Makauniyar Kaddara 61
Page 61*
.............Hannunsa yasa a wuyanta bayan ya sauke little ɗin yana lallashi dan kuka yake nemanyi dan an saukesa a wuyan mamansa.
Tsatstsare ta da idanunsa masu tarin kwarjini yayi, cikin kulawa yace, “Zazzaɓin dai har yanzun?”.
Kanta taɗan jinjina masa batare data kallesaba. A mamakinsu sai gani sukai shima little dake jikinsa ya saka hannu a wuyanta kamar yanda AK yayi, yakuma kwaikwayi zancen daya faɗa. “Zazzaɓine har yanju?”.
Kallon juna sukai suka saki murmushi lokaci guda haƙoransu na bayyana a waje. dan yanda yaron yayi maganar cikin serious dolene kai dariya. Shiko da yayi ko'a jikinsa, dan saima ya miƙe saman gadon ya hau tsallensa.
AK daya samu ya danne dariyarsa da ƙyar sai murmushi ya kamo hannun Zinneerah daketa faman kare bakinta dan da gaske dariyar ke cinta itama amma dai taƙi yarda tayi sai murmushi. “Yaron nan wayonsa yayi yawa, minene sirrin?”.
Ƙoƙarin shanye dariyarta tai da faɗin, “Kawai dai danya tashi cikin yarane”.
“Uhmyim, su Sadiq sun iya raino kenan?”.
Ɗan kallonsa tai mamaki sosai a fuskarta, a tunaninta ina yasan su sadiq har haka. Murmushi yay mata cike da basarwa ya miƙe. Batare daya ƙara cewa komaiba ya fita a ɗakin, ajiyar zuciya kawai ta sauke da juyawa ta kalli little dake cigaba da tsalle-tsallensa hankali kwance. Sai kawai ta yaye bargon ta sauka baki ɗaya duk da kuwa dai tanajin zazzaɓin har yanzun.
Bata sake ganin AK ba sai da akai magriba, ta idar da salla kenan tana ninke sallaya, little na gefe zaune yana raira kukan makesa da tai saboda ɓarna da yake neman mata a mirror ta hanashi yaƙi hanuwa AK ya shigo. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa yana maidawa ga little ɗin. Wajensa ya nufa, ya kamashi ya ɗaga jikinsa yana murmushi, “Wai mi akaima sojan nan ne?”.
Zinneerah little ɗin dake cigaba da kukansa ya nuna. AK ya kalli Zinneerah ɗin shima, “Mami mi mukayi haka aka samu kuka?”.
Ɗan kallonsu tayi tana harar little ɗin, cikin muryarta datai sanyi saboda zazzaɓin da takeji tace, “Ɓarna zaimin nace ya bari yaƙiji shiyyasa na make hannun”.
Hannu yasa yana sharema little ɗin hawayen, “Handsome babu ƙyau a hana mutum abu ya ƙi bari, kaga Mami bata da lafiya ma uhmyim?. Ce mata sorry”. Yay maganar yana matsawa gabanta.
“Mami Shoyi”. Little ya faɗa jin AK ɗin ya kirata Mami.
Ɗan hararsa ta ƙarayi ta ɗauke kanta kawai. AK ya riƙo hannunta, dole ta sake ɗagowa ta dubesu. Sai dai narkakken kallon da yake mata yasata janye idanunta. Batare da ya damu da yanda tayinba yace, “Ai munce ayi haƙuri ko”.
“Nima na haƙura ai, zanje na kwantane sanyi nakeji Yayanmu”.
“A'a ba kwanciya zakiyiba, shirya asibiti zamuje”.
Kanta ta jinjina masa, dama jikinta doguwar riga ce da hijjab. Dan haka sai kawai taɗan ƙara turare a jikinta tabi bayansu dan shi harya fice ɗauke da little.
A general falo ta iskesu, batare da yayi maganaba ya nuna mata hanya alamar suje. Gaba tai ya bita a baya ɗauke da ɗansa. Shine ya rufe ƙofar sannan suka ƙarasa ga mota. Ganin little kamar zai takurasa a wajen tuƙin yasata miƙa masa hannu alamar yazo wajenta, amma sai ya noke.
Baki ta taɓe da hararsa ta ɗauke kanta. Sai da ya tada motar suka fice a gidan yay magana batare daya kalletaba. “Nikam wannan harar ɗan akemawa ko baban? Tunda shima mai laifine?”.
Gefe tai da kanta tana murmushi da faɗin, “Kai Yayanmu ni dai wlhy banceba”.
