Tabarmar Kashi 3

 


*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔

_Arewabooks:Huguma_

https://arewabooks.com/u/huguma


PAGE 03


         Ɗaya daga cikin yammaci ne wadda ke jerin yammacin da albarkar ubangiji ke sauka daga sama zuwa ga bayinsa dake rayuwa a doron qasa sanadiyyan haduwar hadari da samuwar saukan ruwan

sama,kama daga mutane dabbobi aljannu da sauran halittun dake qarqashin ruwa saman bishiyu da sauran bingiren da idanuwa basa iya ganinsu,raunin hankali,nakasa da kasawa irin ta abun halitta ya yiwa hankali shamaki da fahimtar wanzuwar wadan nan halittu dake kewaye damu masu tarin yawa,wanda kowanne yana qarqashin kulawa da tasarrufin ubangiji,bai gaza ba dai dai da qiftawar idanu wajen rabon arziqi ga bayinsa,da kuma isarwa da kowanne bawa gwargwadon rabon da ya kasance mallakinsa ne.


           A dai dai wannan lokacin,cikin qawataccen gidan abincin,muhalli me daukan hankali,sanyaya zuciya da bawa ruhi nutsuwa, sakamakon yadda aka qawata wajen da wani irin tsari mai ban sha'awa da burgewa,kwatankwacin yadda zai ja hankalin abokan kasuwanci suji basu qagara ko gajiyawa da zuwa kashe yunwa da qishirwarsu a wajen ba.


          Saman kujerun dake zagaye da teburan dake jere a wajen bisa tsari na rukuni rukuni,daga hannun damanka bayan ka shigo wajen zaka iya hangenta.


            Kyakkyawar matashiya,fara sol data mallaki wani irin hasken fata,irin farin da ko makaho ya shafa yasan natural ne,wanda ya cakuda da tsantsar kulawa tsafta da kuma hutu,yake kuma nuni da zurfin gogewa da wayewa da mamallakiyar fatar ke da shi.


           Idan har kayi hanzari ko azarbabi zaka iya kiranta da doguwa,saidai kaso me yawa na tsahon nata babu shi sakamakon murjewar da jikinta yake dashi da ya shanye tsahon ya maidashi moderate. Wasu irin manyan idanu gareta amma kuma a russune suke,wannan ya boye girman idanun nata,kai tsaye ba zaka ce suna da girma ba har sai idan taso fidda girman nasu ne. Siraran labbanta masu kalar pink sun dace hancinta mai tsaho da tudu wanda ya hade da kwantacciyar eyebrows dinta dake bisa tsari kamar an zanata.


          Sanye take da wata tattausar exclusive atamfa da bata tara tarkacen kaloli ba,hatta da zanen jikinta bai wuce dayan biyun ba,kalolin da suka dace da yanayin jikin da aka raɓawa atamfar,dinkin doguwar riga ne daya bude sosai daga qasa,daga sama kuma ya zauna mata cas kamar a don ita aka halicci atamfar dama dinkin gaba daya. Ta lullube kanta da wani madaidaicin mayafi wanda yayi mata aikin mayafin dama dankwalin da bata damu da daurashi ba,sai kwantaccen gashin daya kwanta daga gaban kanta,wanda duk bayan minti daya zuwa biyu take sanya zara zara yatsun hannunta tana jan mayafin tana sake rufe gaban kanta da kyau.


            Wasu lafiyayyun plate shoes ne a qafarta,mahadin qaramar handbag dinta ta kamfanin saint laurent dake ajjiye tsakiyar table din dake gabanta wanda ta gagara zama a kai.


           Duk da daya hannun nata wayarta ce a ciki,amma hakan bai hanata harde hannayen nata a qirji ba, kyakkyawar fuskar nan babu digon fara'a ko daya akai,sai dan qaramin bakinta da take dan motsawa kadan kadan,alamun dake nuni da cewa a matuqar qagauce take da tsaiwarta a wajen.


           Ba ita kadai ba,koda kaine a wajen wala'alla ka shiga sahun masu tayata ginsa da tsaiwar,sakamakon yadda idanu sukayi yawa a kanta a wajen. Duk da cewar wannan din ba shine karo na farko ba a rayuwarta ba,ba koma. Sabo ko baqon abu bane cikin rayuwarta ba,amma a yanzun da komai ya canza cikin rayuwarta,al'amura masu yawa suka kutsa cikin rayuwarta suka kuma shude da abubuwa masu yawa da matuqar muhimmanci a wajenta ya sanya komai ya sauya......ya dasa mata tsanar kowanne kalar kallo da zai fito daga qwayar idanuwan da suka kasance mallakin ƊA NAMIJI,idan ka dauke mutane hudu rakkin dake da matsanancin muhimmanci cikin rayuwarta.


