Makauniyar Kaddara 55
Page 55*
.............Motarsa ya buɗe ya shiga badan son tafiya ba sai dan son samun sararin yin tunani. Dan abinda ƙwaƙwalwarsa ke neman ayyana masa game da zantukansu sosai yake figitar da ziciyarsa. Lallai yana buƙatar
haɗuwar Aunty Zakiyya da Zinneerah akan wasu dalilan da yake auna labarin data bama Granny da nasu zantukan, sannan yana son sanin mi zasu tura Farah yi Morocco?, dan idan bai mantaba tunkan tahowarsa Nigeria a wancan karon Mammah ta sanar masa Farah zataje Morocco tayi rainon cikinta kamar na farko har sai ta haihu. A lokacin bai amsa mataba yace ta bari ya dawo daga Nigeria zasuyi maganar, shine kuma komawar tasa ya koma da Hajiya Iya. Kenan tafiyar tata nada alaƙa da wani abu dake ɓoye kenan?.Ya jima yana tarawa da kwashewa, daga ƙarshe ya yanke shawarar komawa cikin gidan bayan ya kira Khalipha yace idan yaje gidan ya jirasa karya tafi. duk da Khalipha nada nashi uzirin shima sai ya amsa masa da to saboda girmamawa. Dan komai girman uzirin nasa zai iya ajiyewa domin amsa kiran Yayan nasu.
Sai da ya gyara yanayinsa sannan ya tada motar ya ƙarasa gaban gate ɗin da ita. Yayi horn kusan sau huɗu sannan aka buɗe masa. aunty Zakiyya ce da kanta dan gidan babu maigadi tazo ta buɗe masa, hasalima mijinta ya sayesane kawai saboda harkokin siyasarsa idan ta kawosa kano yakan sauka.
Yana gama fakin tana ƙarasowa inda yake, yanda tai wani kicin-kicin da fuska sai ya ƙara ɗaure tasa shima. A ɗage yace mata, “Barka da safiya” yay gaba abinsa batare daya jira amsarta ba. Bayansa ta raka da harara zuciyarta na ƙara mata zafi akan rainin wayonsa. Dama can ita bawani shiri take dashi ba sosai. Ta girmesa sosai amma sam baya bata irin girma ɗin nan yanda take buƙata, wani lokacinma idan yana mata faɗa akan abu sai ka ɗauka shine babba, dan akwai lokacin da mijinta ya taɓa sanar masa wata rigimarsu, daya bincika yaga itace bata da gaskiya ya dinga mata masifa harda cewa zai iya mata dukan tsiya har sai fatar jikinta ta fashe.
Suna gab da shiga falon tace, “Kai yanzu Abdul-Mutallab ka ƙyautama kanka kenan?”.
Batare daya juyo ya kalletaba a daƙile yace, “Da nai mi?”.
Cikin hasala tace, “Aure!. Mi kake buƙata ga mace wanda matarka bata da shi? Wane irin rayuwane wannan mutum yayta tara mata a gidansa kamar wani binsuru.....”
Cak ya tsaya tare da waiwayowa gareta tamkar mai ciwon wuya, ya zuba hannayensa duka cikin aljihu yana jifanta da wani irin shegen kallo da har cikin ranta sai da razani ya kamata, “Masu mata huɗu da ƙwarƙwara su kuma wane matsayi kika basu?”.
“What!?”
Ta faɗa a razane tana kallonsa dan tasan da ubanta yake. Gira ɗaya ya ɗage mata yana ƙara kicin-kicin da fuska. Cikin hayayyaƙo masa itama tace, “Mikake nufi Abdul-Mutallab?”.
“Na baki gundarin baƙin ai, sai ki masa fassarar data dace”. Ya bata amsa da juyawa ya cigaba da tafiya abinsa kamar bashi ya aikata tsiyarba.
Wani irin ƙululun baƙin ciki ya saka idanun Aunty Zakiyya cikowa da ƙwalla, cikin ƙunar rai ta fara zazzaga masa masifa. Ko waiwayenta bai sakeyiba harya shigo falon gidan da sallama.
