Makauniyar Kaddara 54
Page 54*
...........Duk yanda taso dojewa a baya doleneta ta yarda suka shigo sashen nata a tare, kusan duk sai da suka ɗago suka kallesu jin sassanyar muryarsa na sallama. Bayansa ta koma ta maƙale saboda kunya da taji na
iyayenta da ƴan uwanta. Gani take kamar kowa zai gane abinda ya faru kafin su shigo, Aunty Salima ce ta bashi kujerar da take zaune. Babu musu ya zauna yana musu sannu da zuwa fuskarsa a ɗan sake.Cikin mutunta juna sukai gaisa. Yana musu godiya suna masa, tare da jera musu addu'oin zaman lafiya mai ɗorewa na har abada da zuri'a mai albarka da nagarta. Gwaggo Maryama ce tai masa bayanin kowa a wajen da matsayinsa wajen Zinneerah, ya ƙara musu godiya yana ambaton masha ALLAH. Kafin ya miƙe bayan suma su Meenal sun gaishesa.
Sai da yazo saitin Zinneerah dake tsaye yay magana ƙasa-ƙasa yana raɓata ya wuce. “Ki sameni idan sun tashi tafiya”.
Binsa da kallo kawai tai ta gefen ido dan ya riga ya shige bai bata damar amsa masaba. Hankalinta ta maida akan ƴan uwanta dake yabonsa da sake jera masa addu'an fatan alkairi. Ita dai uffan bataceba sai zama data sakeyi. Sun ɗan ƙara taɓa hira kafin su mike domin ganin ɗaki. Lungu da saƙo babu inda basu shigaba, Sa'a nata santi da ƙarajin daɗin sauyin rayuwa da ƴar uwarta ta samu. Hakama Yaya Gajeje bakinta yaƙi rufuwa dan farin ciki. Karima da Atine kam dai anata naɗar rahoton da za'a kaima Inna fuska a taɓe.
Babu wanda ya damu dasu, dan ƴan ɗan-musan ma dasu Gwaggo Laritu sai faman yabawa sukeyi abinsu. Bayan sun gama zagayensu sukai haramar tafiya, maganar cewa ta sameshi yasata cewa su jirata tana zuwa. Duk da ranta cike yake da fargabar abinda ya faru ɗazun ga kunyarsa haka dole ta nufi sashen nasa again.
Yanzu kam bata tsaya knocking ba sallama kawai tayi da murɗa kofar ta shiga, yana tsaye alamar shirin fita yake ta shigo bayan ya amsa mata sallamarta da bata izini. Kanta a ƙasa saɓanin shi da yake kallonta kai tsaye, yanda batai magana ba shima baiyiba, sai ma ya ɗauke kansa daga kallon nata yana ƙoƙarin tattare takardun daya baza a falon. Ganin haka yasata faɗin, “Yayanmu zasu wuce”.
Bai amsataba sai da ya gama abinda yakeyi, ƙananun ledoji guda biyu dake a saman kujera ya nuna mata, “Ki bama Gwaggo Maryam ɗaya taba ƴan ɗan-musa, ɗayan ki bama Gwaggo ta danya nasune suma”.
Ɗaukata tai tana kaiwa tsuggune. “ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara arziƙi mai albarka da amfani, ya cigaba da baka kariya a dukan al'amuranka”.
Har cikin ransa yaji daɗi da farin cikin wannan addu'a tata, dan haka yay ɗan murmushi yana amsa mata da “Amin, nagode”.
Kamar yanda ya bata umarni haka ta aikata, aiki suka shiga godiya da masa addu'a harta rakosu harabar gidan ita da su Meenal. Kasancewar motocin da zasu wuce dasu suna ta waje yasata jan birki iya nan tana hawaye. Rungumeta Sa'a tayi itama tana hawayen, dan harga ALLAH tanason Zinneerah. jitake kamar karsu rabu a yanzu, amma yaya zasuyi da ƙaddarar aure sai haƙuri.
Tanaji tana gani suka wuce su Bahijja suka tafi rakasu har waje. Jikin bango ta lafe hawaye na cigaba da sakko mata, ɗan kwana ukun can da taje tayi a Danya sam ba isarta sukai ba, musamman da ayanzu baba ya samu ƴancin kansa daga hannun Inna, sai taji inama tana a zaman gidan ne har yanzu.
