Babban Goro 2

 


Episode___2


Saif na fita parking space ya nufa, yana shiga motarshi yayi mata key yayi horn aka buɗe mashi gate, 

Hanyar da zata kai shi gidan Dr. Salamatu ya bita yana gudu kamar zai tashi sama daman haka al'adarshi take gudu a mota, 

Yana isa yayi horn maigadi na lekowa yaga Saif jiki na rawa ya bude mashi yana ɗaga mashi hannu, 

Yana yin parking ya fito ya cikin gidan, duk inda yabi gaishe shi ake cikin girmamawa da rawar jiki,

 tun kamin ya k'arasa parlor wata tsohuwa ta tareshi bayan sun gaisa tace 

“Hajiya fa bata nan tana asibiti dan gidan ba lafiya” 

“Eh naji ai shi ne abunda ya kawo ni wace asibitin aka kai ta?” 

“Kings Hospital aka kaita”

Bai tsaya jiran ta k'ara cewa wani abun ba ya ya juya tunda yaji abinda yake son ji. 

     Cikin minti biyar ya isa asibitin yana yin parking ya nufi Emergency,

 Reception ya tafi aka faɗa mishi ɗakin da suke, a hankali yake tafiya har ya isa gurin. 

Tsaye ya tararda Dr. Salamatu, wasu mata na tsaye kusa da ita duk kansu sun rakfa uban tagumi especially ita sai ruwan hawaye take, 

Da sanyin jiki ya k'arasa kusa dasu 

“Dr. Salamatu” 

Da sauri ta kalleshi kamin tayi magana ya rigata 

“Mr President yace nazo na duba jikin yarki ko tayi rai?” 

Cikin muryar kuka tace 

“Eh sunce tana da rai sai dai ban tabbatar da lafiyarta ba dan tun jiya basu barni na shiga ba yanzu ma suna ciki suna duba ta” 

“Okey” 

Kawai yace ya juya da nufin tafiya hakan nan kuma sai ya samu kanshi da kasa tafiyar, juyowa yayi ya zauna a kujerar dake gurin yana kallon kofar ɗakin, 2 hours later... 

Likitoci uku suka fito daga cikin ɗakin, da sauri Dr. Salamatu ta nufe su tare da matan har Saif, ɗaga daga cikin likitocin ne ya tsaya yana yi mata bayani kamin ya bata izinin shiga, 

    Da sauri Dr. Salamatu ta nufi ďakin su kuma matan dake tare da ita suka samu guri suka zauna. 


                           *******


Zaune take sanye da k'ananan kaya idanunta sunyi wani fari fatar k'aramin bakinta ta bushe sai faman sauke ajiyar zuciya take,

Babu abinda take ji sai tsanar kanta, 

         A hankali ta kai hannunta a baki ta shiga cizon akaifarta, jin an taɓa kofa yasa ta juyo tana kallon kofar,

      Dr. Salamatu ce ta shigo rungume da hannayenta fuskantar shakaf da hawaye, cijin sayyayiyar murya ta kalleta tace

 “Minal My child...” 

Juyarda fuska Minal tayi  “Dan Allah Mummy ki fita i don’t want to see you anymore” 

Sauke hannayenta tayi ta nufota tana faɗin “Minal ina son ki-” 

Hannu ta ɗaga mata tun kamin ta k'araso kuda da ita 

“No Mummy i don't want to understand i hate you karki zo kusa dani” 

  Cikin tsawa take maganar tana k'ok'arin saukowa saman gadon, 

Da sauri tayi baya tana matsar kukan dake son fito mata, 

Dai-dai lokacin Saif ya shigo ɗakin yanayin yadda yaga Dr. Salamatu yasan ba lafiya ba, sai da ya kalli Minal sannan ya sake kallonta yace 

“Yaya jikin nata?”

Ba tare data kalleshi ba ta bashi amsa, 

“Better” 

Kai ya gyaɗa ya ɗan kalli Minal da itama shi take kallo.... 

    Cikin tsoro Dr. Salamatu tace “Minal zaki sha tea.?” 

Tsawa ta katsa mata kamar mai faɗa da yarta “Bana so bana son ganin ki ever again miyasa kika kawo ni asibiti miyasa? miyasa kika ceci raina baki barni na mutu ba?” 

Cikin kuka da sanyin murya Dr. Salamatu tace “Because I'm your mother bazan iya kyale ki ki mutu ba” 

Kai Minal ta girgiza tana hawaye

 “No you are not my mother ke ba uwata bace stay a way from me” 

“I'm your mother Minal no matter what I'm still your own mother nice na haife ki Minal” 

Dr. Salamatu ce take maganar tana nuna kanta hawaye na mata zuba, 

 Tunda Minal ta soma maganar ya lumshe ido yana ɗan cizon baki, sosai yake jin kalaman sunyi mashi girma, 

       Ya tsinar fuska Minal ta shigayi tana haɗiye yawu da karfi kamar mai shan maɗaci, ta tsire baki ta kalli Dr. Salamatu tace “Ke ba uwata bace ke... -” 

  Tasss Saif ya wanke mata fuska da mari tun kamin ta k'arasa maganar da sauri ta dafe kunci tana kallonshi,

   Baki Dr.Salamatu ta rik'e tana kallon Saif da k'arfin hali irin nashi.

No comments

Powered by Blogger.