Shima murmushin yayi da sumbatar kan little dake cinyarsa suna tuƙin tare. Daga haka ya maida hankalinsa a tuƙinsa itako ta lafe cikin kujera ta lumshe idanu.
Sun isa Shira hospital inda suka samu ƙyaƙyƙyawar tarba ga ma'aikatan. Anata kallonsu cike da sha'awa da birgewa. Yayinda suke nuna son ɗaukar little amma sai yaƙi yana dai maƙale da babansa. A office ɗin Dr Mahmud suka yada zango, shima ya tarbesu cike da murna da girmamawa yanata tsokanar Zinneerah. Yayinda ya ɗauka little kuma da ƙyar.
“Ranka ya daɗe kune da dare haka? Lafiya dai ko?”.
“To da sauƙi dai madam ce babu lafiya”. AK ya faɗa yana duban Zinneerah da kanta ke ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.
“ALLAH ya ƙara lafiya, Ko gajiyar biki ce ƙanwarmu?”.
Murmushi kawai tai batace komaiba. Shima sai ya murmusa da mikama AK little. Kafin ya maida hankali wajen mata tambayoyi. Magunguna kawai ya rubuta musu yay kiran wata Nurse a waya ya bata ta sayo. Ganin an kira isha'i suka fita salla suka barta a office ɗin. Suna dawowa ko zama basuyiba AK yace ta tashi suwuce kar dare yayi.
Har wajen motarsu Dr Mahmud yayo musu rakiya, sai da yaga tafiyarsu sannan ya koma ciki.
Daga asibiti AK wani shagon sai da wayoyi ya kaisu, a mota ya barta suka shiga ciki shi da little. Babu jimawa kuwa sai gasu sun dawo ɗauke da leda. Daga haka gida suka nufa bayan ya sake tsayawa ya sai musu gasashshen kifi.
Sosai Zinneerah kejin barci lokacin da suka shigo gidan, fahimtar hakan da AK yayi ya sakashi dakatar da ita a falon farko na sashenta. Tsareta yay sukai zaman cin kifin tare, bama wani sosai taciba dan bakinta babu daɗi. Ya bata magungunanta ta sha taɗan tattare wajen ta shige. Shima sashensa ya nufa da little. Acan yay masa wanka, sai dai babu kayansa kuma balle na barci. Shaf yama manta da batun amso masa kaya. Pant dinsa kawai ya maida masa ya kwantar dashi a gadonsa dan sai hamma yake. Shima shirin barcin yayi sannan ya nufi sashen zinneerah. Isketa da yay har tayi barci ya sashi fitowa ya dawo sashensa. little ya ɗauka yaje can shima kawai suka saka yaronsu tsakkiya.
Zinneerah batasan da zamansu a ɗakin ba sai da asuba data farka, dan ta rigashi tashi. Ta jima tana kallonsa shi da little zuciyarta fal saƙe-saƙe iri-iri. daga ƙarshe dai ta mike ta shiga toilet. AK da shima ya jima da farkawa ya bata damar cigaba da kallon nasune tana shigewa ya miƙe. A bakin gadon ya zauna harta fito sanann. Ɗan kallonta yayi yana lumshe ido, muryarsa a dasashe irin ta wanda ya tashi barci yace, “Naje massallaci”.
Tace, “A dawo lafiya”.
__________________
AK bai dawo gidan ba sai da rana tai ɗan haske. Ya shigo ya iske Zinneerah nata aikin kimtsa gidan kamar ba itace mara lafiyaba. Har ƙasa takai ta gaidashi. Ya amsa mata da kulawa yana tambayarta yaya jikinta. “Alhmdllh naji sauƙi ai”. Ta faɗa a hankali.
“Masha ALLAH”. Shima ya amsa mata kafin yace, “Ina little?”. “Bai tashiba har yanzun”. “Okay bara to na watsa ruwa dan inason fita da wuri”.
Kanta kawai ta jinjina masa. shi kuma ya juya zuwa sashen sa inda ta fara gyarowa duk da ba wani datti baneba.
Tana kammalawa bedroom ta koma tai wanka. Kammala shiryawarta kenan little ya farka. Wankan shima tai masa, ta shafa masa mai tana tunanin yanda za'ayi akan kayan da zaisa.. A dai-dai lokacin ta jiyo ƙarar doorbell. Little ɗin ta sauke daga kujerar mirror da yake a tsaye tana faɗin. “Ka jirani, idan wani abuna yay motsi anan kaima saina motsa maka jikinka da duka”. Daga haka ta ɗauka gyale ta fice.
