Fulani 16

 


16

A gaban wani madaidacin gate ya faka motar, budurwar ta bude ta fita sannan ta budewa Falmata tana mata alama da ta fito.

 

Cikin rashin kuzari Falmata ta sako da kafafuwanta sannan ta fito daga motar tana jin sanyin ace motar na saukar mata da mura, sai kokarin boye ledar hannunta take tana karewa na unguwar kallo, ba unguwar masu kudi bace haka kuma ba za a kirata da unguwar talakawa ba, irin unguwar nan ce mai kama da sabuwar unguwa wance mutane ba su gama dawowa ba, domin akwai gine gine da yawa da ba a karasa ba, ga kuma ciyawa da tai yawa a ko'ina, tsakanin wani gidan da wani kuma akwa tazara mai tsawo ta filayen wasu mutane. Hannu ta saka a jakarta ta ciro makulli tana kikarin sakawa sai gate din ya bude, ta dan bude ido da far'a sannan ta tura ta shiga. 


“Shigo”


Bayan Falmata ta shiga ta rufe kofar gate din, arba da tai da wata hadaddiyar mota yasa murmushin fuskarta ya kara fadada da sauri ta nufi entrance har tana hadawa da gudu, hakan kuma ba karamin tsoro ya ba Falmata ba, tana a wani gari da ba na ta ba, a wata unguwa kuma a sabon gida da matar da bata sani ba. 


“Karaso mana ko kina jin tsoro ne?”


Matar ta fada ganin Falmata ta tsaya daga can kusa da gate din tana karewa madaidacin gida kallo. Sai da ta tura kofar falon sannan Falmata ta karaso kusa da ita


“Shiga”


Cikin tsoro da fargaba ta nasa kafarta a cikin falon, bayan ita ma ta shiga ta maida kofar ta rufe. 


“Zauna a nan”


Ta nuna mata kujera, cikin rashin natsuwa ta zauna saman kujerar dake kusa da kofa. 


“Mansura daga ina kike?”


Budurwar ta juyo da sauri tana kallon kofar kitchen din. Sirleem ne tsaye jikin kofar rike da gorar ruwa yana kallonta. Cikin murna ta karasa kusa da shi ta rumgume shi. 


“Oyoyo ban taba expecting zaka zo yau ba, what a surprise”


Ya dan kawar da fuskarsa daga kiss din da take kokarin yi masa yana kallon Falmata,  juyawa ta yi ta kalleta sannan ta sake kallonsa tana kokarin kai hannu ta taba sajen fuskarsa, sai ya rike hannunta ya tureta gefe ya dawo falo ya zauna. 


“Na hadu da ita ne a tasha, an kawo min sako daga kano shi ne na je karba sai na hadu da ita, tun cikin tasha tana kuka har waje da na tambaye ta sai tace bata san kowa ba a nan gudowa tai”


Tun da ta fara maganar yake kallon Falmata yana jin kamar ya taba ganin fuskarta but zai iya tuna a ina ba ne. Ya kalleta a natse irin kallon da ita ta san me yake nufi. Sai ta nufo shi tana cire Veil din kanta. 


“You know idan na ga mutum a damuwa ina son na taimaka masa, because ni ma na taba shiga a irin wannan matsalar”


Ya sake kallon Falmata da tai mutuwar tsaye tana kallonsa. Shi din ne ko kum har yanzu idonta gizo yake mata? Ko kuma masu kama da shi ne take gani? Ai ta baro yola ya akai ta ganshi a nan? 


“Me yasa ta gudu daga gidansu?”


Ta zauna daf tashi har jikinta na gogar nashi. 


“Ya za a yi na sani yanzu yanzu fa na hadu da ita ban tambaye ta ba”


“And kika bata masauki, what if karya take? Kika san abun da ya rabota da gidan?”


“Ban sani ba, amman zan sauketa a nan zata zauna tare da ni, tana bukatar taimako”


“This is my own house not yours, hope kin san da wannan?”


“And that mean?”


“Ba zata zauna a nan ba”


Ya fada mata kai tsaye yana kallon cikin idonta, fuskarsa babu annuri. 


“Fine idan baka son ta zauna tare da mu, zan sallame ta, amman rayuwarta zata iya fadawa a hadari ka sani”


Ya mike tsaye yana shafa kansa. 


