Makauniyar Kaddara 70


 Page 70 End😭🙏🏻*


...........Iya ƙokari Zinneerah yi take akan ganin zaman AK da Farah ya dai-daita, dan sai faman fushi yake har yanzu. Itama idan tai maganar sai ya hau fushin da ita. Ya hana taje ɗakinsa balle ta amshi girki. Gudun shiga haƙƙinta yasa Zinneerah riƙa ƙin zuwa

ɗakinsa duk bayan kwana biyu, zatai girki ta kuma gyara masa sashinsa amma bata yarda ta kwana ba duk iya masifar da zaiyi. Dan har cikin ransa haushin Farah da yakeji akan al'amarin nan yaƙi barinsa.

      Randa ya fahimci take-taken Zinneerah yayi mata faɗa kamar zai cinyeta, uffa batace da shiba saima kuka da taci. Washe gari sai ya tsiri tafiya Lagos. Kwanansa biyu ya dawo ran girkinta. 

      Duk da taji haushin hakan da yayi saita sharesa ta amshesa kamar yanda ta saba daya dawo. Takumabi hanyoyin daya dace ta bashi haƙuri da ƙara roƙonsa akan ya mance komai. A lokacin tana lafe jikinsa.

      Cikin lallashi tace, “Yayanmu nasan daga ni har kai duk an mana laifi, amma idan mukai haƙuri muka mance da komai sai ALLAH muma ya yafe mana kurakuranmu. Shi riƙo baida amfani, sai dai ya dinga zafafa zuciyar mutun da ƙuntata ta. Dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy nasan itama tayi nadama. Ka duba fa yanda aunty Farah ta canja tamkar ba itaba, tayi laushi fiye da zaton duk wanda ya santa”.

        Guntun tsaki yaja da yunƙurawa zai tashi tai saurin riƙosa ta sake naɗe masa a jiki. “Yayanmu Please mana, i beg you”. Ta faɗa cikin tsananin raunin murya.

     Dafe kansa yay da ɗan cije baki yana wani luu da idanu, aɗan hasale yace, “Wai ke miyasa bakison kiga mutum yana hutawarsa ne? Sai kin takura masa da silly zantukanki?. Idan ke zaki iya haƙura kamar bakisan ciwon kanki ba, ni bazan haƙuraba. Ban kasance mazinaci ba amma kullum ana haɗa kai da matata ana min rarraba da sperm a jikin wasu matan dama bansan su ba. Wannan wane irin son zuciya ne da yahudanci?”.

         “Duk nasan ba'a ƙyautaba My Heartbeat, amma Please kayi haƙuri tunda sun amsa laifinsu kuma sunyi nadama. Kodan rahamomi da UBANGIJI yay maka kashi-kashi ciki harda yinka musulmi mai imani daya yarda da ƙaddara da jarabawa. Ya azurtaka da dukiya badan kafi saura ba, ya kuma baka ƙyaƙyƙyawar zuciya da damar sarrafa dukiyar daya baka ta tsaftatattun hanyoyi da babu saɓon UBANGIJI a ciki, wannan ma ba dabaranka bace. Ya baka lafiya a jikinka baka kasance gurgu ba, makaho, kurma ko wani abu daban ba. Zakaji sautin kiran salla, kaji na karatun alkur'ani, kaga ayoyin alkur'anin, ka taka kafarka kaje massallaci, ka daga hannayenka ka roƙa UBANGIJI bukatunka ya ɗauka ya baka babu gajiyawa. Ya cika ƙwaƙwalwar ka da ilimin addini dana zamani danka iya shiga ko'ina cikin duniya babu fargaba. Ya baka nutsuwa da tarin hankali da mutunci ga duk wanda zai mu'amulanceka koda ya fika a shekaru. Ya azurtaka da mata har biyu da ƴaƴa a lokacin da bakai zato ko tsammani ba. Ya bama Baffah da Mammah da Granny tsahon rai kanata ganinsu kanajin farin ciki. Yayanmu duk waɗanan tarin ni'imomin basu isa susa ka yafema duk wanda yay maka kuskure ba koda yakai girman duniya? Haba Yayanmu kaifa shugabane a garemu kuma uba, duk abinda kayi dashi zamuyi koyi muda ƴaƴanmu. Wlhy aunty Farah tanada ƙyawawan halaye kawai anyi amfani da wani raunintane wajen ɗaurata akan hakan. Kai mata afuwa muma sai ALLAH yayi mana. Ka haɗamu ka runguma domin gidanka ya zama tsintsiya ɗaya maɗauri ɗaya. Kagafa yanda take jan su Anam jikinta da soyayya irin ta uwa da ƴaƴa batare da nuna damuwa ba. Ina kishinta dan nima mace ce kuma inason mijina, amma wlhy ina sonta tunda har taso jinina”.

