Makauniyar Kaddara 52

 


Page 52*


...........Gargaɗinsa yasa Zinneerah tana canja kayan tayo alwala da sake naɗe jikinta da lifaya ɗin ta fito duk da kayan barcin wandone har ƙasa da riga, kasancewar rigar guntuwa mara hannu yasa taji bazata iya fitowa da itaba gabansa. Gashi ta cire bra

ɗinta dan bata iya barci da ita ciwon ƙirji take sanya mata. Buɗe ƙofar tai a hankali ta fito cike da sanɗa kamar wadda ta aikata wani abu. Ganinsa zaune a saman sofa hasken system ɗin da yake sarrafawa ta haska kamilalliyar fuskarta ya sata satar kallonsa. 

         Duk da yaji motsin fitowar tata bai ɗagoba yanata aikin gabansa, ganin ta cigaba da tsiwa yace, “Ɗakko tea gashi can kizo nan”.

         Cike da dauriyar yanda kanta ke mata tsananin ciwo ta wuce ta gabansa ta ɗakko kofin tea ɗin daya ajiye a bedside drawer ɗin, gabansa tazo tana niyyar kaiwa tsuggune dan duk zatonta shine zaisha abinsa sai taji yace, “Zauna anan”. Ya nuna mata gefensa yana cigaba da aikinsa.

      Taji ko tamkar ta kurma ihu, dan duk da kujerar doguwace yazo kusan tsakkiyane ya zauna, hakan yasa inda ya nuna mata ɗin dolene zai basu kusanci matuƙa idan ta zauna. Shiɗin ba abin wasanta bane a kafin yau ma ballantana kuma a yau ɗin da take jinsa a sama ƙololuwa da girma, a can ƙarshe takai zaune tana ɗan gyara lafayar dake neman zamowa.

       Ɗan dubanta yay a karo na farko ya ɗauke kansa ya maida ga abinda yakeyi, “Maza shanye ki bani kofin”.

        A yanda yay maganar ya sake tabbatar mata da umarninsa, sannan ko banza ma dai tanajin kunyar, dan dama dawowarsu daga wajen walima ne Hajiya iya ta tilasta mata shan tea ganin bataci komaiba a can sam. Kusan rabi tasha tace ta ƙoshi, bai tanka mataba bai kuma kalletaba yanata aikinsa. Tsahon minta ɗaya ta fahimci baima da lokacinta sai ta cigaba da shan shayin hawaye na ziraro mata, cikin dabara take saka bakin lafaya ɗin tata tana sharewa harta kammala shanyewa ta miƙe da kofin a hannu.

     Tunanin ina zata kai ya sata duƙar da kai ƙasa, muya na rawa tace, “Ina ne kitchen?”. A yanda tai maganar ya tilasta masa ɗagowa ya dubeta na kusan sakan huɗu, ajiye lap-top ɗin yayi gefe ya kamo hannunta ya sake zaunar da ita kusa da shi, kansa tsaye ya janye lafayan data sa har a saman kai da ɗaura hannunsa a saman wuyanta. Sosai jikinta yay zafi. Kansa ya ɗan girgiza batare da yace komaiba ya miƙe tare da ɗaukar cup ɗin ya fice, zamewa tai a hankali ta jingina da kujerar tana lumshe ido da jan ajiyar zuciya, acan ƙasan ranta kuwa fal mamakinsa take da gulmarsa akan ashe yana da ɗan sauƙin kai.

        Tashi tai zaune jin ya sake dawowa, kanta a ƙasa harya ƙaraso ya sake zama a inda ya tashi yana miƙa mata magani da ruwa daya zubo a glass cup, babu musu ta amsa dan tana buƙatar maganin kodan ciwon da kanta ke mata.

        “Tashi ki cire wannan abun da kika naɗe jiki kamar magani kije ki kwanta”. Ya faɗa kansa tsaye yana ɗaukar lap-top ɗinsa ya cigaba da aikinsa. Miƙewa tai cikin bin umarninsa, sai dai gaba ɗaya tama rasa ta ina zata fara warware lafayar saboda tsananin kunya da shakkarsa. Ta saci kallonsa yafi sau goma, ganin shi hankalinsa ma nakan aikinsa yasata juya masa baya da fara warwarewa da sauri-sauri, ko batun linkewa bataiba ta ajiyeta gefenta ta haye gadon taja bargo har wuyanta tana sauke ajiyar zuciya dajan numfashi a gwame.

