Makauniyar Kaddara 62

 


Page 62*


.........Kawai jitai hawaye sun ɓalle mata babu gaira babu dalili, ta zube a farkon kujerar shiga falonta na farko ta cigaba da zirarwa batare datayi yunƙurin sharesuba ko sau

ɗaya. Har cikin ranta tanajin nadamar shigar masa ɗaki kai tsaye ba tare da jiran izini ba, sai dai ALLAH shine shaidarta batai tunanin matarsa na cikiba, dan duk tunaninta sashenta itama ta nufa.

      Zumbur ta miƙe da saka bakin gyalenta tana share hawayenta saboda jin takun tahowarsa, tai saurin nufar ƙofar itama dan bata buƙatar ma ya shigo ya sameta. Kusan cin karo sukai yaja da baya itama taja tana ambaton, “Sorry bansan ka tahoba”.

       Yanda yaji muryarta a shaƙene ya sakashi kallonta da ƙyau batare da ya amsaba. Abinda kawai zuciyarsa ta bashi akan maganarsu aunty Zakiyya ne, dan haka ƙarasa shigowa da jawota jikinsa kawai yay ya rungume. Wani irin sabon kuka ne taji ya taho mata dan haka ta sakeshi dan duk yanda taso riƙesa ta kasa. Ba komai ya sata gagara riƙewarba kuma sai ƙamshin turaren aunty Farah da taji jikinsa nayi. Ƙoƙarin janye jikinta tayi ba tare da shi ya ɗagotaba. Tai saurin nufar ƙofar fita tana share hawayen da mayafinta.

        Da mamaki yaɗan bita da kallo zuciyarsa na raya masa ‘Anya kuwa zancen su aunty Zakiyyar ne kawai. Dan idan bai mantaba yaga basket a ƙofar falonsa da ƙamshin turarenta. Kafin ya shigo nan din yayi tunanin ko Khalipha ne daya shiga ɗazu ya ajiye dan lokacin da yazo a bedroom ya samesa, kamshin turarenta kuma ya barsa akan kawai dan ya shaƙane sanda suna tare a falon.

     Kansa kawai ya ɗan girgiza dayin murmushi, a kan laɓɓansa ya furta, ‘Oh mata kenan’ dan yanzu ya gama da Farah itama, koda ya rakata mota ma ya bartane tana kukan.

      Bayan Zinneerah ɗin ya bi, sai ya isketa a general falo tsaye. Tana ganin fitowarsa tai saurin ficewa baki ɗaya kuma. ‘Tofa babbar magana’  ya faɗa a fili murmushi na suɓuce masa.

          Shi ya rufe ƙofar sannan ya iso wajen motar inda Zinneerah tai tsaye bata shigaba. Fuskarsa ya daidaita da ƙyau yana isowa, batare daya kalletaba yace, “Shiga muje”. Yay maganar yana buɗe mata baya. Ganin yanda yay kicin-kicin da fuska dama kuma ba wasan yake da itaba yasata shiga babu musu, sai da ta zauna ya gyara mata mayafinta daya fito sannan ya zagaya ya shiga shima mazaunin driver, Farah na gefensa itama ta cika tai fam.

          Har zai sama motar key sai ya fasa, Kallon Farah yay sannan ya juya ya ɗan kalli Zinneerah. “Kun gaisa da juna?”. Ya faɗa a dake.

        Kusan a tare sukace masa a'a. Sai Zinneerah kuma tace, “Aunty Ina kwana”. Kamar Farah zata share saita motsa laɓɓanta ciki-ciki tace, “Lafiya” saboda hararan da AK ya zubo mata. 

       Daga haka motar ta ɗauka shiru. Shima bai sake cewa komaiba yay mata key da harbata gaban gate. Ficewa yay kai tsaye dan dama maigadi ya buɗe masa tun ganin sun fito sun shiga.