“Idan rayuwarta ta fada a hadari ina ruwanki? Kin santa ne? Idan kina tsoron ta fada a hadari then take her to her parents house”


“Amman ka san abun da yasa ta baro gidansu? Duk ba mu sani ba bata son zama kusa da kowa na ta that's why she run”


“Kin fi kowa sanin hali da mace take fadawa idan ta rubu da iyayenta, uhmmm?”


Ta yi shiru tana kallonshi.


“Lokacin da kika gudo daga gidan iyayenki da kika fada mugun hannu ba karuwanci kika fara ba? So on kika bata future dinki that's why Hajiya ta hana na aureki, kowa kallon karuwa yake miki kina son ki koma cikin familynki kin saka saboda kin lalata alakarki da su, look at her bata wuce 15 ba, and if you want to help her take her back to her parent house”


Hawaye ne masu zafi suka fara sauko mata, ta kalli Falmata a tsawa ce tace. 


“Ke tashi ki fita”


Falmata ta kasa motsi balle ta mike tsaye ta fita kamar yadda ta umarta, bata ji duka kalmansu ba amman ta ji wannan tsawar kuma ta ji turancin da Sirleem yai mata a karshen maganarsa da ya karasa a fusace, and now hawaye Mansura take, hakan na nufin matsala ta samu da mijinta a dalilinta.


“As how? Ki kawo ta unguwar da bata san kowa ba kuma ki ce ta tashi ta tafi idan aka tambaye ina ta fito tace a nan gidan ko?”


“To ya kake son nai mata?”


Ta fada a tsawace tana hawaye, tass ya wanke mata fuska da mari. 


“How dare you, dan ina son ki ba shi zai baki damar yin duk abunda kike so da ni ba, kamar yadda so na be hanaki kula wasu mazan ba”


Sai a yanzu ta gane fushinsa ba na shigowa da Falmata kawai ne ba, har na fitar da tai da Yasir, durkushewa tai a gurin ta fashe da kuka. Falmata dake rike da fuskarta sakamakon marin da akai wa Mansura ta mike tsaye ta sauri ta nufi kofa. 


“Ke....”


Ya kirata a watsawa sai ta juyo jikinta na rawa ta fashe masa da kuka tana girgiza kai. Kallonta kawai yake kamin ya nuna mata kujera alamar ta zauna, sai ta dawo kusa da kujerar ta zauna a kasa tana hawaye. Ganin tana ta boyon hannu a hijab ga hawaye sai sauko mata suke yasa ya nufo inda take sai ta kara fashewa da kuka tana bashi hakuri. 


“Dan Allah kai hakuri, dan Allah karka min komai”


Hannunsa ya kai ya daga hijabinta sai ta mike tsaye tai saurin sakin ledar hannunta shinkafar dake ciki ta fadi kasa. Kallon shimkafar yai kamin ya sake kallonta da fuskar dake nuna alamar ba wani abun zai mata ba, cikin tattausan lafazi ya ce. 


“Daga ina kike?”


Bakinsa kawai take kallo kamin ta kalli fuskarsa da kwarjininsa ya cika mata ido. 


“Bana ji sosai sai an yi kusa da kunnena ko an fada sosai”


Kallonta kawai yake for no reason, kamin ya kai hannanyensa ya dafa kafadarta ya zaunar da ita saman kujerar. 


“Ya zaka taba ta, ina ruwanka da ita”


Ta fada tana mikewa tsaye ta nufo inda yake tsaye kusa da Falmata. Dan murmushi yai irin murmushin nan na mamaki daman ya san za tai magana, saboda Mansura tana kishinsa ko sunan wata macen ya fadi a gabanta sai ta nuna kishinta, amman ita ta kasa tsare masa kanta duk kuwa da irin kudirin da yake da shi na aurenta. 

  

Falmata ta kalleta a tsorace gaba daya ta firgice ta rasa gane kansu yanzu, gashi ba komai take ta ji ba. Juyowa Sirleem yai ya kalleta sai ya nuna mata kofa alamar ta tashi ta fita, sannan ya juyo ya kalli Mansura. 


“Me yake damunki ne Mansura?”


“Kai ba ka ga abun da kake ba?”


Be ce nata komai ba ya hade rai ya fara bin bayan Falmata sai ta riko rigarsa.


“Ina zaka je? Ina zaka kaita?”


