Bakar Inuwa 78

 


*_Episode 78_*

..........“Tabbas dole Hannah ta mutu kafin a miƙata kotu”.

    Forma first lady ta faɗa tana duban su Alhaji Yaro glass dake tare da ita harma da god fathers nasu a yau. Mr MM da duk yake a firgice yay saurin faɗin, “Ina bayanki your excellency maa”.

       Gaba ɗaya falon dubansu suka maida ga Alhaji Yaro glass da tunda ya shigo baice komai ba, sai ma uban tagumi daya rafka. Numfashi yaja mai ƙarfi ganin sun dawo da kallonsu garesa alamar amsa suke nema. Yaɗan ɗage kafaɗa da yarfa hannuwa. “Ni a gareni babu matsala, da nasan ma wannan ranar zata zo da dakaina zan kashe Hannah tun kafin zuwanta. Dan tun randa case ɗin kuku ya shigo ya kamata a ɗauka wannan matakin, amma sai muka ɗauka hakan ba komai ba. Sai dai ku sani ba Hannah ce kawai zata mutu ba harda Kuku, dan kuwa Hannah da Bushira kuku ya sani ba Hannah kawai ba”.

        “Amma kasan shi ɗin ɗanane jinina ko?”.

    Cewar Forma first lady Bushira hamada a harzuƙe.

       “Nima ai Hannah matata ce, cewa a kasheta bashike nufin bana sonta ba. Sannan idan baku manta ba matar Ramadhan jinin Hannah ce, amma da akace zata iya mutuwa a cikin shirinmu batai jayyya ba, ashe kuwa indai nasara muke bukata dolene mu ɗanɗani ɗacin rashin jinanannmu koda kuwa ƴaƴan da muka haifane”.

     A take kowa ya goya bayan maganar Alhaji Yaro glass. Hakan yasa Hajiya Bushira hamada yin shiru. Oga kwata-kwata da baice komai ba sai da duk suka gama hayaniyarsu sannan yay gyaran murya. Dukansu hankali suka maida garesa.

      “Idan har ta kisan wane da wane ne zamubi ta hanyar rufe sirrikanmu mutane da yawa zasu mutu a wannan gaɓar. Dan haka ba shine mafita ba, babbar mafita a garemu yanzu harin maƙiyinmu kai tsaye. Ramadhan shine kawai zamu hara kai tsaye mu sami nasarar daƙile duk wata damuwarmu. Amma dan mun kashe su Hannah kamar mun kashe macijine bamu datse kansa ba, domin kuwa kisan nasu tamƙar buɗe hanyar da masu bincike suke nemace kai tsaye muka bayar.

     A take ɗakin taron ya ɗauka kananun hayaniya. Dan kuwa zantukan shugaba sun fargar dasu abinda basu hango a farko ba. Dan haka a daren yau basai gobe ba Ramadhan zai baƙunci lahira..... 


       “Idan shi bai baƙunceta ba, ku zaku baƙunceta ai”.  Cewar Alhaji Balarabe Andu daya daɗe tare da su da fuska biyu. Alhaji Balarabe Andu tsohon jami'i ne da tun komawar tsohon shugaban kasa Usama D. Hamada mulki na biyu ya shigo jikinsu. Koda yake zamu iya cewa tun a mulkin farko ma yana tare da su, sai dai basu sakin jiki da shi har sai lokacin mulki na biyu da suka tabbatat yana tare da tafiyarsu. Tun usul ya shigo tawagarne akan binciken wani gagarumin ƙulli da akai a wancan mulkin, sun buga sun buga suka kasa gane kansa. Shine yay shigar burtu ya zama ɗaya daga cikinsu. Yaso barinsu bayan kammala mulkin Usama D. Hamada, sai dai ƙullin da suka fara akan daura Alhaji Hameed Taura a mulki ya sashi dakatawa. Duk abinda suke yana biye da su, hatta da ac da suka saka poison a ciki na gidan gwamnati yaso zama silar da zai sa a cire sai Raudha ta rigasa, amma da taimakonsa su bappi suka cire batare da suma sun sani ba. Ya cigaba da tattara bayanan sirri akansu batare da sun sani ba, kuma ko ayanzu da aketa faman kama musu yara duk da saka hanunsa a ciki....

     A firgice duk suke kallon Alhaji Balarabe Andu, dan wasunsu sun ɗauki abin wasa ne ko almara ko subutar baki,

      “Alhaji balarabe kasan mi kake faɗa kuwa?”. Cewar Alhaji Haladu Gwandu.

     Alhaji Balarabe yay wani murmushi tare da rausayar da kai gefe ya tafa hannayensa yana kallon Alhaji Haladu Gwandu batare da yace komai ba. A take jami'an tsaro suka shigo falon suka zagayesu su da makaman da suka tile a tsakkiyar falon wanda a yau ɗin nan aka iso da su ƙasar NAYA.....


