Makauniyar Kaddara 6
Page 6
.........Tun bayan wucewar su Zinneerah kusada Inna ta kasa zaune ta kasa tsaye. Ba komai ke mata kai kawo a rai ba sai maganar Gajeje da take cewa babu wanda ya binciki Zinneerah yaji ina taje. Idan har bata ɗauki matakiba to lallai abinda bata buƙatar ya fito da ga bakin Zinni shine zai fito, dan suna dawowa gida kowa zaiso jin ina taje ɗin? Yaya akai kuma ta dawo?.
Tsulum ta miƙe da ga zaman da tayi a bakin gado, ta rarumo yamutsatstsen gyalenta daketa tsamin dauɗa. Tana ƙoƙarin warwaresa ta yafa Magajiya ta shigo ɗakin...
“A'a, Asabe ina zuwa kuma?”.
Ɗan duru-duru tayi na alamun rashin gaskiya. Sai kuma tai saurin faɗin, “Uhm Magajiya zanje nan ƙauyen kwangi ne na amso kuɓewar dana bada a daka saboda miya. Na sha'ahwa gaba ɗaya sai yanzu na tuna. Gashi Atine tace tuwo aka ɗora yanzu da za'aci da rana. Kinga kuma dole ne miyar ɗaurin aure ma na gobe a haɗa da miyar yauƙi dan taushe ɗin nan ba isa zataiba”.
Kai Magajiya ta ɗan kaɗa mata, sai kuma tace, “Amma nikau da dai kin aiki ko Tinene ko Sa'a mana. Ke da mutane keta shigowa kuma ace kinje wani waje ai babu daɗi. Sannan waɗanan masu tahiya asibitin ya kamata ki jira kiga dawowarsu ko”.
Nannauyan numfashi Inna ta sauke tana ƙyaɓe fuska. Tace, “Kinga Magajiya hita batun waccan watsatstsiyar yarinyar. Dan babu mai ɓata mani taro aradu. Maganar amso kuɓewa kuwa gara naje da kaina. Dan daga Tinene har Sa'a mashiririta ne da kike ganinsu”.
Magajiya tace, “To ni haɗani da Tinenen muje. Ai in dani dai batacewa bata zuwa ko?”.
Sosai wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ya turniƙe zuciyar Inna. Ji take kamar ta kaima Magajiya duka. Da ƙyar ta shanye abinda ya tokare maƙoshinta ta ƙaƙaro murmushi dan tasan nacin Magajiya batun yanzu ba. Tace, “To nahi yarda da wagga shawarar kau. Bara naga giccin Tinenen saina hiɗi maki ku tahi”.
Da to Magajiya ta amsa, tare da ɗaukar buhun da garin masara ke ciki wanda dama shita shigo ɗauka ta fita. Da wata muguwar harara Inna ta raka bayanta tana jan tsaki. Ta sauke gyalen nata tana ƙudundunesa ta cusa cikin lalitar bujenta na ciki. Ganin ya kwanta babu mai ganewa ta fito a ranta tana ayyana. (Ai idan kinsan wata bakisan wataba magajiya).
Shigewa tai cikin masu hidimar aikin abinci ta cigaba da harkokinta. Sai da taga kowa hankalinsa baya kanta tai wuff zuwa bayinsu tabi ta cikin dannin geza da akai musu sakamakon zubewar katangar bayin lokacin damuna daya wuce. Har yanzu kuma ALLAH baiba baba damar gyarawa ba.
Saurin zaro gyalenta tai ta warware ta aza bisa kai. Cike da sauri da sassarfa ta dinga ratsawa ta cikin gonaki dan kar wani ya ganta........
★★★★
A asbiti kam bayan tabbatar da Zinneerah ba suma tayi ba ruɗanin maganar likitace kawai ta haifar mata da hajijiya sai suka saka mata ƙarin ruwa. Hankalin su Gwaggo Laritu bai kwanta ba sai da likita yay musu bayani.
