Bakar Inuwa 76
*_Episode 76_*
..........Tsaf ta zayyane masa komai data sani na firar su Aunty Hannah da taji, har zuwa aikama bappi takarda, da batun canja driks nashi da ake kawowa cikin gidan.
Ya daɗe da bincike akanta game da drinks saboda yanda kuɗi ke yawan fita a accaunt ɗinta, wanda duk watan duniya ake saka mata kason kudi na Taura family da ake bama kowa. Bai mata magana ba ya shiga bincike akan son sanin mi take da kuɗi, cikin ikon ALLAH kuwa yay azamar ganowa saboda companyn da take aikama kuɗin. Ta hanyarsu ya gane ana kawo drinks gidan, baiyi ƙasa a gwiwa ba yasa akai masa bincike akan wanda take canjawa da wanda take sakawar. An gano wanda take cirewar wasunsu akwai guba a jiki mai shiga jiki a hankali, wanda take canjawar kuma lafiya lau yake. Tun a sannan yasan Raudha tasan wani abu, shiyyasa koda suka samu rubutunta yazama irin na wanda aka aika musu wasiƙa bai tada hankalinsaba. Burinsa kawai yasan asalin tushe da mafari, yau kuma ta zayyane masa komai.
Kyawawar runguma ya bata yana mai sanya mata tarin albarka. Sai dai hakan bazai hanashi kafa kwamitin bincike ba domin tabbatarwa. Badan bai yarda da itaba, sai dan haka dokar shari'a take shaidarta bazata wadatar ita kadaiba dole sai da wasu shaidun musamman da su forma president suka zama manyan kusoshin ƙasar. Dama Dr Ingoze dake hanun security na gidan ta tabbatar musu ita ba laifinta bane sanyata akai ta hakala Raudha da jaririnta inba hakaba itama za'a halaka kaf family nata.
*_WASHE GARI_* akai jana'izar Inna da driver aka mikasu gidansu na gaskiya. Ciki kuma harda Shugaban ƙasa Ramadhan da yaje har makabarta. Bayan sun baro makabarta kuma ya wuce ya duba jikin Muneera da batasan ma ina hankalinta yake ba. Sosai ta canja kamanni saboda yanda motar ta kife ta dinga katantanwa da su a kan titi ga harbin data samu har biyu a ƙafa ɗaya da ƙugunta. Cike da damuwa da tausayin ƴar uwar tasa ya koma gida.
Sosai a wannan karon ma su Alhaji Yaro glass sukai baƙin ciki na rashin nasara. Har zukatansu suna sanar musu lallai Alhaji Hameed Taura na tsafi shiyyasa dukkan harin da suke kai masa sai ya kauce masa. Acewarsu to ai idan yasan wata baisan wata ba. Suna kusan sahun farko na zuwa yin jaje da ta'azziya Taura House. Sun kumaje har government house sunma Ramadhan shima dan ana gama jana'iza ya koma gida.
Randa akai addu'ar uku ranar Raudha ta koma government house tare da sabuwar mai kula da ita. Dama Anne nata faɗan zuwanta tun randa akai rasuwar acewarta tana riƙe da laɓuɓun yaro yawo ba nasu baneba ai. Duk da ba wankan jego take irin na mutanem da ba tana samun kulawa sosai dan babu ɗaga ƙafa Hajiya Mama ta dinga mata wankan towel. Yanzun ma koda suka dawo haka ta dinga kula da ita da ƙyau ita da Abdull. Dan Ramadhan ya hana a ɓoye masa suna. wasu kan kirasa Abdull wasu suce Abdull-Hameed ɗin. Shi dai Bappinsa yake kiransa, itama kuma takance bappi wani lokacin ko tace babban mutum.
A haka kwanakin jegonsu suka shuɗa duk da dai wajen da akai mata cs ya warke sarai Alhmdllhi. Ga gyara tana samu na musamman daga shahararriyar mai gyaran nan ƴar Nigeria dake jihar sokoto *_Maman Zara sokoto 07034251528_* (hummm kunga maman zarah ɗin nan karku bari kayanta su wuceku, ku garzaya domin kwasar rabonku, dan koda kuɗinka sai da rabonka kuwa) Gefe kuma Miss xoxo na kasheta da kayan gyaran jiki na musamman dana kamshi. Duk wanda yaga Raudha dole ya sake kallo, dan haihuwar ta sata buɗewa ta zama wata babbar mace da zaka iya bata shekaru ashirin da tara bawai sha tara ba. Shi kansa gogan nata haƙuri kawai yake da juriyar ɗauke kai. Amma inhar ya samu damar ritsata a ɗaki su kaɗai yana ɗan rage zafi ko rokonmi zata masa baya saurarenta. Dama aunty Zuhrah ce ke saka musu ido, ita hajiya Mama akwai kunyar surukuta shi kansa baya yi idan yasan tana kusa.
Ana saura kwanaki uku suyi arba'in Anne ta sanar masa ya kamata yabar Raudha taje hutawa, ta kuma je Bina masarauta duka tayo kwana bibbiyu. Fuska sosai ya tsuke kamar yana gabanta, sai da yaji ta sake maimaita masa sannan yay magana cikin marairaicewa.
“Amma Anne dan ALLAH...”
Kaga Ramadhan ni bance tilas ba. Ina dai tunatar da kaine abinda ya dace. Kai yanzu kana ganin ya kamata ace har yanzu matarka bata taɓa takawa gaishe da mai-martaba ba? Sannan tunda akai bikinta bata taɓa zuwa gaida mahaifinta ba?. Nasan dole ne ai muku uziri saboda a yanayin da kuke yanzu, amma bashi ke nuna bazakuje ayi zuminci ba. Kodan kaga tanada haƙurin shanye komai batare data matsanta maka ba”.