         ★Cikin ƙanƙanin lokaci ƙasar NAYA da kewaye ta ɗauki sabon labari na kama waɗan nan manyan mutane da wasun su ko'a hasashen zuciya bata taɓa kawo zasu aikata abinda ake zarginsu da shi ba. Bakin ƴan siyasa ya buɗe ta ko'ina bakajin komai sai kace nace. Abinda ma ya takaice kace nacen tsayawa akan jam'iyya mai mulki kawai waɗan nan mutane gaba ɗayansu suna tarayya ne a cikin mabanbanta jam'iyyu. Hakan na nufin kenan dama ƴan siyasa da yawansu a bayan fage kanwunansu a haɗe yake a zahiri kuma suyita gwara kan talakawan ƙasa da sasu luguden laɓɓa batare da sun hankalta ba. (Ƴan uwa idan zamuyi soyayya muyita dan ALLAH kuma saisa-saisa. Hakama kiyayya muyita saisa-saisa kuma domin ALLAH musamman irin ta siyasa. ALLAH yasa mu cika da imani).


     A yinin wannan rana kawai hankalin al'ummar ƙasar NAYA ya dawo kan shugaban ƙasa Ramadhan. Aka dinga sanbarka a garesa da wanke laifukan da ake kallonsa da su. Yayinda wasu keta faman bankaɗe-bankaɗen abubuwanma da ba'asan da su ba sai yanzu.

      A wani fanin Raudha na farin ciki, wani fanin kuwa tana baƙin cikin kasancewar yayar mahaifiyarta cikin tawagar waɗannan azzalumai. Ga laulayin ciki mai wahala da take fama da shi a wannan karon. Ga karatunsu ya ɗau zafi dan suna lavel 3 ne. har zuwa yanzu kuma bata taɓa kuskuren nunama wani ita wacece ba. Abdull bada shi take zuwa makaranta ba. Gida ake barinsa wajen Mama Ladi. Dama Alhmdllhi yana ɗan takawa zuwa yanzun, damma haƙora na maidashi baya idan yay zazzaɓi. Bayyanar cikin nan na Raudha kuma yasa Anne zuwa ta ɗaukesa a gidan ma baki ɗaya ya koma Taura House yaye. Sudai basu da ikon cewa komai, amma gimbiya Su'adah taji haushi dan ta ƙullama ranta itama abinda akai mata na ƙwace Ramadhan saita kwace Abdull, sai gashi Anne ta sake mata kwaf ɗaya kafin ta farga ta ɗauke ita (🤣😂Bashin gaba lol).


★★________★★★________★★


           Rayuwa ta cigaba da shurawa su Alhaji Haladu Gwandu na cigaba da zama a tsare a gidan yari, a gefe kuma ana sauraren ƙararsu a kotuna mabanbanta saboda laifukan nasu sunzo daban-daban. Kowanne akwai babban laifin da yake shugabanta da ake tuhumarsa a kansa kai tsaye. Wanda sukai tarayya akai shine cin hanci da rashawa da shigo da makamai.


     Ɓangaren shugaban ƙasa kam zamuce abubuwa sun fara dai-daita, domin ɓarnakun da tashe-tashen hankali ya kawo su akebi ana gyarawa kafin a ɗora sauran ayyukan da aka fara. A gefe kuma ya sake samun kwanciyar hankalin kasancewa da matarsa abar sonsa da alfaharinsa ƴar darunsa kuma dake fama da ciki. A haka ALLAH ya sake saukar Raudha lafiya, a wannan karon kam da kanta ta haihu yaronta namiji again, shima yaci sunan Pa wato Basheer. Suna kiransa Alhaji ƙarami. Duk da Ramadhan yaso kar ai taron suna dan bai manta abinda ya faru ana Abdull ba su Bappi sukace sai anyi. Haka dai akayi taro mai kayatarwa anan ɗin ma Raudha ta cigaba da shayar da yaronta.

          Yankema su Alhaji Usama D. Hamada tsohon president hukunci dai-dai da abinda suka aikata yayi dai-dai da sake kaɗa tamburan siyasa. Dan hatta yunƙurin kisan Ramadhan da sukai tsautsayi ya koma kan Amnah ɗiyar Alhaji Haladu Gwandu sai da jami'in tsaro Balarabe ya fallasa. Wannan hukunci da aka yankema waɗannan azzalumai ya zama makamin campaign na Ramadhan a wannan lokaci, dan kuwa yanda abubuwa ke tafiya bama sai ance maka shine zaiyi nasara ba kowace alama ta nuna hakan. 

     Sai kuma wani babban abin farin ciki da Ramadhan ɗin ya aywatar a wannan lokaci shine hana bangar siyasa yin tasiri a ciki dabai na ƙasar NAYA. Duk ɗan siyasar da aka samu ya bama yara makamai ko kayan maye domin masa campaign ko makamancin hakan to takararsa ta ruguje bazaiyiba. Wannan al'amari shine ya saka ƴan siyasar shiga hankalinsu, matasan kuma dama mafiya yawansu sunda aikinyi wasu sabo dayine da kuma shegen kwaɗayi ke ingiza zukatansu.