“Ku kwantar da hankalinku tana cikin ƙoshin lafiya. Kuma Alhmdllhi bama suma tayiba. Yanayin da take cikine ya kawo hakan, da alama kuma ko karin kumallo bataibama kuka fito”.
A kusan tare suka sauke ajiyar zuciya. Rabilu yaron Kawu Haruna daya kawosu yay saurin faɗin, “Likita to ko za'a samo mata wani abune taci?”.
“Eh za'a iya. Amma a yanzu dai mun saka mata ƙarin ruwa ta samu barci. a cikinsa kuma akwai abinda zai taimaka mata akan yunwar, da alama dai kai ne mai-gidan nata ko?”.
Murmushi kawai Rabilu yayi batare da ya amsawa likitan maganarsa ba. Sai dai Cikin ƙarfin hali duk sukai masa godiya. Amma a ƙasan ransu su kaɗai sukasan irin tashin hankalin da suke ciki game da wannan ciki na jikin Zinneerah. Suna tsananin tausayin yarinyar saboda halin data tsinci kanta a ciki a gidansu na rashin mahaifiya. Ga yayansu shi da babu duk ɗaya a gidansa saboda makircin matarsa Asabe. Sunyi iya ƙoƙarinsu dan ganin sun maidosa hayyacinsa tun tuni amma Asabe ta sake shiga ta fita ta raba tsakaninsu da shi. A yanzu haka ko mu'amula bayayi da kowa a cikinsu, ko maganar auren Karima bai sakasuba sai ji sukai a gari. Abin bai ɓata musu rai ba sosai saboda sunsan baya a cikin hayyacinsa ne sam. Yanzu haka maganar cikin nan Sa'a ce taje ta sanarma Gwaggo Laritu tana kuka, kuma da'ace ba Zinneerah abin ya shafaba cikin ƴaƴan Inna ne ko takansu bazasubi ba. Lallai lokaci yayi da zasuyi wani abu game da gidan yayan nasu kam a wannan karon. Dolene kuma susan wanda ya shiga mutuncin Zinneerah kar rayuwarta ta ƙarasa shigewa cikin garari sunaji suna gani.
Kusan su dukansu haka suka dinga tanani a cikin zukatansu har ruwan da aka sakama Zinneerah ya ƙare, sai dai barci takeyi sosai. Sallar azhar su Kawu suka tafi yi massallaci. Itama Gwaggo Laritu saita fito dan neman inda zata gabatar da tata. Bayan duk sun idan da sallarne Rabilu yaje ya samo musu abinci dan su ɗanci, dan su kansu akwai waɗanda basu karya ɗinba a cikinsu..........
★★★★
Sauri sosai Inna ta dinga zabgawa harta iso ƙauyen mahuta dake can yamma da su. Ƙauyene sosai dan gidajen garin bazasu gaza biyarba ma gaba ɗaya. A farkon shiga garin ta gamu da yara sun dawo ɗibar ruwa rafi. Tsaidasu tai ta ɗiba ruwan tasha sosai tana sauke numfashi a jajjere. Dan ba ƙaramin sauri ta zabgaba a tafiyar tata.
Daga haka ta isa gidan dake ƙarshe a jerin gidajen ƙauyen. Tun a ƙofar shiga zauren gidan ta zabga sallama. Daga ciki akai gyaran murya tare da amsawa, sannan aka bata iznin shigowa. Babu kowa a soron, sai dai akwai ƙofar dake nuna alamun ɗakine, dan akwai labule da takalma a ajiye, sai wata a gefe ta shiga ainahin gidan kuma.
“Gahwaranku dai”. Inna ta sake faɗa tana matsawa ga ƙofar ɗakin. Daga ciki muryar namiji dattijo ta sake amsa mata da “ALLAH yay mana aikin gahwara shigo”.
Labulen ta ɗaga ta shiga ɗakin dake cike da shirgin da zama lissafasu ma ɓata lokacine, sai Dattijon dake zaune yana rubutu a allo da tawwada da alƙalami. Kallonta yay cike da fara'a kamar yanda itama take faman washe haƙwara.
“A'a Asabe ce a garin yau?”.
