Fulani 14


 *14*


Gaba daya ta koma kamar ba ita ba, daman a duk lokacin da suka zo gidan Waziri haka take zama wata saliha, bata sakewa har sai sun bar gida, wannan karon kuma zuwan gaba daya tai dan bata san ranar komawarta ba. 

Gashi nan tana jinta kamar tana gidan yari, domin yaran Baba Waziri basa fita ko'ina daga makaranta sai gida sai kuma wata hidimar idan ta tashi, gara ma a can masarautar tana iya yin karyar zuwa wani guri Ammy ta barta ko ta samu Sirleem ya fita da ita ko Hajiya Karama, nan fa? Gaba ta kasa sakewa ko breakfast bata fitowa ayi da ita kamar yadda aka saba yi tare da kowa sai ta shige cikin daki ta zauna ita kadai sai idan an kawo mata nata abun karyarwa haka ma da rana, gashi nan dole ne taje makaranta kuma school bus din da bata so ce take kai ta kullum ta dauko ta. 

 Gaba daya ta rasa yadda za tai, wata zuciyar na raya mata ta ari wayar wani ta kira Hajiya Babba ta fada mata dan ita kadai ta ke da tabbacin zata taimaka mata ta cireta daga wannan kangin. 


 Misalin karfe biyu da yan mintuna Motar Hajiya Karama ta shigo gidan, ta window Nana ta leka tana hangota ta sauka saman gadon da sauri ta fita a guje har tile din na kokarin zameta ta fadi. Zainab na kokari rufe motarta sai ga Nana ta fito da gudu ta zo ta rumgume ta, Zainab ta saka dariya tana cire gilashin idonta. 


“You miss us right”


“Yes Hajiya Karama ki ce Ya Shattima am sorry kuma zan ce ma Ammy sorry pls ya maida ni gida”


Zainab ta taba kumatunta tana mata dariya. 


“Shattima ma baya garin nan, ya koma aiki”


“Ni bana son nan Hajiya dan Allah”


“Dukanki suke?”


“No”


“Tau why? Kanen mahaifinki ne Nana yayansa kuma yan'uwanki ne, ni kaina idan na gaji da zaman gidan can wani lokacin a nan nake zuwa na kwana biyu sannan na koma, a gida nan ma ina da gata komai kike so za ayi miki, komai kike so shi zaki ci to miye matsalar ki Nana?”


“Ba a zuwa ko'ina kuma dole sai an je school both islamiya and boko”


Zainab ta rika fuskarta. 


“Can baya na san kina son makaranta yanzu miyasa ba ki so?”


“Ni dai bana so kuma, kuma.... Ni bana son na gama bokon saboda kar na auri Sirleem”


Kyalkyalewa Zainab tai da dariya. 


“Saboda ba ki son Sirleem sai ki lalata karatunki? To idan ba ki son zuwa makaranta ai sai ya ce ayi muku auren da wuri, Nana ki kwantar da hankalinki idan ba ki son babu dole ki bada lokaci kawai zan yi supporting din ki na hana auren Sirleem”


Nana ta zare ido. 


“Har da Hajiya Babba ma za ta goya min baya ko? Shikenan ma na huta”


“Ya za ayi Hajiya ta goyi bayanki, ki ki auren danta na cikinta? Ke har yanzu ba ki da wayo?”


“Ai tana so na”


“Amman ta fi son danta dake, ki daina wannan tunanin, yanzu dai zuwa nai na ganki kuma na dauke ki muje mu sha ice cream dan san kina so”


“Yes yes, amman kina shiga cikin gidan nan Hajiya Maryam ba zata bari ba, zata ce Baba Waziri yace kar na je ko'ina”


“Okay je ki dauko veil ko hula mu je”


Da gudu Nana ta juya ta koma dakinta dake cikin gidan ta dauko wani karamin veil ta saka a kanta, ko da ta fito har Zainab ta yi reverse ta bude nata front seat. Da sauri ta shiga Zainab ta fara tukin tana kai hannunta ta dauki kwakwarda ke gefenta ta ci sai kuma ta dauko wata ta mikawa Nana, ita kuma ta karba ta fara ci, tafiyar ta su ba tai nisa ba Nana ta hango AA tsaye kusa da wani gida mai karamar kofa yana waya.