        Shaiɗan ɗin daya fahimci yana kai kawo a zukatan matan nasa ya sakashi saka karatun alkur'ani a motar, a ransa yana nema musu sassauci ga ALLAH dan shima yasan zafin kishi tunda yana dashi. Lokaci-lokaci yakan kalli Farah ya duba Zinneerah kuma ta mirror. Ganin yanda duk suka maida fuskoki gefe sai suka bashi dariya amma ya gimtse baiyi a fili ba sai a ransa. Harko suka iso gidan nasu daga Farah har Zinneerah babu wanda yayi ko tari. Bayan ya gaisa da maigadi ya ida shiga cikin gidan ransa fal mamakin ganin motoci da yawa a harabar gidan kamar har yanzu bikin sukeyi basu gamaba danma babbace.

        Babu wacce ta motsa a cikinsu, dan haka shima sai bai tanka musuba ya buɗe motar ya fita. Ganin haka yasa suma duk suka fito kusan lokaci guda. Kallon juna sukai, sai kuma kowacce ta ɗauke kanta. Farah tazo ta gitta Zinneerah ɗin tanabin bayan AK da yay gaba abinsa ya barsu a wajen, dan harga ALLAH idan ya cigaba da zama yana kallonsu dariya zata iya kufce masa. Dan tsaf ya fahimci itama Zinneerah ɗin A ce a fannin kishi kenan. Koba komai kishin nata a karo na biyu ya tabbatar masa da shima ya samu karɓuwa a gareta, miskilancine kawai ya hana ta bayyana kamar yanda ya buƙata.

       Sashen Hajiya iya suka nufa kai tsaye, inda sukaci karo da tarin takalma kala-kala ajiye, da alama baƙin da suka tara waɗan nan motocin duk sune anan ɗin. 

        Cikin nutsuwarsa da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga, Farah na biye dashi Zinneerah a bayanta. Da sauri Farah ta nema komawa da baya saboda cin karo da fuskar mahaifinta da tai hakimce cikin kujera. AK yay saurin riƙo hannunta yana magana ƙasa-ƙasa. “Malama ki nutsu mana” Ya faɗa yana duban Zinneerah datai musu kallo ɗaya ta ɗauke idonta.

         Kai Farah ta ɗaga masa idanunta cike da ƙwalla. Ya nuna musu hanya alamar su wuce. Babu musu suka nufi ƙarasawa cikin falon ran Farah fal mamakin zuwan Abban nata babu dogari ko ɗaya, sai ƙannensa biyu Matawalle da waziri, da babban amininsa da kowa ya sansu tare wanda ƙanine a wajensa shima amma kusan tare sukai rayuwarsu, sai dai ba mahaifinsu ɗaya ba. Sai da suka zo kusan tsakkiyar falon Zinneerah ma taci karo da Babanta da Abbah, harma da Maman Sadiq.

     Ita kanta tsoro ne ya kamata, dan babu shiri ta fara satar kallon mutanen dake a falon, sai ga idonta akan Hajji lanti, da Hajiyar da aka kaita gidanta wadda ta kaita gidan aunty Zakiyya. Ai batama san lokacin da ƙafafunta dake rawa suka goceba ta durƙushe a wajen.

      Hajiya iya ce tai murmushi da faɗin. “Haba Inno ya da zubewa haka ƙasa. Tashi kizo nan kinji, kema Farah taho”.

       Miƙewa Zinneerah tai da ƙyar tabi bayan Farah da itama gaba ɗaya ganin Abbasu ya sata tsurewa, dan tsoronsa suke matuƙa saboda bai musu da sauƙi duk da yana tsananin sonsu kuwa. Shi dai AK tuni yakai zaune gaban Uncle Ahmad yana gaida iyayen nasa da surukansa cike da girmamawa. Ganin haka yasa Zinneerah da Farah suma suka shiga miƙa gaisuwa garesu duk da basusan iyayen juna ba, garama ita Zinneerah tasan su Mammah.

