Saran Boye 70

 


No. 70


............Sai dai kuma ɗagowar da zaiyi cikin matsanancin fushi sai idonsa akan Momynsa daya yasar a ƙasa. A matuƙar razane yace, “What!!. Momy! Innalillahi wa'innalillahirraji'un”. Cikin karkarwa jiki ya shiga bin ɗakin da kallo, tabbas daga shi sai ita ne, hakan na nufin ba Mira ba. Ƙirjinsa ya sake bugawa da ƙarfi. Yay azamar jawo

rigarsa dake gefe danya saka Madam Chioma da ALLAH yaba damar tashi tai saurin riƙe masa hannu. Dan ita haukanta gaba ɗaya bai nuna mata maganinta baya aikiba. Faɗa masa tayi ajiki tana faɗin, “Haba my boy ya kake abu kamar wani.......”

      Ai kafinma ta ƙarasa ya sake hankaɗata da rawar jiki. “Momy kina lafiya kuwa? Ninefa Yoohan?! Kodai kinsha barasa ne?!”.

       Duk da mamakin yanda yakeyi ya fara sata dawowa hayyacinta, ga zafin maguzar daya sake mata hakan bai hanata sake nufosa ba. Hankalin Yoohan ya sake kololuwar tashi, dan shi yafi tunanin Maman tasa bata a hayyacinta ne. Ta sake riƙe rigar daya ke ƙoƙarin sake kai hannu ya ɗauka tana wani narkewa hawaye na zirara mata. “My boy kaine mafarkina. Kai ne farin cikina. Tunda ka kai shekarun girma ka ɗauke hankalina ga kowanne namiji a duniya. Hatta da papanku baya birgeni gaba ɗaya duk da auren soyayya mukayi. Please masoyina kazo na baka zumar da wata a duniya bata taɓa baka itaba, na maka alƙawari........”

      Duk yanda Yoohan yaso jurewa yama mahaifiyar tasa uziri ya kasa, dan haka ya fisge hanunsa data riƙe wani matsanancin tsoro na sake kamashi. Da sauri ya nufi hanyar ƙofa danya kuɓuta. Sai dai kuma ya sameta gam alamar ta kulle. Sunayen ALLAH ya shiga kira babu ƙaƙƙautawa, yay azamar kaucewa ganin ta sake nufoshi ido rufe. Dan har ta cire rigar jikinta tana ƙoƙarin cire wandon ma.

     Wata azababbiyar ƙara da hatta Miracle da Blessing dake ƙasa a laɓe sai da suka jiyosa ya daka mata. 

        “Momy!!!! Are you mad?!!” Ya faɗa yana hankaɗata da iya ƙarfinsa da matsanancin fushi dan gaba ɗaya hankalinsa ya kai ƙololuwa a tashi. Sai ko gata a ƙasa wanwar. Wata wahalalliyar ƙara ta saki saboda faɗawa datai akan hannun damarta. 

      Ya cigaba da magana cikin fushi na ficewar hayyaci. “Wane irin ruɗaɗɗen al'amarine haka momy? Momy na tabbatar wlhy baƙya cikin hankalinki. Ninefa ɗanki Yoohan. Mikike shirin aikatawa haka?!!.......”

       “Cikar burina John. Idan har bakai tarayya dani ba zan iya halaka Yoohan. Dan ALLAH ka daina ɗaga murya kazo gareni. na maka alƙawarin a yau duk ƙishirwarka ta shekara da shekaru sai na gusar maka da ita, nima ka gusarmin da taw......”

       Da sauri ya tura yatsunsa cikin kunneta alamar baya buƙatar jin kalamanta. Sai da ya fahimci tayi shiru sannan ya nufeta. Da wani irin zafin nama ya kai hannu ya fisge key ɗin ɗakin daya hanga a yatsan hannunta. Ƙara ta saki dan taji zafi. Shiko ko saurarenta baiyina ya nufi ƙofa ya buɗe ya fice. Rasa inda zai dosa yayi a sashen nasa. dan ko ina a kulle yake. Cikin azama ya nufi ƙofar falon ya buɗe dan tabar key ɗin a jiki. Yana buɗewa tana fitowa daga ɗakinsa da jan jiki tana kuka da roƙonsa karya tafi.

