Saran Boye 57

 


No. 57


...........Ƙarfe goma dai-dai na safiyar wannan rana agogon ƙasar Nu'aymah ta farka a gaban Dr Yoohan da sauran likitocin da sukai mata aiki. Sai baba malam da Umm. Dan ana buƙatar tabbatar da ingancin lafiyar ƙwaƙwalwar ta da kuma tabbatar da idan bata manta komai ba.

         Gaba ɗayansu idanunsu cak akan yatsun ƙafarta dake motsawa. Har zuwa hannayenta biyu da suma ke motsin. A hankali gashin idanunta suma ke motsawa, sai numfashin ta dake sauya salon fita daga na barci zuwa na wadda take a farke. 

      Da farko bata ia ganin komai, ta cigaba da motsa idanun a sannu-sannu har ta fara ganinsu dishi-dishi. Idanun ta maida ta rufe tana matse fuska, babu dai wanda ya motsa a cikinsu harta sake buɗewar a hankali. Akan Dr Sophia ta fara saukesu, tayi kusan sakan goma tana kallonta kafin ta janye zuwa ga na kusa da ita. Shima dai tai masa kallo mai tsaho ta sake maidawa kan ɗayan likitan. Idanun ta lumshe ta sake buɗewa akan Dr Yoohan. Yanda take kallonsa haka shima yake kallonta cike da fargaba. Tafi tsayin mintu uku tana masa kallon ƙurullah da duk ya basu tsoro, dan tamkar tana hasashen wanene?. Ɗauke kanta tai a gareshi ta maida kan Baba malam dake a kusa da shi, sai kuma ta kalli Umm. Haka ta ringa raba kallo a tsakaninsu na tsahon mintuna.

      Gaba ɗaya jikinsu duk yayi sanyi har likitancin, dan da alama ta manta komai. A bazata sukaji ta fara magana da ƙyar,

      “Yah Yoohan da gaske su Abbana ne?”.

       Maganar da ƙyar take fita. Amma duk sunjita duk da a hankali ne. Rikicewa sukai da farin ciki. Yoohan yay azamar zuwa gabanta ya riƙe hannunta data dafe kai da shi saboda yunƙurin tashi zaune da taso yi.

       “Please relax koma ki kwanta”. 

Cikin rawar murya hawaye na zirara mata a idanu tace, “Kaina namin ciwo kamar zai rabe biyu”.

      “Okay, kiyi shiru ki daina magana”.

Ya sake faɗa yana maidata ya kwantar. Kunyar su baba malam da yakeji ne ya hanashi rungumeta dan farin cikin yanda komai yazo yanda sukai fata. Ya ja baya kaɗan dan bama su Umm damar ganinta da ƙyau. Idanunta a lumshe kuwa ta miƙoma su Baba malam hannu alamar suje gareta.

      Kallon Yoohan baba malam yay. Ya jinjina masa kai yana murmushi da sake matsawa baya yanda wajen zai ishesu. Ya kuma jawo musu kujeru su zauna.


      Tabbas Yoohan da su baba malam suna cikin ɗunbin farin ciki, hatta da Richard ma farin cikin da yaga ɗan uwansa a ciki shima sai yake tayasa. Duk da dai a yanzu shima jin wani girma da mutuncin baba malam ya keyi a ransa. Mutumin yana da wani kwarjini na musamman da iya mu'amula wa mutane.

      Hatta da Solomon duk da munafunci nacin ransa sai da ya nuna farin cikinsa. Kafin ya zagaye can baya yay kiran papa ya sanar masa halin da ake ciki. Aiko dai ba ƙaramin baƙin ciki papa ya shigaba. saboda karma Yoohan yay kiransa ya sanar masa farkawar Aymah sai ya sakashi a black list. Sai dai abinda ma bai saniba Yoohan sam bai nemesa ba a lokacin. Dan sunata shigi da fici akan Aymah daketa complain ɗin ciwon kai. Ko idanunta data ɗan buɗe da farko yanzu bata iya buɗesu. Tsoron kar matsalar ta shafi idanunta ya sakasu sake mata allurar barci na awa huɗu. Sunason suga ko barcin bai gama wadatar kanta bane jijiyoyin basu gama dai-daita ba.