      Alhmdllhi campaign ya wanzu cikin nutsuwa da burgewa, inda har akai aka gama babu wanda yaga matar shugaban ƙasa ko da a poster. Sai dai Ramadhan yasha fita da Abdull da Alhaji ƙarami da shima yake neman cika shekara guda da haihuwa. Zuwa yanzu mutane da yawa sun fahimci shugaban ƙasa Ramadhan baya ra'ayin matarsa a harkokin siyasa ne kawai, yana kishinta yana killace abarsa matsayin tashi shi kaɗai. Hakan ya matuƙar birege mutane, harma a wannan campaign ɗin wasu ƴan siyasar sukai koyi da hakan musamman ƴan takarkaru. 

      Dan hatta abubuwan alkairi da Raudha ke shimfidawa a bayan fage bazaka taɓajinsa a bayyane wa duniya ba, acewarta tayine domin ALLAH badan wani ya sani koya yaba mata ba. Mijinta kuma ya bata goyon baya ɗari bisa ɗari.


       Alhmdllhi an gama campaign lafiya ankumayi zaɓe shima. Yayinda sakamakon zaɓe ya tabbatar da sake zaman *_Ramadhan B. Hameed Taura_* matsayin shugaban ƙasa a karo na biyu a ƙasar NAYA. Duk wani masoyinsa ya tayasu murna da fatan sauke nauyin al'umma a kansu. Inda a wannan karon ya shigo sabon tsarin da sabon tsare-tsare da ƙudirirrika na musamman. Yayi sauye-sauyen wasu a cikin ministers da suka kasance zabin su Alhaji Yaro glass a wancan karon. Hakama vice president an sake sabo tunda su Alhaji Yaro ana can ana cin gabza a prison😝.

         Rantsar da shugaban ƙasa baifi da sati uku ba su Raudha sukai GRADUATION a makaranta. A kuma lokacin ta bayyanama school mate nata ko ita ɗin wacece. Ansha mamaki, ansha al'ajab da kace nace ga ƙasar NAYA ma ba makarantar kawai ba. Gaba ɗaya hidimar bikin fitar tasu ita ta ɗauki nauyin komai. Ansha hotuna na tarihi kowa burinsa firt lady karta manta da shi duk da bata yarda ta buɗe fuskarta ba ko a wajen bikin kamar yanda Ramadhan ya bada doka. Yadai yarje mata ta sanar dasu ko ita wacece kawai.. 

      A randa suka kamma bikin gama karatu a ranar ta sake fahimtar tana da ciki, taci kukanta tai gum da bakinta, sai dai batasan mai gayya mai aiki shi ya san da abunsaba tunkan ta sani. Sai ranar kawai yake bayyana mata ta gama boye-boyenta shi ya jima da sanin ya samo ribar farautarsa ai.

    Galala tai tana kallonsa, shiko yay mata gwalo ya fice. Jitai kamar ta zauna taita kuka kawai. Ita wannan wane irin abune bata yaye yara sai sabon ciki. To babu yanda aka iya da hukuncin ALLAH, wasuma nema suke basu samu ba da kuɗi.

     Tun tana zumbure-zumɓurenta harta ware suka cigaba da rainon ciki Mama Ladi ta yaye Alhaji Ƙarami. A randa Raudha ta haihu a ranar ALLAH yayma Addah Asmah dake fama da jiyya har yanzu rasuwa. Ba kowa yaji mutuwarba. Dan dama masu jiyyar tata sun matuƙar gajiya. Yanda bata nema yafiyar kowaba babu wanda yace ya yafe matan har gimbiya Su'adah da yanzu akai sanyi. Bata sakema Raudha dai bakuma ta takura mata. Babbar damuwarta ma yanzu zaman Lubnah a gida da Muneera da a yanzu ta koma sai wheelchair saboda ƙafarta ta samu matsala a wancan haɗarin. Har kuɗi da gida da mota aka saka ga wanda zai auri Muneera amma duk wanda yazo ya ganta saboda raunikan da tayi a fuska sun canja mata kamani sai ya gudu. Bilkisu kuwa tuni harta haihu abinta ita da su Fatisa. Yanzu hakama shirye-shiryen bikin su Basma akeyi.


        A wannan karon dai Ramadhan ya dage baza'ai bikin suna ba, ya dai ɗauke matarsa bayan arba'in sukai tafitarsu America domin hutawa na sati biyu tare da yaransu uku vice president ya cigaba da riƙe ƙasar NAYA kafin ya dawo. Dan jinjirin shima yaci sunan Mal. Dauda. amma suna kiransa Dawood. Raudha da Ramadhan na cemasa Abbati.

      Satinsu biyu suka dawo NAYA harkokin mulki suka cigaba da tafiya yanda akai fata...........✍


No comments

Powered by Blogger.