Makauniyar Kaddara 50


 Page 50*


..........Soaai AK yayi mamaki matuƙa da ganin abokansa waɗandama shi kobi takansu bayayi yanzun, hakama abokan harkar business ɗinsa dake anan Nigeria. Dole dai ya ware ya shanye mamakinsa ya shiga basu hannu suna gaisawa da tayashi murna, tare da masa ƙorafin ba'a gayyacesu ɗaurin

aureba sa fatin da babu amarya babu ƴammatan amarya balle Uwargida. Murmushi kawai yakeyi bai iya cewa komai dan baida abin faɗar.

    Daga haka komai ya kasance a nutse cike kuma da birgewa. Dan abune na masu aji sam babu wata hayaniya. Anci ansha an sake taya ango da amarya murna da musu fatan alkairi, zuwa goma taro ya tashi lafiya kowa yana sam barka. Baƙi suka koma masaukinsu masu gidaje anan kano suka kama gabansu. 

     Sosai AK yaji daɗin fatin nasu kuwa. Dan koba komai ya haɗu da tsoffin abokansa da uzurorin rayuwa ya sashi mantawa dasu. Koda ya ɗan leƙa gidan nasu bayan sun tashi kasa zama yayi saboda hayaniyar ƴan biki, wai a hakanma wasu sunyi barci saboda gajiya, dole yayma su Baffah da Uncle Ahmad da suke nane da juna sallama ya gudo gida.

       Lokacin daya shigo gidan Farah tayi barci, dan haka shima kayan jikinsa kawai ya zare yay wanka da neman makwanci saƙe-saƙe fal ransa. Musamman fargabar zuwan su Mammah gobe idan ALLAH ya kaimu da Mahma ta sanar masa. Sam bayason Mammah tazo ta tada hankalinta a cikin wannan taron mutanen ƴan biki, shiyyasa tun ɗazun abin ke damunsa da ƙyar yaketa faman tausar kansa.

    Yau sukai niyyar tahowa Mahma ta sake lallaɓasu akan su zauna zaman shirya abubuwa yanda zasu iya tunkarar Baffah. Dan  sunyi aniyar tahowa su shiga garin danya da akace musu amarya take kafin su wuce kano. Hakan yasa Mahma kautar da hankalinsu har amarya ta isa ɗakinta lafiya sannan. Tasan dai idanma sunzo a gobe insha ALLAH aikin gama ya gama kuma.


     _______________________★


    Washe gari aka tashi da shirin gagarumar walima wadda daga ita kuma sai miƙa amarya Zinneerah ɗakin mijinta. Zinneerah data kwana a ɗakin AK ita da Adilah kuwa da zazzaɓi ta tashi, amma tanata daurewa dan har wasu ƴan sauran gyara da suka rage hajiya Falmata tai mata a daren. Tsabar gyaran data sha maranta har wani ciwo yakeyi mata. Haka dai ta cigaba da daurewa har hajiya Iya ta shigo ɗakin domin dubata. Dan Adilah dake fashin salla ma ko tashi a barci batayiba.

       Sun gaisa da hajiya iya take tattaɓata ganin duk tayi wani iri, “Kai Inno ai zazzaɓi ne a jikin nan naki, haka kika kwana da shi ma ko?”.

      Cikin ƴar shagwaɓar da suka sabama hajiya iyan ita dasu Jamal ta ɗaga mata kai idanunta na cika da ƙwalla. Sannu hajiya iya ta shiga jera mata, kafin ta taimaka mata shiga bayi dan ta samu tayi wanka. Koda tayo wankan ta samu ta shirya cikin atanfa sabuwa ƙal data amshi jikinta ɗas ta fito a amaryarta, Adilah kanta data farka sai yaba ƙyan datai takeyi, murmushi kawai Zinneerah keyi dan sosai take ganin girman Adilah ɗin kasancewarta ba ƙarama ba, sai dai kawai ALLAH ya bata ƙaramin jiki ga kuma yanayin inda ta tashi rayuwar turai, dan ita hausarma ba iyawa taiba tunda ba zuwa Nigeria ɗin Mammah take bari tayiba. Iya kacinta dasu magana da turanci, saiko AK dake iya jin yaren Mammah na larabci sukanyi, shiyyasa basa shiri da hajiya iya sosai saboda takaicin Adilah ɗin bata iya hausaba.