    Ta ƙare maganar hawaye na silalo mata. Sake matseta yay a jikinsa yana bata wasu hot kissis data ƙara tabbatar da yes itama takai mace kuma abinso ga mijinta kuma ɗan uwanta uban ƴaƴanta. Cikin jin daɗin hakan ta sake bashi haɗin kai ya kuma tabbatar mata da ita ɗin mai darajace ta gaske a garesa.

     Koda suka kimtsa jikinsu baice da ita komaiba itama batace da shi ba. Dan tasan idan miskilancin yay miskilanci toshi baya magana da baki sai dai a aikace. Murzar da yay mata yanzu kuma itace amsar komai da furucin bakinsa gareta. Itama hakan ya wadatar da ita dan maimaita maganar bashi da wani amfani ko alfanu sai maida hannun agogo baya.


        Tun daga ranar ta tattara zancen shirinsa da Farah ta watsar da su gefe kamar bata fahimtar komai. Daga ƙarshe ma cemasa tai ita Danya ma take son zuwa sake duba jikin inna dan duk ƙarshen wata sai sunje dama har da shi da yaran.

    Banza yay mata akan hakan tamkar baijiba har tsahon kwanaki da sukai ɗanyi shariya da juna ita da shi itama. Sai kuma suka koma dai-dai.

    Bata sake masa maganar Farah ba ta zuba musu na mujiya. Tun suna fishe-fishesu har dai takai sun shirya batare dama ta saniba. Sai ganinsu tai ana shimfiɗa shika-shikan soyayya ko kunya babu. Duk da tanajin kishi a ranta haka ta danne ta kauda ido dan karatunta na islamiyya data koma cinye mata kaso mafi yawa na zaman gidan da rana yanzu, ga kuma su Saliha da mama A'i na ɗebe mata kewa sosai.. Dama tunda Farah ta dawo gidan ta canja salon girkin gidan kwana bibbiyu, randa taƙi zuwa garesa yay masifar yay faɗan sai dai ta bashi haƙuri kawai tace ga aunty Farah nan.

        Sai gashi tsakanin miji da mata sai ALLAH sun ɗinke abinsu batare data saniba. Duk da tanajin kishin mijinta haka ta cigaba da ƙoƙarin ganin ta danne kamar yanda itama Farah ke ƙoƙarin dannewa a yanzu, suna kuma girmamawa da mutunta junansu duk da ta girmeta nesa ba kusaba. 

        Ya zaunar dasu ya musu nasiha sosai da shimfiɗa sabbin dokoki masu tsauri a garesu. Dukansu sun amsa masa da alƙawarin kiyayewa insha ALLAH.


         Tun daga nan zaman gidan ya canja salo, duk da sunajin kishin junansu haka suketa dannewa kowacce tana nuna bajintarta akan kulawa da shi da saka shaƙuwa tsakaninsu. Ashe Farah har girki ta iya iskanci ke hanata yi ko a baya. Sai gashi yanzu ta zage tanayi, tarema suke haɗuwa suyi dan haka baka iya banbance girkin wance ne inba ka ganta a turaka ba. 

         AK ya ɗaukesu zuwa Family house Farah ta ƙara neman gafarar su Hajiya iya. Inda acanma dai nasihar aka sake musu daɗi kamar ya halaka Mammah. Gata ta dawo gidan aurenta ga ƴaƴanta duk suna cikin kwanciyar hankali a gidan nasu auren, ga kuma ƴan jikokinta dan Adilah ma ta haihu. Itama har nasiha tai musu mai ratsa jiki da roƙonsu su haɗa kansu kar taji karta gani, su duka ƴaƴantane bazata fifita wata akan wataba.

      Sunji daɗin hakan sun kuma mata godiya.


