Saran Boye 62


 No. 62


............Iya wahala Aymah tasha a yau. Hatta shi kansa Sojan nata ya jigatu balle ita. Yama manta kansa matsayin likita, ya manta matsayin Nu'aymah ƴar shekara sha takwas kacal. Ya manta.. Ya manta... Da yawa. 

         Duk yanda yaso ɗaga ido ya duba halinma da take a ciki ya kasa. Wani irin azababben ciwon kai ne da jiri ke yawo da ƙwanyar kansa. ya yunƙura da ƙyar ya sauka a gadon yana layi. Toilet ya nufa. da laluben bango ya ƙarasa ciki, amai ya farayi babuji babu gani. Hannayensa duka biyu riƙe da kansa da yake neman tarwatsewa saboda azabar ciwo.

        Duk da halin da Aymah take a ciki tana jiwo kakarin aman nasa. Sai dai ko idanunta bazatama iya buɗewaba tsabar galabaitan da tayi. Kusan mintuna goma taji motsin fitowarsa. A yanzunma bata iya buɗe ido taga halin da yake a cikiba. Kunnenta dai na sauraren yanda yake fidda wahalallen numfashi, harya ƙaraso ya faɗa saman gadon yana ambaton sunan ALLAH. Hannunta taji ya kamo cikin nasa dake rawa. Ƙam ta ƙara matse idanunta zuciyarta na harbawa da sauri-sauri. 

         Haka suka kasance babu mai iya taimakawa ɗan uwansa. Ga shi kuma barci yaƙi ɗaukarsu su duka. Ga ciwuka sun musu rijif musamman Aymah da ko maganinta dama bata samu damar sha ba na daren, ga yunwa da take bala'in ji a yanzu haka.

       A hankali Yoohan da idanunsa ke a runmtse ya sake jan jikinsa kusa da ita. Muryarsa a ɗashe yace, “Baby. Are you ok?”. Hawaye ne masu ɗumi suka silalo mata, dan ita dai tasan she's not ok ɗin nan. Jin bata amsashi ba ya sakashi buɗe idanunsa da ƙyar yana taunar lip saboda azabar da kansa ke masa. Hannunsa ya ɗora bisa fuskarta ya shiga share mata hawayen dake ziraro mata. Cikin raɗar magana kamar ɗazun muryar a ɗashe yace, “I'm sorry. Forgive me Please Sweet girl”. Ya kare maganar da ɗora kansa jikin nata shima hawayen na tarar masa cikin ido na tausayinta. Dan jikinta ya ɗauki zafi sosai na zazzaɓi. Ga wani ƙaunarta mai zafi na sake ɗawainiya da zuciyarsa. Musamman da ya tuno sharrin da akai mata na zubar da ciki. Gashi shi kuma a yanzu ya sameta cikkakkiyar mace da ya zam shine namiji na farko daya fara ratsata. Hakan ya sake tabbatar masa da zarginsa akan gidansu.

        A hankali ta juyo dan son shigewa jikinsa ko zata sami sassaucin azabar da takeji. sai dai kuma wani zafi ne ya ratsata har cikin ƙwalwar kanta. Ta saki siririyar ƙara da fashewa da kuka. “Wayyo Abba ya kashe muku ni. Ummuna zan mutu”.

      A tsananin firgice Yoohan ya zabura. Ya riƙota jikinsa tare da saurin dafe kansa yana faɗin, “Achss! My head!. Baby Please i'm sorry, kibar kuka na roƙeki”. Sosai ta mamuƙesa tana cigaba da kukanta jikinta na rawa saboda zafin da takeji wajen na mata.

       Gaba ɗaya Yoohan sai ya sake ruɗewa. Duk da matsanancin halin da yake ciki haka ya ɗauketa cak zuwa toilet yana layi, sai jera mata kalmar ‘I'm sorry’ yaketa faman yi kamar shima zaiyi kukan. A wahalcen ya shiga bata taimakon da ya dace yasan kuma zai taimaka mata a irin halin da take ciki. Ya dai sha raki. Dan da azaba ta isheta hardasu ALLAH ya isa tai masa cike da suɓutar baki. Sambatu kuwa iri-iri wani abunma ita kanta batasan mitake faɗaba. Wanda tayi ɗazun yafi wannan, sai dai na yanzu da yake yana a hankalinsa sai yaji ransa duk a jagule. Yana jin haushin kansa akan gaza haƙurin da yay yama tausaya mata kodan ƙananun shekarunta. Yanda take rabzar kuka shima ƙwalla sai famar tarar masa suke a cikin idanu. Da ƙyar dai ya kammala kimtsata ya taimaka mata tasa bathrobe.

