Makauniyar Kaddara 63

 


Page 63*


............“A wannan gaɓar saboda yanda ta nuna tashin hankalinta matuƙa sai nayi amfani da damar wajen sake zaunar da ita na nuna mata muhimmanci haihuwarta.

Tare da kawo mata zancen dashen ciki. Ta razana matuƙa, ta kuma ce ita dai gaskiya tanajin tsoro, dan tasan Abdul-Mutallab ma ba yarda zaiba. Dan haka kawai mubar zancen na tayata da addu'a dan bazata iya zama da kishiya ba zata iya halaka kanta. Wannan furuci nata ya kuma ɗagan hankali matuƙa, dan nasan zata iya aikata abinda ta faɗan, na kuma tabbatar auren Abdul-Mutallab bazai fasu ba inba danginsa sunga ta haihu ba. Ta kuma nunamin su Mammah ma ba yarda zasuyiba dan abune da kowa yasan malamai na nuna illarsa a addinance dama lafiya ta wani fannin. Ban gusaba wajen zaman cigaba da nusar da ita, tare da kawo mata dabarun da zamuyi maganin kowacce matsala. Na farko karmu bari AK ya sani, ayi komai a ɓoye harta wadda za'a sama cikin ta haihu ace itace ta haihu. Ta tambayeni taya za'ai hakan ta kasance bayan koyaushe tana tare da AK. Na ce mata ta bari zanyi tunani. Bayan kwana biyu dayin maganar na samo mafita a wajen Doctor ɗin da zaiyi aikin, idan an dasama wadda zata raini ciki ita zata fara pretending like pregnant, bayan yakai kamar 3months zata koma zama a Morocco ta hanyar wasu dabaru namu na mata har mai ciki ta haihu a bata ɗanta ta shayar ita da kanta. Cikin tsoro tace amma tayaya hakan zata faru bada yardar su Mammah ba. Niko nace mata Mahma ce kawai za'a ɓoyema gaskiyar zance, amma Mammah da ita za'ai komai. Tacemin ta yaya Mammah zata yarda da hakan?. Nace mata ta hanyar yin amfani da ita akan so da kishin da takema mahaifin Abdul-Mutallab da ganin laifin danginsa da take na rabuwarsu, da kuma ƙin son rabata da ƴaƴanta da shine babbar barazanarta a rayuwa. A lokacin Farah bata bani goyon bayaba, dan tace bata yarda a cutar da kowa ba, musamman ma Mammah da ta ɗauketa daidai da nata ƴaƴan saboda ƙaunar da takema mahaifiyarmu. Sosai na mata masifa ni da Muktar a lokacin, dan shine ya taimaka mana da likutan da zaiyi aikin ma. Da dai mukaga taƙi tanƙwaruwa ta sauki sai itama nabi da ita ta hanyar razanarwa da kshiya har tai laushi ta amince. Tun daga lokacin itama Mammah na fara aiki a kanta, sannan Doctor ya tsarama Farah yanda zamu sami sparm ɗin Abdul-Mutallab cikin sauƙi”.

               Babu wanda mamaki bai nema kashewa a falonba, musamman ma Mammah datai mutuwar zaune akan wannan labari na Zakiyya. Zakiyya ta cigaba da faɗin,