Ajiyar zuciya yaɗan sauke, dan yasan tabbas maganar Anne gaskiya ce Raudha nada matuƙar haƙuri, kamar kuma hanata zuwa gaida mahaifinta tauyeta yayi tunda tasha nuna son hakan duk da bata taɓa tunkararsa ba.
Da wannan shawara ta Anne ya shiryama su Raudha tafiya cikin kwanaki biyu. Zatai tafiyar bisa rakkiyar su Hajiya Mama da tawagar securitys. Koba komai hakanma ai ya taimaketa tunda tana son zuwan. Hutawa suka fara zuwa, inda Mal. Dauda ya rikice ya rasa inda zai tsoma ransa dan daɗi. Hakama Baba Nafi da Inna da sauran yaran gidan. Amarya ma dai ba'a barta abayaba, tace dolene ta tarbi first lady kodan baƙanta ran Larai abokiyar hamayyarta. Aiko kamar yanda ta shirya kunna larai tako kunnuta harta kasa riƙe baƙin cikinta ta dinga sakin magana da aibanta Raudha harma da Asabe. Uban gayya Mal. Dauda dake ƙwaƙume da Abdull babu wani jan lokaci ya sauke mata maruka, tare da tabbatar mata yau tata ta ƙare a gidan taje ya saketa. Dan ya rantse duk wanda ya nuna baya son mai sunan Innarsa Raudha to shima bazai taɓa yasosa ba, domin Raudha dai farar haihuwa ce. Da farko Larai ta ɗauka abun wasa, sai da Inna tace “Idan bazata tafi ba ƙara mata guda Dauda”.
Haƙuri Raudha da Aunty Zulfah suka shiga badawa. Yayinda Hajiya mama ko'a jikinta. Take anan ma ta kira Asabe ta guntsa mata. Bawani daɗi Asaben taji ba. Dan acewarta saki koda kaine ka nema bashi da daɗi.
Sosai maƙwafta sun shigo gaishe da first lady, dan ma wasu tsoron securitys dake zagaye da gidan na mal. Dauda ya hanasu. Washe gari da safe taje har gidan hakimi takai gaisuwa da masa godiya. Shiko ya amshi Abdul yana mai sanya masa albarka shi da ƴan fadarsa da matansa. Sunbiyo ta super market ɗin M. Dauda da Raudha taji har ƙwalla ya cika mata ido dan babu abinda zatace da Bappi sai dai addu'a. Da zasu taho jitai kamar karta baro garinta, M. Dauda ya shirya tsaraba mai yawa wai duk na Abdull, ita Raudah abinma dariya ya bata. Yaushe Abdull ɗin yazo duniyarma dazai fara shan kayan zaƙin nan dana ciye-ciye. Da tace a rage cayay bai yarda ba. Itama Inna ba'a barta a baya ba tama Raudha tsaraba da kayan sirrinsu na tsoffi masu kyau da dama ta tanada tunda Raudha ta haihu. Dan ko lokacin suna da sukaje dama takai mata wasu.
Daga Hutawa Bina suka nufa cikin masarauta. To anan dai kam daga mai-martaba ta samu tarba ta ƙwarai. Fulani ce dai kadaran kadahan. Dan ko Abdull ƙin cewa a bata tai sai da Aunty Zuhrah ta ɗauka da kanta ta bata tace a sanya masa albarka. Sai kuma duk taji kunya. Mai-martaba kam acan suka baro masa Abdull, ba'a dawo musu dashi ba sai da ya fara ƙananun kukan yunwa.
Anan ɗin ma dai shatara ta arziƙi mai-martaba da sauran matan sarki suka bama Raudha dan Ramadhan yana girmamasu shidai. Babu ruwansa da wata aƙidar dake tsakanin iyayensa da su.. Ganin sunzo har Bina ta kira Ramadhan ta roƙesa zuwa gaida Aunty Halima itama. Bai hana ba, dan tun farko ma daya san Aunty Haliman a Bina take itama da kwanan akai mata. Sai dai gsky a matse yake da matarsa, burinsa kawai ta dawo. Aunty Halima taji matuƙar daɗi dayin farin cikin zuwan na Raudha. Hakama yaranta. Kasancewar Ramadhan yace sukai har dare sai su biyo jirgi yasata baje kolinsu sosai a gidan Aunty Halima. Dan sai kusan tara suka nufi airport jirgin 9:30 zasu bi.
Ƙarfe goma bataiba ma suka iso Bingo. Motocin da suka tafi tarbarsu da securitys suka kwasosu sai government house. A ranar ma dai Ramadhan yayi kawaicin kauda idonsa saboda yasan da gajiya tattare da su. Dan ko keɓewa bai yarda yayi da Raudha ba. A ɗakin da take jego ya shigo suka gaisa da su Aunty Zuhrah itama Raudha ta gaisheshi ya ɗauka Abdull ya fita. Kusan mintuna talatin yay kiran Basma a waya tazo ta ɗakko Abdull ɗin ta dawo da shi.
Washe gari su Hajiya Mama suka tarkata yan kayansu kafin Ramadhan haƙurinsa yakai karshe ya fara rashin ta ido. Shatara ta arziƙi suma ya haɗa musu suka tafi Raudha na matsar kwalla. Tsabar ya shiryama wannan weekend suma su Basma cayay zuje Taura house suyi weekend. Raudha zatai magana ya dinga zuba mata harara da mintsini. Doleneta tai shiru..........✍
Leave a Comment