“Wlhy nice malam kallamu. Kasan gobe ne ɗaurin auren ƴar wajen tawa, gashi kuma banzo na amshi abinda ka ce ba tun kwanaki idan auren yazo. Bayan nan kuma ga watama matsalar datake neman sake taso mani kuma”.
“Tofa babbar magana. Ai dama inata tsumayen zuwan naki, dan kwanaki hudu da suka shige na shigo Danya ɗin nakejin auren yarinyar wajen naki ya tashi. Harma naita mamakin banji daga garekiba”.
“Ayya, ka gahwarceni malam. Abubuwane sukaima kaina yawa a tsakanin nan wlhy. Amma zuwa nanɗin yana raina kodan a shiryamin yarinyar tunda kaima kasan dai yanda abubuwan suke ai”.
Murmushi yayi yana ajiye allon da yake rubutun da gyara zamansa. Ya jawo wani ƙwarya yana tura mata gabanta. “Kinga komai ma na haɗa. dama ko bakizoba ni zanje ɗaurin auren gobe, to niyyata dama naje miki dasu ai”.
“Kai madallah madallah malam kallamu, nagode nagode sosai da wannan karamci naka. ALLAH ya saka maka kaima da alkairinsa”.
“Amin. Yanzu minene gudar matsalar kuma?”.
Nannauyan nishi Inna ta sauke tana gyara zama. Cike da takaici da baƙin ciki tace yarinyarnan da uwarta ta bar mani ciki ya bayyana ga jikinta jiya. Tofa shine shaggun dangin uban nata sukazo sukai tsaye akan lamarin har suna iƙirarin sonjin ina taje kwanaki. Kasan kuma munyi aiki kwanaki akan rihe bakin kowa bai sake tambayarta ina taje. Itama kuma karta hwaɗi ma kowa ɗin. To wlhy yau malam kallamu suna neman ɓalloman aiki musamman ɗiyar wajena dake aure Sanni. Kasan nayi-nayi na rabata da yarinyar abun ya hwaskara”.
Kai malam kallamu yaketa girgizawa yana saurarenta. sai da taje har ƙarshen zancenta ya fara magana. “Kamar yanda na hiɗi maki tun kwanaki uwar yarinyarnan shu'umace ta gaske. Dan duk da kin hiddata a gidan nan bawai ta barki bane, sannan tana aikoma yarinyar da wasu ayyuka, shiyyasa da munyi aiki akan yarinyar baya wani nisa yake warwarewa. To amma ke kin tabbatar akwai cikin kuma?”.
Cikin wata lalatacciyar dariya Inna tace, “Ciki kau akwaishi malam kallamu, dan ƙuru-ƙuru ya bayyana kansa ga mutane”.
“Tohwa babbar magana. Amma yanzu kunsan wanene yay cikin?”.
“Inaaaa! Babu wanda ya sani, inada tabbacin acan inda nasa ƙawata ta kaita aikataune wani ya ɗura mata shi. Kasan yaran birnin nan akwai basira. Balle ƴar banzar yarinyar tanada ƙyau irin na uwarta. Yanzu haka jiran Hajji Lanti nake tazo naji miya hwaru. Amma itama bullum kakeji kamar an aiki bawa garinsu”.
“Shikenan, yanzu dai ayau ɗinnan zanyi wani aiki. Kamar dai yanda na hwahinta ke dai bakiso yarinyar ta hiɗi ta sanadinki tabar gari ko?”.
“Kwarai ko Malam Kallamu wannan shine hwatana. Dan nahi son kowa ya dinga kallonta da hita tai yawon tazubar ɗinta harta samo wannan cikin. Nihwa idan san samunane tabarma garin baki ɗaya yanda mutane zasu sake yarda komawa tai wajen farkan nata. Bazan ɓoye makaba zaman yarinyarnan a gidan na baƙantan rai, dan ji nake kamar har yanzu uwarta na tare damu, duk da na nisantata da garin tuni, to itama ɗiyar sonake na nisantata da Danya har abada, nahison na rayu gidan mijina dagani sai ɗiyana aradu”.
