Makauniyar Kaddara 65


 Page 65*


............Ganin dare ya fara yasa Hajiya Iya tada Zinneerah, shima AK taje ta tasoshi akan suzo su wuce gida haka nan. Badan Zinneerah taso hakanba ta miƙe, shima AK ɗin ya fito yana faman dafe kai. Kowa bai kallaba a falon yay ficewarsa duk da yasan

akwai su Mammah zaune. A waje ya samu su Haneef da little a hannu, aiko ya maƙale masa. Amsarsa yay suka shiga motar da Khalipha zai jasu dan shi bazai iya tuƙinba. Zinneerah ma da Hajiya iya ta rakota dasu Meenal ta shiga baya.

            

         Koda suka iso Khalipha ne ya buɗe musu ƙofar falon, daga haka ya juya yana musu sai da safe. AK ya ɗauka Little suka wuce sashensa batare daya kula Zinneerah ba. Itama ɗin ba kulashi taiba ta shige nata sashen. (Faɗan masoya hutu😂😝).

        Ko wanka kasa zamanyi Zinneerah tayi, tana shiga gado ta faɗa tai kwanciyarta dan barcin tafi bukata. Musamman daya kasance maganin da Granny ta bata yana saka barci.

    Shima a ɓangaren AK kwantar da little dayay barci tun a mota yayi, ya samu yaɗan watsa ruwan yasha tea dan yanajin yunwa, duk yinin yau ya gagara sakama cikinsa abinci, basket ɗin abincin da suka bari a gidan tunna safe ya ɗauka ya bubbuɗe. jin babu abinda abincin yayi ya sashi ɗauka ya fita dashi ya kaima maigadi yace ya badashi kar ai asararsa. Daga haka ya dawo shima yay kwanciyarsa bayan yaɗan leƙa Zinneerah yaga harma ta kwanta. 


*_WASHE GARI_*


      Da safe sun tashi Alhmdllh, musamman Zinneerah batajin ciwon komai a jikinta. garama AK dai jikin nasa sam baya masa daɗi. dan ko sallar asuba a gida yayi abunsa ya koma ya kwanta. Sai kusan ƙarfe bakwai da little ya farka yana damunsa ya miƙe da ƙyar ya ɗakkosa gaba ɗaya yayo sashen Zinneerah da shi. A lokacin tana cikin saka turaren wuta dan ta gama gyaran ko ina. 

      Sanye take cikin wando da riga na kayan barci farare tas, yanda suke da santsi yasa suka manne mata a jiki sosai, gashi ko bra babu a jikinta. Kallo ɗaya yay mata ya kauda idanunsa, itama cike dajin kunyar yanda ya sameta dan batai zaton shigowarsaba takai ƙasa tana gaidashi cikin girmamawa batare da ta yarda sun haɗa ido ba. 

     Amsa mata yay a daƙile yana dire little kusa da ita dan haushinta yakeji, har itace zata buɗe baki tace zata barsa saboda wasu. Wannan magana tai masa ciwo, tanama cikin masa ciwon. Juyawarsa yay ya fice ta bishi da kallo zuciyarta na raya mata yana fushine saboda matarsa da aka wuce da ita. Haka kawai sai taji ranta ya sosu. Ta ɗan taɓe baki tana miƙewa da ɗaukar little ɗin dake mata ƙorafin shi tea zaisha.

      “Dalla yima mutane shiru abinda ka iya kenan sai cin tsiya kamar ubanka”.

        Kuka ya sanya mata saboda dungure kansa da tayi. “Malam yimin shiru ALLAH kona huce a kanka”. Daga haka ta ɗaukesa suka nufi ciki dan ta masa wanka sannan tazo tanadar musu abinda zasuci dan tacema Granny abar kawo musu abinci zata fara girki.


       Wanka tayi masa itama tayi sannan, tura little tayi wajen AK ya amso kayansa, ita kuma tai ƙoƙarin shiryawa a gurguje ta fito. Sai da ta haɗa ma little tea ta fara nema musu abinda zasuci yanda bazata takura ba. Harta gama bataji ɗuriyar little mai kukan yunwaba, hakan bai dametaba dan tasan wani abun ya samu acan.