         Da wannan damar suma su baba malam sukai amfani wajen komawa masaukinsu suka duƙufa addu'a a gareta a cikin tsaftataccen ruwan zam-zam da dama sunzo da abunsu. 

     

       A wanni huɗuu na cika Aymah ta sake farkawa. Cikin amincin UBANGIJI kuma an dace dan kuwa yanzu tana buɗe idanun, ciwon kan ma tace can ƙasa yake mata. Kowa yayi farin ciki da hakan. Yoohan ya bata ruwan zam-zam da su baba malam sukai mata addu'a aciki ta sha. shine abu na farko data fara sha. Ya kuma ɗiga mata a cikin ido kamar yanda baba malam ɗin ya sanar masa.

     Babu mai shiga inda take sai shi, saboda ba'a son mata hayaniya. Duk da tanata damunsa da ƙara son ganin su baba malam yana lallaɓata.


      A daren wannan ranar su Hajjo suka iso. Hajjo, Abban Adawiya, Abban Abdallah, Abba Musbahu. Sai Addah data takura akan sai tazo taga jikin Aymah ɗin. Duk da kuwa ance baza'azo da matan gidan da yara ko ɗaya ba. Su yi haƙuri har Aymah ta dawo tunda ance jikin Alhmdllh. Amma Addah ta nace, da kantama ta biyama kanta ƙuɗin jirgi. Dan ita dai a ganinta bai kamata a yanda suke da Umm ba ace batazo ta duba NU'AYMAH ba. Shaƙuwar tasu hajjo ta kalla tace a barta taje tunda tace zata biyama kanta. dan bazai yuwu a biya mataba sauran matan suga anyi son kai.


      Suma sunji daɗin ganin yanda jikin Aymahn yayi ƙyau sosai. Dan da taimakon Yoohan suka samu suka shiga wajenta. Alhmdllh kuma duk ta ganesu. Harma hajjo ta tsokaneta aka cuna mata baki. Dariya duk sukayi, Yoohan ya girgiza kai yana wani ɗan munafukin murmushi, a ransa yana faɗin, ‘Ta dawo duniya yanzu zata addabi kowa. Barema ni data gama rainawa’.

      Kamarko Aymah tasan mi yake rayawa. Dan tana can tana masa kallon ƙasan ido ganin yanda ya rame mata a idanu. Sai dai batai tunanin komai a ranta ba ta maida hankalinta gasu hajjo. 


      Bayan wucewar su hajjo Richard ya kawo abincin da zataci lokacin shan maganinta yayi da barcinta. Dan a yau ne zata fara cin abu mai nauyi bayan kullum da ake bata iya mai ruwa-ruwa kawai dan ba'a son ta tauna abu saboda jijiyiyin kanta dake tare dana haƙori.

       Cikin jin daɗi Yoohan ya amsa yana faɗin, “Thanks you Rich”. Ɗan hararsa Richard yayi da faɗin, “Dama akwai godiya ne tsakanina da kai Mr X”. Murmushi kawai Yoohan yayi amma baice komaiba. Shima Richard ɗin sai ya murmusa yana binsa da kallo. Sam baya iya dogon fushi da Yoohan. Ƙauna yake masa ta gaskiya kuma ta haƙiƙa har cikin ɓargonsa. Yanajinsa a jinin jikinsa tamkar ƴan uwansa da suka fito ciki ɗaya. Kuma shi harga ALLAH bai taɓa jin zafinsa akan auran Nu'aymah da yayiba duk da kuwa ta kasance Bahaushiya kuma musulma. Sai dai salla da Yoohan ya farayi yanzu yana matuƙar damun ransa. ya rasa wane kalar tunani zaiyi akan wannan matsalar, wazai tunkara su tattauna domin haɗa hannu wajen dawo da Yoohan cikin hankalinsa?. Da yayi yunƙurin sanarma wani sai yaji rauni da fargaba ta kamashi. dan haka ya barma ransa ko sauran abokansu su Joseph ya kasa faɗamawa....


