Saran Boye 21-25
No. 21
.................“Adawiya!!” hajjo ta faɗa a ɗan tsawace. Yayinda Ahmad da Abdallah ma sukai wani zallon mamakin abinda Adawiya tayi suma.
Kallonsu tai a firgice idanunta na tara ƙwallar takaici da jin zafin ganin abinda batai zato ko tsammani ba. Ta buɗe baki zatai magana a zafafe sai kuma ta tuna abinda ta nema mantawa. Saurin sauke numfashi tayi tana fashewa da kuka, tare da juyawa ta kalli Nu'aymah dake tsaye dafe da kujerar data taimaketa ta hanata faɗuwa lokacin da Adawiyar ta turata.
“Nayi fushi wlhy Aymah, yanzu dama dake za'azo amma kikaƙi sanarmin saboda ke yanzu kinma daina sona?”. Adawiya ta faɗa cike da makirci da waskewa.
Ajiyar zuciya Abdallah da Ahmad suka sauke, dan duk zatonsu Adawiya da gaske da faɗa tayi abinda tayi. Hajjo dai bata motsa ba, amma ta kafesu da kallo su duka huɗun tana nazarin kowa.
Jin abinda Adawiya tace ne ya saka Nu'aymah sakin murmushi, dan tsaf ta fahimci Adawiya canja hanya tayi, inkuwa hakane ai itama tanada wayonta, dan wani abun ma sai dai ta koyama Adawiyar duk da kuwa ta girmeta da wasu wattani. Sake tahowa tai da ɗan gudunta ta rungume Adawiya tana faɗin, “Afuwan habibiya, surprise nai niyyar miki shiyyasa na hana kowa faɗa miki”.
Leɓe Adawiya ta cije dan ta juyama su Hajjo bayane, itama cike da ɗacin zuciya ta rungume Nu'aymahn tana magana cikin kuka, “ALLAH saina hukunta ki tunda kika sani kuka”. Nu'aymah tai dariya hawaye na sakko mata itama, ta ɗago Adawiyan daga jikinta tana durƙusawa gabanta da riƙe kunnuwanta, “Afuwan hassanata, kaina bisa wuya Please”.
Karan farko Adawiya ta saki dariya, itama sai ta durƙusa kamar yanda tayi sunama juna kallon ido cikin ido, Nu'aymah murmushi takeyi, Adawiya kam ta haɗe fuska ganin su hajjo basa ganinta. “Kin haƙura kenan?” Nu'aymah ta faɗa tana wani ɗage ma Adawiyar gira ɗaya da sakin mata lallausan murmushin da yay mata tsaye a maƙoshi.
Kasa magana Adawiya dake mata kallon tsantsar takaici da haushi tayi, sai kawai ta rungumeta a jikinta tana gyaɗa kai........
Gyaran Murya Yah Ahmad yay yana faɗin, “Kunga malamai ya isheku haka, ku barmu mu ƙarasa ƴar yunwar azuminmu da sauran yawu a baki dan ALLAH, idan akasha ruwa komaima sai kuyi zamu tayaku da sulhu”.
“Faɗa musu dai”. Abdallah ya faɗa a wani irin yanayi yana komawa kusa da hajjo ya zauna. Ƙaramar dariya Hajjo tayi kawai tana ɗauke kanta, sai kuma ta kalli Abdallah tana faɗin, “Kaga Audillahi kaini ɗakina na huta kaji, bazan iya luguden laɓɓa ba da azumina a baki”.
Fuskarsa ƙawace da murmushi ya miƙe tare da taimakama hajjon itama ta tashi. Har ɗakin da zata zauna ya rakata, tana zama Nu'aymah na shigowa itama. Duk kallonta sukai shi da Hajjon, ta ajiye jakarta tana zama a kujerar dake a ɗakin ƙwaya ɗaya tal, batare data kalli Abdallah ba tace, “Yah Ab! Ina yini?”. Kallonta yay a karon farko suka haɗa ido, sai ta ɗauke nata gefe tana komawa jikin kujerar ta jingina.
“Kunzo lafiya?”. Ya amsa mata shima cike da basarwa, dan haka kawai yanzu yakejin zafin abinda ta aikata a ranar ɗaurin aurensu. Ƙin sake tanka masa tayi, hajjo kuwa tamayi kamar bata a ɗakin.
Ƙofa ya nufa dan kai Ahmad nasa masaukin yana faɗin, “Ki taso ki koma ɗakin Adawiya, ita hajjo sai ta zauna anan...”. Kafinma ya rufe baki cikin sauri tace, “A'a zan zauna anan tare da Hajjon”.
Da ga Hajjo har Abdallah kallonta sukai, amma saita ɗauke kanta tana ɓata fuska danma kar Hajjon tace dole sai taje. Shima har zai sake magana sai kuma ya fasa ya fita kawai.
“Miyasa bazakije can ɗinba? Bayan ƴar uwarki na cike da ɗokin ganinki?”. Hajjo ta faɗa bayan ficewar Abdallah.
Nu'aymah dake ƙoƙarin cire kayan jikinta tace, “Babu komai Hajjo, nafison kawai na zauna da ke kodan himma akan ibadar da mukazoyi, sannan nifa ma ittiqafin zan shiga insha ALLAH”.
Murmusawa Hajjo tayi kawai tana ɗauke kanta batare da ta sake cema Nu'aymah komai ba, itama Nu'aymahn sai ta shige bayi abinta batare data jira amsar hajjon ba.
★★★
“Kuturun ubancan kayyasa! Yanzu wane algungumine mai wannan shirya tafiyar a gidanmu?”. Adawiya daketa faman zagaye ɗakinta ita kaɗai ta faɗa tana cizar laɓe kamar zata hudashi. Ganin babu mai bata amsa ta rarumo waya ta fara neman maman Aaida. Bugu biyu kuwa ta ɗaga. Harta fara tsokanarta Adawiyan ta katseta da faɗin, “Maman Aaida yanzu ba lokacin wasa bane, ko kinsan sister ɗin nan nawa da zata auri Yah Ab da, ta biyo kakarmu sunzo Umrah tare?”.
Da ƙarfi Maman Aaida tace, “Na shiga uku, da gaske dan ALLAH?”. Adawiya da ranta ya ƙara dugunzuma tace, “Wlhy kuwa. Bama zuwan nata bane tashin hankalina Maman Aaida, kinga kuwa yanda Yah Ab duk ya susuce, gashi kakarmu ɗin nan shegen sa idone da ita wlhy”.
“Tab, lallai aiki ya samemu, dan kuwa wlhy mukai sanya to ki tabbatar nanda wata ɗaya ko sati biyu ma mijinku zai koma na mata uku....”
“ALLAH ya kiyaye” Adawiya tai saurin katse Maman Aaida hawaye na ziraro mata a idanu. Takaicin maganganun maman Aaida ya sakata katse kiranma gaba ɗaya tai wurgi da wayar kan gado.
Abdallah dake ƙoƙarin shigowa ɗakin yace, “Lafiyarki kuwa kike wurgi da waya? Kamar ba kuɗi akasa aka saya ba!”. Da sauri tasaka hannu ta share hawayenta, kafin ta nufesa ta rungume da ƙarfi. Saurin tureta yay yana faɗin, “Haba Adawiya, shin wai kina mantawa muna azumi ne? Duk hanyar da zaki raunanama mutum azumi kin santa”.
“Kayi haƙuri Yah Ab, wlhy ɗokin zuwan Nu'aymah ne ya sakani yin hakan”.
“Umyim! Kina ɗokin zuwan natane kika barta tafiya ɗakin da Hajjo zata zauna ta sauka”. Kamar zatai kuka ta kallesa, acan ƙasan ranta kuma tamkar ana babbaka wuta, cikin shagwaɓa tace, “Damafa jira nake kazo na kawo maka ƙararta ALLAH, nayi-nayi tazo mu zauna anan taƙi, wai batason shiga haƙƙinmu”.
Kafeta yay da idanu kamar mai nazarinta, sai kuma ya ɗauke kawai yana ƙaɗa kansa ya fice batare daya bata amsa ba.
Harara ta raka bayansa da shi harya fice, taja gajeren tsaki, ‘Wlhy tunda aka munafunceni sai yarinyarnan ta gwammaci kiɗa da karatu a gidan nan, ni kama ƙaramin haske akan dawowarta ɗakin nan Yah Ab, dan wannan itace babar damar da zan riƙe wajen tarwatsa zuciyarta, saina maidata mahaukaciyar gaske idan da ƙaramin haukane a kan nata mtsoww!! Aikin banza kawai’.
Oho, ita Nu'aymah ma batasan tanayiba, dan bata sake leƙo falonba har lokacin shan ruwa ya ƙarasa, itama Adawiya bata shiga inda sukeba ta maƙale akan shirya kayan shan ruwa takeyi. Duk da kuwa ba ita ta girkaba. Fita Abdallah yay ya musu order ɗin komai daya dace, dan yasan Adawiya bazata iyaba ita kaɗai tunda sunada yawa. Bai kuma kamata asa Nu'aymah shiga kitchen ba daga zuwansu.
Aikin da Adawiya tayi kawai shine shirya abincin a tsakkiyar falo, wanda saida Abdallah ma ya tayata suka tsara komai a inda ya dace.
Koda aka kira salla ruwa da dabino kawai suka ɗanci, sannan suka gabatar da sallar magriba. Daga hajjo har Nu'aymah basu zaƙeba akan abincin, sukai zamansu gefe suna tsumayen tayi daga Adawiya. Itako hankalinta ma baya garesu, tana can tana ƙullama zuciyarta abinda zata aikata a wajen shan ruwan idan an zauna danta cusama Nu'aymah takaici. Shiyyasa ta fara ƙoƙarin shiryama Abdallah nashi tunkafin su shigo.
“A'a Hajjo ya naga baku fara buɗa bakin ba?”. Abdallah da ke ƙoƙarin ƙarasowa cikin falon sosai ya faɗa idonsa akan Nu'aymah dake danna waya. Wando da rigane marasa nauyi a jikinta, sanin basu kaɗai bane ya sakata ɗoro hijjab a sama wanda yaje mata har gwiwa.
Murmushi hajjo dake kallon Adawiya cike da nazari tayi, sai kuma ta maida kallonta ga Abdallahn tana faɗin, “Ku muke jira mana, dan zaifi daɗin ci ai”. Cike da jin daɗi ya kama hannunta ya sumbata, kafin ya zauna kusa da ita yana gaisheta da mata barka da shan ruwa. Nu'aymah dake a ɗayan gefen Hajjo itama tace, “Barkanku da shan ruwa”. Ahmad dake ƙoƙarin zama kusa da Abdallah ne kawai ya amsa, sai hajjo data ƙwace wayar tana harararta da faɗin, “Sai yanzu kika san damu?”.
“Waini miyasama na biyoki?”. Nu'aymah ta faɗa cikin haushin amshe mata waya tana tura baki cike da shagwaɓa. Hajjo da Ahmad sukai dariya, hajjo tace, “Tambayi kanki mana, ja'ira kawai”.
Adawiya da abun sam bai burgetaba, ta kalli Abdallah da gaba ɗaya hankalinsa akan Nu'aymah yake. Haushine ya sake turniƙeta, murya a cinkushe tace, “Yah Ab ga abincinka”. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa. “Gasu hajjo da suke baƙi baki haɗa musuba sai ni da ko shigowa banyiba........?”
Katseshi Hajjo tai da faɗin, “Kaga barta, ai abincinma so nake a haɗesa a babban tray mu haɗu tare mu sami ladan juna”.
‘Tabɗi jan’ Adawiya ta faɗa a ranta tana jin wani tuƙuƙin baƙin ciki, a fili kuwa sai ta kafe Abdallah da ido a zatonta ko zaice wani abu. Duk da ya ganta sarai baice uffanba, saima ɗauke kansa yay abinsa.
Hajjo da duk take lura da motsin kowa tace, “Zainabu zuba abincin, ki haɗe da wanda Adawiya ta zuba duk a haɗu kowa ya saka hannunsa”.
Murmushi Nu'aymah tayi a karon farko, ta gyara zamanta tana faɗin, “Angama Hajjaju uwar masu gida, uwar gida ran gidan malam Hashimu ɗan jibiya”.
Sosai Abdallah, Ahmad da Hajjo suka sanya dariya da kirarin na Nu'aymah. Hajjo ta ranƙwasheta akai tana faɗin, “Ja'ira”. Adawiya kam wani baƙin cikine ya kumeta a rai, harta kasa daurewa ta miƙe.
Abdallah yace, “K kuma ina zaki?”. Da ƙyar ta iya haɗiye kukanta tace, “Zan ɗakko abune a kitchen”. Bata jira amsarsa ba tai gaba.
Wani shegen murmushi Hajjo da Nu'aymah suka saki, wanda kowa da manufar nasa.
Hawaye sosai Adawiya tayi a kitchen, sai dai gudun kar wani ya biyota yasata saurin wanke fuskarta ta ɗakko ruwa ta fito.
Koda ta dawo babu wanda ya tanka mata, saima ƙoƙarin kai abinci suke a cikinsu. Yayinda Abdallah duk Motsin Nu'aymah na gunada ne a idonsa. Itama Nu'aymahr dai hankalinta na a kansa. Sai dai tana ƙoƙarin fuskewa ita babu mai ganeta.
A haka dai suka kammala buɗa bakin, yayinda kowa yaci komai dai-dai misalin da bazai cutu ba. Duk da akwai gajiya tattare dasu haka suka rarrafa zuwa massallaci sukai isha'i da asham. Kafin su dawo kowa ya nema makwanci.
Abin mamaki sai ga Adawiya tayi shiri ta tafi kwana ɗakin Abdallah.
(😂ta wajena Adawiya gara ki dage ki samu kan, gaskiya fa, dan naga su o'e anzo saudia da shirin Snatching mijin mutane.😎🙄🚶🏻)
_______________________________
*_NIGERIA_*
“Wai tunanin mi kiketayi ne haka da zurfi Darling? indai akan Yoohan ne na samo mana mafita”.
Da sauri Momy ta juyo tana kallon papa da ke maganar da yarensu, bakinta har ɗan rawa yake wajen tambayarsa wace irin mafita ya samo?.
Sai da ya rungumeta kafin yace, “Mu lallaɓashi ya auri Miracle kawai”. A wani irin zumbur ta miƙe zaune tamkar wadda maciji ya sara. Ta nuna Papa da yatsa tana faɗin, “Kasan mi kake faɗ kuwa Darling? duka-duka shekarar Yoohan ɗin nawa da kake maganar yay aure? Indama son Miracle ɗin yake to da sauƙi, amma kana ganin yanda yake mata a gidan nan ai ko”.
Tsuru papa yay yana kallon yanda matar tasa ke masifa kamar zata haɗiye harshenta, sai da takai ayar zancenta tana wani huci sannan yay saurin jawota jikinsa yana girgiza kansa. “Ki fahimceni mana, idan Yoohan yay aure matarsa zata dinga ɗebe masa kewa a duk lokacin da ya shiga irin wannan damuwar, kum.......”
