Fulani 17

 


17

“Fulani ki jefar da tulun ta can sai ki gudu”

Cewar Inna cike da damuwa. Fadime ta girgiza kanta da ya kusa fashewa saboda ciwo, ga kukan da take idonta har ya

kumbura. 


“Aa sai na shiga gida”


Bappa ya nuna ta da sandar hannunsa. 


“Wallahi baka kai min masizi cikin gidan, ka jafar da si ka gudu aka ce maka”


Ta kara fashewa da kuka, ta rasa yadda za tai su fahimce ta, gashi jikinta ya gama mutuwa ga wani uban zafi da take ji, kukan har ya fara zuwa mata ba hawaye, a lokacin ne ta fara yarda ta fara bankwana da duniya, ta sanj Bappa ba zai bari ta shiga gida da maciji ba, ita kuma ba zata sauke shi ya cutar da ita ba. 

Har rana ta soma dagawa ana abu daya, ita ta ki ta jefar da tulu, Bappa kuma ya ce ba zata shiga gida da maciji ba, aka rasa mai taimakonta duk wanda ya tunkaro ta sai ya ga kan maciji kato ya sako masa ido. 


“Ina ganin abun da yafi aje can garin su Ahmadu akwai wani mai majizai kira shi ya zo ya dauke mata wannan lalura”


Malam Adamu ya fada yana saka hannunsa ya kare fuskarsa daga hasken ranar da ke dukan su, domin rana ta bude sosai wanda hakan ke nuna biyu tayi ko ma ta gota. Fadime na zaune kasa har ta fara wata ramar wahala, muryarta har ta dakishe ga wani uban gumi da take. A yanzu kam Inna ta yarda da mafarkin da tace mata tana yi har ta fadawa Bappa.

  A dole dai da aka isa har garin hayin fari, aka dauko wani mutum nai wasa da maciji akan ya zo ya dauke tulun. 

A lokacin ne Fadime ta gane ashe tana da ragowar karfi, da mutumen ya tun karota sai ta mike tsaye ta fara tafiya wata hanyar tana kuka, hannunta daya na rike da tulun da ke saman kanta dayan kuma yana rike da zanenta daya kusan subucewa. 


“Wallahi ba zan bayar ba, yace sai na kai shi gida” 


Idan mutumen ya tsaya sai ta tsaya, idan ya tunkaro ta sai ta nufi wani gurin mutane kan kowa sai gudu yake. 


“Ki saurare ni da kyau, babu abun da macijin zai miki ni zan zo na karbi tulu sai ki gudu”


Bagarden ya fada a kokarinsa na kwantar mata da hankali, sai ta girgiza masa kai. 


“Aa sai na kaishi gida”


“Waya ce ki kai shi gida?”


“Wani mutum ne, wani ne Wallahi”


Ta fada tana kuka cikin rashin kuzari domin har ga Allah bata da wani zarafin kuka a yanzu. Cikin dabara mutumen ya fara takawa yana matsawa kusa da ita yana tambayarta. 


“Wane mutumen a ina kika hadu da shi?”


“A can dajin, yace sai na kai shi gida idan ba haka ba, zai cijeni”


“Yaushe kika fara ganin mutumen? ”


Bata bashi amsa ba ta ranta a na kare ganin yana tunkaro ta har ya mika hannu ya cafkota, tana gudu kan maciji yana rawa a tulu. Mutumen ya koma gurin mahaifinta.


“Abun da yafi kawai ka bari ta shiga da tulun cikin gida, ni kuma sai na bita idan ta jefar da macijin sai na dauke shi”


“A a ba za a shigar min da masizi cikin gida”


Daker aka lalaba shi ya yarda, sannan bagarden ya nufo ta ya tsaya nesa da ita yace. 


“Ki shiga gidan sai ki jefar da tulun haka ya miki?”


“Eh”


Ta amsa tana mutsa kafafuwanta sakamakon zafin ranar da ke cizonta. A gaba aka saka tana tafe tana waige idan mutumen be biyo bayanta ba, sai da ta shiga har cikin gidan sannan ta jefar da tulun a tsakar gida ta juyo da gudu, mutanen da ke leke ma suka auna da gudu ita da su aka rigen rigen kamar masu wasan boya. Abun da ya bawa Bagarden mamaki a lokacin da ta  jefar da tulun sai tulun ya fadi kasa ya fashe da ruwan ciki babu maciji babu alamarsa. Ba shi kadai ba kowa sai da yai mamakin lamarin, wasu na fadin ko dai ya shige wani gurin.