           Yoohan dai tuni ya fice a office ɗin abunsa ya bar Rich da faɗawa dogon tunani. A waje yaga Solomon tsaye. Ya ɗan kafesa da kallon mamaki dan ganin yanda Solomon ɗin yay fakare kamar wanda ya tsorata da ganinsa. Bai dai ce da shi komaiba yay wucewarsa.

      Nannauyan numfashi Solo ya sauke yana rumtse idanunsa da wayarsa dake cikin hannu. Yau shikam ya shiga uku, yana fatan Yoohan baiji wayarnan da yakeyi da papa ba. Gaba ɗaya sai wani tsoro na tashin hankali ya kuma baibayesa. Barin asibitin yayi jikinsa na tsuma. dama zuwansa kenan shi da Richard.

          Yoohan da haka kawai yanayin Solomon yaso ɗarsa masa zargi a zuciya ya ƙarasa ɗakin da Aymah take yana wasiwasi. Kwance take akan gadon jiyyarta idanunta a lumshe. Har yanzu bawai jikin nata yayi ƙarfi baneba. Dan ko magana ma da ƙa'ida takeyinta. Kai duk ma sauran abubuwa komai zatayi da ƙa'idarsa saboda ƙwalwarta ana buƙatar ta samu isashen hutun da komai zai gama dai-daita. Dan yanzu dai su Yoohan sun tabbatar da komai Alhmdllh, sai dai zata ringa yawaita ciwon kai kafin wani tsahon lokaci da suma basusan adadiba. Sannan idanunta sun raunana zatake amfani da glass shima kafin zuwa wani lokaci. Bawai bata gani bane, tana ganin komai Alhmdllh, sai dai ba a yanda ya kamataba. Dan idan abu yayi mata nisa tana ganinsa bibbiyu ko dishi-dishi. Sannan sun tabbatar da zata rage yawan hayaniya yanzun.

        Ƙamshinsa da taji ya yawaita a ɗakinne ya sakata buɗe idanunta a hankali. A kansa ta zubasu, sai dai batai masa kallon sakan uku ba ta janye. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke. ya matsa gaban gadon sosai ya zauna, kama hannunta yay cikin nashi. Cikin magana ƙasa-ƙasa da ko kana a ɗakin bajinsu zakai ba yace,

        “How are you feeling?”.

   Hannunta da ke a cikin nasa taɗan motsa, idanunta a lumshe, cikin magana a hankali fiyema da tasa tace, “Alhamdulillah”.

         “Masha ALLAH”. ya faɗa da harshensa karyayye.

       Batare da yace mata komaiba ya kamata zai tayar. Buɗe idanun tayi sosai. A rashin sanin ita yake kallo suka faɗa a cikin nashi. Saurin kauda kanta tayi tana motsa baki kaɗan. Duk da ba magana taiba yasan tsiwarce ta motso, sai dai yanzu kam babu bakin yi yanda ya kamata. Filo ya saka mata ta jingina yanda zataji daɗi. Ya zauna a kusa da ƙafafunta dake a miƙe. Gaba ɗaya jitai ta gama takurewa a wajen. Ga ƙamshinsa yayi bala'in adabawa numfashinta. Shi dai da baisan tanayi ba, ya san dai tunda ta kasance jinin masoyinsa baba malam bazai taɓa gajiyawa wajen jinyarta ba tamkar yanda yasan iyayenta zasu kula da ita. takeaway ɗin ya buɗe yana fuskantarta. Duk da ya fahimci kallonsa takeyi sai bai nuna ya ganiba. Batare da ya kalleta ba yace, “Yau zaki fara cin abinci mai nauyi. Insha ALLAH yanda jikinki keyin ƙyau zamu samu sallama da wuri. Amma sai kin daure kin ringa cin abinci ko yaya ne. Dan yanzu zakiji ɗanɗanon sa sam baya miki wani daɗi. Sai a hankali ne ɗanɗanon harshenki zai warware”.