“Hajiya tsaya tsaya tsaya....”


Da sauri Zainab ta taka burki ganin yadda Nana ke kokarin tsayar da ita kamar ta ga wani abu. Sai da Zainab ta faka motar sannan ta bude ta fita, AA na hangota ya yanke wayar da yake tana kallonta gabansa sai faduwa yake, wata zuciyar na raya masa cewar ya gudu, ko kuma ya shige cikin gidan ya boya. Wata kuma na ce masa ya daure, dan murmushi da Shaukin da ya hango a fuskar Nana yasa ya dan ji kwarin guiwar tsayawar. 


“AA AA”


Ta fada tana jin kamar ta rumgume shi. Shi kuma ya kasa amsawa sai kallon motar da ta fito yake, sai da Zainab ta sauke gilashin motar ya ga macece sannan hankalinsa ya dan kwanta. 


“Me kika zo yi nan? Waya ce miki ina nan? Biyoni kika yi?”


“A a ba mu fita ni da Hajiya Karama shine na hango ka na ce ta tsaya”


Ta fada tana kara matsawa kusa da shi kamar ta rumgume shi wani irin shauki take ji idan ta ganshi. 


“Nan ne unguwar ku?”


Ya tambaya yana zaro ido wata zuciyar na ce masa ashe baka tsira ba. 


“A a nan gidan aka kawo nan dai, wai bana jin magana shine za min horo”


“Kamar ya?”


“Wai saboda gidan ba a zuwa ko'ina kuma dole aje school, shiyasa aka kawo nan”


“Wane gida?”


“Wacan gidan mai Ash da white paint”


Kai tsaye ya san gidan Waziri take nufi, baki sake ya ce. 


“Gidan Waziri?”


Ta gyada masa kai. 


“Ya kike da shi?”


Shiru tai tana kallonsa sai kuma ta fara dariya. 


“Ina ruwanka kai me kake a unguwar?”


Ya dan shafa kansa yana tunanin karyar da zai mata. 


“Na zo gaishe su ne, ko zan dan samu wani abu kudi na ke nema, ba ki da wani abu nan ki ba ni?”


“Ba ni da kudi amman bari na ce Hajiya.... ”


Yayi saurin dakatar da ita. 


“No no no tsoro nake kar a kama ni, na sani ko kin fadi cewar ni kika bawa 20k din ki kuma ni na jefar da ke akan babur”


Ta fara dariya. 


“Wallahi ban fada ba, ai idan na fada Ammy zata min fada ne tace ashe bana zuwa school, cewa nai driver na ne”


A nan ta fada mishi karyar da tai musu da kuma yadda ta isa gida a ranar. Sosai AA ya jidadin haka ta rufa mishi asiri yanzu kan hankalinsa ya kwanta.


“Bari na karbo maka kudin”


Ta juya ta koma gurin Motar Zainab ta lekar da kanta.


“Hajiya kina da 10k ko 20k ki ara min, ko ma dai ki ba ni”


“Me za ki yi? ”


“Shi zan bawa”


“Waye shi?”


“Malamin mu ne na makarantar islamiya, na masa alkawarin ne shiyasa”


“Karbo account dinsa a tura bani da cash”


Ta juyo da sauri ta zo ta fada masa, sai ya rubuta mata account din a wayarsa ya mika mata yana fadin. 


“Gt bank”


Sai da Zainab ta kare masa kallo sannan tai masa transfer 10k ta mika mata wayar.


“Yi sauri mu je”


“A a na fasa zuwan ki tafi kawai”


“Saboda?”