“Kaga nifa bani da lokacin wannan maganar, ka barni barci nakeji”. Ta faɗa ranta a ɓace da ƙwace jikinta taje gefen gadon ta kwanta. Da kallo kawai ya iya binta har na tsahon lokaci, kafin shima ya kwanta ɗin yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. A cikin ransa kuwa ya ƙudiri aniyar lallaɓata ita da Yoohan ɗin har sai sun amince da ƙudirinsa.
*_WASHE GARI_* safiyar lahadi, tunda safe jama'ar gidan suka shiga hada-hadar shirin fita church, dan papa ma tun da sauran duhun safiya ya fice shi.
Rich daya fito wanka ya kai dubansa ga Yoohan dake zaune kan sofa, ƙafafunsa miƙe akan table, ya jingina bayansa kansa na kallon sama. Duk da idanunsa a lumshe suke ya tabbatar ba barci yake ba.
“Doctor ya kamata ka tashi kai shiri mu shiga church ko? Idan mun fito sai mu ɗan zaga gari danni yau da yamma zan koma Lagos”.
Shiru Yoohan bai motsaba, duk da kuwa sarai yanajin Rich ɗin. Sai da ya ɓata wasu mintuna kafin ya buɗe idanunsa da sukai wani irin kumburowa, fatarsu tayi jaa sosai alamar jin barci tattare da shi, hakama fuskar tayi jajur sosai abin tausayi. Miƙewa yay batare da yayi magana ba, ya wuce toilet yana ɗan ɗingisa ƙafarsa da bata gama sakiba, sai dai hakan kuma sai ya bama tafiyar tasa wani style daban kamar mai tafiyar izza.
Baija dogon lokaciba ya fito ɗaure da towel ruwan gwaiduwar ƙwai. Babu kowa a ɗakin dan Richard ya gama shirinsa ya fice. Ya ƙarasa gaban mirror, shafe jikinsa yay da mai da kayan ƙamshi tamkar yanda ya saba, kafin ya nufi wajen kayansa. Fararen suit ya ɗakko yana ɗan yamutsa fuska da kallonsu. Sai kuma yabar wajen dasu zuwa gaban gado. Tsaf ya shirya a cikin suit ɗin da sukai masifar zama masa a jiki, tare da fiddo surarsa mai jan hankalin mata dama mazan kansu. Necktie ɗin ya ɗauka a hannu tare da jacket ɗin suit ɗin, dan shi kam har yanzu ɗaura tie na masa wahala. Gaban mirror ya sake komawa ya feshe kansa da kalolin designers ɗin turarurrukansa, kafin ya ɗau sarƙa ɗaya a cikin sarƙoƙinsa na Cross da taji zallar diamond tanata ɗaukar idanu ya saka. Ya ɗauki agogo ya ɗaura tare ɗan wani abin hannu na gayu ya ɗaura a ɗayan hannun, ya kuma manna ɗan kunnensa a kunne ɗaya. Yayi ƙyau sosai, duk da kuwa fuskar a turɓune take matuƙa. Amma yanda yau ya gyara kansa da sajensa sai yay ɗas da shi kamar ka suresa ga gudu.
Tun fara sakkowarsa daga benen Mom da Rich, Solomon dake a falon duk suka zuba masa idanu, sake ɗaure fuska yayi yana ƙarasa sakkowa. Saurin tararsa Solomon yay da kofin coffee daketa turiri akan tray, yace, “Good Morning sir”. Kansa kawai ya ɗaga masa yana gyaɗa kai, tare da ɗaukar coffee ɗin ya nufi Mom da ta tsatstsaresa da idanu tun sakkowar tasa, sai dai fuskarta sam babu walwala. Tayi ƙyau sosai abinta tamkar zata gasar sarauniyar ƙyau. Necktie ɗin hannunsa ya miƙa mata batare da yayi magana ba, saima kofin coffee ɗinsa da yakai baki yana curɓa kamar bayaso.
Tsaye ta miƙe, duk da ya fita tsaho, amma da yake tana kan tudun dining ne saita samu damar kaiwa wuyansa cikin sauƙi. Ɗaura masa tie ɗin tayi, tare da amsar jacket ɗin ta koma bayansa. Hannunsa guda ya miƙa mata ta saka masa, ya sake miƙa ɗayan ma ta saka, sannan ta zagayo gabansa tana gyara masa da ƙyau.
Ta ɗan saki murmushi tana masa wani narkakken kallo, kafin takai hannunta saman fuskarsa ta shafa kwantaccen sajensa dayin magana ƙasa-ƙasa kamar mai raɗa. Ɗanja baya yay yana zame hannunta, murya a cinkushe yace, “Thanks Mom”.
Kafin ta samu damar yin magana ƙannensa dake fitowa cikin nasu gayun suma suka shiga gaishesa ɗaya bayan ɗaya. Hannu kawai yake iya ɗaga musu yana cigaba da shan coffee ɗinsa cike da basarwa.
Ganin yanda Mira ke binsa da wani shu'umin kallone ya sakashi miƙama Solomon kofin duk da bai ƙarasa ba, batare da yayima kowa magana ba ya nufi hanyar fita abinsa cike da takun nutsuwa da ƙasaita sai kace wani jinin mulki.
Dukansu baya suka take masa, yayinda Gebrail yay saurin kaiwa inda yake yana riƙo hannunsa. Batare daya kallesaba yace, “What happend?”. Murmushi Gebrail yayi yana susar kai, cikin ɗan in ina yace, “Brother Yoohan kuɗi nakeso Please”.
Yoohan baice komaiba, ya zare hannunsa daga cikin na Gebrail ɗin, ƙarasawa yay jikin motar da yaga Rich tsaye yana waya. Da sauri ɗaya a cikin Guards ɗinsa ya buɗe masa yana gaishesa. Hannu kawai ya ɗaga mar ya shige. Richard ma shiga yay ta ɗayan gefen, Solomon da driver ma suka shiga. Cike da ɗoki Gebrail da yasan matsalarsa ta yanke ya shiga motarsa shima tare da su Mira da taso bin motar Yoohan ɗin. Sai dai ganin Rich datai tunanin ba a gidan ya kwanaba da, ya sakata haƙura ta shiga ta Gebrail ɗin ita da joy.
Motocin na gama fita a gidan Yoohan ya zaro wayarsa dake cikin aljihu, transfer ɗin kuɗi masu yawa yayma Gebrail tamkar baisan ciwonsu ba, kafin ya ajiye wayar gefensa ya maida kansa ya jingina da kujera ya lumshe idanunsa.
Har motocin suka tsaya a katafaran church ɗin da papa ke riƙe da shi Yoohan bai motsaba, duk da kuwa Rich na masa bayani ne akan wata harkar business ɗinsu da sukeyi tare.
Katafaren church ne mai girman gaske, wanda akaima gini na ƙawa da ɗaukar hankali, dan a gaba ɗaya gaban church ɗin da idanuna ke iya gani anyisane da zalkar glass. Yayinda akasa ƙaton tambarin Cross da akayisa da golden ɗin abu. Tun a farkon shigowar titin zaka faracin karo da muryar papa dake lecture. Gaba ɗaya titin wajen sun kashesa babu maibi saboda motocin da duk akai parking masu tarin yawa. Securitys ɗin church ɗin da sauri suka shiga bama motsocin su Yoohan ɗin hanya cike da tsantsar girmamawa. Sai da sukai parking a waje na musamman da aka tanada domin motocin nasu dama sannan aka shiga buɗe musu suna fitowa.
Yoohan ne ƙarshen fita, dan sai da ya gama jan ajinsa kafin ya ziro sandarsa ta gayu sannan ya fito gaba ɗayansa. Gebrail da tun a hanya yaga alert yay saurin ƙarasowa ya rungumesa yana godiya. Baice dashi komaiba sai shafa masa baya da yay kaɗan.
Yanda securitys ke basu kariya da tsantsar kulawa sai ka ɗauka dajin sambisa zasu shiga🤥🙄, suna zagaye dasu har ta ƙofar da take ta musamman domin iyalan papan kawai da shi. Tanan suka shiga cikin church ɗin dake a cike maƙil da mabiya kamar zai fashe.
Duk suka zuba musu idanu suna miƙewar girmamawa a garesu cike da sha'awa da ƙauna. Sai da suk suka ɗaga musu hannu banda Yoohan da ko kallon basu ishesa ba sannan suka ƙarasa wajen zamansu na musamman dake a gaba duk suka zauna.
Papa dake a gaban wani glass mai ƙyau da aka ƙawata da golden ga abin magana kusan huɗu a jiki yay murmushi yana ma iyalan nasa barka da zuwa, kafin ya cigaba da zubo bayani cikin kwakwazo da karaɗin da aka san fastoci da shi, ko haɗiyar yawu bayayi😕.
A hankali sai hayaniyar ta fara takurama Yoohan, duk da kuwa tunda ya zauna yana jingine ne da kujera idanunsa a lumshe kamar mai barci. Siririn tsaki yaja yana yamutsa fuska. Ya shafa kunnensa na dama dake manne da Bluetooth yana cizar lip. Sai kuma ya buɗe ido da motsawa zai miƙe Rich yay saurin riƙe masa hannu. Ransa a ɓace ya kallesa, sai dai baice komaiba.
“Please ka daure” Rich ya faɗa cike da marairaicewa dan kar Yoohan ɗin ya bijire. Siririn tsaki ya kuma ja kaɗan ya maida kansa ya sake kwantarwa ya rufe idanu.
Kusan awa guda Yoohan nata sake daurewa duk da kansa ya fara masa wani azababben ciwo. Kiran daya sake shigowa a wayarsa ne a karo na babu a dadi ya sakashi yamutsa fuska, duk kiran da ake masa bai amsa ko guda ɗaya ba, amma yanzu sai yaji buƙatar amsawar. Miƙewa yay zai fice Rich yay saurin sake riƙosa. Nuni yay masa da Bluetooth ɗin kunnensa batare da yayi maganaba. Hakanne ya saka Rich sakinsa yana gyaɗa kai.
Sama-sama ya amsa mutumin dake gaishesa, kafin yay shiru yana sauraren bayaninsa da magiyar da yake masa akan buƙatar mutanen da kimarsu ta wuce ace Yoohan ɗin yaƙi buƙatarsu.
Ajiyar zuciya Yoohan ɗin ya sauke a karon farko, batare da ya amsaba ya yanke kiran kawai. Wayarsa ya ciro yay ɗan typing ya tura abinda shi kaɗai ya sani. Mintuna uku ba'a rufaba saiga reply an naido masa. Buɗewa yay ya gani, batare da yayi maganaba ya maida wayar aljihu yana ɗan dube-dube kamar mai neman wani abu. Sai kuma ya sake zaro wayar ya sake yin wani abun.
Yanzu kam ya kai tsahon mintuna biyar yana jiran reply ɗin kafin a turo masa. Shiru yay yana ɗan kallon wayar kamar mai nazari, kafin ya gyaɗa kansa da nufar inda motocinsu suke da wasu a cikin guards ɗinsa tsaye a wajen.
Batare da yayi maganaba ya miƙama drivernsa hannu da masa nunin ya bashi key. Kamar driver zaiyi magana sai kuma ya haɗiyeta da sauri ganin kallon da Yoohan ɗin ya zuba masa. Saurin bashi key ɗin yayi, shi kuma ya buɗe motar da kansa ya shiga mazaunin driver yay mata key tare da yin reverse ya bar wajen securitys nata risina masa cike da girmamawa.............✍
To ɗan dabe ina zuwa kuma🤥🤐?.
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
*_INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN:_*
*_HERBALS APHRODISIAC NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*
*_TO KU SAURARA KUJI, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!!_*
*_MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA CIKI DA WAJE_*
*_MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI! LUWAI! TAMKAR TA JARIRAI_*
*_AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*
*_KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*.
*_AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*
*_KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
*_MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_*
_INSTAGRAM LINK DIN MU:_
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac
_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz
_NAMBAR TARHON MU_
08169380189
*_KARKA BARI A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYANMU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._*
__________________________________
No. 22
...............Hankali tashe guards ɗinsa ke kallon juna, kowa nama ɗan uwansa tambaya da idanu dan bakunansu sun musu nauyi har Yoohan yabar sashen church ɗinma gaba ɗaya.
Jigum-jigum sukai da fatan ALLAH yasa ya dawo da wuri kafin madam Chioma ko papa wani ya fito daga cikin church ɗin.
Sai dai kuma addu'ar tasu bataci ba, dan bayan kamar mintuna ashirin da barin Yoohan wajen Rich da ya ga bai dawoba ya miƙe ya biyo bayansa bisa umarnin Madam Chioma. Yanda yaga Guards ɗin sunyi diri-diri da idanu lokacin da yake tambayarsu ina Yoohan ya sakashi daka musu tsawa. Sake rikicewar sukayi, kowa na inda-indar bada amsa. A haka Madam Chioma itama data biyo bayan Rich ɗin ta samesu. Sake ruɗewa sukayi, dan sunsan idanma azaba ce tafi papa akan Yoohan, ga Rich shima ɗan babu sauƙine.
Da ƙyar driver ya iya dauriyar faɗa musu yanda akayi, jikinsa har rawa yakeyi. Yanda Madam Chioma ta rikice sai ka rantse yaronta ɗan shekara biyu ko uku ne ya ɓata. A take ta birkice lissafin Guards ɗin Yoohan da securitys ɗin church ɗinma kansu. Ta kuma tabbatar musu nanda awa biyar idan Yoohan bai dawo ba saisun gane kuransu.
Ana a cikin wannan dambarwar ne aka tashi daga church ɗin. Mutane suka fara tururuwar fitowa suna nufar inda ake rabon abinci. gudun kar ai abin kunya Rich ya shiga lallaɓa madam Chioma akan ta kwantar da hankalinta maybe Yoohan gida ya nufa, tunda duk sunsan a yanayin da yake baya buƙatar kowanne kalar hayaniya. Zata iya yuwuwa ya ƙosa ne da zaman shiyyasa. Da wannan ya samu yaci ƙarfinta suka koma ciki inda suka tarar duk wanda zai fita sai yaje ya jefa kuɗin baikon sa tare da karɓar wani abu da papa ke saka musu a baki sannan mutum ya fice.
Matsawa madam Chioma tai kusa dashi tai masa magana a kunne, kansa kawai ya gyaɗa mata yana murmushi. Ita kuma ta juya ta fito yaranta da su Mira na biye da ita. Koda suka fito sai manyan mata suka zagayeta anata miƙa gaisuwa ga matar Pastor, harma da mazan da matasa kowa burinsa ya gaisheta. Yayinda wasu keta tambayar ina Yoohan dan sun riga duk sun gansa ɗazun. Da yake shi dama zuwan nasa bawani sosai bane saboda yanayin aikinsa sai yazam duk sanda yazo sai su maidashi tamkar wani tauraro mai fitowa a daren sha biyar.
