Saran Boye 68

 


No. 68


............Sun fito har ƙofar gida Muhammad biye da su zai mata rakkiya. Shima Jay ya jashi a jiki da kulawa. Anan ne yake tambayarsa miyyasa yaga yana fushi. Hawaye cike da idonsa yace, “Uncle Please ka bar mana Aunty anan ta zauna. Kaga Aunty N Uncle Yoohan ya gudu min da ita. sai ni kaɗaine a sashenmu. Ni kuma inason na dinga ganina da abokiya kamar Aunty N”.

      Cike da ƙaunar yaron Jay ya sumbaci kumatunsa yana ƴar dariya. Yace, “Oh woow sarkin wayo. inko hakane na maka alƙawarin Aunty Afrah zatazo maka hutu dan tana hutu dama yanzu haka”.

     Cike da ɗoki Muhammad yace, “Uncle yaushe?”.

     Yanda yayi ɗin har saida yasa baba malam da Afrah da Jay dariya. Jay yace, “Karka damu zaka iya ganinta a koda yaushe”.

      Duk da Muhammad yaso jin ranar da zatazo dai sai yayta ɗoki. ya koma cikin gida da gudu ya sanarma Umm.


     Bayan wucewar su Jay da kwana biyu Muhammad ya addabi su baba malam da zancen yaushe Aunty Afrah zata zo? Shifa idan bazatazoba to shi a kaisa gidansu yay hutu. Ganin ba hutu suka samuba shi sai baba malam ɗin ya kira jay da bukatar yaushe Afrah zata zo ɗin. dan sufa an saka musu zuma a baki kuma duk sun ƙagu. Hakan yama Jay daɗi, dan shirinsu na tafiya yanda ya kamata cikin rahamar ALLAH.

      Bai wani ja zancenba yace zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zai kawota da kansa insha ALLAHU. Wannan shine dalilin samun ƙofar shiga gidan su Nu'aymah da Afrah ta samu domin cika aikin ysyarta. Dan haka a safiyar yau kuma lahadi ta tashi da shirin tafiya can zatai zaman wata ɗaya rak insha ALLAHU.

     

      Sai karfe biyar na yamma Anuwar ya gama shirin kai Afrah kano gidansu Aymah. Dan haka bayan ya kammala shirinsa tsaf ya saka Al-hassan Ya kira masa ita a can sashen Uncle Anuwar. Dan ita acan take zaune kamar yanda little bee ma acan tai rayuwarta har tayi aure. Tsakaninta da sashen iyayenta sai dai tazo gaisuwa kawai ko hira. Amma ita Uncle Anuwar da aunty Nabeelah ne iyayenta. Sauran yaran kuma Miemaa da Abie.

      Tana zaune a falo hankalinta akan lap-top tana hidimarta Al-hassan ya shigo  da sallama. Kasancewar yayima Aunty Nabeelah laifi yau da safe. ta kuma tabbatar masa idan ta kamashi sai ta zanesa sai ya dogare a bakin ƙofar yana kalle-kalle. Daga can yace, “Aunty Afrah kizo Abie na kiranki”. Bai jira ko amsarta ba ya shilla waje da gudu saboda leƙowar aunty Nabeelah dake kitchen dan jin muryarsa da tayi.

     Aiko mi Afrah zatai inba dariya ba. Tace, “Mamma wlhy kin hana auta Sukunin shigowa sashen nan yau gaba ɗaya. Ɗazun ina kallonsa daya hangoki kin fita har faɗuwa yake wajen tiƙar gudu zai shige sashensu”.

     Dariya Nabeelah tayi itama da faɗin, “Ai ya gama gudunsa babu fashi saina ruɗa masa jiki da bulala tunda shi bayajin magana. Iskancin yaron nan baya tashi sai ya ga su Miemaa na gida. To in ALLAH ya yarda shi abin nema da tsokana ya samu a wajensa tunda yasan basa bari a taɓasa”.

      Miƙewa Afrah tai tana dariya da zura Slippers a ƙafarta. “A daiyi haƙuri Mamma na. Bara naje Abie na kirana inaga ya gama kimtsawa”.