        “Bayan wani lokaci na tunkari Mammah da batun ya kamata musan halin da Farah da Abdul-Mutallab ke a ciki game da haihuwa, kar muyi sakacin da dangin mahaifinsa zasu aura masa wata zasu rabamu da shine kawai ya koma hannunsu. Na tabbata wannan kalma ta tada hankalinta matuƙa, dan babu abinda tafi tsana arayuwa kamar ace yaranta zasu koma hannun mahaifinsu. Bayan munyi wannan maganar washe gari taima Abdul-Mutallab maganar a gabana, amma sai ya nuna ɗan ɓacin ransa akan duka shekararsu nawa da auren da har za'a fara nuna damuwa basu haihuba, shi wannn maganar dan ALLAH a barta ALLAH ne mai badawa kuma zai basu lokacin da yaso. Da wannan furucin yabar gidan a zuciye. Hankalina ya tashi, dan gashi saura kwana biyu na baro london ɗin, dan haka na sake sabon zaman fanfa Mammah da kawo mata dalilai kala-kala da suka dinga ruɗa mata tunani itama tana ruɗashi. Tashin hankalin data nema sakashi a ciki ya sashi tattaro Farah suka gudo Nigeria a lokacin bamu sani ba. Sai da sukaje ta kira take sanar mini. Naji daɗin hakan, dan nima a gareni wata dama ce. Dan haka na sake buɗe wutar data harzuƙa Mammah harta kirasa ta tabbatar masa da inhar bai yarda da batuntaba wlhy zata iya tsine masa. Sosai Abdul-Mutallab na gudun ɓacin ran mahaifiyarsa. Dan haka furucinta ya tada masa hankali yace ya amince zasuje idan sun koma london. Still nice dai na sake bama Mammah shawarar suga Doctor Hannafi dake nan Nigeria shima kwararrene a wanna fanin kuma a can london ɗinma yay karatunsa da aiki harna tsahon shekara bakwai. Batare da wani jayayyaba ta kirasa da tura masa address da phone Number ɗin Doctor Hannafi dana bata nima kuma na tattaro na dawo Nigeria neman yarinyar da za'aima dashen. Ta farko bataiminba, dan tanada wayo kuma idonta a buɗe yake, hakan yasa nasa hajiya haule canjamin ita.”

         “Biyayyar da Abdul-Mutallab yake ma Mammah ya sashi ɗaukar ƙafa sukaje ga Doctor Hannafi, wanda dama mun gama tsara komai. Dan haka kawai abinda ya buƙata a garesu shine sparm ɗin sa, ita kuma Farah yay mata wasu gwaje-gwaje kamar gaske. Domin kawai bin umarni Abdul-Mutallab ya yarda ya bama Dr Hannafi Sparm ɗin nan, wanda da shine aka haɗa da ƙwan Farah akaima ita Zinneerah dashen bayan mun tabbatar zata iya. Dan ita bata kai waccan girma da wayo ba, amma yanayinta kawai zaka kalla bama zaka ɗauka a ƙauye ta fitoba dan ƙyakyawa ce. Da wannan karancin shekarun nata mukai amfani wajen yin komai na dashen batare da ita ta fahimci komaiba, dan ALLAH ya taimakemu sanda aka kawo min ita tana cikin halin zazzaɓi sai komai ya ƙara zuwa mana dai-dai muka tafiyar da ita akan treating ɗin zazzaɓin nata. Sai dai kuma bayan dashen muna fata da addu'ar ALLAH yasa ya zauna da kwana uku muka nemeta muka rasa. Hankalina ya tashi matuƙa a wannan lokacin, nama kasa sanarma Farah yanda akai sam. Sai dai munta tararrabin mu da neman yarinya ni da Muktar da Dr Hannafi. Gashi Hajiya Haule ta wuce saudia kuma bani da contact ɗinta nacan balle mu binciki garin da ta ɗakkota. Dr Hannafi ne ya kwantar min da hankali ta hanyar sanar min da wahalama cikin ya zauna, dan bai kai kwanakin da ake buƙatar nutsuwarta a waje guda ba, kawai yanzu dabarar da zamuyi a karasa AK ya bada sparm ɗin nasa kafin su wuce sai a sake yima wata dashen, wannan kuma mu ɗaukama bazai zauna ba kawai, musamman da ko magungunan daya kamata tasha sau daya ta shasu. Na ɗanji sanyi da wannan shawarar tasa, akanta kuma na yanke hukuncin tun karar Mammah da batun dashen cikin. A ranar na kirata, na sanar mata Dr Hannafi ya tabbatar mana AK nada matsalar bama mace ciki, amma za'a iya yin amfani da sparm ɗinsa ai dashe, sai dai matsalar itama Farah nada tata matsalar a mahaifa kuma”.

