Makauniyar Kaddara 57

 


Page 57*


...........“Nine kuma bana dariya sai shekara-shekara ko?”. 

      “A'a wlhy Yayanmu bakai nake nufi ba, wani ne acan Danya”. Zinneerah ta faɗa tana duban gefen daya janye hannunsa. Hakan yayi dai-dai da wayarsa ta fara tsuwwa. Aljihunsa ya kalla da ƙoƙarin zira hannunsa zai ɗakko, ‘Alhmdllh’. Zinneerah ta faɗa a zuciyarta tana kwasa da gudu.

           Duk yanda AK yaso danne dariya a yanzu kam ya kasa, dole yay murmushi har haƙoransa na fitowa tare da girgiza kansa kawai.

      yace, ‘Zan kamaki har inda zakije ɗin ai” daga haka ya kai wayarsa kunnensa dan Hajiya iya ce.


      Zinneerah kam bata tsaya a ko inaba sai bedroom ɗinta nacan ciki, ta murzawa ƙofar key tana sauke numfashi da faɗin, ‘ALLAH na godema daka kuɓutar dani, Bahijja taso jamin salalan tsiya yau, dan ƙila zaneni yay niyyar yi ma’.

       Sai kuma ta kwashe da dariya saboda tuno su Bahijja, inama tanada waya yau data kirasu taji yanda aka kwashe. Bata taɓajin takaicin rashin wayarta irin yau ba, harta kaita da zama tunanin yanda wayar ta ɓata abin kamar almara


     ★★★


  Tun abinda ya faru Zinneerah da AK basu sake ganin junaba har akai sallar magriba. Sai lokacin ta fito daga ɗakinta ta duba dining ɗin. Tasha mamaki ganin anci abinci data ajiye. Aranta take tunanin ashe ya shigo yaci abincin. Wajen ta tattara tare da falon, ta saka turaren wuta sannan ta koma ɗaki tai wanka. Tana fitowa sallar isha'i ta gabatar, bayan ta idar tai zamar gyara jikinta ranta fal tunanin mmn sadiq dasu Abdull, harma da Little da rabota dashi tun randa zata wuce danya. Tana kewarsa sosai harma da ƴan danya ɗin, yanzu da tanada waya ai da ta kira taji yanda suka sauka lafiya da jikin Tinene kuma. Tsaki ta ɗan ja ranta duk babu daɗi. Doguwar riga kawai ta saka yanda zata sake, tana ɗaure gashinta data taje taji an turo ƙofar ɗakin.

        Juyowa tai a hankali tana duban ƙofar aɗan rikice, wanda tayi zaton dai shine, yana sanye cikin wando jeans baƙi da baƙar t-shirt, sosai kayan sukai masa ƙyau duk da alamu sun nuna badan kwalliya ya sakaba. 

         Ganin yanda idanunsa ke a kanta yasata yin ƙasa da nata, ya ƙaraso cikin ɗakin kansa tsaye da tafiyarnan tasa daba garaje, ga fuskar kuma babu alamar fara'a kamar ko yaushe, amma hakan bai hana ƙyawunsa da kwarjininsa fita ba a bayyane.

      “Barka da dare”.

Ta faɗa kanta a ƙasa da ƙoƙarin jan gyalen jallabiyar zata yane kanta duk da bata kamla ɗaure gashin ba. AK da tunda ya shigo idanun nasa ke akan gashin nata ya janyesu yana zama bakin gadon. Batare da yayi mata magana ba ya miƙa mata wayarsa.

         Amsa tayi duk da bata fahimci mi yake nufi ba, sai dai ganin sunan Granny da alamar tana online yasata kai wayar kunnenta tai sallama murya a marairaice.

    Dariya Granny tayi daga can da cewar, “Inno irin wannan marairaicewa haka?”.

     “Granny nayi kewarki ne”.

“Nima haka Inno, shiyyasa nace Moddibo ya banike na karajin muryarki kafin na kwanta”.

      A take hawaye suka ziraro a kumatun Zinneerah, muryarta ta fara rawa alamun kuka. Kai kawai AK ya ɗan girgiza da mikewa tsaye, batare da yace komaiba ya zare wayar daka kunnenta....