“Ba zan ga wata mace zata aikata irin abunda kika aikata ba na kyaleta, sake min riga”


Ta saki ba dan ta so ba, sai dan ya karasa a tsawace yana kara hade rai kamar be taba dariya ba. A kujerar ta Falmata ta tashi Mansura ta zauna ta hade kai da hannu tana hawaye wani irin abu take ji a zuciyarta yana taso mata, ta san waye Sirleem bayan ita baya mu'amala da ko wace mace amman tana kishin ganinsa da mace ki da ko yar'uwarsa ce. And the most annoying part is duk abunda za tai ba zai saurareta ba a yanzu saboda ta fita tare da Yasir, da ace a gida tararda da ita, to zai saurari duk kalar haukar da zata masa saboda yana sonta shi ma. 


Ya sauka entrance din yana kallon Falmata da ta kusa isa gate tana waigensa, motarsa ya shiga yai warming dinta sannan yai reverse ya isa gate din da Falmata ta kasa budewa, fitowa yai daga motar ya zagaya ta dayan bangaren ya bude mata front seat, da hannu yai mata alama da ta zo sai kawai ta fashe da kuka ta dukushe a gurin tana girgiza masa kai. 


“Ba wani abun zan miki ba”


Ya fada cikin daga murya, sai dai ba irin muryar da zata ji ta tsorata ba, ni ta yadda zata ji shi. 


“Aa bana so”


Ta fada hawaye na sauko mata, tana jin wata sabuwar nadama da dasani na barin garinsu da gidansu da ke cike da kuncin rayuwa, gaba daya ta tattara zancen da tunanin Sirleem ne ki ba shi ba ta aje a gurin daya, ta rayuwarta take. Ya rufe motar ya karasa inda ya risina yana kallon fuskarta da tsoro ya gama bayyana a kammaninta.

Dark skin dinta sai shining take duk da kasancewar kana ganinta kasan rayuwar wahala take, ga golden eyes dinta masu haske da take ta kallonsa da su. Kallonta kawai yake zuciyarsa na raya masa ya santa amman a ina? The first thing daya kamata yai shi shine ya gusar da tsoronsa da take ji a yanzu, ya kara matasawa kusa da ita sosai kamar zai tabe ta. 


“Kin san ni?”


Ya rada mata da a kunne. Sai ta yi shiru tana ta kallon fuskarsa da sajensa da ya karawa fuskar kyau. Bata son tace eh ko aa tun da bata da tabbacin shi din ne Sirleem ko waninsa? Ko kuma gizo idonta ke mata.


“Kin taba jin wani Sirleem M2 mai waka? Ko ganinsa ko da a hoto ne?”


Nan ma shiru tai sai dai ta dan bude ido alamar wani abu ya zo a tunaninta. Ya dan kalli kofar falon sannan ya sake kallonta ya kai bakinsa kunnenta.


“Kin san shi?”


Ya gyada kai sai ya saka mata murmushi ya nuna kansa. Da wani irin karfi zuciyarta ta fara bugawa tana kallonsa. 


“Ji nake kamar na sanki a ina na sanki?”


Kallonta take kamar ba zata ce komai ba, a yanzu ba kallon tsoro take masa ba na mamaki da tunani. 


“Ka taba kade ni a mota”


Yayi shiru yana nazari, sai ya sake sakar mata murmushi. 


“Yeah few days back ko? Har na baki fula? Amman ai a Yola ne”


Ta daga masa kai ba dan ta san abun da yake nufi da few days din ba, sai dan karasa mata maganar da yai da zancen bata fula ta kara tabbatar da shi din ne ba tantama. Sai ya dan bude ido yana kallon kyakkyawar fuskarta. 


“Hakan na nufin ke yar garin mu ce”


Ta sake gyada kai tana nuna shi. 


“Da gaske kai ne?” 


“Ni ne mana” 


Ya fada yana daga mata kai ba dan yana da tabbacin zata ji ba, tun da ta fada masa bata ji sosai kuma ya ga zahiri sai dai daga mata kan da yai ya isar da sakonsa. Da sauri ta mike tsaye tana masa wani irin kallo kamar ta hade shi, ga wani shauki da mamakin sake ganinsa da tai yana cikata. Sai shi ma ya mike tsaye yana kallonta da murmushi a fuskarsa. 


“Ina son ka sosai, ina yawan sauraren wakokinka lokacin da ina ji, ina son ka sosai kana burgewa ban taba mafarkin zan hadu da kai ba, kuma ban sake saka ran zan sake ganinka ina son ka sosai”


Ta karasa muryarta na rawa idonta kuma yana cika da kwalla irin na fan ya hadu da celebrity. 


