Makauniyar Kaddara 51


page 51*


...........Kamar jira ƴan kawo amarya na wucewa Farah ta farka, sai dai a yanayin data farka ɗin yay matuƙar tada hankalin su Mammah, AK daya tuna cewar tana tare da ciki ya cema Dr Mahmud suje asibiti kawai kar a rasa abinda ke cikinta. Mammah ce tai azamar son dakatarwa Mahma ta tsaidata

itama ta hanyar faɗin, “Maganar Abdul-Mutallab nakan hanya, hakan shine yafi dacewa kar azo ana dana sani kuma daga baya”.

        Cikin tashin hankali aunty Zakiyya tace, “Mahma kubarta-fa komai zai dai-daita, inaga ya ƙara mata allurar barcin sai mu wuce can gidan da ita dan Abban Ameera ya kirani cewar wanda zai kawo mana key ɗin ya iso yana can yana jiranmu”.

      “Addah abi shawarar Zakiyya ɗin na tabbatar shock ne zata dawo dai-dai idan ta ɗanyi nesa da nan ɗin kamar”.

      Ak dake binsu da kallon mamaki ya dafe kansa dake neman fara masa ciwo, dan shikam dai abubuwan na neman masa yawa gsky. Mahma da wani tunani yazo mata a zuciya tace, “To babu damuwa kai mata allurar kawai sai mu wuce”.

      Kallon AK Dr Mahmud yayi, “Amma ranka ya daɗe karfa allurar tai mata illa, ni bansan ma tana tare da ciki ba da ban mata ita ba, tanada ƙarfi, nayi mamakin ma data farka a yanzu dan allurar mai ƙarfice”.

       Karan farko AK ya saki ɗan murmushi, dan shikam dai zuciyarsa ta fara raya masa wani abu game da yanayin Mammah da Aunty Zakiyya, ya ɗan lumshe idanunsa ya buɗe da gyara tsaiwarsa. Cikin rashin sakewarsa yace, “Kaga yimata ɗin kamar yanda sukace, dan a ganina zamanta a farken yafi allurar zama matsala ga lafiyar tata”.

       Kai kawai Dr Mahmud ya gyaɗa masa, dan shikam dai baimaga wani alamun ciki a jikin Farah ɗin ba. Yana ƙoƙarin haɗa allurar yace, “Amma cikin nata yakai wata nawane?”.

      Shiru Mammah da aunty Zakiyya sukayi, sai Mahma ce tace, “Kamar dai biyar ko”.

     “Biyar fa?”.

Dr Mahmud ya ambata mamaki ƙarara a fuskarsa. Ɗan duban Farah ɗin dake riƙe jikin Mammah tana kuka da wani ɗan fisge-fisge yayi ya ɗauke kansa. Batare da yace komaiba yay mata allurar kawai ransa fal wasiwasi.

     Yana gama mata allurar ko mintuna biyar ba'a ƙullaba barci ya ƙara ɗaukarsa. Kallon AK Mahma tayi da cewa, “Taimaka ka kai mana ita mota Abdul-Mutallab, ku kuma kumuje shima ya samu ya huta”.

       Babu shiri Mammah tace, “Addah ai shine zai kaimu, taya matarsa na wannan halin yaga wani ta hutu?”.

     Murmushi Mahma tayi na takaici, muryarta aɗan hasale tace, “Duk mu da muke tare da ita bai wadatarba sai shi ya kasance a wajen?. Ai ya kamata a tausaya masa ya huta ga kuma yarinya an kawo zai barta ita kaɗai kenan komi?”.

      A take Mammah ta sake tamke fuska matuƙa. Ta kalli AK da yay tamkar bayama jinsu yanata latsa waya. Sai kuma ta maida kan Mahma, “Addah to in hakane muyi kwanciyarmu anan ɗin kawai basai yayi wahalar da kike gudar masanba..”

     “Bazai yuwuba, tunda dai ga gida can da zamu zauna mu kaɗai bamu takura kowa ba, ba'a takuramu ba, can zamuje. Abdul-Mutallab ɗauketa”.

     Yanda Mahma tayi maganar babu wasa a ciki ya sakashi zura wayarsa aljihu ya tako a hankali inda Mammah ke rungume da Farah. Ɗaukarta yay cak ya fita da ita duk da nauyin datai masa saboda yanda jikinta ya saki sosai. Duk yanda Mammah keta kumbure-kumbure Mahma batabi takantaba ta tasasu gaba suka fice suma. Dan ita aunty Zakiyya ma ta ƙagu subar nanɗin dama suje inda takeson amayar da abinda ke a bakinta.