Dawowar su Bahijja ya sata share hawayenta suka koma ciki suna mata tsiya ƙasa-ƙasa gudun kar Yayansu yaji. Ita dai hararsu kawai tayi dan basusan yaya takejinta bane. Da taimakonsu ta gyara falon, suna ƙoƙarin dasa zaman hira AK ya shigo. Tsit sukai daga dariyar zancen Meenal dake basu labarin abinda wata innarsu datazo daga bauchi tayi a sashen Granny yau da safe.
“Ku baku wuce ba?”. Ya faɗa idonsa akan Zinneerah. Meenal ce tai ƙarfin halin bashi amsa. “Yayanmu muna nan sai anjima, dan ƴan bauchi ma zasu zo suyi muku sallama”.
Baice komaiba sai kallon agogon hannunsa da yayi ya sake duban Zinneerah. “Ni zan fita, Khalipha zaizo da mai gyaran ruwa dake fita ta baya, idan sun gama ki ɗauka masa kuɗi a ɗaki saman bedside drawer”.
Kanta ta gyaɗa masa da cewa “to” idanunta a ƙasa. Daga haka shima ya juya ya fita a binsa suna masa a dawo lafiya.
Sai da suka tabbatar da fitar motarsa a gidan sannan bakin su Meenal ya buɗe. Suka sheƙe da dariya suna tafawa da faɗin, “Soyayya ruwan zuma. Abin mamaki Yayanmu da auta a gado ɗaya”.
Hararsu kawai Zinneerah tayi ta ɗauke kanta. Bahijja ta kamo hannunta murya ƙasa tace, “Tawan dan ALLAH da gaske ɗaki ɗaya kuka kwana da Yayanmu a gidan nan?”.
“Ya ilahi”. Zinneerah ta faɗa tana zaro idanu, sai kuma ta rankwashi kan Bahijjan da faɗin, “Kirasa a waya ki tambayesa mana, wai yaushe kuka lalace haka ne?”.
“Karkiga laifinmu, tunda kema jiya Yayanmu ya lalataki a gado muma gara dai ku guntsa mana kafin a kaimu dan wlhy nima aure nakeso”. Cewar Meenal tana wani karya jiki.
Bahijja tai zaram tana faɗin, “Haɗa dani ƴar uwa”.
Kallonsu kawai Zinneerah take baki buɗe, suko ko'a jikinsu. A haka su Jamal suka shigo suka samesu ɗauke da abincin rana, yanzu kam a sake suka shigo dan sunsan sun baro boss a can gidan.
___________________★
A ɓangaren su Farah kam lafiya lau ta farka yau, sai dai tunda ta tashi hawaye basubar sauka mata a idanu ba, sai faman sambatu take akan dan ALLAH suce mata mafarki take bada gaske AK yayi aure ba.
Da farko daga Mammah har Mahma lallashinta sukeyi, ganin abun nata bana ƙare bane yasa Mahma fara mata masifa.
“Ke dan ALLAH kin ishemu haka nan, ba'irin wannan ranar ake hanngo mikiba ana nuna miki hanya kina kaucewa. Ni bansan wane irin rashin hankali ke damunku ku yaran yanzu da bakwa aiki da tunaninku ba. Abinda kawai kuka ɗauka idan namiji na sonku dolene ya cigaba da sonku, kun manta ita soyayya ado ce a cikin aure, a duk lokacin da ɗiya mace ta kasa toshe ƙofofi da ramukan ginshiƙan aurenta adon soyayya zai disashe. Duk yanda zakiso miji ki nuna ƙin danginsa rayuwar aurenki na cikin matsala koda kuwa su suna nuna miki basa son nakine ƙiri-ƙiri a gabansa. Koda shike kawo miki sukar danginsa ki faɗi alkairi da tausar zuciyarsa karki yarda ki tofa mara daɗi. Kiyi haƙuri da halayensa ku kashe ku rufe a ɗakinku dan kai ƙarar miji ga iyayenki ko nashi na zubar miki da kima, ke hatta ƙawayenki kikace ke kullum ƴar fallasa asirin gidankice da niyyar neman shawara to kina cikin kwan gaba kwan baya kuwa a garesa da zubar muku da kimar aurenku. Domin shi aure ibada ne ba komai ake samu hundred percent a cikinsa ba. Dole yau ayi dariya gobe kuka, jibi rabi da rabi tsakanin ɓacin rai da farin ciki. Sannan duk son da namiji ke miki kika nuna zaƙewa da yawa akan kishinsa har zargi na zuwa miki a harshe da tunani to lallai ki tabbata zaki koma 0 a