        Yanzun ma da ƙyar ya iya kawota falo ya kwantar saman sofa. Juyawa yay wajen gadon ya cire farin bedsheet ɗin dan ya ɓaci, sai dai bawani faca-faca ba. Jini ne ɗis-ɗis irin na macen data rasa budurci musamman mai ƙarancin shekaru irin nata. Har aransa yaji takaicin fara sanin matarsa a ɗakin hotel, da yasan hakan zata kasance shikam da gida suka koma abinsu. Amma duk da haka wannan bedsheet kam bazai ƙara yarda wani mahaluki ya kwanta a kansa ba. Inda ma yaji daɗi a ransa dama sabone aka saka musu kamar yanda al'adar hotel ɗin take. A washing machine dake toilet ɗin ya saka bedsheet ɗin ya wanke ya busar da shi. Sannan shina ya tsaftace nasa jikin ya fito.

         Kafin ya dawo gareta har barcin wahala yayi awon gaba da ita. Dan idanu ya rumtse sosai da cire tausayinta yay mata gashin ɗaya tamkar da dubu. Cike da dauriya yay order ɗin abinci dan yasan zataji yunwa. kuma ya tunama batasha maganinta ba. Ba'a rufa mintuna goma ba kuwa sai gashi an kawo musu. Lokacin yana ƙoƙarin canja musu bedsheet cike da ƙarfin hali dan jiri yake gani. Ga ciwon kai kuma. Zuwa yay ya buɗe ya amshi abinci ya koma ciki. Sai da ya gama kimtsawa tsaf sannan ya tasheta zaune. Kuka ta sanya masa duk da kuwa yanzu zafin ya ragu, sai dai zazzaɓi da jikinta da takejin na mata ciwo na bala'i. Kasancewar yunwa takeji sai gashi taci abincin daya bata da kansa. Ya bata maganinta daya tabbatar zai taimaka mata tunda zatai barci. Ayko bata rufa mintuna biyarba sai barci. Da ƙyar ma ya samu ya ta yarda ya saka mata kayan barci ya taimaka mata ta koma kan gadon. shima dai kayan barcin ya canja ya kwanta dan jikinsa sai karkarwar zazzaɓi ya keyi. Ga ciwon kai tamkar ana ƙara masa shi.

          Sai gashi ita Aymah ta samu barci mai nauyi, shiko dake rungume da ita ya kasa rintsawa. Ga zazzaɓi da ciwon kai. Sau biyu yana zuwa yay amai. Hakan yasaka shi sake galabaita fiye ma da farko.

          Yau ma Alarm ne ya tadasu, koma nace ya tada Nu'aymah dan shi dai Yoohan bama barcin yayiba. Garama gabannin asuba yaɗan fara figarsa sama-sama sai kuma ya farka. Daga haka bai sake komawaba har alarm ɗin ya buga. Sosai jikin Aymah da sauƙi dan zazzaɓin nata ya sauka ita. Sai dai rashin jin daɗi jiki da sabon al'amari ya haifar. Sai ciwo ƙafafunta dake mata. Jinta take fayau kamar iska zata ɗauketa ta kayar. Bakinta ko ɗaci, ɗan-ɗanɗanon data fara samu yana dawo mata ya sake guduwa. Yanda take tsananin jin kunyar Yoohan ɗinne ya sakata tashi zaune batare data yarda ta kalle sashin da yake ba, sai faman matse baki take dan can wajen kam da zafi har yanzun. 

        A hankali ta dinga tafiya tana hawaye har bathroom, Yoohan na kwance yana kallonta cike da tausayi, duk yanda yaso ya yunƙura ya sake taimaka mata ya kasa saboda ciwon da kansa ke masa ga zazzaɓi irin wanda shikam a rayuwarsa zai ce ya mata rabon da yayi zazzaɓi mai zafi irin wannan. 

       Aymah na shiga bayin ta fashe da sabon kuka mai sauti tana kiran baba malam da Umm suzo su taimaketa. Ta kai mintuna huɗu zaune a aɗan step ɗin hawa wajen bathtub ɗin kafin ta miƙe da sanɗa ta nufi madubi wani daɗi na ratsata na hango wayar Yoohan a jiye. Da alama dai a daren jiya ya manta da ita kenan. 