      Aunty Zakiyya ce ta jasu. Suna ficewa daga gidan AK yaɗan lumshe idanunsa da murza goshinsa yana furzar da huci. Sai kuma yay murmushi da girgiza kansa saboda harar da Mammah keta faman antaya masa da gargaɗi da idanu.  

       Juyawa yay zuwa cikin gidan dan shima wani ma zazzaɓi-zazzaɓi ke neman rufesa, sashen Farah ya koma ya kashe komai da maida ƙofar ya rufe, koda ya fito sashensa ya nufa dan yafi buƙatar watsa ruwa a yanzu.  


      ★★★


    A ɓangaren Zinneerah kam kuka taci sosai, sai da Mahma ta leƙo tai mata sallama akan suma zasu wuce, ta kuma ɗan lallasheta da ƴar nasiha sannan ta sassauta. Fitsarin da takejine ya sakata tashi dole ta shiga toilet ɗin ɗakin tayo, tana fitowa ta sake komawa saman gadon ta kwanta dan zazzaɓi takeji yana neman rufeta ga ciwon kai. Ba tare data damu da cire komai ba ta kwanta a haka dajan bargo ta lulluɓa har kanta saboda sanyi da takeji yana ratsata. Ga kuma ac a ɗakin dake aiki ta kasa kashewa.

        Batafi mintuna goma da kwanciyarba barci ya kwasheta sama-sama. A ɗan firgice ta farka saboda ƙarar buɗe ƙofa da taji, ta ƙanƙame jikinta waje guda jin tabbas mutum ne ya shigo. Sai dai ta kasa ko motsi saboda yanda zuciyarta ke wani harbawa da sauri sauri na tsananin tsoron wanda zataci karo da shi a matsayin mijin nata.

      AK da tun shigowarsa ɗakin idanunsa suka fara sauka akanta ya cigaba da takowa cikin ɗakin a hankali sassanyan ƙamshin turaren wutar da ɗakin yaji, da ƙamshin sabbin furnitures dana fenti na rige-rigen shiga masa hanci, a hankali ya sauke ajiyar zuciya yana ƙarasawa gaban gadon sosai. Hannayensa ya tura duka biyu cikin aljihun wandon blue pyjamas ɗinsa har lokacin idanunsa akan Zinneerah dake ƙudun-dune cikin bargo zuciyarta na nemam faso ƙirjinta ta fito.

       “Assalamu alaiki”. Sassanyar muryarsa ta daki cikin kunnuwanta. Sosai ƙirjin Zinneerah ya buga fiye da farko, dan idan har babu kuskure ai muryar Yayansu taji kam. ‘Kai ina ganganne’ ta ayyana a zuciyarta dake raunana.

       “Nasan ba barci kike ba”. Ta ƙara tsinkayar muryar tasa a karo na biyu, a yanzu kam kasa jurewa tayi dole tai ƙasa da bargon a hankali daga saman fuskarta. A hankali ta buɗe idanunta zuciyarta na gudu dai-dai da jinin jikinta dake tsinkewa daga cikin jijiyoyinta. A wani irin firgice ta yaye bargon babu shiri tana miƙewa zaune jikinta na rawa. “Y...y....Yayanmu!”.

      Ta faɗa da wani irin kiɗimammiyar murya dake nuna tsantsar tashin hankalinta a fili. Sosai yanda tayi ɗin ta bashi dariya, amma sai ya daure ko ɗigon fara'a babu a fuskarsa, sai dai idanunsa kafe suke a kanta ko ƙyaftawa bayayi yana ƙarema ƙwalliyar tata kallo, dan zaburar da tayi ta saka lafayar warwarewa daga saman kanta zuwa jikinta. Sai baƙar rigar jikinta mai dogon hannu data lafe da bayyana  ainahin surarta da gyaran da fatarta ta samu wajen hajiya Falmata.

           Janye idanunsa dake binta da kallon yayi yana maidawa akan fuskarta, ganin yanda take ɗan ja baya da rawar jiki laɓɓanta na rawa alamar sonyin magana ya sakashi lumshe idanu ya sake buɗewa a kanta yana zare hannayensa daga aljihun wandon barcin nasa. Cikin nuna rashin damuwa da yanayin nata ya kai zaune a bakin gadon yana facing ɗinta. Hannunsa ɗaya yakai akan goshinsa yaɗan shiga murzawa. Sai kuma ya ɗago ya dubeta da birkitattun idanunsa dake rikitata, batare da yace uffanba ya miƙa mata hannunsa ɗaya alamar tazo.