      Fuska kawai taɗan yamutsa. Dan harga ALLAH kam abincin ma ganinsa kawai da takeyi yanzu amai yake neman sakata, sai dai kuma itama tana buƙatar ganin an sallameta ta bar asibitin nan da duk take jinta a takure.

      Bai damu da rashin yin maganar tata ba. Ya ɗiba abincin a spoon ya nufi bakinta da shi. Har zata kauda kanta yay saurin faɗin, “No, Please!”. Daurewa tai ta buɗe bakin idanunta a rumtse. Ya zuba mata tausayinta na ƙara ratsasa. taja kusan minti biyu tana juya abincin a baki sannan ta haɗiyeshi da ƙyar. Sake ɗiba yayi ya bata. Nanma dai sai da ta ɓata lokaci. Da ƙyar ya samu taɗanci, sai dai sunja lokaci mai tsaho ana ƙaƙa nakayi, dan harda hawayenta shaɓe-shaɓe a fuska. Da ga ƙarshe dai ganin ta ɗanci ya haƙura ya barta. Tissue yasa ya goge mata bakinta da hawayen datayi. Yana ƙoƙarin tashi ta riƙo hannunsa. Kallonta yay kawai sai dai baice komaiba.

      A mamakinsa sai yaga ta ɗauki cokalin daya bata abincin ta ɗibo ta nufo bakinsa. ba ƙaramin harbawa zuciyar Yoohan yayiba. Duk da ba abincine daya cika damuwa da shi ba haka ya buɗe bakin kawai yana kallonta. Zuba masa tayi kuwa batare da ta yarda sun haɗa ido ba. Ta ƙara ɗebowa tana magana a hankali. “Ka rame da yawa. da alama kaima baka da lafiyar kuma bakacin abinci. Amma gashi ni kazo ka tsareni sai da naci. To kaima tsareka zanyi sai kaci”.

        Yanda tai maganarne a sakalce ya sakashi yin murmushi. ya fahinci kuma da iya gaskiyarta take faɗin abinda ke a ranta. Hannu ya kai saman fuskarta a hankali yana faɗin, “Thanks you”. Kallo ɗaya tai masa ta janye idanunta batare datace komaiba. Sai dai taji daɗin thanks you ɗin daya ce mata. Hannu tasa akan hannunsa dake saman fuskarsa ta janye, dan yanda yake mata a kumatu jitake tsigar jikinta na tashi. Murmushi ya kumayi yana cigaba da amsar abincin. itako taƙi yarda su haɗa idanu sam, sai danna masa abinci takeyi.

       A wannan yanayin Dr LiLiya shigo ya samesu. Da tsokana yake cewa, “Irin wannan soyayya haka bazasu bari a warke ba?”.

      Sosai Aymah ta waro idanu akan baturen likitan. Sai dai kuma batai magana ba. Ta ɗan harari Yoohan dake murmushi. Sai kuma ta ajiye spoon ɗin ta kwanta abunta da juya musu baya. Ƙaramar dariya Yoohan yayi har haƙoransa na bayyana sosai. Ƙasa-ƙasa ya cema Dr Liam “Kaga ka jamin an bar bani”.

       Dr Liam dariyar shima yayi yana haɗe hannaye waje guda alamar Sorry.

