Namijin Zuma 4


Free page4

     *WAYE AEEZAD?*

Asalin sunansa Ahamad sunusi Ahamad  (Aeezad) Ahamad sunan mahaifin babansa yaci. Asalinsu cikakkun yan jahar katsina ne a karamar hukumar malunfashi. su biyu kawai mahaifinsu Ahamad ya haifa da

matarsa Daya tal  bilkisu itama cikakkiyar bakatsiniya ce., Abubakar ne babban dansu se sunusi na biyu kuma na karshe. Alhaji Abubakar cikakken Dan kasuwa ne wanda akeji dashi a jahar katsina dama wasu  Garuruwan, yanada mata daya tal wadda itama cikakkiyar yar garin katsina ce. iyayensu Ahamad  da bilkisu bakowa bane Arziki yara ne yasa suka zama wasu a halin yanzu, sosai Allah   yayima Abubakar da Sunusi   nasibi bakaman sunusi wanda yake Dan boko ne sosai ma'aikacin gwamnati kuma Dan kasuwa, sannan ya rike mukamin minister a abuja, kana yadawo katsina ya rike mukamin governor a shekarun dasuka shude. Alhaji sunusi Ahamad ya Auri matarsa Aisha yar asalin jahar niger , dayaje kasuwanci niger din suka hadu da Aisha, Sam iyayenta basu so Aurenta da Sunusi ba Kasancewar sa ba Dan kasa ba,  Amma ba yadda sukaso a haka akayi auren kasancewar suna tsananin kaunar junansunsu.  haihuwar farko Aisha ta haifi diya mace akasa mata sunan  mahaifiyar bilkisu wato hafsa, bayan shekaru Aisha tasamu cikin Aeezad gun haihuwarsa ta rasu ko d'anma bata gani ba, hauka ne kawai Alhaji sunusi beyi ba kasancewar Yana tsananin San matarsa, mace ce me hkri da tarbiya, yasan baze taba samun kamarta ba. Bayan rasuwar hajiya Aisha danginta sukace a basu yara Alhaji sunusi yaki yace ai yaran yake gani yaji dadih, aka tirza aka tirza yaki bada yara, Dan haka suka hakura suka bar masa yaransa,kanwar Aisha fatima ta nemi alfarmar Alhaji sunusi kan tasamo musu nanny amintacciya wadda zata dinga kulawa da yaran    musammanma jaririn wanda yaci sunan mahaifin Alhaji sunusi, ranar da aka haifesa ranar mahaifin Alhaji sunusin ya rasu,.  Alhaji sunusi yace ya amince asamo masa nanny din amintacciya wadda zata tarairayar masa yaransa.  Cikin jin dadih fatima ta koma kasarsu ta nufa Wani kauye a cikin agadex, gidansu  nabeelah, mahaifiyar nabeelah wato rukayyah  ita ta rainesu hatta Aisha mahaifiyar Aeezad ita ta raineta itadin tsohuwar maid dinsu ce Tin tana karama  aure ne datayi ya rabasu. Ta isa gidan ta tadda rashin sa'ah  wato ciwo me tsananin ya kama rukayyah kusan 4yrs tana kwance sede a kwantar a tasar, zuwan fatima yasa aka kaita asibiti domin ko kudin asibitinma Basu dashi, mahaifin nabeelah ya rasu tun nabeelah na jaririya be bar musu komi ba se daki daya dasuke ciki, shima seda suka sayar dashi duk a kan ciwon mahaifiyarta suka dinga bin  masu maganin gargajiya suka cinye kudin tass sukace ai iska ne, Amma sam sun kasa sama mata lafiya.  Rayuwa ta musu tsada Ainun cin yau dana gobe ma da kyar suke samu a haka har nabeelah ta tasa zuwa 10yrs ita kadai suka haifa, mahaifiyarta marainiyace ba uwa ba uba basu da Wani gata sena ubangiji, bame kallonsu dasigar tausayi, zuwan fatima gidan ne yasa har aka Kai rukayyah asibiti, a Nan likita ya fahimci tanada cancer din mahaifa wanda hakan ke barazana ga lafiyarta. Nan fatima ta biya aka dubata aka daurata a kan maganguna masu tsananin tsada,da kyar aka samu rukayya tasamu, aka dawo da ita gida a Nan fatima ta zayyana mata abinda ya kawota tace daman tazone ta tafi da ita Nigeria ta kula da yaran Aysha domin ta rasu,..." Rukayya ta jinjina rasuwar Aysha sosai ta tausaya Ainun,taji daman tanada lafiya ta biya Alkhairin da fatima ta mata ta hanyar kulawa da yaran yayarya, Sam bataji dadih ba. Fatima ta tashi zata tafi nabeelah wadda bata wuce 10yrs ba tace ita zatayi, fatima ta kalleta taga tayi kankanta tace "Bazaki iya ba..." Nabeelah  tace zata  iya Dan Allah A taima a dauketa..." Nabeelah  ta tashi da burin ta kula da mahaifiyarta tin tana 6yrs ciwo ya kama mahaifiyarta ita ke kulawa da ita har zuwa yanzu bata da Wani matainaki  tanaji a ranta ba abinda baxata iyaba A kn uwarta. Ganin yadda yarinyar keta magiya yasa fatima yarda zata tafi da ita, sbda ta kula da yadda yarinyar keda kokari da juriya a jinyar mahaifiyarta,, se kuma fatima tayi tunanin inta tafi da nabeelah waze kula da rukayya, dan haka tace aah gaskiya bazata tafi da nabeelah ba, nabeelah tace "Akwai wata makwabtansu hassana tanada kirki ita ke tayata kulawa da mahaifiyar ta,  tasan ko bata Nan zata kula da mahaifiyarta tamkar tana Nan..." Haka badan rukayya taso ba, suka Rabu da nabeelah itama nabeelah badan taso ba kawai halin rayuwa ne  yasa tilas se anyi hakan, basu da mataimaki Dan haka dole nabeelah ta nema kodan ciwon dake jikin mahaifiyarta Daba na kare ba.  


