🎶🎶

*Ni zan aadanaaa sirri In ka bani..*

*Naki In bayyana ko an takurani..*🎶🎶

*sam ba kowa idanuuu ba wadda suke gani..*🎶🎶

*kai ne de wadda tun asali muka yo shakuwaaa..*🎶🎶


Shi ya maimaita *fadli falala anyiwa d'an Adam se godiya ciki nassamoki nai nasara aso ba damuwaa*🎶🎵🎼🎶Ai bata san sadda ta daka tsalle ta rungumeshi ba cikin farin ciki duk jama'ar hall d'in suka mike suna tafi tsabar burgewan da sukayi, M.C kam ya san yazo bukin girma tsaban nairan da haisam ya jikashi dashi an watse taro lafiya inda ango ya d'auki amaryarshi se gidanshi inda su haisam ma sukayi gidansu a gajiye se mu ce 'Alhamdulillah'


   

   6years laterWata kyakyawar yarinya na gani 'yar shekara uku da d'auriya se gudu takeyi tana dariya sanye take da top pink an rubuta 'I want to be like mummy' a jikinshi da manyan baki se blue jeans gashinta me tsai da ya kai har bayanta a kwance a gyare anyi mata kitson babies wadda kasan ne kawai aka kama da kananan multi color ribbons ba tare da an Kitsa sauran gashin ba kyakyawace black beauty in ka ganta toh kaga haisam tsaban kama ba abunda ta d'auko na hamrah, wani farin kyakywan yaro da be wuce 2years ba ke binta a baya yana ihu da kiran Addaaa Addaaa sanye yake cikin green top da black jean In ka ganshi toh kaga hamrah se kuka yakeyi yana binta suna zagaya parlorn da sukayi kaca kaca dashi hamrah ce ta fito sanye da black silk half gown me hannun vest kanta a wargaje da alamun daga bacci ta tashi kiran namijin ta fara inda take cewa "Saiful islam, saiful islam" aiko yana ganinta  ya nufeta da gudu ya rungume d'aga shi tayi tana cewa "shhh babana kai da waye? Wa ya ta'ba min uba?" Duk da ta san Nihal ce aiko ya fara gwaranci yana nuna Nihal ba abunda ke fita se Addaa murmushi hamrah tayi tace "Nihal me ya had'aku?" Cikin shagwa'ba irin na hamrah tace "momma fa I was watching Moana at destiny world shine wai se na bashi remote control kuma danne danne zeyi har ya chanzamin ko ya shiga wani wurin da bazan iya mayarwa ba se Appah ya dawo"...........


Hamrah tace "yanzu da kika hanashi yayi ta ihu har ya tashenin nan ya miki daadi? You know I'm not feeling fine but you keep troubling him yadda ze hanani sakat?" Shiru tayi kanta kasa juyawa hamrah tayi zuwa d'akinta tana danna kiran Maid da zata zo ta gyara mata parlor bin bayansu Nihal tayi da fuskan tausayi ta shiga inda ta samu hamrah zaune a kan gado tana sharewa saiful islam baki daya 'bata da cheese ball  kunnenta ta kama tana cewa "am sorry mommah bazan kara ba" hararta hamrah tayi se ji sukayi daga bakin kofa ance "we are really sorry mommah plz don't be mad at us" mikewa tayi da sauri jin muryan haisam cikin farin ciki ita da yaran suka fara rigerigen rungumeshi yaran ne sukayi nasara ya d'aga su sama yana juyi dasu yana saukesu ta shige jikinshi tana cewa "what a surprise?? Dazu munyi waya fa shine ko ka fad'amin yau zaka dawo nigeria?" Seda yayi pecking goshinta da lips dinta tukun yace "just wanna surprise you love" tana dariya tace "Ai kuwa kayi nasara I missed you" yace "miss you guys too, me mamana tayi ake fushi da ita?" Nan ta bashi labari dukawa yayi yana d'aukan Nihal wacce asalin sunanta Aisha yace "stop it baby in mommah na bacci ki dena sa saiful islam kuka kinji? Baki san momma na d'auke da little baby ba?" Cikin farin ciki tace "really??zata sayimana yadda ta saya mana saifu?" Kai ya gyad'a mata aiko ta fara murna sauketa yayi ta fice da gudu tana murna saifu ma da asalin sunanahi mas'ood ya bi ta da gudu se kace yasan murnan da takeyi, jikin haisam hamrah ta shige tana cewa "Kaiii zauji wa ya fad'a maka Ina d'auke da little?" Yace "karki manta ni dr ne fah se an fad'amin?" Shafa cikinta yayi yana cewa "am I right? Akwai lil faruq anan?" Kai ta gyad'a, d'aga ta sama yayi yana juyi da ita har suka fad'a gado yana nuna mata yadda yayi kewanta a take ta bada kai bori ya hau inda suka turani waje suka rufo kofarsu............


Zuwa wannan lokaci Qudra ta zama Dr qudratullah Abdallah education ta karanta inda har ta kai matakin dr degree kawai tayi a nigeria masters da PhD dinta tayi su ne a Cyprus inda wani course ya kai sagir yanzu haka yaransu biyu twins ne Fadeel da fadeela da cikin na uku tana turawa, kawancen hamrah da simra na nan inda suke ziyartar juna In sun samu time yaranta hudu yanzu bayan namecyn hamrah, Allah yayi wa Daada rasuwa last two years, mom da dad an kara manyanta yayin da hajja nana ta rigamu gidan gaskiya some months back, a masarautar jordan kuma Abbah ya sauka mulki a lokacin da elhussein ya haifi d'anshi Abdallah tare da matarshi Ummusulaim da ya samu a nigeria cikin familyn sagir Abbah da Ammah na nan soyayyah se abunda yayi gaba💃💃 Ummi tsohuwa me ran karfe ma tana nan tana fama da jarabar tsufa..........*Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Anan na kawo karshen book dina d'in nan me suna hamrah Abunda muka rubuta daidai Allah ya bamu lada abunda mukayi kuskure Allah ya yafemana Allah ya sadamu da alkhairinsa**🙏🙏🙏Special thanks to special people:


1:- My wattpadians waenda zasu karanta su yaba su kuma nuna ina kaunarku sossai🥰🥰


2:- my whatsapp group Hamrah fans group Ina godiya da kaunarku gareni heart you so much❤️❤️❤️


3:- MU KARU DA JUNA group da ba don ku ba da ban kai haka ba I'm what I am today with ur support and love Allah ya bar kauna i love you guys so very much4:- My Family what can I do without you? Ur love and du'as are always with me especially mama and daddy, my sisters and brothers I just want you all to know that I love you so much😭😭❤️❤️❤️❤️💞💝


5:- Ride or die 


Hauwa ibrahim yahya💞

Hassana Abdullahi fagge💝

Muhsina Idris maikano❤️

Sadiya Muhammad💞💞

Khadija danbaba sanusi♥️♥️

Fatima usman hadejia💞❤️


Da ma waenda ban kira suna ba should I say I love you??😘❤️💕 oh ohk I love you guys so much thanks 


#vote

#share

#comme

'Yar mutan AdamNo comments

Powered by Blogger.