         Da wani irin mugun sassarfa ya fice yana karasa saka t-shirt ɗin daya fito da ita a hannu. Wani irin mahaukacin jiri yakeji, kansa tamkar zai tarwatse saboda firgici. Da steps bibbiyu ya sauka a benen. Hakan yasa Miracle dake ɓoye fitowa ta biyosa da sauri tana ƙwala masa kira. Yana gab da ficewa ƙofar falon gaba ɗaya ta riƙo masa hannu. A wani irin juyowa tamkar wani walƙiya yayi sai jin saukar tagwayen maruka tayi a duk kumatunta. Kafin ta dawo hayyacinta ya hankaɗata ya fice abinsa duhu na mamaye masa cikin idanu. Hakan yasa sam ya daina ganin hanyar da yake ajiye ƙafa da ɗaukewa........


★★★

   

           A hankali yake buɗe idanunsa ya saukesu akan Omar dake a kujera zaune. Nauyin da sukai masa ne ya sakashi sake maidasu ya lumshe a hankali. 

       “Sannu Son”.

Muryar Dr Shikurah ta shiga kunnensa. Sake buɗe idon yayi a hankali yana mai juya kansa kaɗan ya kalleta itama. Babu zato sai kawai sukaga hawaye na gangaro masa ta gefen ido. Da ga ita har Omar dake jera masa sannu shima a tsorace suke kallonsa. Dr Shikurah ta shiga jera masa tambayar ko wani waje na masa ciwo ne?.

       Karan farko yay guntun murmushi mai ciwo da ƙunan zuciya. Dan ya tabbatar da ciwon da yakeji a zuciyarsa gara ace duk jikinsane ke masa wannan ciwon da raɗaɗi zaifi masa sauƙin ɗauka. Yunƙurawa yay a hankali zai tashi zauna. Sara masan da kansa yayine ya sakashi saurin dafewa yana faɗin, “Ya ALLAH!”. 

        Da sauri Umar ya riƙosa. Yana faɗin, “Dude be careful mana”. Yayinda Dr Shikurah kuma ta gyara masa filo Omar ya jinginasa a jiki itama tana jera masa sannu tamkar zata fasa kuka. Dan har ikin ranta takejin zafin halin da yake ciki. Gyara masa drip ɗin da ake ƙara masa tayi, kafin ta dubi Omar da shima dai yana cikin tsantsar damuwa. “Omar kodai allurar za'a sake masa ne? Barcin kamar bai ishesa ba”.

     Kafin Omar yay magana Yoohan yay saurin girgiza kansa. “A'a Momy babu buƙatar haka. Bazan iya sake kwana a ƙasar nan ba, dan zuciyata zata iya bugawa.....”

       Cikin katsesa Umar yace, “Taya zakai maganar barin ƙasa kana a cikin wannan halin? kana son yin wasa da lafiyarka ne komi Yoohan?”.

      Kallon Umar ɗin yayi da idanunsa dake jajur yana wani murmushi mai ciwo, gazafafan hawaye na ziraro masa a saman kumatu. “Bazaka ganeba Omar, duk bayanin dazan maka bazaka fahimceni ba. Tafiyata ba itace wasa da lafiyata ba, zamana a ƙasarnan shine wasa da lafiya ta. A yanzu haka inajin tamkar na rufe ido naga bana numfashi saboda ruɗanin da ƙwaƙwalwata take a ciki. Umar ni Momy zata n......”

     Sai kuma ya fashe da kuka mai cin rai batare daya iya ƙarasawa ba. Jikinsa sai wani irin rawa na ɓacin rai yakeyi dan Yoohan akwai zuciya dama. Hankalin Dr Shikurah da Omar ya sake ƙololuwar tashi. Umar ya riƙo hannunsa yana lallashinsa. Amma sam hankalin Yoohan baya a jikinsa gaba ɗaya. Babu abinda ƙwalwarsa ke tariyo masa sai abinda ya faru shi da Momynsa tamkar a film. Gaba ɗaya ƙwalwar kansa da tunaninsa neman jirkicewa suke.

