Sanadin Caca Book 2

 


BOOK 2*

...1...

Yana shigowa kaman yanda Sadeeq yayi shima haka yayi,ganin wani a akan kujera mai kama da ɗansa,wanda ya fidda saka ran ganinsa tsawon shekara biyar,yau gashi yana kallonsa a gabansa tamkar alamara.

A hankali yake tafiyah har yana dafa hannun kujera saboda kar ƙafafunsa su kasa ɗaukarsa i zuwa ga gudan jinin nasa..

Hannu yakai wanda yake rawa kan kumatun Ahmad ɗin,wanda yayi tafiya cikin duniyar suma bai san mai suke ba.

"Ah......ahhmmad dama kana raye duk tsawon wannan shekarun,toh ina ka shiga hakane bamu sani ba,ya akayi labarinka ya bace ƙasa ko sama babu shi babu alamarsa?"

Ɗagowa idanuwansa yayi ya kalli detective Sadeeq bayan lokaci daya ɗauka yana sambatu ma ɗannasa.

A tsaye yake kyam tun shigowar AM Aliyu yana kallonsu,saidai ya juyo tukunna ya rusuna.

"Sadeeq kacemin daya shigo ƙalau yashigo,to menene ya sakashi yin haka?"

"Am Abbah Nima bansani ba,kawai kafin ka shigo ya riƙe kai,saikuma ya naga ya suma"

"Kuma mai ake jira,kalli fah jikinsa kaman bashiba,maza ka sanar da masu kulada samfuri maza a shirya private jet na fita dashi waje,yana buƙatar a yimasa gwaje gwaje a duba lafiyarsa,a ƙalla ya samu hutun shekara biyu kafin ya dawo""

"To abbah an gama,yanzunnan za'a shirya komai kaman yanda kace"

Yana gama faɗin hakan kuwa a take aka fara shirye shiyen fitada Gen Ahmad ƙasar waje domin a duba lafiyarsa.

Kasancewar abune na masu hannu da shuni,kafin dare an gama komai sun ɗaga Egypt,shikaɗai AM Aliyu ya tura shi,dan dama yawancin rayuwarsa a can yayi,bazaiji wani wahalar zama ba.


Sameer ne a zaune a falo da remote a hannunsa,wani film ɗin sojoji yake gani,gabaɗaya yabada hankalinsa ga wajen. Gefensa kuma Fatee Ce tayi kicin kicin kaman zata fashe dan haushi,sai zabgawa Sameer harara take ta gefen ido,Maimuna ce ta kulada itah,wacce take a zaune a opposite ɗinta tana danna labtop.

"Kai Fatee da wanann hararar kije ɗakinki mana kiyi,kina fah da komai a side ɗinki ba wai bakida shi ba,menene na wannan fushin haka"

Maimuna tayi mata magana cikin sanyin rai,amma ko a jikinta kamam an mintsini kakkausa.

"Haba anty Maimuna ya zakice haka,bakya ganine nice fah na fara ɗaukan remote ɗin amma ya kwace,sai mutum yayi magana ace za'a dakeshi dan anfishi ƙarfi,miye abin kallo a waɗannan gardawan"

Ta faɗa tana nuna tvn,shikuwa Sameer yana jinta amma babu abinda yace,saima ƙara volume da yayi,tafi kowa sanin shuru yayi,ana jimawa idan ta cikashi zai mata duka,saboda zafin zuciya gareshi kaman mahaifiyar tasu.

"Ai wlh ma saina faɗawa Abbah,yana tafiya aiki kake dawowa gida ka damu mutane"

Ajiye remote ɗin yayi tareda sakin ajiyar zuciya yanayimata kallon takaici.

"Ke wai ina wasa dakene,kodan kinga kece ƙarama a gidannan sai akace kiyi yanda kika ga dama,ai ummah bata nan kiyi hankali kona kakkaryaki anan wajen,zakice wani saikin faɗawa Abbah cewar ina dawowa daga wajen aiki,to in kin fasa,ko kinace banda labarin fashin da kike na makaranta. To duk mu faɗamasa mana"

"Ehh naji amma ai bana bin saurayi yawan shaƙatawa dai"

Taƙarisa maganar tana murguɗa baki.

Sakin baki Sameer yayi yana kallonta,ya tashi zai bugeta kenan yaji wayarsa tayi ƙara,tsayawa yayi tareda duba wayar. Wani ɗan wajen aikinsu ne ya ƙirashi dan haka ya ƙyaleta ya ɗaga a zatonsa ko akan akinne.

Su Maimuna da suke falon sai gani sukayi ya samu waje ya zauna,tareda cewa.

"Mai kake cewa ne,yah Ahmad wai ka gani anya kuwa,kuma har abba ma yaje ya ganshi?........"