     Tea hajiya iya ta kawo mata a sha da magani ta sake kwanciya kafin lokacin walimar. 


★★★


      A katsina kam ko breakfast ɗin arziƙi basuyi zaman yiba suka kamo hanyar kano, lokacin da suka iso gidan anata kwasar mutane zuwa ƙaton hall ɗin da za'a gudanar da walimar. Yanda anguwar ta rikice da kai kawon motoci masu kwasar mutane yasa dole su Mammah suka fakin tun a waje, Mahma ce kawai ke dauriyar gaisawa da mutane, amma Mammah da Aunty Zakiyya sunata shan ƙamshi.

    Koda suka iso cikin gidan sun sami Baffah tare da baƙi, yana ko ganinsu yabar baƙin da uncle Ahmad ya nufosu fuskarsa ɗauke da murmushin daya sake fusata Mammah, aiko tayi kicin-kicin da rai tamkar zata fasa ihu. Sai dai batace komaiba bisa ga gargaɗin Mahma da sukasha.

      Duk yanda Aunty Zakiyya taso nuna halin nata ga Baffah kasawa tai, dan wani irin kwarjini yay mata da cikar kamala. Dole tai ƙasa da kanta tana gaisheshi da girmamawa. Shima cike da fara'a ya amsa mata harda tsokanarta.

     Yanda Mammah ta ɗauke kanta daga garesa haka shima yayi tamkar bai gantaba, cikin girmamawa yacema Mahma su shiga ciki. Murmushi tai masa, yay gaba suna binsa a baya har sashensa tacan baya da ƙofar falonsa ta ainahin bedroom ɗinsa take. Dan yasan acanne kawai babu wani hayaniyar mutane da hankalinsu zai kai kansu saboda wutar bala'i daya hanga a idanun Mammah.

     Kafin su shige ya aika Jamal da sukaci karo ya sanarma hajiya iya zuwansu, daga nan ya wuce a haɗo abinci a kawo musu. Mammah zatai magana cikin masifa Mahma ta dakatar da ita da idanu, dole taja bakinta tai shiru tana haɗiyar zuciya.


          Cikin ƙanƙanin lokaci hajiya iya ta ƙaraso tareda su Bahijja dake ɗauke da abinci, suna ajiyewa suka gaishesu suka fice. Mahma da aunty Zakiyya ne kawai suka gaida hajiya iya, Mammah kuwa sai da Mahma ta harareta sannan ta gaisheta da ƙyar. Hajiya iya bata damuba kam, dan ba yaune farauba.

         Yanda hajiya iyan ta nuna rashin damuwarta ya ƙara zafar Mammah ta fara magana a ƙufule, “Kabeer  miye wannan ke nufi?”. Tai maganar tana ajiye masa invitation card a tsakkiyar centre table. Uncle Ahmad daya shigo falon ne ya ɗauka ya duba ya maida ya ajiye. Kasancewar shima ɗan zafin kan ne a gadarance yace mata “katin gayyatar walimar liyafar cin abincin auren gudan jininmu mana”.

     Kallonsa tai rai a ɓace tana juya idanu, “Kai kuma bansa da kaiba mijin tace, kaji da taka matsalar kafin ka tsoma baki a ta wasu”.

        “Hakan na nuna miki cewar wadda ta maidani mijin tace ɗin tafiki komai, tunda ke kin kasa maida Yayana mijin tace ɗin saboda ƙarancin ƙyaƙyƙyawan nazari da kishin hauka dake damunki. In banda abinki Hindatu tayaya kike tunanin raba ƴaƴa da mahaifinsu ta ƙarfin tsiya? Ke waya rabaki da naki har suka bar duniya”.

         “Wlhy Ahmad ka kiyayeni, kasan na fika zafin kai”.

    “Anƙi kiyayar taki, kiyi duk abinda zakiyi”.

       “Zako kaga mizanyi ɗin, dan wlhy wannan auren kun ɗaura banza saina rabashi, in banda son zuciya taya yaro yana zamansa lafiya da matarsa zaku ƙaƙaba masa auren yarinya baƙauya mara galihu.........”

