Makauniyar Kaddara 53

 


Page 53*


............Bai nuna yama fahimci yanda ta firgitan ba ya fara magana a hankali da ƙoƙarin buɗe kular tana a jikinsa. “Wannan ba aikin amarya bane, koda yake amaryan marowaciya ce”.

      Yanda yay maganar a saitin kunnenta yasa tsigar jikinta tashi, ga ɗunbin mamakinsa dan batai zaton sa  hakaba sam. ta ɗan ƙanƙame jikinta daya fara rawa dan wannan shine karon farko a rayuwarta data kasance da namiji a irin wannan kusanci. Abin tashin hankalin ma da ɗunbin kunya namijin ya kasance Yayansu, abinda bata taɓa kawowa a mafarkintaba balle hasashe.

        Ƙamshin naman kazar da akaima gyara na musamman dake kular daya buɗe ɗin taɗan kalla jin yace, “Uhm-uhm Momie ta hutar dani sayen kazan amarya kenan”.

        Ba ƙaramin mamakinsa ke ƙara dasuwa a rantaba, ta haɗiye yawu da ƙyar dan bata da burin daya wuce ya matsa daga manneta da yayi. Harta fara murna ganin ya maida kular ya rufe, ya ɗan matsa baya kaɗan yana raba jikinsa da nata. Sai kuma taji ya kamo hannunta cikin nasa ya juyo da ita suna facing juna.

      Sake dulmiyewa cikin matsananciyar kunya tayi, tai azamar duƙar da kanta zuciyarta na harbawa da sauri-sauri. Shiko tsaywa ya gyara da ƙyau yana tura hannayensa cikin aljihun wandonsa. Duk da kanta a duƙe yake tanajin yanda idanunsa masu kaifi da ƙarfi suke yawo a jikinta. Tsahon mintuna biyu suna a haka har takaita ga daburcewa takai tsugunne tana cemasa ina kwana.

      Dariya ta bashi sosai, musamman daya san dama da biyu yay mata hakan, amma ya gimtse baiyiba. Sai ma ɗan ranƙwafowa yay ya kamo kafaɗunta ya miƙar da ita tsaye tare da jawo kujerar dining ɗin ya zaunar da ita. Shima sai yaja ta kusa da ita ya zauna.

        Yana ƙoƙarin buɗe kular dake kusa da shi cikin ɗan rawar muryar da jin nauyinsa ya haifar mata tace, “Kabari zan zuba maka Yayanmu”.

      Komai baice mataba ya janye hannunsa. Hakan yasata miƙewa tsaye ta jawo plates ɗin data ajiye sannan ta bubbuɗe kukolin.

         “Miza'a zuba a ciki”.

Tai tambayar batare data yarda ta kallesaba.

         “Duk wanda yay miki” ya bata amsa yana ƙoƙarin ɗaukar wayarsa da kira ya shigo.

      Cike da fargabar karta zuba abinda bayaso ta haɗa komai a gabansa, harda kunun gyaɗa dake cikin flask madaidaici, daga haka ta ɗanja kujerar baya da nufin barin wajen ya riƙo hannunta. Juyiwa tai ta ɗan kallesa dan ta zata wani abun yake buƙata. Da idanunsa dake lumshewa da buɗewa kamar maijin barci yay mata nuni data zauna. Babu zance musu a tsakaninsu dan haka ta koma ta zauna.

       Wayarsa ya cigaba da yi da ɗaukar wani cokalin bayan wanda ta saka masa ya ajiye a gabanta, ya ja kofi ya fara haɗa kayan tea dake a dining ɗin a ciki. Ita dai bata motsaba tanata satar kallonsa da tunanin ko bazaisha kunun bane?, harya kammala komai ya buɗe ɗayan flask ɗin da ruwan zafi ke ciki ya tsiyaya. Motsawa ya farayi dai-dai suna sallama da Huzaifa dake faman masa sheri, ya ajiye wayar gefe da ɗaukar kofin ya ajiye gabanta muryarsa ƙasa-ƙasa yace, “Bismillah”.

      Dole ta ɗago kai ta dubesa. A lokacin shi kuma yana ƙoƙarin kai Irish daya ɗebo bakinsa. Kai ta ɗan girgiza tana marmar da idanu tace, “Yayanmu na ƙoshi ni sai anjima zanci”.

       Bai fasa cin abincinsaba bai kuma tanka mataba. Hakan da yay ta tabbatar bata da amsa kenan, dan haka ta ɗauka kofin tea ɗin ta fara sha badan yana mata daɗi a bakiba saboda zazzaɓin da take fama a kwana biyun nan.