     Ya kuma kaisu gidan mmn sadiq data nuna jin daɗinta sosai itama da dawowar Farah ɗin. Dan dama kullum itace ke ƙara ɗora Zinneerah a kan taita lallaɓasa har matarsa ta dawo su haɗa kai su zauna lafiya. Karta yarda ya guji matarsa akan laifinta itama wataran idan tai masa kuskure koda ba irin wannan ba zai iya gudarta. Dan duk abinda namiji ya ƙware wajen yima matarsa ta farko ke amarya kikaji daɗi har kika zuga ya ƙara fusata kema wataran sai ya aikata miki fiyema da wanda yay mata. Itama kuma ta musu nasiha ta kuma karɓi Farah hannu biyu kamar komai bai faru ba, Farah ɗinma kuma ta mutuntata da gurfana a gabanta ta nema gafararta.

      Mmn sadiq tace karta damu komai ya wuce wlhy ALLAH dai ya kiyaye na gaba ya ƙara musu zaman lafiya da haƙuri da juna. Dan shi kishi tamkar jinin jiki ne ga mace, sai dai idan ta iya sararafashi zataci riba a duniya da lahira. Zafafa kishi a zuciya babu abinda yake haddasawa sai ƙunci da tarin baƙin ciki da kaucema dokokin UBANGIJI batare daka fargaba. Kaɗan daga aikin kishi ya ɗoraka a hanyar zuwa wuta ya sakeka a ciki ya kama wani kuma. Amma daka iya sarrafasa sai gaka ka tsira da mutuncinka da farin cikinka. Ka kuma zama tauraro ga mijin ga kowama, duk mai son ganin bayanka sai dai shi ya wahala kaiko ALLAH yayta ɗaga darajar ka.

     Sunji daɗin nasiharta sosai sun kuma mata godiya su duka. Dan shi kansa AK daya dawo ɗaukarsu yanda ya samesu sunata wasa da dariya sai hakan ya ƙara masa farin ciki dajin ƙaunarsu. Ya dinga kashesu da salon looks nashi da duk yake rikita manyan mata sujisu suna sake dulmiya a tarin sonsa da ƙaunarsa.


      Daga haka rayuwa ta cigaba da turzawa. AK na ƙoƙarin gina adalci a tsakanin matan nasa. Duk ƙwaƙwƙwafinka baka isa banbance wayafi so ba. Ya bar wannan sirrin a ransa da ga shi sa UBANGIJIN daya haliccesa. Idan saɓani ya shiga tsakaninki da shi bazai taɓa yarda ya wulaƙantaki gaban ƴar uwarkiba sai dai kuyi abunku ku kashe ku rufe ke da shi a ɗaki. Ku kuma shirya batare da kowa ya sani ba. 

      Idan a tsakanin saune saɓanin ya shiga tunda yau da gobe sai ALLAH sukanyi ƙoƙarin ganin sunyi saurin fahimtar juna kafin abin yay musu zurfi.

      Su Anam gaba ɗaya saboginsu ya koma sashen Farah saboda jansu da take a jikinta. Little ne dai duk yanda taso ya sake da ita yaƙi. Komai zakaga yana yinsa a ɗarare indai tana a waje. Kuma babu abinda take masa mara ƙyau sai ma sakin fuska da ganin ya saki jikin da ita, amma hakan ya gagara. Takansha kukanta a ɗaki da godema ALLAH. Wani lokacin idan AK ya gani ya lallasheta da nuna mata ƙuruciyace kawai ke damun little ɗin zai daina wataran.

       Takance ita badan wani dalili take kukanba dan har ranta ta cire kallon little daga wani sashe na jikinta. Hundred percent kallon jinin Zinneerah kawai take masa. Amma koyaya tanason ya dinga sakewa da ita kamar su Anam.

    Itama Zinneerah abun na damunta dan kulum cikin yima little ɗin nasiha take amma abu ya kasa ƙarewa duk da dai yana ragewa Alhmdllh.


      Yaye su Amaan Zinneerah tayi dan zata fara karatunta da AK yay alƙawari. Sai dai kuma ya fara mata zancen samun ciki tana zillewa dan ita tasan wahalar data sha. Ganin yanda take zame-zamen ma ya fara faɗa ko wani abu tasha akan hakan.

      Rantsuwa ta dinga masa ita batasha komaiba wlhy ALLAH ne dai bai kawo ba, tunda yanzune ma fa ta yaye su Anam ai. Badan ya yardaba ya barta. Amma dai yace zai ƙara himma yaga ƙaryar zame-zame.

    Ita dai dariyace kawai tata dan bata da abin faɗa kuma.


      Rayuwa ta shuɗa abubuwa da yawa sun faru wasu sun canja. Su Sa'a dasu Adilah, Raheena matar Khalipha tuni sun hahhaihu. Hakama ansha bikin su Bahijja dasu Moos'ab. 