       A fusace hajiya iya ta katseta da faɗin, “A rashin galihun nata shi ɗan naki ya gani yakeso, tunda har ya iyama yarinya ciki a waje ta haihu ita ƴar son naki bata haifaba. Hindatu ki kiyayeni wlhy, ina ɗaga miki ƙafa saboda ɗanki, amma inaga wannan karon saina fito miki a Amina ta, moddibo ne dai ya dawo gidansu kenan daga shi har ƴar uwarsa babu kuma yanda kika iya. idan buƙatar kasancewa kike dasu kema saiki dawo gidan ubansu ki zauna cikin kishiyoyin da kike gudu. Dan daga yau na yanke shawarar moddibo ya dawo ƙasarnan da zama kenan da iyalansa idan kin gansa a wata ƙasa sai dai yaje harkokinsa ko gaisheki ya dawo wlhy”.

       Tsabar yanda zuciyar Mammah takai maƙura a hasala sai kawai ta fashe musu da kuka. “Wlhy bazan yardaba, bazan yarda a rabani da ƴaƴana ba tunda nice na haifi abuna bayan wahalar rainon cikinsu dana sha. Ita matar Ahmad data kwace miki shi miyasa kika kasa komai sai ni zakibi ki sama ido akan nawa ƴaƴ.......”

      “Hindatu!!”. 

Baffah ya daka mata tsawa jikinsa har rawa yake na ɓacin rai. Murmushi hajiya iya tayi da ɗaga masa hannu. ta duba Mammah da ƙyau tana faɗin, “Itama ba ƙarfina tafi ba, kamar yanda kika ɗauke su moddibo muka barki yanzu kuma lokacin dawowarsu cikinmu yayi, itama lokacin da zan nuna mata nina haifi Ahmad ɗin yayi ai”.

        “Wlhy ni kuma nayi alƙawarin yin amfani da ƙarfina na uwa wajen raba wannan auren, ɗa kuma da suka haifa a waje zaimin bayanine dalla-dalla dan ubansa”.

      Ran Mahma da yay matuƙar ɓaci da abinda Mammah keyi bayan sai da ta ƙwaɓeta kafin su taho ta kama hannunta ta maidata ta zaunar a fusace. “Hindatu wai mike damun kanki? A ganina kamata yay ki nutsu ayi magana ta fahimta amma kinzo kinama mutane shirme. Kifa sani yanda kike da haƙƙi akansu Adilah haka shima mahaifinsu keda haƙƙi a kansu, yakumayi iya bakin ƙoƙarin sa wajen yimiki kawaici akansu, ai idan kinason yaranki su kasance dake basai ta hanyar ƙarfi da iko ba tunda suma sunsan ke uwa ce a garesu. maimakon ki damu dajin ta yanda akai Abdul-Mutallab ya samar da yarog yarinya a waje ke damuwarki kawai ƴaƴanki zasu suɓuce miki, haba wane kalar son kai ne wannan?”.

    Kuka sosai Mammah keyi, tace, “Haba Addah kinajinfa yanda suka haɗa kai zasumin taron dangi, taya zasu ma yaro aure bada saninaba haka ake rayuwa?......”

      “Ke sanda kikai masa aure bada saninmu ba wace gadarace baki manaba”.  Baffah ya katseta a fusace. Ransa a ƙololuwar ɓace ya cigaba da faɗin, “Hindatu idan kin manta bara na tuna miki, matar da Adnan ke aure karki manta sai ana gobe ɗaurin aurensa da ita kika faɗa mana, amma duk da rannmu ya ɓaci Inna ta tilasta mana haƙuri mu barki tunda aurene, yarinyar kuma ƴar uwarki ce. Haka muka danne zukatanmu muka amsheta a cikinmu da hannu bibbiyu amma ki ka ɗorata akan keken ɓera wajen nuna mata muɗin mutanen banza ne bama sonki da ƙaunarki, sai kuma a yanzu dan mun maimaita abinda kika aikata zakiji zafi? Ai dama na faɗa miki ƴaƴana sai sun dawo gareni tunda ke bakisan mutunciba, burinki kawai ki nisantasu dani da ƴan uwana to muzuba mu gani ɗan halak ka fasa ni da ke a garin nan”.

