Najma 3-4


 👄👄👄👄👄👄

      *NAJMA*

💋💋💋💋💋💋

By maman noorul hudah


   🅿️3️⃣👄4️⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


       Tace"saude Wai Ina kike ne kina Jin yariyar Nan ta tada aljanai sunce kaza suke son ci ki fito ki leka d'akin  yusifa ya fito ya kamo a yanka"


        Umma ta fito tana danne dariyarta Wanda da k'yar ta iya yin Haka ta sauke idanunta Kan iya ba abinda jikinta yakeyi in ba rawa ba  kafin ta maida kallonta Kan uwani dake kwance idanunsa na had'uwa uwanin ta janye nata gudun umma ta b'ata Mata shiri,umma ta girgiza kanta ta saki wani murmushi wanan uban d'aurin gindin da uwani ke samu gun iya  take sheka ayanta inda take so 


    Sanin halin iya da Kuma ashar da ta Fara saki tana cewa mutum Dan kaniyarsa a ce yayi abu da jiki ya tsaya Yana b'atawa mutane lokaci ko sai jinin uwanin ya Kare an fa ce da jini suke amfani 


Jin Haka yasa uwani sake Mika straight ta Fara girgiza jiki tana cewa"a siya Mana Madara gwagwani pakmik(peak milk) da marina in ba hakan....


    Iya ta saki wani ihu tace"ohoho saude Wai sai sun ce in Basu Raina ne zakiyi Abu da jiki a Basu su ci ko zasu tafi duk munti d'aya in Kika b,'ata fah tambaya abubuwa zasuyi tayi 


Ummi ta Kara sauri ta buga kofar yusifa yana kwance Yana bacci ta buga kofar da karfi ya mike a firgice 


Tace"iya Wai ka Zo ka kama zakaranta uwani ta hau aljanu Kuma sunce 

Kaza suke so shine take son a Kama Mata 


      Rai b'ace ya kau da Kai yace"kowa fa  yasan yariyar nan  fa aljanun karya takeyi Amma sai ayi ta biye Mata haba umma Ina Jin dadin baccina a tashi ne Salan inyi ciwon ka....."


        Sake mika uwani tayi Jin abinda ya fad'a tace"a daina karyatamu ko muyi ba daidai ba 


Iya tace"wane mutum ai Babu Wanda ya Isa ya karyata .....Kai yusifa so kake in uanka ya dawo  yayi maka hukunci 


Mikewa yayi Yana kunkunin Yana fitowa ya kalli uwani Suka had'a Ido 


Tace"wal a daka yaji wal ci da kaza yaji Maggi Fara"


    Iya tace"yanzu yusifa zai daka yajin ai, uwar me yake in Banda baccin asara da Kuma zaman gulma 


         Cikin tsarewar gida yace"wallahi iya ban gan Wanda ya Isa ya sani in dakawa wanan yariyar yaji in banda ta maidaku gaulaye yariya tayi ta karyar aljanu Kuma ku hau Kuna biye mata"


       Iya zatayi magana uwani tace"Wal karki takura Masa dan bazai daka ba Wal mu zamu daka da kanmu ai da hanun mu"


     Iya tace"Kuma naku zaifi laushi kila ma ko sekan biyu bazakuyi ba ya daku Abu na jinnu Kuma"


Wanan gab'ar ko Saida umma ta kyalkyale da dariya 


Iya cikin seriousness tace"kull karki kuskura ba ayiwa jinnu dariya 


      Cikin kankanin lokaci umma ta fara had'a miyan had'adiyar kaza sai kamshi yake irin dahuwar su ta kauye me Romo 


Itako uwani tana gindi tabarya tana fama da yaji a wahalce  bashi da alamar dakuwa gashi a rayuwa Bata son harka da yaji dan ko Yaya ta tab'a jikinta sai taji zafi 


Iya ta kalleta ta gan idanan sunyi jajur tace"ya haka manya Baki Ina tunanin zaku Gama a cikin kankanin lokaci sai gashi har kazar ta daho ba labari 


        Uwani tayi wurgi da tabarya tace"Ina..... mu bamu son yaji"


      Ummadai kallonta take wani lokacin tana tunanin ko uwani Bata da Kai ne oho "


          Zama tayi a taburm yusifa dake zaune kofar d'akinsa rike da madubi ya saki murmushi yace"aljanai sunji maza ikon Allah 


          Bata kulasa ba tana zaune umma ta juyo Mata kaza a kwano ta kawo Mata daman iya ta aika Mata maltina 


Natsuwa tayi tana cin kazar sai kada Kai take kamar kadargaruwa  Saida tayi nak ta saki gyasa umma tace"toh zamu iya cin ragowar aljani?"


       Tace"lah lah a ajiye Mana anjima zamu ci"


      Iya tace"toh mu dai kamshi muka ji kenan baza a dan bamu mu maida y....."


Kallon da uwani tayi Mata ne yasa ta maida maganarta 

     


    Tana wanke hanun sai ga fareeda ta shigo da gudu tace"uwani Yana faruwa a hayi su deluwa suna can sun cakume juna suna dambe ke abin dadin kallo*


Ai ko takalmi Bata sa ba kamar giftawar aljan ta haye guntuwar katangan gidan ta tsallake  a guje 


   Iya ta saki salati Dan ko Dan kwali Babu kanta sai Kuma ta fashe da kuka tace"ya bazatayi ta Kama aljanu ba


         Tana gaba fareeda na binta a baya Kan kace me ta Isa hayin ta gan delu na maida numfashi ga malam sani gefensu alamun ya rabasu 


   Cikin daga murya tace"al'quran sai an sake haba dai bazanyi gudu a banza ba 


Malam sani ya dubeta suna had'a Ido ta kauda Kai tace"eh dambe Nike son a sake Dan ban gan ta farko ba 


       Yace"Baki da kunya in rabasu ki ce su sake ke wace irin shad'aniya ce?"


      Ta wani d'aure fuska cikin kunkunin tace



Please share 


Maman Nur

No comments

Powered by Blogger.