      Wani irin bahagon numfashi ya fara ja da ƙyar alamar motsawar Asthma ɗinsa. Hankalin Omar yakai matuƙa a tashi, dan yasan Yoohan nashan wahala akan Asthma ɗinsa. Takan daɗe bata tashi masa ba. Amma duk lokacin data motsa yana shan wahala sosai. Gashi shi koma yawo da inhaler bayi yakeba saboda yana jimawa bai yiba.

        Ganin abin babbane yasa Dr Shikurah tambayar Umar a ruɗe. 

     Shina Umar ɗin a rikice yace, “Mom yanada Asthma, sai dai tana jimawa bata motsa masaba. Da alama yanzu kuwa itace”.

       “Hasbinallahu wani'imar wakil”. Dr Shikurah ta faɗa tana fita da hanzari.

       Babu jimawa sai gata ta dawo suka shiga bashi taimakon gaggawa ita da Omar. Basu ƙara samun nutsuwa ba sai da Yoohan ya koma barci mai nauyi.

     Cikin sauke tagwayen ajiyar zuciya Dr Shikurah tace, “Omar anya kuwa ba wani abune mai girma ya firgita ɗan uwanka ba?”. Duk da Umar yasan ainahin abinda ya faru. saboda Blessing ta sanar masa ta waya sai ya ɓoyema Dr Shikurahn. “A'a Mom, faɗowar Momynsa daga benen ne kawai ya firgitashi”.

        “ALLAH sarki, ai jikin nata itama da dauƙi, duk da bata farfaɗo ba har yanzun, amma Alhmdllh bataji wani mummunan ciwobama kamar yanda mukai hasashe”.

     “ALLAH ya basu lafiya”. Umar ya faɗa a taƙaice. Daga haka Dr Shikurah ta fita daga ɗakin. 

          Fitar Dr Shikurah ɗakin tayi dai-dai da shigowar Papa da Uncle Joshua cikin asibitin. Dan isowarsa kenan ƙasar ya iske gidansa a harmutse. bayan ya tambayi dalili aka sanar masa Yoohan ne ya yanke jiki ya faɗi batare da ansan dalili ba. Wajen biyosa kuma madam Chioma ta faɗo daga bene. (Dan su iya abinda suka gani kenan. Miracle da Blessing ne kawai sukasan ainahin abinda ya faru. Su kuma babu wanda yace komai. ita dai Blessing tsoron rasa aikinta takeyi. Itako Miracle bamusan dalilinta na ɓoyewarba).

     Sun sanar masa Richard yazo gidan a daidai faruwar al'amarin, shine ya tafi da su asibiti su duka. Wannan shine dalilin zuwan papa a sibitin da hanzari.

        Kasancewar Yoohan sannan likita duk ma'aikatan sun sanshi. papa na ambatar sunansa da kuma tabbatar musu shi din mahaifinsane ko sai gashi an rakosa har office ɗin Dr Shikurah. Itace ta fara kaisu ɗakin da Madam Chioma ke kwance a sume har yanzun, sunata dai tsammanin farfaɗowarta. Duk an mata dressing ciwukan da taji, tare da gyara mata tsagewar ƙashi data samu a hannunta. 

        Papa harda su hawaye yayi na tausayin matar tasa. Dan yasan yanda take tsananin son ɗan nasu. Suko su Dr Shikurah sai faman masa sorry sukeyi. Daga haka suka fito zuwa ɗakin da Yoohan ke kwance shima. Anan ma hankalin papa ya tashi da ganin halin da yaronsa yake a ciki, dan tashin Asthma ɗinsa sunsan bata musu daɗi.    


*_WASHE GARI_*


         Washe gari suka tashi da farkawar madam Chioma. Sai dai tanata faman raki akan hannunta. Dan kuka ta dingayi kashirɓan kamar ƴar yaye. Papa kuwa dake nane da ita yana tayata da tattali. 