      Kamarko ta sani dan AK na gama saka masa kaya tea ɗin ya haɗa masa da ruwan dispencer, ya haɗa masa da biscuits. Shima wankan yayi dan yanason yaje asibiti kar abin yay masa nisa. Koda ya fito wankan rashin ƙarfin jikin ya sakashi sake komawa ya kwanta har takai barcin ya sake figarsa. 

       Lokacin da Zinneerah ta shigo falon da kayan abincin little kawai ta samu a falon ya barbaza filos ɗin kujera yayma falon kaca-kaca. “ALLAH ya shiryeka” kawai ta iya cewa ta ajiye abincin a dining. Kayan shara ta ɗakko ta fara a tunaninta AK yana wani abunne a ciki. Waje ɗaya ta saka little zama harta kammala kimtsa falon tasa turare. Ganin har lokacin shiru babu motsin dadynsa ga goma harta gota ya sata nufar bedroom ɗin a ɗarare danta sanar masa ga abinci. Kusan sau uku tai sallama babu amsa. hakan ya sata tura ƙofar ta ɗan leƙa kanta a tunaninta koma dai baya gidan ne.

       Zaune ta hangosa a bakin gado dan dai-dai ya tashi kenan saboda sallamarta. Hannunsa dafe da kansa dake masa tsananin ciwo. Jitai tamkar ta juya da baya dan da ga shi sai boxer ne, amma ganin yanda ya dafe kansa yasata tunanin ba lafiya ba. tunda jiya dai ga a yanda suka dawo su duka, kuma tanaji sanda yake sanarma Khalipha kansa na masa ciwo a jiyan.

        Kanta a ƙasa ta ƙaraso cikin ɗakin, sai da tazo kusa da shi sannan ta rissina tana gaishesa batare data sake yarda ta kallesa ba. A yanda ya amsa ɗin kuma sai tsoro ya sake kamata, cikin damuwa tace, “Yayanmu baka da lafiya ne?”.

      Shiru kamar bazai amsaba har kusan mintuna biyu sannan ya ɗago idanunsa da sukai jajur yana dubanta. Kwalliyar tata tayi masa ƙyau, dan haka yaɗan lumshe ido ya sake buɗewa a kanta da cewa, “Kaina ke ciwo. Haɗamin ruwan wanka inason naje asibiti”.

           Sosai damuwa ta bayyana ƙarara a fuskarta. ta shiga jera masa sannu kamar zatai kuka. Shi dai kallonta kawai yake dan duk da yana cikin halin ciwo yanda takeyi ɗin tada masa tsigar jiki take. Ga mayatattun turarurrukan ta da ƙamshinsu ke ɗaga masa hankali zuwa ga buƙatarta.  Ya ɗan cije lips ɗinsa yana komawa da baya a saman gadon ya ɗan kwanta kafin ta kammala haɗa ruwan.

     Sai da ta tsaftace masa toilet ɗin duk da ba wani uban datti yay ba sannan ta haɗa ruwan, ta fito hanunta da tissue data warwaro daga can tana gogewa. Da ƙyar ya iya yunƙurawa ya tashi zuwa bayin.

       Ta ɗan sauke numfashi da fara ƙoƙarin gyara masa gadon, daga haka ta zarce da tsaftace ɗakin gaba ɗaya. Ɗan jimawa da yake a wanka yasa harta kammala kafin ya fito, tana fesa fresheners take jiyo little na ƙwala mata kira daga falo. “Aunty! Aunty!!”.

       “Oh ALLAH! Na'am”. Ta faɗa tana ajiye gwangwanin freshener ɗin. hakan kuma sai yay dai-dai da fitowar AK daga bayi. Bata yarda ta dubesaba, sai sake amsama little kiran da yake mata tayi. Ta ɗaga ƙafa zata nufi hanyar fita taji an ruƙo mata hannu. cak ta tsaya dan tasan dai shine.

        “Idan kin tafi wazai shiryani”. Ya faɗa a hankali yana jawota ta juyo tana fuskantarsa. Kasa kallonsa tai dan dagashi sai guntun towel. Ganin yanda taketa sinne kai ya ɗago fuskar tata da ƙoƙarin saka idanunsa cikin nata. “Nazama surukinki ne?”.

       “A'a” ta faɗa a hankali tana ɗan murmushi. 

        “Hum” ya faɗa da kama hannunta yajata suka ƙarasa gaban mirror ɗin. Duk yanda taso zamewa dole tabi umarnin sa. dan dolenta ta shafa masa mai da kanta, ta kuma ɗakko masa kayan da zaisa wanda bazai takura ba. A gaɓar shiryawane dai kam ta kasa duk yanda yaso dole ya barta ya shirya da kansa.