         Har yanzu guri daya idanuwanta suke kalla ba tare data barsu sun gusa da kallon gurin ba ko sau daya,nisan taku masu dan tazara ne a tsakaninsu da budurwar data zubawa idanu,wadda ke tahowa gurin da mabanbancin yanayi tsakaninta da wadda ke a tsayen ta kasa zama, idanuwanta cikin nata tana sake karantar zallar tsanar data yiwa wanzuwarsu a gurin harta iso


"Am very sorry bestie......" Ta fadi a taqaice cikin son kaucewa ganin yanayin fuskarta,ta miqa hannu ta gyara mata zaman kujerar dake bayanta,sannan ta mayar da dubanta gareta


"Have a seat" ta fadi mata suna hada idanu. Tsareta da ido tayi na wasu sakanni,ba tare data shirya ba dariya ta qwace mata,tasa hannu tana qoqarin rufe bakin


"Afifa....." Ta buda baki ta kirayi sunanta da wata irin murya me zaqi da laushi,fararen manyan idanunta na ragaita saman fuskar wadda ta kira da afifan


"Kiyi haquri ki daina kallona da manyan idanun nan naki haka,sai ki saka na daburce,kiyi haquri ki zauna,mintuna kadan zasu kawomin na gaya musu sauri mukeyi" jimmm tayi na wasu sakanni sai kuma tasa hannu ta matso da kujerar dab da ita ta koma da baya ta zauna.


            Hirarrakin mutanen dake zaune daura dasu ta fara shiga mata kunne tana haura mata ka,duk da cewa ba suna magana bane da sauti sosai,zamanta tsakiyar halittun da a wajenta suke masu ban tsoro yasa takejin kamar a kunnenta ake maganar,sai tasa hannu taja jakarta ta fara kici kicin fiddo earpiece ta maqalawa kunnenta ko zata samu sassaucin jin muryoyin da bata qaunar jin irinsu.


        Tsaf afifa ke karantar ta,ta zuba mata idanu tana kallon yadda gaba daya walwala tayi qaura daga kan fuskarta,kamar wadda ke zaman waqafi cikin kurkuku.


          A nutse ta sanya earpiece a dukka kunnuwanta bayan ta sadar dashi da wayarta,tana jin feeling na insecurity a tattare da ita. Duk da taqi yarda idanuwanta su kalla kowanne sashe na wajen,gudun yin tozali da mugayen halittun MAZA dake wajen,amma all her body tana jin akwai wani ido dake karakaina saman jiki da fuskarta,bayan idanuwan da suka jima suna kallonta na mafi yawan mazan dake zaune a wajen.


           Cikin wani irin coolness take latsa wayarta,ranta yazo mata iya wuya,tayi watsi da hirar da afifa keta qoqarin sanyata yi akan dole dole. Rashin samun hadin kan SÃAHAR din ya sanya afifa kama kanta bisa dole,tana zuge zip din jakarta order dinsu ta iso,waitress ta ajjiye tray din a tsakiyarsu cikin nutsuwa da girmamawa,tana kuma basu haquri na delay din da aka samu


"Ki maidashi takeaway" saahar ta fada a taqaice da sassanyar muryarta tana miqewa a nutse,karo kuma na biyu kenan da tayi magana tunda sukazo wajen,ta miqa santala santalan fararen yatsun hannunta tana daukar kyakkyawar handbag dinta tare da zare earpiece din kunnenta ta riqesu a hannu daya,ta tura kujerar baya ta fice a tsakiyarsu tana laluben hanyar fita da kyawawan fararen idanunta da suke da wani irin sheqi da daukar hankali


"Ki making payment kafin ki fita" afifa ta fada a gaggauce tana miqewa hadi da tattara sauran kayansu dake kan table din,tasan tsaf saahar din zata fita ta barta da karbo kayan da kuma biyan kudin.


           Kallo daya ta yiwa gun biyan kudin ta sauya akalarta zuwa parking lot na gurin cikin takunta me jan hankali,koda karen hauka ne ya cijeta ba zata yarda ta qarasa da qafafunta wajen ba,ba don komai ba sai don gun cike yake da maza,mai amsan pyment din,wanda zai bata receipt.....kai kowa da kowa ma,wannan ya qarawa zuciyarta qunci da damuwar data tashi da ita yau,damuwar da bata shura wasu satittika bata tsinci kanta a ciki ba,wani abune daya zame mata tamkar JARRABI,duk kuwa da irin qarfin tuwo dana qwanji da take sanyawa kowacce fitowar rana da faduwarta gurin yaqar komai da komai,tare da sake samun nutsuwa da tabbatuwar binnuwar komai,binnewa ta har abada,saidai tasan cewa......ba komai KADDARA ke shafewa ba.....ba komai tsahon zamunna ke samun nasarar lullubewa ba...ba kuma komai zuciya da ruhi ke sarayarwa shekaru ba.


              Amsa kuwwar sallamar dake ratsowa daga bayanta zuwa cikin kunnuwanta tayi dai dai da sanda take zura key zata bude kyakkyawar qaramar farar motar,cak ta dakata da abinda take shirin yin yanayin fuskarta yana sauyawa kadan kadan kamar wahainiya,kwanyarta ta sarqe da tunani da kokwanton ba ita ake aikewa da saqon sallamar ba,wannan ya bata karsashin sake zura key din tana murzashi.