      Ita dai Aymah bata sake kulasuba. Da za'a bata magani ma ƙin yarda tayi ta kalli kowa a cikinsu. Tana sha kuwa ko mintuna goma cikakku batayi ba barci mai nauyi yay awon gaba da ita. Sassanyar ajiyar zuciya Yoohan ya sauke. Ya kama hannunta data bashi abinci ya sumbata yana wani lumshe idanu. Daga haka suka fito suka bar mata ɗakin shi da Dr Liam


____________★★


            Yau kwanakin su Hajjo biyu da zuwa. gobe idan ALLAH ya kaimu kuma zasu koma harda su baba malam ma. Sunzo sun duba Aymah da jikinta keta ƙara warwarewa Alhmdllh. Sai dai batason cin abinci sai Yoohan yata lallashi da dabara. A hakanma bata yarda taci ita kaɗai. sai dai idan ya ɗeba spoon ɗaya ya bata itama sai ta ɗiba ta bashi. Ita a ganinta wayo takeyi dansu cinye tare ya rage mata aiki. shiko hakan ba ƙaramin shauƙi yake sakashi a ciki ba, da jinsa on top. Ta kai ko ruwan addu'arta ya bata tasha itama shima sai ta rage ta bashi ya sha. Dan harga ALLAH ramar da taga yayi kuma na damunta a cikin rai. Ta tabbatar koda rashin lafiya yayi to harda damuwar halin da take a ciki. Dan ta fahimci shi mutum ne mai tausayi sosai dama.


         Dr Yoohan da Dr Liam Sai Richard sun fito daga Ward ɗin dake gefen wanda Aymah take sai wayarsa tai ring. dakatawa yay domin ya amsa su kuma suka wuce. Papa ne, sun gaisa da maganar data shafesu ya maida wayar cikin aljihun farar rigarsa ta likitanci daya ɗora ya cigaba da tafiyarsa dansu Rich sun wuce. 

      Kamar da wasa sai yaji ana hausa ta lungun daya gitta. Duk da bajin hausar yake ba mu'amula da hausawa da yakeyi a yanzu tana ƙara sakashi fahimtar yaran hausa kaɗan-kaɗan. musamman zama da Nu'aymah duk da bawani jimawa sukai tareba. kawai dai shi mutum ne mai kaifin basira ɗaukar yare dama.

        Samun kansa yay da ɗan komawa da baya. Na daga ƙafa zan bisa nima na ɗakko muku rahoto xoxo da rano sukazo suka tsaidani da surutu🙄, wai su nan sunga wadda suka sani a ƙasar Austria, sunja mana rashin samun wannan rahoton. Dan ina gaisuwa da su ne hankalina nakan lungun da Yoohan ya shiga. Kafin mu gama sai gashi ya fito fuskarsa a tsuke. Kuma tamkar wanda yaga wani abun dayay matuƙar rikitashi ko ɗaure masa kai. Da kallo na bisa. batare dana tsaya munyi sallama da su Rano ba nai azamar binsa a baya. Suna ɗagamin hannuma ko saurarensu ban ƙaraba. Nai gaba ina faɗin, “Maƙalallu sun maƙalle a asibitin nan sun hanani ɗaukar rahoto”. Ina ɓullowa na hango Huguma da Mamu sun ɓullo suma. da alama tare suke dasu xoxo dinma dai. Washe baki suka fara irin su sunga wadda suka sani dinnan dai. saurin ɗauke kai nayi ina cuskule fuska na canja hanya kamarma ban gansu ba. Ina jiyo su Rano na basu labarin wai yanzu suma na gama musu yarfi dan ina tare da Dr Yoohan, Wai ai zamu koma Nigeria zan gane kurena, suma zasu rama ne😣😒.


        A office na iske Yoohan nata kaiwa da komawa. da alama dai tabbas abinda ya tada masa hankali ya jiyo ya kuma gano. Dan yanayin nasa yayi kama da wanda ke acikin ruɗani da al'ajab, harma da kullewar kai.