Kai Malam Kallamu ya jin jina yana murmushi saboda shima mugunne na haƙiƙa, shiyyasa tasu tazo ɗaya da Inna. Kuma wai a haka shiɗin malamine, harda almajirai a ƙarƙashinsa yana basu ilimi🤦🏻.
Ya sake haɗa mata abubuwa da yawa. Tare da tabbatar mata a daren yau zaiyi wani aiki akan Zinneerah. Ta ajiye masa kuɗi tana masa godiya ta taho akan sai gobe yazo ɗaurin aure zai tahoma da Karima wani haɗin neman sa'a a gidan Babawo.
(Humm ALLAH ya shirya mana zukatanmu. Babu wani banza daya isa baki ƙyaƙyƙyawar rayuwa a duniya sai UBANGIJI. Domin shima idan kura na maganin zawo yayma kansa mana. Idanma asirin kikayi akan wani kikaga yacisa dama can ƙaddararsa kenan koda bakiyi komaiba tunda ALLAH yay alƙawarin shigarsa wannan halin saiya shiga ɗin. Abindama jahilai suka gaza ganewa shine. Da yawan jarabawa tsanice na kaiwa ga nasarorin rayuwa ga bawa. Dan da wahala kaga mutum yaci wahala a rayuwarsa daɗi da farin ciki basu biyo bayansaba. Bawai dole sai a duniyaba. dan UBANGIJI yay mana alƙawarin samun babban tagomashi a lahira da yafi na duniyar komai. Dan kaci wahala a rayuwarka ba dolene sai kayi arziƙiba a ƙarshe. Ba dolene saika zama mai ɗaukakaba a ƙarshe. ba dolene saika zama tauraron al'umma ba a ƙarshe. UBANGIJI zai iya sakanka makane ta hanyar da kaima bakai zatoba. Amma fa saika zama mai juriya da haƙuri wajen karɓar jarabawarka da ƙaddararka. ALLAH kai riƙo da hannayenmu a komanmu😭🙏🏻).
★★★★
Bayan farkawar Zinneerah a barci kusan ƙarfe huɗu suka baro Kusada zuwa danya. Kallo ɗaya zaka fahimci ransu a dagule yake su duka. Zinneerah kam bama a iya tantance halin tashin hankali da ruɗanin da take a ciki. Sam zuciyarta da ƙwaƙwalwar kanta basa aiki irin na kowanne mutum. Abubuwa da yawa ke zuwa mata a rai game da wannan ciki, har kashe kanta ta ayyana yi amma wani ɓangare na zuciyarta ya ƙwaɓe akan wannan ba mafita bace.
Tunda mashinansu suka shigo garin idanu caa a kansu. A take ƙananun magana suka fara tashi akan wai ankai Zinneerah kusada ne an zubar da ciki. Su dai basu san sunayi bama. Wani matsanancin tsoro ne ya shiga zuciyar Zinneerah ganin sun iso gida. da ga ita sai Gwaggo Laritu suka iya shiga gidan. Su kawu juyawa nasu gidajen sukai abinsu dan basusan yanda zasu tunkari yayansu da wannan magana ba. Gashi likita yace abar Zinneerah ta huta na kwana biyu kamar yanda jikinta ke buƙata.
Mata ne cike da gidan danƙam anata arerewa da guɗa. Dan masu kiɗan ƙwarya Inna ta kira suke wasa a gidan wai yau take nata yinin bikin. Da farko har suka shigo gidan sukama kusa kaiwa ɗakin kwanan su Zinneerah babu wanda ya kula da su. Suna gab da shigewarne Inna ta hango Zinneerah. A tsawace tace, “K! K! K! Dakata mani. Masu kiɗa ku saurara kaɗan ina zuwa”.
Kamar wadda tai busa da sarewa a kunnuwan jama'a a take gidan yay tsit, hankalin kowa ya dawo kan Zinneerah da Yaya Gajeje yasata saurin nufosu itama. Kusan a tare suka iso gaban Zinneerah ɗin, inna ta kalla Gwaggo Laritu datai kamar batajiba tana neman shigewa ɗakin su Zinneerah ɗin.