       Zinneerah ta dage da ƙyar ta ƙara santaloma AK ƙyaƙyƙyawar budurwa data ci sunan Mammah. Sai dai yasha mita suna mata dariya shi da Farah akan saura shidda ya rage ta ciko musu tunda bakwai ne a lissafi. Baki ta dinga kumbura musu da cewar ita wajen Granny zata koma tunda basa sonta. Aiko suka sami abun tsokanarta daga shi har Farahn da itama a yanzu ake shirin mata aikin mahaifarta saboda cigaba da aka samu akan masu matsalarsu. Fatansu kuma ALLAH yasa a dace.

     Dan yanda takema su Anam saita baka tausayi. Gaba ɗayama yaran yanzu sun koma hanunta. An barma Zinneerah Little da mai sunan Mammah da suke kira Nu'aymah.


    Anyi aiki kuma Alhmdllh an dace. Dan ƴan watannin da Farah ta ɗauka na jinya sai gata ta warke sarai kamar ba'ai mata komaiba, ta koma normal rayuwarta da fatan ALLAH ya kawo rabo mai albarka. Dan AK ya dage ba wasa. Addu'arsa kullum ALLAH yasa su harbu su duka dan shi fa ƴaƴannan basu gama isarsa ba.

    Bayan kusan watanni takwas da aikin saiko gashi andace Farah da ciki. Zokaga murna wajen ƴan uwa da abokan arziƙi tare da uban gayya AK. Nanfa suka shiga bata kulawa da tattali dan cikin nata mai laulayine sosai tana shan wahala. Da yawan nauyinta sai ya dawo kan Zinneerah. Ga karatu ga yara dan ma akwai mama A'i da Saliha a gidan. 

     Haka a ka dinga cuɗawa cikin amincin ALLAH har ciki ya shiga watan haihuwa ta haihu lafiya ƴarta mace ƙyaƙyƙyawa mai kama da sauran ƴan uwanta. Zokaga murna wajen su Amaan anyi ƙanwa, har iyayi sukema little da suke kira da big bro waisu an musu ƙanwa. AK da Zinneerah kanyi dariya, yakance, “Mami to gaskiya kema ki dage ki cikoma big bro sauran shidansa, dan nima su naketa jira fa”.

     Duk sanda ya faɗi haka sai tace, “Ka rufamin asiri Yayanmu ga Momy nan tayo ɗaya ita zata cika mana sauran biyar ɗin ai”.

         Farah kuwa ta karɓe da “Uhm-Uhm Mami ƙarasa biyar ɗin nan wlhy akwai wuya kece da biyu, ni nawa ukun nan sun isheni. Amaan, Anam, Manha”.

      Baƙaramar dariya suke mataba akan hakan, dan gaskiya tasha wahalar cikin nan sosai, musamman ma a wajen haihuwarsa kamar bazata kai ba.


      Ƴan uwa da abokan arziƙi nata tururuwar zuwa har ranar suna.

    Ƴan katsina dasu Mammah sun cika gida fam ansha shagali, itama dangin Zinneerah sunzo Alhmdllh dan zuwa yanzu kam an zama ɗaya sai haƙurin yau da gobe. Dan itama Farah ɗin tasha zuwa Danya musamman akan duba Inna da har yanzu aketa ibadar ALLAH na jinya. Yarinya taci sunan Mahma Zaliha. Za'ake kiranta Manha.

    Tunda abin nan ya faru sai a sunan nan Zinneerah ta ƙara ganin Aunty Zakiyya. Tanata ɓoye-ɓoyen karsu haɗu dan kunya. Ita Zinneerah ma saita bata dariya. Ta shirya da kanta ita taje ta sameta aka gaisa.

       Ansha suna an shashshare dan walima kawai akayi tamkar sauran ƴaƴansa. Aka bar su Zinneerah da zaman gyaran gida da barcin gajiya. 

      AK na jera kalmar Alhmdllhi da wannan ni'imomi na samun haɗin kan zuri'arsa da yayi. Fatansa kawai ƙarewa da rayuwa lafiya tare da samun ƙwarin gwiwar bama ƴaƴansa tarbiya har lokacin data ALLAH zata kasance akan kowannensu.✍😭🙏🏻


*_TAMMAT BI HAMDULLAH_*


_To nima dai bara na dakata da alƙalamina a nan, kuma ku huta dan ansha fama. Abinda na rubuta dai-dai ALLAH ka haɗamu a ladansa. wanda nayi kuskure ALLAH ka yafe min daku masu karatu baki ɗaya_.