Cike da yaƙe madam Chioma ke basu amsa da cewar wani uzirin gaggawa ya sakashi tafiya, amma wani satin zai tsaya yay gaisuwa da kowa.
Da ƙyar ta samu kanta daga wajensu, gashi rabin hankalinta duk yana ga Yoohan da Rich keta faman kira yaƙi ɗaga waya. Daga ƙarshe ma wayar bata shiga.
Tun shigowar motocinsu ƙaton harabar gidan suka fahimci Yoohan ba gida ya zo ba, dan babu ko mai kama da motar da ya shigo acikin jerin mitocin dake gidan. Sai da suka gama fita sannan Madam Chioma ta ƙwalama maigadi kira cikin ƙaraji. Jikinsa na ɓari ya ƙaraso gareta cikin cika umarni.
Kafinma takai ga jefa masa tambaya Miracle ta rigata. Mai gadi yay saurin basu amsa da cewar Yoohan baizo gida ba. Gaba ɗayansu hankalinsu sake tashi yayi, kowa ya fiddo waya suka shiga nemansa..........😒
🙄😏Mufa an ishemu kamar wani ɗan gwal🤕😤.
_____________________________
Koda Yoohan yabar gidan wani ma'aikata ya nufa, duk da kuwa da ƙyar yake jan motar saboda nauyin jiki dana zuciya da rashin baccin ya haddasa masa.
Yana tsaida motar a inda ta dace ya ɗan kife kansa a sitiyarin motar na wasu sakkani, zuciyarsa ce keta faman masa kai kawo akan abinda yake shirin aikatawa. wani ɓangaren na ƙarfafasa akan dai-dai, wani kuma na raunana masa niyyar tasa. A haka dai ya kwashe mintuna har biyu kafin kiran daya shigo masa waya ya maidashi cikin hankalinsa. Ɗagowa yay a hankali yana yamutsa fuska, ganin mai kiran nashine ya sakashi ɗagawa tana gab da tsinkewa.
“Na shigo” ya faɗa kawai cikin harshen nasara. Bansan amsar da aka bashiba. ya dai yanke kiran tare da buɗe motar ya fita.
Wani matashin saurayi da zasu iyayin sa'anni ya fito daga cikin ginin ma'aikatar fuskarsa ɗauke da murmushi. Kallo ɗaya zakai masa ka shaida shiɗin musulmine, dan yana sanye cikin shadda bara sol dataji ɗinkin tazarce, ga ƙaton tambarin salla a goshinsa ya kuma murza baƙar dara mai taushi.
Tunda ya tunkaro Yoohan ɗin kallonsa yake ta ƙasa ido cike da nazari. amma ba kowa zai fahimci yana kallon nasaba musamman idan akai dubi da yanda yay wata tsayuwar basarwa yana busar iskar dake kaɗawa ta hantsi mai gauraye da ɗumin rana.
“Ina fatan dai baƙo nane?”. Saurayin yay maganar fuskarsa ɗauke da fara'a duk da kuwa tun daga nesa ya gama shaida Yoohan ɗin ba musulmi bane.
Duk da Yoohan yana mu'amulat da musulmai batun yanzuba, a mabanbanta ƙasashe da yarurruka kuma, baya iya sakin jiki da su. Dan shi kullum yana cikin yin taka tsantsanne karsu cutar da shi kamar yanda aka ɗorasa a hakan tun ƙuruciya. Ya dai yarda zai ƙyautatama mai buƙatar taimakonsa ko a wane irin yare yake ko addini, zai kuma gudanar da aikinsa da gaskiya ga kowa. Amma bai aminci da yayi dogon aminci da musulmin ba.
Sai dai kuma gashi yau a karan farko na tarihin rayuwarsa matsashin saurayi ya burgesa, harma da shigar kamalar dake a jikinsa. Duk da babu ɗigon fara'a kota sisin kwabo tattare da shai sai ya jinjina kansa cikin lumshe ido yana mai miƙama saurayin hannu.
Saurayin ya sake faɗaɗa fuskarsa da murmushi yana faɗin, “Ina godiya ƙwarai da amsa wannan gayyata tawa da banyi zaton zata karɓu ba. Sunana Hamza Ibrahim khalil, manager mai aiki a wannan kamfani namu mai albarka”. Yanda matashi Hamza yay magana da harshen ingilishi haka Yoohan dake binsa da kallo kwarjininsa na sake cika masa ido shima ya mayar masa da murtani cikin harshen nasaran. “Dr Yoohan Goshpower”. Ya faɗa a hankali kamar bayason maganar, sai dai hakan bai hana voice ɗinsa mai amo fita da ƙyau ba. “Ina sake godiya da amsar gayyata ta a karo na biyu Doctor”.
“Karka damu” Yoohan ya faɗa a taƙaice. Hamza Ibrahim da kansa yayma Yoohan jagora har cikin office ɗinsa dake a haɗe masha ALLAH, dan babban kamfanine dake fidda kayan masarufi masu ingaci da lafiya ga jikin al'umma.
Sai da Yoohan ya zauna kafin Hamza Ibrahim ya kawo masa lemo, ya tsiyaya a cup tare da ajiye masa gabansa a kan table ɗin. Godiya Yoohan ɗin ya masa. Hamza Ibrahim ya sake yin murmushi yana gyaɗa kansa tare da yima kansa mazauni shima.
Sun sake gaisawa a karo na biyu. Yoohan ya sake bin ba'asin kiran da ya samu daga garesu. Babu wani ɓoye-ɓoye Hamza Ibrahim yay masa bayani cikin nutsuwarsa, tare da miƙa masa envelope yana faɗin, “Wannan itace takardar da suka aiko da ita a baka, abinda yasa ban badata kai tsaye taje garekaba saboda gudun ha'incin mutane, zata iya yuwu akai takardar amma taƙi isa gareka. Shiyyasa na buƙaci dama nazo ni gareka da kaina na kawo maka. Sai ma kace min zakazo da kanka.
Yoohan daya gama duba takardar ya ɗan ɗago kansa yana kallon Manager, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya haɗiye abinsa a rai yana ƙoƙarin maida takardar cikin envelope ɗin.
Duk da Hamza yayi mamaki da ganin Yoohan ɗin a matsayin wanda yaketa faman hidimtawa bayin ALLAH haka ya haɗiye mamakinsa, dan yayi imani da UBANGIJI na fidda rayayye a cikin matacce, kuma ana samun mutanen kirki a cikin kafiranma, wanda wasu musulman mu sukan gaza gyara zukatansu su zama haka duk da addininmu ya koyar damu komai. cikin hikima irinta masu ilimin addini dana zamani yace, “Yallaɓai ina fatan dai zaka amsa wannan gayyatar? Dan suma mutanene masu karamci da mutunci kamar kai, na tabbata alkairinkane kuma yake sake girmamarsu shiyyasa suka shirya wannan liyafar a gareka domin nuna girmamawarsu a kanka”.
Karan farko a rayuwar Yoohan da kalaman hikima sukai masa daɗi a rai, har yay wani ɗan motsi da laɓɓansa mai kama da murmushi amma ba murmushin bane ba. Idanunsa ya ɗan lumshe na wasu sakanni yana nazari. Ba zuwan bane matsalarsa, ciwonsane damuwarsa. Bayason kowacce kalar hayani, ba kuma ya buƙatar shiga cikin kowanne irin mutane gudun ƙuntatama wani. To amma kuma maganar Manager tai tasiri a ransa harma da tunaninsa.
Buɗe idanunsa yay a hankali ya ɗan gyaɗa kansa, “Babu damuwa zanje ɗin, sai daifa ka shirya ayi tafiyar tare da kai”. “Ni kuma Doctor?”. Manager ya faɗa yana ɗan waro idanu. “Indai kace bazakajeba nima kam zan fasa, dan saboda kaine dama zanje. Banyi musu komai dan su damu da sanina ba, sannan wanna shine karo na farko da aka buƙaci yimin karamcin da bai shafi aiki na ba ko yarena ko addinina ba. Shiyyasa nakeson na halarta ko zai shiga tarihin farko da ƙarshe na rayuwata”.
Manager ya gyaɗa kai a ransa yana faɗin ‘daga ganin wannan a Christians ɗinma inaga ɗan ɗariƙar Catholic ne, ALLAH yasa ina ɗaya daga mutanen da zasu jagoranci duhunsa ya samu haske’ a zahiri kuma sai yay murmushi da faɗin, “Babu damuwa, indai kana buƙatata a tawagar masu rakkiya bazan ƙi ba”.
Hannu Yoohan ya miƙa masa tare da yin godiya, kafin ya miƙe alamar zai wuce dan yasan hankalin families ɗinsa nacan a tashe da rashin ganinsa.
Har mota Manager yay masa rakkiya yana ƙara masa godiya sosai, dan yana cikin mutanen da ayanzu company ɗin ke jin daɗin shigowarsu cikin manyan Customers.
★★★
Lokacin da Yoohan ya iso gidansu ya iske kowa a birkice, dan har papa ya baro church yayo gida. Harma yana shirin kiran police station yay report.
Tun a harabar gidan ya fuskanci akwai abinda ke faruwa a gidan, dan yaga baƙin motoci da yake ƙyautata zaton na Uncles nashi ne. Sannan yanda yaga Guards ɗinsa da sauran securitys ɗin gidan na sauke manya-manyan ajiyar zuciya yasan da walaki. Amma kowa bai tankamawa ba ya nufi ƙaton ƙofar falon nasu na glass da yaja manya kuɗaɗe masu nauyi koda ba'a faɗaba.
Wani ihun farin ciki Miracle ta kurma dan itace ta fara ganinsa, kafin ta kwaso a guje tazo zata ɗane masa jiki. Sai dai yanda ya wani uban tsumewa ya sakata jan birki a gabansa ta kama hannunsa kawai ta ƙanƙame a ƙirjinta. A take sauran yaran gidan da baƙin ƴammata da samari yaran Uncles ɗinsa suma duk suka taso kansa. Basubi takan tsumewar tasaba sukam duk suka rungumesa.
Da ƙyar madam Chioma ta samu suka sakesa, itama ta matsa ta rungume abinta tsam yanda takeso hawaye na gangaro mata akan fuska. Hannunsa yasa ya ɗan buga bayanta kaɗan tare da ɗagota yana mamakin hawayen na miye? Batare da yace komaiba ya ciro handkherchief a aljihunsa ya share mata hawayen.
Ƙarasowar su Papa da Uncles nashi uku yasa madam Chioma matsawa suma duk suka rungumesa, hakama matansu. Shikam dai kansa sake ɗaurewa ya keyi, dan haka ya tambayesu wai ko lafiya?.
Basu bashi amsaba sai da Madam Chioma data kama hannunsa ta kaisa har saman kujera, Victoria ta kawo masa ruwa dan kowa yasan yafi ƙaunarsa sama da kayan zaƙi. Bai musaba ya amsa yasha kusan fin rabi, sannan ya sake binsu da kallo da sake tambayar yaya akayi wai?.
Gebrail ne ya sanar masa da komai. Hakan ya saka Yoohan ɗin dafe kansa dake sara masa kaɗan-kaɗan yana ɗan lumshe idanu. Shi abin nasuma takaici ya bashi sosai. Amma sai baice komaiba. Sanin bazai ceɗinba yasa babu wanda ya damu da jiran sai yace ɗin. Saima ringuɗa da sukai Dining domin yin breakfast ɗin da suka kasa yi tun ɗazun.
Shi dai Yoohan duk a takure yake matuƙa, amma sanin baƙar masifar Uncle Zamani yasa shi haƙura ya zauna akai breakfast ɗin da shi, wanda shi sam ma baici wani abin kirki ba. Bayan sun kammala sukai sama shida sa'anninsa su uku, sai Rich daya dawo daga nemansa. Amma duk masifar da yay masa akan ɗaukar mota ya fita shi kaɗai a wannan halin da yake ciki sai bai kula Richard ɗinba. Shima bayan gama masa masifar sai ya watsar dashi ya biyema su Osen kawai da suka baje a falon Yoohan ɗin suna kwasar dariya da hirarsu ta shaƙiyanci akan ƴammata.
A haka Solomon ya shigo da kwalaben barasar da sukai Order, sai kofuna da ƙanƙara. bayansa cikin ma'aikatan gidanne ɗauke da tray da aka shiryo gasashen naman kaji a cikinsa wanda zasuyi amfani dashi wajan shan barasan.
Sai da suka jera musu komai yanda ya dace kafin su fice su barsu. Miƙewa Yoohan yay zai shige bedroom dan ya rage kayansa. Da sauri Godwin yace, “Mr-x ina zuwa?”. (Dan haka duk abokansa ke kiransa da shi, Rich kawai yafi kiransa da Doctor) Yamutsa fuska Yoohan yay yana hararsa, dan dama abokin bugawarsa ne, kawai dai dan yau baya cikin good mood ne. “Ina zuwa” ya bashi amsa a taƙaice yana shigewa.
“Wai mike damun Boss ɗinka ne?”. Joseph ya faɗa yana kallon Richard. Cikin damuwa Rich yace, “Matsalarsa ce dai ta rashin barci ta motsa, nayi-nayi yasha barasa ko nai masa allura yaƙi”.
Godwin ne yace, “Shegen taurin kan Mr-X ai ba ƙarewa yakeba, ni wlhy sonake wataran na samu wata na biyata tai disvirgin ɗin gayen nan kozai ware yaji daɗin rayuwarsa. Duniya ai sai da jin daɗi, amma shi yabi ya wani ƙanƙame kansa kamar wanda bai wayeba ko ba'a turai yay rayuwa ba. Minene a giya? Dama da shanta kawai nishaɗine, kuma tunda munada aikin yinmu sai fa lokaci- lokaci muke shanta, ba kuma mai cutarwa ba.......”
Katsesa Joseph yayi da faɗin, “Kaga G. Ka barsa, Mr-x tsarinsa kenan shi da ra'ayinsa, koka manta tun muna secondary shi dama komai nasa da ƙa'ida ya keyi. so ni banga abin damuwa da har zaku shiga masa rayuwa da yawaba, kubarsa ya tsara ma kansa yanda yake buƙatar ya rayu Ok?”.
Richard yace, “Hakane Joseph, amma idan ka lura shima fa bawai jin daɗinne baya buƙata ba, kawai shi dai ya ɗauki burin duniyane ya ɗaura akan aikin nan namu, a tunaninsa duk abinda zai sha zai iya shagaltar da shi akan aikinsa, sannan mata ma zasu iya takura masa su hanashi yin rayuwarsa da ƙyau, kunsan mutum namu ɗan hutune, ko mace bata faɗa masa son jiki ba”.
Dariya suka kwashe dashi gaba ɗaya suna mai haɗa kofunan da suka zubama barasa a ciki alamar chssss.