“Wow”


Ya fada still yana murmushi kamin ya kama hannunta. 


“Zo muje”


Ba musu ya bishi yana rike da hannunta idonta suna kan fuskarsa, har ya zagaya da ita ya bude motar ya saka ta gidan gaba shi take kallo ji take kamar a mafarki ne. Rufe motar yai sannan ya je ya bude gate din ya dawo cikin motar yaja suka fita ya sake rufewa ya dawo ya rufe gate din sannan ya dawo cikin motar yaja suka fara tafiya. 

Bata kallon komai sai fuskarsa wani abu mai kama da jindadi yana ratsata zuciyarta kamar zata fito waje akan bugawar da take da karfi, time to time yake kallonta sai ya dan sakar mata murmushi har suka isa wata kyakkyawar unguwar da tafi kama da GRA.

Horn yai ba bata lokaci aka bude masa katon gate din, sai da ya kalleta sannan ya ja motar suka shiga cikin katon gidan. Gaban entrance ya faka motarsa ya bude ya fita sannan ya zagayo ya bude mata ba tare da yace komai ba, ita ma din bata jira yace ba ya sauko da kafafuwanta ta fito. Kato gida ne mai kyau gaske an kawata ko'ina da flowers an masa kwaliyar zamani gwanin burgewa. 

  Hannunta ya rika ya fara takawa tana biye da shi har yasa key ya bude kofar ya shiga tare da ita. Tsaye tai bakin kofa ganin babu alamar mace tana rayuwa a cikin gidan, sai ya juyo ya kalleta, hakan ya bata damar janye hannunta daga rikon da yai mata. Sai ya dawo kusa da ita ya tsaya ita kuma ta daga kai tana kallonshi, ko bata fada masa ba ya san abun da take nufi wanda hakan kuma ba halinsa ba ne, ko ma halinsa ne shi me zai yi da teenager irinta. Yana kokarin yi mata magana wayarsa tai ringing, ciro wayar daga aljihun wandonsa ganin sunan Hajiya yasa shi daga kai masa ya sauke sannan yai picking.


“Sirleem ban isa da kai ba ne? Ban isa na maka magana ka ji ba?”


“Hajiya i swear to the seven heaven zan dawo gobe, ba gurin Mansura na je ba, wani aiki ya kai ni”


“Na ai dai fada maka karka wuce yau ko gobe, wato mallakar da take maka ta fara yawa har zaka bar garin Yola kaje gurinta ba tare da ka sanar da ni ba ko?”


Yayi shiru dan be san abunda zai ce mata ba kuma. 


“To ya maka kyau ka cigaba da abun da kake karka fasa, taya dan albarka zai kula yarinyar da mahaifiyarsa bata so? Ka cigaba karka fasa”


Kit ta kashe wayar cike da fusata, sai ya sauke ajiyar zuciya ya busar da iskar bakinsa ya kalli Falmata. 


“Ke ma mamarki na miki fada kamar ni?”


Ya rada mata a kunne, sai ta girgiza masa kai.


“Ni ba ni da Mama, Mamata ta rasu”


“Ayyyah... ”


Ya fada yana kallonta cike da tausayi, sannan ya cire talkamin kafarsa ya karasa cikin falon sai kuma ya juyo ya kalleta ya dago mata hannu. 


“Karaso mana”


Ta girgiza masa kai. 


“Look ni ba wani abu zan miki ba, za ki kwana nan ne gobe sai na maida ke gida”


Ya fada da muryar da zata ji yana ware hannayensa, sai tai saurin girgiza masa kai. 


“A a ni ba zan koma ba, idan na koma Babana yanke ni zai yi”


“To shigo ki zauna”


A hankali ta fara takawa har ta iso cikin falon, ya nuna mata kujera sannan ya dauko remote ya kunna plasma dake falon, ya nuna mata wasu dakunan dake facing inda plasma take.