          Umm ta riga da ta mata tarbiyyar duk abinda ya sameta ita take fara sanarmawa, sai dai a yanzu abinda naga Aymah na shirin aikatawa ya sake tabbatar min da tsabar wautar dake a kanta, dan kuwa number ɗin Umm ta shiga lodawa cikin wayar tai dailing. Kuka ta sanya da dariya a lokaci ɗaya jin kiran ya shiga. 

       Daga can Nigeria kam Umm na idar da sallar magriba kiran ya shigo. Da mamaki take kallon Number dan bata kawo Aymah a rantaba. Tunda tasan indai zasu gaisa a wayar baba malam mijinta ke kira sai shi kuma ya bata su gaisa. Tana gab da tsinkewa dai tai ƙuru ta amsa, tare da kaiwa kunne tai sallama. Maimakon mutuniyar taku ta amsa sallanar sai kawai ta fashe ma Umm da kuka. Shiru kawai Umm tai tana saurarenta dan ta gane abarta. Sai da ta barta tayi kusan na minti ɗaya sannan tai gyaran murya. “Mike faruwa?”. Umm ta jefa mata tambayar.

     (Nazata bazata iya faɗaba fa😱) sai kawai Aymah ta gyara zama ta fara faɗin, “Umm dan ALLAH kuce ya maidoni gida. wlhy ban taɓa iskanciba. Na rantse da ALLAH Umm ba laifina baneba, sai da naita roƙonsa karyayi banaso, amma shi mugune sai da yayi. Gashi na kasa tafiya, wajen kamar zai fita, ciwo yake min, gashi inajin fitsari inajin tsoron yi Um........”

       Harga ALLAH dariya ta bama Umm, amma sai ta danne abinta tai saurin faɗin, “To ya isa zubaina sarkin magana. Wai nikam yaushene ranar hankalinki Nu'aymah?. Kai ALLAH na gode maka ni Firdausi. Yanzu shi mijin naki yana ina kike zubamin zance haka?”.

      Baki ta kumbura na haushin ba'a barta takai ƙarshen labariba tace, “Yanacan ɗaki bai tashi ba. Ni kuma ina toilet asuba fa tayi anan”. Ta ƙare maganar hawaye na silalo mata.

     Ajiyar zuciya kawai Umm ta sauke hawayen farin ciki itama na silalo mata. Koba komai dai ta fahimci yarinyarta takai mutincinta gidan aurenta. ALLAH ya ƙara wanketa a garesu ga ƙazafin da akai mata. Hawayenta ta share. Tace, “Ki shiga ruwan zafi kinji ko, ki daure duk zafinsa ya ratsaki sosai zakiji daɗi”.

       “Umm wlhy jiya daya sakani kamar zan mutu. Dan ALLAH ki faɗamin wani maganin sai nace ya sayo min zansha. Amma dan ALLAH kice Abbana ya kirashi ya kawoni gida yau”.

      “To naji, yanzu ki ƙara shiga ruwan zafin bazakiji zafin kamar na farkoba kinji ƴar albarkana”.

      Cikin jin daɗin sunan ƴar albarka da Umm ta kirata tace, “To Ummuna. In kiraki video call ki ganni, ƙila zakifi ƙarajin tausayina ma”. Da sauri Umm tace, “A'a jekiyi abinda na sakaki, kije kiyi salla lokaci na shigewa”.

        Fuska ta ƙwaɓe zatai wani sabon kukan, zatai magana Yoohan da shirunta ya sakashi a damuwa ya taso da ƙyar ya biyota yay azamar zare wayar daga hannunta dan yaji maganar video call da taima Umm, sai dai baisan amsar data bataba da ga can.

       Zabura tayi dan batasan da shigowar tasa ba. Shi kuma ya zaune a step din yana dafe kansa da faɗin, “Acshh!! Kaina”. Miƙewa ta nemayi duk da ganin yanayinsa ya bata tsoro, yay saurin damƙo hannunta ya maidata ya zaunar. Hannunsa dake akan goshinsa ya cire yana dubanta da idanunsa dake jajur. “Zeeynab baki da hankali wa kika kira? Ba dai Uncle ba?”.

          Tana cika kumatu da iska tace, “Ni ban kira Abba ba, Ummna na kira na faɗa mata abinda kaimin. Nace tasa Abbah yasa ka maidani gida”.

   Tuni ya manta da maganar ciwon kai, ya waro idanu waje yana faɗin, “Kin kasheni Zeeynab. Kika faɗa matafa kika ce?”.