“Ni dai na fasa dan Allah ki tafi, Wallahi ba guduwa zan yi ba, zan yi magana da shi kawai na koma gida you have my word”


“Promise?”


“I promise”


Ta fada tana daga hannu alamar ta dauki alkawarin. 


“Okay take care of yourself, kuma kin san kika dade har aka fito aka ganki babu ruwana zan ce ni ban ma zo gidan ba”


“Na zan yi haka ba i love you”


Zainab ta yi murmushi tana daga gilashin motarta, sai da ta wuce sannan Nana ta dawo inda yake ta mika masa wayar. 


“Ban san ko nawa ta saka maka ba”


Ya karbi wayar ya duba alert din da ya shigo na 10k.


“Dubu goma ne thank you so much Allah ya biyaki”


“To zaka ara min na kira Hajiyata?”


“Yes ba dai tona min asiri zaki yi ba ai”


“Aa”


Ta karba wayar ta saka number Hajiya Babba ta aika mata kira, sai da ta jera mata miss calls kusan uku a ana hudu aka daga cikin tsawa.


“Waye wannan?”


“Hajiya ni ce fa Nana”


Hajiya ta sake fuska jin Nana. 


“Daughter da sabowar number?”


“Eh to ba Baba Waziri ya karbe min waya ba, kuma gashi nan Ya Shattima ya dawo da ni gidan wai bana jin magana, Hajiya dan Allah ki zo ki dauke ni yau yanzu”


Ta fashe da kuka.


“Wai me yake damun mutanen nan ne? Gani nan zuwa yanzu”


“To sai kin zo Hajiya yanzu pls ko minti biyu kar ayi”


“Yanzu daughter”


Ta katse wayar ta mikawa AA.


“Wa kika kira?”


“Step mom dina ce ita ai tana so na, yanzu za ka ga ta zo ta dauke ni”


Ya saka wayar aljihu yana kallonta. 


“Kin rame”


“To ina ruwanka?”


Ta watsa mishi harara sai kuma tai yar dariya. 


“Yanzu tana zuwa zan ce ina son ta daukar min kai driver”


Ya kalleta da sauri. 


“Kuma zata yarda?”


“Eh so na take sosai”


“Bari na koma kar ta zo ta gan ni a hanya”


Ta daga mishi hannu. 


“Bye”


“Bye”


Ya amsata yana binta da kallo har ta isa gaban gate din gidan Waziri ta shige. Ba tai minti talatin da shiga gidan ba sai ga Hajiya Babba ta iso tare da driver ta furka a murtuke kamar da gaske ranta a bacen yake. Nana na hangota ta windows ta fara tsalle tana rawa tana jindadi. 

Kai tsaye ta wuce bangaren Uwargidan bata biya inda kawarta kuma amiyarta Talatu ba, amasama ta gaisa da matar kanen mijin nata Hajiya Maryam daman can ba sa shan inuwa daya sannan tace. “Zuwa nai na tafi da Nana”


Hajiya Maryam ta kalleta.


“Nana kuma? Shattima ne ya kawo ta nan ta kwana biyu”


Hajiya Balki ta yi mata wani kallo.


“Ikon Allah kina nuna min ban isa da Nana ba kenan? Ko kuma kina nuna min ita din ba yata ba ce? Ban gane ba?”


“A a Wallahi ba wannan, kawai dai ance ana son ta kwana biyu nan ne shiyasa na fada miki”


“To bata kwana biyu ba, Nana ba ta kusa sati a gidan nan ba?”