     Da sauri ta kallesa dai-dai yana maida wayar kunnensa. Idanun nasa ya ɗan juya mata da faɗin, “Daga gaisuwa kuma sai ki samin ita kuka Granny? To an fasa gaisuwar dake sai da safe”.

      Da alama wata baƙar maganar ta faɗa masa daga can, dan janye wayar yay yana murmushi. Batare da yacema Zinneerah dake sharar ƙwalla uffanba ya raɓata ya wuce inda ta ajiye masa system ɗinsa daya bari a ɗakin jiya. Ɗauka yay tare da nufar ƙofa yana faɗin, “Ki kawomin lipton”.

        Baki ta kuma tunzurawa tana matso hawaye da bin bayansa da kallo harya fice, babu yanda ta iya dole bayan ta gama kukanta ta share hawayen da ɗaukar turare ta ƙara a jikinta, hardasu fesa much freshener kamar yanda Hajiya Falmata ta koya mata, ta ɗauka wani ɗan kwalban turare da batasan kona minene ba ta shafa a bayan kinnenta da wuyanta, kamar yanda Hajiya falmatan ta sanar mata ta ringa shafa shi duk dare idan tai wanka, ta kuma ƙara da khumra mai shegen daɗi da narkar da mai shaƙa.

     Daga haka ta ɗau hijjab mai hannu jaa ta saka sannan ta fito. Kitchen ta nufa ta ɗaura masa lipton ɗin da ganyen shayin da hajiya Falmata ta bata shima, rashin wayonta yasa batai tunanin ko ganyen shayin na wani abu baneba daban. A wani butar shayi mai azabar ƙyau daya ɗauka hankalinta ta juye tare da kananun kofunansa tasa biyu, sai ɗan bowl ɗin data zuba suger shima ta ɗora da tea spoon guda ɗaya ta ɗauka tray ɗin tana addu'ar ALLAH yasa tayi komai dai-dai.


         Yana zaune a doguwar kujera ƙafarsa a miƙe yasa filo da ɗaura lap-top ɗinsa saman filon. Koda tai sallama bai dagoba amma ya amsa mata a saman laɓɓa yana cigaba da aikinsa. 

       Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke idanunta, a centre table ɗin tsakkiyar falon ta ɗaura ƙaramin tray ɗin da jawosa kusa da shi tace, “Yayanmu gashi”.

     Ɗan ɗagowa yay yayi mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa, a taƙaice yace, “Zuba”.

        Kanta ta jinjina masa kawai ta tsugunna gaban table ɗin tana ƙoƙarin fara zubawar, yanda hijjab ɗinta yay ɗan bula lokacin da take kaiwa tsugunne ya bama hancinsa damar shaƙo fitinannun ƙamshin turarurrukan data sakama jikinta, duk da tun shigowarta ya jisu, sai haka datai ya ƙara ƙarfinsu fiye da farko a cikin hancinsa. 

     Wani irin harbawa zuciyarsa tayi, har baisan yatsunsa sun kauce wajen tafa saƙon shirme ba a system ɗin. Ya lumshe idanu ya sake buɗewa a kanta yana ɗan cizar lip dinsa na ƙasa. 

     Zinneerah da batasan mi yake cikiba ta miƙo masa ɗan mitsilin tea cup ɗin irin na larabawa bayan tasa suga ɗaya dan tasan yanda yake so tunda yasha sata aikin sanda suna gida, tsaf ta gama haddace adadin da yake so.

       Idanunsa da suka canja launi lokaci guda ya zuba mata, dai-dai yana amsar shayin muryarsa a ƙasan maƙoshi yace, “Cire wannan hijjab ɗin banaso”.

       Mamakin maganar tasa yasata ware idanu sosai tana kallonsa. Sai dai yanda fuskarsa ke a ɗinke ya sata yin ƙasa da kanta ta hau ƙoƙarin cirewa tana haɗiye abinda ya tokare mata maƙoshi, dan duk da doguwar riga ce a jikinta tsananin kunyar zama take a gabansa a haka saboda santsin rigar yasa ta kwanta mata a jiki ta lafe, musamman da yazam ita da kanta ta rage faɗin rigar tun suna gida ita dasu Bahijja.