     Kanta ta shiga jujjuyawa tana ƙara nanema fuskar gadon, hawaye na gudu a saman fuskarta kamar an buɗe fanfo. “Yayanmu dan ALLAH kace bakai bane ba”. Ta faɗa cikin tsananin rauni da rawar harshe.

      A karan farko ya ɗanyi luuu da idanunsa da sakin guntun murmushin da ita ko alamarsama bata ganiba, ya ɗan ƙara ware idanunsa a kanta da kai hannunsa ya shafi sajensa dake a kwance luf duk da ba gyaransa yay ba, dan koda yay wankan ma turare kawai yasa da kayan barci ya fito domin dubata. Cikin muryarsa ta rashin sakewa yace, “Bani bane mi?”.

       Cijin suɓucewar baki Zinneerah tace, “Miji!, mijin da aka kawoni gidansa matsayin matars.......”

     Ta kasa ƙarasawa saboda yanda yay bala'in kafeta da idanunsa masu cikar gashi da kwarjini. “Ban cancanta bane?”. Ya faɗa yana cigaba da tsatstsareta da idanu.

    Babu shiri tai ƙasa da kanta kuka na sake kufce mata. Kansa ya ɗauke daga kanta jin wayarsa na vibration, hannu yasa ya cirota daga aljihun wandon barcinsa yana jan guntun tsaki alamar baiso shigiwar kiranba dai. Sai dai ganin Number aunty Zakiyya ya sakashi yi kamar bazai ɗagaba sai kuma ya ɗaga ɗin batare da yayi magana ba.

      Cikin sake fusata daga can Mammah tace, “Abdul-Mutallab nasan kana jina”. 

     Runtse idanunsa yay da cije lip ɗinsa na ƙasa. yay ƙoƙarin daidaita kansa wajen faɗin, “Am sorry, bansan ke bace ba”.

       “Ai yanzu ka sani, na kiraka ne na gargaɗeka, wlhy ka taɓa musu yarinya sai ranka yay mummunan ɓaci, dan nayi alƙawarin wannan auren sai na tsinkashi wlhy, saboda haka karma ka ƙwaɗaitama kanka abinda zai dameka daga baya na faɗa maka”.

         A bazata ya saki murmushi mai sanyi da kai hannu ya shafi kansa, dan tana gama faɗa ta yanke kiran bata jira amsarsa ba. Ajiye wayar yayi yana miƙewa gaba ɗayansa idonsa akan Zinneerah dake cuɗa yatsunta cikin juna tana cigaba da kukanta  harda shashsheka.

      Batare da tunanin kanta ya nufoba sai ganinsa tai ya hawo gadon sosai, filo ƙarami ya jawo daga gefenta ya kishin giɗa, dan ɗaura gwiwar hannunsa ɗaya yay ya tallafe kansa da tafin hannun yanda yake iya kallonta da ƙyau, sai kuma ya saka yatsunsa biyu na ɗayan hannunsa ya tallafo haɓarta yanda zasu haɗa ido.

      Suna haɗa idanun kuwa tai saurin son maida nata dake kwarar da hawaye amma ya hanata wannan damar. Sai kawai ta shiga sake matso hawayen. Dan irin kallon ƙurullar da yake yima fuskar tata ne yake ƙara ƙarya mata zuciya ga kwarjininsa daya cika mata idanu.

           “Shi wannan kukan ba'a gajiya dashi?”. Yay maganar da muryar lallashi data sakata ɗago idanu ta sake kallonsa, yanda yay ɗan yi luuu da idanun nasane ya saka tsigar jikinta tashi, cikin harɗewar harshe tace, “Yayanmu!”.

       “Uhmyim ƙanwata”. Ya faɗa yana sakin haɓar tata da janye hannunsa daya tallafe kansa shima yana gyara kishingiɗar tasa da matsowa daf da ita yanda takejin har saukar numfashinsa shima yanajin nata. 