      Ko'a can gidan tasan baya wasa da abinci, cinsa yake bil haƙƙi idan ya samu musamman zaɓinsa. Dan haka ta dinga satar kallonsa zuciyarta na tuno mata ko ina little yake yanzun?.

     Ganin batacin abincin ya ɗago ya dubeta, karaf ya kamata tana satar kallonsa. Janyewa tai cike da basarwa. Yanda tayi ɗin ya sakashi sakin wani munafikin murmushin daya tsaya masa iya maƙoshi yana mai jinjina miskilancinta a ransa.

       A fili kam sai yace, “Gulma dai ajaline. Kisa hannu kici abinci kona ɗura miki shi dan na gaji da wannan jan ajin.”

       Wani irin waro idanu Zinneerah tayi a kansa babu shiri, har cikin ranta mamakine ke neman kasheta dan batasan bakinsa ya iya zaro zanceba kamar haka. Ganin yanda shima ya waro mata nasa manyan idanun masu kwarjini da faɗin, “Zancen nawa akwai gyara ne?” ya sata saurin janye nata zuciyarta na wani irin harbawa da sauri. 

        Dolene ta ɗauka cokalin ganin ya cigaba da tsareta da idanu, gashi duk wannan zaro maganar da yakeyi fuskarsa a ɗinke take kamar yanda ta sanshi. Tsakurar abincin ta farayi. Shima daga haka ya ɗauke kansa ya maida ga cin abincin.

    Shine ya fara kammalawa saboda yangar da ita takema cin abincin ko nace kunya, ya cira tissue yana goge bakinsa da faɗin Alhmdllhi. Harta fara murnar zai tashi ya barta sai gani tai ya ɗaura hannunsa akan nata da take cin Irish ɗin da shi ya zare cokalin. Ɗebowa yay ya nufi bakinta yana ambaton “Haaah”.

      Itakam yau taga idi, ta ayyana a ranta tana buɗe bakin domin bin umarninsa. Feeding ɗinta ya cigaba dayi har sai da ya tabbatar taci da yawa ta shanye tea ɗin daya haɗa mata rabin cup, dan tun acan gidan ya gama karanceta akan rashin son cin abinci. 

         Batare da yace mata uffanba ya miƙe ɗauke da wayarsa ya nufi bedroom ɗinta. Da kallo ta bisa tana sauke ɓoyayyun tagwayen ajiyar zuciya. Duk yanda taso tashi ta fara tattare kayan hakan ya gagara harya fito yazo ya wuce hannunsa ɗauke da ɗayar wayarsa, yanzunma baiyi magana ba.

     Miƙewa tai ta shiga tattare dining ɗin tana ɗaukar kwanin da sukai amfani dasu takai kitchen. Zaman wankesu tayi, tana kammalawa kamar jira ta jiyo ƙarar door bell. Hannunta ta goge da ɗaukar mayafinta data ajiye ta yafa ta fito daga sashen nata gaba ɗaya zuwa general parlor. Ƙofarma ba wani a rufe yakeba, turawa kawai yayi, amma sai ta buɗe da tunanin ko bamai hurumin shigowa bane sai da izini.

      Wani irin ɗan karen daɗine ya tsarga mata saboda ganin Bahijja da Meenal da tawagar su Yaya Gajeje da ƴan ɗan-musa. Suka rungume juna dasu Meenal, sannan ta sakesu ta koma gasu Gwaggo Laritu. har Tinene dake nishi da ƙyar na ciwo dasu Yaya Atine da suka saki baki suna kallon ikon ALLAH. Wai wannan shine gidan Zinneerah? Yarinyar da suke kallo a wulaƙance a ƙasƙance a cikinsu?......

       Da wannan tunanin a zukatan mafi yawan ƴan Danya suka shigo ciki, inda anan nefa kallo ya koma sama. Bata barsu anan ba tai sashenta dasu, inda suka zube a falon farko su Meenal na mata magana ƙasa-ƙasa suna waige-waige.

       “Madam naji ƙamshin turaren Yayanmu. ko yana ciki ne?”.

      Hararsu Zinneerah tayi cikin gatse tace, “Eh kunada matsala da shi ne?”. 