   Hannu ya miƙa mata alamar ta bashi, dole ta miƙa masa, kusa dashi ya ajiye hijjab ɗin dan son tabbatar da shike ƙamshin ko ita?.

      “Zauna”. Ya faɗa yana matsar da ƙafafunsa. Yanzun kam kasa haƙuri tayi sai da tace, “Yayanmu zanje na kwanta inajin barci”.

      “Nima ba gadin gidan zanyiba ai”. Ya bata amsa a daƙile.

     Tashi tai tsam ta zauna inda ya nuna matan har jikinta na neman hayemasa ƙafafu, tai saurin muskutawa kanta a ƙasa.

       Idanu ya tsira mata yana kurɓar shayin kaɗan-kaɗan saboda zafinsa. Amma dai haka yafi bukatarsa musamman wannan da yay masa matuƙar daɗi, ga wani irin ƙamshi mai daɗi dake fita a cikinsa. 

       Ya fahimci ta matuƙar ƙwarewa da iya cuɗa hannunta cikin na juna idan tana waje a takure ko makamancin hakan. Ya danyi gyaran murya nason gusar da shirun nasu. Ɗagowa tai ta kallesa.

        Idanunsa a cikin nata yace, “Kin kira su baba ne? Kinji yanda su gwaggo sukaje gida lafiya”.

      Ya sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi, atake idanunta suka ciko da ƙwalla ta girgiza masa kai. “A'a ai bani da waya ta ɓata”.

      “Ɓata fa? A ina kenan?”.

   Da damuwa sosai a fuskarta tace, “A can gida, tun lokacin da Granny bata da lafiya zaku wuce london”.

       Cikin ɗan taɓe baki yace, “Kin dai jefashi wani waje”.

     “A'a wlhy Yayanmu, nifa ina gama waya da Mama a ranar daga ajiyewa naje na tarosu na nemeta na rasa. har yanzu kuma ban ganshiba, kuma ko ina su Meenal sun tayani na duba”.

       “Uhm to wani ya sace kenan”.

Ya bata amsa cike da basarwa.

     Itako tace, “Amma kuma a gidan nan wazai saci waya?”.

            Wani ɗan murmushin daya bata mamaki taga yayi yana lunshe idanunsa. Cikin basar da maganar yace, “Ganyen shayin nan yanada daɗi waya baki?”.

      Badan taso barin waccan maganarba tace, “Hajiya Falmata”. 

    “Wacece ita?”.

“Nima sai kwanan nan na santa suna mutuncine da Granny”.

       “Uhm! Itace ta baki wannan turaren mai ƙamshi haka?”. Ya faɗa murya a shaƙe dan shayin da yasha ya fara aikinsa.

     Rasa amsar da zata bashi tayi, sai ta ɗan jinjina kanta kawai. 

    “Baki da baki ne?”.

“A'a kayi haƙuri itace ta haɗa, khumrah ne”.

       Komai bai sake faɗaba ya sauke lap-top ɗin dan aikin kam bazai iya cigabuwaba, ƙafafunsa ya zaro daga kusa da ita ya ajiye ɗaya a ƙasa ya tanƙwashe ɗayar, sake ɗaukar butan shayin yayi ya tsiyaya dasa suga ɗaya a ciki ya motsa. Cigaba da shan abinsa yayi da maida hankalinsa ga television. Itama gyara zamansa da yayi ya sakata jin ɗan sanyi ta koma kallon television ɗin da satar kallonsa. dan ya dage sai ɗora shayin yake hankali kwance. Daya shanye yake karawa, tanata lissafi sai da yasha kusa cups bakwai duk da dai ɗan mitsitsine kofin.

       Sai da aka kammala labaran da suke kallo ya miƙe, batare da yayi mata magana ba ya fice gaba ɗaya a sashen har tana mamakin ina zaije? Bata da mai bata amsa dan haka ta ƙudiri aniyar zaman jiransa ya dawo ita dai taje ta kwanta ta farajin barci.


     Shiko daya fita kai tsaye sashenta ya nufa, kitchen ya fara shiga ya kaso wutar can ya rufosa. ta Dining ma ya kashe tare da leƙa bedrooms ɗin dake a falon duk yaga akashe sannan ya nufi nacan ciki da take amfani da shi.