Hakan yayi dai-dai da fitowar Yoohan daga ɗaki, ya canja kayansa zuwa wando da riga duk blue na kamfanin adidas. Duk da hayaniyar tasu bai sonta haka ya zauna a cikinsu dan gaba ɗayansu childhood Friends ɗinsa ne, kuma ƴan uwansa na jini dan duk ƴaƴan ƙannen papa ne, sai Osen ne kawai ɗan aboki shima kuma iyayen nasu sun zama kamar ƴan uwa, sai kuma Richard shi kuma abokinsa. Amma tare sukai secondary school dukansu, hasalima duk ajinsu guda.
Osen ne ya miƙa masa cup duk da yasan ba sha zaiba. Aiko Yoohan ɗin ya yamutse fuska da girgiza masa kai tamkar mai ƙyanƙyamin giyar ma. Dariya suka sanya masa suna zuba masa shaƙiyancin da suka saba, tare da labarin daɗin da ƴammatansu ke jiyar dasu harma da karuwai dan dukansu ji suke da ƴan kuɗaɗe a aljihu. iyayensu kuma sun tara, sanna suma ɗin gwasaken kansune sosai. Shiyyasa suke zuba tsiyarsu a garin Abuja da Lagos kamar babu gobe.
Duk abinda sukeyi saboda Yoohan yaji haushine yay budurwa, dan har maganar ƴammatansa dake bala'in sonsa suke kawowa harda Miracle, tare da koɗa ƙyawunta dama na sauran ƴammatan da Yoohan ɗin shi yake nuna kullum basa gabansa.
Joseph yace, “Mr-x daga yau ka fara taka tsantsan da G-boy, dan ya shirya yanda za'a maka fyaɗe, kaga sai kasan zaman da zakai da shi”.
Mangare ƙeyar Joseph Godwin yayi yana faɗin, “Munafiki, halan giyan ya fara kai maka karo zaka haɗani da shi”. Dariya suka kece da ita duka. Yoohan dake harar Godwin ɗin yace, “Barma wani kare kanka naji sanda kake faɗa ai, an faɗa maka ni irinka ne da baida damuwa saita kwana da mata. Please, try and change your habit kaima”.
Nanma dariya suka sanya, dan sunsan kam G-boy shege ne akan mata, duk yanda zai yaudareki ya biya buƙatarsa ya sani. Rich yace, “Calm dawn my Doctor, duk randa ya aikata maka haka zuwa zakai kawai ka tona masa asiri wajen babien sa, dama gata da shegen kishi kamar taci wuta a cikinta.......”
Osen dake ƙoƙarin yagar nama yace, “Ashe ka ganota, nifa haushi take bala'in bani, amma G-Boy sam baya ganin laifin hakan da take masa, da kayi magana saiya nuna cewar son da take masa ne”.
Ajiyar zuciya Yoohan da warin giyar ya fara hawar masa kai ya saki, ya miƙe a hankali ya ɗauki basket ɗin da aka zubo musu kwalaban giyan ya nufi hanyar fita. Da sauri suka shiga kwala masa kira akan ya kawo musu abinsu, amma baiko juyoba ya fice yama kullesu ta baya ya sauka ƙasa. Canma iske su Papa yay suna ɗora tasu suna hira da dariya harda su Momy suma sha suke. Sosai ransa ya sake sosuwa, sai kace ba yanzu papan ya gama wa'azi a church ba. Tsaki yay ciki-ciki ya wucesu batare da ya tanka musu ba yana ƙwalama Solomon kira.
Da gudu ya shigo kuwa, ya miƙama masa basket ɗin kawai babu bayanin komai ya fice a falon. Garden ya nufa. Sai dai kuma yana shiga ya hango su Miracle a cikin swimming pool suna wanka. Cike da farin ciki duk suka zuba masa idanu, kowacce kwaɗayinta a kansa na fitowa fili saman fuskarta. sai dai kuma tuni ya juya yana jan wani tsakin takaici. Wannan taron yasa sam bayason zama gidan ranar lahadi, yanzu haka zuwa anjima gidan sake cika zaiyi da wasu baƙin kuma. Solomon ya bama key ɗin ƙofar sashensa daya kulle su Rich, yace yaje ya buɗesu, shi kuma ya fice gidan a ƙafa duk da kuwa rana ta fara ɗagawa kuma akwai ɗan zafi............✍
Amin afuwa jiya ciwon kai ya hanani sukuni na kasa typing ɗin🤦🏻.
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
No. 23
................Tun sakkowar Yoohan daga sashensa Momy tai saurin ajiye kofinta na barasa, dan Yoohan ya daɗe da hanata shan giya, kuma ta masa alƙawarin dainawa. Sai dai wani lokacin damuwar da take ciki kansa tasha abinta musamman da daddare idan zata kwanta barci. duk da dama wani mai yawa take sha ba. Binsa tai da wani shegen kallo tamkar idanunta zasu faɗi ƙasa, yayinda fuskarta ma ta nuna shauƙi sosai fiye da yanda suke zaune. Yunƙurawa tai zata tashi amiyarta madam Monecca tai saurin riƙe mata hannu tana girgiza mata kai cikin hikima. Duk da bataso hakanba saita koma ta zauna tana sauke wasu tagwayen ajiyar zuciyar da harsu Papa da fira ya ɗaukema hankali basusan da wucewar Yoohan ɗinba suka juyi suna kallonta.
“Lafiya Darling?” papa ya faɗa cike da kulawa a gareta. Murmushi yaƙe ta masa da cewar “Babu komai, bara naɗan rage kayana dai sun fara min nauyi”. Murmushi yay mata da aika mata kiss daga inda yake. Ta miƙe tana fadin, “Thanks Honey”.
Rakata da idanu yay cike da so da ƙauna harta haye sama sashen bedrooms ɗinsu. Sai da ta wuce da kusan mintina goma kafin Madam Monecca ta miƙe itama tana neman excuse ɗin zuwa toilet. Duk da kowa yasan dama amintarsu tafi zuwa ɗaya da madam Chioma babu wanda yay zargin komai a sauran matan. Sai ma maida hankalinsu ga hirar mazajen su da sukayi kawai.
A bakin gado Madam Monecca ta iske Momy zaune ta dafe kanta. Ta ƙarasa kusa da ita ta zauna, cikin harshen nasara take tambayarta damuwarta?.
Ɗagowa Madam Chioma tai idanunta cike da hawaye tana kallon ƙawarta, tace, “Monecca! Ina cikin damuwa sosai akan Yoohan, gaba ɗaya ya sake canjamin, ɗan kusancin da nake murnar ya ƙara shiga tsakaninmu a yanzu neman hanyar kakkkaɓar da shima ya keyi. Rungumarsa ma yanzu bayason yaga nayi, sai kiga ya kama ɗacin rai. Nifa na gaji da ɓoye-ɓoyen nan, dan gashi Honey harya fara tunanin wai yay masa maganar aure.…..”
“Aure!?” Monecca ta faɗa cikin tashin hankali.
“Ki bari kawai, jiya da yay maganar naji kamar na bindige shegen nan nama huta da wahalansa, Monecca zan fitoma Yoohan a mutum kawai da buƙatata, duk da kuwa nasan shegen taurin kansa”.
Cikin sauri Madam Monecca tace, “Karkiyi haka, dan zaki samu babbar matsala. kidai bari muyi tunani akai. Wai ita Mira bazata koma gidansu ba ne. sai naga kamar itace ke ɗauke masa hankali?”.
Cikin dariyar da Madam Chioma batai niyyar yiba tace, “Miracle fa? An gaya miki kalloma ta ishesa ne a gidan nan. Dama fa Zamani ne keta son ganin Yoohan ɗin ya aureta. kuma ni na gama fahimtar shima akwai tasa manufar akan hakan, shi kuma Yoohan ɗin duk da ƙyan Miracle ɗin bata gabansa shiyyasa nima zamanta a gidan bai taɓa damunaba”.
Ɗan taɓe baki Monecca tayi tana hararar Madam Chioma a kaikaice. a ranta kuwa rayawa take duk rintsi saita bi hanyar mallakar Yoohan ɗin, dan itama wani Masifaffen sonsa take, tana dannewa ne a gaban ƙawar tata kawai. Sun tattauna sosai ta yanda suke ganin ya dace a samu Yoohan ɗin a hannu. Kafin su fito wajen sauran ƴan uwansu a cigaba da hira.
Haka gidan ya cigaba da karɓar baƙi har dare, dan yau ranace ta ziyara a garesu, musamman ma gidan papa daya kasance babban mutum a wajensu.
Yoohan bai dawo gidanba sai yamma lis, ya samu giyar dasu Osen suka sha ta ɗan sakesu, harma sun fito daga sashensa Solomon ya shiga ya gyara. Duk suna harabar gidan zaune dan wasu abokan nasu sun ƙaru saboda jin Yoohan ɗin na gari, shima sai kawai ya zauna a wajensu duk da ba firar yakeba sosai.
______________________________
*_SAUDIA_*
Duk da Adawiya na ƙoƙarin ɓoye halayenta hakan bai hanata sakin layi a wasunl lokutan, dan babu abinda ke sakata takaici da ƙunar zuciya kamar yanda Nu'aymah taƙi nuna damuwarta akan duk abinda take mata. Gaba ɗaya Nu'aymahr ma ta maida hankalinta ga ibada ne kamar yanda ta ɗauro niyya tun daga gida.
Tayi mugun yin watsi da shirmen Adawiyar dan ta gama karantarta tsaf akan lamarin nata, to dama tasan tun suna secondary ma Adawiya tasha haɗata faɗa da ƙawayensu, ta kuma koma ta noƙe ta nuna ba ita tayiba. Amma sai bata taɓa nuna mata ta gane komaiba akan hakan, dan duk sanda taje ta sanarma Umm Adawiya ta mata kaza sai Umm ta lallasheta da nasiha da nuna mata muhimmancin haƙuri da ɗan uwa. Hakanne ke daƙile Nu'aymah daga ramuwa ga Adawiyar gashi har hakan ya zame mata jiki.
A wannan tsukun kuma data fahimci Adawiya ta canja sabon salon halaye sai itama ta canja takunta a kanta tana binta da gashi cikin ruwan sanyi, a ranta tana zargin kenan dama Adawiya na son Yah Ab komi?. A duk sanda tai wannan tunanin takanyi ƙoƙarin ganin ta ƙaryata zuciyarta, dan bata taɓa ganin alamar hakan ba ga Adawiya a dacan baya. A ganinta yanzu dai daɗin aurene yasa take ganin tafita kusanci da Abdallahn shiyyasa take shirya yaƙarta a kansa.
Yau ma kamar kullum Nu'aymah na ɗan yin barcin rana a falo, dan da daddare tafi maida hankalinta ga ibada ne, Abdallah ya shigo gidan. Adawiya ta wuce makaranta. daga hajjo sai Nu'aymah. Da tare suke da Hajjon a falo zaune suna ɗan hira sai barci ya kwasheta, itama hajjon saita nufi ɗaki ta kwanta danta huta.
Kafe Nu'aymah da idanu Abdallah yayi ko ƙyaftawa ba yayi, ya ƙaraso inda take yay tsaye kanta yana cigaba da kallonta tamkar mai nazarin wani abu. Cikin barci Nu'aymah taji alamar tsayuwar mutum a kanta. A ɗan firgice ta buɗe idanu saboda barcin nata baiyi nisaba sosai. Ganin Yah Ab tsaye a kanta ya sakata sake zabura tana binsa da kallon tuhuma itama. Sai kuma ta kumbura baki tana ɗauke kanta cike da takaicinsa.
Fuskarsa a haɗe ya zauna a kujerar da take kwance, hakan ya saka Nu'aymah saurin miƙewa sosai tana faɗin, “Yah Ab minene haka wai?”.
“K kika cancanci wannan tambayar ai?”. Ya faɗa shima yana miƙewa yasha gabanta fuskarsa a haɗe, ya cigaba da faɗin, “K harkin isa ki dinga wulaƙantani akan wani banza can Nu'aymah? Kinzo inda nake amma sai wani basar dani kikeyi”.
Cikin rashin fahimta take kallonsa, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta raɓashi zata wuce. Sake shan gabanta yayi yana mazurai, “Nabaki izinin tafiya ne?”.
Idanunta cike da ƙwalla tace, “To idan na zauna mizan maka? Kodan kaga nazo na zauna a gidanka kakeson ƙuntata rayuwata?”. Hannu ya ɗaga tamkar zai ƙwaɗa mata mari sai kuma ya fasa ya dunƙulesa yana taune lip ɗinsa jikinsa na tsuma. Yace, “Uban wanene Ameer?”.
Cike da takaici Nu'aymah ta kallesa ta watsar, kamar karta bashi amsa sai kuma mamakin abin nasa yasa ta kallesa da ƙyau. “Ban gane mikake faɗa ba Yah Ab?”. A hasale yace tayaya zaki gane mara mutunci. Nu'aymah wai harni zaki iya gudammawa a daren aurenmu saboda wani jaki? Kinsan baƙya sona miyyasa kika yarda aka saka mana ranar aure?”.
Sallamar Adawiya da batai zato ko tsammanin Abdallah zai dawo gidan a wannan lokacinba ya hana Nu'aymah da mamaki ya kume bashi amsa. Turus Adawiyan tayi tana kallonsu, dan wanda bai saniba zai ɗauka ne wata maganar arziƙi sukeyi da juna.
Binsu take da kallo tamkar idanunta zasu zubo ƙasa, Abdallah yay ƙaramin tsaki yana barin wajen ya nufi ɗakinsa. Har Nu'aymah ta cira ƙafa itama zata bar wajen Adawiya ta dakatar da ita ta hanyar riƙo mata hannu. Juyawa tai tana kallonta fuska a haɗe sosai, “Malama sakeni”. Nu'aymah ta faɗa a hasale.
“Anƙi a sakekin, idan kin isa kiyi duk abinda zakiyi. miya haɗaki da mijina?”. Kallon tsantsar mamaki Nu'aymah kema Adawiya, sai dai kuma a fili saita saki lallausan murmushi da har ya bayyana haƙoranta. Tace, “Tunda kinsan mijinkine mizai hana shi kije ki tambayesa miya haɗashi dani? Inaga kamar hakan zaifi birgewa a gareki shashasha kawai”. Ta ƙare maganar da fisge hannunta tai gaba tabar Adawiya da huci.
Hajjo data hango tahowar Nu'aymah saita saki labulen cikin ɗakin ta zauna a bakin gado. A haka Nu'aymah ta shigo ta sameta. “Hajjaju kin tashi ashe?”. Nu'aymah ta faɗa tamkar babu wani abu daya faru. Murmushi Hajjo tayi tana kallonta, “Ba dole na tashiba tunda kin gaza zuwa ki tadani mu wuce massallaci”.