ziciyarsa. Matan yanzu da yawa ba kishin mazansune kaɗai matsalarsu ba, harda zargi. Idan miji ya fita zuciyarki na miki kaikawo yanacan tare da wasu matan, idan ya shigo gida ya ɗauki waya bazakiyi masa zaton alkairi ba sai kice yana cheating da wasu matan. Idan yana huɗɗa da mata a ikinsa ko kasuwanci zuciyarki taita kitsa miki karuwansa ne, idan mai yawan sakewa ne da mutane ki zargesa da yawan son mata. To dama kin taɓa ganin namijin daya rayu babu mace a ransa? Komin tsanani da tsantsenin ki baki isa hana namiji ɗabi'ar son mata ba dan haka ALLAH ya haliccesu, ba kamar ke bace da akai miki iyaka dakinyi aure shikenan. Daga lokacin da kishi ya sakaki yawan zargin miji koda hankalinsa baya kan matan ma to zai fara nutsuwa wajen fuskantarsu, daga ƙarshe kodai ya ƙaro auren da kike tsoro, ko ya fara bin matan a waje su halakashi kema ya halakaki, waya janyo?. Ki nutsu ki zama jaruma ta kowanne fanni, nasan yaƙine ba ƙaramiba amma inhar kinsa kanki zaki iya, koda kina kishin mijinki ki dinga dannewa kinayin mai aji wanda shi kansa zaisa yaji shakkarki akan wata macen, da kuma shiga damuwar anya ma kina sonsa? Ya dingaji ƙaimi wajen kafa soyayyarsa a gareki dan yaga wannan kishin naki amma hakan ya gagaresa, sai kiga yafi lalacewa a wajenki fiye da wadda yake hange a wajen. Duk da nasan maza kala-kala ne kuma kowanne da irin nashi salon, ki nutsu ki karanci nakin, ki daina kuma tilastama kanki sai kin samesa ɗari bisa ɗari yanda kike buƙata. wannan bamai yuwuwa bane a gareki, dan kema baki cika hundred percent ɗin ba a garesa. Mijinki na sonki Farah, yana kuma miki kawaici darajar mahaigiyarsa da na zuminci, amma kinata ƙara sakaci da damarki, wadda idan har kikai wasa anzo gaɓar da zaki iya rasashi ma baki ɗaya wlhy, dan Abdul-Mutallab yana tarakine kawai, ina jimiki tsoron randa zai kai ƙarshe a al'amuranki, duk yanda kike tunanin Hindatu na tsaya miki bazai sauraretaba itama, sai kuma kin fita kwana a ciki dan ita uwa ce babu yanda zai mata. Aurensa bashi ke nufin ƙarshen rayuwarki yazo ba, yanzune ma ya dace ki zage damtse wajen dawo da kimarki da martabarki a wajensa, inba hakaba kuka yanzu kika fara dan zaibi ta hanyar ƙara auren nasa ya rama dukkan ƙuntatawar da kike masa ke da Hindatu, hakama danginsa zasuyi amfani da ita wajen ganin sun rusaku ke da ita ɗin tunda kin shiga makarantarta babu gaira babu dalili, itama ɗin da take hura hanci sun mata laifi banga ta inda sukai matanba balle ke da kikai taka haye akan abinda bakisan yaya yake ba. Ƙiri-ƙiri tana amfani dake akan wani shashanci nata mara tushe balle makama. Sai ki shiga hankalinki idan zaki shiga, dan daga ita har Zakiyyar ba hanyar da zata ɓille dake suke ɗauraki ba”.
Tana kaiwa nan ta miƙe ta barta da sharɓar kuka tana nazarin maganar Mahma ɗin dalla-dalla. Dan tabbas sanda bata zama haka ba dukkan kulawa da tattalin rayuwa Yah Abdul-Mutallab yana batasu, danshi mutum ne mai kawaici, idan kuma ya ɓalle bayajin bari. Yasha nusar da ita illar kai ƙararsa da takeyi ga Mammah da Aunty Zakiyya amma ta kasa fahimta, dan a ganinta Mammah da Aunty Zakiyyar ne kawai zasu iya saita mata bauɗaɗɗen halinsa na tsiya koda yanaso ko bayaso. Ashe ba haka bane, sake kangarar masa da zuciya kawai sukeyi da kusantashi da dangin nasa da suka tsana. Itakam ta shiga uku, wlhy bazata iya zama da wata ɗiya mace a matsayin kishiya ba koda kuwa ƴar waye.