“Lallai ko ba'a faɗaba yanayin da kuka shigo mani gida kawai ya tabbatar da zancen ciki......”
Da sauri Gajeje ta katseta da faɗin, “Haba Inna wacce irin maganace haka? Wannan ai zancene na cikin gida ko”.
Harara Inna ta watsama Gajeje, ta kai hannu ta finciko hannun Zinneerah da kanta ke a ƙasa hawaye masu zafi na ziraro mata a saman kumatu. Hannu tasa ta yaye hijjab ɗin jikinta ta jefar. Ta kama rigarta zata cire Gwaggo Laritu ta riƙeta a fusace. “Wlhy! Wlhy wlhy kinji na rantse sau uku, inhar kika hiddama yarinyar nan riga yau saina nuna miki ni jinin gidan baduku ce Asabe. Wai kina tunanin ana tsoronkine ko me? Mi yarinyarnan ta tsare maki a gidan nan ne wai shin? Idan ma cikkinne da gaske a jikinta ai kece silarsa. Dan kece kika hana mata rayuwa zaman lahiya kamar yanda kika hana ubanta. Ya auro mahaifiyarta dan yaji sauƙi kika shiga kika hita sai da kikaga tabar gidan saboda son zuciyarki. Wama yasani yanzunma ko kece kika biya aka lalatama yarinya rayuwa, dan wlhy duk abinda akace kinyi Asabe nasan zaki iya mahiyinsa saboda son duniyarki”.
Tofa babbar magana. Waɗan nan zantuka na Gwaggo Laritu a take ya hargitse gidan, kafin kace mi taron biki ya zama taron faɗa da bala'i. Tun anayi a cikin gida har aka koma ƙofar gida, abu kamar wasa sai ga ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa dai faɗa ya juye tsakanin dangin Baba dana Inna. Yayinda jama'ar gari suka rabu gida biyu, wasu na goyon bayan Inna wasu na goyen bayan dangin Baba da Zinneerah. Abu yay tsamari har magriba babu alamar zasu sarara, daga ƙarshe dai sai da zance ya kaisu ga gidan mai-gari daya aiko aka tattaresu zuwa can.
Sosai zancen ciki a jikin Zinneerah ya tayarma mai-gari hankali. dan har ransa yakejin ƙaunar yarinyar da tausayinta. Tun a randa sukazo shari'arnan shi kaɗai yasan abinda ke ransa game da Zinneerah. Dan ya ɗaukama kansa alƙawarin zai tsaya mata tai karatu, kuma ɗansa dake karatu yanzu haka a Katsina shi yake burin zama mijinta. Sai kuma gashi yau wannan magana maiban tashin hankali ta ɓullo rana tsaka.
A yau ma tambayar duniya anma Zinneerah akan wanene mai ciki tace ita bata taɓa aikata iskanciba, dan haka batasan ina ta samo ciki ba. Lallai wannan al'amari ya kai a kirasa MAKAUNIYAR ƘADDARA, ita da ciki ke jikinta batasan yanda samuwarsa ta wanzuba, su kuma dake tuhumarta ina zasu kama?.
Ganin dare yana neman rufawa mai-gari yace suje gida gobe idan ALLAH ya kaimu zai nemesu, dan wannan magana babbar maganace dolene sai sunje ga hakimin kusada ko a samo bakin zaren a can. Wannan magana ta tadama Inna da Zinneerah hankali matuƙa. Ita Inna tsoronta ALLAH tsoronta a gano gaskiyar da sa hannunta Zinneerah ta tafi Katsina. Saukinta ma Hajji Lanti bata dawo garinba ai tun tafiyar da tai dasu Zinneerah ɗin. To amma tasan akaje gaban hakimi ai ca za'ai sai wajen ƴan doka (Police) da ga haka kuma sai wajen alƙali. Lallai tsugunne bata ƙare ba kenan, ba burinta kenanba, babban burinta kawai Zinneerah tabar mata garin baki ɗaya dan bata ƙaunar ganinta a cikinsu kamar yanda ta tsani mahaifiyarta sanda tana tare da su.