A kusan tare Mammah da Mahma da Farah suka ɗago suna kallonsu, musamman Zakiyya dake masifa iya iyawarta.
“Ku lafiya kuwa?”.
Mahma ta faɗa tana tsare Abdul-Mutallab da idanu. Zama yay kusa da ita cike da basarwar da ya iya yace, “Mikika gani Mahma?”.
Sosai ta sake zuba masa idanu dan tasan halin Abdul-Mutallab ɗin ya iya manni ya kuma fika tsare gida, sai kuma ta maida ga Zakiyya dake masifa iya iyawa har hawaye na sauka mata a fuska. Kafin ta sake cewa dasu wani abu Mammah tace, “Wai miya faru Zakiyya kike wannan zantukan?”.
Hawayenta ta share da nuna AK dake zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya ya jingina da kujera ya lumshe idanunsa, yayinda Farah ta kafesa da ido zuciyarta na harbawa da sauri-sauri akan yanayinsa. “Mammah waini Abdul-Mutallab zai jefa ubana da kalmar suna bunsuru!”.
A kusan tare Mammah da Mahma sukace, “Bunsuru kuma?”.
“Ai gashi nan ku tambayesa mana”. Ta sake faɗa tana fashewa da kuka.
Ganin ko motsi baiyiba yasa Mahma kallonsa da ƙyau tace, “Abdul-Mutallab!”.
Idanunsa ya buɗe a hankali ya kalleta batare daya motsa ba. “Miya kaika wannan zance haka babu daɗin ji? Zakiyya ba yayarka bace?”.
Murmushi ya saki mai ƙayatarwa a karon farko da ɗan yamutsa fuska, kansa tsaye yace, “Mahma ni ƙarya takemin, ita da bakinta ta kirashi hakan”.
Ba mahma ba har Farah sai da ta maida kallonta ga Aunty Zakiyyan da tace, “Kaji munafiki, dagafa na masa magana akan ƙara aurensa nace miyasa zaita tara mata kamar wani bunsuru shine yace wai masu mata huɗu da ƙwarƙwara fa? Kenan yana nufin Abbanmu ko?”.
“To ke miya kaiki faɗa masa haka Zakiyya da girmanki? Aure ba ALLAH ya halasta ayisa ba? Taya za'a danganta wanda yay koyi da MANZON ALLAH (S.A.W) da wannan mummunar kalmar domin ALLAH idan ba neman tada zaune tsaye ba? Dan ALLAH ku ringa sassautama kanku, rayuwarma duka nawa take ALLAH natuba. Kai kuma Abdul-Mutallab baka ƙyautaba daka bata wannan amsar, saika fahimtar da ita kuskurenta ko kai mata shiru”.
“Am sorry Mahma” ya fa ɗa batare da nuna nadamar abinda yay ma aunty Zakiyya ba. Mammah kuwa kasa cewa uffan tayi. Zakiyya ma ƙin cema Mahma komai tayi, dan kai tsaye ta fassara abinda Mahma tayi da son kai. Duk da Mahma ta fahimceta batabi dakantaba ta fara musu nasiha su duka. Sai da ta gama AK ya samu damar gaishesu.
Rai ɓace Mammah tace, “Sai yanzu muke ganinka a gidan? Bayan kasan matarka na cikin halin rashin lafiya, Abdul-Mutallab! Abdul-Mutallab! kana shigarmin hanci fa da yawa”.
Murmushi yayi yana gyara zamansa. Cike da girmamawar da yake bata yace, “To yi haƙuri karki fyatoni Mammah, ba gani nazoba yanzu kuma nama ganta ragal”.
Harara Mammah ta zuba masa kawai dan takaici, zata ƙara magana Mahma tai saurin katseta da faɗin, “Tunda ya nema afuwa basai a sarara masaba a kama wata tashar kuma”.