      A take mood ɗin Nabeelah ya canja. Cike da damuwa tace, “Kai ni dai wannan aiki nasu Abie yana moremin, da ƙarfi da yaji ya maida kowa jami'insu a gidan nan, ALLAH banason kina nesa dani ko kaɗan. Amma yaya zanyi, nanda lokaci kaɗanma zaki gudu gidan aurenki ki barni da kewa ta haƙiƙa kamar yanda little taimin. 

      Ƙasa Afrah tayi da kanta kawai cike dajin kunaya. Sai dai bata iya cewa komaiba dai.

        Sallamarta Nabeelah tayi ta tafi dan tasan Jay jiranta yake. Ilai kuwa ta iskesu a falonsa shi da Miemaa suna jiranta. sai da tayi sallama suka bata izinin shiga sannan ta shiga. Bayan ta durƙusa ta gaishesu ne Jay ya nuna mata gabansa alamar ta zauna. Babu musu tazo jikin ƙafafunsa ta zauna cike da ladabi da ƙaunar iyayen nasu.

      Gyaran murya Jay yayi yana kallonta fuska babu wasa. Yace, “Afrah!”.

       “Na'am Abie”. 

Ta amsa masa kanta a ƙasa.

      Zamansa ya sake gyarawa sannan ya cigaba da faɗin, “Inason ki nutsu ki saurareni. Duk da bani da fargaba a kanki game da aikin nan tunda nasha sakaki inason sake jaddada miki muhimmancin na wannan lokaci. Kisa hankalinki da ƙyau dan banason kuskure a ciki. Baba malam yanada muhimmanci mai girma a gareni dake kanki. Inason kiyi komai da ƙwazo da hikima ok?”.

       “Insha ALLAHU Abie zanyi duk yanda kace. Kuma zan kula nayi komai yanda ake buƙata. Kudai tayani da addu'a”.

        “To Alhmdllh, addu'a kuwa dama akoda yaushe cikin yi muku ita muke. ALLAH ya baki nasara yay riƙo da hannunki kiyi komai cikin sauƙi. Wannan camaras ne”. Yay maganar yana miƙa mata wasu ƴan ƙananan dutsuna tamkar diamonds kusan goma. “Dasu zaki tafi, inason kibi duk sashen gidan ki maƙalasu a kowanne parlors. Idan sun wadata har Backyard na gidan dan suma wajene da masu baƙin hali zasu maƙale suyi magana. Ki ajiyesu da tsantsar kulawa yanda babu wanda zai gane minene. Duk da nasan koda a zahiri suke bawai ganewar zasuyiba inba dai ganinsu da yawa yasa suyi tunanin wani abun kuma daban ba. Inhar kika samu nasarar saka cctvs ɗin nan a ko ina na gidan to aikin zaizo da sauƙi insha ALLAHU. Dan zasu bamu damar kula da motsin kowa hankali kwance. Banason Little da Dawood susan komai kan camaras ɗin nan, wannan aikinane ni kaɗai zakimin.  Abu na biyu shine saka ido akan duk wani baƙo da zai shigo gidan. Ma'aikatan gidan da yaran gidan suma. Banda wauta da surutu mara amfani, duk da namasan waɗanan ba halayenki bane. Biyayya ga nagaba. Aiki basai ance tashi kiyiba tunda nasan iyayenki sun tsaya akanki babu abinda baki iyaba. Dan ALLAH ki kula da mutuncin kanki dan gidane family house akwai samari a ciki. Duk da har raina bana zargin rashin tarbiyya daga wannan zuri'ar koda a mafarkina. Amma dai dolene na jadada miki kame kanki da kuma kula da ibada dan na fahimci aikin zai kaiki har cikin azumi dake gabatomu”.

        “Inasha ALLAHU Abie zaka sameni mai kiyayewa”.

    “To ALLAH yay miki albarka da sauran ƴan uwanki baki ɗaya”.