Sanin halin inna yasa Gwaggo Laritu tafiya da Zinneerah gidanta, bayan ta saka Sa'a ta tattaro mata duk kayan Zinneerah dake a can gidansu dan dolene ta dawo zama a gidajen ɗaya daga cikinsu har ALLAH ya sauketa lafiya.
Tunda suka shigo gidan sam hankalin Zinneerah baya a jikinta. A hankali wani irin tsanar garin Danya da komai nasa ke shiga jikinta. Koda Sa'a ta kawo mata kayanta tana zaune can rakuɓe kanta cikin ƙafafu, ba kuka takeba ba kuma tunani ba. baƙon al'amarin dake shiga cikin jikinta ne kawai ke ratsata. Ta ɗago ta kalli Sa'a data dafa ta, ganin yanda Sa'a ke hawaye ya sata sakin wani murmushi maiban mamaki, batare da tace komaiba ta maida kanta yanda yake.
Hankalin Sa'a ne ya ƙara tashi, dan a duk sanda taga irin wannan murmushin a fuskar Zinneerah to takai ƙololuwa a shiga tashin hankalin rayuwa kenan. Dan duk lokacin da takurawa da matsawar Inna yaymata yawa bata kuka. Ko nuna tausayinta sukai kuma sai dai tai musu wannan murmushin bazata taɓa ta tanka ba.
Zuciyar Gwaggo Laritu a kusa take ainun da baƙin cikin halin da suke ganin Zinneerahn ta jefa kanta. Da kuma haushin Inna dana Baba da ya koma tamkar mara amfani agaresu, yanzu haka a kaf ruguntsumin nan da akeyi yaƙi cewa ƙala. Wanan takaicin da sukai mata yawane ya sata shigewa ɗaki tabar Zinneerah waje zaune batare da tace taje ta kwanta ba. Sauƙinta ma itama su kaɗaine a gidan sai matan ƴaƴanta biyu, suma kuma an katangema kowa sashensa babu mai ganin wani.
Abinka da ƙauye ahankali garin ya fara ɗaukar shiru. Har takai Zinneerah dake zaune a ƙofar ɗakin Gwaggo Laritu barci ɓarawo ya saceta har takai ga zamewa ƙasa ta kwanta akan sumintin wajen tai filo da jikkar kayanta da Sa'a ta kawo da yake ba wata babba bace, dan kayan nata basu wuce a ƙirga ba.
Barci ne sosai mai nauyi yay gaba da ita, yayinda itama acan Gwaggo Laritu datai tunanin idan Zinneerah ta gaji da zaman wajen zata shigo ɗaki ta kwanta barcin yay gaba da ita dan gajiya.
Tamkar wadda akace ta tashi Zinneerah ta miƙe zumbur, babu wani tunani ta ɗauki jikkar kayanta ta nufi hanyar ƙofar gidan nasu Gwaggo Laritu. A hankali ta zare sakatar murfin gidan ta fice kamar tana tsoron wani ya jita koya ganta. Kallon gabas da yamma kudu da arewa tayi, garin tsit babu alamar akwai wani rai mai numfashi, ga wata yayi nisa babu wani hasken kirki, ga sanyi kasancewar lokacinsane sai dai farko-farko dan baiyi ƙarfi ba. Ta sauke wani nannauyar ajiyar zuciya ta fara tafiya babu alamar tsoro ko fargabar jin garin shiru tattare da ita sam.
A cikin daren nan Zinneerah ta nausa kanta cikin daji batare da alamun akwai hankali a jikintaba, dan yanda take matsoraciya ko fitsari ya kamata da dare sai ta tada Yaya Sa'a ta rakata. Amma yau sai gata a hanyar daji cikin tsakkiyar dare babu ko gezau.............✍
Hasbinallahu wani'imal wakil. Ya rabbu ka iya mana da abinda yafi ƙarfinmu, harma da wanda mukafi ƙarfinsa.😭🙏🏻
Leave a Comment