A fari Alhaji sunusi yayi gaddamar daukar nabeelah sbda a tunaninsa tayi kankanta da kyar ya yadda ya dauketa Amma aka hadata da wata babbar mace babah lantai.  Tinda nabeelah taga Ahamad zuciyarta ta kamu ta kwadaitu da sanshi, ta daukeshi ta dinga tattalinsa tamkar ita ta haifesa da cikinta, taci kashinshi taci fitsarinsa, in beyi bacci ba itama bata bacci, ita tasa masa sunan Aeezad kuma tasa masa suna jarumi, Sam bata barinsa yayi kuka , in ko yayi kuka ko yaya Ne itana setayi kuka, bata kaunar abinda ze tabasa,tsananin kula take basa ba wanda ze gansa yace maraya ne, harma tafi babah lantai kulawa dashi ita Hafsat kawai take kulawa da ita, Aeezad Kam kullum Yana jikin nabeelah bata kaunar taga ta raba jikinta da nasa haka shima baya kaunar yaga ya bar jikinta, duk wanda ya daukesa se kuka, koda daddy ne ya daukesa se yayi kuka, babban burinsa kawai ya bude idonsa yaga Nabeelah tin Yana Dan 2month yake qiwa, nabeelah kawai yasani, a gabanta aka masa kaciya ita tayi jinyarsa har ya warke,, tinda Aeezad ya bude Ido nabeelah yake gani da santa ya tashi dashi ya girma, a fari yasha ita ta haifesa seda ya kara girma ya fahimci nanny dinsa ce, Amma sam ko diss bata taba barinsa yayi kukan maraiciya ba, ta koyi sanshi tin randa tafara ganinsa , shima ya taso da santa tamkar san uwa da d'a .  Time to time hajiya bilkisu na zuwa tagansu domin ta roki a bata su mahaifinsu yaki, shi yafiso a kullum yayita ganinsu beson yayi mssing ganinsu kona second ne. Haka dangin Aisha ma na zuwa suga yaran sosai  duk bayan month, sosai sukaji dadin ganin yadda Nabeelah ke kula da Aeezad sunsha mamakin ganin yadda take kula dashi tamkar macen datasan zafin haihuwa. Alhaji sunusi ma yaji dadin yadda take kuka masa da yaransa, daman yanada  Labarin ciwon mahaifiyarta yasa aka fita da isa kasar waje aka duba lafiyarta sosai aka daurata a kan magani doctor yace zata warke Amma da kamar wuya, haka de zata kare rayuwarta ashan magani tin bata saba ba har tasaba yanzu. Tin Nabeelah na karama ta kulla a ranta bazatai Aure ba sbda larurar dake jikin mahaifiyarta, duk wata kudin da ake biyanta mahaifiyarta take turawa ake siyan mata magani in babu ita waze se mata? Ta tabbatar ko mijinta na Aure wata rana seya gaji , ita abun ya kama itace zata jure har abadan,Sam bata damuwa dukda tanada burin Aure Amma yanzu ta cire burinma a ranta,burinta ta kari rayuwarta a kulawa da lafiyar mahaifiyarta. Mahaifiyar Nabeelah cikakkiyar buzuwa ce sadakar yallah, mahaifin  Nabeelah  cikakken buzu ne shima Dan asalin niger aurensa da rukayya Auren zumunci ne, nabeelah ta gaji kyau gaba da baya,da wuya d'ana miji ya kalleta be sake kallanta ba,tin tana 20yrs maza ke kawo mata hari abokan Alhaji dake zuwa Amma sam taki,tunaninta in tai Aure waze kula da Ammahnta da kuma  Aeezad dinta, a halin ynzu sbda Aeezad ma bazata ita aure ba. Tin Aeezad na 2yrs ya fara zuwa makarantar islama data boko, shidin ya taso da hazaka Sam baya ko shekara a aji aje chanza masa class, yanada kokarin sosai