“Ba wai ana nufi kwan nan biyu ba, kwana biyu na malam bahaushe ake magana Hajiya”


“Wai wacece ke da kike fada min wannan maganar? Banza a banza kashi a masai? Shattima ya fi ni iko da Nana ne ko kuma me? Ke kina kara nunawa Ammy wannan bakin abun na ki na wani yan uba, mu yaran gidan mu ba su san wannan ba, kowata da yai nan ma ai bata mata tarbiya za ayi”


Hajiya Maryam ta yi dariya


“Hajiya kenan, ke kuma abun da kike gyara mata tarbiya ne? Shattima ai ya san da ke a gidan amman ya dauke ta ya kawo ta gurin kanen ubanta kuma be ce a kawo ta ko'ina ba sai a nan bangarena, har waya sai da ya daga ya kirani yace na kula masa da Nana, kin ga kuwa dan gyara aka kawo ta ba baci ba”


“Eh Lallai Hajiya Maryam, ni kike fadawa magana haka? Yanzu da Ammy ce za ki mata haka? A a sai ni da nake kishiyarta ko? Ba komai komai yana da lokaci ai wata rana sai labari, Ke Zarah tashi ki kira min Nana”


Hajiya Balki ta karasa tana kallon karamar yar Hajiya Maryam. Zarah ta tashi ta fita daga falon zuwa bangaren da dakunansu suke, ta kira Nana suka fito tare, Hajiya na ganinta ta mike tsaye.


“Idan Waziri ya zo ki ce masa na dauki yata, idan kuma ban isa da ita ba, sai ya zo ya dauko ta”


Haka ta saka Nana na gaba suka fice daga falon, tun kan su karaso driver ya bude musu baya, Hajiya ta shiga Nana ma ta zagaya ta shiga ko tsinke bata dauka ba a gidan. Sai da direban yaja motar suka fita daga gidan sannan Nana ta rungume Hajiya a cikin motar.


“Na gode Hajiya”


Hajiya ta yi murmushi. 


“Anything for my daughter”


“Ke ba kamar Ammy kike ba kina so na sosai kuma kina min duk abunda nake so i love you so much Hajiya”


“I love you too Daughter”


“Kuma Hajiya ina son sabon driver, bana son school bus tana kai ni makaranta, shi zai rika kai ni islamiya da boko ma, tun da can na fadawa Ammy ta dauka min sabon driver ta ki”


“Karki damu zan daukar miki sabon driver, duk abunda kike so shi zan miki daughter zan saka a samo sabon driver ya rika kai duk inda kike so”


Ta dago da sauri tana kallon Hajiya cikin wani irin jindadi marar misaltuwa. 


“Akwai wanda yai min magana Hajiya, yace zai iya kuma yana so”


“To ki nemo shi daga gobe zai fara tukaki ki bashi keys din motar kuma ki fada masa yadda ake biyan wacan driver ni zan din ga biyansa every month”


Da sauri Nana ta kara rumgume ta ta kwanta jikinta tana jin wani son ta fiye da Ammy. ***   ***   ***

Kofar wani gidan ta kwankwasa aka bude mata, matashiyar matar ta leko. 


“Hajiya kuna siyen danyen man shanu?”


“A a muna da Allah bada sa'a”


“To amin”


Ta amsa tana lasar bakinta, a nan ta janyo kurwarta ta warware zanenta ta saka yar tsokar ta kulle, ta maida zanen ta daure ta yi saurin bari wajen har da hadawa da gudun, duk da bata matsi kurwar ba ta ta ga matar tana da aljanu kuma za su iya tashi, ko da yake na Amo sun fi na matar karfi.

  Cikin unguwar Nasara ta shigo gidan data saba kawo musu danyen manshanu suna siye, tana buga gate din mai gadin ya bude mata, ta gaishe shi da far'arta tana kallon kurwarsa dake kasan kafafuwansa. 

 Nisa kai tai cikin gidan har ta isa bakin kofar falon da ke bude ta zauna kasa tana sauraren hirar da Hajiyar ke yi da kanenta yaranta su ka zo da gudu suka rumgume Amo. 