          “Hankalinta ya tashi, harta buƙaci na haɗata da Dr Hannafi ɗin, na kuma haɗata dashi ya sake mata bayanin daya kamata akan dashen da tsarin da za'ayi. Ta tabbatar masa da zata iya yarda ayin kodan a samu ɗan danginsa su daina harar mata yaro dason mallakesa. sai dai babbar matsalarta shine Abdul-Mutallab, tasan bazai taɓa yarda da hakanba koda zata tursasashi a wannan gaɓar. Cikin dabara Dr Hannafi ya shigar mata da shawararmu na yanda tsarin zai kasance batare da Abdul-Mutallab da kowama sun fahimci hakanba bayan mu. Tace ya bata dama zatai tunani da shawara. Cikin amincin ALLAH sai tai shawara dani, dan a tunaninta bansan komaiba game da dabaran. Babu wani ja'inja na nuna mata hakan shine dai-dai, tare da sake kawo mata dalilaina nima. Sai ko aka dace ta yarda dan nayi amfani da inda ke mata ƙaiƙayi. Amincewar tatace ta zama ginshiƙin tushen aikinmu na biyu, sai dai a wannan karon cikin bayin gidanmu na ɗakko, kuma da amincewarta dana iyayenta, ana kuma gamawa na maidota gidana ina kula da duk motsinta har ALLAH tasa ciki ya zauna ya kai wata biyu da wasu kwanaki sannan Mammah tazo da kanta ta tafi da ita Morocco. Zuwa sannan kuma Abdul-Mutallab da wasu a cikin danginmu sunsan Farah nada ciki, sai dai mun gargaɗi Abdul-Mutallab da sanarma danginsa zancen ciki har sai Farah ta haihu saji hakan zaisa sufi murna ya kuma musu surprise. Ya amince da hakan kuwa sai dai bamusan dalilinsaba. Sai dai ashe kana nakane ALLAH na nashi, dan randa Farah ta baro london da nufin zuwa tai goyon ciki a Morocco wanda tursasawar Mammah yasa Abdul-Mutallab yarda washe gari yarinyar tayi barinsa. Ranar ba Farah kawai ba hatta ni da Mammah sai da mukai kuka wlhy, Abdul-Mutallab kuwa a ranar ya baro london zuwa Morocco hankali a tashe. Shima har kukan yayi saboda ya ƙwallafama cikin nan rai kamar mi. Bayan gama wannan taraddadin bawai na haƙura bane akan ƙudirina. Na cigaba da zungurar Farah da Mammah suna zillewa. Dan kai tsaye Farah tace min alhakin Abdul-Mutallab ne yasa cikinma ya zube. Faɗa mukaita mata a lokacin, amma taƙi saurarenmu. Mun tattara mun ƙyaleta a lokacin danta huta dan naga itama Mammah na neman fara zamemin. Taimakon da ALLAH ya sakemin shine takurawar Abdul-Mutallab ya ƙara aure daga hajiya iya, wanda har takai ga ya ɗauke kafarsa da Nigeria, sukuma suka tura masa ƙaninsa. Tun daga nan na fahimci hankalin Farah baya tare da ita, dan duk wani abinda ya faru tsakaninta da Abdul-Mutallab sai ta kira ta sanarmina lokacin. Abinda na fahimta shine kishin zancen ƙara aurensa na cinta har take ganin kasancewar wani nasa tare da shi zai sa danginsa suci galaba a kansa. Na biyu kuma tashin hankalin Mammah itama na kada Abdul-Mutallab ya komawa danginsa yasa take goyama Farah baya.”

      Takai ƙarshen zancenta tana share hawayen da tun ɗazun basu gajiya wajen kwaranya ba daga kumatunta, dan muryarta har dashewa takeyi dan kuka.

      Tsitt falon yayi motsima kowa ya kasa dan al'ajabi, wane irin masifa ne wannan da haɗa boom. dan wannan al'amari na Zakiyya yayi kama da haɗa boom. Dan kawai kinason ƴar uwarki sai ki ƙulla abinda zaki cutama rayuwar wasu.