“Kin ga daki can idan zaki yi alwala da sallah ko fitsari, kuma a can zaki kwana, ni zan je masallaci yanzu”


Yana fadar hakan ya nufi hanyar fita, gaba sai tsoro ya kamata gidan ya mata girma ita kadai kuma tana ji a jiknta be kamata ta kebi da namiji duk kuwa da bata da tabbacin zai mata wata illar ko akasin haka. Sai da taji kara rufe kofar ta kara raina kanta sai ta zauna kusa da kujerar ta fara kuka a hankali tana tuna gidan, no matter irin wahalan da yake sha ta fi sakewa a can fiye da wani gurin, a yanzu ta kara nadamar guduwa da tai, tunawa da yace zai maida ta gida. Har yai sallah ya dawo tana nan a inda ya barta banbanci dazun da yanzu shine a yanzu rabe take jikin kujera tsakanin dazun da ya fita ya barta a tsaye. Be ce mata komai ba ya karasa inda take zaune ya rika hannunta ta mike tsaye sai ya nufi dayan dakin da ita. 


“Dan Allah karka min komai dan Allah ka rufa min asiri”


“Waya fada miki idan na kebe da mace iskanci nake wai? Me zan yi da ke?”


Ya fada a tsawace duk ta wani hada mishi zafi, ga fadan da Hajiya take da shi ga fitar da Mansura tai da Yasir yanzu kuma tana son kara masa wani ciwon kan. Ba shiri Falmata ta sha jinin jikinta.


“Wuce kije ki yi sallah na ce”


Ya daka mata tsawa, da sauri ta wuce ta shiga dakin mai kama da na mata, an tsara komai an jera furniture ga wani kyakkyawan zanin zago an shimfida. After ta shiga ya karasa shiga ya kunna ac ya karasa gaban windows din ya dage labulayen sannan ya bude mata kofar bathroom. Ba tare da yace mata komai ba ya juya ya fice ya sakawa dakin key daga waje. 

Zaunawa tai a kasa tana hawaye tana kallon dakin da bata taba mafarki wata rana zata kwana a irinsa ba, sai da ta ji ana kiran sallah isha'i sannan ta tashi ta shiga bandakin, sai ta rasa yadda zata kunna fanfon dan domin bata saba ganin irinsa ba bata taba amfani da irinsa ba. Har ta juya zata fita sai kuma ta dawo ta kai hannunta ta murda sai ta ga ruwa ya fara sauka. 

Fisari ta fara yi sannan tai alwala ta kuma tara hannunta ta sha ruwan ta fito. Dankwalin da ke kanta ta cire ta shimfida ta fara rama sallolin da ake binta sannan ta gabatar da isha'i. 




FADIME POV. 


sai kusan magariba Fadime ta farka, gaba daya mafarkinta na abun da ya faru ne, duk mutumen dake shigowa suna Allah kyauta sai dai su ganta tsakar gidan tana sharar bachin wahala. Amo na aiki tana kallon Fadime da tunani kala kala wasu ranta, ita kanta a yanzu ta yarda Fadime ta hadu da iska da suka fi nata karfi to ga zahiri ta gani, bayan nan kuma ga wutar da ta saka mata an cire mata. Jin tai yatsanta na zafi kamar wutar, wanda hakan ke nuna alamar a cikin kuryoyin da take ajiya akwai wacce masu ita suka matsanta da addu'a da kuma neman taimako, kwayar da ke hannunta ta aje ta tashi daga gaban murhun ta nufi dakinta. Dukawa tai karkashin gado tsobuwar kwaryar da take ajiya a ciki ta bude ta dauko wani abu mai kama da laya tana dubawa, sai jin zafin tai yana shiga har cikin kanta, kan ta ankaro ta soma ganin daki na juya mata sai zafin ya game ilahirin jikinta, can cikin kanta ta soma jin wasu muryoyi na kiranta duk da bata san inda kiran ke fitowa ba amman sai son tafiya take. Da sauri ta fito waje ta nufi bandaki ta warware zaren ta daga yar tsokar marar kyau ganin a sama ta wurga iya karfinta, a maimakon ta fadi kasa ko ta fada wani guri sai ta zama yar tantaba yar karama tai sama sosai zuwa ga mai ita. 

Daga ita sai ire-irenta suke iya ganin kurwar da ta kakareta ci. 

 Masai ta bude ta jefar da zaren ta fito tana jin wata rahama na sauko mata.


‘Lallai wannan kurwa ba ta ci ba ce’


Ta fada a ranta, a fili kuma maganin da Inna ta aje gaban Fadime take kallo, tana ganin Inna ta shige daki tai saurin isa gaban Fadime ta saka hannunta tana taba ganin, ba karamin dadi ta ji ba na samun sa'ar lalata aikinsa, daman can idan maye ya taba magani baya aiki komai aikinsa kuwa musamman idan na maganin mayu ne. 