      Amin ta amsa ita da Miemaa dake saurarensu. itama daga baya ta ɗora da nata nasihan da wasu dabarun aikin. Duk da kuwa tunda aka tsura maganar cikin koya mata take salo-salo harma Jay din kansa. To Alhmdllhi kuwa tana haddace komai. Dan dama itama bata wasan yara bace wajen tsayawa tsayin daka akan aikin nan da ba yau iyayenta suka fara tsundumata a ciki ba. 


        Anuwar da kansa ya kai Afrah ɗin Kano. Dan akwai harkar business ɗinsa da zaiyo acan. Koda jirgi ya diresu kuwa ana sallar magriba. Amma duk da haka sai ya fara kaita suka gaisa da baba malam yay sallar har isha'i acan sannan ya wuce nasa harkokin. Duk da baba malam ɗin yaso ya kwana anan amma fir ya ƙi saboda uzirinsa.

         Da ga Muhammad har Umm sunyi matuƙar jin daɗin zuwan Afrah. Dan gaba ɗaya saita ɗauke musu kewar Nu'aymah. Tun a daren Umm ta kaita sashen hajjo ta gaisheta. Nanma ta samu tarba sosai a wajen ƴar tsohuwar. Dan nutsuwar Afrah ɗin ya saka hajjo jinta a ranta. Taita tsokanarta kuwa tamkar yanda takema jikokinta idan taso. Afrah komai bata iya cewa sai murmushi. Dan miskilace ta gaske itama kamar little. Tama dama Jay da bily ɗin a miskilanci dan ta gada a uwa da uba da yaya. Idan kaji tana hira da dariya to Mammata ne (Nabeelah) ko Daddynta (Anuwar). Sai ko Miemaa da Abienta shima.

       Basu baro sashen hajjo ba sai lokacin kwanciya. Umm ta kaita ɗakin Aymah da aka gyara mata tsaf, kayantama tuni suna can. Sosai ɗakin yayma Afrah ƙyau. Taita kallon hotunan Nu'aymah da aka mammaƙala a bango. A hankali tace, ‘Masha ALLAH ƙyaƙyƙyawa da ita kuwa’.


_______________★★★


           *_U.S_*


   Sosai Nu'aymah batajin daɗi. Dan ma Juliet tsaye take sosai wajen kula da ita. Dan ta fahimci laulayin ciki takeyi. Sosai taji tausayin yarinyar ya kamata. Yaushema aka gama rainonta da za'ace itama ta samu ciki. Gaskiya tana mamakin ganganci irin na baƙar fata. Kasa haƙuri tayi sai da taima Omar wannan complain ɗin. Shiko yay dariya tare da mata faɗaɗɗen bayanin data gamsu, harta koma bin Nu'aymah da addu'ar fatan sauka lafiya.

              Duk da Aymah tanata ɓoyema kowa halin da take ciki na ciwon da ita ɗauka take Thypoid ɗinta ne ya motsa yau dai ta tonama kanta asiri batare data farga ba. Dan suna waya dasu Umm da Muhammad ya takura a kira a kirata ya sanar mata yayi sabuwar Aunty. Bayan sun gaisa da Afrah da Muhammad ɗin Umm ta amsa wayar suka gaisa itama. Cike da shagwaɓa Nu'aymah tace, “Umm Yah Yoohan yazo?”.

      “Oh dama ya shigo ƙasar?”.

“Eh Umm. Yaufa kwanansa uku”.

      “To Abbanki ya manta, ni koma maganar bamuyi da shi ba. Amma kinsan shi da uziri, nasan zaizo insha ALLAH”.

       “Umm idan yazo kiyi min yajin daddawa da farin yaji, da ɗan wake, da alawan madara, da iloka. Da fara. Da manja. Da aya suyan gishiri. Da.......”

       “Oh ni Firdausi wannan lissafin kumafa Nu'aymah?”.

       Baki ta tura gaba kamar tana gabanta. “Umm duk so nakeyi fa dan ALLAH”.

       Ɗan jimmm Umm tai na hasashe. Sai kuma tace, “Niko Nu'aymah ai period ɗinki ya dawo ko?”. Tai mata tambayar cike da salon bugar ciki irin na manya. 