"Wanne Ahmad ɗin?"

Yaji muryar Hajiya Maryam ta tambayeshi,wanda shigowarta kenan ta dawo daga fitar da tayi da safe,doguwar rigace a jikinta abaya,wacce aka narka kuɗi kafin a fansheta,saikuma gyalenta data yane kanta,jakarta da kuma takalminta suma designer ne masu zaman kansu,wanda ko matan gwamna saisun shirya. Shi kansa AM Aliyu yana mamakin yanda take samun waɗannan kaɗaɗe da take narkawa kanta su,wanda kuma hakanne ya kankaro mata mutunci a wajen mutane da dama.

"Nace maka wanne Ahmad ɗin,ba tambayarka nake bane?"

Ta sake maimaita maganar tana kafe Sameer da kallo,su kansu sunsan dramar da ake sha a gidan da mahaifiyar tasu da kuma yayannasu,idan wani ya shiga harkar wani.

"Uhm ummah dama.....dama....?"

"Dama me.!!!?"

Dafaɗa cikin ɗaga murya,shikansa da yake soja saida ya raxana daganin yanda yanayinnata ya sauya..

"Ummah Ahmad aka gani yau da safe,abba ma yaje wajensa,saidai wai ya suma an fita dashi ma egypt a lokacin"

"Egypt,kawai daga ganinsa sai a fitada shi akan me toh?"

"Ummah ance bashida lafiya ne bayan ya farfaɗo ɗin"

"Uhm"

Tafaɗa tana sauƙe wani numfashi mai nauyi haɗe da dunƙule hannunta,a lokacin inka ganta zaka kasa gane inda yanayinta yake,shin baƙin ciki take ji kokuma tsoro da fargaba.

"Ke Fatee abbanku ya dawo?"

"Ahah baidawo ba ummah"

"Inya dawo ki sanar dani"

Daga faɗin hakan bata sake cewa komai ba tayi hanyar sashenta,dan inda su Sameer suke babban falon gidanne.

Tun a hanyar ɗakinnata ta fito da waya tana dannawa,da alama wani ko wata take nema a wayar cikin gaggawa.

"Hello Neelah? Maza ki bincikamin yanzu,shin da gaskene wanda ya bayyana Ahmad kokuma wani ne daban,ina son bayanai yanzu yanzu,sannan ki tabbatar ba'asan kinyi ba,karki saka ƙungiya ma a ciki"

"To shikenan Ranki ya daɗe yanzu kuwa zan bincika"

"Idan har ya tabbata shine to da akwai gagarumar matsala,don shirin da mukeyi gabaɗaya wargajewa zayyi,dan haka ki taka tsantsan ki ganomin komai. Am har yanzu bakiga wani aikeba?"

"Bangani ba ranki ya dade,amma karki damu Inshaallah babu wata matsala,komai zai tafi daidai,babu wanda zai gano komai"

"Batun akwatin fah?"

"Uhmm shima dai normal tunda babu wani zance kan gwamnati tanada shi,kokuma bayyanar sa a wani wajen,dan haka da sannu komai zai tafi daidai"

"Wai to garin ya haka ta faru a bazata,duk shirin da mukayi na ya bata a duniya saida ya dawo....mtswwww"

Sauƙe wayar hajiyah Maryam tayi,harta buɗe ƙofah zata shiga tajiyo fasa glass a falon data bar su Sameer. Muryar Mulaifah tajiyo,tasan kuma dama babu mai wannan abin sai ita,runtse ido tayi tareda jijjiga kai kana ta koma falon.

Center table ɗin tsakiyar ɗakin ta fasa raga raga,tana kuma tsaye fuska shabe shabe da hawaye.

"Meyasa za'ayimin haka,sanin kowane duk tsawon wadannan shekarun jiran Ahmad nake da yaƙinin dama nasan watarana zai dawo gareni,to yanzu kuma ya dawo ace wai an fita dashi abroad batareda na sani ba?"

"Ke Mulaifah wannne iskanci kika zo kinayi a nan wajen,wanene ya damu da jiransa da kikeyi dazaki zo kin wargazamin gida,kinyi fah ya isheni haka,zanyi mungun maganinki idan baki nutsuba"

Hajiyah Maryam ce take maganar cikin masifah da takaici.

"Ke wacece dazaki yimin masifah iyaee,dan kina matar gida bashine zaisa ki zama matar gidaba,kuma gidannan kokiso kokuma ki ƙi inada iko nima dashi,tunda mahaifiyata ƴar gidance. Nasan wannan masifar da kike dan kinka duk abinda kikeyi bai yi aikiba saida ya dawo shiyasaka,kuma ki zuba ido ki gani,auren da aka fasa ɗaurawa saboda mutuwarsa sai an ɗaura shi yanzu ehe"

"Cabɗijan uban mai zayyi dake,kina bazawara sannan kika sani ko a inda yake yanada mata da ƴaƴa?"