*_LITTAFI nishaɗi ne, faɗakarwa ne, tunatarwa ne, ilimantarwa ne. Idan kayi gamo da faɗakarwa ɗauki ka amfana gwargwadon iyawarka, idan kaci karo da tunatarwa ɗauki ka amfana gwargwadon fahimtarka, idan kaci karo da ilimi a ciki, ɗauka ka amfana gwargwadon nazarinka. Idan kaci karo da nishaɗi, tabbatar ka tace shi ka rairaye koda ace zaka iya kwatantashi a zahiriyyarka. Idan nazarinka ya baka mai cutarwane barsa a nan inda ka-gansa nishaɗine kawai ba lallai saika sakama zuciyarka ba. dan babbar matsalar masu karatu. kunfi ɗaukar nishaɗi ku fifitashi a littafi ko ku ƙalubalanci marubuci da shi, ko aiki dashi. Sannan ku kuma kunmafi kowa son ganin nishaɗin a littafin fiye da duk sauran abubuwa masu ma'anar. Ƙalilanne a cikinku sukafi yarda da ilimi, faɗakarwa, tunatarwa da makamantansu, amma ƴammatan nan namu (kuyi haƙuri) ku daina sakama ranku tunanin rayuwar novels da wasu abubuwan nishaɗin cikinsa a zukatanku da tunanin samun irin rayuwar. Kisa a ranki ALLAH ya baki miji nagari mai addini dazai kwatanta miki rayuwa mai albarka agidan aurenki ba nishaɗin hikayoyin marubutaba. Sai dai kamar yanda kuke tunanin babu rayuwar novels ko yanayin jin daɗin cikinsa a zahiri wlhy akwai, akwaima wanda suka ninka rayuwar novels jin daɗi da nishaɗi a cikin gidajenmu, sai dai basu da yawa. Masu shan wahalhalun gidan aure sun rinjayesu. Mata ku ƙara haƙuri, kuyi haƙuri kuyita haƙuri. Idan baki samu hakanba karki damu, ki nutsu wajen ibadar ALLAH dan aure ibadane. Wata rana sai ALLAH yay miki sakamako da abinda yafi duk wannan jin daɗin da kika rasa. Dan duniya zaman wucin gadine. Kowa burinsa samun aljanna maɗaukakiya. (ALLAH ka sadamu da aljannarsa musami farin ciki mai ɗorewa na har abadan acan😭🙏🏻)._*


*_YA rabbi ka gafartama mahaifina, ka yafe masa da dukkan ƴan uwa musulmi da suka rigamu tafiya. ALLAH yasa ranar mutuwarmu ta zama ranar farin cikinmu, ALLAH ya ƙara mana tsoronsa a zukatanmu da soyayyar MANZON ALLAH (S.A.W)😭🙏🏻_*


_Duk wanda naima kuskure a yayin rubuta littafin nan ya gafarce ni, dan ban saniba ko shine littafi na ƙarshe da zan rubuta a rayuwata. Nima na yafema kowa waɗanda suka saya, muka kasance tare dasu a inuwa ɗaya, kuma suka cika alƙawarin ƙyautata mana basu cutar damu tako wata hanyaba. ALLAH ka ƙara mana haƙuri da juriyar zaman tare. mun gode, mun gode, mun gode ƙwarai da gaske da ƙoƙarin haƙurin bibiyarmu da kukayi. Zafafa biyar basu da bakin nuna muku farin cikinsu sai dai muyitama juna fatan alkairi har ƙarshen rayuwa🙏🏻😭_.


*_ZAFAFA biyar na sake muku bankwana a karo na ƙarshe, tare da bangajiya sai mun haɗu a ZAFAFA BIYAR 2K22 insha ALLAHU_*.


Ƙauna irain trillions ɗin nan. Dan kuɗin na dabanne, idan nace na daban ina nufin nadaban har acan ƙasan zukatan ZAFAFA BIYAR😉🤗🤗😁😁😍😘😍😘😍🤗🤗🤗🚶🏻.



      _Idan kunga kuskure a rubutunmu Please kubi ta ƙyaƙyƙyawan hanyar nusar damu, insha ALLAH zamu duba, zakuma mu gyara, hakan da zaku mana shine ƙauna🤗._


   

No comments

Powered by Blogger.