     Falo suka fito a tare suka sami little, baiyi tunanin ita tai girkinba, sai dai ya masa daɗi, kaɗan yaci yau kam dan da gaske bayajin daɗi, yana gamawa ya koma falo ya kwanta cikin kujera saboda jiri, wayarsa yace ta ɗakko tai kiran Doctor Mahmud yazo ya dubashi, dan bama zai iya driving ba. Cikin damuwa ta ɗakko ta lalubo masa no ɗin Dr Mahmud ɗin, yana ɗagawa ta miƙa masa wayar yay magana da shi.


       Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga Doctor Mahmud da Khalipha tare. Bayan ta gaisa dasu ta bar musu sashen saboda kallon da AK ke mata na gargaɗi dan ko mayafi babu a jikinta yau. 

        Koda ta koma a can tai zaman karyawa itama. Bata sake leƙo sashenba sai da little yazo ya kirata. Hijjab ta zunbula dan hanyar lafiya a bita da shekara. Khalipha kawai ta samu tare da shi sai Huzaifa da batasan da zuwansaba. Ta gaisa da Huzaifa daketa tsokanarta da amarya amarya. Ita dai murmushi ne nata kawai babu bakin ramawa.

    Ta ɗan dubi AK da akema ƙarin ruwa idanunsa a lumshe. Sannu tai masa dan ta fahimci idonsa biyune, saboda riƙe yake da hannun little dake tsaye gaf da fuskarsa yana masa maganar da batasan kota micece ba. Khalipha ne ya sanar mata abinda zatayi, dan haka ta juya ta sake fita ta barsu.


           ★*********★


Abu kamar wasa sai ga AK yasha zazzaɓi kwana biyu, dan sai da takai har Baffah da Uncle Ahmad sai da sukazo dubashi, hakama su Mammah dake shirin komawa gobe idan ALLAH ya kaimu sunzo sun dubata da sake neman gafarar Zinneerah. Yanda Mammah taketa tattalin Little sai ta baka tausayi, gashi shi saima wani ƙiwan wulaƙanci yaketa faman mata. 

     Shima AK ɗin sun ƙara masa nasiha da nuna masa muhimmancin yarda da ƙaddara. Mammah ta sake neman gafararsa duk da ta fahimci fushi yake da ita. Nuna mata yay shifa komai ya wuce, amma ita tasan bai wuce ba tunda ya kasa sakin jiki da kowa sai ɗansa da matarsa.


        Yau Alhmdllh ya tashi jikin nasa da sauƙi sosai, dan har fita yay zuwa gidansu shi da little. Bayan sallar la'asar Zinneerah na falonta na biyu zaune tana cire ƙumba ya shigo da sallama. Gaidashi tai da masa sannu da dawowa. Ya amsa mata yana kaiwa zaune. Ita kuma ta miƙe dan kawo masa ruwa. Amma sai jitai ya ruƙota. Duk yanda taso zamewa ya hanata damar hakan. Cikin wani irin kasalalliyar murya yake mata magana a kunne. “Wace irin amaryace wannan mai rowan tsiya nikam?”.

        Ɗan dubansa tai dan bata fahimci ina ya dosaba, ya ɗage giransa ɗaya yana kasheta da kallonsa mai sakata nutsuwa. Itama dai yau tayi dauriya da jarumtar kallon nasa cikin idon, da wannan damar yay amfani wajen ɗora lips ɗinsa kan tausasan nata. Sukaja numfashi a tare da lumshe idanunsu. Sai gata luff ta nutsu tana amsa saƙonsa. Sai da labarin ya fara canja salo kuma ta nema raina kanta. Ko saurarenta baiyiba ya ɗauketa cak yay cikin bedroom ɗinta da ita. Ganinfa irin na ranar yake son maimaitawa tuni ta fara tsuma da neman roƙomsa shikam baima jinta ya antaya duniyar kodumo.


      Duk yanda taso daurewa yau ma dai kasawa tai, sai da ta kaita da masa kuka, dan wannan yayan nasu bana wasan yara bane, baisan sauƙi ko sassauci ba har sai ya kai boader.