“Oyoyo Amo ta zo Oyoyo”


Ta muku ya zaunar da su saman kafafuwanta tana dariya tana musu wasa. “Shi fa be ma san da maganar ba, kuma ita Ammy tace kar na bari ya ji sai komai ya kama”


“To sai matsalar wannan abun da ke tare da shi”


“To ai ni ma shine, kar a aura masa yar mutane ta mutu, shi kansa yanzu abun da yake tsoro kenan shiyasa ya cire ransa daga auren ma”


“Sai dai idan ba za a fada ba”


“Idan kuma ba a fada ba, ai an cutar da yar mutane, kuma ita yanzu Ammy tace ta damka min ragamar komai, wai ko a nan Katsina din ne su zauna tukunan”


“Ai kam samun mata yanzu ga Shattima aiki ne, ga kudi ga kyau ga ilmi ga sarauta amman fa ana tsoron mutuwa”


Ra'ees ya shafa kansa cike da damuwa dan wannan aikin da Ammy ta bashi ba karamin aiki ba ne. Karamar yar Hajiyar ta shigo tana tsalle. 


“Momy ga Amo can ta zo”


“To yar gidan Amo”


Ta fada tana dariya sannan ta mike tsaye ta fito waje suka gaisa da Amo. Sai da ta bude manshanun suka fara ciki ta siye wanda zata siye sannan Amo tace. 


“Hajiya na ji kuna neman mata”


Hajiya ta yi dariya.


“Muna nema kan amman ai shi mai son matar ne da matsala”


A nan Hajiya ta labarta mata waye Shattima. Sai Amo tace. 


“Kai duk canfi ne Hajiya, ku bar wannan maganar ma, karku sake fadin haka abun da Allah ya kawo ai shi yake kasancewa, ni da za ku yi shiru da bakinku akwai yar da nake riko sai a bashi ita, indai za a saka ni gaba ayi komai”


“Aiko da kin kyauta mana, zancen fadin haka daga yanxu ma mun daina”


Amo ta yi dariya tana kallon sabon cikin Hajiya take dauke da shi, da be wuce sati biyu ba, amman ita tana ganinsa da idonta hudu na maita. A nan ta fada musu addirenshi da wanda za a nema idan aje. 


“Indai da gaske suke suka je Malam zai bashi aurenta, dan shi kanshi neman mijin da zai aureta yake, shekara goma sha 16 babu wanda ya taba tambayar amrenta”


Har lokacin tana kallon cikin, wata zuciyar na ce mata ta taba wata na cewa ta bari sai ya kara kwari. Bayan sun gama yanke komai ta siye manshanun ta sallame ta taso tana ta jindadin indai ta zama jagaba ita ce zata samu kudin komai ai. 
FADIME POV.


A yadda ta kabartawa Inna labarin cewa tai wani ta ji a jikinta akwai wata wuta tana binta kuma wutar maita ce, bata son ta fadawa Inna gaskiya dan kar ta mata fada ko kuma ta hana ta zuwa gurin kiwon. 


“Dubi kike ne da kika fara ne Fulani?”


“Minene Dubi Inna?”


“Bokaye suke yinsa su duba hannun mutu ko idonsa su fada masa abu, ana basu kudi”


Gyada kai Fulani tai tana dariya a ranta tana tunanin ta samu sana'a. 


“To yanzu idan nai miki Inna za ki ba ni kudi ko?”


Inna ta watsa mata harara.


“Bari Malam ya ji da wannan dabi'ar sai ya zaneki kin san dai babanki malami ne ko?”


‘To ni ina ruwana da wata malantarshi’


Ta fada a ranta tana turo baki gaba, a dayan bangaren kuma tana ayyana irin kudin da zata samu idan tai wannan sana'ar. Waya sani ma ko aljani ne ya zo ya taimaka mata? 


Bayan kwana biyu Inna da Fadime na zauna waje, Amo ta fito daga bukkatar tana fadin. 


“Inna Fadime na yi ma Fadime miji”


Kamin Inna tace komai Fadime ta nufe ta da far'a tana dariya, kwatakwata a rayuwarta babu wanda ya taba zuwa yace yana sonta sai yau. 