   “Mu mun isa mu faɗa”. Cewar Bahijja tana sheƙewa da dariya da nufar ɗayan falon cikin sanɗa zata leƙa. Ɗauke hankalinta Zinneerah tai daga garesu ta maida kan ƴan uwanta daketa kalle-kalle kowa da kalar tunaninsa. Har ƙasa ta durƙusa ta gaida Gwaggoninta da yayunta, suka amsa mata suna jera mata addu'ar fatan alkairi da samun zaman lafiya a gidan aurenta. Ita dai bata iya ta amsa a fili ba dan kunya. sai su Meenal ke amsawa. Ita kuma ta kamo hannun Tinene dake kwance a ƙasa tana faɗin, “Tinene lafiya kike kuwa?”.

      Da ƙyar tace, “Zazzaɓi nake tunda mukazo”.

      “Ya salam amma shine ba'aje asibitiba? Anya Granny ta sani?”.

     Meenal ce tace, “Gaskiya babu wanda ya sani, muma sai yanzuma mukeji”.

      Sosai Zinneerah ta nuna tausayin ƴar uwar tata tanata faman jera mata sannu-sannu. 


       Tana kitchen tana haɗo musu abin sha Bahijja ta kawo mata waya zasuyi magana da Granny. Cike da ɗoki da kewarta ta amsa tana mata sallama a shagwaɓe. Daga can Hajiya iya tai ƴar dariya da faɗin, “Inno na kinfa girma”.

    Sake marairaicewa Zinneerah tayi idanunta na tara ƙwalla tace, “Nidai a'a Granny. Ina kwana”. Hajiya iya na dariya ta amsa mata da tambayar lafiyarsu, sai kuma ta ɗora da tambayar “Baƙi sun sami Moddibo a gidan ko?”.

       Cikin rashin tabbas Zinneerah tace, “Eh, amma dai basuga juna ba”.

     “Oh to ai dama abinda nakeson ji kenan. Ki kira musu shi su gaisa ya sansu su sanshi. Ki nuna masa Gwaggonninki da ƴan uwanki su Gajeje”.

      A ɗan tsorace Zinneerah tace, “Amma Granny......”

       “Amma mi? Inno idan bai sansuba a yanzu yaushe zai sansu? Suma kuma ai ya kamata su sanshi. Banason shashanci maza jeki kira musu shi su gaisa karya fice wannan sarkin sabgogin”.

      A sanyaye tace, “To Granny”. 


Dole badan taso ba ta nufi cika umarnin Granny bayan ta kawoma baƙin ruwa da lemon da aka tanada dansu ita da su Bahijja, tana ɗan sissinne kai tacema Gwaggo Laritu “Bara na kira Yayanmu ku gaisa”.

       Cikin fara'a Gwaggo Laritu tace, “Eh to ai haka shine dai-dai, ya kamata muga ɗan namu kar ai shirme shima ya gammu kuma”.

    Ita dai Zinneerah kai kawai ta kaɗa mata, ranta fal fargaba ta fito daga sashen nata, dan ko nashi sashen ba sani tai ba. Tsaye tai a general falo tana ƙarema kowacce kusurwa kallo cike da fargaba. Ita yanzu ina ita ina shigar masa ɗaki banda dai rigimar Granny da bata ƙarewa dan ALLAH?.

       Ƙofar dake facing sashenta ta fara zuwa ta taɓa. jinta a kulle sai zuciyarta ta bata maybe sashen matarsa ne. Ta kalli wadda take a tsakkiyarsu ranta na biya mata nan ne nashi. Mayafinta ta gyara da ƙyau ta nufi ƙofar zuciyarta na rawa na shakku da ganin kamar ta zaƙe. Sai dai tasan bata da mafitar daya wuce bin umarni. Koda ta buɗe ƙofar tana rumtse ido da corridor ta fara cin karo saɓanin nasu da falo ne. Ta ɗan ƙarema corridor ɗin daya sha ado da kallo kafin ta ɗaga ƙafa daƙyar zuwa ƙofar data gani ita kaɗai. Anan kam batai gigin tafiya kai tsaye ba sai tai knocking a hankali kamar mai tsoron a jita. Shiru babu alamar akwai motsin mutum sai ta ƙara da ɗan ƙarfi fiye dana farko. Nanma dai shiru, ta ɗaga hannu zata ƙara na biyu aka buɗe ƙofar. Baya taɗan ja tana mar-mar da idanu.

       Jin ƙamshin turarensa yasata ɗan dubansa zatai magana ya juya ciki da barin mata ƙofar buɗe alamar dai ta shigo. Sai da ta cije leɓe da dafe goshi irin (mutum nan ko) sannan ta bi bayansa.

