Makauniyar Kaddara 56
Page 56*
..........Sai da ya tsaya yay sallar azhar a hanya sannan ya ƙarasa gidan. Tun daga falon farko yake jiyo dariyar su Meenal da Jamal. Ya ɗanyi shiru na wasu sakanni a wajen amma baiji muryar Zinneerah ba ko sau ɗaya, firar tasu kuma dukta makaranta ce Nawaf na basu labarin makarantarsu ta Turkey shima. Kamar zai nufi can sai kuma ya fasa ya ɗauka hanyar sashensa.
Khalipha dake zaune yana kallon television a falon nasa ya ɗago yana amsa masa sallamar da yayi. Cikin falon ya ƙaraso yana faɗin, “Am sorry besty na barka jira ko?”.
“No babu damuwa Yayanmu, nima ban wani jima da zuwanba sai da na biya ta asibiti”.
“Thanks”.
Yace masa kawai yana nufar hanyar bedroom ɗinsa. Kusan mintuna goma sai gashi ya fito sanye da ƙananun kaya da alama waɗan can ɗin sun damesa. Yana zama Khalipha ya miƙe ya buɗe fridge ya ɗakko masa ruwa.
“Thanks Darling”.
Murmushi Khalipha yay kawai ya koma wajen da yake ya sake zauma. Sai da AK yasha ruwan sosai dan ƙishirwar yakeji dama. Kofin ya ajiye yana gyara zamansa ƙafa ɗaya kan ɗaya ya ƙara komawa serious.
“Khalipha akan maganar da muka farone ranar, inason ka amsa min wasu tambayoyi”.
“Okay Yayanmu kaimin, inhar na sani zan baka amsa insha ALLAH ”.
Kansa ya jinjina masa da kai hannu yaɗan shafo sajensa zuwa gemu. “Yanzu idan nace kamin bayani akan dashen cikin gaba ɗayansa zaka iya?”.
“Zan iya Yayanmu, sai dai zai cimana lokaci matuƙa, kai kuma nasan bakason a cinye maka lokutanka”.
Sassanyan murmushi yayi yana ɗauke kansa daga Khalipha ɗin. “Ai wannan nine na bashi lokacin da kaina, sai dai kuma barsa kawai muje ga tambayoyin zasu wadatar dani insha ALLAH ”.
“Okay Yayanmu ina saurarenka to”.
Ɗan jimm yayi na wani ɗan lokaci kamar mai nazari, kafin ya duba Khalipha da ƙyau, “Bani bayani a taƙaice ta yanda za'a iya dashen cikin?”.
Zama sosai Khalipha ya gyara da nutsuwa. “Abunda kake magana ana ce mishi artificial insemination Yayanmu. Ana daukar maniyyi namiji (semen) a tace, a ɗauki sperms sai a haɗa da Kwan mace (ovum). Shi Kwan mace sai an shirya ake ɗaukan shi shima, anabada magunguna kafin ayi hakan, sannan ba haka kawai ake ɗauka ba sai an duba lokacin da matar take ovulation, ma'ana Kwan yayi girma sai ayi amfani da na'urar scanning a ɗauka. Ta Mara ake ɗauka bata al'aura ba, sai a haɗa a Laboratory (invitro fertilization). Idan anyi sa'a an samu fertilization sai a ɗauki abunda ake cewa fertilized ovum kamar guda biyu a sa a mahaifar matar wannan ta vagina ɗinta za'a saka sai a jira a gani idan dashen ya kama. Idan ban mantaba kuma na fahimci tambayarka wannan itace amsar”.
Sosai AK ke ɗan jinjina kansa yana taunar lip ɗinsa na ƙasa a hankali da haƙiri. “Okay Thanks. Next, za'a iya ɗaukar sperm daga wani ƙasa a kawo wani ƙasa batare daya lalace ba?. Misali kamar daga london zuwa Nigeria?”..
“Eh to Yayanmu za'a iya ɗaukar semen akai wani wuri, amma gaskiya yanada matuƙar wahala saboda sai an sashi a ma'adani na musamman (Google: transport sperm from one place to another). ba kowanne likita banema zai iya maka wannan juriyar kai tsaye”.
“Lallai kam. To amma za'a iya ɗaukar sperm ɗin namiji bada saninsaba aje a aikata dashen?”.
“Yayanmu idan na fahimceka kamar ace matarsa ta ɗauka a ɓoye bada saninsa ba? Dan ko likita sai dai ya saka a kawo, bawai ya ɗiba kai tsaye ba tunda ba kamar jini bane ko fitsari da sauransu”.
“Good, haka nake nufi?”.