A lokacin da Mahma da Farah ke wannan maganar Zakiyya da Mammah nacan sun kulle kansu a garden suna maganar da suka gagara samun sararin yi tun ɗazun.
“Mammah inajin tsoro wlhy, anya mutanen nan basu fahimci wani abu daga garemuba suketa ambaton zancen dashen ciki? Gashi munyi sakaci wannan harmutsin na neman kaimu ga tonon silili, lokaci yayi da Farah zata koma Morocco da zama harta haihu amma hakan ya gagara. Kigafa yanda abokinsa yayi jiya da akace tanada ciki”.
“Hakane Zakiyya, nima kaina da abin nan na kwana a raina jiya, babban tashin hankalina kuma yaƙin da mukeyi ɗinma baiyi amfaniba, tunda gashi dai Kabeer na neman cin galaba a kaina tunda sun aura masa wadda suke so ɗin, amma na ɗau alwashin sai Abdul-Mutallab ya saketa wlhy. Babban tashin hankalina a yanzu zancen yaron nan da Abdul-Mutallab ya haifa da yarinyarnan. Nasanshi sarai akan faɗar gaskiya, da ace ya aikata wani abu a gareta har aka samu cikin ko zamu kashesa sai ya faɗi yanda akayi, amma ki dubafa yace shima baisan yarinyarba sai a gidansu, kuma ma idan mukai aiki da hankalinmu muma ta ina zai santa? ita da akace a wani ƙauyen ƙayau take da ko kwalta basu da. Wlhy na rasa ina tunanina zai shiga, yarinyar dai dana san anyima aikin farko a gabanmu tai ɓari balle muce ko ƙarya tai mana taje ta haihu a wani waje. Kuma bama ita bace wannan dan waccan babbace ma ai, wannan kuwa yarinyace ƙarama fa sweet 17”.
Gumi aunty Zakiyya ta share wani bahagon tunani nason mata kutse a ƙwaƙwalwa, ta haɗiye yawu da ƙyar tana gyara tsaiwa, “Mammah inason ganin ita wannan yarinyar dan kinsan ni bamma santaba”.
“To Zakiyya miye amfanin ganinta tunda tunda ba wani abu muka haɗa da itaba. Ko akwai wani abu da kike tunani wanda ni ban sanshiba?”.
“A'a wlhy Mammah ”. Tai saurin faɗa tana girgiza kanta da ƙara share gumi.
“To kin gani. ai ganin nata baida amfani dan jira nake yazo gidan ma yanzun nan ya rubuta mata takardar saki ta kama gabanta. A yau kuma nakeson mubar ƙasarnan da Farah kafin ita kanta Addah da farga da halin da muke ciki, dole kuma mu sake neman wanda zai mana bincike sosai akan yarinyarnan, dan na kula wancan da yay mana shirme kawai ya tafka yaci kuɗi shegen, dan binciken nasa akan auren Abdul-Mutallab da yarinyar kawai ya tsaya. Ni kuma ta inda yarinyarnan ta samu ciki nakeson sani, dan ta wannan hanyar ne kawai zamu fahimci inda matsalar ta faro mukumayi maganinta kafin su Kabeer su kaimi ƙasa. Duk da yaron na tsananin kama da Abdul-Mutallab ban yarda da gwajin da akace an musu ba, gani nake kawai haɗin bakine dasu Kabeer dan a tabbatar da ɗan nasane a kaini ƙasa wajen aura masa yarinyar da maidosa zama cikinsu”.
Nanma kai kawai Zakiyya ta gyaɗama Mammah dan tunaninta ya fara ƙarfi akan abinda zuciyarta keta mata kai kawo....
AK dake tsaye a ƙofar garden ɗin tun fara maganarsu ya dinga jan ƙafafunsa da sukai masa nauyi da baya-baya zuciyarsa na wani irin harbawa, idan har lissafinsa da abinda yaji zasu iya zama a muhalli dai-dai kamar akwai lauje cikin naɗi a maganar Mammah da aunty Zakiyya. Dan tun fara maganarsu akan kunnuwansa suka shiga kaf. Kasancewar a can wajen gate ya ajiye motarsa ya shigo shi kaɗai. Hango a yanda su Mammah suka nufi garden ɗin lokacin da yake shigo gidan ya sashi tunanin ko wani abune ya faru shine yabiyo bayansu. Furicin Zakiyya na farko ya sakashi dakatawa daga yunƙurin shiga cikin garden ɗin da yayi ya tsaya saurarensu.............✍
Leave a Comment