“Babu inda ya shiga a lokacin da ta jefar ai ina kallonta ruwa ne ya zubo a ciki, lallai ka bincike yarinyar nan akwai ifiranta dake tare da ita”


Bappa yayi shiru yana kallon tulun da ya tarwatse ga kuma ruwa a tsakar gidan. Ya san baya wasa da addu'a haka mahaifiyarta ita kanta Fadime be yi zaton zata wuni ba tare da ta yi addu'a ba. 


“Zan mata karatu In-Sha-Allah, idan ma iskokin za su bar jikinta da yardar Allah”


Hannu ya saka aljihu ya dauko dari biyar ya mika masa yana masa godiya sannan ya raka shi har gurin wanda zai kai maida shi gida akan babur dinsa. Bappa da kansa ya riko hannun Fadime ya shiga da ita gida a nan ta samu damar rafkewa masa tana lumshe ido, sai a lokacin ne ta san ta wahala, daker inna ta dauke ta ta kaita bandaki ta wanke mata jikinta tas sannan ta rikota suka fito tare, doguwar rigar atamfa Inna ta saka mata ta shimfida mata tabarma waje, Fadime ta fito daga dakin tana tafiya kamar zata fadi, tana kwantawa saman tabarmar sai bachin wahala yai gaba da ita, sai wani sauke ajiyar zuciya take. 


FALMATA POV.


Falmata bata fito daga dakin ba sai da aka gama sallah magariba sannan ta fito tai alwala ta koma dakin tai sallah, gaba daya addu'arta na neman Allah yasa kar Baba ya doke ta ne, tana cikin dakin aka kira sallah isha'i ta sake shimfida dankwalinta tai sallah sannan ta koma saman shimfidarta ta takure guri daya tana ta hawaye. 

  Naja sai dariya take mata tana Allah ya kara. 


“Wai ke kin yi dan ki barawa Umma suna ace bata baki abinci ko kuma ace tana cin bashin gari a shago sai gashi Allah ya toni asirinki kin dai ji kunya”


Uffan Falmata bata ce mata ba, dan bata ji abunda take fada ba, ko da ma taji ba zata tanka ta ba, domin yanzu ba ta kowa take ba sai ta Baba, gaba daya jikinta ya dauki rawa sai wani tsam take ji kamar ana shada mata bulalar. 

  Kamar saukar aradu haka ta ji sallamar Baba a kunnenta, tana jin lokacin da Tumba ke labarta masa abunda Falmata take har da kukanta wai tana son bata musu suna. 


“Haba wannan wane irin abun kunya ne Fisabilillahi ace yarinya kamar Falmata zata je shago tace na ce a bani bashin gari kwaki, salon a zage mu ne ko kuma dan ta lalata kanta ne da irin tarbiyar da kai mata?”


Ran Baba yai matukar baci zuciyarsa ta soma bugawa da karfi har wani huci yake. 


“Ina Fulani take?”


“Gata can dakinsu, ni ina ganin idam ba albarka ka cirewa yarinyar nan ba ba zata taba hankali ba”


Tumba ta fada tana matsar kwalla kamar gaske. Jakar hannunsa ya aje ya nufi icen dake tsakar gidan ya karyo ya nufo dakinsu, da sauri Naja ta shiga dakin Tumba ta dauko masa fitilarsa ta hannu ta mika masa kasancewar babu wutar nepa kuma dakin ba a kunna fitila ba. Hannunsa ya kai ya karbi fitilar ya shiga dakin ya maida kofa ya rufe, tana ganinshi ta mike tsaye ta hade hannayenta jikinta nata rawa. 


“Baba dan Allah ka yi hakuri ba zan sake ba, idan na sake ka kashe ni, ka yanka ni ka gasa nama na, amman yanzu ka min afuwa Baba dan Allah”


Tsaye yai yana kallonta idonsa suka cika da kwalla, tausayin yarsa ya cika masa zuciya, amman ba zai iya yafe mata ba idan be dake ba ya san Tumba ba zata ji dadi ba, shi kuma baya son bacin ranta. 