       Kallonta kawai AK yace cike da tsana da takaici. idanunsa sun kaɗa sunyi jajur, hakama jijiyoyin kansa sunyi ruɗu-ruɗu. Hakama Farah kuka take tamkar ranta zai fita, dan tasan dai komai Zakiyya tayine dominta, gashi tun ba'aje ko'ina ba komai ya ƙwaɓe. Kishiyar da take tsoro kuma an mata ta sanadinsu. 

         Mammah ma kanta duƙe a ƙasa dan tama rasa mi zatace dan tashin hankali da baƙin cikin kanta da kanta, tayaya ta zurma haka da yawa yarinya ƙarama ta ɗana boom ɗin da a ƙarshe yake neman tashi da ita? Tayaya idonta ya rufe haka da yawa ne akan abinda yana a hannunta amma gashi sakacinta ya ta miƙashi ga mai shi?.......

         Cikin ƙunar Zuciya AK ya katse tunanin kowannensu ta hanyar faɗin, “Shima cikin da take dashi yanzu na ƙaryane kenan? Randa mukaje asibiti da nufin sake duba lafiyata kune kuka ƙulla?.”

          Kasa magana Farah da Zakiyya sukayi. sai Mammah ce cikin kuka tace, “Kayi haƙuri Abdul-Mutallab, tabbas wannan duk laifinane, da ace ban bata goyen bayaba babu yanda za'ai hakan ta kasance. Nayi nadamar saninki Zakiyya, wannan wane irin haline haka da kika nema jefamu a ciki. Har takai na saka hannu wajen cutama gudan jinina ta hanyar makircinki”.

        “Dama shi son zuciya ai ɓacin zuciya ne, daga lokacin da kake ganin wayonka ko dabararka zai baka abu to lallai a lokacin ka ɗaura ɗammara da ɗambar rasashi, dan koka samu sai ya suɓuce maka. Kin biyema yara ƙanana saboda wani shirmen banza da wofi Hindatu, yanzu da ALLAH bai ƙaddara yarinyarnan ta faɗo cikinmu ba yaya kenan? Duk da dai sanda sukayi na farko basu sanar miki ba, amma na biyun da'an haifesa fa? Shikam kinada kamasho a ciki ai”. Uncle Ahmad ne ke magana cikin ƙunar zuciya.

       Kauda kai AK yayi yana rumtse idanunsa saboda zafi da ƙirjinsa ke masa. ga kansa sai juya masa yakeyi alamar hawan jininsa na neman motsawa. Cikin harɗewar harshe yace, “Uncle idan wancan ya salwanta aiga waninan ma sun sake dasawa. Tunda sunce tanada ciki kuma likitoci sun tabbatarmin babu wani ciki tare da Farah”.

     Yanzu kam duk yanda mai martaba da mukarrabansa sukaso daurewa sun ƙasa. Cikin kaushin murya yace, “ALLAH zai sakamin ɓatamin suna da kukayi. musamman ke Zakiyya dan kece kika ƙulla komai, kece kika ɗora ƴar uwarki akan abinda sam babu shi a ranta, ni yanzu bamma san mizance mukuba wlhy, dan yanda nakejin raina zanma iya tsine muku. Amma inason sanin gaskiyar zancen shi cikin da akace tana dashi yanzu, dan nikam kotun musulinci zan kaiku a yanke muku hukunci dai-dai da laifinku”.

      Sosai Farah ta fashe da kuka. Ta rarrafo gaban mai martaba ta kama ƙafafunsa da fashewa da kuka. “Dan ALLAH Abba kayi haƙuri, nidai wlhy bazan sakeba, wannan ma kota haufa banaso zanyi haƙuri ALLAH ya bani nawa. Na tuba Abbah dan ALLAH na tuba”.

     Banza yay mata yama ɗauke kansa ya maida ga Zakiyya da itama kukan take. “Wai bada Zakiyya nake maganarnan ba?!”

     Zabura ta ɗanyi saboda yanda yay maganar a tsawace, ta shiga jinjina kanta da faɗin, “Abba hakane, shima dasawar akai, amma wannan ƴar Morocco ce, kuma da amincewarta itama wlhy”.

