Babban Goro 1


 BABBAN GORO...! 

       

          NA 


KHADEEJA CANDY1___Tsaye yake gaban wani k'aton dressing mirror, sanye da black suit yana gyara necktie, 

 _Give me freedom give me fire give me reason take me higher see the champions take the field now you define us make us feel proud_

A hankali yake bin sautin wak'ar suna rerewa tare, wani _pear watch_ naga ya ɗauko yasa bayan ya feshe jikin shi da turare _the real man_ tsaye yayi yana kallon kanshi a mirror, nan nima na tsaya ina k'are mashi kallo.

Dogone kuma fari fes mai dogon hanci gashi da manyan ido a gefen bakinshi an manna mashi dimples. 

Murmushi yayi ganin yadda suit ɗin ya zauna jikanshi yayi mashi kyau sosai kamar dan shi akayi shi, sai da ya ɗauki wani _blue oil_ ya shafa a kanshi sannan ya nufo wani ɓangaren na ɗakin, 

Babu komai a gurin sai sai jerin talkama na gani na faɗa, wasu _half cover shoes_  ya ɗauko yasa, 

   Sai da ya sake duba kanshi a madubin sannan ya nufi part ɗin maihaifiyarshi. 


*****


Da sallama ya shigo Safiya ta amsa mishi, zaunawa yayi yana faɗin 

“Ina Momi.?” 

“Tana ɗaki wanka take” 

“ok” 

Hannu ya kai ya ɗauki wani littafi dake saman Center table _The broken heart_


“Man ka karanta news kuwa.?” 

Nasir ne ya shigo yana maganar rik'e da jarida a hannunshi, kai Saif ya girgiza 

“A'a miya faru ne.?”

Jaridar ya mik'a mishi yana faɗin 

“Wai wata yar minister ce tayi k'ok'arin kashe kanka”

“Wow a ina.?” 

Saif ya tambaya bayan ya k'arɓi jaridar,

“A Nigeria”

 Nasir ya bashi amsa 

“Toh mi akayi mata.?” 

Zaunawa yayi yana bashi amsa

“Nima abinda nake son sani kenan nida yan'jarida” 

Sai da Saif ya ɗan karanta jarifar sannan yace 

“Yar minister man fetur ce Dr. Salamatu Abubuwa Yola kuma ita kaɗai ta haifa” 

Safiya ta rik'e baki

 “Amman dai ta mutu ko?” 

“A'a bata mutu ba tana dai cikin mawuyacin hali” 

Saif ya faɗa still yana duba jaridar, 

Safiya ta cige baki 

“Amman wallahi naso ta mutu dan ina jin daɗi ne yayi mata yawa” 

Murmushi Nasir yayi 

“Haba dai kiji ance ita kaɗai mahaifiyarta ta haifa kiyi mata wannan fatan yanzu haka fa mahaifiyarta tana cikin kiɗima” 

“Toh ai gani nake iskanci ne yayi mata yawa idan ba shi ba miye na kashe kai?”

Nasir yace 

“Baki san dalilinta ba” 

“A'a Ya Nasir babu wani dalili ina jin dai kawai ta gaji da duniyar ne ko kuma bata da hankali” Faɗar Safiya, 

Tashi Saif yayi “Allah ya kyauta ni bari na lek'a part ɗin Dad idan Momi ta fito kice mata na fita” 

Kai Safiya ta ɗaga mishi yasa hannunshi aljihu ya fice, 


_LABARAN DUNIYA,_

_Mai Karantawa  Fareeda Muhammad Yabo. Da Farko Ga Kanunsu Bom Ya Fashe A Wata Mashaya Dake Amerika, Isra'ila Ta Shiga Teburin  Tattauna Da Falasdin, Wata Kotu A K'asar Masar Ta Yan Kewa Wasu Matasa Hukuncin Shekaru Goma Gidan Kaso , Shugaban K'asar Turkiyya Zai Kaiwa Takwaransa  Na K'asar Faransa Ziyara, A Najeriya Kuma Wata Yar ' Minister Tayi Unkurun Hallaka Kanta.._


Alhaji Bashir Bature ne kishingiɗe cikin makeken ɗakinshi da aka k'awata da kayan alatu yana sauraren radio dake gefen shi yana aiki,

Salamar da Saif yayi ne yasa shi ɗago kai tare da amsawa 

“Wa' alaikassalam” 

Guri ya samu kusa dashi ya zauna

 “Barkada Safiya Dad” 

Hannu Dad ya kai ya kashe radio sannan ya amsa mishi

“Barka dai Ka tashi lafiya.?” 

“Lafiya kalau Alhamdulillahi” 

Tashi Dad yayi zaune ya kalli Saifa yace “Ya maganar Matarka?” 

Kawarda Fuska yayi yana ɗan sosa kai, 

Dad yace “Saifullahi Hak'uri fa ake da mata, duk wani mai iyali da kake gani hak'uri yake muma da ba muyi hak'urin ba da bamu kai yanzu ba nan gaba kaɗan fa Uba zaka zama idan babu hak'uri yaya kenan? Kaga itama kanta tayi nadama tunda har kaga iyayenta sunyi magana”

Wani guntu numfashi yaja “Dad ni Wallahi halinta ne bana so kuma nayi nayi da ita tak'i ta chanja” 

“Ka daiyi hak'uri ka dawo da ita muga abinda Allah zaiyi” 

“Shi kenan Dad zan maida ta In Sha Allah” 

“Toh Allah yayi maka albarka ya baku hak'urin zama da juna” 

“Amin Dad thank you” 

Tea cup ɗin dake gabanshi ya ɗauka ya kurɓa sannan ya sake kallon Saif 

“Saifullahi” 

A natse na amsa

 “Na'am Dad” 

“Ina son yanzu idan ka fita kaje gidan Dr. Salamatu Abubakar Yola ka bincika min lafiyar yarta dan faɗa min tayi unk'urin hallaka kanta kuma yanzu ma naji a labarai” 

“Ok Dad zanje yanzu dana fita amman Dad an faɗi dalilin yin hakan da tayi?” 

Gyaran murya Dad yayi 

“Har yanzu ni dai banji wani dalili ba ina dai son kaje ka bincika” 

“Yanzu ma dana fita daga nan can zanje” 

“Yayi Kyau karfa ka manta da zancen Matar ka” 

Tashi yayi yana murmushi “Toh Dad bazan manta ba” Sai da yayi mishi Sallama sannan ya fice.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...! 

No comments

Powered by Blogger.