“Gaskiya Yayanmu kamar ba zai yiwu ba, saboda idan za'ayi irin wannan abun shi namijin shine zai bada maniyyi asa a kwalba na musamman a tace sannan ayi, ba zai yiyu ayi irin wannna kuskuren ba, kamar yanda na faɗa maka sai an shirya ake ɗaukan Kwan mace, sannan akwalba ake haɗawa sai ya haɗu sannan za'a ɗauka a dasa a mahaifar macen. Sai dai a sakashi ya bada da kansa ta wata sigar batare da shima ya san mi za'ai da shi ba nakega”.
Ɗan jimmm AK yay yana wani tunani da ƙiyasta shekarun Zinneerah a ransa. Kafin ya duba Khalipha ɗin,
“Okay, kenan za'a iyama yarinya ƴar 14years dashen cikin?”.
“Eh Yayanmu za'a iya yi, sai dai kamar yanda na faɗa maka kafin ayi sai an shirya, ma'ana akwai lokacin da akeyinshi sai an duba menstrual cycle ɗin matar, sabida haka idan bata fara al'ada ba, ba zaiyi wuya ba, idanko ta fara zai iya yuwuwa”.
“Akwai ta hanyar da ku likitoci kuke iya gane ɗan na dashe ne?”.
“A iya sanina babu yanda za'a iya gane dashe ne, bandai saniba ko ga wasu manyan likitoci da suka fini ƙwarewa kasan har yanzu ni ɗalibin ilimi ne”.
Ɗan murmushi AK yayi yana sake gyara zamansa. “A nawa tunanin idan har dashen ciki akai ma yarinya, ya kuma kasance cs akai mata bata haihu da kanta ba, kenan zata iya cigaba da kasancewarta cikkakkiyar mace dazai iya bada dukkan amsoshin ko hujja akanta tunda babu wani dalili dazai iya gusar mata da budurci”.
Murmushi ne ya ɗan suɓucema Khalipha, dan sai yanzu ya fahimci dai Yayansu yana magana ne kamar akan Zinneerah, ya dai ƙi fitowa fili ne, zama ya ƙara gyarawa da ƙyau yana faɗin. “Eh to Yayanmu idan dai mace ta haihu ai babu zancen virginity ya kare nake gani ko kuwa?. Sai dai kuma da kace idan ya kasance an mata cs ne. Abunda mutane ke cewa budurci abun ba haka bane, virginity shine idan bata taba saduwa da namiji ba ko an zura wani abu a vagina babu yanda ake ganewa saboda mata da yawa wannan abun mai kama da yaɗi da yake ɗan rufe bakin vagina ba kowa keda shi ba, hasalima idan mace tana manyanta abun yana raguwa, sannan tsallle-tsalle da irinsu hawan doki ko Keke duk yana sawa a rasa shi, haka kuma Koda mace tana dashi ba kowa ke zubar da jini lokacin saduwar farko da ɗa namiji ba. Shi yasa yanzu duk ake hana abubuwa kamarsu vaginity testing. Kaga nauyin ciki zai iya sa ta rasa wannan yaɗin kenan itama inhar tanada, amma ba haka na nufin ta rasa budurci ba, dan dole a kirata virgin inhar bata taɓa sanin ɗa namiji ba, ko kuma wani abu makamancin haka kamar haihuwa bai ratsata ba”.
AK ya ɗan sauke numfashi, “Sannu da ƙoƙari Khalipha. to amma za'a iya yin dashen batare da ta saniba kuwa? Kamar a bugar da ita ko something hakan?”.
“Tabbas za'a iya bata maganin bacci ayi, amma bazai yuwu ayi a gida ba ko ɗakin likita ba, a ɗakin theater akeyi, bai kuma zama lallai a samu nasara ba a yin farko, wasuma sai kaga sunyi sama da sau hudu biyar goma ma basu daceba, ƙwayayen sukan mutu kafinma a dasa ko bayan an dasa cikin yaƙi zama. Idan kana buƙata zan iya baka number wani likita ƙwararre akan wannan fanin kawai dazai maka ƙarin bayani sosai, zaima iya nuna maka yanda akeyin komai insha ALLAHU”.
Murmushi AK yayi da ɗaukar ruwa yasha. “Ai ko haka aka tsaya ma na gamsu Khalipha, na kumaji a raina baka wasa da karatunka, tunda gashi tun a yanzu mun faracin tagomashinsa, inaga nan gaba kuma ka zama cikakke. ALLAH yay maka albarka ya ƙara ƙwaƙwalwa. Akwai wasu bayanai da nakeson sake tattarawa, dana kammala zan baka wani aiki insha ALLAHU”.
“To yayanmu ngd sosai. ALLAH ya ƙara girma da nasarorin rayuwa”.
Murmushi kawai AK yayi da amsawa da amin akan laɓɓansa. Daga haka suka koma wata hirar kuma.