      Yoohan kam Alhmdllh tun a daren ya farka. Ya kuma takurama Omar sai ya nema masa ticket ɗin wucewa U.S. duk lallashin da Omar ya dinga masa sam yaƙi saurarensa. Ya dage akan shifa sai ya bari ƙasar. Kuma bayason papa ya sani. dan duk da ya farka duk shigowar da papa yazoyi dubashi sai ya nuna bai farka ɗinba. Badan Umar yaso ba dole yaje ya nema masa ticket, sai dai bana zuwa U.S bane direct. Amma duk da hakan Yoohan yace ya yarda. Sannan yaje gidan ya haɗoma Yoohan ɗin kayansa na buƙatar yau da kullum kamar su waya da sauransu.

     To kuwa a safiyar yau ƙarfe goma batai masa a asibitinba. Dole Omar ya fita da shi a ɓoye batare da ko Dr Shikurah ta sani ba. Shine ya kaisa airport ɗin ma. Yanaji yana gani Yoohan ya wuce ya barsa da damuwa.

      Asibitin ya dawo, inda ya tarar anata neman Yoohan. Shima kawai sai yayi pretending ɗin shiga cikin ƴan nema. Dan baisan wace amsa zaiba papa akan tafiyar Yoohan ɗinba. Bayan kuma shi kansa Yoohan ɗin ya masa magiya da roƙon bayason su papa susan ya wuce da saninsa.  

             Jin Yoohan ya wucene yasake birkita madam Chioma, yanda ta tashi hankalin nata har mamaki ya bama Uncle Joshua shi dai, amma sai baiyi maganaba dan hakan ba huruminsa baneba. Daga ƙarshe ma allurar barci sukai mata saboda yanda take faman rubzar kukan ita dai a nemo mata yaronta. Shi kansa papan itace ta sake birkitasa. Dan yasan dai Yoohan bazai ɓataba. Abinda kawai ya tsaya masa a rai shine minene ya saka Yoohan ɗin tafiya bayan kuma baida lafiya?. Dama tun jiya yaketa tunanin akan faɗuwar da akace yayi babu gaira babu dalili tunda har waya shidai yayi da shi a ranar da safe, kuma baiji wata damuwa tattare da yaronsa ba a lokacin da shuke wayar. Dan shine ma yace karya faɗama Momyn nasu zai dawo a jiya yana son ya mata surprise ne. Har Yoohan ɗin na masa dariya akan hakanma. Sai kuma gashi ya dawo ya iske waɗanan rikitattun tashin hankali da gaba ɗaya ya rasa makamar riƙewa akan faruwarsu.

  


___________________


       Nu'aymah na gidan Juliet Omar ya kira akan taje gida ga Yoohan nan a hanya. Abin ya bata mamaki dan sunyi da shi sai nan da sati biyu ma zai koma. Haka dai tai shiri ta koma gidan nata ttareda Juliet da tai mata rakkiya danta tayata gyara waje. Duk da ma tasan baza'a samu datti sosai ba tunda duka yau kwananta biyar da barinsa.

     Babu dattin dai kam sosai. Amma sai da suka gyara komai tsaf. Juliet ta tayata sukai har girki saboda tausaya mata da takeyi na halin da take a ciki. Sai da suka gama komai tsaf sannan ta wuce tabar Aymah na wanka.  

       Bata wani jimaba ta fito tai shiri cikin doguwar rigar atanfa mai faɗi data ɓoye cikinta. Wayarta ta ɗauka ta nufo falo dan yunwa takeji ta bala'i. Turus ta tsaya tana kallon Yoohan dake kwance a kujerar falon idanu a lumshe. koda wasa bataji motsin shigowarsa gidanba sam. Cigaba tai da takawa a hankali inda yake. Batare da tayi magana ba ta zauna a gefensa da kai hannunta ta janye nasa hannun daya dafe kai da shi.

      A hankali ya buɗe idanunsa dake jajur ya zuba mata su. Itama kallonsa take cikin ido sosai. Sai kawai yaji zuciyarsa ta ƙara raunana. A take hawaye suka cika idanunsa. Ɗayan hannunsa ya kai saman cikinta yana murmushin ƙarfin hali.