"Ahhhhh aikuwa da saina kasheta na ƙonata,Ahmad nawa ne ni kaɗai,babu wata shegiya a bangon duniyar nan dazata rabe shi,ba'ayita ba kuma babu itah. Ke kuma ni kikecewa bazawara ko,dan ma kema uwar taki a bazawarar aka aureta ai......"

Tass hajiyah maryam ta ɗauke Mulaifah da mari a kuncinta na dama,wanda hakan ya tsaida ta daga masifar da take jajjagawa.

Magana Mulaifah zatayi amma ganin AM Aliyu yasa ta fashe da kuka tareda yin inda yake.

"Abba kalli ka gani koh,yanda shararamin mari dan kawai nace Ahmad ya dawo,dama kowa yasan sun tsaneshi basaso ya dawo,abba ka faɗamin a wace ƙasa yake zanje na ganshi,bazan iya kwana ɗaya va batareda na ganshi ba"

Kuka take tana narkewa kaman ba ita ce ke faɗin maganganu ba a lokacin.

"Shikenan kiyi shuru haka,ke Maryam meyasa kika ........"

Maƙale maganar yayi ganin yanda ta jefeshi da wani arnen kallo mai haɗe da harar.

Juyawa tayi ma tabar wajen ƙwass ƙwass kana jin ƙarar takalminta akan tiles saboda yanda take taka shi da ƙarfi.

Sauƙe a jiyar zuciya yayi tareda kallon Mulaifah.

"Kinga kiyi shuru haka,jeki wajen Mammah nima yanzu ina zuwa"

Daga haka shima ya wuce nasa sashen,su dai Fatee kallo ne nasu kawai a falon,dan inda sabo sun riga sun saba da ganin wannan dramar a da,abin lafawa yayi saboda babu wanda za'ayi rigimar akai,to yanzu da ya dawo za'a cigaba.

Heeho shagali shagali dama wlh nayi missing gidannan ba'a drama,amma yanzu tunda yah Ahmad ya dawo nasan za'a shigaba da gashi"

"Ke Fatee kinada hankali kuwa,tashin hankali da ake a tsakanin iyayenki shine abinda kikeso koh?"

"Ahh to ya zanyi anty Maimuna,in kaji haushima ba fasawa za'ayi ba,dan haka gwanda ka zuba ido kayi kallo ka more....Mulaifah bazata daina haukar nunawa yah Ahmad soyayya ba,shikuma bazai daina nasan dizgata ba kaman da,sannan mommy bazata daina nuna masa ƙiyayya ba,yayinda shima bazai raga mata ba.....kinga kuwa ai za'a sha drama saidai in wani ne ya sanja hali,wanda bana tunanin hakan"

Tana gama faɗin hakan tayi hanyar sashen ta tana waƙa.

A bangaren Mammah kuwa da gudu Mulaifah tashiga kaman an jefata,sakaliyace ta zubawa a taro,duk da cewar akwaita da masifa a tantiranci,mahaifiyar ta ƙanwar AM Aliyu ce,bayan ta rasu Mammah ce ta riƙeta maimakon gidan ubanta,wanda hakan yasa suka shaƙu take ganinta tamkar ƴar ta.

Tun shekara goma baya da Ahmad ya dawo daga Egypt Inda yake zaune ta kamu da sonsa. Tun yana shareta har yafara tsayar mata na shiga rayuwarsa da take,amma hakan duk a banza,daga baya ma sai aka saka zancen manya a ciki. Ahmad yana ji yana gani aka tsaida bikinsu itada shi badan ya so ba.

A na shirin bikinne yayi hatsari ya mutu,bayan haka Mulaifah tayi ta kuka har ƙaramar hauka saida tayi da mutuwar tasa,tayi aure ma baije ko ina ba ta kasheshi ta dawo gidan.

Basa shiri ko kaɗan da hajiyah Maryam saboda nuna ikon da Mulaifah take,da kuma nunawa Ahmad so,a bangaren hajiyah Maryam kuwa kowa yasan bataso taga wani yana baza iko a fadarta,sannan duk wani abu daya shafi Ahmad bata ko buƙatar jinsa ballantana da dunga gani.Dan haka bata kawo Allah a wajen magance matsalarta ballantana mutum,wanda itama Mulaifan haka take a nata bangaren.


Wannan kenan a shafin farko na littafin SANADIN CACA BOOK 2.DOWNLOAD HERE

No comments

Powered by Blogger.