Dole Mammah ta haɗiye maganar tana marairaice fuska. “Ke kam Addah bakison ace yayi abu saiki fara karesa, to naji yanzu sai ya nema mana ticket ɗin tafiya Morocco”.
“Morocco kuma Mammah? Mizakuyi acan a irin wannan lokacin daba komai akeyi ba?”.
“Eh to lallai ubanmu, sai ana wani abu zamuje tushen uwarmu kenan? To Farah zamu kai ta ƙarasa rainon cikinta acan har sai ta haihu.”
“Kaji kuma wani abu, to banda abinki Mammah sai kace mai cikin fari? sannan wancan karonma bacan tajeba har ya zama sanadin fitar cikin? Ni wannan karonma na yanke shawarar a Nigeria zata haihu babu inda zataj......”
Tassss!!! kakejin sautin fashewar kofin hannun Farah da take shan tea tun shigowarsa. aunty Zakiyya kam a bazata tace, “What!”. Mammah kuma ta ɗan zabura jikin kujera da faɗin, “Baka isaba ko!”.
Yanda sukai ɗin ba ƙaramin mamaki ya bama Mahma ba, shiko sai yay wani shegen murmushi da komawa ya lafe jikin kujera yana zuƙar sassanyan numfashi da iskar ac ke busowa.
Mahma tace, “To minenen abin razana anan? Dan kawai yace a Nigeria matarsa zata haihu? Ai hakan da yay shine dai-dai, kuma shine zai ƙara kawo dai-daito tsakaninta Farah da ƴan uwansa ko?”.
“Adda bazai yuwuba wlhy, karma ki goya bayansa a wannan gaɓar dan tafiya da Farah kamar nayi na gama ne, sannan maganar yarinyar dake gidanka yaya muke ciki?”.
“Ki tayamu addu'a kawai Mammah”. Ya faɗa kansa tsaye.
“Uban addu'a zan tayaku ba addu'a ba Abdul-Mutallab, ni kake gayama na tayaka addu'a akan wannan figaggiyar yarinyar da'a haihuwar kaji ka isa haifarta, to wlhy tunma muna shaida juna ka sakar musu yarinya ko na ɓata maka ranka”..
“To amma Mammah baƙya ganin idan na aikata hakan shima Baffah zai ɓata ran nawa? Kiyi haƙuri kawai kamar yanda nai biyya a zaɓinki shima nayi biyayya anasa. sannan kuma idan ina sonta kuma fa....”
Kafinma ya rufe baki Farah ta fashe da wani irin razanannen kuka sai da Mahma ta daka mata tsawa tasa hannu ta toshe bakinta tana faɗawa kan Mammah.
A zafafe aunty Zakiyya tace, “Wlhy inma baka saketaba da ƙafarta saita bar gidan”.
Banza yay kamar bai jitaba, zata sake magana Mahma ta harareta dole tai shiru tana ƙunƙuni. Cikin rawar murya na alamar jin zafi Mammah tace, “Abdul-Mutallab na rantse zan iya tsine maka akan auren yarinyarnan. Dan haka na baka kwanaki bakwai kacal ka sallameta. Idan kuma ka kuskura ko ɗan yatsanta ka taɓa ALLAH ya is......”
Da sauri yace, “Oh Mammah Please!.....”
Yanda yay maganar cike da ƙosawa ya sata dakatawa tana kallonsa. Cikin ƙunar da zuciyarsa ke masa yace, “Bama sai kinyi wani ALLAH ya isaba haba sweetheart, nifa wasa nake miki kawai dan naga yaya ƴarki zatayi? Tana sona har yanzu kokuwa?, indai nine ki bani wata ɗaya kacal zanyi komai a tsare yanda shima Baffah bazaiga na masa tsageranci ba harya canja wata hanyar da ni dake zamu gaza ganewa kuma ok?”.
A yanda yay maganar seriously yasata yarda dashi, dan tasan halinsa bayason dukkan abinda zai ɓata mata rai, cikin gamsuwa tace, “Idan ka saɓamin alƙawari Abdul-Mutallab bazan maka da sauƙiba fa”.