      To nidai bansan tayaya zanbi na san mi wannan bawa ya gano ba. Sai dai mu cigaba da bibiyarsa kuma kozamu fahimta anan gaba.


        Washe gari da safe su baba malam suka wuce Nigeria harda Richard. Akabar Aymah da Yoohan da Solomon kawai. (Jelar Yoohan😜). Kuka sosai Aymah tasha dan bataso wannan tafiya tasu baba malam ba. gudun samun matsala su Yoohan suka danna mata allurar barci data jata tsahon lokaci.

      Su kansu su Umm ɗin badan sunsoba suka taho, sai dai tunda jikin nata Alhmdllh gara su dawo kan harkokinsu suma tunda mijinta tsaye yake akan dukan lamuranta, ko a fuska basu taɓa ganin gajiyawa daga garesa ba. Hakan yasa ƙaunarsa ta ƙara shige musu zuciya da bargo sosai. Suna sake taya Nu'aymah murnar dacewa da tai da miji na gari mai kyawawan halaye. Hakan na nufin a haifeka cikin musilinci ka rayu da girma a cikinsa bashi bane ke nuna zakafi kowa kyawawan halaye. Balle har kayi tunanin samun lasisin hantarar wanda ya tuba daga baya da masa takama kai kaine mai addini. Shi wannan da kake kalubalanta da jifansa da kalmar tubabbe dan kawai ya shigo addinin islama daga baya sai kaga ya fika rabauta a wajen UBANGIJI. Ya fika ƙyawawan halaye nagartattu abin koyi. Mu kiyayi aibanta waɗanda suka shigo musilinci saboda mu an haifemu a cikinsa, dan wlhy mu hausawa munada wannan banzan halayen a rayuwar zahiri. ALLAH ka shiryemu dai.


       Sun iso Najeriya zukatansu cike dajin daɗin yanda suka baro jikin Aymah. Sun kawoma sauran ƴan uwa labari mai daɗi da saka kwanciyar hankali. Fatan kowa kuma ALLAH ya ƙara mata lafiya ya kuma maidosu gida lafiya.


_________★★★★__________


         Nu'aymah ta cigaba da jiyya da samun kulawa ga mijinta. Duk da kuwa bayan tafiyar su Umm taso rikita kanta da damuwa. Amma Yoohan yayta lallashi da lallaɓa harta haƙura ta cigaba da sakin jikinta da shi yanda ya kamata. Dan duk abinda ya fahimci tanaso shi yake mata. Wannan ya saka ƙara samun nasara sosai game da lafiyarta, wata shaƙuwa ta musamman kuma na sake shiga tsakaninsu. uwar ramar da tayi ta ɗan fara cikowa. Yakan kama hannunta yaɗan fita da ita su zagaya cikin asibitin dan tasha iska. Hakan kuma na sakata farin ciki da sake godema UBANGIJIN daya bata lafiya. Dan idan taga halin da wasu suke ciki zuciyarta na ƙara raunana. Taga ciwonta ba komai baneba ashe. 

      Haka rayuwar ta cigaba da gungurawa har ga su Yoohan da cika sati uku a ƙasar Austria, cikin birin Vienna. Alhmdllh yanzu kam jikin Aymah ko makiyi ya gani yasan an dace. Sai dai tana amfani da glasess ɗinta da yay mata wani masifar ƙyau kai kace na kwalliyane ma. Sai ko yar ramar da har yanzu bata gama cikowaba yanda ya kamata. An basu sallama a daren yau, tare da ɗorata a kan magunguna da zata sha na tsahon watanni biyu har komai ya karasa dai-daita. Sai allurai guda hudu da za'ai mata a kowanne wata sau biyu suma.

      Sosai Yoohan yake a tsananin farin cikin cikama baba malam burinsa na ganin lafiyar Nu'aymah. Hakama Solomon ya nuna jin daɗinsa. Uwar gayya Nu'aymah kam ai ba'a magana. Dan tsabar jin daɗi har rungume Yoohan tayi batare data farga da abinda tayi ba. Gaba daya saita sake sagar masa da gaɓɓan jiki. dan a yanda take masa abubuwa a asibitin nan gaba ɗaya rikita masa lissafin tunani takeyi. 