Khalipha ne da kansa ɗauke da kayan little da breakfast ɗinsu. Ta matsa ta bashi hanya tana gaishesa. Cike da fara'a ya amsa mata idonsa akan little da batasan ya biyo bayantaba. “Uhm my boy ashe anan ka kwana?”. Ya faɗa yana mika mata basket ɗin ya ɗauka little daya nufosa baki a washe. Dan shi indai mazane to baya jimawa yake sabo dasu. Shiyyasa ko a gidan da wuri ya gama haddace samarin gidan. Kai tsaye sashen AK ya nufa abinsa. Itama sai tai ƙoƙarin juyawa nata sashen.
Kamar jira tana shiga aka sake danna doorbell ɗin. Sake dawowa tai zata buɗe taci karo da Khalipha ya fito shima. Barinsa tai ya ƙarasa ita kuma ta tsaya jiran ganin wanene?.
Farah ce ta fara shigowa idanunta jajur alamar tasha kuka. Sai Aunty Zakiyya a bayanta, Mammah na biye dasu. Ba karamin bugawa zuciyar Zinneerah tayiba da cin karo da Farah, tai wani diri-diri da ita dan koba komai dole taji hakan tunda ta aure mata miji. Jin muryar Mammah datai ya sata sake duban bayan Farah ɗin duk da kuwa sau ɗaya ta taɓa ganin Mammah ɗin.
Wani irin mahaukacin bugu ƙirjin Zinneerah yayi ta zabura baya batare data saniba. Wani irin duban aunty Zakiyya da itama ɗin dai ita take kallo takeyi baki a hangame.
Har abada bazata manta da wannan fuskarba. Koda shakara ashirin tai kuwa balle uku kacal. “H....h...hajiya?!”.
Zinneerah ta faɗa cikin rawar baki matuƙa. Wanda hakan yay dai-dai da fitowar AK da yasan da zuwan su Mammah ɗin a yanzu-yanzu da Mahma ta kirasa take sanar masa nan suka taho batare da sanintaba. Yayi duk yanda zaiyi karya bari Zinneerah ta haɗu dasu. Sai dai kuma hakan bai yuwuba tunda aikin gama ya gama.
Ba shi da Khalipha ba, hatta Mammah da Farah kallon Zakiyya suke da mamaki ganin yanda tai wani diri-diri tana kallon Zinneerah ɗin itama. Dan da hasashe kawai take, amma muryar Zinneerah ɗin ta tabbatar mata da eh lallai itace duk da ta ƙara girma ta kuma canja sosai.
“Kin santa ne?”.
AK ya faɗa idonsa akan Zinneerah. Kanta ta shiga jinjina masa, kafin tace, “Itace Hajiyar nan ta katsina da aka kaini gidanta”.
“What!!” AK ya faɗa duk da kuwa dama aunty Zakiyya suke zargi.
Mammah da abun ya harzuƙata ta dakama Zinneerah tsawa. “K!! Shashasha daga ganinmu sai kice wani itace hajiyar da aka kaiki katsina wajenta. To aka kaiki kikai ubanmi acan?”.
Kafin Zinneerah tace wani abu AK yace, “Mammah kwantar da hankalinki Please. Inaga ai magana ta ƙare kawai. Khalipha kira Faisal kace ya kai matan nan gidan Baffah gamu nan zamu samesu acan”.
“Abdul-Mutallab banson iskanci, ya ana wata maganar kana ɗakko wata kuma?”.
“Nace ki kwantar da hankalinki Mammah, kumuje can gidan kawai, dan akan wannan sanin junan da sukai akwai magana”.
“Magana!?” Mammah ta faɗa tana kallon aunty Zakiyya da sai yanzu ta samu bakin cewa wani abu.
A firgice tace, “Magana! Dawa za'ai maganar?. Dan kawai ta kirani da hajiya sai kace wani akwai magana. Ke dan ubanki a inama kika sanni dazaki wani kirani da hajiya?”.
Mamaki ƙarara a fuskar Zinneerah tace, “Hajiya kin manta dani? Nicefa wadda wata hajiya Haule mai jiki ta taɓa kai miki har bani da lafiya kikaita kaini asibiti ana dubani, nikuma tsoro ya sani gudowa bayan na warke dan canake gidan yankan kai kika kaini”.
Zinneerah ta kara maganar kanta a ƙasa tana tuno komai a ranta tamkar yanzu yake faruwa.
Baki Zakiyya ta buɗe zata sake magana AK ya dakatar da ita. “Please kunga ya isa haka, kumuje can gidan tunda dama ai akwai maganar da akace za'ai bayan gama taron nan”.
Mammah ta kallesa, dan harga ALLAH ita tama kasa fahimtar ina suka dosa kai tsaye. Ta buɗe baki zatai magana sai ga Mahma data biyo bayansu, sallamar da tayi ya sakasu juyawa su duka suna kallonta.