     Mammah zata sake magana Mahma ta dakatar da ita da sauri. “Kuyi haƙuri Kabeer, tabbas Hindatu ta aikata laifi, amma inason ku fahimceta itama, kunsan a duk sanda mace ta rabu da uban ƴaƴanta babbar fargabarta shine barin masa ƴaƴanta wata tazo ta cuta musu koshi uban ya nisantasu da ita. Na tabbata wannan shine fargabar Hindatu tun a wancan lokaci da yanzu haka. Amma bawai hakan na nufin ina goya mata baya akan abinda takeyi nason ganin ita ta nisantasu da ku ba duk da kawaicin da kukai mata na tsayin shekaru. Ina son dan ALLAH a wannan gaɓar mu haɗu wajen yafema juna, mukuma fahimci juna dan mu duka munada ƙarfin iko akan Adilah da Abdul-Mutallab. Sai dai hakan ba yana nufin mu cigaba da raba hankalinsu ba da ƙarfin ikon da ALLAH ya bamu akansuba na iyaye”.

     Tsit falon yayi dan maganar Mahma tayi tasiri a zukatansu sunkuma san gaskiya ta faɗa. Hakan yasa AK dake tsaye tun ɗazun daga bakin ƙofa ya ƙarasa shigiwa. Zama yay ya gaidasu batare da ya yarda ya haɗa ido da kowaba dan ransa a jagule yake babu daɗi.

     Mahma ce ta dubesa da kulawa, “Abdul-Mutallab nasan duk kaji mike faruwa. Sai dai jin naka bashine mai muhimmanci ba, a yanzu mu munfi buƙatar son sanin a ina aka haihu a ragaya game da haihuwar yaro mai sunanka?”.

        Iska yaɗan furzar kansa a ƙasa. “Mahma wlhy nima ban saniba”.

    “Kamarya baka saniba, a ruwa ake shan ciki balle kace mana itama acan tasha?”. Aunty Zakiyya tai magana karon farko tun shigowarsu a hasale

         “Tabbas ba'a sha, amma inaga itakam dai acan ta shashi. Dan ni dai ban taɓa tarayya da wata mace bayan matata ba ALLAH shine shaidata. Sannan ban taɓa ganin yarinyarnan da idanuna ba sai a gidan nan. Amma kuma tabbas na yarda Abdul-Mutallab ɗa nane, ina kuma kan binciken ta yadda aka samar dashi insha ALLAH”.

      Shiru falon yayi tsahon lokaci, sai Uncle Ahmad da wani tunani yazo masa a zuciya dan shidai shedane akan AK bai iya ƙaryaba yace, “Abdul-Mutallab maganar nan ba wadda mutane zasu ɗauka bace balle su fahimceka. Amma sai nake tunanin ko kun taɓa yunƙurin yin wannan dashen na zamani da aketa nusar al'ummar musulmi rashin anfaninsa?”.

      A karon farko AK ya ɗago ya duba Uncle ɗin nasa da rinannun idanunsa. Hakama Mammah da aunty Zakiyya a razane suka dubi Uncle Ahmad har hakan ya bama Mahma da Hajiya iya mamaki. Da sauri AK ya girgiza masa kansa. “Wlhy Uncle ni ban taɓa son hakanba dan bayama birgeni, na tabbatar idan ALLAH yaso zai bani, da bai baniba kuma ƙila haka shine mafi alkairi a gareni”.

       Cikin jinjina kai Uncle Ahmad yace, “Na yarda da kai Adnan dan baka taɓa min ƙaryaba, sai dai wannan al'amarin na buƙatar bincike, musamman ga matarka kota taɓa wannan yunƙurin aka samu kuskuren ɗaukar sparm ɗinka aka saka ga ita yarinyar bada sanin ku ba ku duka tunda wannan matsalar kan faru saboda son zuciyar wasu likitocin, kokuma daga likitocin matsalar take baki ɗaya”.

