Bakar Inuwa 73

 


*_Episode 73_*



..........A wata juma'a datai dai-dai da saura kwanki huɗu cikar shekarr Ramadhan guda a mulki aka ɗaura auren Alhaji Sageer Dogarai da amaryarsa Asabe. Aure ne daya tara ɗunbin al'umma musamman daya

kasance juma'a ne mutane duk sun halarci masallaci. Aure ne daya saka wasu farin ciki wasu saɓaninsa musamman aunty Hannah da tun farkota nuna adawawta akai, sai dai kuma babu abinda ta isa ta hana daga hukuncin ALLAH. 

      Ƴar walima kawai akai amarya ta tare ɗakinta cikin aminci da mutuntawa. A kuma daren Ranar M. Dauda da abokinsa suka iso Bingo a haukace a dalilin M. Gambon ya samo labarin a shanun ƴan talla. Inda ALLAH ya taƙaita al'amarin ya kira Bappi ta waya kafin su tunkari ko'ina. Hakan yasa Bappi saurin taka masa birki yasa Malam Adamu zuwa ya ɗakkosu. Babu wanda yasan da zuwansu Taura House sai Anne da Bappi. Aka basu masauki mai ƙyau da abinci kafin safiya. Da farko M. Dauda ya nuna shifa ba wannan ya kawosa ba Bappi dai ya sake lallashinsa. 


     Washe gari da suka zauna akan batun fir ya nuna shifa sai Alhaji Sageer Dogarai ya sakar masa matarsa inhar ana buƙatar zaman lafiya a NAYA. Iya nasiha yaƙi har sai da Bappi ya bama Ramadhan Umarnin sakawa a kawo masa Raudha gidan. Tana makaranta M. Adamu yaje ya ɗakkota. Gaba ɗaya hankalinta a tashe yake dan batasan mike faruwa ba. Gashi babu damar kiran Ramadhan ta damesa tasan yana office. Sai da suka iso taci karo da Abbansu ta sauke ajiyar zuciya. Yay sakalo yana kallonta da cikinta daya fito ɗas duk da ma hijjab ne a jikinta har ƙasa. Sai dai a yanda tai zaman sai da cikin ya fito.

       “Oh ALLAH sarki Raudha ashe wannan irin arziki ALLAH yaymin naketa shirme ma? Dama ciki ne da ke?”.

     Ina ƙasa Raudha ta shige dan kunya, Bappi yay murmushi mai faɗi da gyaran murya. “To kaga kariga ka fara zama babban mutum tunda ga jika kana shirin amsa duk da nasan bashi bane na farko. Ya kamata wasu abubuwan a ajiyesu hakanan kodan wasu dalilai Malam Dawood. Shi aure raine da shi, sannan ƙaddarace ta ALLAH. Ya riga ya ƙaddaro zaka zauna da mahaifiyar yaran nan na wani lokaci ku rabu, idan kuma da rabon sake zama sai kaga ta sake baro can ta dawo gareka ai”.

     Hawaye malam Dauda ya share dan harga ALLAH yana son Asabe, so irin wanda bai tabama wata mace ba. Dan ko auren nan daya kara na budurwa dal a leda bai maye masa gurbin rashin Asabe ba a ransa. Nasiha sosai Raudha da Bappi sukai masa, sai dai M. Gambo nata zungurinsa akan karya yarda wai. Tsaf Bappi ya fahimci M. Gambo, ya kuma gane shine matsalar M. Dauda. Dan haka a ranar ya saka aka maidashi Hutawa bayan ya haɗashi da shatara ta arziki.

      Sosai M. Gambo yaji zafin hakan, dan acewarsa ƙiri-ƙiri an nuna banbanci tsakaninsa da M. Dauda. hakan ya sashi ƙudirin abubuwan mugun abu da yawa cikin rai game da M. Dauda. Acewarsa in bai samu Asabe ba ai akwai hanyoyin ramuwa da yawa.

   

      Kwanan malam Dauda biyar a Bingo, dan har gidan gwamnati aka kaisa ya kaso kwarkwatar ido wannan karon. Bappi kuma ya riƙesa akan ya zauna har sai anyi bikin cika shekara guda na Ramadhan a mulki. Hakan ya masa daɗi sosai, ya kuma sakashi farin ciki. Su Fatisa ma har nan Taura house sukazo gaida shi, har kuma zuwa yanzu bayan su Anne babu wanda yasan da zamansa a gidan.