      Zimbir Nu'aymah ta miƙe zaune. Dan ita kuwa man kanta ma ya tsiyaye tas ta shafa'a da zancen rashin ganin period. Ai idanma bata manta ba rabonta da jini tun na abinda ya faru. A randa ta fara jin alamun zuwansa kuma Accident ɗin nan ya faru suka wuce Austria. Daga nan bata saniba tayi ko batayi ba? Tunda bata cikin hayyacinta........

      “Kinajina kuwa Nu'aymah?”. Umm ta katse mata tunani. 

    Da ɗan rawan muryan shiga ruɗani tace, “Umm wlhy ni tun na lokacin nan ban sakeyiba. Na shiga uku Umm na kamu da wani ciwo ko?”.

      Dariya ce taso kufcema Umm, amma sai ta gimtse da sauri tana saurin faɗin, “A'a lafiyarki ƙalau. Inaga saboda kinyi wancan rashin lafiyarne shiyyasa. Zanma mijinki magana ya baki magani”.

     Cike da sanyin murya tace, “To Umm. Amma dan ALLAH ki haɗamin duk abinda nace idan Yah Yoohan zai taho yazomin da su. Harda garin dawa na tuwo fa Umm. Da daddawa da kuka da bushashshen kuɓewa dan ALLAH”.

         “To zan haɗa miki duka insha ALLAH. Amma kayan kamar zasu masa yawan ai Nu'aymah”. 

     “Ni dai Umm dan ALLAH ki taimakeni. Wlhy duk banason abincin garin nan yanzu. Coffee kawai nake iya sha sai gasashen kofi. Amma sauran abincin da naci sai nayi amai. Abincin Austria yafi na nan min daɗi”.

       Umm dai na murmushi ta amsa mata. Daga haka sukayi sallama dan Juliet jiranta suke zasu fita shagon shan coffee ɗin na ƙa'ida. Itama taɗan motsa jiki daga can.


____________★★★


         Tunda ya kawosa hotel ɗn ko sau ɗaya bai tambayesa miya fruba. Shi kuma baice dashi komaiba dan ransa a ƙololuwar ɓace yake. Yadda Al-qur'anin nan yafi komai zafafa masa zuciya. Dan har yanzu fushinsa yaƙi sauka. Daya rufe ido dan yai barci sai ya hango Qur'an a ƙasa a yashe. Daga ƙarshe dai har dasu yin hawaye.

      Sanin halinsa idan yay fushine ya saka Omar yanke shawaran kiran Nu'aymah. Juliet ya turama text message dan taja ra'ayinta.

       A lokacin basuyi ko mintuna biyar da shigowa gidan ba. Aymah na kwance a falon saman tiles idonta a rufe. Sai dai ba barci takeba. Hasalima tunanin Yoohan takeyi dan rabon da suyi waya tun jiya da yace mata zai koma Abuja daga kd....

      Gyaran muryar da Juliet tayine ya saka Aymah buɗe ido tana kallonta. Juliet ta ɗaga mata gira ɗaya tana murmushi, yayinda duk hannayenta ke akan cikinta tana shafawa. “Da zaman tunani ai gara kiyi kiransa” tai maganar cike da tsokana. Murmushi Nu'aymah tayi da gyara kwanciyarta tana fuskantar Juliet ɗin. “Ke dai faɗa mana gaskiya. Ko kina kewar Yah Umar ne ni zaki nanamin?”. Kusan a tare suka kwashe da dariya. Juliet ta miƙe tana faɗin, “1-1 kenan. Ni bara naɗan watsa ruwa na kwanta”.

        Juliet na shigewa Aymah ta sauke numfashi. Cike da son jin muryarsa kuwa ta lalubo hotonsa a wayarta tana kallo. Kamar kuma an tsikareta sai kawai tai kiransa. Shigowar kiran Aymah yayi dai-dai da sake sakkowar hawayen Yoohan. Dan ji yake kamar zuciyarsa zata ƙone. Sam dukan da yayma Gebrail ɗin bai wadacesaba....