“Sha za ki yi Fulani?”


“Eh maganin mayu ne Inna tace min”


“Ai wlh kam sun yi yawa yanzu ko'ina Allah dai ya kyauta”


Ya mike tsaye ta karasa gaban murhu ta gyara wutar, sannan ta koma dakinta ta dauko hijabi mai kaloli ta saka ta fice da sauri daga gidan. 

Bata yada zango a ko'ina ba sai gidan aminiyarta Lami, tana yi sallama Lami taja ta sukai cikin bukkarta dan kar kowa yaji abunda za su fada. 


“Lahiya kike kau Amo”


“Ina lahiya Lami, kurwa nan da nace zan sai da miki na sake ta yau?”


“Saboda me?”


“Wallahi ina zaune na fara jin wuta da azaba, daga gani gurin wani babban malami suka kaita, dan har kirana yake, da asiri ya tonu ai kara na sakar musu kurwar ƴa”


“Kai kiken Amo baki da juriya Wallahi, ai da kin gwada rikewa ki gani, ba a saurin saki fa yanzu, ko kuma ki sassauta mata daurin ta samu lahiya suna barin gurin mai magani ki kawo min ita na yanke shegiya”


“To nikam na sani, ke ai kika maida abun wasa da kin bani kudi da yanzu na siyar miki ita, kuma Wallahi mai garita, daurin da na mata har wani naso take”


“Aikin gama ya gama tun da kin sake, amman Wallahi da kin sha kudi, kuma irin wannan cikin ruwa zaki ajenta saboda mai kitse kin san bata son zafi in dai ba yankawa za ayi ba, saboda gudun irin haka, kila kin aje ta guri mai zafi azaba ta yi ma macce yawa dole aje neman magani”


“Aa Wallahi cikin kwarya na aje ta, ni yanzu damuwa ta Fulani ce, an cire mata wuta?”


Lami ta rike baki. 


“Dazun aka kawo min labari wai anganta da kan maciji”


A nan Amo ta kwashe labarin duk abunda ya faru ta fada mata. 


“To ai ba gajiya ake ba, ki sake aika mata wutar idan kuma kika samu sa'a ki kame kurwar daddake mata kai hankali ya juye”


“Ai in bata ciwo gareni ba zata mutu, dan na samo mata wani miji mai kashe mata, ance duk mace da ta aureshi sai ta mutu ina tunanin shi ma maitar yake amman ta sayarwa dan ance kudi gareshi sosai, kin san masu saidawa sun fi arziki ba kamar mu ba”


“A ina? Kuma?”


A nan bata kowaye amiyar ta ta komai ba.


“Bari na yi sauri na koma na bar girki kan wuta”


“To ko kam kar Malam Jaure ya dawo ya fara nemanki, bari sai dare mu hade gurin rawa”


“A a yau ba ni fita tun da dakina yake, sai jibi”


Daga haka tai mata sallama ta dawo gidan a guje, ta shige cikin daki ta cire hijabin ta aje ta fito waje tana kallon kofin maganin da Fadime ta sha magani da shi. ta san ta sha ne kawai amman ba zai mata aiki ba tun da saka masa hannu. 


Bayan sallah magariba Bappa ya shigo shi da wani abokinsa Malam Isuhu Inna ta shimfida musu tabarma aka kira Fadime ta fito daga bukkar Inna bayan ta kare sallah magariba ta zauna saman tabarmar. 


“Kina da alwala?”


“Eh yanzu nai sallah”


Ta amsa tana kallon wata doguwar takadar da Malam Isuhu yake budewa.


“To Malam Bissimillah”


Malam Isuhu ya matso kusa da ita ya haska fitilarsa yana ya fara karanta mata ayoyin kona aljanu, tun da aka fara karatun Fadime take zaune guri daya tana saurare, idan ya karanta ya karanta sai yace 


“Wanene?”


Sai Fadime tace 


“Ni ce Fulani”


Tun yana yi yana tsayawa ya tambaye ta har ya gaji ya daina sai karatun kawai yake mata, da Fadime ta ga abun nasa ba mai karewa ba ne sai ta fara lankwashewa tana burkice ido kamar da gaske aljannu ne suka zo. 


“Muna aljanu gamu nan mun zo, mu ne”


“Ku suwa?”


“Mu aljanu”


“Miye sunanka?”