Ganin yanda sukai cirko-cirko yasa Mahma faɗin, “Lafiya? Mike faruwa anan?”.
Mammah da dama magana ke bakinta tace, “Wlhy Addah nima da nake tare dasu anan na kasa fahimta, waifa muna shihowa gidan nan sai yarinyarnan mara kunya take kiran Zakiyya wai da hajiyar da aka kaita gidanta a katsina”. Tai maganar tana nuna Zinneerah da al'amarin masu ya ɗaurema kai itama. Dan harga ALLAH ita bataga wani abun tada jijiyar wuya anan ba. Daga ta nuna ta santa ai bai kai ya zama tashin hankaliba.....
Mahma data ɗauke kanta daga kallon Zinneerah da Mammah ke nuna mata ta maida ga AK, kai ya jinjina mata kawai. Hakan ya sata fara maganar data katsema Zinneerah tunanin da tatafi.
“Kunga duk a ajiye wannan shirmen nake ga. kuzo muje can gidan dama Kabeer ne ya kirani wai yanason magana damu akan Adilah”.
Tuni Mammah ta saki batun aunty Zakiyya da Zinneerah ta maida hankalinta ga Mahma wajen faɗin, “What!. Mi kuma yake nufi da zancen Adilah? To wlhy Addah wannan karon duk abinda zanyi karki tsayar dani, dan dama yau-yau ɗinnan nai niyyar zuwa har gidan na tarkatota itama gobe zamu wuce Morocco”.
Mahma ma nuna ɓacin ranta tai ta hanyar cewa, “Nima ai shiyyasa na biyoku nan ɗin, dan a wannan karon ba ɗagama Kabeer ƙafa zanyiba kuwa koda na mintuna ɗaya ne. Ku muje can, idan an gama mazo ayi wannan batun nasu Zakiyya ɗin”.
Kafinma Mahma ta rufe baki Mammah takai ƙofar fita, aunty Zakiyya da gaba ɗaya take a harmutse tai saurin fara magana cikin borin kunya. “Kuje, ni dai zan wuce katsina idan kun gama kwa sameni acan”.
AK daya saki wani murmushin mugunta yace, “Ai hardake za'aje hajjaju, dan maganace data shafi family, idan kuma kin fidda kanki a cikinmu sai muji”.
Wani shegen kallo ta bisa da shi mai kama da ruɗani da tsana, ta buɗe baki zatai magana Mahma ta katseta. “Kunga nifa banason wannan fitinar taku, ke Zakiyya wuce muje, da an gama maganar ai baki ɗaya zamu wuce komai dare”.
Badan Zakiyya taso ba tabisu, Farah dai ko motsi bataiba dan da ido AK yay mata gargaɗin tsayawa. Khalipha kuwa dama tuni ya fice shi da Little.
Sai da AK yaji fitar motarsu daga gidan sannan ya kalli Farah da Zinneerah ɗin. “Kuma kuje ku shirya zamu bisu”.
Jiki a sanyaye Zinneerah ta kaɗa masa kanta, sashenta ta nufa zuciyarta duk babu daɗi da abinda ya faru. Duk da dai tasan ita mai laifice kodan gudowar da tai bada sanin hajiya ba batai tunanin abin zaiyi girman haka ba tunda da ya wuce kusan shekara huɗu fa kenan.
Zinneerah na shigewa Farah tai saurin bin bayan AK, kusan a tare suka shiga falonsa. babu zaton tana biye da shi yaji ta rungumesa ta baya tana sakin kuka. Shiru yay kawai yana saurarenta dan yasan kukan mi takeyi, shi shaidane akan kishin Farah, amma yana ƙara hauhawane bisa karatun Mammah da Zakiyya.
Dalilin dayasa kuwa ta dawo gidan a yau Mahma ta sanar masa jiya ta zaunar da ita tai mata nasiha mai ratsa jiki, tare da tuna mata abubuwa masu yawan gaske waɗanda suka tada mata hankali, tun a daren tace zata taho nan gidan shine aunty Zakiyya ta rufeta da masifa. Ta ringa zaginta ta uwa ta uba daya kai har Farah kiran Abbansu ta sanar masa. Shine ya buƙaci ta haɗashi da Mahma suyi magana. Itako Mahma bata ɓoye masa komai dake faruwaba harma wanda su su Farah basu san ta saniba. Ya nuna matuƙar tashin hankali saboda shi mutumne nagartacce, ko zaman Farah a hannunsu dan anfi karfinsane kawai, amma duk sauran yayunta suna tare da shi sai dai irinsu Zakiyya da sukai aure. A yanzu hakama soyake yay murabus a ɗora babban yayansu Farah ɗin a karagar mulki. Zantukan da Mahma ta sanar masa ɗinne ya sashi sanar dasu yau zaizo kano, Farah kuma ta tabbatar ya sameta a gidan mijinta inba hakaba wlhy sai ya saka AK ya saketa saki uku, kuma ta dawo zaman Nigeria cikin masarauta.