_______★
Sam su Zinneerah basusan da dawowar AK gidanba, tunda su Jamal suka ƙaru sai sukai zaman sake babin sabuwar shafta, sun dai san Khalipha na nan, tunda bayan mai gyaran ya kammala ya sanar mata zai jira dawowar Yayan nasu.
Kiran sallar la'asar ya saka Jamal da Nawaf fitowa massallaci, shine suka haɗu da Khalipha da yayan nasu. Sunata faman sinne kawuna da tunanin zai musu faɗa sai sukaji tsit, tundama ya amsa gaisuwarsu yay gaba bai sake cewa dasu uffanba har aka idar da salla suka fito.
Khalipha ne ya dubesu lokacin da suke shigowa harabar gidan. “Guys kuje ku tattaro waɗan can sauran yan-yan ɗin muwuce gida haka nan”.
Cikin marairaicewa Jamal yace, “Wayyo Yaya Khalipha Please sai anyi magriba zamu dawo fa, can gidan duk mutane, ni wlhy suna takuramin”.
“Ƙaniyarkace mutanen, dalla jeka kirasu mu wuce. Mutanen da kake magana ba duk sun kama gabansu ba, ga aiki can a gida kunzo nan kun zauna”.
Baki cike da iska Jamal ya wuce ciki kiransu Meenal. Duk wannan abin dake faruwa AK na ɗan gefensu kaɗan yana waya, sarai kuma yanajinsu amma sai baima nuna kunnensa na akansun ba. Ba'afi mintuna uku ba sai gasu sun fito harda Zinneerah da fuskarta ke a ƙwaɓe.
Sam bata lura da AK ba, dan haka kai tsaye ta isa gaban Khalipha. “Wayyo Yah Khalipha dan ALLAH ka barsu, hirafa suke tayani”. Ta ƙare maganar hawaye na sakko mata a kumatu.
Tausayi ta bashi dan yasan shaƙuwa da sabon dake a tsakaninsu, sannan kuma akwai rashin sabon nan ɗin tattare da ita. Balle Yayan nasu daba sakewa ya iya da jama'a ba sai yaso dan kansa.
Murya ya kwantar sosai cikin lallashi yace, “Haba auta ai abun sai ya zama rashin hankali kuma. Kiyi haƙuri gobe idan ALLAH ya kaimu sai su dawo ku ɗora daga inda kuka tsaya tunda ku shiririta bata ƙare muku. Kinga yanzu aikine a gidan can sosai, su kuma da zasu taimaka sunzo nan sun zauna aikin yama su Ni'ima yawa.”
“Amma Yah Khalipha zasu koma ai, kaga yanzu suna tayani hira”.
“Indai hirace karki damu ga Yayanmu nan a gida ai zai tayaki”.
Batare da tunanin yana a wajanba tace, “Tab, Yayanmu ne zaiyi hira? Wanda ko dariya yana shekara baiyita ba ma......”
Karaf Bahijja ta katseta da faɗin, “Baya hira, amma ya iya soyayya, nifa nan gidan zanma dawo da zama yasin nasha kallo, dan na taɓa ganin wata zazzafan soyayyar Yayanmu da aunty Farah wani zuwa da sukayi na rakasu gidan Uncle Yusif, ku kunga abu, wlhy Zinneerah zaki sh.......”
“K!”.
Khalipha da abin ya ishesa yay saurin katseta. tun fara sakin zancen nata yake mata alamar tai shiri amma taƙi fahimta. Suko su Jamal hannu suka ɗora bisa kawunansu suna zaro ido da bubbuga bakinsu na mata alamar tai shiru, amma ina yarinyarnan kamar an kunna mata batir. Tsawan da Khalipha yay mata kuwa baki ta turo, cikin ƙunƙuni tace, “Yah Khalipha labarifa nake baku dan kuma ku koya irin ƙwarewan Yayanmu kuma ku dinga yi”.
Kai kawai Khalipha ya girgiza yana ƙoƙarin danne dariyar dake neman kufce masa ganin Yayan nasu ya nufo inda suke yana saka wayarsa aljihu alamar ya gama.
Gyaran murya ya ɗanyi, ba Bahijja mai bada lecture ba hatta Zinneerah sai da hanjin cikinta ya wantsala suka juyo a firgice su uku harda meenal dan sune dai suka juyama inda yake baya.
Kafinma yace dasu wani abu Bahijja da Meenal sun kwasa da gudu hanyar gate, Jamal da Nawaf duk da sunsan dashi a wajen suma dai rufa musu baya sukayi dan hanyar lafiya a bita da shekara.