     Haka dai suka tattaro zuwa hotel ɗin da Yoohan sukai masauki. Bayan sun gumtsama ƴan 9ja labarin sallama. Masoyan su na gaske sun sake tayasu murna. Yayinda maƙiya kam sam ba hakan bane. Wasunsu ma sai shiri da suke musu na wasu bala'oin domin tarbarsu da shi. Dan a cewarsu babu abinda za'a fasa. Yanzu ne ma wasan zaiyi zafi.


Nidai nace, “Hummm”.


______________________________


            Tunda suka iso ƙayataccen Hotel ɗin daya gama haɗuwa da ƙawatuwa, Nu'aymah take jinjina girman UBANGIJI da rahamarsa. Hotel ne daya ginu, ginuwa mai ban mamaki da al'ajabi. dan wannan ba fasahar masu gini bace, wani ikone da rahamar UBANGIJI da hikinarsa. Ginine mai tsananin tsayi da ado, harma batasan yaya zata musalta gamai karatu ba. Mutane nata kaiwa da komawa duk da kuwa dare ne, maza da mata harma da iyaye da yaransu. Daka gani dai kasan wajene na hutawa, dan harda baƙakenmu tsilli-tsilli a wajen ana more rayuwa.

        Cike da neman tsokana Yoohan yace, “Kar dai kisa ace mana ƙauyawa hajjaju”. Hararsa ta ɗanyi, sai dai batace komai ba dan yanzu ba Aymahn da baceba. Sam bata cika son magana ba da hayaniya. Shiyyasa wani lokacin idan yaji shirun nata yayi yawa sai ya takaleta koda hararsan tayi. dan yanason yaga ta dawo kamar da ɗinta mai tsiwa abin na masa daɗi. Amma yasan sai a hankali. Koda kuwa zata koma kamar da ɗin ba hundred percent ba.

        Batare da tasan daga ina Solomon ya ɓullo ba ta gansa a gabansu. Cike da girmamawa ya risinar da kansa yana gaishesu da mata sannu da zuwa da taya murnar samun lafiya.

        Ta amsa masa kadaran kadahan. Dan mamakin irin wannan lamari takeyi, kenan a ko ina Yoohan yake suna tare da wannan mai gadin ko mi?. Bata da mai bata amsa dan haka ta hadiye abunta ta maida hankalinta ga sauraren bayanin da Solomon ke ma Yoohan akan ɗakin da zasuje, ya mika masa wani ɗan card. Nu'aymah ta fahimci da ba'anan suka saukaba kenan. A yau ne Yoohan ɗin ya saka suka dawo nan ko kuma yaya ai oho dai. Sai dai batasan minene dalilin yin hakanba, bakuma ta tambaya ba.

       Hannunta ya kama suka shiga har cikin hotel ɗin har masaukinsu. sai dai har suka iso ƙofar ɗakin tanata faman kalle-kalle. dan da gaske ta zama baƙauya. Duk da kuɗin gidansu iyayensu basa taɓa barinsu zuwa irin waɗanan wajajen koma tace ƙasashen. Iyakar yawonsu baya wuce Saudia shima Umrah ko aikin hajji ke kaisu. Sai ko mazansu da kan je harkokin kasuwanci dana karatu wasu ƙasashen. amma dai su mata ba'a barinsu sam. 

     Kati ya fiddo a aljihun green jeans ɗinsa ya saka a wani abu kamar na atm yay danne-danne ƙofar ta zuge kanta gida biyu. Zare katin yayi ya kalleta da mata nunin ta fara shiga. Bismilla tayi haɗe da sallama ta saka kafarta cikin ɗakin.............✍

        

No comments

Powered by Blogger.