Kusa da ita ta zauna tana dariya, “Ho hajjonmu, yanzu kuma dana tadakin cazaki ban barki kin rintsa ba, gara mu maidake da ƙwarinki karsu Abba suga kin sake rugurgujewa”.
Duka Hajjo ta kaima Nu'aymah da filo. Hakanne ya sakata tashi ta shige bayi da gudu tana dariya. Cike da tausayinta Hajjo ta sauke ajiyar zuciya, a ranta kuma tana ƙulla abubuwa da dama game da rayuwar Nu'aymahr
A falo kam Nu'aymah na shigewa Adawiya ta nufi ɗakin Abdallah a fusace, babu ko sallama ta tura ƙofar ta shiga. Sai dai ganinta yay kawai a kansa kamar an jehota. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa. Hakan ne ya sake hasala mata zuciya, sai ta fashe masa da kuka. “Yanzu Yah Ab abinda kakemin kana ganin adalcine? Ni dake matarka baka da lokacina amma kanada lokacin dawowa gida da wuri dan ka kasance da Aymah? Badan ALLAH yasa yau na shigo gidan da wuri ba bama zansan hakan na faruwaba tsakaninku. Shin wai da mi Nu'aymah ta fini ne? Wlhy sai ALLAH ya sakamin duk cin amanata da akeyi, kuma ni na gaji zan kira baba malam na faɗa masa komai tunda naga ita hajjo goyon baya take baku ma, ƙilama wataran a gabanta zaku shiga ɗaki ku rufo bazata tankaba saboda tana tsoronku......”
Wani wawan mari ya sauke mata a fuska da saida taga stars na mata kaikawo, balle dama ga azumi. A take ta zube ƙasa da sakin wata ƙarar kuka data kai har kunnen Hajjo.
“Kai Abdillahi lafiya kuwa? Mike faruwa hakane nakejin kukan Adawiya?”. Ta ƙare maganar tata dai-dai lokacin da take ƙarasowa cikin ɗakin. Ganin Adawiya kwance ƙasa dafe da kunatu ya saka hajjo zaro idanu, “Mikai mata Abdullahi?”.
Cikin ɓacin rai yace, “Hajjo barni da ƴar iskar nan kawai, wlhy tai wasa wataran saina karya ƙasusuwanta a gidan nan tunda ita kamar dabba take”.
“Ya isa haka”. Hajjo ta faɗa tana ɗago Adawiya dake ƙasa tana cigaba da sakin gunjin kuka. Saida ta zaunar da ita saman kujera sannan ta sake tambayar Abdallah miya faru?. Faɗa mata komai yayi amma banda tsayuwarsu da Nu'aymah, baisanma ita taji komaiba.
Cikin ɓacin rai Hajjo tace, “Adawiya dama baki da wayo haka? Ita ƴar uwar takice kuma tazama abar kishi a gareki? Har kike jifansu da wannan mummunan lafazin ita da mijinki? Adawiya yaushe kika bari ƙawayen banza suka canja miki tarbiyya ne? Har haka. To wlhy ki shiga hankalinki, idan kuma ba hakaba ni bazan ɗauki wannan banzan halayen a cikin zuri'ata ba, saina ɓatama kowa rai a cikinku har iyayen naku ni babu ruwana. Bandama iya shege kowa na fama da ibadar ALLAH a baki ke kina biyema sheɗan yana ɗoraki akan dokin zuciya. To idan na sakejin makamancin wannan zancen lallai sai kinyi nadama shashasha kawai. Banda ƙaddara da yanzu ita wadda kike cin zarafin ba itace matsayin matar tasa ba”.
Haka Hajjo taima Adawiya tas sannan ta fito ta barsu. Duk abinda akeyi Nu'aymah najinsu, sai dai ko tari bataiba balle a fahimci ta sani ɗin. Daga ƙarshema sukai shiri suka wuce massallaci, suda gidan kuwa sai anyi sallar asuba kuma.
Tun daga wanan ranar Adawiya ta shiga fishi da kowa a gidan. Daga gaisuwa bata sake tankama wani. Ahmad yamata nasiha harya gaji ya watsar da ita shima. Bayan kwana biyu da yay dai-dai da cikarsu kwanaki biyar da zuwa, ashirin kuma ga watan azumi Nu'aymah ta tattara inata-inata ta koma massallaci zaman ittiqafin.
Abdallah yaso hanata, sai dai Hajjo tace ya barta tai ibadarta yamafi zaman nata a gidan aita fitina. Badan yasoba ya haƙura, dan yaso a wannan zaman suyi magana ta fahimta da Nu'aymahr ya samu ya lallaɓa hajjo dasun koma a ɗaura musu aure.
Bayan barin Nu'aymah gidan sai ga Adawiya ta saki jikinta, ashe dama Nu'aymahr ce natsalar rayuwarta. Babu wanda yace mata komai. Saima hajjo ce taima Abdallah magana akan su shirya shi da Adawiyan dan tare zasu wuce Najeriya ayi bikin salla. Kai tsaye Abdallah ya nuna cewar bazaije ba, sai dai Adawiya, dan shi bai manta ALLAH ya isan da mahaifiyarsa tai masa akan zuwan nasaba.
Balbalesa da masifa sosai hajjo tai dan ita batasan dalilinsa na bijirewarba. da taga dai ya tirje ɗin saita kira baba malam ta faɗa masa komai. Shine ya kira Abdallahn cikin bada umarni ya sanar masa ya shirya suzo salla gida tunda suna samun hutu a wannan lokacin.
Abdallah ya shiga tsaka mai wuya sosai akan hakan, dan yasan dai umarnin mahaifiyarsa dana baba malam babu wanda yake da damar tsallakewa a ciki, dan duk sunada daraja da kima a idanunsa da rayuwarsa.
_________________________
*_NIGERIA_*
A kwanaki biyun nan abubuwa sun sake tsamari akan Yoohan, gaba ɗaya neman birkicewa yake saboda rashin samun barci, tun daga jiya zuwa yau yaƙi magana da kowa a gidan, yama kulle kansa a ɗaki ya hanama kowa ganinsa. Momy tayi kukan tayi roƙon amma yaƙi buɗewa. Hakama su Gebrail sunyi nasu ƙoƙarin ya sharesu.
Amma saboda ƙarfin hali da burinsa nason cika alƙawari sai gashi a safiyar yau talata yayi shirin tafiya kano. Tunda safe ya bama Solomon umarnin faɗama guards ɗinsa su tafi kano. Su kuma ya nema musu ticket guda uku. Solomon nason tambaya akan hakan yanajin tsoro, dan haka yaja bakinsa yay shiru yaje dai ya cika umarninsa
Kusan ƙarfe huɗu na yamma sai gashi ya sauka ƙasa cikin shigarsa ta suit blue mai haske. sun masa bala'in ƙyau duk da yana a yanayin da a kallo ɗaya zaka fahimci akwai damuwa tattare da shi.
Momy ce kawai zaune a falon sai Victoria da Abraham. Cikin girmamawa a garesa yaran suka shiga gaishesa. Hannu ya ɗaga musu kawai tare da ƙarasowa inda suke duk ya shafa kansu batare da yayi magana ba..
Ya maida dubansa ga Momy da idanunta suka kumbura saboda kuka, ɗauke kanta tayi ita a dole fushi take da shi. Baice komaiba ya ƙaraso inda take ya tsaya a gabanta tare da riƙe kunnuwansa da hannayensa alamar ban haƙuri.
Bata iya dogon fushi da Yoohan ɗinta. Dan haka tai murmushi tare da miƙewa ta rungumesa. Yau dai ya daure bai tureta ba, sai da ta gaji dan kanta ta sakesa sannan, ta amshi tie ɗin hannunsa ta ɗaura masa tana faɗin, “My Boy nikam yaushe zaka fara saka necktie da kanka?”.
Bai bata amsaba, sai dai ya sake ɓata fuska alamar shagwaɓa. Da ƴar dariyarta ta shafa masa kwantaccen sajensa da yasha gyara yau, ya kama hannun nata ya sumbata kaɗan.
“Ina zakaje ma wai?”. Ta tambaya tana tsatstsaresa da idanunta manya. Da ƙyar ya buɗe baki wajen bata amsa da “Kano”. “Kano!! kuma Yoohan? Mizakayo a kano kaida kake cikin wannan halin? Badai aiki ba?”. Kansa ya girgiza mata, batare daya bata wani ƙarin bayani ba yace mata, “Bye” yana nufar ƙofa.
Saurin binsa tai tana kira, amma sai yaƙi tsayawa, saida ta haɗa daɗan gudu ta cimmasa, duk da kuwa tafiyarma ba wani sauri yakeba saboda rashin ƙwarin jikinsa. Yanda ta riƙosanne ya sakashi waigawa ya kalleta. Tace, “Ina tambayarka mizakayo acan amma ka taho baka kulaniba Yoohan”.
Kansa dake faman masa ciwo ya dafe kaɗan, kafin cike da ƙosawa yace, “An gayyaceni ne” danshi baison yin ƙarya a rayuwarsa, kamar yanda ya tsani kuma saɓa alƙawari. Yana gama faɗa ya zare hannunsa zai juya ta kuma riƙewa. Yanzunkam bai juyoba sai da yaja wasu sakanni. Muryarta da damuwa ta zagayo gabansa tana magana. Amma maimakon ya bata amsa sai ya saka yatsansa akan baki yace “Shiii!!!”.
Shirun kuwa tayi tana kallonsa, ya ɗaura yatsunsa saman baki yay mata alamar *_Smile_* kamar yanda ya saba mata aduk sanda ya ganta a damuwa tun yana yaro. Duk da batason yin hakan saita murmusa. Yay mata jinjina yana ɗan lumshe idanunsa dake a kumbure sosai.
Tanaji tana gani ya shiga mota driver ya jasu shi da Solomon suka bar gidan, gashi Papa bayama ƙasar jiya sukai tafiya shi da Uncle Zamani.
★★★★★
Airport driver ya kaisu. inda acan suka haɗu da Manager Hamza Ibrahim yana jiransu. Sun gaisa cikin mutunta juna Hamza na mamakin ganin Yoohan ɗin a ƙunci fiye da waccan ranar. Ga idanunsa da fatarsu tai jajur hakama farar fuskarsa. Haka kawai yaji a ransa akwai abinda ke damun Yoohan ɗin. amma sai baiyi magana ba suka nufi ciki.
Ƙarfe biyar da rabi jirginsu yabar Abuja zuwa birnin dabo kodami kazo mun fika🤗😜.
Kamar yanda Yoohan ya iske Guards ɗinsa na jiransa haka suka iske motoci biyu na tarbarsu kuma. Hakan ya sai ya sake birge Yoohan matuƙa, dan haka bai shiga tasa motarba ya shiga wadda aka aiko musu, Guards ɗinsa kuma suka bisu a baya.............✍
No. 24
...............Baba malam daketa kaikawo na ƙoƙarin ganin komai ya kammala yanda yake buƙata ya nufi sashen nasa a karo na babu adadi. Yanda ya hana kansa sakat akan tarbar baƙonsa haka ya hana Umm sakat itama, dan baiwar ALLAH nan tun ƙarfe biyun ran take a kan ƙafafunta tana hidima. Sauƙinta ma Addah ta shigo tana taimaka mata, ga kuma mai aikinta.
Omar ne biye da shi, dama yafi shaƙuwa da shi a samarin yaran gidan fiye da kowa, duk da dai ada kam sunfi shaƙuwa da Abdallah, amma daga baya da Omar ɗin yafi Abdallah zaman kano sai shaƙuwarsu ta zarce ta tsakaninsa da Abdallah ma. Dan shi Omar yarone mai tsananin ƙwazo da biyya ga iyayen nasa, sannan baba malam shine babban malaminsa na addini fiye da kowa, shiyyasa koda yaushe yana kano bai cika son zaman Abuja ba shi.
Kai tsaye kitchen suka nufa, inda suka iske Umm da Addah suma dai kamar su tsinke nasu ran, dan tare suke aikin daya rage ɗin. Bayan Baba malam yay sallama baima bari an amsa masaba yace, “Umm Muhammad yaya kun kammala?”.
Ɗagowa Umm tai taɗan kalli mijin nata, sai kuma ta maida akan aikin gabanta tana cewa, “Abban Nu'aymah wlhy nikam dai zakama sake rikitamu gaba ɗaya, insha ALLAH muna gab da kammalawar, dama zuwa kai kayi wanka dan magrib ta gabato”.
Murmushi shimfiɗe a fuskarsa ya ƙaraso yana amsar abinda take tace lemon mangwaron daya rage su haɗa. “Ke dai kawo na taimaka miki ki kammala kawai, dan yanzu haka an wuce ɗakkosu fa”.
Dariya Umm da Addah da Omar sukai, ya ƙaraso wajen baba malam ɗin yana faɗin, “Abba kawo ni nayi basai kayi da kanka ba. Dan nikam yau namafi kowa zumiɗin son ganin wannan baƙo mai daraja a wajenku Abba, dan naga gaba ɗaya hankalinku na kan son ganin an ƙyautata masa, yau kota abincin buɗa bakinmu bakwayi sai na baƙo”.
“Kace ido ka saka mana? Hakama malam ƙarami (baban yaron Addah) sai da ya gama ƙorafi kafin ya wuce airport ɗakkosu”. Ita dai Umm da Addah dariya sukayi musu kawai, ta matso suka ƙarasa haɗa komai ita da baba malam ɗin. yayinda Omar da Addah kuma suke ɗorawa tray. Omar ne ya ƙarasa kwashewa ya kai komai can sashen kakansu inda za'a sauke baƙon. Hakan kawai ya isa kasan an daratta baƙon sosai, dan duk baƙon da su Baba malam zasu kai da shigo dashi cikin gidansu to lallai ya isa kuwa.
Sai da yaga an fita da komai sannan ya sauke ajiyar zuciya, tare da ficewa domin aiki da shawarar Umm ta farko. Cike da gulma irin ta aminai Umm da Addah suka kalli juna, sai sukai murmushi kawai dan Baba malam ɗinne ya basu dariya.
Ficewa sukai a tare suma zuwa sashen da aka shirya abincin, suka ƙara gyara komai tare da saka turaren wuta da kuma Air Fresheners masu ƙamshi. Kamar Umm ta sani har zasu fito saita yanke shawarar fita da kaskon turaren, acewarta kar ko a baƙin asamu mai Asthma ya cutu. Ta ɗan ɗaga labulen Windows ɗin kaɗan hayaƙin turaren ya ragu sosai. Cikin sa'a ma sai gashi Omar yaje ya tada Genretor. Ac suka kunna tare da sake duba komai suka tabbatar yayi dai-dai sannan kowa ya nufi part ɗinsa Umm nama Addah godiya.
Dan tasan badan itaba da aikin baiyi sauriba sam. Mama amaryar Abba Musbahu kuwa dama ita sai a hankali ce, San jikinta bai bari tama kula da sashenta ba balle taimakon wani kuma, komai ƴan aikine keyi, kodan taga mijin ba mazauni bane oho.