     Kamar bazai kula wayar ba sai kuma ya buɗe idanu a hankali. *_My Sweet girl_* daya ganine ya sakashi ɗauka a kasalance. A kunne kawai yasa batare da yayi magana ba. Daga can Aymah ta sauke sassanyan numfashi. Sai dai itama batayi maganarba. Sun share kusa sakan goma sannan ta ƙara sauke numfashi da faɗin, “My boo yau miskilawan ne a kusa?”. Shiru baiyi maganaba. Hakan yasata fahimtar akwai damuwa. Dan a ɗan zamansu ta fara fahimtar wasu da yawa halayensa. Musamman fushinsa da farin cikinsa. Kwanciya ta gyara tana lumshe idanu. Cike da nutsuwar data ɗan farayi na wahalar ciwo tace, “Waya taɓa ɗan lelen Abba ne? To lallai ya nema wajen ɓuya tun kafin na kira Abba na sanar masa ɗan lelensa na fushi da kowa har Silly girl ɗinsa”.

       A bazata murmushi ya ɗan kufce masa. Sai dai idanba lura kayi ba bazaka taɓa fahimtar yayinba. A hankali yace, “Parrot, ke dai bakison barin bakin mutane ya zauna shiru”.

     Baki ta kumbura cike da sakalci tace, “Ai yanzu parrots ɗin biyu ne. Dan kaima ALLAH ka shigo tawaga Yah Yoohan”.

     “Silly girl”.

Ya faɗa yana gyara kwanciyarsa.

      Murmushi tayi mai faɗi tana lumshe idanu. Sai kuma ta dai-daita muryarta, cikin nutsuwar da inta gadama zaka sameta da ita tace, “I'm so sorry My Handsome. Nifa kaga idan aka bani haushi a gidanmu mi nakeyi da?”.

       Yace, “Uhm-uhm”.

Sake gyara kwanciyarta tayi tace, “Sai in ɗauki Al-qur'ani naita karatu. Zakaga inata kuka a farko, kafin wani lokacin kuma sai na samu nutsuwa na cigaba da karatun da nishaɗi. Cikin amincin ALLAH bana ajiye Qur'anin nan sai zuciyata tamin sanyi”.

      Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke. Murya da matuƙar sanyi yace, “Zeeynab I love you. Ke ta dabance a rayuwata”.

      Murmushi tayi kawai. Kafin a hankali tace, “Thanks you Uncle Boo”.

     Kansa ya jinjina mata a hankali. Sai kuma ya yanke wayar batare da yace mata komaiba. Omar dake gefe yana jinsa sai dariya yake dannewa. Batare da Yoohan ya kallesa ba yace, “Umar Al-qur'ani”.

      “Okay bara na kawo maka a mota”.


  Cikin mintuna ƙalilan Omar ya dawo masa da Qur'ani. Tashi yayi yayo alwala ya dawo ya zauna. Cike da bin shawarar Aymah ya fara karatu. UBANGIJI mai Rahma mai jin ƙai sai ga Yoohan ya sami nutsuwa cikin lokaci ƙanƙani. jiyay tsoron ALLAH ya ƙara ratsashi. Ya shiga jeramasa kirari da godiya bisa koyarwar Nu'aymah.

      Umar ma yaji daɗin ganinsa ya dai-daita a lokaci ƙan-ƙani, dan haka yaje ya samo masa abinci har suka ɗan zauna suka tattauna akan abinda ya farun. Omar yaji a ransa ba Gebrail bane ya shiga ɗakin Aymah. Ya taka sawun ɓarawone kawai da kuma zafinsa da Yoohan ɗin yakeji dama. amma sai yay shiru baice komaiba. Dan yafi buƙatar Yoohan ya fahimci wanene mahaifinsa da kansa.


______________★★


          A gidan su Yoohan kuwa uffan papa baiceba game da dukan Gebrail da aka kai asibiti a sume da Yoohan ɗin yayi. Su Uncle Mike ne ma keta faɗa da son jin miya kawo rikicin? Sai dai amsa ɗaya suke samu. Shine kowa bai saniba. Dan iya abinda idanunsu ya gani kawai suke faɗa jama'ar gidan.