Itako a duniya ta tsani zaman masarautarsu saboda yanda ake komai a takure, ga matan babansu sam basa ƙaunarsu saboda son da baban ke nuna musu a dalilin rashin mahaifiya. Dama can kuma yaso mahaifiyarsu sosai dan tunkan tabar duniya matan sun mugun tsanarta itama. Abu na biyu maganar sakin da yace zaisa AK ya mata. Tasan Abbansu sarai, wlhy zai iya sakawa AK ɗin ya saketa dan kaɗan daga aikinsa. Shima murɗaɗɗen mutumne mai tsayawa akan gaskiya duk ɗacinta.
A hankali AK ya janyeta daga jikinsa yana zagayo da ita gabansa. Ƙyawawan idanunsa masu cikar kamala da kwarjini ya zuba mata hannayenta duka biyu riƙe a cikin nasa. Sake fashe masa da kuka tayi kishinsa mai tsanani yana taso mata, amma tanata ƙoƙarin ganin ta danne dan duk runtsi bata iya rabuwa da shiba saboda tana sonshi.
Karan farko AK ya saki murmushi da kai hannu ya share mata hawayen dake sauka a fuskarta. “Nifa kinsan banason kuka ko?”. Ya faɗa yana rungumota jikinsa dan shima yanason kayarsa.
Ƙanƙamesa tai tana sake fashewa da wani kukan, “Dan ALLAH Yah Abdul-Mutallab kayi haƙuri wlhy Abbah zai iya rabamu, ka taimakeni karka faɗa masa na tuba”.
“Toni dama miya haɗamu da har zan sanar masa?”. Ya faɗa yana ɗago fuskarta. Cigaba yay da faɗin, “Kece kike biyema su Mammah ai dama, suna amfani dake wajen biyan buƙatunsu batare da kin fahimtaba. Sannan kina barin kishinki na rinjayar tunaninki bayan kinsan ina sonki. Sokike ne na dinga binki kamar wani sakarai dan kawai ki tabbatar ina sonki? Ko sokike nabar mahaifina da ƴan uwana dan kawai ina sonki Farah? Wannan abun shina dinga tsoratar miki dama. Randa zan iya ƙosawa da halayarki na fara tunanin ƙara aure. Iyayena da baki ragamawa suma su bani goyon bayan yin. Amma sai kika kasa fahimta, ke ga mai Mammah da aunty Zakiyya ko?. Gashi nan duk yanda nake ɓoyema Maimartaba halayyarki sai da takai kin tonama kanki asiri da kanki”.
“Na tuba wlhy, dan ALLAH ka taimaka karka faɗa masa yanzuma, dan wlhy yace yana hanyar zuwa kano. Na rantse yana tambayarka ka faɗa masa sai ya raba aurenmu kasan halinsa”.
“Idan kinmin alƙawarin zaki nutsu, ki komamin Farah dana sani a baya, mai tattalina da ƙaunata bazan faɗa masaba. Sannan duk abinda za'a tattauna a gidanmu yanzu zaki faɗi gaskiyar abinda kika sani bazan taɓa yarda a rabamuba koda kuwa zan hukuntaki da laifinki ne”.
Batare data nutsu ta tace zantukansa ba tace, “Na amince wlhy Yah Mutallab”.
Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe a kanta, tare da sunbatar goshinta da laɓɓanta. A dai-dai lokacin da Zinneerah ta shigo falon da sallama, hannunta ɗauke da basket ɗin da Khalipha ya kawo musu breakfast. Dan harta fito saita tuna ko karyawa basuyiba. Shine tai tunanin kawo masa koshi zaici dan ita kam bazata iya shan ko shayi ba.
Wani irin bugawa ƙirjinta yayi, tai saurin ja da baya jikinta na rawa, dan shigowar tata yayi dai-dai da ɗaura lips ɗinsa akan na Farah, itako ta cafke tana kara rungumesa kamar yanda shima ya sake rungume abarsa.
Jin basket ɗin hannunta zai faɗi ya sakata saurin ajiyewa a ƙasa ta juya da sauri ta fita dama a farkon shigowa take.................✍
Leave a Comment