     Sake ɗaukar sallalamu falon yay gaba ɗaya, hajiya iya dake sharar ƙwalla tace, “Gaskiya baku ƙyautaba, wannan zaluncine wlhy dason zuciya. A barshima mutum shi ya yarda yay muku wannan aikin da sauƙi ai, amma kamar yarinyarnan aikun zalunceta. Inda ALLAH bai ƙaddara tamu bace kamar yanda Ahmad ya faɗa harta mutu baza'a daina mata kallon wannan tabon ba. Yaya zakuyi da alhakin wannan yarinyar kawai ma balle na sauran suma, sai dai idan da yardarsu kukayi sukam. Nikam dai ina bayan mahaifinku a kaiku kotun musulinci a bin kadin jikata na rainon cikin da tayi. kuma wlhy ko sama da ƙas zata haɗe ɗannan ya zama nata har gaban abada marasa mutunci”.

          A take su waziri suka shiga goyama hajiya iya baya, kowa na tofa albarkacin bakinsa. Mmn sadiq, Abba, baba sune dai basuce komaiba, sai dai duk sai da sukai ƙwallar tausayin Zinneerah harma da AK da little. Sai da ƙyar Baba ya fara magana ganin kowa ya yarda da zuwa kotin.

      “Ranka ya daɗe nikam kuyi haƙuri zance wani abu”.

      Duk hankalinsu suka maida garesa. Ya ɗan muskuta zamansa yana gyarama little dake a jikinsa kwanciya, dan shi yaune karon farko daya ga jikan nasa, “Kuyi haƙuri nasan tabbas basu ƙyautaba, kuma zaluncine abinda sukayi dan yarinyarnan taga rayuwa mai zafi kala-kala a dalilin cikin nan. To amma Alhmdllh ta wani gaɓar ya zamar mata alkairi. Dan a sanadin samunsa ta sadu da mahaifiyarta, ƙaddara ta ɗakkota ta kawota cikinku da har a yau ya zama sillar bayyanar komai, bugu da ƙari yay mata ƙyauta da miji uban ɗan kuma saboda hikimarsa. Sannan a sanadinsa nima kaina nabar gida harna samu waraka daga kaidin matata, na kuma ƙara aure a yanzu haka matata ta haifamin yara maza ƴan biyu guda biyu tun washe garin da suka koma gida. Waɗanan kaɗanne daga ni'imomin UBANGIJI gagara misali daya lulluɓe Zinneerah dasu a sanadin cikin yaron nan da batajiba bata ganiba. Tabbas duk mai haƙuri zai dafa dutse harma yasha romonsa. Su dai duk sun aikatane akan dalilai biyu zuwa uku. Mahaifiyarsa dalilinta kawai kar ya dawo hanun ubansa ne da rayuwa, sai kuma gashi ya dawo cikin sauƙi. Ita wannan yarinya saboda kar mijinta ya ƙara aure ne, kuma gashi ya ƙara ɗin harma suna zaune a inuwa ɗaya. Ita wannan ƴar uwa tata kar wata tazo ta haihu ba ƙanwartaba. Gashi kuma watan ta haihu ba kanwar tata ba. To idan mukai tsam a nazari zamu fahimci UBANGIJI ya bama kowa sakamako nan duniya dai-dai da shi da tabbatar musu cewar wayo ko dabarar bawa bata kaisa da nasara. duk saurinka kuma saika jirayi zartar da ƙaddarar UBANGIJI gamai ita. Tunda su duk sunyine a ɓoye domin bama kayinsu kariya akan abinda yake gaibu kuma dauɗar duniya amma daga ƙarshe gashi duk sun rasa, kuma wanda sokaso ƙwata daga wajensu ALLAH ya maido musu. A ganina kuma miya rage banda mu barma UBANGIJI ikonsa ya ƙarasa zartar da hukuncinsa. Basai anje kotuba, dan mu dukanmu ALLAH ya haɗamune a ƙarƙashin inuwar zumunci sai muyi haƙuri wajen haɗiye duk wani saɓani da zaizo a garemu duk da kuwa wannan ya banbanta ba abune mai saukiba. Amma idan mun sauƙaƙashi a ranmu sai ya zame mana alkairi kamar yanda ya zamewa Zinneerah. Sai dai kuma su sauran yarenne bamuda hurumi a kansu inhar suma tirsasu sukai ko yaudararsu. Abin na gaba shi annamimin likitan dake wannan aikin ya kamata a dakatar dashi, dan gwara ace ma'auratan dake buƙatar hakan da kansu suka amince suka kai kansu bawai ta irin wannan hanyar dabita wagga ɗiya Zakiyya tabi ba. Wannan al'amarima malamai sunata nasiha akansa. barinsa yafi alfanu fiye da yinsa. Dan UBANGIJI shine yasan miya gani har bai bakaba, zata iya yuwuwa rashin haihuwar sai yafi zame maka alkairi fiye da yinta. To mizai hana bazaka dogara ga UBANGIJIN talikai harya baka ba kuma?. Sai kuma ina roƙon alfarmar ku taimaka kuje can garinmu ku wanke wannan yarinya agaban al'ummarmu, dan inba hakaba harta mutu wannan tabon na biye da ita. Haka shima wannan yaron bazasu taɓa kallonsa da darajaba dan ɗan shege zasuke kallonsa bayan ba haka bane. Ayi haƙuri da juna ayi sulhu dan ALLAH shine mafi alkairi a garemu fiye da mu tonama kammu asiri kodan kasancewar ku manyan mutane danmu namu mai sauƙine iya garine kawai, idan yazu kuma mukace mun barsa zance ya ƙare. Kuko magauta sun sami abin faɗa a gareku kenan har takai shi yaron ana goranta masa duk da kuwa ba alfasha aka aikata wajan samuwarsa ba kai tsaye”.