     Ganin yanda ta kasa ci gaba da maganar sai juya yatsun hannunta take a cikin na juna ya sashi ɗaura hannunsa akansu yana kallon zanen baƙin lallen da ja dayay matuƙar ƙyau a kansu, “Kuka ga amarya a ranar da aka kawota gidan miji cikar kamalace da bayyana adon mutuncinta, sannan kuma tarbiyyace da nuna tsantsar soyayya ga iyaye, sai dai idan yayi yawa yana gundurata. Karki damu da neman amsar duka tambayoyinki, a hankali zaki samu amsarsu. Inason mutum mai biyayya akan umarnina, banason hayaniya, banason taurin kai, banason ƙarya. Duk wanda zan rayu dashi inhar zai kiyaye waɗannan zaiji daɗin zama dani fiye da yanda yake zato. Bana yanke hukunci ga mai laifi da sauri ko cikin fushi har sai na bisa mataki-mataki wajen fahimtarsa da dalilinsa. Mun sami juna a yanayin da banso ba, sai dai ba hakan na nufin zanyi sakaci da damata bane, komu samu tsaurin idon bijirema hukuncin ALLAH dana iyayenmu, dan sun cancanci sadaukarwa koda ace mu zukatanmu basa buƙatar hakan, ina ƙyautata miki zato bisa ga wasu dalilaina, dan haka sai kiyi ƙoƙarin tabbatar mini da hakan”.

       Hannunta ɗaya ta zare daga cikin nasa a hankali ta share hawayen da suka jiƙe mata fuska.

     “Good” ya faɗa yana tashi zaune daga kishingiɗar da yayi. Sauka yayi gaba ɗaya a gadon Zinneerah na binsa da kallo ta ƙasan ido da ƙoƙarin ganin ta shanye hawayen dake shirin sake zubo mata. Akwatin daya gani a gefe ya ɗakko, ya ɗaurashi a gadon tare da buɗewa. Da kayan barci dake sama ya fara cin karo, batare da damuwaba ya ɗakko na saman kawai ya maida ya rufe. Takowa yay ya ajiyesu gabanta fuskarsa a tsuke kamar yanda ta santa, cikin rashin sakewarsa yace, “Ki tashi ki sauya kayanki ki kwanta”.

     Daga haka ya juya ya nufi ƙofa. Da kallo ta sake binsa tana share hawayen da suka ziraro mata. Yana fita ta ɗaura hannu duka a kai tana sake fashewa da kuka. A fili tace, “Na shiga uku ni Zinneerah ina ni ina zaman aure da Yayanmu? Wlhy yafi ƙarfina, matarsa tafi ƙarfina bazan iya da bala'inta dana Mammah ba”.

    Sai kuma ta zame ta kwanta tana jan numfashi dake sarƙe mata a ƙirji da ƙyar. Tabbas bazatace batason Yaya Abdul-Mutallab ba, dan ya cancanci zama abinso ga kowacce irin mace ciki harda ita da a yau zata iya kiran kanta mai sa'a ma, amma tasan yafi ƙarfinta ta kowanne fanni na rayuwar duniya, duk da tasan zata iya finsa a lahira itama wannan hukuncin ALLAH ne. Miyasa MAKAUNIYAR ƘADDARA zata rasa a inda zata jefata sai cikin rayuwarsa?. Ta inama zata fara kwatanta zaman aure dashi itako?.

             “Idan nace bana son abu sau ɗaya to a kiyaye mini, inba hakaba zan ɓata ran mutum kamar yanda ya shirya ɓata nawa”.

     Ta tsinkayi muryarsa a bazata batare data san ya sake dawowa ɗakin ba. Zumbur ta miƙe zaune da kwasar kayan barcin daya ajiye mata tana sauka a gadon batare data yarda ta kalli ko sashen da yake ba. Kamar ƙyaftawar ido ta afka toilet ɗin ɗakin.

        Tea cup ɗin hannunsa ya ajiye a bedside drawer yana ƙoƙarin zaro wayarsa datai alamar shigowar saƙo. Ganin no ɗin aunty Zakiyya ta sakashi buɗe saƙon dan yasan Mammah ce.

       _Ina ƙara tabbatar maka karka taɓa yarinyarnan Abdul-Mutallab, dan zaka gamu da ɓacin raina da baka taɓa ganiba a tsahon shekarun rayuwarka talatin da huɗu_.

       Murmushi ne ya suɓuce masa, yaɗan girgiza kansa da faɗin, “Mammah problem”. Akan laɓɓansa. sai ma ya kashe wayar baki ɗayanta ya ajiye ya ɗauka lap-top ɗinsa daya shigo da ita ya shiga hidimar kunnawa dan akwai abinda yake son yi daya shafi business ɗinsa da wani abokin harkarsa mai turo masa kaya daga dubai...............✍

    

No comments

Powered by Blogger.