*_GOVERNMENT HOUSE_*


          Sosai aka shirya bikin cika shekara ɗayan nan har abun ya ɗan so bama mutane mamaki, dan lamarin tamkar wani arashi. An shirya ɗakin da taron zai gudana cikin tsarin ado na tutar ƙasar NAYA. Duk da gwamnoni suma zasuyi nasu a jihohinsu hakan bai hanasu halarta ba. Hakama sarakunan gargajiya da abokan kasuwancin Ramadhan.

        Su Alhaji yaro glass da muƙarrabansa harma da god fathers nasu kam sun halarci taron. Sai tarin manyan ƴan jam'iyya na kowace jiha. Kamar ko yaushe First Lady da mijinta shugaban ƙasar NAYA *_Ramadhan B. Hameed Taura_* suka iso wajen taron cikin shiga ta kamala ana take musu baya. Sanye take da hijjab har ƙasa fari ƙal mai hannu, sai kaɗan daga ƙasa ake iya ganin ƙasan doguwar rigarta mai kalar tutar ƙasar NAYA. Daɗin daɗawa akwai facemask a fuskarta tare da siririn farin glass iya hannayenta kawai ake iya gani da tsadajjen agogonta. Hakama shugaban ƙasa Ramadhan sanye yake cikin ɗanyar shadda fara ƙal daketa maiƙo da haska idanun mai kallo. Ta gaurayu da ɗinki na musamman daya ƙawatata ya kuma tabbatar fitar tutar ƙasar NAYA. Hakama hularsa zannah tayi matuƙar murzuwa. A kallo guda zaka tabbatar da tarin kwanciyar hankali da farin ciki tattare da shi. Yana riƙe da hanun matarsa har akai masa rakkiya wajen zamansa sannan mutane da suka miƙe dominsa na girmamawa suka koma suka zauna.

      Kamar yarda shari'a ta tanadar malamai sun gudanar da addu'oi kafin a fara gudanar da abinda ya tara mutane a wajen. Inda bayanin shugaban ƙasa yay matuƙar birge mutane da ƙara darajarsa a idanusu. Lokacin da aka buƙaci cewar first lady.

       Wata hamshaƙiyar mace ta miƙewa da takarda a hanunta ta tabbatar musu ga saƙon first lady ita  wakiliyarta zata isar bisa umarnin shugaban ƙasa amma matsayin miji ba shugaba ba basai tace wani abuba.

      Hakan ya bama wasu mamaki, ya birge wasu. Wasu kuwa sun gumtsi gulma da sauya zancen a muhali na daban. Oho hakan bai damu Ramadhan ba, shidai burinsa tsare mutuncin iyalinsa da kuma kishinta da yakeyi. Bayanan da aka gudanar matsayin na first lady ma sun kayatar kuma sun birge mutane daban-daban. Daga haka taro ya cigaba da guna. Anci ansha anyi hani'an first lady da shugaban kasa babu wanda yasha ko ruwa a wajen.

       Sai da ana gab da tashi a taron ne Raudha ta hango Abbanta tare da Alhaji Hameed Taura cikin shiga ta kamala tamkar bashi ba, dan kayan daya saka sun masa ƙyau matuƙa duk da jikin ya nuna ba'a saba sakawa ba. Taji daɗin yanda ya kame kansa a wajen har aka tashi lafiya.

     

     Duk yanda Raudha ke ɓoyen cikinta a hijjab hakan bai hana wasu ganewaba, tuni kuma yan jarida suka hau yaɗa cewar shugaban ƙasa gab yake da zama angon karni kuma Baba dan firt lady na ɗauke da ciki. A fanin ƴan adawa kuma sun gama baza zance first Lady dai turancine bata iyaba shiyyasa Ramadhan ya hanata magana a wajen aka samo kwararriya aka fake da kishi.

     Maganar tayi nisa sosai, sai dai cikin Raudha yaso danneta tare da manyan ayyukan da aka zano shugaban ƙasa Ramadhan ya shinfiɗa a shekara guda kacal. 

      A ɓangare. su Alhaji Yaro glass sunyi zaman meeting akan cikin nan, inda kai tsaye suka ƙalubalanci Aunty Hannah data ɓoye musu hakan. Ta nuna batasan Raudha nada ciki ba itama, amma hakan bashike nuna batai murnaba. Dan ita tanada manufa akan cikin koba komai zasu kasance da wani kaso na dukiyar Taura family musamman idan aka dace Raudha ta haifo namiji.