yafi hafsat nesa ba kusa ba,. Tin tasowa Aeezad yakeda burin zama soja a rayuwarsa , Aiko da wannan burin ya ginu, yana gama makarantar primary yashiga makarantar secondary a makarantar sojoji, a Nan yayi karatu me zurfi, mahaifinsa yaso ya fita waje Aeezad yaki sbda baze iya tafiya ya bar Aunty nabeelah  ba, in yaje school har Allah Allah yakeyi yadawo gida yaganta,. A School suka hadu da Zaks, Nan suka dinke suka zama frnds na kut da kut, sede Zaks tin Yana karamin ya koyi nenan mata, domin school dinsu mata da maza ne, tini  Zaks yake kwakule yaran mutane, lokacin Aeezad besan komi ba shide romances kawai yakeyi ba ruwansa da shigewa gindin mata. A bangaren Alhaji sunusi har lokacin be Kara Wani Aure ba, seda babban Amininsa da Alhaji Abubakar suka matsa masa kan dole se yayi aure domin zaman haka ba aure ba daraja. badan Alhaji sunusi naso ba, yacema abokin nasa yasamo masa mace me nagarta wadda ta dace..." Alhaji hamza abokin Alhaji sunusi ya nufa gidan me dalilin Aure Nan aka basa photos dayawa idanuwansa suka hau kan Hajiya rafi'ah yaji ta kwanta masa a ido seyasha mutuniyar kirki ce sbda tanada fuskar mumunai, Aiko ya hadata da Alhaji sunusi, sukaje neman Aure a jahar daura , ita haifaffiyar yar daura ce,mahaifinta cikakken bakatsine Bashi da sana'arh data wuce wankin hulah da ita yake ci Yake ciyar da iyalansa matansa hudu yara talatin da uku, rabin yaran nasa mata ne kuma duk karuwai ne dasun samu namiji yadanse musu abun dadih to shikenan se su mallaka masa martabarsu, babbar yayarsuma batai aure ba tana can cameron tazama uwar karuwai,.   Rafi'ah na ciki daga manyan yan iskan yaran Audu, tin tasowarta takeda kwad'ayin Tsiya, Aiko tadinga bin Maza suna bata kudi, da kyar malam Audu me wankin hula ubanta yasamu tayi aure bayan yasama mata mijin Aure Wani babban amininsa, ta auresa tadinga gana masa azaba sbda bashi da kudi, bakin cikinta ya kashe mas'udu ,ya mutu ya barta da yarinya yar shekara goma sha biyu wato na'eema, a daddafe rafi'ah tagama takaba ta bazama yawon siyasa hadi da yawon bariki 2 in one. akwai wata babbar kawarta asiya itama bazawara ce.  ita tabasu shawarar su Kai photos dinsu gidan me dalilin aure shine suka Kai, cikin sa'ah  rafi'ah tasamu mijin Aure wato Alhaji sunusi.  Dukda Alhaji sunusi yaga talakawa ne  su rafi'ah na gidi, Sam be damu ba a tunaninsa ze samu kwanciyar hankali da ita. Aiko sati daya da Auren sunusi da rafi'ah komi na rayuwar Alhaji ya chanza,  rafi'ah ta kwaso Rabin danginta takawosu gidan daman tin randa aka kawota a matsayin Amarya taxo da yarta Na'eema wadda bata da kunya ko kadan idanta tsakiyar Kai, bata bin maza ammafa sam bata da tarbiya.  Tin Alhaji sunusi na magana a kan wasu abubuwan da rafi'ah  keyi  marasa kyau har yazo yadena mgnr ma baki Daya, rafi'ah ta shanyeshi tass be iya komi,gashi bata kaunar yaransa, sbda ta kula yana san yaransa.  