     Sai da ya ga ya samu kansa ya koma tsokanarta da suna ragguwa. Ita ko ta dinga tura baki har a wajen wanka da ya taimaka mata ta kuma gasa jikinta yanda zataji daɗi. Suna fitowa ya gudu sashensa dan kiran sallar magrib ake tayi.


      Bata sake ganin ƙeyarsa ba sai bayan sallar isha'i, ta fito domin nema musu abinci shi kuma ya shigo hannunsa ɗauke da leda alamar ya biya ta ɗakinsa kafin yazo nan. Zama yay da kiran sunanta, dan haka ta nufosa zata zauna ƙasa ya nuna mata gefensa. Sai da takai zaune sannan ya miƙa mata ledar. Amsa tai tai godiya duk da batasan minene a cikiba, tana buɗewa taci karo da waya mai ƙyau. Ai tuni jin daɗi yasa ta manta da Yayansu ne fa. Ta miƙe ta ɗane masa jiki tana murna.

           Murmushi yalwace da fuskarsa ya karɓe abinsa yana cusa kansa a wuyanta. “Yanzu kin ɗaneni, da an taɓaki kuma ki hau yima mutane raki”.

     Kanta ta cusa a ƙirjinsa tana dariya da faɗin “ALLAH akwai wuya Yayanmu, kai dan baka sani bane”.

     Dariya ta basa, amma sai baiyiba ya cigaba da murmushinsa yana cusa hannunsa cikin gashinta, “Ni kuma gashi ba wasa zan tsayaba ƙannen little nakeso da wuri, dan naga shikam ba barmana zasuyiba haka zai ringa yawo tsakanin danya, gidan Abba, gidan Baffah, london. Kinga saiki sama mana namu muma”.

      Ƙwaɓe fuska tai cikin marairaicewa. “Yayanmu ba yanzuba akwai wahala wlhy”.

     Kansa ya ɗan girgiza mata da sumbatar lips ɗinta. “Haba my Neerat ai ke jarumace tunda kika haifo Abdul-Mutallab tun kinada shekaru sha huɗu, yanzu kam ko ƴan huɗu ne zaki iya ai”.

       “Sai dai in zaka tayani”. 

Ta faɗa tana ɓoye fuskarta a jikinsa. Sosai yanzu kam ya ƙyalƙyale da dariya. “Mizai hana na tayaki nikam Mrs Shira, ai tare zamuyi rainon cikin muyi naƙuda abunmu mukuma rainesa idan ya fito”.

    Dariya sosai Zinneerah keyi itama mamaki fal ranta na Yayansu. Ashe haka yake da sauƙin kai da sakin jiki, amma yayta musu mazurai a gida.


        Washe gari suna kammala breakfast yabar gidan zuwa jigawa. Da wannan damar ta samu zaman gyara gidan sannan tai zaman kiran ƴan uwa da abokan arziƙi data samu nombobin wasu a wajensa. Wanda bata da shi mmn sadiq ta tura mata da su hajiya iya. Ƴan danya ne ƙarshen kira. Inda tai farin ciki matuƙa dajin muryar babanta. 

      A wayar tasune yake sanar mata shagalin suna da za'ai gobe idan ALLAH ya kaimu. tare da abinda ke faruwa akan Karima na zancen sarƙa data sata acan Kaduna aka kaita kotu, a yanzu kuma babu sarƙar babu kuɗin ga Babawo ya saketa saki har uku. Ya ɗora da faɗa mata halin da Inna take a ciki da zancen cikin Tinene. Harma da wanketan da mai martaba yaje yayi har danya bayan sun bar kano tare.

       Zinneerah tayi kukan daɗi tayi na damuwa tayi na baƙin ciki a wannan yinin. dan har AK ya dawo daga jigawa a jigace ya isketa. A kallo ɗaya ya fahimci damuwar dake tare da ita. Baice mata komaiba harta taimaka masa yay wanka yay zaman cin abinci, sai da ya kammala yaje sallar magrib da isha'i ya dawo sunyi zaman kallon labaran dare ya tambayeta. Da farko tata noƙewa akan ƙin faɗa ya nuna ɓacin ransa. 

       Kuka ta fashe masa da shi ta shiga basa labarin abinda duk ya faru. Shima yaji daɗin abinda maimartaba yayi. yakuma taya baba murnar samun ƙaruwa. Tare da jajanta abinda ke faruwa ga Inna da ƴaƴanta. Sannan ya ɗaura da lallashin matarsa ta hanyar daya dace.