     Ita dai Aymah kallonsa take tamkar wata sokuwa, dan yanzu kam sai dai ta bama wani labarin mijinta badai ita a bataba. Cikin sanyin murya tace, “Baka da lafiya?”.

        Haɗiye abinda ya tsaya masa a maƙoshi yayi da ƙyar, sannan ya yunƙura ya tashi zaune yana cije baki daboda kansa dake masa ciwo har yanzun. Zama yay da ƙyau ya rungumota jikinsa, hannunsa nakan cikinta yana shafawa a hankali. Cike da raunin murya yace, “I miss you Sweet girl”. 

       Maimakon ta amsa masa sai ta ƙara jefa masa kalar tambayar ɗazun. Murmushi ya sakeyi da sumbatar kanta. “Lafiya ta ƙalau baby, sai dai kewarki ce”. Duk da Aymah bata yardaba saita ƙyalesa kawai a hakan. Itama ta rungumesa tare da haɗe bakinsu waje ɗaya. Duk da ciwo da ƙunar da yakeji zuciyarsa na masa bai hanashi bata haɗin kai ba. Tsahon mintuna uku suna a haka kafin ta janye bakinta a cikin nashi suna maida numfashi. Batare data bari wani cikinsu ya sake magana ba ta kama hanunsa suka wuce bedroom. Sai da ta rakasa har bayi, duk da tana fama da kanta ta taimaka masa yay wanka. Da suka fito ɗinma da taimakonta ya shirya sannan sukai salla.

       Bata samu matsala da shi ba sai a wajen cin abinci, dan cayay mata shi ya ƙoshi. Hankalin Nu'aymah ya sake tashi matuƙa saboda ta kasa gane kansa gaba ɗaya. da ƙyar dai ta samu yaci kaɗan ya sata ta ɗakko masa magani ya duba wanda ya dace ya sha. Bedroom ya koma ya kwanta daga haka sai barci.

      Gadon tazo ta sauna tai tagumi kawai ta zuba masa idanu tana kallonsa cike da tausayi da damuwa akan da tasa damuwar data fahimci yana son ɓoye mata ne kawai.


*_KANO NIGERIA_*


           A lokacin da madam Chioma ke can neman sa'a akan Yoohan anan kano su Little bee ne suka samu damar ƙwamushe Rabi mai aikin su Aymah da ta zo yima Umm aika a kasuwa. 

     Tunda ta fito gida suke biye da ita batare data sani ba. Sai da tazo bakin titi domin tsallakawa taga mota a gabanta kawai. Kafin ta wani yunƙuri aka fisgota ciki tare da daɗe mata baki yanda ta kasa ihu. Daga ƙarshe ma suka danna mata allurar data bugar da ita. Harko suka iso garin abuja bata sake sanin ina hankalinta yake ba, sai wayar gari tayi taga kanta a wani ɗakin da bata saniba. Da matuƙar tashin hankali ta tashi tana ƴan waige-waige, sai kuma ta fashe da kuka ganin da gaske dai fa baƙon waje aka kawota......

        Tsawar da aka daka matane ta sakata sake gigicewa harda sakin guntun fitsari. Murɗeɗen ƙatone da iya gani kasan ya damƙi namiji ma sai ya shinshino ƙamshin lahira bare ita mace da girma ya kama. Abincin hannunsa ya dangwarar a tebirin ɗakin dake tare da kujera ɗaya. Sai yololuwar guntuwar katifar da Rabi ta kwana agefe. Da tsananin kaushin murya yace, “An gaya miki nan gidan kuka ne. Karna dawo na samu wannan abincin da hawayen fuskanki”. Ya ƙare maganar da juyawa ya fita abinsa.