       AK daba kallonta yake ba, burinsa kawai ya kammala aikin shima ya kwanta dan kansa ya fara ƙarfafa ciwo ya ɗan dubeta jin ajiyar zuciyar data ja da ƙarfi. Ita kam runtse idanunta tayi da fatan barci ya ɗauketa ko zataji sassauci da nutsuwar halin da take ciki a yau. Har yanzu ta kasa daina imagine cewar Yayansu ne mijinta. Ta rasa miyasa su Granny sukai tunanin yin wannan kwamacalar? Inama laifin a bata Khalipha ko Moos'ab, amma maganar ta girmama Yah Abdul-Mutallab matsayin mijinta na aure.

     Da wannan tunane-tunanen barci ya ɗauketa, harya kammala abinda yake ya fita a ɗakin kusan mintuna talatin sannan ya dawo, fitilar ɗakin ya kashe zuwa ta barci, ya nufi gadon ya hau yana ɗan yamitsa fuska saboda kansa dake masa ciwo. Sai da ya zauna yaɗan jingina da gadon yana furzar da huci da lumshe idanu, kusan minti ɗaya sannan ya buɗe da waiwayawa yana kallonta ‘Komanta mai sanyi dai-dai da yanayinta’ ya ayyana a ransa dakai hannu ya gyara mata bargon dake neman toshe mata hanci. Ya mata kallon kusan mintuna uku kafin ya janye idanun nasa da sauke ajiyar zuciya.


        Cikin barci Zinneerah taji kamar an sakata cikin wani abu mai ɗumi da yafi bargon bata kariya daga sanyin da takeji, taja numfashi da iskarsa ta haɗa da daddaɗan ƙamshin turarensa wajen shige mata hanci, gabantane ya faɗi dan tabbas ɗumin yayi kama dana jikin mutum, babu shiri ta buɗe idanu duk da ɗakin babu wadataccen haske kuma kanta na'a ƙirjinsa ne. Ba ƙaramin harbawa zuciyarta tayiba na tsoro, sai dai can wani shashi na gargaɗinta akan karta nuna ta farka zaifi taimakawa tsananin kunya da fargabar dake tare da ita.

     Dole ta ƙarajin zuciyarta da jinin nikinta na cigaba da tsitsinkewa da tsananta sauri wajen gudu. Sarai ya fahimci ta farka, amma sai ya shareta saboda taimakama zuciyarta dake harbawar da har yake iya jiyowa bata salama. Su dukansu sun jima basuyi barciba kowa yana saƙa mai fisheshi, yayinda ɗumin jikinta ke raguwa saboda taimakon daya bata da jikinsa.  Daga ƙarshe dai su duka barcin ya ɗaukesu saboda maganin da suka sha.


_________________★


          A ɓangaren su Mammah kuwa ita da aunty Zakiyya barci sai dai ɓarawo ne ya figesu, sunason zaman tattauna abinda ke musu kaikawo hakan ya gagara saboda Mahma, daga ƙarshema Mahma hukunci ta yanke ita zasu kwana ɗaki ɗaya da Mammah, aunty Zakiyya kuna ta kwanta wajen Farah.

     Wannan abu ya musu ciwo su duka amma babu damar magana. Itako tayi hakane saboda fahimtar take-taken Mammah akan son hana AK nuna kulawarsa ga amaryarsa. Rashin mafita yasa Mammah amsar wayar aunty Zakiyya ta sake turama AK saƙo bayan ta kirasa a wayar ta masa gargaɗin farko. sarai Mahma na lure da ita amma sai batai maganaba ta girgiza kai kawai tana nemawa ƴar uwar tata shiriyar UBANGIJI danshi tafi buƙata a yanzun.


       ★★★★


   Kiran sallar farko ya buɗe idanu kamar yanda ya zame masa jiki, dan ko a london yake a irin wannan lokacin yake farkawa duk asubahi saboda alarm da yake saitawa. Sam barcin bai isheshiba, hakan ya saka idanunsa yi masa nauyi matuƙa amma ciwon kan ya sauka. Akan Zinneerah dake nannaɗe a jikinsa ya saukesu, yanda fuskarta tai wani fayau a barcin ya sakashi nutsuwa wajen ƙare mata kallon kusan mintuna uku, hannunsa dake a saman cikinta ya ɗaga a hankali yakai ga fuskarta yaɗan tallafi kuncinta ta gefe da ɗaura babban yatsansa akan laɓɓanta da suka daɗe suna tsole masa idanu. Yatsan ya shiga zagayawa a kansu taushinsu da santsinsu na masa daɗi, duk dama aɗan bushe suke a yanzu.