     Har zuwa lokacin da labarin farfaɗowar Gebrail ɗin yazo kunnensu papa dai yaƙi yace uffan. Sai da daddare bayan sunje sun duba shi a asibiti bisa tursasawar mama debora da maman madam Chioma da yau sukaci masifa har bakunansu sukai tsaho. Bayan barowar tasu asibiti ne papa ya kira Baba malam da shi har yanzu ma baisan Yoohan na ƙasar ba. Dan sunata shirye-shiryen bikin sauka da auren yaransu na gidan marayu nanda bayan salla babba. Yayi Busy da yawa. Rabonsa dayin waya da Yoohan tun yana Oman.

      Yasha mamakin ganin kiran papan. Amma sai ya ɗaga yana ambaton sunan ALLAH. Baiyi sallama ba, sai cewa da yay, “Barka da dare Pastor Goshpower. Yau kaine ka tuna da Soorajidden bin Hashim?”.

      Wani wawan tsaki papa ya sauke a jere. Batare da jiran cewar baba malam ba ya fara zazzaga masifa. “Kai ɗin banza da zan ɗauki waya na kiraka. Gargaɗi na kira na maka a karo na farko kuma na ƙarshe. Ka rikitamin yaro gaba ɗaya ya fita hayyacinsa. Sai yanzu na gama fahimtar manufarka akan ɗana. So kake ka maida minshi ɗan ta'adda shiyyasa ka aura masa wannan shegiyar ƴar taka mai zuciyar dutse? To wlhy Sheikh Sooraj kafin kaga bayana nine zanga bayanka. Sanna kayi gaggawar sakarmin kurwar yaro. Ka kuma saka ya maido maka ƴarka gida tun kafin lokaci ya ƙure maka. Idan ba hakaba na rantse saina halakata da hannuna kafin kaima na halakaka...”

     Kafin baba malam yace wani abu papa ya yanke wayar. Nannauyar ajiyar zuya baba malam ya sauke kawai yana girgiza kansa. a gaba ɗaya kalaman papa babu wanda ya bashi tsoro. Abinda ya fahimta kawai shine cikin fushi yake. Duk da kuwa yasan papan zai iya aikata duk abinda ya lissafa masa. Abinda kawai ya sakashi a ruɗani shine, ‘Miya faru?’. 

      Ganin bashi da mai bashi amsa sai kawai ya ajiye tunanin ya cigaba da harkar gabansa.


__________★


       Yoohan ko takan gidansu bai sake biba. ya dai saka Omar zuwa da mai saka keys ya sabunta duk keys ɗin dake a sashensa. Da yake lokacin duk ƴan gidan sun fita, su mama debora kuma na wajen Gebrail sai babu wanda yasan mi akayi. Solomon dai yaso shiga ya duba sai dai fitowar Omar yay masa katanga da hakan. Dan yana kai mai saka keys ɗin shi fitowa yay dan ya hana su Solomon ɗin kowacce damar sanin abinda ya farun. Sosai ya jima da fahimtar wanene Solomon dama. Labarin korosa da Aymah tasa akayi kuma da Yoohan ya bashi ne ya sake tabbatar masa akwai wata a ƙasa. Sai dai komai sake ɗaure kansa yakeyi shikam. Dan baiga miye dalilin aikata abu a sarƙaƙe da su papan keyiba game da Yoohan ba.


           Shiri yay tsaf domin shiga Kano. yanason daga Kano Lagos zai nufa. Yay kwana uku su juya U.S shi da Omar.

     Misalin huɗu kuwa Yoohan da Omar suka iso anguwar su Nu'aymah. Kasancewar anata hada-hadar shiga salla sai kawai suma sukai alwala suka shiga. Bayan an idar sun fito Yoohan yaketa faman jan ƙananun tsaki saboda kallon damutane suketa musu. Duk da yasan wasu a cikinsu sunriga da sun sanshi zuwa yanzun. Amma duk sanda zaizo basa iya daina binsa da kallo kamar wani baƙo. Ya rasa mi suke kallone wai? Gashi shi kuma ya mugu-mugun tsanar a sakamasa ido.