    Bayan an gama gaishe-gaishe duk da su sun gaisa dama a tsakaninsu harma da gabatar da juna tunkan isowar su AK ɗin. Harma mai-martaba mahaifin su Farah ya shigar da ƙorafinsa na rashin sanar masa da auren AK ɗin na biyu. haƙuri Baffah ya bashi tare da masa bayanin a yanda abun ya kasance bada shiriba. Yasha mamaki matuƙa, amma cewar hajiya iya zaman nasu nada nasaba da auren yasa mai-martaban yin shiru bai nema ƙarin bayani akan zancen little ba da yana a falon jikin Abbah, dan tunda ya gansu shi da mmn Sadiq kuma ya maƙale musu cike da murna dan duk duniya su yafi sani fiye da kowa, tunda ko uwarsa batai wahalar da sukai a kansaba bayan ta haifesa.

       Waziri ne ya gabatar musu da addu'a. Kafin hajiya iya ta fara magana.

        “Zan fara da sunan ALLAH mai rahama mai jinƙai, dan shine yay sanadi da silar taramu anan ta dalilin wani saka mai sarƙaƙiya da duk ta sarƙe zukatanmu kafin shi wannan zaman. Anan mu dukanmu iyayene kuma kakannine, dan haka ina fatan zamu bada haɗin kai wajen nutsuwa mu fahimci abinda ya taramu, sannan duk wanda al'amarin ya shafa dan ALLAH ina mai roƙonsa dayaji tsoron ALLAH mai zartar ga hukunci a sanda yaso ga wanda yaso ya faɗi gaskiyar abinda ya sani. Mun cire hukuma ne a wannan zancen saboda wasu dalilai. Ba kuma hakan na nufin bazamu iya maida komai garesu bane duk da mun kasance a ƙarƙashin inuwar zumunta ta dalilin aure da sauransu. Wannan yarinya da kuke gani.....”

     Ta nuna Zinneerah da kanta ke a durƙe tamkar Farah.

      “Sunanta Zinneerah. Malam Sulaiman gashi nan zaune shine mahaifinta. Wannan kuma Hauwa'u ɗiyar ƙanwata itace mahaifiyarta. Waɗan nan iyaye sun rabu sanadin ƙaddara data saka Zinneerah zama a hannun matar uba bayan barin Hauwa'u gidansu. Inda ita wannan matar uba nata ta raineta cikin gallazawa da son zuciya, a ƙarshe kuma ta miƙata aikatau bada sanin mahaifintaba. Sanadin wannan aikatau ta dawo musu da ciki da suka rasa daga ina ta samosa. Aka turketa da tambayar duniya da barazana tace ita bata aikata komaiba kuma batasan mai ciki ba. An turza iya turzawa tace bata saniba. To a yanzu dai wannan yaro dake jikin Alhaji Abubakar shine ɗan data haifa. Nasan kuma duk wanda ya kallesa zaiyi mamaki da ruɗani akan kamanninsa da Moddibo. Kuma komi za'a faɗa bazai yardaba zai dangantashi da shi a matsayin mahaifinsa kamar yanda muma mukaitayi. Bazan kaiku da nisaba, ga dai wadda ta kai Zinneerah aikatau birni, zamu fara ji daga gareta yaya aka haihu a ragaya. Hajiya Lanti bismillah”.

    Hajiya iya ta ƙare zancenta da kallon Hajji lanti dake zaune ita da hajiya Haule da kallo ɗaya zakai mata ka tabbatar a gigice take tun zuwansu gidan.