     Tashin hankali iya tashin hankali Rabi ta shiga. Hakan yasa ta share hawayen nata ta zauna ta fara cin abincin data san bazata ƙoshiba. Ga uban yaji a ciki na tashin hankali. Amma tasan inhar batacinba yunwa halakata zatayi. Mutumin nan kuma kashetama zai iyayi ƙila. Sai da ta kammala da kusan minti talatin, zuwa lokacin yajin ya gama wajiga rayuwarta sannan aka kawo mata ruwa rabin gora. Jikinta har rawa yake wajen ɗauka ta sha, dan ita kaɗai tasan a tashin hakalin da take ciki game da cin yajin nan...


      Haka aka ringa wajiga rayuwar Rabi har tsahon kwana goma. Tayi kuka harta rasa hawayen zubarwa. Sai da suka tabbaar tayi laushi iya laushi sannan suka nema su sanarma su Yoohan. Sai dai an samu akasi Yoohan ya wuce U.S sai Omar kawai ne ya amsa zaizo, dan jikin madam Chioma yayi sauƙi sosai anma sallameta tun kusan kwanaki uku kenan, satinta ɗaya a asibitin. Ranta dai na nan danƙare da damuwar rashin sanin inda Yoohan ya nufa da kuma rashin samun cikar burinta. Duk da tun a asibiti sun yake magana da Rebecca zasu koma gidan Bangaruta, sannan Marcy ma tace zata rakata wajen wani bokan a Lagos.


____________★


          Bayan isowar Umar kai tsaye office ɗin Dawood sukaje. Sai da sukai zaman jiran Bilkisu Adam Makaho, mata ga Oga Jay sannan, dan itace oga kwata-kwata akan case ɗin. Tana isowa kuwa suka amsa kira ta hanyar telephone.

       Sun sameta a office ɗinta. Bayan sun gaisheta ta basu iznin zama. Sam babu wasa tattare da ita, dan yanzu bayan miskilancinta girma ya ƙaru ga daraja. Babbar Officer ce da aikinta ke girgiza sansanin duk wani mai kunnen ƙashi. 

    Batare data kallesu ba tace, “Dawood azomin da matar nan”.

     “Okay maa”. Dawood ya faɗa da sauri yana miƙewa. Kusan mintuna goma sai gashi ya dawo tare da Rabi dake wujiga-wujiga, dukta fita hayyacinta a kwanaki goma kacal. Kuma babu zagi babu duka. Zai gurfanar da ita a ƙasa Bily ta hanashi. Wata kujera dake can gefe ta bashi umarnin ya bama Rabi ta zauna. Shi dai Omar nata kallonsu ne da mamakin ganin yanda Rabi ta koma. Gashi kuma ko ƙwarzanen duka shi dai bai gani a jikinta ba. Itako bama ta gane Umar ba saboda a jigacen da take.

          Little bee ce ta shigo bayan tayi knocking an bata izini. Tai salute ɗin mahaifiyar tata kuma ogarta a wajen aiki kafin ta ajiye takardun hannunta a tebir ɗin. Takardun Bily taja gabanta ta duba kafin ta ajiyesu gefe ta kalli Rabi.

        “Nasan dai zuwa yanzu kinsan a inda yake ba wajen wasan nanaye bane. Dan haka ya rage ruwanki nutsuwa ki bamu duk amsar tambayar da zamu miki, ko kimana ƙarya”.

      Muryar Rabi na rawa tace, “In ALLAH ya yarda bazanyi ba ranki ya daɗe”.

      “Wannan ya rage naki”.

Bily ta faɗa cikin halin ko in kula tana sake ɗaukar takardun da Little bee ta shigo da su. A gaban Rabi ta diresu dai -dai lokacin da fuskar Yoohan dake zaune a office alamar yana a asibiti ta bayyana a cikin lap-top ɗin da Omar ya ajiye inda Yoohan zaiga kowa dake office ɗin.

        “Wannan takardun bayanai na duk abinda ke cikin wayarki. Randa kika sayi layi, randa kika fara ɗorashi a waya. Sau nawa kina canja shi a wasu wayoyi. Mutanen da kika taɓa kira ko suka kiraki duk akwai bayanansu anan. Dan haka ki nutsu sosai”.

        “In ALLAH ya yarda ranki ya daɗe”.