      Akwatin kayanta ya buɗe, duk da shi ba mutum bane mai buƙatar matarsa tasa kayan barci idan zasu kwanta tare ba, yafi buƙatar tazo masa a natural ɗinta, hakan bai hanashi ɗauka mata suba. Sai dai yau ba kamar jiyaba sai da ya zaɓo dai-dai da ra'ayinsa. Gaban Mirror ɗinta yaje nanma ya shiga shinshina turarurrukan wajen kamar mai neman wani daban. Sai dai abin mamaki ya kasa tantance wanda yake buƙatar jin, har takai ya fara buɗe kwalaben khumra dake wajen kusan kala shidda dan bama a kawo mata sauranba tukunna. Ya ɗan samu wasu a ciki, harya ɗauka biyu sai idonsa ya sauka akan kananun ƙwalabe dake cikin wani haɗaɗɗen kwandon saƙa na kaba da aka zubasu ciki kusan kala goma nanma. Murmushi ya danyi dan shi mutum ne mai son ƙamshi, ƙamshi yana ɗaya daga cikin abinda Farah tai galaba a kansa kenan dan itama gwanace wajen baza turare. Nanma shinshinawa ya ringayi ɗaya bayan ɗaya, sai dai ya kasa tantance wanda yafi daɗi da wanda yaji a jikinta. Sai ma neman rikita masa lissafi sukeyi. Nanma biyu ya zaɓa a ciki ya fice bayan ya kashe komai. falukanma duk kashe komai yayi ya rufe sashen baki ɗaya ya nufi nasa.


       Zinneerah da har ta gaji da jiran dawowarsa ta jingina da makarin kujera tana lumshe idanu ta buɗesu a hankali jin sallamarsa. Bataga mike hannunsaba dan kai tsaye bedroom ɗinsa ya nufa. Zamanta ta gyara da ɗaukar hijjab ɗinta ta riƙe a hannu gudun kar tai laifi.

    Babu jimawa kuwa sai gashi ya fito, batare da yay mata magana ba ya ɗauka remote ɗin tv ya kashe tare da nufar fridge, yana juyowa ɗauke da fura a hannu tana miƙewa. Fuskarta a marairaice tace, “Yayanmu zanje na kwanta barci nakeji”.

       Baiyi maganaba sai da ya karaso, ya ajiye roban furan da kamo hannunta ya zaunar. “Zauna kisha wannan sai kije ki kwanta”.

      Cikin langaɓe kai tace, “ALLAH yayanmu na ƙoshi barci nakeji kawai”.

        Harar daya zuba mata tasata ɗauka dan harya buɗe mata robar, cokalin dake haɗe da robar furan ta ɗauka ta fara sha a hankali tana lumshe ido dan barci takeji, sosai furan na mata dadi sai dai barci na neman kwafsa mata. Shiko lap-top ɗinsa ya ɗauka yana ƙarasa aikin nasa.

      “Yayanmu ALLAH ta isheni barci”.

Ɗan ɗagowa yay ya kalleta, yaɗan jinjina mata kai kawai yana ajiye lap-top din daya kashe gaba ɗaya. Miƙewa yay hannunsa ɗauke da remote na ac ya kashe. Sannan ya tattara wayoyinsa da nuna mata hanyar ɗakinsa.

      Sosai ta ɗan waro masa manyan idanunta dake cike da barci waje. Sai dai yanda ya tsuke fuska dole ta haɗiye abinda ke bakinta ta maida kanta ƙasa. Sum-sum ta fara tafiya hanyar ɗakin da bata taɓa shigaba. Kasancewar ya tsaya kashe fitila ta rigasa shiga ɗakin. Da wani ni'imtaccen ƙamshi tafara cin karo, ta ware idanunta sosai tanabin bedroom ɗin da kallo baki sake. Komai yaji masha ALLAH, white and golden kamar kaci dan ɗaukar idon mai kallo. Ga uban sanyin ac.

     Tana tsaye a wajen harya shigo bata saniba. Sai jitai kawai anyi sama da ita gaba dayanta. Sosai ta firgita sai dai babu damar yin magana. Bai direta ko inaba sai toilet ɗinsa da komai yake a tsare kuma a tsaftace. Dan shi kansa kamshi yake na musamman.