Aeezad ne kawai ya zame mata kadangaran bakin tulu. Tinda zuwan  na'eema ta kyallara Ido a kan Aeezad tace ta kamu da Azababbiyar soyayyarsa, tin baya kulata harya dawo ya fara kulata,shima ya kamu da  Azababbiyar kaunarta,  zuwa lokacin tini   yazama soja shida Zaks sede shi Aeezad  ya fito da  babban mukami yafi Zaks, Asalin sunan Zaks (zakariyya),. Tin lokacin Aeezad na  tare  da Esther, da akasa ranar bikinsu da na'eema ne Aunty nabeelah ta matsa dole Aeezad ya rabu da Esther , itama se lokacin tasan suna tare da Esther din, Tasha fama sosai kafin Aeezad ya rabu da Esther. Esther yar asalin osun state ce, tanada tsananin kyaun fuska Amma sede a jiki bata da shape,  Aiki ne ya kai Aeezad can osun din suka hadu da Esther iyayenta nada kudi Allah ne kawai ya jarabceta da soyayyar Aeezad har tabiyosa garin Kano suka dinga sha'anin rayuwarsu kusan 1yr suna tare, Aeezad ne ya fara bare Esther a cikin leda. Yanajin dadinta  Sbda nabeelah kawai ya rabu Da Esther ta koma gidansu bayan sunyi kaca-kaca, a zuciyarta har yanzu bata bar sanshi ba, kawai ja da baya tayi tasan dole akwai ranar daze nemeta  ko ita ta nemeshi. Zuwa lokacin tini Hafsat yayar Aeezad ta gama karatunta na low ta hadu da Wani babban Dan kasuwa sukayi aure daman ta kosa ta rabu da gidan ubanta sbda ba dadih kwata-kwata Tin zuwan hajiya rafi'ah ta rikita gida, ta raba Sunusi da uwarsa ko gidanta baya zuwa, ta rabashi da Dan uwansa Daya tilo Alhaji Abubakar Wanda keda iyalansa yaransa hudu biyu mata biyu maza,, Sam Alhaji Abubakar be rabu da Dan uwansa ba duk yadda Rafi'ah taso su rabu abun beyu ba, time to time Yana zuwa da iyalansa gidan su gaisa ya tafi dasu, Sam baya damuwa da Amsar karnukan da hajiya rafi'ah ke musu, ita Sam bata kaunar taga kowa ya rabi gidan inba ita da danginta ba, kaf Yan uwanta Da kawayenta sun maida gidan Alhaji sunusi kamar gidan ubansu, hatta wanda yayi sanadin aurenta da sunusi wato alhaji hamza seda rafi'ah ta rabasu da sunusi .  A haka Aeezad ya Auri na'eema Daren farko kawai yasamu ya kusanci na'eema 2tyms,daga lokacin be kuma samun abinda yakeso ba kullum na'eema na gidan hajiya  mommy, hajiya mommy kuma liyafa taci gaba tini ta bude manya manyan kantuna wanda akeji dasu a garin katsina, ta shiga tura na'eema kasashe saro kaya domin ita hajiya rafi'ah bazeyu taje ba sbda ba boko, na'eema ce tayi karatu Sosai daman kuma kasuwanci ta karanta, itace a kan komi na kasuwancin hajiya rafi'ah ita bata San komi ba, ba Arabi ba boko, a haka itama na'eema take gina nata kasuwancin. Auren  Na'eema da aeezad  Ba abinda yasawa Aeezad se dumbin bakin ciki, ada bashi da wata damuwa seda ya Auri na'eema yashiga tashin hankali mara misaltuwa, nabeelah ce kawai ke bashi hakuri a kan  na'eema wallahi da tuni ya saketa, nabeelah tace wlhi inya saketa bashi bata, shine fa Aeezad ya shiga taitayinsa kawai yaci gaba da hkrin zama da Na'eema Amma fa Yana cikin bakin ciki, tin Yana 20yrs yayi Aure Amma Auren mara amfani, gashi ba halin yayi mgna se kallo kawai. Hajiya rafi'ah kuwa duk yadda ta kaiga San ta haihu da Alhaji sunusi, Allah beyi ba, ko bari  bata taba samu dashi ba,tabi bokayen harta gaji. 