       Kallon sashen da Dawood da Little bee suke Bily tayi, kafin ta kalli lap-top ɗin. Kai Yoohan ya risinar cike da girmamawa ya gaisheta. Itama ta amsa masa da kulawa kafin ta nuna masa Rabi.

     “Ina fatan kana ganinta da ƙyau?”.

“Yes maaa!”.

        Duk da Rabi ta kalli fuskar lap-top ɗin itama bata kawo komaiba, tadai ga kamar hoton mijin Nu'aymah, kafin tunaninta ya faɗaɗa Little bee ta katseta da faɗin, “Minene sunanki?”.

         Murya na rawa tace, “Rabi?”.

“Shekararki nawa kina aiki a gidan Sheikh Soorajidden Hashim Jibiya?”.

       “Goma sha takwas. Dan an kainine lokacin matarsa nada tsohon cikin dake wahal da ita dan na taimaketa”.

    “Kin taɓa aure?”.

             “Eh na taɓayi harda yarana biyu”.

  “Keda ke aure miya kaiki gidan aiki har tsahon wannan shekarun?”.

      “Ranki ya daɗe ai auren ya mutu ne a wancan lokacin. To domin neman na kaina saina samu aikatau ɗin dan nayi saboda iyayena duk sun rasu ni marainiyace”.

       “Ƙwaɗayin zama gidan masu kuɗi yasa baki sake tunanin sake ƙara aure ba kenan?”.

       Shiru tayi kanta a ƙasa ta kasa bada amsa. Shima Dawood da yay maganar sai ya shareta da ga haka ya sake jeho mata wata tambayar.

     “Waye ya kaiki gidan?”.

A take ta ruɗe jikin na rawa, sai in ina take ta kasa bada amsa. Hakan yasa Dawood daka matsa gigitacciyar tsawa. Fashewa Rabi tayi da kuka. “Dan ALLAH ku gafarce ni zan faɗa”.

     Babu wanda ya tanka mata. Sai bindiga da little bee ta ciro a gefen ƙugunta ta dire a gaban Rabi. Hakan yasa ta kuma diriricewa. Cikin hadiye kukanta tace,

       “Ranku ya daɗe ni bansan ainahin wadda tasa aka kaini gidan ba. amma naje ta hannun wata matace amma yanzu ALLAH yay mata rasuwa”.

       “Oho, idan na fahimci amsar nan taki kenan dama an kaiki gidan ne da wata manufa? Ba wadda kike a wajenta bace tasa aka kawoki gidan!!”.

     Yoohan yay magana a matuƙar zafafe. Maimaita mata Dawood yayi da hausa. Dan duk da Yoohan ya haɗa da kalmomin hausa a maganar Rabi bata fahimta da ƙyau ba. Amma shi Alhmdllh yana fahimtarta sosai tunda jin nasa yafi faɗi da baki.

       A take Rabi ta ƙara rikicewa, dan har ga ALLAH tazatafa hoton Yoohan ɗinne kawai a wajen. Suma dai su Bily yanda yay maganar duk sai da ya sakasu kallonsa. Tebir ɗin Little bee ta daka da hannu, da tsawa tace, “Ki basa amsar tambayarsa malama kin ɓata mana lokaci”.

       Jikin rabi na cigaba da rawa tace, “Ranka ya daɗe ba haka nake nufi ba. Ni dai kawai an kawonine na kula da mai ciki, daga haka babu wani dalili dana sani na rantse muku da girman wanda ya halicceni”.

      A karan farko taji saukar mari mai gigitarwa a fuskarta. Kafin ta dawo hayyacinta Dawood ya ƙara mata wani. Sannan kuma Bily dake zaune duk tana kallonsu ta hanata kuka. Dole Rabi ta haɗiye hawayenta sai ajiyar zuciya.

     Dawood yace, “Inhar zakiyi mana ƙarya to zakiyita amsar irin waɗanan marukan babu ƙaƙƙautawa. Wa kikema aiki a gidan?”.