       Wani irin mugun tarine ya sarƙe aunty Zakiyya har sai da aka bata ruwa. Ita kanta Mammah sai zufa take gogewa a kaikaice. Cikin rawar murya tace, “Hakan bamai yuwuwa bane, tayaya za'ai yunƙurin hakan shi bada saninsa ba, kuma shi da ke a london yarinyar na ƙauyen katsina taya ya hakan zai faru, yadai zauna yayi tunani ko wani akasi ya taɓa faruwa”.

       Hajiya iya da zuciyarta keta kaikawo da nazarin kowa a wajen tace, “Inaga to wannan maganar babbace gaskiya, mu ajiyeta a yanzu idan an gama biki lafiya saimu yita a tsanake, dan yanzu haka ga Huzaifa nata kirana kunsan ana jiranmu a wajen walimar can”.

       Baffah da shi kansa tunanin zuciyarsa ya fara canjawa daga akalar zargin Ak da yake har yanzu zuwa zancen ɗan uwansa cikin gamsuwa yace, “Hakan shine dai-dai Inna”.

      Tabbas a wannan gaɓar suma su Mammah sunfi buƙatar tsayawar zancen su sami dama da sararin yin nazari, dan haka duk suka amince. Sai dai basuso zuwa wajen walimarba Mahma ta takura musu akan saifa sunjeta dole ko shima AK ɗin zaiji sanyi a ransa ai.

      Gudun zargin wani abu daban daga AK yasasu yarda zasuje. Dan ya tsatstsare su da idanunsa da gaba ɗaya suke a birkuce da abubuwa kala-kala da shima baisan adadinsu ba.


★★


      Sun isa ƙaton hall ɗin da za'a gudanar da walima and liyafar cin abinci rana daya ƙawatu matuƙa. Ya kuma cika taf da al'ummar MANZON ALLAH (S.A.W). Ga manya manyan malamai da zasu gabatar da lectures. Sashin mata daban na maza daban babu ruwan wani da wani, hakkane ya samama AK nutsuwar da yake buƙatar samu. Suna isowa aka gabatar da addu'oi da suka shafi komai na rayuwa bayan ma'auratan, kafin a fara abinda ya tara mutane.

     Malamai sun ragargaza lectures masu ratsa jiki akan aure da zamantakewar rayuwa data saka jikin mutane da yawa yin sanyi, Zinneerah amarya da duk da basan waye mijin nataba tasha kuka itama, lectures ɗin kuma sun shigeta matuƙa. Lokacin salla nayi aka fita akai sallar zuhur sannan aka dawo aka ɗora dacin abinci, a hakanma dai malamai na cigaba da aikinsu har zuwa la'asar da aka rufe da addu'oin fatan alkairi ga ma'aurata damu da muke a gidan auren sannan aka tashi.


      Da yawan mutane daga nan suka fara kama gabansu, wasu kuma suka koma gidansu AK domin rakiyar amarya ɗakinta da za'ayi da wuri, duk da dai hajiya iya tace ƴan danya bazasu koma a yau ba kamar yanda suka sanar, tace su bari sai ALLAH ya kaimu gobe su da ƴan ɗan musa saisu tafi.

       Sunkiji daɗin haka dan sam garin ba isarsu yayiba. Musamman da kowa yake samun isashen abinci mai rai da lafiya nama har ba'a cewa komai.

     Suna dawowa ba'a zaunaba Hajiya falmata ta hau yima amarya shiri na musamman wanda ya kaisu har bayan isha'i, ana idar da salla ta kammala naɗeta cikin haɗaɗɗiyar lifaya datai mata matuƙar ƙyau kamar ba an Zinnin danya mai tallar riɗi da gyaɗa ba. Daga haka aka miƙata wajen su Baffah da manyan iyaye ƴan bauchi sukai mata faɗa da nasiha matsayinsu na iyaye gareta, sai ga hajiya iya na sharar hawaye kuma, hakama su Meenal kuka rurus suke sha abin tausayi, Sa'a ma sai ta kama kuka dama tasha wani a danya. Tinene kuwa tana kwance rijib babu lafiya dan ko a wajen walima kasa sakewa tayi, danma Yaya Atine nata mata masifa wai harda langwai daga zazzaɓi.

     Yaya Gajeje najinsu dai bata tankaba dan ita tasan mita hango tattare da Tinene ɗin, tanata ƙoƙarin dannewane harsu koma lafiya gida kawai.      