        “To wa yace kayi? Gobe ma ka ƙara kaga idan bankira harda Hajjo da Abbana da Addah duk na faɗa musu ba ALLAH. Kai harma Ananah sai tasan halinka”. 

      Gaba ɗaya kunya ta lulluɓe Yoohan, ji yake tamkar yana a gaban Umm. cike da ƙarfin hali yace, “Yarinyar nan ALLAH har yanzu kanki da motsi, dole na sake maidaki wajen su Dr Liam”.

     Umm da duk take saurarensu da ga can ta yanke wayar tana dariya. Dama ta tsayane ta sake gaskata zancen Nu'aymah. Wayar ta ajiye tana faɗin, “Yaron nan kaga takanka indai Nu'aymah ce. Bayan motsin ciwo dake a kanta akwai ma na hali wlhy. Ni harma ka bani tausayi”.....

       “Waye ya bada tausayi?”. Cewar baba malam dake shigowa ɗakin. Dan dawowarsa kenan gidan. Juyowa tai tana cigaba da dariyarta. Ya zauna a bakin gadon ya riƙo hannunta. “Jannat da alama dai kina cikin farin ciki, zoki ɗan sammini nima muyi tare”. Sosai take ƙara faɗaɗa dariyarta. Ta shiga bashi labarin kiran da Nu'aymah tai mata da drama ɗin data gama ji tsakaninta da Yoohan a ƙarshe. Shi kansa baba malam sai da ya dara. 

      “Ai Jannat lamarin mamana sai ita. Yarinya tamkar goyon kaka. Amma koba komai ni hakan yamin daɗi tunda munji cewar dai sharri dai akai mata kamar yanda zukatanmu ke faɗa mana. Wannan shine amfanin ka bama yaro tarbiyya akan duk abinda ya shafesa ya sanar maka. ALLAH yay musu albarka su duka. Ya azurtasu da zuriya masu albarka da alkairi. Wadda zata zama maijin ƙai a garesu damu baki ɗaya”.

       “Amin ya rabbi. Sai dai kuma naji muryar mijin nata kamar wanda baida lafiya ma. Dan da ƙyar yake magana”.

        Ɗan jimmm baba malam yay yana sauke numfashi. Yace, “To inaga dai bara na sanarma yaron nan abokinsa shi sai ya nema wanda zaije ya duba halin da suke cikin, dan yanzu ni idan na kirashi a kunya zan sake sakashi tunda mamana ta ɓallo masa aikin data iya na wauta”.

     Dariya Umm tayi shima yana tayata. A take ya kira Richard dan yanzu yana da Number sa. Sai dai bata shiga ba. hakan na nufin Rich baya Nigeria kenan kokuma wayar a kashe. ya barsa akan zuwa anjima zai sake gwadawa kawai.


          A nan Austria kam Yoohan da ƙyar ya iya taimakama Aymah ta sake shiga cikin ruwan zafi. Sai dai yau batai rakin jiyaba. Hawayene dai kam tanata abunta. Baiyi maganaba dan shima takansa yakeyi, da alama ma yafita jin jiki yanzun. Tana ganin ya shiga wajen wanka tai alwala ta fice daga bayin tana ɗingishi. Yau ko jiransa ya jasu salla batayiba. Tana idarwa yana fitowa. Komawa tai kan gado ta kwanta.

      Bazai iya salla a tsayeba saboda jiri yake gani ga ciwon kai. Hakan ya sakashi yinta a zaune, yana idarwa shima gadon ya koma ya sake kwanciya. Wayar landline ya ɗauka da nufin kiran yima Aymah order ɗin breakfast saboda shan maganinta sai yaga wayarsa na haske. Hotel ɗin ya fara kira, kafin ya ɗauka wayar tasa dan silent take dama. Richard ya gani, cike da mamaki ya amsa kiran dan alamu sun nuna Rich ɗin yana a cikin Austria tunda da Number ƙasan ya kirashi. 

         Ko gaisawa basuyi ba Richard ya fara jera masa tambaya a rikice saboda jin muryarsa, cikin son kwantar masa da hankali Yoohan yace, “Ciwon kai ne kawaifa. Dama kana Austria?”.

       “Jiya da dare na iso, yanzu dai idan ba damuwa bara nazo ɗakin naku na dubaka hankalina zaifi kwanciya”. Murmushi kawai Yoohan yayi da faɗin “Okay”. Daga haka ya ajiye wayar ya juya yana kallon Nu'aymah data juya masa baya. Ta naɗe a cikin bargo alamar sanyi takeji. Maida idanunsa yay ya lumshe tunda yasan akwai kaya jikinta.