“Karki wani damu kanki Noorunnisa, sai dai ga shawara, dan akwai abinda naɗan hango idan akace na saketa yanzun, kiɗan sassauta kinsan shima Baffah akwai taurin kai, idan wata ɗaya bataiba zan iya kaiwa biyu ko uku haka, dan dole na haɗa da Granny, kinga hakan na nufin kenan gara ayi sakin cikin hikima yanda zan ɗaura laifin akan wani abu taimin ita yarinyar bawai kece kika saniba. Dan wlhy yanda Baffah ya fusata nace zan saki yarinyarnan yanzu to kuwa zai auramin mata uku rana ɗaya, ya kuma kafamin sharuɗɗan masu tsauri da bazan iya yin wani abuba, kinga kema yaci galaba a kanki kenan, amma idan cikin hikima mukai komai sai a rabu lafiya. Taɓa yarinya kuwa ki ɗauka ko kallo bata ishi Abdul-Mutallab ɗinki ba, na Farah ɗinkine kawai har a aljanna”.
Karan farko ta saki tattausan murmushi da cewa, “To ALLAH yay maka albarka, naɗan gamsu da bayaninka danni shaidace akan Kabeer da halayensa, amma kamar yanda ka faɗa ta wannan hanyarne kawai zamuyi maganinsa da wannan kakar taku sarkin iko wa ƴaƴan wasu”.
“Amin sweet Mammah”. Ya faɗa yana wani shegen murmushi daya zafafa zuciyar aunty Zakiyya ta miƙe fuuu ta shige. dan itakam tsaf ta fahimci shirya rainama uwar tasa hankali yayi kawai.
Mahma kuwa murmushi tayi itama da cewar “Nasan zaka iya Abdul-Mutallab, kamar yanda Hindatu ta faɗa haka mukeson kayi, abinda yasa zan goya bayanka kamar nan da wata ukun saboda dalilan daka faɗa suna akan hanya”.
“Nagode Mahma” ya faɗa yana wani lumshe idanu da komawa jikin kujera ya lafe abinsa.
Sosai dariya kecin zuciyar Mahma tanata ƙoƙarin danneta, a ransa kuwa tanata saka masa albarka da ƙarajin ƙaunar AK ɗin har cikin ranta. A kullum ƙoƙarin sa yaga ya kauce ɓacin ran mahaifiyarsa koda ace ya fita gaskiya, irin wannan ƴaƴan sune abin buƙatar kowa, dan suna ƙoƙarin kiyayewa daga fushin mahaifiya, su kuma kautar da ita faɗawa halaka itama dake zuwa akan dokin fushi kona son zuciya.
Farah ma tashi tai ta shige ɗaki tana rusar kuka. Hakan yasa AK miƙewa yabi bayanta. Mammah zata bisu Mahma ta dakatar da ita.
“Kinga barsu ya lallashi abarsa da kansa. Babu ruwanki a wannan sabgar tunda kinji daɗi yace zai miki abinda kika buƙata saboda ƴar so ɗin taki”.
Ƙaramar dariya kawai Mammah tayi da komawa ta zauna. “Oh Addah kemafa kina bayanmu wannan karon bare kimana wa'azi”.
“Ai nabi bayankunne kawai saboda farin cikinki, sannan nima matar tasa bataminba tayi ƙarama da yawa”.
“To kema dai ƙya faɗa Addah, bandama namiji baida kunya ba, ta ina zai fara nuna wannan ƴar ficilar yarinya matsayin matarsa”.
Dariya sosai Mahma tayi abinta.
AK da Farah kam kusan tare suka shiga ɗakin, ta faɗa saman gado tana sake fashewa da kuka mai cin rai. Shiko yana shigowa ya ɗaure fuskarsa tamau da murzawa ƙofar key sannan ya ƙaraso gaban gadon cikin takun izza da bayyanar ɗacin da zuciyarsa ke masa ƙuru-ƙuru akan fuskarsa. Cikin tsananin kaushin murya yace, “K tashi zaune!”.
