Makauniyar Kaddara 46


Page 46*


.........Koda akazo yin breakfast yau gaba ɗaya gidan aka haɗu harsu Momie domin nuna murnar dawowar Hajiya iya. Aiko taji matuƙar jin daɗi dan bakinta yaƙi rufuwa.

Little na jikinta tana bashi da kanta. Ita Zinneerah ma har mamakin yanda ya saki jiki da kowa takeyi, gashi yanzu ta fahimci dai yana neman zama ɗan gidan. Har ranta tanajin daɗin yanda kowa bai taɓa gano alaƙarta da little ɗinba. Amma idan ta tuna randa zasu iya sanin abin na damunta da sakata a fargaba.

        Tunda ta zauna bata yarda ta kalli inda AK yake ba, dan ta samu ta ɗan maƙale ne jikin aunty Safiyya ba sosai ake iya ganinta kamar kowa ba. Garama Huzaifa da yazo zai zauna sai da ya tsokaneta. Murmushi kawai tayi dan ita kam ba iya irin wannan wasan tayiba saboda miskilancin ta. Shima dai ya fahimci miskilarce, hakan ya sashi faɗin, “Like Husband like wife”.

     Murmushi su Baffah duk sukayi, yaran kuwa kowa yay ƙasa da kai yana gumtse dariya. Ita dai Zinneerah ba sanin inda ya dosa tai ba. AK kuwa yi yayi kamarma baiji mi Huzaifa ya faɗaba, ya maida hankali gacin abincinsa kawai dan hajiya iya ta riga tai musu sabon idan suka zauna gaban abinci shi kaɗai suke bama dukan nutsuwarsu har sai sun kammala.

      Shine farkon tashi, kamar an tsikari little shima ya miƙe daga jikin hajiya iya yana faɗin, “Abbana zanje”.

      Yanda yay zaram ɗin ya miƙe da maganar tasa data fita raɗam ya saka kowa yin dariya, banda Zinneerah da aranta take raya (kajimin yaro da shegen ɗafa, wai Abbana).

     AK kam dawowa yay da baya yasa hannu ya ɗaukesa yana murmushi, ba komai kesa little na ƙara manne masaba sai yawon da yake fita da shi, shiko yaro dama akwai son yawo shiyyasa duk inda sukaga maza koda basu da wayo suke maƙale musu. Balle little dake da wayo masha ALLAH.

       “Sweetheart kaima fa ka iya yawo na lura”. AK ya faɗa lokacin da suke nufar ɗakinsa shi da little. 

      Mommy dake binsu da kallo ita da Baffah tace, “Ƙuruciyar little tamkar Adnan, har wayon tsiyar ya kwaso bai rageba. Wani irin bugawa ƙirjin Zinneerah yayi a take, har takai ta ɗago ta kalli Mommy batare data saniba. Haɗa ido sukai da Hajiya iya dake kallonta cike da nazari ita, tai saurin maida kanta ƙasa. Harga ALLAH maganar ta daketa shiyyasa duk abincinma ya fita mata a rai. 

       Ganin yanda taketa faman juya cokali a cikin abincin Hajiya iya tace, “Inno kin ƙoshi ko?”. Da sauri tako ɗaga kanta jin ta samu mafita, kafinma Hajiya iya ta sake cewa wani abu ta miƙe da sauri. Sauran da duk basu san mike faruwaba basu fahimci komaiba. Da wannan damar Zinneerah ta samu ta silale daga wajen ta koma ɗaki.


     Tayi zurfi a tunani sosai Hajiya iya ta shigo, harta zauna Zinneerah batasan da zuwantaba, sai da ta gama mata kallon nazari tsaf sannan ta taɓata. Nufashi Zinneerah ta kawo a zabure, sai dai ganin hajiya iya ya sakata sauke ajiyar zuciya da ɗan ƙaƙaro murmushi. 

      “Granny ashe kin shigo? Bara na ɗauka miki maganinki kisha”. Tai maganar tana ƙoƙarin tashi. Kamo hannunta Granny tayi ta maida ta ta zaunar. Hakan yasa Zinneerah ɗan kallonta. Amma ganin itama kallonta Granny keyi saita maida kanta ƙasa dan kallon ya banbanta da wanda ta sani. “Kamannin Abdul-Mutallab da Moddibo na ruɗaki ko? Muma haka suke ruɗamu a koda yaushe. Sai dai nasan jinine kawai yasa Hauwa'u haifo mai kama da Moddibo”.

     Ɗan murmushin yaƙe kawai Zinneerah tayi kanta a ƙasa har yanzu, Hajiya iya taci gaba da magana batare da ta damu da yanayin Zinneerah ɗin ba. “Ki shirya zuwa anjima da yamma hajiya Zulai zatazo ku wuce katsina akwai wani aike da zaku kaimin amma ke da ita kawai zakuje”.