Ta dan yi shiru tana tunanin sunan da zata fada, can kuma ta fadi sunan Bappa. 


“Sunana Sama'ila”


“Miyasa kika shiga jikinta?”


Mutumen ya tambaya. 


“Saboda.....saboda... Muna son mu bada magani”


“A ina kuka hadu da ita”


“A daji..... ”


“To ku fita daga jikinta ko na kona ku”


“Ba zamu fita ba”


Ta fada tana ta mulmula a kasa kamar wata mai aljanun gaske, sai mutumen ya cigaba da karatunsa da nufin kona su, Bappa kuma ya shiga dakinsa ya dauko bulalar dorina ya shada mata, a take tai saurin tashi ta zuba da gudu zuwa wajen shanun da suke gidan. 


“Mun fita ba zamu sake dawowa ba”


Malamin yace. 


“Karya suke haka suke idan suka ga ana kona su”


Bappa ya bita har can ya zuba nata wata bulalar yana fadin


“Ku fita daga jikinta yanzu nan”


“Bappa sun fita tun dazun ni ce dan Allah ka tsaya”


Ina Bappa be yarda Fadime bace sai auna mata bulalar yake, tun tana fadin sun tafi har ta fara kiran Inna ta ceceta.


“Inna nice Wallahi ni ce dan Allah ki zo kar Bapppa ya akashe ni”


Inna ta zo da sauri ta rike bulalar tana fadin. 


“Sun fa tafi Fulani ce kake duka”


Sai a lokacin Bappa ya sarara mata bayan ta sha buloli da sunan aljannu. 





HAJIYA BABBA POV. 


Tsananin mamakin da yake fuskarta ya wuce misali, ta san Jarma ba zai mata karya ba, amman sam bata gane inda labarinsa ya dosa ba, Fadime Falmata Sardauna za su watse musu shiri?


“Wacace Fadime?”


Ta tambaya a fili tana kallon Jarma. 


“Ni ma abunda na gagara sani kenan, balle kuma Falmata da Sardauna, amman ni ina ganin kamar Sardauna na Yola yake nufi” 


“Sardauna ai yana da nisa da Sarautar nan, balle nai tunanin haka, idan na shi ne to su waye Falmata da Fadime?”


“Abun da na gagara sani kenan, kuma na yi wauta ko da yake tsoro ne a ya hanani tambayar ko me suke nufi, kuma ita Ammy ai Zainab ne sunanta ba Fatima ba balle nai tunanin ko ita ce....”


Be karasa ba Hajiya ta daga masa hannu alamar yai shiru sai dai har lokacin mamaki be bar fuskarta ba. Kwankwasar dakin da ake take saurari kamin ta ji muryar Nana. 


“Hajiya Hajiya....”


“Daughter ke ce?”


“Ni ce”


Hajiya ta tashi da kanta ta bude mata dakin tana kokarin kirkiro murmushi. 


“Daughter na ya aka yi?”


Ta tambaya tana rike da kofar dan bata son Nana ta hango Jarma a dakinta, duk da ta san ya saba shigowa sai dai rufe dakin da makulli da akai zai saka shakku a zuciya. 


“Wayarki za ki bani sai na kira wanda na ce miki ina son ya zama driver na”


“To tsaya nan bari na dauko miki”


Hajiya ta rufe kofar ta dawo ta dauki wayar sannan ta koma gurin kofar ta bude ta mika mata. 


“Tafi da ita can idan kin gama ki bawa Karima ta aje min”


“Okay”


Ta karba ta juya cike da jindadi, dan ta san Number AA na cikin wayar Hajiya, saboda ta ari wayar shi ta kira Hajiya da line, duk kuwa da bata da tabbacin number tana nan har yanzu ko an goge, ba dan zata iya ganewa number ba sai dan ta gwada sa'arta.


Bayan ta wuce Hajiya ta sake rufe dakin ta dawo ta zauna. Sai Jarma ya rage murya yace. 


“Ashe Nana ta fara dan hali?”


Hajiya ta yi murmushi. 


“Ai har abun da yafi dan hali sai Nana ta yi, matukar ina raye  ƴaƴan Ammy ba za su taba albarka ba Wallahi har a abada kuwa, yadda take son ganin bakincikina ita sai na ga nata kukan”


Ta karasa tana wane kashe ido zuciyarta cike da kiyayyar Ammy. 


No comments

Powered by Blogger.