 Kama ana daga kafarsa dole haka ya isa inda take ya fara dukanta kamar dan dukanta kawai akai shi, yadda yake auna mata lulalar a jiki sai ka rantse da Allah be tana jin tausayi a zuciyarsa ba. Sai da bulalar ta ƙalle sannan ya bude dakin ya fito. A lokacin Falmata bata ko iya kuka sai kakarin wani abu take kamar za tai amai.

  A gurin ta kwana har safe, ta saba tashi sallah azuba da wuri, wannan karon sai ta kasa sakomakon tsamin da jikinta da yai ga uwar yunwar da ta wuni da ita kuma ta kwana da ita, ga azabar ciwon duka ga na ciwon kai. 

 Har kusan bakwai Falmata bata fito daga dakin ba, sai da Tumba ta shigo ta hau ta matsifa.. 


“Wai salon karki je aikin ne yasa kika fara wannan makircin, kika ki fitowa ki yi sallah ki yi aikin gida? Tun da kin ji ance za ki yuni can ko? Zan samu karin albashi”


Daker ta daga idonta daya da jinin ya kwanta a ciki ta kalli Tumba dan dayan ya like sakamakon bulalar data same ta a fuska. 


“A a wallahi jikina ciwo yake bana iya tashi”


Ya fada kamar mai karyeyen harshe.


“Ke nan wannan ya anyi makira, Wallahi ko ki tashi ko na ci ubanki da kaina”


Ba dukan take tsoro ba dan tasan duk dukan da Tumba zata mata a yanzu be kai wanda Baba yai mata ba jiya da dare. Hakan yasa ta koma ta kwanta a gurin, tana maida numfashi daker kamar mai nakuda. Kwafa Tumba tai ta fice daga dakin dan ta san ba zata iya tashin da gaske na ganin ta mata warning da karin wani amman bata tashi ba, ita kanta ta san ba karamin duka Baba yai mata ba.


Sai kusan tara Falmata ta samu kuzarin mikewa tsaye ta fito daga dakin tana jin jikinta na mata mugun tsami, daker ta cika buta da ruwa ta dauka ta nufi bandaki, tufafin jikinta ta cire ta dauko soso da babu sabulu ta fara goge sai ta ji wani azaba kamar tana likawa jikinta wuta. Da sauri ta aje soson ta saka maida tufafin ta wanke fuskarta ta fito waje tai alwala ta shiga dakinsu tai sallah tai addu'a sannan ta fito sanye da hijabinta ta nufi tukuyar ruwa ta bude ta cika kofi ta sha, sai ta ji cikinta ya tsuke ya fara murdawa. 

  Daker ta karasa bakin kofar Tumba ta leka. 


“Umma zan je aikin”


“Da dai karki je, yar iskar yarinya kawai Allah in baki yi hankali ba sai na saka Babanki ya tsine miki albarka”


Bata ce komai ba, ta sanda kanta kasa ta juyo ta fara tafiya. 


“Ki tafi gidan Asabe ki kai mata wannan”


Ta juyo ta shiga har cikin dakin ta karbi kudin da Tumba ta mika mata. Ko ba fada mata ba ta san ko kudin adashe ne da take zubawa duk wata 5k wanda a cikin kudin zancen da ake bata da kuma kudin Baba take samu ta zuba tun da ba wata sana'a take ba. 

  Falmata na tafiya tana juya kudin a hannunta zuciyarta na raya mata abubuwa da dama, a take ta ji wani kuzari ya kara mata, tana tafiya mutane na tambayar abun da ya same fuskarta sai tai musu shiru kawai ta wuce. 

 

Bata hanyar da zata sadata da ta gidan Asabe mai adashe ba sai ta dauki hanyar titi wacce hanya daya ce da hanyar zuwa gurin aikinta. 

 Sai da tai nisa sannan ta tari Napep ta hau. 


“Ina za a kai ki?”


“Tasha”


“Tashar da ake zuwa wani gari”


“Wane gari za ki je?”


Ta yi shiru kamar mai tunani, bata san garin da zata ce ba, hasalima ita bayan kauyen Babansu sai na Mamanta sai kuma na su Tumba bata san wani guri ba. 


“Maiduguri ko Kano ko Kaduna? Ko Kauye?”