    Wannan magana tata ta banƙanta ran su Alhaji Yaro glass, harya faraji a ransa Aunty Hannah bazatai dogon zangoba zai kawar da ita. Dan ya tabbatar shi ɗinma zata iya yin kalar tunanin da take furtawa akan dukiyar Taura family akansa kenan. Duk da kuwa Samha ce kawai a tsakaninsu har yanzun.

     To komadai miye, mudai ƴan kallone ai.🤣


Kwanaki biyu da yin wannan biki na cikar masu mulki shekara ɗaya akan madafun iko Malam Dauda ya koma hutawa da shatara ta arziƙi. Dan kuwa kujerar makka har uku, tare da kuɗi masu yawa da galleliyar mota da alƙawarin buɗe masa manyan shaguna a hutawa da kuɗi zasu dinga shigo masa akoda yaushe. Wannan farin ciki ya sashi danne son Asabe daya san har Abada bazai iya dainawaba. 

        A randa M. Dauda yabar Bingo a ranar hoton wani video ya karaɗe yanar gizo da duk mai wayar da take iya buɗe data zai gani. Video ne daya kasance na Aynah a cikin club ana aikata masha'a da ita. Sai kuma wani shima a cikin ɗaki kusan su biyar duk mata. Abinda zai baka mamaki na club ɗin babu face mask kamar yanda Ramadhan ya sani.

      Aminu ya saki wannan video ne bayan ya saka dukan abokansa sunyi amfani da Aynah a wannan dare wasuma harta baya (Wa'iyazubillah😭) yayi hakane a dalilin kawo mata ƴammatansa da yay gidan ta nuna itafa ta gaji ya sallameta hakanan kokuma ta tona masa asiri ga iyayensa da yake yaudarar nuna musu shi ɗin mutumin kirkine. Shiko ya tabbatar mata kafin tayi hakan shi zai fara tona nata a sirin wa duniya sai yaga nata da nashi wannene zaifi gawurta da kayatarwa. Tayi kuka ta roƙesa iyakar roƙo amma yay kunnen uwar shegu da ita sai da ya saki.

      A lokacin da wannan video ya riski su Addah Asmah data haukata kanta a neman asirin hallaka Ramadhan da wulƙanta rayuwarsa data Gimbiya Su'adah har ƙasar China ta yanke jiki ta faɗi. Kwannta biyu kenan da dawowarta NAYA, wata kawarta ta rakata China wajen wani gagarumin masanin tsafi. Sun dawo zuciyarta cike da jin ɗunbin nasara saboda abinda matsafin ya haɗo musu, ta tabbatar idan har tai amfani da su Gimbiya Su'adah da zuri'arta sun zama labari kenan. Sai gashi a yau da take shirin zuwa Taura house da fuskar yaudarar roƙon gafarar gimbiya Su'adah danta aiwatar da aikinta wannan mummunan labari ya  baje ƙasar NAYA dama duniya tunda abune na media ako ina zaka iya ganinsa.

     A firgice ma'aikatan gidan nasu da kanwar Aynah suka rufu a kanta sai dai babu alamar numfashi tattare da ita. Dole Zulfah tai kiran asibitin da suke ganin likita dan ta nema no na daddyn su ma bata samuba kasancewar shi bayama kasar.

      


          Hatta da gimbiya Su'adah da ayanzu babu wanda ta tsana a duniya sama da ƴar uwar tata abin ya firgitata, balle kuma Fulani da itama ta yanke jiki ta faɗi ƙasa a sume dalilin tanada hawan jini.

     Raudha ma ta gani kafin Ramadhan, amma ta kasa nuna masa sai zama datai taita kuka dan abun ya ɗaga hankalinta. Musulma ɗiyar muslmai gaba da baya itace a wannan halin duniya ke gani babu ko kunyar mahaliccinmu. Kaicon wata wayewar, kaicon wata dukiyar, kaicon wata damar dan da wata BAƘAR INUWA ce da ita gara rana ma.

      Koda Ramadhan ɗin shima ya gani baiji abin saboba tunda a gabansa aka aikata, sai dai abinda ya bashi mamaki fitar videon bayan shekaru. Hakan na nufin dan kinyi barna ko kayi ka binneta da tunanin ta wuce mutane bazasu ganiba watarana UBANGIJI idan yaso sai ya tonota ta hanyar da kai bakai tunani ko tsammani ba. Sannan ya jiraka a madakata kazo ya hukuntaka dai-dai da laifinka dan shi bai kasance azzalumin sarki ba...........✍


No comments

Powered by Blogger.