        Zama hajji lanti ta gyara. Kanta tsaye ta fara magana da iya gaskiyarta. “Ni Lantana nayi alƙawarin faɗar gaskiya kamar yadda Hajiya mama ta buƙata, zanyi hakanne kuma domin na fita har a wajen UBANGIJI na. Wannan sunanta hajiya Haule. a garin katsina take zaune. Na santane dalilin wata ƙawata ƴar kankia da muke zuwa sarin kayan koli kano, itace ta haɗani da ita akan na dinga kai mata yara masu aikatau. Zuminci ya ƙullu a tsakaninmu mai ƙarfi saboda kai mata yara da nakeyi akai-akai. Har ALLAH yasa Zinneerah ta shiga sahunsu a dalilin matar mahaifinta Asabe. Labarin kuɗin da ake samu a dalilin aikatau yasa Asabe ɗaukar Zinni ta bani saboda ta mallake babanta ga shinan bai iya ce mata bai iya musata. Na ɗauka Zinni na kaita garin katsina aikatau tare da wasu yara, washe gari na juyo da nufin komawa gida ƴan doka suka kamani a tsaranci dalilin wata yarinya. Kusan shekarata biyu a gidan kaso, na fito shine naci karo da mummunan labarin Zinni ta dawo da ciki. Wlhy, wlhy, wlhy, wannan shine kawai abinda na sani, amma bansan komai game da cikin Zinni ba”.

        Kowa ya gamsu da zancenta, dan haka suka maida dubansu ga Hajiya Haule dake sharar zufa.

      “Nima nayi alƙawarin zan faɗi gaskiyata ni Hajiya Haule, dan faɗan da yafi ƙarfinka masu iya magana sunce ka maidashi wasa. Kamar yanda Hajiya lantana ta faɗa duk anyi haka. Ta kawomin yara ciki harda wannan yarinya Zinneerah saboda dama muna irin wannan huɗɗar. Inda ni kuma na danƙata hannun Hajiya Zakiyya. Amma kafin ita Zinneerah dama akwai wata yarinya da na taɓa bama ita Hajiya Zakiyya ɗin. Wadda ta sanarmin zasuyi mata aikine kuma zata bani maƙudan kuɗaɗe harda iyayen yarinyar. Babu wani ja'inja na yarda duk da kuwa bata fito ta sanarmin da ainahin aikinba, amma jin kuɗi ya sani ruɗewa na amince mata. A tashin farko ta diremin dubu ɗari biyar, hakan yasa a haukace na kai mata wata yarinya da aka kawomin dan sama mata aiki. Sai dai kuma bansan yaya akaiba bayan kusan sati ɗaya ta dawomin da yarinyar akan na sama musu wata ita bazata iya aikin da suke buƙataba. Nasha mamaki saboda yarinyar dana basu babba ce, nasan kowane irin aiki aka sakata zata iya. Dan haka na kasa daurewa na tambayeta duk da inajin tsoro saboda girmanta da kasancewar wadda ta fito daga masarauta. A lokacin bata kulani ba. ta daice naje idan an samu tana jira. Haka na baro gidanta cike da wasiwasi amma bani da mai bani sani sai ALLAH. Anyi haka da kusan wata ɗaya sai ga Hajji Lanti da yara. Da farko dai ƙyawun ita wannan yarinya yasani jin sha'awar kai mata ita, dan nasan masu kuɗinnan dason ƴar aiki mai tsafta da ɗan fasali haka. Cikin amincewar UBANGIJI kuma tana ganinta sai tace tayi, ta kuma ɗauka cikon kuɗina har naira miliyan ɗaya ta bani, duk da dubu ɗari biyar ya kamata ta cikamin. dan munyi da itane akan miliyon ɗayan, nawa dubu ɗari biyu na iyayen yarinya dubu ɗari uku, na yarinya ɗari biyar, amma ban saniba ko jin daɗin samo yarinyar yasata bani ƙarin dubu ɗari biyar, bakuma tamin bayanin ta karanba sai da naje gida na kirata dan duk zatona ko bata kulaba ta bani. Amma sai tace min tana sane. Samun yarinyar dai-dai da ra'ayinsu yasata ƙara mana waɗanan kuɗi mu da iyayen yarinyar. Ta kuma ɗora da faɗamin zasuma yarinyar dashe ne na ciki, idan yakai wata biyu zasu ɗauketa zuwa ƙasar waje har saita haihu musu su sallamota da tagomashin arziƙi, amma wannan sirrine tsakaninmu, ko iyayen yarinyar bataso su sani kawai nace dasu ta tafi turai ne da yarinyar inda take zama da mijinta. Iya abinda ta sanar min kenan ta yanke wayarta. Harga ALLAH na girgiza da zancen sai dai inda aka fi ƙarfi nane bani da damar cewa komai. Kamar yanda ta buƙaci karna bar Nigeria sai aikinsu ya kankama na amince, dan dama kuɗin data bani so nake na koma ƙasar saudia inda dama can nake zaune a da. An yayonine an maidoni rashin kuɗi yasa ban komaba. Gaba ɗaya na mallake kuɗi har na iyayen yarinya dana yarinya da tace, ko Hajji Lanti data kawomin yarinya ban nema ba. Dan na shirya kamfinma ta dawo amsar kuɗaɗen yaran data kawo nabar ƙasar insha ALLAHU. Bayan anyi haka da sati uku inata shirina sai ga wayar hajiya Zakiyya, ta tabbatarmin aiki yayi zan iya tafiyata cikin murnarta. Nima naji daɗi sosai dan dama kayana a shirye suke, hakan yasa kwana biyu dayin magana da ita na wuce saudi-arebia da yara guda biyu. Daga haka ban sake sanin komaiba sai jiya da ƴan sanda sukazo har gida batun kamani. Wallahi tallahi ALLAH shine shaidata wannan shine abinda nima na sani, dan ALLAH ku gafarceni na tuba”. Ta kare maganar tana share hawaye.