“Da gaske? Ina miji?”


“Ke arrr Fulani babu kunya”


Inna ta fada cike da jin haushin yadda Fadime take rawar jiki. Fadime ta rufe ido ta dawo da gudu ta rufe kanta jikin Inna sai a lokacin take jin kunya wai. 

Amo ta zauna tana dariya ta labartawa Inna.


“A can bunni inda nake kai mansanu, samarayin gidan abokaine yake neman mata nace ga Fadime nan tun ita yar boko ce kuma tana da kyau ba kamar hajjo ba”


Inna ta jidadi sosai cikin ranta duk da tasan Amo ba zata kawo mata abun alheri ba, amman jin yau ana son yarta yasa ta jidadi abun da ba a taba ba ko da wasa. 


“Ai na ce su zo su yi magana da Malam indai da gaske suke.”


Amo ta fada sai Fadime ta ce


“Allah yasa su zo Allah ya kawo su lafiya, yana da kyau?”


Inna ta rafka uban tagumi tana kallonta, Amo kuma ta saka dariya domin ita dadin rashin kunyar da Fadime take, take ji domin ba al'adar fulani ba ce. Ganin yadda Inna take hararta yasa ta fita daga gidan da gudu tana dariya, kai tsaye ta nufi gidansu Ma'u ta fada labari, tana isa ta tarardar Ma'u na yi ma wasu mutane kwatancen wani gari da ke yamma da su. Mutum uku ne da wata dalleliyar mota daya na tuki daya a baya daya kuma a mazaunin gaba. Gurin madubin motar Fadime ta je tana duba fuskarta kamin ta fara shafa motar, wanda hakan ya ba Jarma tsoro yana ganin kamar lekensa take ta ga ko waye ne, kamin a gama musu kwatance su kama hanya duk ya takura. 


“Kiyaye....”


Ta fada tana daga musu hannu kamar ta san su, ta bi motar da kallo sai da ta daina hangota sannan ta talkamo kawarta ta fara bata labari. ***    ***     ***


Jarma yaja tsaki cike da jin haushi. 


“Wai yanzu kai Saminu ka san baka san gari ba kasa mu ka kamo hanya haka?

Saminu dake gaban mota ya juyo yana kallon abokinsa. 


“A a fa na san hanya, garin da shi jafaru yake zuwa ci rani ne ban sani ba, amman muna isa muka ce gidan liman ance babu wanda be san shi ba a garin, ka ga sai mu tambayi Jafarun sai ya shige mana gaba mu shiga cikin garin tun da shi ya san yan garin da yawa kuma yana yi wa mutane jagoranci amman mu kai tsaye ai ba za mu shiga garin ba”


Jarma be koma cewa komai ba, har suka isa garin Dan burki, suna tambayar gidan liman aka nuna musu, a gidansa suka sauka yai musu tarbar ban girma duk da be san su sai dan karamci irin na mutanen kauye. Sai da suka huta sannan aka kira musu Jafaru suka kama hanyar garin, ba Saminu ba ko Jafaru da ya saba zuwa garin sai da tsorata da suka kusa isa balle kuma Jarma danke jin kamar fitsari za su zubo masa ganin yadda ake ta yankan daji kamar ba a dubiya ba. 


“Ai dai ba za su mana komai ba ko Jafaru?”