      Umar daya san dokar dai yanata murmushi. Dan ya tabbatar kallon ne ya bama Yoohan ɗin haushi. Bai dai ce komaiba har suka sami iso daga baba malam ta hanyar malam ƙarami daya fito ya gansu. Sakawa yay malam ƙarami shiga dasu cikin gida, shi kuma ya nema alfarmar ɗalibansa shima yabi bayansu. Sashen hajjo aka kaisu. Dan mutuniyar Yoohan ce yanzu sosai. Danma bajin zancen juna sukeba sai da tafinta. Amma a wannan karon hajjo ta fahimci Yoohan ya fara jin hausa kaɗan-kaɗan. Takoji daɗi, duk da harshen nasa a karye yake. Wani abunma koya faɗa bata ganewa.

      Sosai aka cika musu gaba da kayan ciye-ciye. Shi dai Omar nasa kallo ne da tayasu dariya. Dan yau ne karan farko daya shigo gidan. Anan baba malam ya samesu kuwa. Suka gaishesa da tsantsar girmamawa. yayinda shima da kulawa yake amsa musu da tambayar iyali. Da ga haka suka ɗan zauna hira. Anan hajjo kejin Omar ma abokin Yoohan ɗinne, kuma ya muslinta. Daɗi sosai ya sake kama Hajjo. Lallai tarkonsu ya kama kurciya. Dan ga nasasorin auren Yoohan da ɗiyarsu nan sun fara bayyana.

      Daga Sashen Hajjo baba malam ya shiga da su dan su gaida Umm. Yasan dai ganin Yoohan ɗin zaisa taji sanyi a ranta da raguwar kewar Nu'aymah. Aiko hasashen baba malam ɗin yayi dai-dai. Dan sosai Umm taji ɗunbin daɗi, duk da kuwa akwai ƴar kunya a tsakaninsu. Dan daga ita har shi babu wanda ya iya saka idon juna. Da yake sun iske Addah a sashen itama suka gaisheta. Ta amsa musu da kulawa tanata tambayar ɗiyarta Nu'aymah.

      Suna ɗan hira da Addah ne, wadda ta kasance duk akan Nu'aymah Afrah da Muhammad da suka dawo daga islamiyya suka shig falon da sallama. Kallonta duk su Yoohan sukayi. Itama fuska ɗauke da nuna rashin sani a garesu, dan miskilace ta gaske, ga salon aiki. ta shiga gaidasu tana ƙoƙarin wucewa ɗakin Aymah daya zama nata yanzu batare ta nuna alama tama taɓa ganin mai kama dasu ba a rayuwa. Su dai da kallo kawai suka bita. Yayinda Yoohan ya miƙama Muhammad hannu alamar yazo garesa.

       Muhammad akwai wayo, dan haka tsaf ya gane Yoohan. Hannu ya bashi sukai musabaha. Yoohan ya shafa kansa yana murmushi, yace, “Oh my dear Friend ka ƙara girma fa”. Cike da jin daɗi Muhammad ya zauna kusa da shi yace, “Thanks Uncle. Ina Aunty N ɗina?” Yay maganar yana waige-waigen neman Nu'aymah.

           Murmushi Yoohan yayi yana ɗan rungumo Muhammad ɗin jikinsa. Yayinda Omar ke bashi amsa yana dariya. “Ta maka wayo tana U.S abinta”. Da ƴar damuwa Muhammad yace, “To Uncle yaushe zatazo itama?”. 

       Yoohan yace, “Soon insha ALLAH Darling. Amma karka damu idan kunyi hutu zan kaika ka ganta”.

     Daɗi sosai ya kama Muhammad, nafa ya shiga tsallen murna su Addah na masa dariya.

       

      Sai bayan isha'i su Yoohan suka bar gidan da kayan Nu'aymah ghana must go guda. Baba malam baicema Yoohan komaiba game da wayar da sukayi da papa. ya da masa nasiha cikin hikima shi da Omar ɗin akan muhimmanci iyaye. Ta hakane Yoohan ya ɗan tsargi akwai abinda ya faru kenan. Amma sai shima baice komaiba. 

        Ƙarfe goma na dare suka wuce Lagos. Inda zasu kwana uku yay aikin daya kawosa 9ja ɗin.