Motocin na shigowa anguwar ana fara kiraye-kirayen sallar magriba. Yoohan na kwance shiru a jikin kujera idanunsa a lumshe. Baisan inda ake shiga da fita ba har saida motocin suka tsaya a ƙofar katafaren gate ɗin. Hakan sai yayi dai-dai da fitowar baba malam da Abban su Adawiya, sai Malam ƙarami da Omar da sauran samarin gidan da yara amma iya mazan kawai.
Duk da yanda guards ɗin Yoohan suka firfito suka zagaye motar da yake a ciki hakan bai saka fuskokin su baba malam sauyawa daga fara'ar dake tattare da suba. Akan idonsu Hamza Ibrahim ya fita. Kafin Yoohan da Solomon ya buɗemawa shima.
Shima a gaban idanun nasu ya fito, bayan ƙafarsa kuma da sarƙar Cross ɗinsa suka fara cin karo kafin cinkusashshiyar fuskarsa. Abinda zai baka mamaki a tare su baba malam sukayo caa a kansu. Cikin ƙyaƙyƙyawan tsari na masu ilimi da baiwar hikima suka tarbesu. Wani iri Yoohan yaji a ransa shima duk da kuwa dama ya fahimci masu gayyatar tasa musulmai ne, amma sai ya dake ya basar.
Duk yanda yaketa faman musu shan ƙamshi da cika da batsewa babu wanda ya canja yanayin nasa, saima sannu da zuwa da suka shiga jera musu tare da basu hannaye suna musabaha har guards ɗin. Kafin baba malam ya bama Malam ƙarami da Omar damar shiga da Yoohan ɗin ciki. Danshi Hamza Ibrahim ya buƙaci a inda zaiyi alwalane kai tsaye.
Yoohan dai baiyi musu ba yabi bayan su Omar, sai dai idonsa da zuciyarsa nakan hasaso masa a inda ya taɓa sanin fuskar baba malam a rayuwarsa. Guards ɗinma bin bayansu sukai. Omar zaiyi magana baba malam ya girgiza masa kai alamar ya barsu.
Tun a farkon shigowa gidan Yoohan yasan masu gidan sun wuce raini, dan babu abinda nasu gidan zai nuna masa sai dai kayan ƙawa da ƙyale-ƙyale, nasu baba malam ma yafi nadu girma sosai. A haka su Omar suka kaisa har falon, guards ɗinsa biye da dasu kamar wasu jela ko suna ganin za'a cutama Yoohan ɗinne oho musu. Sai da sukaga ya zauna suka ajiye masa ruwa da lemo kozai buƙata sannan sukai masa sallama suka fito, duk da basuji ya amsa musu da ƙyau ba. Dan Solomon ma tunda ya fahimci inda suka kawo kansu sai takaicin ogan nasa da buɗaɗɗen ra'ayinsa ya shiga masa zafi a rai. Dolene yay saurin sanarma Madam Chioma kafin a bama Boss ɗin nasu wani abin yaci a tsafesa.
Yana cikin shawara da zuciyarsa ta yanda zai silalo daga cikin falon ya kira madam ɗinsu sai ga sallamar su Baba malam, da alama ana idar da sallar magrib basu zaunaba suka shigo gidan. Aiko takaici kamar ya kar Solomon, amma duk da haka saida yayi dabarar turama Momy text message ko za'a dace wayar na a hannunta ta gani.
Koda suka shigo Yoohan na'a zaune yanda yake baiko motsaba, sai dai yana binsu da kallo ne ta ƙasa ido. Abban Adawiya da suka taɓa haɗuwa a orphanage ranar da suka buge yaron nan sai ganin Yoohan ɗin ya sakashi matuƙar jin mamaki. Duk da ya jima a ransa yana zargi da hasashen kodai shine mai musu wannan ɗawainiyar. Rashin tabbas ɗin hasashen nasa yasa bai taɓa yin magana ba sai yanzu ya ɗan gwargwaɗa ma baba malam cikin harshen larabci.
Murmushi kawai baba malam ɗin yayi, cike da kulawa ya maida hankalinsa akan Yoohan da suka fahimci a takure yake da kasancewarsa a wajen. Basu damuba, dan sunyi gamo da waɗandama suka fisa taurin kai da aƙida amma cikin amincin UBANGIJI sun sami nasarar canjasu. To balle shi kuma dama suka fahimci zuciyarsa nada rangwame tunda har ya iya kasancewa maison ƙyautatawa marayu.
Duk da baba malam yaga saɓanin abinda yay tammani daga Yoohan hakan baisa ya canja komaiba daga ɗokantuwa da mutunta baƙon nasu. Hakam ɗan uwansa da ƴaƴansu basu nuna wani mamakinsu a fili ba ko ƙyanƙyamin su Yoohan ɗin, kowa ya shanye a ransa. Ba Yoohan kawai ba, dai-dai da guards ɗinsa an mutuntasu fiye da zatonsu, dan suma ca akai su zauna ayi buɗa bakin dasu. Duk da suna noƙewa saboda boss ɗinsu haka baba malam ya matsanta musu. Ganin Yoohan kuma bai tanka musu ba, yamayi kamar baisan mi akeyiba sai suka saki jiki aka kwashi gara da su, a ransu kuma suka koma zuba santi dajin kimar mutanen musamman yanda aka nuna musu suma mutanene masu daraja ba bautace kawai aikinsu ba.
Yoohan kansa da keta noƙewa da farko tuni baba malam ɗin ya tsaresa sai yaci, harda nuna masa idanfa baici da hannunsaba shi zai basa da kansa to, kuma ɗura zai masa. Karan farko a rayuwata da ni kaina mai ɗakko muku rahoto naga murmushi a fuskar Yoohan yau. Dan shi kansa a bazata ya saki lallausan murmushin ga baba malam ɗin.
Baba malam yace, ‘Masha ALLAH’ a ransa, duk da yau ya fara ganin Yoohan sai yaga murmushin yay bala'in masa ƙyau. Haka dai suka gudanar da buɗa baki cikin nishaɗi da farin ciki. Guards ɗin Yoohan dake ɗar-ɗar harda Solomon mai hasashen banza sai gasu sun kwashi gara suna washe baki dajin farin ciki a ransu.
Kiran sallar isha'i ya saka su baba malam ficewa massalaci akabar Yoohan da tawagarsa. Sai dai kuma bayan fitarsu babu jimawa shima sai ya miƙe da nufin ɗan yin tattaki ko cikinsa zai sauka. Shi kansa yasan ya jima a rayuwarsa baiyi irin wannan cin abincinba, ballema a ɗan tsakanin nan da yake cikin halin ha ula'i. Ta ƙaramar ƙofar da yaga su baba malam ɗin sunbi shima ya bi, kai tsaye ta kaisa ƙatuwar harabar massalacin kuwa.
Ko'ina ƙwanyar yake da haske tamkar rana. Ga mutane maza da mata harma da yara cike da massalacin harda mata. Yoohan yay tsaye jikin katanga yana kallonsu cike da nazari har aka tada salla. Ba massallacin kawai ba hatta anguwar kanta sai yaji ta ɗauki shiru gaba ɗaya, babu abinda kakeji sai sautin karatun salla da baba malam keyi. Lokacin da ya kammala karanta fatiha mamu suka amsa da “Amin!!!!” sai gaba ɗaya tsigar jikin Yoohan ta tashi, zuciyarsa tai wani bala'in tsargawa har saida ya rumtse idanunsa.
Baisan dalilin daya hanashi komawa ciki ba, haka ya cigaba da tsaiwa har sukai ruku'u. suka sake ɗagowa sukai sujida. Tsigar jikinsa sake tashi tayi a karo na biyu, dan yanda sukai sujidan gasu a sahu nagartacce dolene ko musulmin ya gani yaji ƙarin imani a ransa balle wanda bai taɓama yin sujudar ga UBANGIJI ba.
A hankali Yoohan ya ɗaga ƙafafunsa ya fara ja baya da ƙyar harya fice a harabar massalacin ya koma cikin gidan. Haka ya cigaba dajan jiki harya isa falon da aka saukesu da ƙyar. Tsitt guards ɗinsa daketa faman surutun santin abincin da sukaci sukayi ganin ya shigo kamar a birkice. Da sauri duk suka miƙe tsaye domin girmamawa. Solomon ya taimaka masa ya zauna.
Sai kuma duk hankalinsu ya tashi, amma yanda baiyi maganaba suma sai basuyiba sukai dai masa tsaye cike da tsoron kodai an cutar dasu ɗinne kamar yanda sukai hasashe tun farko?.
Har aka idar da sallar asham Yoohan bai dawo hankalinsa ba. Baba malam da ayau baije tafsir ba dama ya ɗauki alfarma suka sake shigowa. A yanda yaga Yoohan ɗinne ya saka hankalinsa tashi. Tambayar guards ɗin ya shigayi a ruɗe. Nan sukai masa bayanin abinda suka sani kawai. na cewar Yoohan ya fitane shan iska sai ya dawo musu a haka, dama kuma bashi da isashen lafiya, bama suyi zaton zai iya zuwa nan lafiya lau hakaba.
Ɗan shiru Baba malam yayi cike da nazarin bayanin da Solomon yay masu na rashin yin barcin Yoohan, kafin ya zauna kusa da Yoohan ya janye hannunsa daya dafe kansa da shi ya maye gurbinsa da nasa, addu'oi ya fara masa yana tofawa, ya kuma saka Abban Adawiya yin wasu addu'oin a ruwa ya miƙo masa. Kamar Solomon zaiyi maganar karsu bashi sai dai ya kasa saboda nauyin da bakinsa yay masa da kuma kwarjinin mutanen.
A gabansu akaba Yoohan ruwan addu'ar yasha. baba malan ya zuba a hannunsa kaɗan ya kuma shafa masa a fuska. A take ya fara sakin tagwayen ajiyar zuciya a jajjere. Ya buɗe baki da ƙyar yace, “Thanks”. Murmushi baba malam yayi kawai, kafin yace, “inaga ya kamata a kaiku masauki ka huta, dan da alama idanun nan naka barci sukeji”. Cike da mamaki Yoohan ke kallon baba malam, duk da dai ya kasa yarda su haɗa idanu da ƙyau dan bala'in kwarjini baba malam ɗin ke masa shikam. Sake murmusawa baba malam ɗin yayi. Ya ɗauke kansa ya maida gasu Omar.
“Farukh a kaisu masauki ko”. Da sauri Omar yace, “To Abba”..
Da gaske Yoohan barci yakeji fiye da zatonsa, dan haka ya kasa musama baba malam duk da kuwa shi a yau yaso su juya zuwa Abuja shi da Solomon da Manager, guards ɗinsa kawai yay shirin bari su kwana a kanon da safe suma su wuce. Amma sai yaji babu abinda yafi buƙata kamar kwanciya a yanzun.
Su Malam ƙarami sun kaisu gida mai ƙyau matsakaici dake gaba da gidansu kaɗan, inda nanne masaukin da su baba malam ɗin kan sauke baƙi daman. Tsaf yake gidan, saima uban ƙamshi mai saka kwanciyar hankali da ya keyi. Duk da babu wutar nefa nanma an tada gen.....
Abin mamaki sai ga Yoohan kamar bugagge, suna shiga wajen kwanciya ya buƙata. Yana ganin gado kuwa ya zube akai yana sauke ajiyar zuciya abin tausayi.
Takalma da necktie ma sai Solomon da Manager ne sukai
dabarar zare masa. Hakama jacket ɗin suit ɗinsa. Sai suka barsa da shirt ɗin da dogon wando kawai.
Manager ne ya kwana tare da Yoohan duk da shi Solomon baiso hakaba. Bawan ALLAH nan yanda ya kwana bautar UBANGIJI haka ya ja doguwar addu'ar samun haske daga Yoohan ɗin. Hakama su baba malam, ranar mafi yawan addu'oinsu akan Yoohan suka yisu da ga su har iyalansu. Da asuba aka kawoma Hamza abin buɗa baki, daga Yoohan har guards ɗinsa barci suke kwasa masu a lokacin.
★★★WASHE GARI★★★
Washe gari sai ga kowa ya tashi banda Yoohan, barci yake cike da kwanciyar hankali, dan haka baba malam daya zagayosu har sau kusan uku ya hana a tadashi.
An kawo musu lafiyayyen breakfast sukaci suka ƙoshi, wajen sha biyu ma aka sake kawo musu abinci nanma. Ganin har ɗaya saura bai tashiba Solomon ya bama sauran ƴan uwansa shawara akan su tafi, shima zaije ya sayoma Yoohan kaya ya kuma nema musu ticket. .
Basu musama wannan shawara ba, suka shirya suka tafi harda Solomon ɗin, dan sai da suka kaisa ya kammala uzirinsa kafin su sake maidosa gida, sukaje sukai sallana da baba malam da yake a lokacin sun samesa tsaye a ƙofar gidansa ya dawo daga orphanage ne..
Baiso tafiyar tasuba, amma sai bai hanasuba tunda ƙila sunada uziri. Ya musu godiya sosai tare da basu tsaraban da aka shiryama Yoohan ɗin dan suyi gaba da ita, suma kuma aka basu tasu. Yanda su baba malam ke musu godiyar sai duk abin ya ɗaure musu kai da saka jikinsu yin sanyi akan a ƙidarsu. Har suna hasashe a ransu dama haka musulmai keda kirki da karamci amma ake aibantasu da nuna musu suba mutanen kirki bane? To su dai gashi jiyane karon farko da sukai mu'amula da musulmai hausawa mai tsaho amma sai basuga hali mara ƙyau ɗin da ake faɗar suna da shiba saima alkairi da ƙyawawan halayya abin koyi.
Sun tafi da wannan alkairai da akai musu cikin rai sosai.
Bayan wucewarsu baifi da mintuna talatinba Yoohan ya farka. Yayi matuƙar mamakin ganin inda ya kwana, manager ya taimaka masa da ruwan wanka, Solomon zai shiga gabatarma Yoohan ɗin da kayan daya siyo masa sai ga malam ƙarami da kaya sabbi fill ya kawo. Sai kuma abinci da aka shiryoma Yoohan ɗin tunda sunsan bai karyaba shi.
Haɗa kayan Solomon yay gaba ɗaya ya kai ɗakin ya ajiye. Ya juya zai fita Yoohan ya fito. Dakatawa yay ya gaidashi cike da girmamawa. Yoohan da kejin kansa sakayau kamar ba shiba ya amsa masa idanunsa nakan kayan da Solomon ɗin ya ajiye masa. sai dai baiyi maganaba sai shi Solomon ɗinne yay masa bayani.