     “Wlhy yallaɓai iya gaskiyata nake faɗa muku. Bani yima kowa aiki sai Hajiya Firdausi matar Sheikh Sooraj ɗin”.

           Sai a yanzu Umar yay magana. “Eh ansan dama ita kikema aiki a zahiri. a baɗini kuma akwai ogarki mai sakaki shiryamata sharri ita da tilon ƴarta. Bayan ƙyautatawar data dinga miki a rayuwarki na tsahon shekaru goma sha takwas”.

       Dawood ne ya sake fassara mata. Dan haka cikin rawar harshe da kuka mai cin rai tace, “Na rantse da ALLAH. wlhy tallahi ban taɓa cutar da Hajiya Firdausi da zuriyar ta ba. Ko Nu'aymah da muke yawan faɗa wani lokacin ina takalartane kawai wlhy saboda nasan bata barin saita kwana. Amma bada wata manufaba. Ko a mafarki bana fatan na cutar da waɗan nan bayin ALLAH ai balle a zahiri”.

       Cike da ɗaurewar kai suka shiga kallon juna. Amma duk da haka bayan Dawood ya gama sanarma Omar abinda ta faɗa sai Umar ɗin ya bada vr ɗin nan na kwanaki da sukaji tare da Nu'aymah. Aka kuma tabbatar mata a wayar wanda aka samu.

       “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ni Rabi. Wlhy wlhy kinji na rantse ni ban taɓa waya da mai aikin Nu'aymah ba. Hasalima sam ban santaba tunda randa akazo za'a wuce da ita abuja a sashen hajjo Umm taje ta sameta itama. Yanzu haka ko zaku kasheni bazan iya nuna fuskartaba balle harna samu Number ta nayi waya da ita akan Nu'aymah. To niko idan ta faɗamin halin da Aymah ke ciki gidan aurenta ribar mi zanci bayin ALLAH?”.

        Tsawa little bee ta daka mata. “K bama son rainin hankali. Idan kince bake bace waɗan nan lambobin dake akan wayarki harda ta Uwaliya ɗin na uwar waye? Wa kuma ya sakasu da har zaiyi zaman magana da su a wayarki batare da kin saniba?”.

       “Wlhy iya gaskiyata nake faɗa muku. Ni yanzu haka ko waya zanyi ma sai naba Muhammad ya dubamin lamba. Dan shine kemin sebi idan ko zansa lambar wani ɗan uwana. Idan kuma zanyi kira shima ke dubamin abinda ya samun dan banyi boko ba. Da Nu'aymah ko Adawiya kemin, to sai suyita jamin rai, shine na koma bama Muhammad ganin ya iya. Amma ni lambar ma ƴan gidan bata kowa gareniba wlhy”.

     Hannu Dawood ya ɗaga zai ƙwaɗa mata mari Bily ta dakatar da shi. Dan ita duk shirun datai musu nazarin komi takeyi. sannan kuma Jay ma duk yana saurarensu daga office ɗinsa ta hanyar na'ura. Shinema yay saurin cema Bily ɗin kar Dawood ya mareta yanzun ta hanyar abibda ke a kunnenta da su basu fahimta ba.

     Dakatawa kuwa Dawood yayi yana huci. Bily dake kallon Rabi cike da nazari tace, “To amma ranar da Nu'aymah tai bleeding ko zamu iya sanin miya faru? Dan bincikenmu ya nuna mana kece kika bata abu na ƙarshe tasha a gidan. Daga haka ta fara ciwon ciki sai jini kuma ya ɓalle”.

      Shiru Rabi tayi tana tunani dan tama manta. Sai zuwa can kuma tace, “Lallai kuwa ranki ya daɗe kamar anyi hakan. Ta sakani na dafa mata ruwan shayi baƙi”.

       “Kenan a ciki kika saka mata maganin zubda jini da aka ɗauka cikine ta zubar??”..............✍

       


*_Tofa masu karatu man kai na fa zai fara malalewa a dalilin amsoshin Rabi, nama rasa mizan tunano kuma. amma bari mu bita muji wace amsa zata bada a gaba??😱🤧._*


No comments

Powered by Blogger.