“Ka... Ka... Kadun... Na.... ”


Ta fada muryarta na rawa sai waige take tana jin kamar an biyoyata.


“Dari uku zaki bada”


“To muje”


Mutumen ya kunna napep dinsa ya hau titi ya fara tafiya yana kara sautin kidan dake tashi. A tsorace take har suka isa babbar tashar ta mika masa kudinta ta fita daga napep din ta shiga cikin tashar. 

 Tana tafe tana waige waige har ta isa gurin manyan motocin. Masu neman passengers na ta aikinsu sai tambayar inda zata je suke.


“Kaduna”


Ya fada ba dan tasan hanyar da za a bi a tafi can din ba.


“Zo ga mota nan mutum biyu ake jira” 


Ta bi mutumen dake nuna mata motar, sai da ta shiga ta zauna sannan suka fada mata kudin motar ta cire ta ba su, tana kokarin gyara zamanta ta hango wata mai abinci a gafen wata mota, sai ta fita cikin tsoro zuciyarta sai bugawa take. 


“A bani shinkafa da miya”


“Na nawa?”


Ta mika dari biyar din dake hannunta. 


“Na 100”


“A leda ko a plate?”


“A leda”


Falmata ta amsa tana ta kallon hanyar shigowa tashar dan jin take kamar Tumba zata biyota har nan ne ko Baba. 

Matar ta zuba mata shimkafar da bata wuce loma biyar ba a leda ta saka mata miya. 


“To samin ta duka”


Ta fada dan ta san ta darin ba isarta zata tai ba tun da ta wuni da yunwa kuma ta kwana da ita. Da sauri ta kai hannu ta karba ta sake ciro dari biyu ta mika mata. 


“Ba ni ruwa mai sanyi na daya”


Matar ta karba ta cire kudinta ta mika mata ruwan da canjinta, Falmata ta juyo da sauri ta baro wajen, a lokacin data dawo cikin motar sai ta saka cin abincin saboda kunya, duk kuwa da ta lura da wasu matan da maza suna ci amman ita ta kasa ci saboda bata saba ba. Sake fita tai ta koma can bayan masallacin dake tashar inda babu mutane ta zauna ta bude ledar shimkafar ta fara ci hannu baka hannu kwarya kamar wacce ta shekara bata ga abinci ba. Ko rabin shimkafar ba tai ba sai ji ta koshi saboda tsoro da kuma daurewar da cikinta yai, sai kawai ta sha ruwa ta kulle sauran a leda ta boye a hijab ta dawo cikin motar ta zauna. 

Ba a jima ba aka samu wani passenger ya shigo. Basu bata lokaci ba driver ya shiga suka dauki hanyar gidan mai, sai ta ya sha mai sannan suka kama hanyar Kaduna. 


Duk tafiyar da ake da firar da wasu ke yi Falmata na cikin motar ta yi zugum tana tunani, idan ta je Kaduna ina zata sauka? Wa zai karbe ta? Ina zata kwana? A lokacin ne ta soma jin kamar tace wa Direban ya juya da motar su koma gida, idan kuma ta koma gidan wahalar ce zata sake sha, kuma ta riga da taba kudin Tumba idan ta koma ma me zata ce mata?

 Wasu na bachi su farka su cigaba da fira ko kallon titi ko taba waya ban da Falmata dake ta aikin zubar da hawaye a cikin hijabin da ta boye kanta. 

Bata gasgata ta bar garin yola ba har sai da ta soma jin wani yanayi na dabam yana rabarta, duk tsayawar da direban yake yai sallah Falmata bata daga kai ta kalli kowa ba, dan bata son a gane kuka take. 

 

Kamin su shiga cikin garin Kaduna direban ya fara kiran mutane yana sanar da su ga sakonsu ya shigo da su su zo su zo su karba, a lokacin ne hawayen Falmata suka kara yawa ta soma jin kamar zazzabi na sauko mata. Bata kara tausayin kanta ba sai da diraban ya isa cikin tasha, mutane dake motar suka fara fita suna yi ma Allah godiya na sauka lafiya da su kai, sai da kowa ya fice sannan ta fito daga cikin motar yana jin wani yanayi na dabam. Inda ta ga mutane na fita ta nufa tana tafe tana sharar hawaye tana nishi kamar wata mai ciki sakamon nauyin da zuciyarta tai mata. Haka ta fito cikin tashar dunkule da hannu a hijab kana kallonta ka ga marar galihu, ga fuskarta da kwancin bulala idonta daya kuma ya kankance ya bar dayan, Hijabinta a kode kamar dai tufafin da ke jikinta. 