★★★


       Tunda suka shigo lagos Yoohan bai samu kansa ba. Aiki yake tuƙuru tamkar yanda ya saba hidima ga al'umma. Ya ɗanyi wasu ziyarce-ziyarce dake ransa. Batare daya sake bi takan su papa ba suka wuce U.S shi da Umar.


  *_U.S_*


        Kasancewar su Nu'aymah sunsan da dawowar mazajen nasu a ranar da safe Juliet ta maida Nu'aymah gidanta. Yaɗanyi ƙura kaɗan kuwa saboda rashin mutane. Dan haka Juliet ta taimaka mata suka gyara duk da Aymah na hanata. To itama dai ƙarfin haline dan a jigace take komai. Bayan sun kammala Juliet tai mata sallama ta koma nata gidan. 

      Cike da ƙarfin hali Aymah taima Yoohan girki. Da ƙyar kuwa ta kammala tai wanka. Batare da tabi takan wani kwalliya ba tai shiri cikin Bomshort jeans bleu da pink top kawai tazo falo ta kwanta a ƙasan tiles kamar yanda takeyi a yanzun. Duk da kuwa da farko taci alwashin masa kwalliyar tarba amma hakan ya gagareta. Cike da rashin jin daɗin jiki kuwa barci yay awon gaba da ita a wajen. Ga zazzaɓi mai zafi daya fara saukar mata na yamma.

        A ƙagare Yoohan yake da son ganinta. Hakan yasa yaƙi yarda su hau cab ɗaya shi da Omar. Duk da kuwa kusan anguwa ɗaya suke. Sai ma an fara sauke Omar ɗin a gida kafin a ƙaraso nasu.

        Tsabar zumuɗi a barandar gidan yabar kayan da yazo dasu ya shige ciki. Sassanyan ƙamshin daya doki masa hancine ya sakashi lumshe idanu. Kafin ya buɗesu a hankali kan Aymah dake kwance a ƙasan tiles barcin wahala yay gaba da ita. Kallonta yake da matsanancin shauƙi da kewa. Ya taka a hankali zuwa inda take. Tsugunnawa yay a gabanta ya ɗaura tattausan hannunsa saman fuskarta dake shining na masu ciki ya shafa yana sauke ajiyar zuciya. Ko motsi batayiba kuwa. Sai ma numfashi da take saukewa a hankali. Zamewa yay ya zauna. ganin baya ganinta da ƙyau sai kawai ya kwanta shima ya ɗora kansa saman filon datake kwance yana kallonta da ƙyau. Sai dai kwanciyar tasu ta kasance tamkar kai da ƙafa bawai a jere ba. Hakan yasa goshinsa na saitin haɓarta ne. Itama nata goshin na saitin tasa haɓar. Yanda take busa masa numfashinne shima yana busa mata nasa ya sakashi sauke ajiyar zuciya idonsa ƙyam akan ɗan bakin tsiwarta. Matsar da kansa yayi a hankali ya daidaita bakinsu. Tare da ɗora hannunsa ya ringumo kanta jikinsa ya fara kissing nata cike da zalama da kewa.

       Cikin barci Nu'aymah taji salon da duk duniya na mutum ɗaya ne a gareta. Batare data buɗe idanuntaba cikin kasala itama takai hannu bisa kansa ta ringumosa tana mai bashi haɗin kai yanda tasan yana buƙata. Sunfi minti shida a haka sannan ya barta yana sauke numfashi da sauri-sauri. Dan harga ALLAH harya hau network.

      Shanyayun idanunta ta buɗe a hankali tana kallonsa. Dan har yanzu yana akan filon bai tashi ba. Murmushi yay mata mai sanyi, ya maida hannunsa akan fuskarta suna kallon juna cikin ido. 

    “Welcome my boo”.

Tai maganar a hankali kamar mai tsoron ajisu. 

     Lumshe idanunsa yayi ya sake buɗewa a kanta. Cikin ɗan sake matsar da kansa jikin fuskarta yace, “Sweet girl mike damunki?”. 

     Maimakon ta bashi amsa sai hawaye shar. Saurin tashi yayi zaune har jikinsa na rawa..........✍

       

No comments

Powered by Blogger.