A bazata dariya ta suɓucema Zinneerah duk da itama fa a tsoracen take. Amma yanda su Jamal suka dafe ƙeya dasu Bahijja ya bata matuƙar dariya. Khalipha da shima dariyar yake dannewa tana kufcewa ya afka mota yana faɗin, “Mu kwana lafiya Yayanmu”.
Kai kawai ya jinjina masa tashi fuskar babu ko ɗigon murmushi ammafa a ransa dariya yake ɗan rainin wayon😂. Dan duk dauriyarka dolene abinda su Meenal sukai ya baka dariya. Maigadi kansa dariya yakeyi dan har bangajesa sukai wajen gudu.
Ganin Khalipha zai wuce Zinneerah ta shirya nata gudun itama amma tana ɗaga ƙafa zata fece taji an cafko mata hannu. Gaba ɗaya ta rikice, dariyar data rage a saman fuskarta ta ɓace ɓat. Baya ya dawo da ita gabansa yana kallonta da birkitattun idanunsa dake neman sakata sakin fitsari dan fuskar ta kuma tsukewa tamau. Shi dai Khalipha motarsa ya harba yana dariyar ƙeta, dan yasan dai Bahijja ta kunno wuta. Kuma gaskiya ta faɗa indai soyayya ce kam Yah Abdul-Mutallab ba'a magana, shi da yake rayuwa a gidansu yake shan kallo.
Cikin tsagwaron marairaicewa Zinneerah da idanunta ke tara ƙwalla tace, “Yayanmu wlhy bance komaiba, ALLAH Bahijja ce ka tambayi Yah Khalipha kuma. Uffan baice mataba, sai jawota da yay a hankali ta faɗa saman jikinsa, rawa jikinta ya fara, batare da yabi takanta ba ya ɗauketa cak a bazata. Babu shiri ta cusa kanta a ƙirjinsa dason sauka amma tama kasa motsawa. Koda suka iso ƙofar falon da ƙafa ya tura, hakama da sukaje ta sashensa da ƙafa ya tura, duk yanda take zame-zame bai direta a ko inaba sai falonsa.
Tanajin ya ajiyeta ta ɗago fuskarta daga jikinsa dajan jikinta dake ɓarin tsoro baya dan catake ko duka zataci, duk da dai bata taɓaji a tarihi ko labarinsa ya taɓa dukan kowaba a gidan nasu, barsa dai da barazana da mazurai, hana rantsuwa marin da yayma matarsa a london sanda ta shaƙeta, shima ba wani lura tai da ƙyauba ranar dan a firgice take sai da su Meenal suka bata labari.
Baya ta dinga ja tana girgiza kanta. “Yayanmu ALLAH bance komaiba, ka tambayi Yah Khalipha”.
Hannayensa ya zuba a aljihu duka biyu yana binta a baya fuska a tamke, sai wani lumshe idanu da buɗewa yakeyi akan lips ɗinda dake motsawa a hankali da yanayin tsoron daya bayyana ƙarara a fuskarta. Tana tafiya yana binta sai ji tai ta dangane da bango, juyawa tai a firgice ta kalli bayanta, ganin dai da gaske tazo ƙarshe hankalinta ya ƙara tashi, ta dubesa da saurin yin ƙasa zata durƙushe ya riƙo hannunta.
“Yayanmu wl.....”
“Shiiii!!!..”
Ya faɗa a hankali yana saka idanunsa da suka canja launi cikin nata, tare da saka duka hannayensa a bangon ya dogareta yanda babu damar kuɓuta kenan. Gashi ya hana kuka dole kuma ta haɗiyesa, sai dai zuciyarta kamar zata faso ƙirjinta ta fito.
A wani irin ƙasa da murya sosai ya fara magana idanunsa cikin nata da takeson janyewa ya hana. “Dama idan kuka zauna gulman mutane kawai kuka iya ko?”.
“Wlhy a'a Yayanmu, bama gulmar kowa ka tambayi Granny”.
“Ni yanzu danaji ana tawa fa?”.
“Y...y...Yayanmu ba gulm...ma bane fa?”.
“To miye sunansa?”
Shiru tai dan batasan mi kuma zatace ba itakam. Hakan datai ya sashi juya idanunsa yana sauke hannunsa ɗaya dake dafe da bango ya maida cikin aljihu. Yace, “Anyhow zan fara hukuntaki kafin ita mai baku lecture ɗin na kamata da sauran ɗaliban nata”.
“Wayyo Yayanmu, wayyo Yayanmu”. Zinneerah ta faɗada iyakar marairaicewar data saka AK cije lip ɗinsa, yana binta da wani irin ƙasalallen kallon daya saka hawayen ƙaryarta ɗaukewa ɗaf ta shiga mar mar da idanu zuciyarta na harbawa da sauri-sauri..........✍
Leave a Comment