           Kamar yasan abinda kai kawo a zuciyar tata ya rage mata wahala ta hanyar sake kusanto inda take tsayen yana maimaita sallamar da muryarsa mai sanyi,ta dan runtse idanunta kadan cikin salon da yafi kama da lumshesu sannan ta budesu kai tsaye tana zubesu saman fuskar matashin dake tsaye a gabanta,cikin jikinta tana jin kamar ya yarfa mata garwashin wuta.


            Wani irin kwarjini ya dakeshi,karon farko da ya fara jin irin haka kaf tsayin rayuwarshi akan wata diya mace,cikin salo da gogewa ya dunqule hannunsa yakai bakinsa yana jan gyaran murya tamkar mutumin daya qware,idanunsa cikin nata yana son ya koyawa kansa juriya a kallonta. Ba tun yanzu ba,tun sanda suka wanzu a cikin wajen cin abinci ya fahimci akwai wani kwarjini na musamman a tattare da ita,wanda yayi imanin shine ya zame mata qaqqarfar garkuwa daga zamantowa abar tayawa ko tunkarar kowanne irin namiji,yayi imanin a irin kyan da Allah yayi mata,ba kowanne namiji bane zai iya mata kallo daya ya kauda kansa,koda ya kauda kansa yana da yaqinin ba kowa keda qarfin mallakar zuciyarsa ya hanata qyasata ba


"Am sorry,kiyi haquri na tsaidaki ba tare da nasan naki uzurin ba.....but......da farko dai sunana mahmud,ko zan iya sanin naki sunan tare da yimin alfarmar aron lokaci koda mintuna biyu ne rak cikin tsadaddun lokutanki?" Kyansa,ajinsa da qwalisarsa masu dukan zuciya da idanun kowacce diya mace da suka bayyana muraran basu nata narkakkun idanun da matacciyar zuciyar ke kallo ba,abinda take gani yasha banban da abinda kowacce mace zata hanga daga gurin mahmud din......tafi hangen wata muguwar dabba dake neman abun farauta......muguwar halittar ɗa namiji dake laluben halitta mafi rauni irin ta diya mace ya cutar da ita.......dukansu haka suke!,dukansu halinsu daya!,gaba dayansu basu da tabbas!,babu imani ko tausayi a qirjinsu!. Kalmomin da suka tasowa daga qasan zuciyarta suna mata amsa kuwwa a kowanne kunne nata,suka kuma taso da wani lullubabben yanayi me tarin daci dake danqare qasan narkakkiyar zuciyar dake dauke da tarin ciwo,suka soma sauya kalar launin fatarta zuwa bacin rai qarara,saita juya tana jan siririn tsaki,ta dora hannu zata buda murfin motar ta shige don yiwa kanta katanga da kuma kariya daga shaqar inuwa guda ita dashi.


             Hannu yasa ya dafe murfin motar yana karyar dakai


"Kar muyi haka dake beauty.......kaina bisa wuyana indai cikin kalamaina akwai wadanda suka bata miki rai" sakar masa murfin tayi,taja da baya a nutse ta zagaya daya side din motar,zuciyarta tafasa takeyi kamar ta ballo ta fito daga qirjinta,ta bude kujerar zaman banza ta fada,ta maida murfin ta rufe ta kuma saka lock ta kulle kowanne murfi. Relaxing bayanta tayi da makarin kujerar hadi da lumshe idanunta,don ko inuwar mahmud batason gani a wajen bare mahmud din kanshi,ta fitar da siririyar iska me zafi daga bakinta hannunta na dafe da kanta.


           Ba zata ce ga yadda mahmud yayi yabar gurin ko kuma adadin mintunan daya dauka a wajen ba,itadai taji afifa na knocking glass din,tunda ta buda ido sau daya taga itace,saita maida idanun ta rufe,tasa hannu ta laluba key din ta cire mata lock din hadi da dora key din daga gaban motar.


             Sau daya afifa ta kalleta ta dauki key din ta saka ta tayar da motar ba tare da tace mata komai ba,bata da buqatar ji ko tambayar komai daga bakin saahar,tunda ta tarad da mahmud a gurin,to amma shin rayuwar saahar zataci gaba da tafiya a haka?,da kanta ta bawa kanta amsa ta hanyar girgiza kanta,dole dole......koda zasu dinga fada sau dari a rana suna shiryawa......ya zama dole ta dinga gayawa saahar din gaskiya,koda yau bata gani ba.....koda a gobe bata gane ba zuwa jibi lallai hankalinta zaikai kai,lokaci kuma zaiyi mata aikinsa,da wannan tunanin bayan sun danyi nisa saman hanya,motar shuru kamar kurame ne matafiyan,afifa tayi gyaran murya qasa qasa,cikin nutsar da muryarta tadan kalleta ta gefan ido kafin tace......



FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥

No comments

Powered by Blogger.