     Kwana biyu dayin wannan maganar Zinneerah ta kira taima Baba barka da tashin baƙi dajin yaya jikin Inna yake sanar mata ai jiya AK ya aika Khalipha danya. Yanzu haka Inna na asibitin katsina yau da safe aka wuce da ita. Ya kuma biya kuɗin sarƙar Karima ɗin.

     Wannan zance ya saka Zinneerah matuƙar farin ciki dajin ƙaunar mijinta kuma Yayanta. Yana shigowa gidan tai masa ƙyaƙyƙyawar tarbar da bai taɓa samu daga garetaba. Dan yau fidda kunya tai abinta ta manne bakinta da nashi ta shiga masa salo akan karatun da yay mata. Wannan al'amari ya gigita AK musamman daya kasance ta cuɗe jikinta da turarukan dake neman zauta masa tunani. Yako zage wajen bata haɗin kai har sai da ta koma masa raki. 

     Sai da ya kai boader ya koma mata dariya da tambayarta wai minene sirrin?. Baki ta dinga tura masa tana zuba masa shagwaɓa. Sai da suka tsaftace jikinsu ta zaman masa godiya. Nuna mata yay shi baima san anyi hakaba. Maybe Khalipha ne yayi kawai.

        Tasan sarai yayi hakane dan ya goce, bawai dan abinda ya faɗa gaskiya bane.


      Haka rayuwar waɗanan ma'aurata ta cigaba da tafiya cikin aminci da kwanciyar hankali, duk da dai wataran saɓani kan gifta musu har rai ya ɓaci. Musamman daya zamto halinsu na kamanceceniya da juna wajen miskilancun tsiya. Little kan leƙosu kwana ɗaya biyu ya tafi, wani lokacin yana gidansu Granny wani lokacin yana gidansu mmn sadiq. Khalipha kuma kanje Danya shi da Dr Mahmud daya fola Sa'a tun a wajen biki batare da sanin su AK ba.

         Sunata shirye-shiryen bikin ƴammatan gidan daketa gabatowa. Adilah ma na Nigeria bata komaba su Mammah ne kawai suka tafi. 


      Bukatar komawa ganin likitan Granny yasa AK shirya musu tafiya harda little. Dan yanason zuwa shima yaɗanyi wasu abubuwa acan kafin su dawo wajen biki kuma.

      Zinneerah batasan da wannan shiri nasaba sai ana saura kwana biyu ya ɗauketa suka nufi Danya shi da ita da little. Wani irin farin cikine ya baibayeta ganin inda suka nufa. Ta kwanto jikin hannunsa da faɗin, “Oh oh thanks you so much Yayanmu”.

     Murmushi ya ɗanyi yana sake maida hankalinsa ga tuƙi. Yace, “Yayansu dai, dan kekam kin gama gane Yaya ciki dabai yarinya”.

     Kunyace ta kamata, ta maida kanta gefe tana ƙyalƙyala dariya. Little dake baya yanata harkokinsa da game da Khalipha ya saya masa shima jin dariyarta ya sashi ƙyalƙyalewa da tasa. Dariya suka shigayi saboda yanda yay dariyar abin dariya.

      Tarbar data bama Zinneerah ɗunbin mamaki suka samu a garin Danya, dan bama ƴan gidansu ba hatta da maƙwafta shigowa suketayi. Itako cikin mutunci taketa gaida kowa. Suka dinga daukar little zukatansu fal mamakin yanda aka samar dashi. Tausayin Tinene ya kamata saboda itama ta ɗanɗana rainon cikin nan taji yanda yake musamman a irin wannan yanayin da mutane ke tsanarka da ƙinjin tausayinka. Dan Tinene dukta rame ta lalace cikin na bata wahala. Yayinda ta ɗauka ƴan biyun amaryar babansu kuwa sai daɗi ya kanainayeta ta dinga samusu albarka. Cikin tsokana amaryar Baba ke faɗin. “Ai saura ke ɗiyata, dan wannan ƙyawun da kika ƙara ai in kaji gangami da labari”.

        “Kai Mama ni ALLAH bani da komai, kawai dai idanunki ne”.

       Yaya Gajeje dake bama little abinci tace, “Haba Zinni ai duk wanda ya dubeki yasan kinada ciki, fatanmu dai ALLAH ya raba lafiya muje musha shagalin suna kamar na aure”.