A bangaren Hafsat ta haifi yaron farko yaci sunan Alhaji sunusi ake kiransa da Noor,  hajiya bilkisu tazo ta zauna da ita hartai arba'in, haihuwar ta biyu ce datayi tace a kawo mata Aunty nabeelah sbda hajiya bilkisu takuma tsufa sosai.  tinda nabeelah tadawo gidan bata koma ba, daman tagaji da zaman gidan hajiya rafi'ah, sbda kiyayyar da rafi'ah ke nuna mata ya shahara, ita ke kaf girkin gidan, sam bata kaunar taga nabeelah ta zauna,ta tsaneta tsana me tsanani,haka itama na'eema ta tsani nabeelah sosai, har marinta ta tabayi Aeezad ya rama mata, Aiko ranar ansha fada a gidan , rafi'ah tace dole se Nabeelah ta bar gidan Aeezad yace baze yuba,, da kyar akayi settling problem din. Nabeelah batayi karatun boko ba Amma tayi na islamiyya har ta sauke alqur'ani a gidan, Amma batasan komi ba a kan karatun boko ba sede ta iya hausa kadan-kadan, tana saving number  sosai Nabeelah takeson karatun boko tin tana karama Amma Allah be rubuta zatayiba. Sun taba zuwa da  Aeezad  kasarsu sau biyu ya rakata yaga mahaifiyarta wadda a ynzu tana iya komi da knta sede kullum cikin shan magani take, Aeezad ya yaba da dattako irin na mahaifiyar Nabeelah, Nan ya nemi madaidaicin gida yase mata a birnin niger ya zuba mata kayan Alatu, Ya Kaita unrah da hajji,.  murna gun nabeelah baze misaltuba, sosai kima da darajar Aeezad ta karu a kwayoyin idanuwanta, saboda darajar mahaifiyarta da Aeezad ke gani  yasa nabeelah Kara kaunar Aeezad tasawa ranta  itama insha Allahu wata rana seta biyasa da ALKHHAIRINSA  gareta, sede tasan har abadan ba wannan ranar saboda bata da abinda zata biya Aeezad dashi a rayuwarta. Sosai Nabeelah kejin dadin zamanta a gidan Hafsat, a fari de tasamu cikass ta yadda mijin hafsa ya fara nunawa  nabeelah so na aure, taki yarda da hakan,  shi kuma mijin hafsa  ya kamu da soyayyarta,yadawo yace ko bazata Auresa ba ta bashi kanta domin ya riga ya kwad'aitu da surar jikinta, a Nan nabeelah tashiga tashin hankali, daman  tin zuwanta gidan ta fahimci Baban Noor din nada neman mata, lokuta da dama in hafsa ta tafi Aiki har mace yake kawowa gidan su gama abinda zasuyi su tafi,  Sam nabeelah bata sanar da Hafsa ba, kuma tayi alqawarin bazata sanar da ita ba har abadan, shima kuma baban Noor din ya kula nabeelah nada sirri shiyasa har yake wannan iskanci, a karshe yadawo kanta wai ze aureta yaga babu nasara yadawo yana nemanta da iskanci, Aiko nabeelah tace wlhi in be rabu da ita ba zata sanar da matarsa komi, Sam baban Noor ko a jikinsa domin yasan da wuya kota gayawa matarsa ta yarda, sbda ya gama mata komi, be raketa da komi ba,shi mutum ne me rike gida sosai ko cokali hafsa bata taba siya ba a gidan shike komi, aiki datakeyi raayinta ne, Amma duk month seya mata salary ita da yaranta, akwaisa da kokari,  Amma sede yanada azabar neman mata,har yanzu kuma matarsa bata  Saniba, domin yana bata so da kauna be taba chanza mata a fuska ba daze nuna yana neman matan waje ba.  kalubalen Aure nada yawa, babu macen dake samun πŸ’― a dakin aurenta dole seta samu nakaso a wasu abubuwan sede Adduarh kawai yanayin mazan yanzu marasa control se hkri. Da Adduarh nabeelah tasamu ta kaucewa kaidin baban noor, amma fa har yanzu da kwad'ayinta a ransa,ita kuma nabeelah wannan shine kalubalenta nazaman gidan Hafsat gashi intace zata tafi hafsat zata dasa question mark a kan nabeelah, Dan haka dole ta jure daman ita damo ce sarkin hakuri, ba kasafai ka fiye gano damuwar taba, tanada dauriya da juriya. 

Gameson littafin namijin zuma da Namijin duniya ze biya 1500 a wannan account din 0542703718 Saadatu Abdullahi gT bank cantact 08101626484🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝

No comments

Powered by Blogger.