     Harga ALLAH kowa maganar baba ta sanyaya masa ransa. Kuma kimarsa da darajarsa ta ƙaru a cikin idanunsu, hajiya iya ta shiga jera masa tagwayen addu'oi shi da zuri'arsa kowa na amsawa da amin.

     Sai da kowa ya natsa sannan mai martaba ya fara magana bayan yayi gyaran murya. “Ni a nawa hukuncin to Abdul-Mutallab da Sageer (mijin aunty Zakiyya) duk ku saki waɗanan marasa mutuncin, kowacce ta koma masarauta sai sunyi zaman shekaru bibbiyu kafin na barsu su dawo gareku idanma kuna sha'awa kenan, kokuma su sake auran wasu mazan suji, dan masu iya magana sunce idan kai nada tsoka taɓa naka kaji. hukunci na biyu koda na faɗa ko ban faɗaba musilinci ma ya bama wannan yarinya yaro duk da dai malamai sunyi bayani kala-kala akan hakan, dan haka ko da wasa idan kuka ɗauka yaron nan kuka bama Farah matsayin uwarsa ALLAH ya isa ban yafe mata ba idan ta amsa. Yaro na Zinneerah ne har abadan kuma itace zata cigaba da iko da shi matsayin mahaifiyarsa har ƙarshen rayuwarta, kai bamma yarda koda wasa wani ya dangantashi da Farah ba zan ɗauka mataki mai tsauri koda kuwa Abdul-Mutallab ne yayi hakan. Koda alaƙa zata shiga tsakaninta da shi sai dai ta zumunci ko matsar ubansa amma ba uwa ba. Hukunci na ƙarshe idan waɗancan da sukaima wannan ƙullalliyar yazam suma bada saninsu bane to lallai zan kaisu kotu a bi musu kadin haƙƙinsu. Wannan shine hukuncina a matsayina na maihaifinsu”. 

    Kuka wiwi Farah da Zakiyya keyi musamman akan zancen sakin da mazajenau zasu musu dana haramta mata Little. Dan Farah a yau karo na farko ƙara ganin little yasa ya shiga ranta dan kamar an ɗakko ƙaunrasa mai tsanani an dasa mata a ƙirji takeji. 

      Babu wanda ya iya jayayya da wanan hukuncin na mai martaba dan shine kawai zai iya zama darasi garesu. Sai dai yanda suke kuka dolene su baka matuƙar tausayi..............✍

 

No comments

Powered by Blogger.