      Cikin shagwaɓa tace, “Kai Yaya Gajeje nifa banda komai”. Dariya suka sanya mata harda Karima da a yanzu take jin wani son Zinneerah ɗin, dan badan mijintaba lallai da yanzu tana birsin. Yanzu ɗinma a zuwansun nan sai da taje tai masa godiya ta musamman harda kukanta.

      AK yace karta damu, shi komai zai iya musu akan Zinneerah. Fatansa dai ALLAH ya kiyaye na gaba kuma. Baba ma ya masa godiya sosai. Sukaje kuma har gidan maigari ya gaishesa tare da su Baba Sabi'u.

       A firarta da Yaya Sa'a takejin batunta da Dr Mahmud. Taji daɗi tayi farin ciki. ta kuma taya Yaya Sa'a murna duk da Dr Mahmud nada mata da yara biyu. To amma tasan shi mutumin kirkine, dan haka ta taya ƴar uwarta farin ciki da wannan abun arziƙi.

     Inna na asibiti har yanzu tare da wata kanwarta dake jinyarta. Suma sai lokaci-lokaci suke zuwa su dubata su dawo. Zinneerah taso lallaɓa AK suje ta dubata itama amma tanajin tsoro, dan dataje kai masa abinci take roƙonsa ko zasu ƙarasa katsina su gaida Aunty Farah wani shegen harara daya kaɗa hanjin cikinta yay mata. Dole ta fito sim-sim tana dana sanin yin maganar. Itako tayine saboda sanin har yanzu Yayan nasu na ƙaunar matarsa. Yana dannewane kawai saboda fushin laifin da suka aikata masa. Amma Sometimes idan suna fira zakaji yakan sakkota koyin misali da wani abunta yace Farah kaza Farah kaza. Tanajin zafin hakan sabida kishi, amma bata ganin laifinsa. dan tasan soyayyar da yake nunawa ga aunty Farah itama ko aure ya ƙara zai iya nunawa gareta bazai wulakantataba. Dan tunda suke bai taɓa kushe Farah a gabantaba, bai kuma taɓa yimata wani zancen halinta mara ƙyau ba indai kaji zancen Farah a bakinsa to alkairintane.

         Yini guda sukai a Danya, dan basu tahoba sai gabannin magriba. Lokacin da suka shigo garin kano ana sallar isha'i.

    Washe gari kuwa nan ma da kansa ya kaita gidan Mmn Sadiq danta yini. Sunyi farin cikin ganin juna itada mamanta da yan uwanta matuƙa. Duk da kuwa a yanzu tana waya dasu a koda yaushe. Hakama mmn halima da Abbah tare da ƴan biyun mmn Halima da suka fara zama ƴan mata. Dan jira kawai suke a kauda Sakina da miji ya gagara samuwa suma su ƙara zabgewa. 

    Nanma yini tai zur dan sai dare ya aika Khalipha ya ɗakkota saboda shi ya tafi wata sabgar shi da Dr Mahmud. 


     A ranar da daddare yake sanar mata gobe idan ALLAH ya kaimu zasu wuce london su da Granny. Bazasu dawoba sai bikin su Safiyya daya gabato gab danma ɗagashi da akayi saboda na Adilah daya shiga ai da wannan watanne za'ayisa.

       Jin harda Granny za'a tafi yasata nuna jin daɗinta sosai. dan ita dai duk da Mammah ta nuna ƙaunarta daga baya tana shakkar matar har cikin ranta. Sai dai taso ace harda su Bahijja ma a wannan karon amma yaya zatai tunda aure take yanzu. Ga ssce exams ɗinsu zasu fara batasan yaya yake nufiba, amma dai bazatai maganaba tunda tasan ya fita sanin muhimmancin karatun ai. Suma kuma su Bahijjan zaman yaran Uncle Ahmad a gidan yanzu ya ɗebe musu kewarta sosai. Danfa Granny ta kafa ta tsare ta hanashi komawa. Dan kuwa dai bai shirya kara aure ba. Matarsa taci kuka harta gode ALLAH ta haƙura. Dan harma yaje ya tattaro musu duk abubuwansu masu muhimmanci da yoma yaransa transfer ɗin makaranta zuwa Nigeria. Manyan ne kawai dake jami'a zasu koma su ƙarasa.............✍


No comments

Powered by Blogger.