       “Kiyi alwala”. Ya faɗa kansa tsaye. Sabo da alwalar kwanciya barci yasa bataji komai a rantaba, gashi dama ko shafa'i da wutiri ma bataiba. Alwalar ta ɗaura yana kallonta cike da nazari, da alama yana tabbatar da ingancinta a fannin addinine ne. Sai da ta kammala shima ya ɗaura tasa suka fito tare kamar yanda yay mata alama da ido.

     Da kansa ya sa musu abin salla. Ganin yayi tsayuwar alamar jansu salla yasata kallonsa da mamaki. “Yayanmu nayi sallar isha'i”.

     “Nima nayi ai”.

Shiru tai bata ƙara maganaba harya tada sallar, itama tayarwar tayi dan bin umarni shine masalaha a gareta. Sunyi salla raka'a biyu suka ɗora da shafa'i da wutiri, sannan ya juyi ya dafa goshinta da ambaton.

*اَللَّهُمَّ  إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا، وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا، وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ*

*_Allahumma innee as-aluka khayraha wakhayra ma jabaltaha 'alayh, wa-a'oothu bika min sharriha washarri ma jabaltaha 'alayh._*

        _Ya ALLAH ina rokon Ka laherinta da alhrin da Ka dabi'antar da ita a kansa, kuma ina neman sarinka daga sharrinta da shaarrin Da ka dabi'antar da ita a kansa._ 

      Lumshe idanunta tayi tana sauraren daddaɗan muryarsa mai cike da kamun kai da nutsuwa. Bayan ya kammala ya juya da ɗaga hannayensa sama ya cigaba da kwararo addu'oi kala-kala da harshen larabci.

       Sai da suka kammala addu'ar ya juyo yana fuskantarta da ƙyau. Tambayoyin ya fara mata a fannoni daban-daban daya shafi addini, wasu ta amsa wasu tace bata saniba dan a yanzu take kan neman ilimi, danma Alhmdllh batai wasaba akan hakan tunda ta dawo da zama kano. 

     Ya gamsu da yanda tayi ɗin, ya kuma karba uzirinta, daga haka ya miƙe yana magana batare daya kalletaba. “Ga kayan barci nan ki canja”.

    Yana fa ɗaya yana nufi hanyar toilet. Kaɗan ya rage Zinneerah ta saki kuka amma ta dake ranta fal tsoro. Kenan anan zata kwana tare da shi yau ma?. Ta ayyana a ranta. Sanin bata da mafita kuma baya maimaita magana, gashi batason ya fito ya sameta batai abinda yaceba yasata ƙoƙarin canja kayan. Ganin turarrukanta tare da kayan ta mulke jikinta dasu duk da kuwa ƙamshin take dama. Tana gamawa yana fitowa ɗaure da towel jikinsa nata raɓar ruwa. Ƙasa tai saurin yi da kanta tana gyara zaman hijjab ɗinta data ɗora saman kayan barcin. Komai baice mataba ya hau tsane jikinsa da towel ɗin daya ratayo a wuya. 

    Da wannan damar ta wuce toilet ɗin nasa sumi-sumi danyin brush tunda taga sabbi a toilet ɗin, dan ta tuna Hajiya Falmata tace duk rintsi karta kwanta batai brush ba, idan da dama ma ta haɗa da much freshener, sannan ta tabbatar duk sanda zata kwanta barci tayi tsarki da ruwan ɗumi koda ace ta yini amfani da shine.

      Brush ɗin ta farayi, sannan tai fitsari dayin tsarki da ruwan ɗumi. Much fresheners ɗinsa data gani ajiye a ɗan drawer ɗin glass ɗin toilet ɗin ta ɗauka, dan gasunan kala-kala, banana, cucumber, kai kala-kala ta fannin fruit duk gasu nan. Son da takema S...barry ya sata ɗaukarsa shi da banana ta saka sannan ta fito cikin sanɗa, a ranta tana addu'ar ALLAH yasa ya gama shiryawa dan shiyyasama ta daɗe danta bashi dama.

     Tsaye ta iskesa gaban mirror sanye da wando 3quarter iya cinya da riga mai buɗaɗen ƙirji farare tas. Yana fesa turare. Ta madubi yake kallonta harya kammala sannan ya juyo...........✍


No comments

Powered by Blogger.