 Tafiya ta fara yi tana kallon kasa hawaye na ta zubar mata kamar dan kukan kawai aka yi ta, ina zata je? Ga yamma na yi sallam ma ina zata yi? Abinci fa wa zai bata? Kamar daga sama ta ji an dafata. 


“Ke....”


A firgice ta juyo ta kalli matar wacce ke sanye da doguwar rigar atamfa, sai dan karamin gyalen da ya bayyana gashin dokin da ke kanta. 


“Ina magana ba ki ji ba lafiya kike kuka?”


A nan din ma bata ji komai ba sai dai ta san magana take mata tun d har ta taba gashi kuma bakinta na motsi kamar yadda idon matar ke sanar ita saboda irin kallon da take mata. 


“Bana ji sosai ai an daga murya ko an yi kusa da kunnena”


Falmata ta amsa mata tana kokarin fashewa da kuka. Kallon tausayi matar wacce tafi kama da budurwa take soma mata, kamin ta matsa kusa da ita ta rada mata a kunne. 


“Me kike yi wa kuka?”


A nan Falmata tai shiru kamar ba zata amsa ta ba, hawayen kuma ya cigaba da sauko mata. 


“Ban san kowa ba a nan, ban san inda zanje ba”


“Daga ina kike?”


“Yola”


Murmushin budurwar tai.


“Allah sarki garin masoyina”


Ta fada da sigar da ita kadai zata iya jin kanta sannan ta sake kai bakinta a kunnen Falmata.


“Me kika zo yi nan?”


“Komai, kawai gudowa nai daga gida”


A lokacin ne ta fara mata kallon mamaki.


“Au.... Okay...”


Sai kuma ta sake kai bakinta kunnen Falmata.


“Miyasa?”


Falmata tai shiru tana murzar ledar da ke hannunta wacce ta boye a cikin hijabinta. 


“Za ki iya bina muje gidana zan sauke ki a can sai na baki abinci da gurin bachi”


Da sauri Falmata ta daga kai, daman abun da take nema kenan kayanta ya tsinke a gindin kaba, ko da yar yankan kai ce ita zata iya binta. Hannu budurwar ta dagawa wata jar mota dake nesa da su kadan alamar mai jan motar ya karaso, kamar daman can umarni yake jira sai gashi a kusa da su in few seconds. 


Da kanta ta budewa Falmata gidan baya, ita kuma ta bude gidan gaba ta shiga ta saurayin yaja motar mai cike da sanyin ac da hannu daya dayan hannunaa kuma rike da wayarsa. 


“Tun a tasha kike bin yarinyar nan”


Ya fada ba tare da ya kalleta ba, sai ta dan kalleshi kadan tana daukar lemun gwangwanin dake gefenta ta sha. 


“No ai ina ganinta na gane tana ciki damuwa, kuma tana tafe tana kuka, you know idan na ga mutum a irin yanayin na ina son taimakonsa saboda ni na san wahalar da na sha”


Ta fada tana sauke ajiyar zuciya kamin ta cikawa bakinta iska ta busar, sai ta dan juya ta kalli Falmata da kanta ke sunkuye sannan ta kalli wayarta da ke ringing. 


“Kina picking call din nan zamu samu matsala da ke, idan ya jira ki jiki na rawa ki dauka”


Saurayin ya fada yana kallon wayar cike da fusata. Murmushi kawai tai ta cigaba da kallon wayar tana jin kamar tai picking din. 

HAJIYA BABBA POV. 


“Talba wai baka sha'awar yadda mahaifinka yake milkin garin nan ne? Baka lura da yadda mutane suke ba shi girma ba, a duk lokacin da ya so ganin governor zai ganshi a take, idan ya so ganin shugaban kasa ma zai kira waya a fada masa ya same shi su gana, baka lura da irin arzikin da mahaifinka ya tara ba, baka lura da yadda yake juya duk wanda yake so ba? A sanadinsa kuka zama abun da ku ka zama a yau, da isarsa da kudinsa kuke yadda kuke so duk wannan abun be taba burge ka ba”


Talba yayi shiru yana nazarin kalamanta. 