         Bayan an kwashi masu rakkiyar amarya a motoci aka fito da amarya daketa rusar kuka wadda Hajiya iya zatai mata rakkiya har ɗakin mijinta. Aiko Zinneerah na naɗe a jikinta tanata kuka ranta fal fargabar wanda zata tarar matsayin mijin nata har suka iso ƙyaƙyƙyawan gidan na AK da yaji kayan more rayuwa. Duk da yace kar iyayenta suyi komai sai da suka nuna bajintarsu suma gwargwadon ƙarfinsu. Dan kuɗin baba dana abba aka dunƙule waje ɗaya akai mata kaya ƴan ubansu da gara, hajiya iya kuwa dama itace tayi komai na kayan kitchen. 

      Ɓangaren ta daban na Farah daban, duk da dai babban falon farkon shigowa ya haɗa ɓangarorin gidan uku, dole ta cikinsa zaka doshi kowanne ɓangare harna mai gidan, amma kuma kowacce a sashenta tanada faluka guda biyu kuma da bedrooms har uku sai kitchen. Tun kafin fitowa mota sai da hajiya iya ta saka zinneerah dake lulluɓe har kanta tana kuka yin addu'a, hakama da zasu shiga babban falon da sashenta.


      A lokacin da ƴan kawo amarya ke shigowa su Mammah suna sashen Farah cikin tashin hankalin sumar da tayi, dan tunda aka taso wajen walima su nan gidan suka nufo kai tsaye, tarbarau tayi da murnarta dan batasan mike faruwaba, kuma ko daɗewa dayin waya da AK bataiba. Sai dai halin da taga aunty Zakiyya da Mammah a ciki ya ɗaga mata hankali ta shiga tambayarsu lafiya? Duk yanda Mahma taso ƙwaɓar aunty Zakiyya da ido akan karta sanar mata sai da aunty Zakiyya da hankalinta ke tashe da zancen Uncle Ahmad na dashen ciki tai suɓutar baki wajen sanarma Farah zancen auren AK. Ko rufe baki batayiba Farah ta yanke jiki ta faɗi a sume.

    ALLAH ya sosu hakan yay dai-dai da shigowar AK gidan a gajiye. Hankalin sane ya tashi matuƙa shima, babu shiri ya tsaida Dr Mahmud da ya kawosa gida. Tofa shine tun lokaci suka rufu akanta da ƙyar suka samu ta farfaɗo Dr Mahmud daya sa aka kawo masa kayan aiki daga asibiti yay mata allurar barci mai nauyi da har yanzu take kanyi bata farkaba.

       Mammah sai masifa take akan wlhy idan Farah ta rasa ranta sai tayima Kabeer abinda bazai taɓa mantawa da ita a duniya ba. Tanayi tana sharar hawaye hakama aunty Zakiyya kuka take rurus dan tana tsananin ƙaunar autar tasu Farah da tausayinta ke damunsu saboda mahaifiyarsu na haihuwarta ta rasa ranta ko ganin Farah ɗin ma batayiba.

     Koda sukaji an kawo amarya Mahma ce kawai tai ƙarfin halin fita tarbarsu kar ace babu kowa a cikinsu tunda ansan suna gidan kuma. Bata nunama hajiya iya komai na halin da ake cikiba ta rungume Zinneerah tana mata barka da zuwa cikinsu. Ita dai Zinneerah ba sanin wacece tayiba tunda kanta a rufe yake, tanata dai sharar hawayenta musamman da taji mutane nata sallama suna ficewa dan ance ba zama za'ai ba. Duk maison ganin ɗakin amarya yazo gobe idan ALLAH ya kaimu ya gani da ƙyau.

     Wannan yasa Zinneerah batasan sanda hajiya iya ta sulale ta gudu ba ita dasu Yaya Gajeje. Kafinma ta farga sai jin hayaniyar tayi ta ɗauke ɗaf daga inda take sai acan harabar gidan take jiyosu.

    Zamewa tai a gadon ta kwanta tare da sake fashewa da wani irin sabon kuka maiban tausayi dacin rai.............✍


No comments

Powered by Blogger.