          Cikin barci ta dingajin kamar ana shafa mata lips, ga kuma hannunsa da kusan nauyinsa ke a ƙirjinta, ɗan motsawa ta shigayi alamar zata farka, sai kawai ya janye hannun nasa ya tashi zaune tamkar bashi ya aikata ba, buɗe idanunta yayi dai-dai da saukarsa a gadon yana faɗin, “Ki tashi kiɗan watsa ruwan ɗumi zakiji jikin ya saki gaba ɗaya”. Cikin muryar barci yay maganar dan haka ta fita a sanyaye da ɗan kauri kuma.

      Bata iya motsawaba harya fice dan wata irin matsananciyar kunya ke cinta, wai yau itace kwance a gado ɗaya da Yayansu. Jikinsu manne da juna, kai itako ina zata kai wannan abun kunya yau. Da wannan tunanin ta miƙe da ƙyar ta nufi toilet domin yin amfani da shawrsa nayin wanka.

        Tako ji daɗin wankan, dan jinta take fayau saboda zazzaɓin ya saketa, tana fitowa jikinta kawai ta tsane ta ciri doguwar rigar jallabiya a akwatin daya cirar mata kayan barci jiya ta saka, ta ɗauka turare a handbag ɗinta ta fesa sannan ta saka hijjab domin yin salla.

                     Bayan ta idar da ƙyar ta iya zaman yin azkar, tanayi tana gyangaɗi harta samu ta kammala da ƙyar ta sake komawa gadon ta kwanta dan wani irin barci takeji bana wasaba.

     Shima koda ya dawo daga massallaci sashensa ya wuce ya sake kwanciya koma azkar ɗin shi bai iya zaman yiba.

          

★★★


         A gidansu Hajiya iya kusan baƙi duk sun tashi da haramar wucewa yau, musamman ma ƴan danya da jikin Tinene ya rikice, dan kwana tai tana sheƙa amai a daren jiya, sai gabannin asuba tai barci. Da safe basu tadataba har suka kammala shirinsu, kusan ƙarfe takwas aka kawo musu abincin kari suda ƴan ɗanmusa da suma suke shirin fitama da wuri dan zasu biya ta gidan mmn sadiq su.

         Zuwa ƙarfe goma duk suka kammala abinda sukeyi, har Tinene ma an tadata ta shirya sai dai ta kasa cin komai duk ƙaunar abinci da takeji a ranta. Hajiya iya data shigo suka gaisa ganin sunta shiri take tambayar badai tafiya da sassafen nanba kamar korarru?.

       Cikin jin nauyinta da girmanta sukace tayi haƙuri zasu tafi haka nan ai anci biki Alhmdllh. Da yawansu sunbar yara a gida kuma. 

      Godiya tai musu da addu'oin fatan alkairi, tace su ƙarasa shirin to a fara kaisu gidan amarya. Gwaggo Laritu ce tace, “Hajiya ai dama an barshi kawai tunda jiya munje”.

        “A'a ya kamata kuje gaskiya itama zataji daɗi, jiya duka zuwan minti nawa akai, ku ƙarasa shirin kawai bara naje na shirya abincinsu suma”. Daga haka tai sallama da su ta fice.


   

★★★


     Kusan tara da rabi Zinneerah ta farka, yanda ta ƙarajin ko ina na jikinta ya ƙara saki taji daɗi, gadon ta gyara tsaf, duk da ɗakin ba wani datti yay ba ta fito neman kayan shara. Sosai falon yay mata ƙyau, komai na cikinsa ya kasance ash color da ɗan ratsin pitch kaɗan-kaɗan, sai ƙamshi ke tashi mai daɗi na turaren wuta. Sake fitowa tai inda nanma falo ne da yafi na ciki girma sosai mai ɗauke da bedrooms biyu sai ƙofar kitchen da zakabi ta dining, kalar komai dake a falon ta kasance lemon green and light orange. Fallon babbane dan yafi wanda ta baro, samun kanta tai da leƙa bedrooms ɗin suma ta gani, ɗaya akwai gado a ciki da komai na kayan ɗaki brown da sukai matuƙar ƙyau, dan shima ya burgeta sosai, tana kuma ƙyautata zaton sune ƙoƙarin iyayenta. Har bathroom sai da ta leƙa tana maijin ƙaunar Abba da Baba har cikin ƙoƙon ranta. Daga haka ta fito ta leƙa ɗayan ma. Shikam katifa ce kawai aciki babba sai ƙaramar drawer da mirror. Shima dai ya mata ƙyau ɗin. Ta dining tabi zuwa kitchen, shi kansa dining ɗin abin kallone. Data shiga kitchen kam ai bama tasan sanda hawaye suka silalo mata ba, tasa hannu ta share da jama iyayenta da Granny ƙyawawan addu'oin gamawa da duniya lafiya. Anan ta samu kayan sharar datazo nema ta ɗakko ta fito. Iya bedroom ɗinta kawai ta share ta goge dan shine kawai tama fahimci yana buƙatar hakan, sauran kuwa ta bisu da fresheners masu daɗin ƙamshi da turaren wuta kasancewar akwai nepa. Gaba ɗaya sashen ya ɗauki ƙamshin dake sake tabbatar da ita a amarya, daga haka ta koma ta sake kintsa jikinta ta shirya cikin shadda less skirt da riga kalar light pink. Sosai kayan sukai mata ƙyau, tana tsaka da ɗaura ɗan kwali take jiyo ƙarar door bell. 