“Shin baka taba son ka saka mahaifiyarka a cikin farinciki ba? Baka taba jin cewar ya kamata ka gaji mahaifinka ba?”


“Hajiya ba zan iya gadon Mai Martaba ba, tun da Shattima da Baba Waziri da Baba Jarma da mutane da yawa suna raye”


Hajiya ta yi murmushi tana dauke kai daga barin kallon dan nata. 


“Ai Shattima da duk wani da kake gani ba komai ba ne, matukar zaka saka son abun a ranka kuma ya cusa kanka komai na gidan nan, kai baka lura da yadda Shattima yake ba, Ammy ta nuna masa cewar Mai Martaba na mutuwa shi za a dora, shiyasa yake ta shiga yana fita ana komai da kai, kai kuma sun maida ka can gefe babu wanda ya sanka, shi Shattima ba kula da kanen mahaifinsa ba ne? Talba na dade da sanin cewar ciwon Mai Martaba har da sa hannun Ammy saboda Shattima ga samu sarautar”


A firgice Talba ta mike tsaye yana yi ma Hajiya Balki wani irin razanenen kallo. 


“Ammy fa kika ce Hajiya”


Hajiya ta kalleshi. 


“Baka lura da yadda take mulkar gidan nan ba ita da danta? Tun kamin yau ai kasan yadda ni da ku ta maida mu bayi, Mai Martaba baya jin maganar kowa sai nata, yanzu kuma da ya kwanta ciwo a gidan nan bata jin maganar kowa sai nata da na danta, Shattima ya taba kiranka a matsayinsa na yayan uba daya yace kuje wani guri ko ka yi wani abun a matsayinka na jinin Mai Martaba?”


Talba yayi shiru yana nazarin kalaman Hajiya, tabbas biri yayi kama da mutum. 


“Zauna mana”


Ya zauna kamar yadda ta bukata. 


“A karatu ma Shattima American yai nasa, kai fa ta bari a an kai ka ne? Ga Karima nan babu yadda bata so barin kasar nan taje Karatu ba, amman Ammy ta hana Mai Martaba, sai Jurry aka kai da Salima”


Talba yaja wani dogon numfashi ya sauke, ya dade da kiyayyar Ammy a ransa amman ba irin na yau ba, domin be taba lura da wannan ba sai a yanzu da Hajiya ta fada masa abun da ya kasa fahimta shekaru da dama. 

  Hajiya ta kai dubanta a gurin wayarta da kiran Jarma ke shigowa. 


“Dauko min wayata”


Talba ya tashi yaje ya dauko mata ya mika mata, sai da ta dan kalleshi sannan taj picking call din. 


“Hajiya ke kadai kike? Gani nan zuwa yanzu”


“Sai ka shigo”


Ta amsa masa tana murmushi, sannan ta aje wayar.


“Shiyasa nake son kai da Sirleem ku hada kai ku taya ni wannan yakin, ba ni da burin da ya wuce na ga ka hau Sarautar nan Talba”


“Ni”


Ya nuna kansa yana jin wani irin abu na ratsa shi na isa da kwadayin Sarautar. 


“Kai mana, Uwa kawai kuka hada da Sirleem da ace mahaifinka ne ya haife shi, da shi ya kamata mu marawa baya ya samu sarautar nan, amman kai ne jinin Mai Martaba kai ya kamata ka hau Sarautar nan Talba, ka samu Sirleem ku tattauna akan maganar nan ka nuna masa illar abun da Ammy take mana, amman karka nuna masa ni na fada maka, domin ba zai fahimta ba”


“Sirleem ina jin baya nan yace min zai je Kaduna”


Da sauri Hajiya ta kalleshi. 


“Yaushe?”


“Be fada min ba ban san ko ya tafi ba, maybe kuma yana nan tun da be fada miki ba”


“Ai ba zai fada min ba tun da zai je gurin wacan yar'iskar karuwar, amman zai dawo ya same ni”


Ba kalamanta kadai suke bayyana bacin ranta ba har da fuskarta da numfashinta. 


“Tashi kaje Jarma zai shigo yanzu ”


Ta fada ba tare da kalleshi ba. Shi kuma ya mike tsaye cike da tunani kala kala a ransa ya fice. 


No comments

Powered by Blogger.