        Kusan a tare Richard da ma'aikaciyar hotel ɗin suka iso. Rich ya amshi abinci kawai sannan ya danna door bell. Miƙewa Yoohan yayi da ƙyar hannunsa dafe da kansa. Ya gyarama Aymah ɗan kwalin kanta daya zame sannan ya nufi ƙofar ya buɗe. Saurin riƙesa Rich yayi ganin yanda yake layi, duk ya rikice masa da faɗan yaya zai zauna da ciwo irin haka baije asibitiba?. Amma yana faɗin wai ciwon kai ne kawai. Murmushin ƙarfin hali kawai Yoohan yay masa shi dai, ya zaunar da shi a kujera yana sake jera masa sannu.

       Kansa ya ɗaga masa yana magana cike da ƙarfin hali. “Shine zaka shigo baka sanar min ba?”. 

       Rich da damuwa duk ta baibayesa yace, “Manta da batun shigowata faɗamin mike damunka Please X-man”.

      “Kai dai ka cika ruɗiya. Ciwon kai ne kawai da zazzaɓi”.

     Hararsa Rich yayi da faɗin, “Shine bazakaje asibiti ba? Ina madam?”.

      Da idanu ya nuna masa gadon da cewa, “Gata can, itama bata da lafiyar”. 

       “Oh GOD. Miya faru haka?”.

Murmushi kawai Yoohan yayi baice komaiba. Hakan yasa shima Rich ɗin bai sake magana ba ya miƙe ya fita yana faɗin, “Ina zuwa Please”.

       “Okay” Yoohan ya faɗa da jingina jikin kujerar ya lumshe idanunsa. Yanason tashi yaje ya tada Nu'aymah data fara barci taci abinci amma jiri da yake gani ya hanashi motsawa. Har tsahon mintuna sha biyar Richard ya dawo da kayan magani. Sannu ya sake yima Yoohan ɗin sannan ya zauna yay allurai a cikin drip. Yana gamawa ya dubi Yoohan.

       “Ya kamata ka koma kan gado sai a saka drip ɗin”. Idanu Yoohan ya buɗe da ƙyar, batare da yayi magana ba yay ƙoƙarin tashi tsaye. Taimaka masa Rich yayi har kan gadon. Aymah nata barcinta batasan hidimar da sukeyi ba ita dai. 

       Ɗaura masa ruwan yayi, sai da ya tabbatar ya fara shiga jikinsa sannan yace, “Ita kuma yaya zamuyi da ita?”. Isaka Yoohan ya ɗan furzar idanunsa a lumshe yace, “Inaga ita barta kawai, dan allura ya kamata ai mata kuma bazata tsaya ayi da arziƙi ba. Dan bata ƙaunar allura sam”.

      “Okay, idan ka tashi kayi mata. Sai dai akwai alluran a wajenka ko sai an siyo?”. 

       “Sai an siyo”.

Ya bashi amsa a yanayin barcin daya fara fisgarsa. Sai kuma ya faɗama Rich ɗin sunan allurar da yake buƙata.

        Idanu Richard ya ɗan waro waje jin allurar da Yoohan ɗin ya faɗa. Cike da neman magana ya shuri ƙafar Yoohan ɗin yana faɗin, “Shegen sama, ashe kasan tsiyar daka aikata”.

       Shi dai Yoohan baice masa komaiba dan barcin ya fara masa Nauyi, Richard ya fice cike dajin daɗin ɗan uwansa ya zama babban mutum yau.

      

        Yanayin rashin jin daɗin jikin ya sakata kasa barci yanda ya kamata, ta buɗe idanunta a hankali kansa. Barci yake sosai yanzun. Ganin kamar ana ƙara masa ruwa ya sakata tashi aɗan zabure. Cike da ruɗewa ta kai hannunta ta ɗora a bisa kansa. Har yanzu kan nasa bai gama hucewa ba da zafi. Sosai damuwa da tausayinsa suka bayyana ƙarara a fuskarta. A fili tace, ‘Bawon ALLAH, ashe shima bashi da lafiya, shiyyasa ɗazun yaketa magana da ƙyar. Ɗan balarabe ALLAH na zata duk muguntar da kaimin ce ta sakaka komawa kalar tausayi ai’. Ta ƙare maganar da ɗora kanta bisa ƙirjinsa hawayena cika mata idanu ganin an saka masa allura a jiki. Dan itafa ba'a taɓa mata ƙarin ruwa cikin hankalinta dan bazata yardaba. Inhar yazam za'a ƙara mata ruwa to lallai sai an bata maganin barci ko an mata allurar barci saboda tsabar ƙiyayyar dake a tsakaninta da allura.