“Babu abun da za su mana tun da ina tare da ku, amman ba za mu shiga garin da motar nan ba”


Cikin manyan duwatsu suka ratsa har suka isa bakin kofar gate din garin da ba zaka iya fadar da me kai ta ba, itace ko katakaye ko kafara katuwar kofa ce mai tsayi sosai ga masu gadin kofar sanye da warki sai kallon su motar su Jarma suke. Jafaru ne ya fita yaje yai magana da su sannan ta dago musu hannu suka fito suka karasa inda yake. Shine gaba suna biye har suka shiga cikin magarin, sannan aka kawo musu motar jaki suka hau aka nisa cikin garin da su. Sai da aka isar da su gurin sarki suka gaishe shi ya san da zuwansu sannan aka wuce da su gurin boka, duk abunda ake Jarma be wani motsin kirki ko kallonsu be son yi gudun kar yai laifi, shi a rayuwarsa be tana ganin mutane haka ba sai yau, you ashe akwai irin mutanen nan har yanzu. Amman kam garin akwai kyau ga manyan duwatsu da itatuwa ga kuma ruwa ta ko'ina gwanin burgewa kowa sai hada hadarsa yake.

A nan ma sai da Jafaru ya shiga yai magana da su sannan akai musu iso, sun san Jafaru sosai dan ya saba kawo musu mutane kala kala kuma yana cikin irin mutane da suke bawa kudi ayi musu sako a burni ko daga wani gari zuwa wani gari. 

  A saman agalami suka samu mutanen mai kama da munanan tsofi kansa da aski an masa tas idonsa kamar garwashin wuta, kana ganinsa ka san aka gawurtaccin ifiritai a tare da shi, yawanci mutane garin suna jin yaren hausa da fulatanci duk da kasancewar ba su cika mu'amala da kowa ba, sai wanda suka yarda da shi, amman ban da wannan baya jin ko wane yare sai na su. Sai dai a kusa da shi akwai mai fassara musu komai. 

 Suna zama ya fara karaton musu abun da ya kawo su. 


“Ka zo nan saboda a kawarda dan'uwanka, da matarsa da dansa ka hau sarauta, kana son a kashe Shattima da Talba da sannan a nakkasa Zainabu da Balki”


“Wallahi haka ne”


Jarma ya fada yana kara gyara zamansa mamaki duk ya cika shi, ta dayan bangaren kuma yana jin kunyar jin sirrinsa da abokinsa Saminu yai. 


“To ga tafiya nan da ba dawowa, ga Fadime nan ga Falmata, ga Sardauna su za su lalata muku shiri”


Jarma ya nisa a cikin tunani yana ta neman gano waye Fadime waye Falmata? Kuma waye Sardauna? Sardauna na na Yola ko kuma wani sardauna nan dabam? 


Wata kwarya ya dauko mai ruwa ta aje gaban Jarma, ya fara karanta wasu abubuwa sai ga Mai Martaba ya bayyana a cikin ruwa, wani irin zabura Jarma yai ya matsa baya. 


“A harbe maka shi? Yanzu nan za mu yi masa harbin kanko”


Jikin Jarma sai rawa yake yayi sauri cewa.


“Aa shi ai mun samu nasarar kwantar da shi, yanzu Shattima muke son a fara harbewa tukuna”


Mutumen ya fara karance karance yana kiran sunan Shatttima amman ya ki ya bayyana a cikin ruwan. Tun yana daukar abun da wasa har ya fara yi da gaske Shattima ya ki bayyana a cikin ruwan sai sunansa. 


“Akwai abun da ke kare shi, lallai shi ma be tsaya haka nan ba”


“Yanzu ba a iya harbe shi kenan?”


“Za a iya amman idan akai be same shi ba, zai dawo gurinka”


Jarma ya mike tsaye yana lalaba jikinsa. 


“A a bari dai sai mun yi shawara tukuna”


“Ba a shawara a nan ku tafi can gari”


Jarma ya mike tsaye da sauri ta ciro kudin da za su kai dubu 30k ya aje musu, sai ya girgiza masa kai mutumen ya fassara masa. 


“Kudin siyen dabba ake ba mu”


Jarma ya karo 50k ya aje musu sannan suka juya jikinsa sai rawa yake. Duk shige shigensa be tana shiga irin wannan gurin ba, ba tana ganin tsafi kararsa irin yau ba. 

No comments

Powered by Blogger.