      Masha ALLAH ta ambata a zuciyarta saboda yin tozali da ni'imtaccen falon nasa dayaji kayan kuɗi. Komai na cikinsa lemon green and milk color ne. Sai ƙamshi ke tashi ga uban sanyin ac da tsigar jikinta har tashi takeyi. Bata da zaɓin daya wuce ƙarasawa inda yake dan tuni ya koma inda ya taso zaune cikin kujera 1seater takardu barbaje a kan centre table ɗin daya maida gab da kujerar alamar aiki yakeyi. Sai dai yanzu ya zauna ne ƙafa ɗaya kan ɗaya yana kallonta harta ƙaraso tana harhaɗewa saboda idanunsa masu kaifi gareta.

       Idanunsa ya ɗan lumshe yana ɗauke kansa daga kanta zuciyarsa na jinjina rashin saurin sabonta, ganin zata kai tsugunne ya sake maido dubansa gareta, “Banason wannan durƙuson zauna a kujera”.

    Bata musa masaba ta zaune a kujerar dake gab da ita. Kanta a ƙasa tace, “Dama baƙine su Gwaggo sukazo, sh.... Shine Granny tace na faɗa maka ku gaisa”.

       Kallon yanda take cuɗa yatsun hannunta dake cikin jan lalle da baƙi kawai yake, ya ɗan ɗauke kansa yana girgizawa. “Taso nan ki sake maimaitawa banjiba”.

       Ɗagowa tai ta ɗan kallesa. Ganin yanda ya ɗauke kai gefe yana ƙoƙarin rage sautin tv ya sata ɗan tura baki, dan ita dai tasan babu yanda za'ai ace ba'a jitaba. Miƙewa tai ta nufesa. Zuwanta gab da shi dai-dai da ajiye remote ɗin hannunsa. jitai kawai ya riƙo mata hannu sai gata a saman cinyarsa.

     Ba firgitaba kaɗan ya rage tayo aman zuciyarta a tafin hannu dan razana da ɗunbin mamakinsa. Ganin yanda ta daburce ya riƙo haɓarta yana juyo da fuskarta saitin tashi, ƙoƙarin ganin sun haɗa ido yake amma taƙi. Sai jikinta dake tsuma. “Maimaita”. Ya faɗa yana ƙara ɗago haɓarta.

      “Granny ce dama tace na kiraka ku gaisa da baƙi”. Ta faɗa da in ina.

      Idanunsa akan laɓɓanta yace, “Inda bataceba fa?”..

Shiru tai dan batasan amsar da zata bashiba. Cikin matso da fuskarsa daf da tata yace, “Uhmyim”.

    Sosai tsigar jikinta ya tashi ta fara marmar da idanu dake neman fara tara ƙwalla.

     “Oh, inada hanyoyin da zaki magantu ai”. Ya faɗa yana sake matso da fuskarsa daf da tatan har hancinsu na gogar na juna. Ba ƙaramin wantsalawa hanjin cikin Zinneerah sukaiba, mamakin Yayan nasu na neman kasheta. A bazata taji saukar laɓɓansa saman nata. Bama tasan ta zazzaro idanuba. da wannan damar ya samu saka nashi idanun cikin nata suna kallon juna. Duk yanda taso ta kauce nata hakan ya gagara sai jikintane ya hau ɓari jin yanda yake sarrafa lips ɗinta cikin bakinsa.

       Tsabar ruɗewa bama tasan ta faɗa jikinsa ta ƙanƙamesaba saboda neman hanyar kuɓuta. Hakan datai ya masa dai-dai shikam, sai kawai ya lumshe idanunsa yana ƙara adanata a jikinsa. 

        Sai da ya tabbatar ta ruɗu sannan ya sarara mata. Jin ta ƙubta ta cusa kanta a ƙirjinsa jikinta na wata irin tsuma. rungumeta yayi shima da ƙyau yana murmushi da lumshe idanunsa wani irin kasala na neman saukar masa. Bakinsa ya kai saitin kunnenta muryarsa a ƙasan maƙoshi sosai yace, “A ƙara ne?”.

      Duk da yanda jikinta yay laushi bata san tama zabura ta miƙe ba. Karan farko a rayuwarta dataga yayi murmushi har haƙoransa na bayyana. Baya ta juya masa tana rumtse idanunta itama murmushin na suɓuce mata da sabuwar matsananciyar kunyarsa. 

         Batare da ya sake ce mata komaiba ya miƙe shima yana gyara rigarsa data ɗan yamutse saboda zama da tai a cinyarsa. Raɓata yay ya wuce. Sai da yaje fita ya ɗan juyo ya kalleta har yanzu fuskarsa da sauran murmushin ɗazun. Saurin jan mayafinta tai ta rufe fuska............✍


No comments

Powered by Blogger.