        Ta daɗe jikinsa kwance kafin ta tashi ta zauna, tagumi tayi hannu bibbiyu ta zuba masa idanu kaikace television ta samu. Ta shafe kusan mintuna talatin a haka kafin ta miƙe saboda fitsari da takeji. bayan ta fito kuma idonta ya sauka kan abincin. Yunwa takeji bana wasaba, dan haka ta zauna ta faraci dan ta fahimci natane dama. Tanaci tana kallonsa harta kammala dan kaɗan ma taci saboda rashin daɗin bakinta, cike da son ƙarfafa kanta da rashin daɗin da jikinta ke mata ya sakata ɗaukar magungunanta tasha kamar yanda taga yana bata kullum. Kasancewar barcin da suke sakata idan tasha ya sa ta ƙara ɓingirewa barcin a wajen.


★★★★


        A hankali Yoohan ya buɗe idanunsa saboda kaɗawar alarm alamar lokacin sallar zuhur yayi. Hakan kuma yay dai-dai da farkawar Aymah dake can kan sofa itama. Sai dai har Yoohan ya miƙe zaune ita ɗin bata tashinba tana kwancenta. Inda take ya kalla yana sake lumshe idanu da buɗewa. Sosai ciwon kan nasa yay ƙasa. Zazzaɓin ma kuwa duka ya sauka. Ya zare drip ɗin da kaɗan ya rage ya ƙare. Fuskarsa a yamutse na alamun wanda ya tashi a barci ya sauke ƙafafunsa ƙasa yana ambaton Alhmdllhi a cikin ransa. Sai da yay kusan minti uku a zaune sannan ya miƙe zuwa inda Nu'aymah ke kwance.

        Da sauri ta maida idanunta ta rufe, shikam batare da yasan idanunta biyu ba ya ɗora hannunsa saman kanta. Alhmdllh ya faɗa jin babu zafi. Ya taɓa wuyanta ma nanma sanyi ƙalau. Maganganun data sha ya dudduba yaga tashasu dai-dai, hakan ya sakashi miƙewa ya nufi bayi zuciyarsa sakayau da farinciki da nishaɗi. Jinsa yake tamkar wani sabon mutum a duniyar mutane. Aymah na ganin ya shige ta tashi zaune fuskarta a curkuɗe kamar zatai kuka. Gaba ɗaya jitake tama rasa abinda ke mata daɗi a duniya. Babu abinda tafi buƙata kamar ta ganta a gaban Umm ɗinta. Ta haɗiye ƙwallar daya cika mata idanu tare da zabga uban tagumi.

       A haka Yoohan ya fito ya sameta. Kallo ɗaya tai masa tai azamar maida kanta ƙasa saboda ganinsa da ga shi sai boxer da ƙaramin towel a hannu. Direct yayo kanta yana faɗin, “Kin tashi?”. Kunya ta hanata masa magana, sai kai kawai ta kaɗa masa. Bai damuba dan ya fahimci kunyarsa takeji. Ya zauna a hannun kujerar yana cigaba da goge wuyansa idanunsa a kanta. “Mike miki ciwo yanzun?”. 

     Murya na rawa tace, “Komai ma”.

A ransa yace, ‘Abin nemafa ya samu ga iya madam hajjaju malamar tsiwa da shagwaba'. A fili kam sai yace, “Oh so sorry Mrs Yoohan. Jekiyi wanka sai na duba wajen na gani”.

     Da sauri ta ɗago tana hararar sa kai kace idanun faɗowa zasuyi ƙasa. Gashi dama sun kumburo saboda kukan data sha sannan akwai ja a cikinsu. Da sauri ya kauda kansa gefe gudun kar dariya ta kufce masa ya ƙara laifi. Miƙewa tai tabar wajen tana ƙunƙunin da baisan mitake faɗaba a ciki saboda hausa takeyi. Ya ɗan lumshe idanu ya sake maidasu kanta. Sosai yanda take tafiya da ɗingishi ya ƙara masa tausayinta da ƙaunarta a cikin zuciya. Tana gama shigewa ya sauke ajiyar zuciya ya miƙe..............✍


No comments

Powered by Blogger.