Babban Goro 8


BABI NA TAKWAS___8


Kallon shi kawai ta bishi da shi har ya zauna a kujerar dake facing ɗinta, 

Shiru yayi yana kallonta sannan yace, 

“Miyasa kika tsani Dr Salamu bayan ita ce ta haife ki?” 

Shiru tayi kamar baza amsa mishi ba can kuma ta soma magana, 

“Mummy ba ita ce ta haife ni ba bansan waye mahifina ba bani da kowa ban kuma san haka ba sai da wadda muka kulla maganar aure dashi yace min iyayenshi sunce ba zai aure ni ba dan bani da uba kuma Mummy ba ita ce ta haife ni ba, 

Ni kuma ban musa masa ba saboda na sha tambayar Mummy waye Mahaifina taki ta faɗa min sai ma cewa take na daina mata maganar na daina damuwa zata yi min duk abinda nake bukata, 

Kuma lokacin dana same ta da maganar sai tace min lallai ni ba da aure aka haife ni ba ni kuma da naji haka sai nayi unkurin hallaka kaina” 

Tana maganar hawaye na mata zuba, 

   Tunda take maganar Saif ya natsu yana saurarenta har ta kai aya, tausayinta ne ya kama shi idan har abunda ta faɗa gaskiya ne ta chanchanci a tausaya mata dan rashin uba ko gurin namiji akwai ciyo barre ya mace, 

Tashi yayi ya koma kusa da ita ya zauna yaja kanta ya dora saman kafaɗar shi, 

Cak.! Kuka ya tsaya mata wata rahama ta ratsa mata jiki, lumshe ido tayi ta kusa kanta cikin jikinshi tana shakar daɗadden kanshin dake fita daga jikinshi. 

    Sunyi minti goma sha biyar a haka, sai can ya ɗago kanta yasa handkerchief mai ɗauke da sunanshi sai kanshi turare yake ya share mata hawaye, sannan ya tashi tsaye, 

   Kallo ta bishi dashi har yakai bakin kofa sannan ya juyo ya kalleta, 

“Ki kwantar da hankalinki Deen ɗinki zai dawo yanzu” 

Kai ta ɗaga mishi “Atm ɗina fa? ” 

Bai bata amsa ba sai kawai ya juya zai fice, ganin hakan yasa tace “Please karka faɗawa Mummy ina nan” 

Nan ma baice da ita komai ba ya fice, 

A hankali ta kwantar da kanta hannun kujera tana kallon handkerchief ɗin shi da bari gefen kujerar, wani sabon kuka ya taso mata.Driving yake yana shan karatun Sheik Shuraim, har ya isa Maitama Ministers hill tunanin Minal yake, gaskiya duk wadda yake cikin gata irin na Minal ya wayi gari akace bashi da uba xaiyi bakin ciki sosai, 

Yana yin parking Dr. Salamatu ta fito da sauri ta nufoshi, 

“Anyi nasara kuwa?” 

Kai ya ɗaga mata ya mika mata abubuwan daya karɓa hannun Minal, 

“Anyi nasara ki rike wannan nasa a kasa mata takunkumi bata iya zuwa ko ina a yanzu koda tana da waɗannnan abubuwan” 

Da sauri tace “Ina take Saif?” 

“Wannan ne kawai bazan faɗa miki ba dan ta rik'i haka a gareni kuma kinsan ke kika saka ta cikim halin da take ciki yanzu” 

Yana kaiwa nan ya juya ya shiga motarshi, jiki a sanyaye ta k'arasa kusa dashi “Kaima kana zargi na kamar ita?” 

“Toh misaya ba zaki faɗa mata wacece ita ba? A yanzu ta riga tasan ba kece kika haifeta ba idan ma har shine kike jima tsoro karta gujeki ko? da kin faɗa mata gaskiya tun farko da bata shiga halin da take ciki yanzu ba” 

Tana kokarin maida hawayenta tace “A shirye nake na faɗa mata komai Saif nayi nadamar yin hakan da nayi” 

Kafaɗunshi ya ɗaga “Idan bukarta hakan ta taso ita da kanta zata neme ki” 

 Bai tsaya jiran abinda zata ce ba yayi ma motarshi key, itama bata kara cewa wani abun ba har ya bar gidan.
                  ********
“Dear wai mi yake damunka ne naga cin abincin kawai kake amman hankalin ka baya gurin?” 

Drink ɗin dake gabashi ya ɗauka sha yana murmushi, 

“Wai yanzu Huda idan kika wayi gari Hajiyar ki tace ba ita ta haife ki ba kuma Abbah yace ba shi ne mahaifinki ba kuma duk family da kika gani ba naki bane ya zaki ji?” 

Kallon mamaki tayi mishi “Wannan wace irin magana ce wannan Saif?” 

“Please just answer me” 

Kai ta jinjina “Gaskiya zanji ba daɗi zan kuma yi bakin ciki wata kila har na gudu saboda takaici kuma zanso sani suwaye iyayena ya kuma akayi na zo hannun waɗanda ba iyayena ba” 

A hankali ya kaɗa kai alamar gamsuwa yace “Kuma ace akan haka har na rabu dake ya zaki ji?” 

6ata fuska tayi "Haba dai dear miye na wannan maganar kuma gaskiya idan ka rabu dani kashe kaina zanyi ko kuma na haukace gaskiya ka daina bana so” 

Hannayenshi ya ɗaga “Na daina Dear” 

Cigaba yayi da cin abinci yana tunane tunane, 

“Wai miyasa kayi min wannan tambayar?” 

Kallonta yay da murmushi “Saboda kina kaunar Saif” 

Dariya tayi ta tashi tsaye, 

“Toh angon Huda nidai na koshi over” 

Tashi shima yayi tsaye “Nima ai na koshi daman ke nake daku” 

Hannunta ya rik'a suka nufi bedroom bayan ya kashe wutar parlor.


No comments

Powered by Blogger.