Sosai yanda taji muryarsa ya ƙara razanata. Dole ta miƙe zaunen dayace tana kallonsa idanunta cike da tsoronsa. Ƙafarsa ɗaya ya ɗora saman gadon ɗayar na ƙasa yana binta da wani shegen kallo daya saka jikinta fara tsuma tana girgiza masa kanta hawaye na rige-rigen fitowa.
“Share waɗan nan hawayen, kuma ki nutsumin wlhy kona karyaki a ɗakin nan na karya banza”. yay maganar yana matsar da fuskarsa gab da tata da nunata da ɗan yatsansa cikin gargaɗi. Hannu tasa da sauri ta goge hawayen tana magana cikin rawar murya, “Yah Abdul-Mutallab wlhy ba laifina bane, ni bani nace zanzo nan ba, tashi kawai nayi na ganni anan gidan”.
“Bashi na tambayekiba, dan matdalarkice ba tawaba wannan”. Ya katseta a kausashe.
“Dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy banason kishiya, zan iya mutuwa ka taimakeni ka barni ni kaɗai, na rantse da ALLAH zan dinga maka duk abinda kake so daga yanzun”.
“Daga baya kenan yarinya. ai kin makaro kuma, dan na baki damammaki bama damaba amma kika cigaba da ɗaukata ɗan iska ko maijin tsoronki ma. Dama na tabbatar miki a randa yaran nan sukaje London inhar kika sakamin ciwon kai sai na baki na zuciya. Koda yake wannan duk bashine a gabanaba yanzu, dan idan na tafi kema kinsan bana waiwaye. Gargaɗi zan miki idan kinbi kin huta, idan kinmin taurin kai da shirya samun ciwon kai wlhy sai na saka miki na jini bayan na zuciyar da kika samu yanzun, kindai sanni sarai. Koda ban miki gargaɗin nanba nasan baki da wata dama ta sake barin ƙasar nan yanzu, amma dole zan miki. Kiyi duk yanda zakiyi ki tabbatarma da Mammah zaki haihu a Nigeria, inba hakaba wlhy ki kuka da kanki, dan inhar ta ɓata ranta a kaina toke zuciyarki da kamanninki zan ɓata gaba ɗaya a rasa ganeki. Ki kuma nutsu akan wannan haukar sumar da kuka da kikema mutane, bake kika jawa kanki kishiyar ba, saurama biyu zan ƙaro bayan wannan shashasha kawai”.
Ya ƙare maganar da sauke ƙafarsa ƙasa yana binta da wasu shegun looks masu riƙe maƙoshi da ƙahon zuciya.
Sai da yaje gab da ƙofa ya juyo cikin wani gargaɗin yace, daga nan zuwa kwana biyu ki dawo inda na ajiyeki, na baki kwana biyunne ma dan banason takurar kowa a cikinsu, idan kuma kin fita yanzu ki sanar musu duk abinda mukai a ɗakin nan, ni kuma na tabbatar miki sunana Abdul-Mutallab Kabeer Shira”.
Daga haka yay ficewarsa. Koda ya fito falon babu wata alamar akan fuskarsa dazai nuna ba lallashin Farah yayba da gaske. Bai zaunaba yay musu sallama akan yana son yin wani uziri ƙilama ya wuce Jigawa duba masu aiki.
Mammah ce ta kallesa cikin harara, “Ban gane zaka wuce Jigawa ba tickets ɗinmu fa?”.
“Oh GOD, Mammah Please kibar maganar zuwa Morocco ɗin nan dan babu ita, idan haihuwarta a london ne baƙyaso nace miki zata haihu anan ne. Zaku iya barmata Mahma su zauna tare kokuma a samo tsohuwa daga Morocco ɗin ta zauna da ita, ke kanki akwai maganar business da nakeson nayi dake wani abokina yanason kaya naga kuma kina dasu. Bye bye ana jirana nikam”.
Daga haka ya fice abinsa dan baiso ta ƙara tofa komai................✍
Leave a Comment