Zama yay ya gyara jikinsa tsaf, ya buɗe kayan duka, na Solomon ƙananun kayane, nasu baba malam kuma shaddace ruwan zuma da akaima ɗinki mai ƙyau kuma dai-dai shi kamar an gwada. Tunda yake a rayuwarsa bai taɓa saka kaya makamanta hakaba. Duk da kuwa suma a nasu yare suna ɗinka shigensu amma shi bai taɓa sha'awar yin hakanba. A yau kam sai yaji sun birgesa har yay sha'awar sakawa. Haka ya warwaresu ya saka.
Baisan lokacin daya furta kalmar ‘Woow!’ ba a fili yana sake kallon kansa a mirrorn ɗakin. A haka manager da shima yay shiri tsaf a kayan da aka kawo masan ya shigo ya samesa. Sosai yake yaba ƙyawun da Yoohan yayi a kayan shima, sai ko Yoohan ɗin ke sanar masa shi bai taɓa sakawa ba sai yau. Hamza yayi mamaki sosai, duk da daga jiya zuwa yau ya fahimci su Yoohan sunada tsauri ko a cikin Christians ɗin ma, dan ya karanci yanda guards ɗinsa suka ringa gudanar da al'amiransu.
Sun fito falo Yoohan yaci abinci, bayan ya kammala babu jimawa sai ga Abba da Baba malam sun shigo. Su kansu bakinsu bai iyayin shiru ba sai da suka yaba ƙyawun da Yoohan yayi a kayan. Ya duƙar da kansa ƙasa saboda kwarjinin da suke masa yana godiya a garesu, musamman yanda suka sakashi yay barci jiya bayan kwanaki tara daya kwashe baiyi ba.
Cikin hikima ta masu ilimi baba malam ya nuna masa basune ba, UBANGIJI ne yay ikonsa, su nasu kawai roƙone cike da yaƙinin samu. Duk da Yoohan bawai ya fahimci maganar tasu bane sosai saiya gyaɗa kansa kawai. Sun ɗanyi hira kaɗan, duk da Yoohan dai bai saki jikiba sosai. Hamza ne ke biyema su baba malam ɗin, Solomon ma baya saka baki. Wannna ɗan zaman nasu ya saka Yoohan ɗin sake jinjina mutuncin mutanen da sanin darajar ɗan adam ɗinsu. Sai da su baba malam sukayi sallar la'asar sannan sukai musu rakkiya har airportda kansu suna sake roƙon Yoohan ɗin yazo musu bikin salla harma da Manager.
Yako amsa zaizo kodan yay gaisuwa da yaran orphanage.
________________
Guards ɗin Yoohan sun iske madam Chioma ashe bata gari tayi tafiya zuwa ƙauyensu mamarta babu lafiya, saƙon kuma ya risketa bayan wucewarsu kano babu jimawa. Dan haka ta wuce hardasu joy da Gebrail. Su Victoria ne kawai da ƴan aiki suma saboda makaranta ne.
Sun shiga da tsaraban cikin gida suka ajiye har boss ɗinsu ya iso. Aiko zuwa biyar na yamma sai ga kiran Solomon yace suje su ɗaukesu a airport.
Su Abraham sunyi murna sosai na dawowar yayansu, sunata kallon kayan jikinsa mamaki na cinsu. Sai dai sun kasa tambaya dan babu fuska. Shi kuma bayan yaji komai na ciwon kakar tasu sai ya shige sashensa yay kiran momy.
Sun tattauna sosai ya basu shawarar ɗakkota a taho da ita nan Abuja ya dubata, dan ashe dama tun jiyan suke neman layinsa amma bai shigaba. Bayan sun ajiye wayar sai yay kwanciyarsa. Wani barcinne ya sake ɗaukarsa mai nauyi yauma. Bai kuma farkaba sai gabannin asuba.
Washe gari tun kusan goma na safe su Momy suka iso abuja, sun iske Yoohan ɗin ya gama shiryawa tsaf game da jikin kakar tasu. Suna isowa kuwa ya dukufa kanta. Cikin amincin UBANGIJI sai gashi tun aranar jikin nata ya fara sassautawa.
Wannan hidimar jinya ce ta mantar da madam Chioma sake bin ba'asin zuwan Yoohan kano har ma hutunsa ya ƙare yabar abujan.
*_A KWAN A TASHI_*
Babu wahala wajen UBANGIJI, dan gashi yau saura kwana biyu kacal salla, kowanne yanki na musulmi suna cikin shirye-shiryen ta da yin bankwana da azumin watan ramadhan😢.
Yayinda su Nu'aymah ƴan saudia keta shirin dawowa suma a ranar sallar...........✍
_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________
Wani kaya sai amale ka ɗauka🤗.
SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.
Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.
*_Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!._*
_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba'a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara_.
Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.
Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.
*_Siyen nagari😇, maida kuɗi gida😉 sai SAHFAT PREORDER🤗🤗😘😍😋_*
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
Alhmdllh, barkanku da salla. Barkanmu da dawowa filin daga.
Da farko zan fara da baku haƙuri akan ɓacewata ɓat tun kafin azumi. Uzirine babba kuma mai ƙarfi da bazan iya ajiyesaba ya riskeni. Amma Alhmdllh komai ya daidaita. Na kuma gode sosai da haƙurin da kukaimin.
Kufara da wannan kafin gobe idan ALLAH ya kaimu.
*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biyaba ki haƙura domin ALLAH🙏🏻☺️_*
No. 25
...............“Hajjo nikam mizai hana tunda kince bayan salla da sati uku za'ai bikin su Hajarah mu bari sai lokacin bikin muzo ni da Adawiya? Abinda zaki duba abune bana kusa ba, kuma gashi mu duka karatu mukeyi, musamman ma ni da nake gab da kammalawa. Idan har nace zan ringa jeka ka dawo zan iya samun matsala wlhy”.
Hajjo da ke sauraren yah Abdallah ta jinjina kanta cike da nazarin maganganun sa, ta sauke numfashi da gyara zamanta saboda ƙafarta mai mata ciwo. “Gaskiya kam Abdullahi ka fimu gaskiya daga ni harsu ɗan malam, duk da nasan suma ɗin kansu, abinda yasa wannan tunanin baizo musu ba, saboda ba'a gama dai-daita maganar su Kubrah ɗin bane ba. Na kula kamar shi mai auren Hajarah keson kawo wani tsaiko akan batun shiyyasa suka jinkirta harni na koma. Amma yanzu inaga ka barni dasu, zanyi magana ta fahimta da ɗan malam insha ALLAH”.
“Nagode sosai Hajjo, ALLAH ya ƙara lafiya da tsahon rai mai amfani. Ki daɗe kiyi ƙarko hajjajun mu”.
Murmushi kawai hajjo tayi da shaƙiyancin jikan nata. Daga haka suka cigaba da firarsu har zuwa wani lokaci ya fice ya barta tana ƙarasa shiri, dan Nu'aymah nacan ta tare a massallaci tana ibadar ALLAH.
Cike da farin ciki Abdallah ya faɗa saman gadonsa yana murmushi, insha ALLAH indai su baba malam suka amince zuwan nasu ya koma sai bikin su Kubrah yanada yaƙinin samun cikar burinsa. Dan babban fatansa shine shirinsa akan mallakar Nu'aymah ya tafi dai-dai, shima ranar ɗaurin auren su Kubrah a ɗaura nasa da masoyiyarsa, farin cikin rayuwarsa.
Wayarsa ya jawo dake a gefensa, ya shiga ma'adanar hotunansa yana kallon hotunan da yaytama Aymah a wannan zuwan nasu batare da ita kanta tasan yana ɗaukarba. Ya jima yana kallon hotunan kafin barci yay awon gaba da shi a wajen
Barcin nasa bai kai mintuna ashirin da ɗaukarsa ba Adawiya ta shigo gidan ita da maman Aaida. Ganin ɗakinsa a buɗe ya sakata nufar can tana faɗima maman Aaida, “Aminiya zauna ina zuwa, naga kamar Yah Ab yana gida ma”.
Ɗan murmushi maman Aaida tayi da bata amsa cike da zolaya. “To adaibi a hankali azumi ake hajjaju”. Batare da Adawiya ta bata amsa ba ta shige tana dariya.
Hajjo da dariyarsu ta sakata farkawa da ga ɗan barcin daya figeta itama ta fito dan taji ba muryar Adawiya bace kawai. “Baƙuwa mukayi a gidan?”. Ta faɗa lokacin da take fitowa falon. Maman Aaida dake latsa waya ta ɗago idanunta ta sauke akan Hajjo. Sai kuma tace, “Barka da fitowa hajiya”.
Hajjo dake mata kallon sani tace, “Barka dai ƴar nan, gashi kuma kamar na sanki”.
Da sauri maman Aaida ta zaro idanu waje da mamaki, sai kuma ta tuna maganar hajiya datai mata gargaɗi tun farko akan zuwa gidan, amma yau tsabar taurin kai sai gashi ta biyo Adawiya data dinga mata daɗin baki..........
“To ko dai kamanni ne?”
Hajjo ta katse mata tunani. Da sauri maman Aaida tace, “Eh gaskiya hajiya inaga hakane, dan ni ƴar nance”. Cike da nazarinta Hajjo tace, “Oh to ALLAH sarki, kinsan idon tsufa ƴar nan. To barka da zuwa, halan ke ƙawar Adawiya ce?”.
“Eh hajiya”. Maman Aaida ta bata amsa a ɗarare, dan tasha jinin jikinta da kallon ƙurulla da hajjon ke binta da shi...
Ɓangaren Adawiya kam tana shiga ɗakin Yah Ab sai ta iske yana barci, ga wayarsa ajiye saman ƙirjinsa kamar wanda ya rungume mace. Harta juya zata fita, sai kuma zuciyarta ta ƙwaɗauta mata wani abu daban. Dawowa tayi da baya a hankali ta ɗauka wayar, kasancewar ta jima da sanin password ɗinsa sai batasha wani wahalar buɗewa ba. Gabanta yay bala'in faɗuwa saboda cin karo da hoton Nu'aymah da tayi, ta kafe hoton da idanunta da suka ciko da ƙwalla, sai kuma ta kalli Abdallah dake barcinsa hankali a kwance batare da yasan tanai ba. Harararsa tayi kamar idanunta zasu faɗo, mikuma ta tuna oho mata, saita ajiye wayar a inda ta ɗauka ta fito a ɗakin.
Karo da taci da hajjo ta fito suna ɗan hira da maman Aaida yasata haɗiye damuwarta ta zauna tana gaisheta.
WASHE GARI
Washe gari ya kama ranar salla, a kuma ranar Nu'aymah ta fito daga ittiqafi bayan sakkowa sallar idi. Duk da tayi ƴar rama sai gata ta ƙara haske saboda yanayin zafinsu da kuma zama cikin ac a koda yaushe. Tayi mamakin ganin Abdallah yazo ɗaukarta. Da farko taso taƙi binsa, amma ganin rana zatayi saboda yau zasu wuce sai ta haƙura ta bisa.
Motar tayi shiru babu mai magana a cikinsu har suka isa ƙofar gidansa. Tana ƙoƙarin buɗe ƙofar yay saurin saka lock. Juyowa tai tana kallonsa fuska a ɗaure, shima sai ya ɗaure tasan, batare da ya kalleta ba yace, “Inason muyi magana da ke a yau”.
Kamar bazata tanka masaba, sai kuma tace, “Yah Ab maganar mi? Dan ALLAH ka cire komai a ranka kamar yanda na cire nima, bana buƙatar wata sabuwar fitina dan girman ALLAH”.
Cikin zafin rai yace, “Saboda kin samu wanda ya fini? Nu'aymah minai miki ne a rayuwa har kika zaɓi sakamin da waɗanan abubuwan? Mina rasa irin na sauran maza ne.....?”
“Baka rasa komaiba Yah Ab, sai dai ka sani mu wannan itace ƙaddarar mu, UBANGIJI kuma shine yasan hikimar dake cikin yin hakan. ALLAH shine shaidata ban gujeka ba, ban kuma daina sonka ba. Sai dai wata katanga mai tsauri tariga da tayi gicci a tsakanin ƙaddarar mu. A ganina kuma babu amfanin maida yanda akayi domin bakin alƙalami ya riga da ya bushe.........”
“Sai dai idan kece kika busar da shi Nu'aymah, idan har kin amince inason a wannan karon mu cika burinmu na mallakar juna, na yadda da kaifin wuƙar data datse zaren ƙaddarar mu a wancan karon, sai dai a yanzu na sake ɗaura ɗammarar ɗaure zaren domin mu zama abu guda kamar yanda mukai fata”.
Murmushi mai ciwo Nu'aymah tayi, ta gyara zama tana fuskantar Yah Ab, cikin raunin murya tace, “Yah Ab, karka manta a yanzu kai ɗin mijin Adawiya da Yusrah ne, tayaya kake tunanin zan yarda ka sake ƙulle wancan zaren ƙaddarar da kaifin wuƙa ya datsa ta. A ganina muyi haƙuri kawai da yanda yau tazo garemu, domin kuwa jiyanmu ta wuce sai labari. Muyi haƙurin fuskantar gobenmu sai muzama masu cin riba. Wlhy Yah Ab bazan taɓa iya haɗa zaman kishi da Adawiya da Yusrah b.........”
Da sauri ya saka hannu ya rufe mata baki, cikin matuƙar ɓacin rai yace, “Hakan ya zamemiki dole kuwa Nu'aymah, idan kuma kikace zakimin taurin kai, wlhy a yanzu sai kunbar ƙasarnan da Adawiya tare da takardar sakinta ɗai-ɗai har uku kuwa”. Yana gama faɗar haka ya cire lock ɗin motar tare da ficewa a fusace.
Nu'aymah da tun farkon fara maganarsa akan su Adawiya ta ɗaura hannu a ƙirji da faɗin, “Na shiga uku ni Zainab! Yah Ab mi kake faɗi haka?”. Bai saurareta ba ya shige gida, da sauri itama ta buɗe motar ta fito ta bisa da ɗan gudu tamkar zata faɗi.
Adawiya dake a ƙwance bayan motar tai saurin cire hannunta data toshe baki, dan daƙyar tai control ɗin kanta lokacin da Abdallah ya furta zai sakesu inhar Nu'aymah bata amince da buƙatarsa ba. Motar ta buɗe ta fito itama da sauri tana faɗin, ‘Tabɗi jan, ashe lokacin yin yaƙin duniya na uku ya gabato kenan, lallai yanzune za'a fara wasan na gaske wlhy’. Ta ƙare maganar hawaye masu zafi na gangarowa a kumatunta.
Tun lokacin da taji Abdallah na sanarma Hajjo shine zaije ɗaukar Nu'aymah bayan an idar da sallar idi ta ƙudiri aniyar binsa a ɓoye. Dan haka kawai taji a ranta akwai manufa a zuwa ɗaukar, dan ta gama fahimtar take-taken Abdallah tun lokacin dasu Nu'aymah suka zo ƙasar. Shinefa ta lallaɓa taje ta shige motar ta ɓoye sannan ya samama hajjo inda zatayi sallar idi a massalacin, shi kuma batare dayin wani tunani ba yana zuwa yaja motar ya wuce. Kuma harya ɗakko Nu'aymah hankalinsa bai kai akan Adawiya dake lafe a ciki ba. wadda ko sallan idi ita batayi ba.