        Da sauri ta ƙarasa da ɗaukar turare ta ƙarama jikinta taja mayafi ta rataya a kafaɗarta tunda bata da tabbacin wanene. Tana tafiya tana ƙoƙarin saka abin hannunta da suka rage bata sakaba.

        Tana isowa babban falon gidan daya haɗa duka sassan nasu shima yana fitowa daga nasa sashen cikin ɗanyar shadda daketa maiƙo da ɗaukar idanu, ɗinkin heif jamfa data sake fidda ƙuruciyarsa da kwarjini honey color. Dabircewa Zinneerah ta nema yi, babu shiri taja birki da saurin duƙar da kanta ƙasa.

       Shikam kansa tsaye yake dubanta daga sama har ƙasa yana cigaba da takowa. Ta gabanta ya wuce zuwa ƙofa da aka ƙara dannawa ya buɗe yana ƙoƙarin dai-daita yanayinsa.

       Babu shiri Jamal da Nawaff ɗan Uncle Ahmad suka sake nutsuwa da fara gaishesa. Batare da ya amsa musu ba ya matsa baya ya basu hanya alamar su shigo. Shigowar sukai kowanne ɗauke da basket da aka lulluɓe da farin ƙyalle. Sake gaishe da yayan nasu sukai sannan suka dubi Zinneerah fuskokinsu washe da murmushi kamar yanda itama nata murmushin yaƙi ɓoyuwa duk da batasan Nawaf ɗin ba ita.

     Jamal nason ya tsokaneta babu dama. Dan haka murya ƙasa-ƙasa yace, “Good morning auta”.

       Sai da ta ɗan saci kallon AK daya wucesu sannan ta amsa masa da, “Morning small bro”. 

     Ƙaramar dariya Nawaf yayi shima yana gaisheta. Duk da bata sanshiba ta amsa da kulawa dan kamanninsa da Jamal ɗin ya tabbatar mata shima jininsu ne, sai tayi tunanin ko cikin ƴaƴan Mommy ne tunda Huzaifa kaɗai ta sani har yanzun.

       Sanin halin yayansu yasa Jamal haɗiye duk wani surutunsa yace, “Ga abinci inji Momie mu bara mu wuce tunda boss na gida, amma daya fita zamu dawo yasin”.

       Murmushi kawai Zinneerah tayi da girgiza kanta. Ta amshi baskets ɗin hannayen nasu biyu tana godiya da tambayar Granny dasu Meenal?.

      “Granny na gaisheki, su Meenal kuma anjima zamu dawo, ki kuma shirya baƙi na nan tafe inji Granny. Bara muje sai mun dawo”.

     Daga haka yaja hannun Nawaf suka fice. Jitai kamar karsu tafi, badan tasoba ta nufi hanyar sashenta dan can AK ya shiga. Zaune ta samesa a falon farko yana waya, da alama da Mammah yakeyi saboda ambatar sunanta da taji yayi. Saɗaf-saɗaf ta wuce dining da kayan shiko ya bita da kallo.

     Duk da bata da buƙatar cin abinci tasan ya kamata shi ta bashi, dan haka ta nufi kitchen ɗakko plate da abinda duk ya kamata bayan ta ɗaurayosu. Har lokacin wayarsa yakeyi, sai kawai ta shiga ƙoƙarin duba abincin kafin ya gama taji mizaici a ciki?.

       Tana ƙoƙarin buɗe kular farko ta kasa kawai taji ƙamshin turarensa ya sake kusantota. Batai yunƙurin juyawaba ta cigaba da abinda takeyi. A hankali AK ya sake matsota, ta bayanta shima ya ziro hannayensa da ɗaura kansa bisa kafaɗarta har gashin sajensa na tsikarar mata fatar kafaɗa zuwa gefen wuya, numfashinsa na sauka a dokin wuyan nata, ya manna ƙirjinsa da bayanta sai kawai ta saki kulan da take ƙoƙarin buɗewar babu shiri jikinta na rawa...............✍


No comments

Powered by Blogger.