        Gaba ɗaya falon ya ɗauka salati ana duban Zakiyya da tai ƙasa da kanta, daka ganta kasan a firgice take matuƙa. Hakama Mammah a ruɗan take amma duk tasan itama akwai sunanta a ciki so take taji ta bakin Zakiyya game da cikin Zinneerah da ita dai harga UBANGIJI batasan da zamansaba.

      Zinneerah kam mutuwar zaune tayi tanabin kowa da kallo kawai tamkar butun-butumi, dan harga ALLAH suna neman rikitar mata da tunani. Ita kanta burinta kawai aunty Zakiyya tayi magana.

     Mai martaba da zuciyarsa har wani tafasa take ya kafe Zakiyya da kallo yana kuma duban Farah dake kuka itama wiwi. A zafafe yace, “To dan uban daya haiheki sai kimana bayani muji lalatacciyar yarinya kawai. Wannan wane irin kafurcine kuma daga ina kika samosa ko kuka samosa tunda dai babu yanda za'ai dashe masu ƙwai basu saniba. Shi ƙwan na wanene? Kuma yaya akai?”.

         Ƙasa ta zamo ta dirƙushe jikinta na rawa, dan tafi kowa sanin wanene mahaifinsu. Inhar kuma tai gigin faɗar abinda ba haka bane lallai zai mata abinda gwamma ta faɗi gaskiyar.

      Kafin tace komai Farah da tsoro ke neman gigitata na tsawar mahaifin nasu ta fara rawar jiki da faɗin, “Wlhy Abbah babu ruwana nidai, duk aunty Zakiyya ce ta tsara komai, itace tasa muyi wlhy badan inaso ba......”

       Hankali tashe itama Zakiyyan ta fara magana, “Dan girman ALLAH Abbah ka gafarceni. dan ALLAH kar kayi fushi dani, Baba wambai ka bashi haƙuri dan ALLAH”.