Tana shigowa cikin gidan duk a falo ta iskesu har Nu' Abdallahn. Duk suka bita da kallon mamaki dan sunta nemanta bayan idar da salla basu gantaba, shine Ahmad yace suyi tahowarsu tunda ita ɗin ƴar garice ai.
“Ke kuma dama ba gidan kika dawo ba?”.
Abdallah ya faɗa cikin kaushin murya dan har yanzu ransa a ɓace yake. Kamar bazata tanka masa ba, dan ranta a bala'in cinkushe yake, ji take kamar ta burmama Nu'aymah wuƙa ta mutu kowama ya huta. Amma komi ta tuna oho mata, sai tai kalar tausayi tana haɗiye ƙududun daya tokare mata maƙoshi. “Eh na biya nan maƙwafta wajen Umm-Farukh, dama wasu kayane mukai da ita zan amsarma su Aymah to kuma ma dai anyi rashin sa'a basu isoba, dama daga Mexico ake kawo matasu”.
Ɗauke kansa yay bai tanka ba, sai Ahmad ne da Hajjo sukai magana. Nu'aymah da tasha jinin jikinta akan yanda Adawiya ke magana ma bata tanka ba, sai dai a ƙasan ranta bata yarda da itaba sam.
★★★
Duk yanda Abdallah yaso sake keɓewa da Nu'aymah dan su sake cimma matsaya akan zancensu taƙi basa dama har suka wuce Nigeria bayan awanni huɗu da sakkowa idi, dan kobi takan bikin sallar da ƴan saudia ke gudanarwa basuyi ba, dama Adawiya ƙin dafa komai tai saboda takaici. Abdallah zaiyi magana kuma Hajjo ta hanashi, acewarta su da zasu tafi yanzu mizasuyi da wani abincin salla bayan nasu nacan na jiransu a ƙasarsu.
Sun sami ƙyaƙyƙyawar tarba kuwa daga su baba malam, dan ana sakkowa daga sallar juma'a (da yake ranar sallar ta kama juma'a ne) suka nufi airport domin tarbar mahaifiyarsu tamkar yanda suka saba. Babu kunya Nu'aymah taje ta rungume Baba malam, dan harga ALLAH tayi kewarsa shi da Umm da Muhammad. Kai dama ƴan gidan duka.
Fuskar baba malam ɗauke da murmushi ya shafa kan ƴar tasa yana faɗin, “Ja'ira, duk ga iyayenku cike da wuri bakiga kowaba sai ni ko?”. Fuskar Nu'aymah washeda murmushi tace, “Abba nayi kewarka ne sosai, kuma ALLAH kullum sai nayi mafarkinka kai da Ummuna”.
Baice da ita komaiba sai murmushi kawai daya sakeyi, dan shi mutum ne mai tsananin kawaici ga yaransa, yanama ƴan uwansa kara sosai. Dan haka suma a kullum suke ƙoƙarin koyi da ɗabi'unsa akan nasu ƴaƴan.
Bayan Nu'aymah ta ƙarasa ta gaida sauran iyayenta uku suma cike da girmamawa. Suma suka amsa mata da tsananin kulawa sai suka runguɗa gaban mahaifiyarsu suna jera mata sannu da zuwa. Cike da kulawa da kewa take dubansu, fuskarta faɗaɗe da murmushi. Ta kama hannun Abba Musbahu tana faɗin, “Wayyo autana duk ka faɗa, ko azuminne?”.
Dariya Nu'aymah da Ahmad sukayi, Malam ƙarami da Omar na tayasu kuwa. Hakama su baba malam sunata murmushin akan diramar autan nasu da mahaifiyarsu.
Lokacin da suka iso gidan nasu sun iskeshi da dangi da yaransu na ma'auri duk anzo tarbar hajjo da kuma yawon salla. Inda gidan ke wadace da tarin abinci kala-kala da kowanne sashe ya tanada. An gyarama hajjo sashenta tsaf an kuma kai mata abinci daga kowanne sashe an ajiye mata. (Dama haka suke mata).
Motocin na gama tsayawa Nu'aymah bata tsaya sauraren masu tarar tasu ba ta shige sashensu da gudu tana ƙwalama Umm kira. Da sauri Umm dake ƙoƙarin fitowa taja baya dan kaɗan ya rage suci karo da Nu'aymah.
Faɗawa jikinta tai ta ƙanƙameta tana faɗin, “Wayyo Ummuna, nayi kewarki wlhy”. Umm dake murmushi ta amshi ɗiyar tata da hannu biyu ta rungumeta itama, sai da ta tabbatar sunji ɗumin juna kowa na sauke ajiyar zuciya kafin ta ɗagota da ga jikin nata. “Nu'aymah! Yaushe ne zakiyi hankali kisan kin girma ne? Bakisan yanzu ba da bane, shekararki goma sha bakwai fa kina shirin shiga sha taƙwas”.
Cike da shagwaɓa ta saka kanta a kafaɗar Umm tana faɗin, “Umm ni indai ina gabanki wlhy jaririyace sabuwar haihuwa, nayi kewarki ne sanyin idaniyata. Ina Muhammad yake?”.
“Nayi cinikinsa” Umm ta bata amsa tana janyeta daga jikinta ta fice domin shiga tawagar masu tarbar surukar tasu.
Baki Nu'aymah ta tura gaba, ta ɗaga ƙafa zata biyo Umm tajiyo muryar Muhammad a bayanta yana faɗin, “Marhaban biki Aunty na”. Saurin juyowa tai garesa, sai kuma ta nufe da sauri kamar yanda yake nufota suka rungume juna cike da kewa da ɗoki.
Haka gidan ya kasance a hargitse ranar saboda shagalin bikin salla, Nu'aymah bataje ko inaba, dan bayan tayi salla taɗanci abinci sai ta shiga ta gaida kowa na gidan, kafin ta koma ɗakin Umm tai kwanciyarta, duk wanda yazo musu yawo a ranar bai samu ganinta ba, dan ta ɓoye kanta a cewarta saita huce gajiyarta da ƙyau tunda dai tasan zasu zaga gari yawon sallar gobe idan ALLAH ya kaimu ai.
___________
Kiran sallar la'asar ne ya tada Nu'aymah dake kwasar barcin gajiya. Ta miƙe da ƙyar dan jikinta ko ina ciwo yake faman mata. Wanka ta farayi, ta saka ɗaya daga cikin kayan sallarta. Tayi ƙyau sosai cikin shaddarta ruwan hoda, taji aikin stones da yay ƙyau sosai. Kayan sun mata ɗas ajiki, tare da sake fiddo haskenta saboda ƴar ramar da tayi.
Lokacin data fito Umm kanta sai da tace, “Masha ALLAH”. Hakama ƴaƴan yayun Umm ɗin su uku da sukazo mata yawon salla duk sai da suka yaba ƙyawun da Nu'aymahr tayi. Ta zauna fuskarta da murmushi tana gaidasu cike da girmamawa. Dan dukansu matan aurene, kuma duk suna da yaransu. Cike da kulawa suke amsa mata, kowanne na mata ƙorafin rashin zuminci, musamman babbarsu.
Nu'aymah tace, “Lah Aunty Zulfah wlhy ba rashin son zuminci bane, ni abinda yasa banason zuwa gidanki wannan ƙanin mijin naki takuramin yake wlhy. ya cika shegen kallo kamar ɗan daudu”.
Dariya suka sanya gaba ɗayansu, aunty Zulfah tace, “To kwantar da hankalinki, indai Fa'iz nema aurensa zaiyi, tunda ke kinƙi. Kinga nima dakin yarda ai dana samu ƴar uwata kusa dani ko.......”
Da sauri Nu'aymah ta katseta da faɗin, “Taf, aunty daina faɗa dan ALLAH, wlhy ya cika iyayi, banason namiji yayta gwalli kamar wani mace, shiba ɗan daudu ba shiba mata maza ba”.
“Amma Nu'aymah baki da kirki wlhy, kin gama ɗebema ƙanin mijin aunty Zulfah albarka gaba ɗaya”. Aunty Rafi'a ta ta faɗa tana dariya. Ita kanta Nu'aymah dariyar takeyi, Umm dai batace musu komaiba. duk da kuwa tana zaune tana jinsu.
Sai da suka tsagaita da dariyarne Nu'aymah ta miƙe tana faɗin, “Umm yunwa nakeji, ALLAH yasa akwai waina dai?”.
“Kin kuwa makaro, dan su Basira na ɗeboma ita gaba ɗaya, kinsan zakici wainar kikaƙi ɗiba ki ajiye?”. Kamar Nu'aymah zatai kuka tace, “Kai Umm! ALLAH yanzu kin daina sona, amma yanzu duk wainar dana gani ace ta ƙare? Su su aunty Basiran miyasa basu zauna sunci a sashen Addah b.......”
Harar da Umm take jefo matane ya sakata yin shiru, dan su Basiran ƙannen Adda ne. “ALLAH ya shiryeki to, to ance miki sune kaɗai suka cinye. Ga yayunki nan suma duk ita sukaci, sannan Abbanku da yay baƙo duk da baya a gidan shima ita yace akai musu kafin ya iso gidan”.
Komawa tai ta zauna kamar zatai kuka, su Aunty Zulfah nata tsokanarta wai ta amshema Muhammad guri tana shagwaɓa bayan shine auta.
Umm tasan yanda Nu'aymah keda jarabar son waina, dan haka ta dubeta sau ɗaya ta ɗauke kanta tana faɗin, “ki wuce sashen hajjo idan bata ƙareba”. Aiko zumbur ta miƙe, a ranta tana fatan ALLAH yasa ta samo.
Duk da takalman data gani na maza a ƙofar falon na hajjo kusan ƙafa biyar bata damu ba, sallama tayi kawai, kafimma su gama amsa mata ta shige dan duk zatonta yayunsune a ciki, tunda tasan duk suna gidan. A shagwaɓe ta buɗe baki zatai magana. sai dai cin karo da fuskar da batai zato ko tsammanin gani ba ta sata waro manyan fararen idanunta waje cike da al'ajabi.
Yoohan dake zaune shima cikin Suit ruwan babypink kallon nata yake cike da mamaki, a ransa faɗi yake, ‘Dama yarinyarnan ba'a cikin Orphanage ɗincan take ba? No wander ɗazun baiga komai kama da itaba a cikin yaran’. A fili kuwa sai ya ɗauke kansa cike da shan ƙamshi kamarma irin bai ganta ba ɗin nan shi.......
“Lafiya wai kika tsayama mutane ƙerere a kai Zainabu?”. Maganar Hajjo ta katse mata tunaninta. Juyawa tai inda hajjon take, har yanzu mamakin ganin Yoohan ɗin bai barta ba, “Hajjo wannan mutumin kuma ina kika sanshi?”.
“Wa ɗin?”. Cewar Hajjo tana kallon inda Hamza Manager, Yoohan dasu baba ƙarami ke zaune.
Maimakon Nu'aymah tai magana sai ta je ta zauna kusa da hajjon, matsar da bakinta tai dai-dai kunnen Hajjo tace, “Hajjo arne ne fa wlhy”. “Aina sani” Hajjo ta bata amsa cikin nuna halin ko in kula.
Sosai mamaki ya kume Nu'aymah, tai tsai tana kallon Hajjon, kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta sake maida dubanta ga Yoohan daya maida dukan hankalinsa kan wayarsa.
“Wai lafiyarki kuwa? Kina ganin mutane baki iya gaisuwa bane? Sai shegen kallo malama”. Yah Ahmad ya faɗa idonsa akan Nu'aymah. Sai da taɗan tura baki kafin ta duba Hamza manager data wuce da dukanin imaninsa tace, “Ina yini”. Cikin narkakkiyar murya da shi kansa baisan ta fitaba ya amsa mata da “Lafiya lau ƙanwarmu, kinyi salla lafiya?”. Kai ta gyaɗa masa kawai, dan duk sai taji kuma ta takura da kallon da yake mata. Ganin bata gaida Yoohan ba ya saka Malam ƙarami hararta, yace, “Shi kuma fa?”.
Yanzun kam baki ta kumbura sosai, ta kalli Yoohan ɗin da yay tamkar baisan da zaman kowaba a falon tace, “Good evening.
Sarai yajita, amma sai ya share baiko motsaba. Sai da Hamza ya ɗan taɓasa da faɗa masa ana gaishesa sannan ya ɗago manyan idanunsa farare tas ya sauke a cikin nata. Karan farko da sukaima juna kallon ido cikin ido. Kusan lokaci guda kowanne gabansa ya faɗi. Nu'aymah tai saurin fara janye nata da ƙoƙarin juyawa daga saitinsa.
Shima ɗan lumshe nasa yay ya buɗe (dan hakan ya zame masa kamar wata ɗabi'a) cikin muryarsa mai amo ɗin nan yace, “Kina lafiya?”.
A mugun razane Nu'aymah ta sake waigowa inda yake, har taune harshenta take wajen faɗin, “What?! Dama kanajin hausa?”.
Yanda tayi tambayar sai da ya saka su hajjo yin dariya. Hakan sai ya ƙarama Nu'aymah takaici, musamman ganin yanda Yoohan ɗin ya wani yamutse fuska, tare da miƙewa saboda wayarsa da aka kira, dama shi baiyi dariyarba. Sai da yazo daf da ita a hankali yace, “Yeyye girl”.
Kafin wani ya sake magana a cikinsu, ko ita ta bashi amsa Abban su Adawiya da Abban Musbahu suka shigo falon da sallama. Shi kuma ya fice yana amsa wayar.
Daurewa tai ta shiga gaishesu tana ɗan harar ƙofar da Yoohan yabi ya fice ta gefen ido, a ranta kuwa sai cewa take, ‘Oh ALLAH, amma dai gayen nan akwai munafurci, dama yanajin hausa amma duk sanda suka haɗu yake nuna mata bayaji, jibesa da wani shegen aski kamar kan zakara, sai kuwa yaga yeyye kafin yabar gidan nan yau’.
Duk kallon harar Yoohan da take Manager yana kallonta ne ta gefen ido shima, sai da Abban Musbahu ya kira sunansa ne sannan ya maida hankalinsa garesa, a ransa yana mamakin yanda alamu suka nuna akwai sanayya tsakanin Yoohan da wannan Zuƙeƙiyar budurwar data gama tafiya da dukkan imaninsa a kallo ɗaya.
Ita kam Nu'aymah da batasan yanayi ba sai ta lallaɓa ta fice dan jitai tama fasa cin wainar, yau duk yanda za'ai sai taji dalilin shigowar wannan kahirin cikin gidansu, harma falon kakarsu...........✍
😜Kina ruwa Aymah😸.
Leave a Comment