        Aminin mai martaba da suke kira da baba Wambai ya gyara zamansa cikin kasaitar mulki da dattako yace, “Zakiyya kafin azo ga neman gafara ai nakega ya dace musan yaya akai ko? Kinsan mai martaba bayason jayayya, dan haka ki buɗe baki kiyi bayani tamkar yanda suma waɗanan mata sukayi, inaga shine zaifi sauƙi kamar kafin muzo ga gaɓar da kike so”.

      Kanta ta jinjina masa tana sharce hawaye.

         “Kowa yasan Farah dai autarmu ce da tausayinta yasa duk muka ɗauka son duniya muka aza mata, musamman ma ni daya kasance itace kawai ƴar uwata mace, sauran ukun duk maza ne. Farah a Morocco ta rayu hannun kakarmu data baro london, bayan rasuwarta Mammah yayar mahaifiyarmu ta amsheta ta koma da ita london. Tausayin da kowa yakema Farah a cikin dangi shi Abdul-Mutallab ke mata shima. Hakan yasa yafi kowa nuna jin daɗinsa da komawar Farah garesu. Kamar yanda take samun gata daga Mammah haka shima take samu a garesa, ta sanadin hakan shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, daga karshema ta juye soyayya. Kowa yaji daɗin hakan a dangi, dan babu wani ja'inja aka yanke zancen aurensu. Bayan bikin su da kusan shekar biyu babu wani labari koda na ɓatan wata daga wajensu, babu kuma wanda ya damu da hakan sai ni dana farajin damuwa. A wani zuwa da tayi Nigeria na takura mata mukaje Doctor ya dubata, inda mukaci karo da mummunan labarin daya nema zautani, dan ita koma a jikinta saboda ƙuruciya na ɗawainiya da ita a lokacin. Doctor ya tabbatar mana akwai wani tsiro daya toshe bakin mahaifar Farah gaba ɗayanta. Yanda da wahala ace ciki ya shiga, kodama ya shigan bazai zaunaba. Na bukaci ai mata aiki a ciresa idan zai yuwu, sai ya tabbatar mana taɓashi babbar matsalace, dan zata iya rasa ranta, sannan basu da wani maganin da zai iya gusar da shi a yanzu haka dai. Naci kuka sosai na kuma shiga damuwa da tunanin neman mafita ma yar uwata. Da farko dai son ganin jinin autarmu yasani damuwar, amma dalilin shigowar wasu maƙudan kuɗi ga Abdul-Mutallab da zantukan danginsa na ya ƙara aure ya far canja alkiblar tunanina, zuciyata ta fara rayamin idanfa ƴar uwata ta haihu da shi komi ya tara mallakintane ita da ɗiyanta. Idan kuma nayi sakacin hakan suka aura masa wata akwai matsala tunda likita ya tabbatar mana akwai matsala game da mahaifarta ita. Wannan tunanin ya sani ɗaukarta a wani zuwa london da nayi muka fara bin likitoci ba tare da sanin Abdul-Mutallab kosu Mammah ba. Sai dai duk inda mukaje amsar dayace mahaifarta nada matsala, kuma irin bayanin wancan likitan suma suke mana dai. Hankalina ya ƙara tashi haka itama nata, dan haushin rashin damuwarta yasani zama na fahimtar da ita. Nasha takaici ganin daga baya ta nuna ita fa ba komai bane, tunda Abdul-Mutallab na sonta tana sonshi ko bata haihuba babu damuwa, ballema bata fidda ran a gaba su samuba dan bata yarda da maganar likitocinba ALLAH ne maiyi. Duk da gatan da mukema Farah na tsiya nasan tanada zurfin tunani da aiki da hankalinta matuƙa, sai dai banyi zaton zata kasa fahimtataba musamman dana san tanada kishi mai zafi irin namu musamman akan Abdul-Mutallab. Lokacin da suke cika shekaru uku da aure kakarsa ta ƙara bijiro masa da zancen aure a time ɗin sunzo Nigeria tare, hankalin Fara ya tashi matuƙa, dan tanada tsananin kishi”...........✍        


No comments

Powered by Blogger.