      Saurin ɗagowa Zinneerah tai ta kalli Hajiya iyan a karo na farko, dan itafa tama kanta alƙawarin bazata ƙara taka ƙafarta katsina ba saboda tsoron karsu Hajiya su ganta. Duk da a yanzu tafi ƙarfin a ƙara kaita inda aka kaitan, kuma tasan ba gidan yankan kai baneba kamar yanda ƙuruciya ta sata kiran wajen a baya.

    Cike da basarwa Hajiya iya tai ɗan dariya, “Oh wai kokin taɓa zuwa Katsina ne Inno?”.

      Murya a raunane Zinneerah tace, “Sau ɗaya Granny”.

      “Kai, duk da kasancewarki bakatsina? A to karma ki faɗa gaban su Jamal sumiki dariyar Danya kawai kika sani”. 

     Ƴar dariya tayi saboda yanda hajiya iya tai maganar cike da raha. Batare da tunanin komaiba tace, “Granny ai shima aiki Inna tasa wata mata taje dani nayi bama yawo naje ba”.

       “Aiki kuma? Kina nufin aikatau fa kenan?”.

      A take damuwa ta bayyana akan fuskar Zinneerah, ƙwalla suka ciko mata idanu, murya a raunane tace, “Eh aikatau Granny, ni bansan miyasa Inna bata sonaba. Dagafa wata ƙawarta tazo ta bata labarin kuɗin da ake samu shikenan tasa na bita ko baba bai saniba. Amma tsabar sharri dana dawo sai tace wai yawon banza naje, wlhy kuma ba yawo najeba”.

        “Toke miyasa baki faɗama Babanki gaskiyar abinda ya faruba?”.

     “Haka kawai naji inajin tsoro Granny, koma nayi niyyar faɗa masa saina kasa dan Baba tsoron Inna yakeji saboda masifarta wlhy, bama shi kaɗaiba ƴan garinmu da yawa tsoronta sukeji dan jarababbiyace sosai”.

      “Kai wannan mata ALLAH ya wadaran halinta, ina daɗi ace miji na tsoronka. To amma ke miya faru har tasa aka tafi dake aikatau babu wanda ya sani, harma ta samu damar miki sharri kinje yawo?”.

    Hannu Zinneerah tasa ta share hawayenta daketa sakkowa saboda tuna a yanda tabar Danya wancan lokacin, babu wani tunanin wayon manya Hajiya iya ke mata ta fara zayyana mata yanda abin ya kasance.

      “Hajja lanti ƙawar inna ce sosai, dan nidai tare na sansu tunda na fara wayo, dan Hajja Lanti dillaliyace a garinmu, tana kuma saida abubuwa iri-iri. Daga baya kuma ta koma ɗaukar yara tana kaiwa aikatau a birni. Hajja lanti ba sona takeba itama, shiyyasa bana murna da zuwanta gidanmu, dan duk randa tazo da wahala kaga harta tafi Inna bata dakeniba saboda tsaban iya haɗa gulmanta. A wata ranar asabar na dawo daga tallan gyaɗa da riɗi a gajiye na iskesu zaune a tsakar gidanmu suna magana da ban san kota micece ba. Ni dai na gaidasu na bama Inna kuɗin tallar na shige ɗaki dan tace karna sake zama a tsakar gida idan tayi baƙi. Ban jima da shiga ba ta ƙwalamin kira. Koda na fito sai da suka gama min kallo na wani lokaci ne naji hajja Lantin na cewa “Ai wannan ma itace dai-dai a yanzu. Dan za'a jima ana samu tattare da ita”. Bansan ina zancen nasu ya dosaba. Ni dai Inna tacemin naje na canja kaya nawuce can bakin ɗorawar kan hanya na jira Hajja Lanti zamuje anguwa. Ban musa mataba naje na canja kayana na fito, saita sake korani da cewar naje na saka kayan sallata. Zuwa nai na sake canjo kayan na fito, a gabansu na tafi inda tace naje na jira hajja Lanti ɗin. Na jima a bakin ɗorawa zaune sannan hajja lanti tazo ita da wasu yara da ban sansu ba. Batare da itama tamin bayaniba ta bani hijjabi da nikab wai na saka. Nidai ban musa mataba na saka. bayan na sakane ta kira masu mashin su uku suka daukemu zuwa Gozarki. A Gozarki muka kwana dan maraice ya rufa lokacin. Washe gari tunda farar safiya muka tafi inda ake hawa mota muka shiga motar Katsina da naji ana faɗi a wajen. Nasha mamaki amma a raina ina ɗoki zanje katsina da nakeji a labari. Koda muka isa Katsina an saukemu a wani waje mai tarin jama'a, mudai muka shiɗa a motar kamar yanda tace mana. Daga nan an ɗibemu a napep zuwa wani waje da naji hajja Lanti ta kira da suna anguwar yari.

          Kamar yanda ƴan uwan tafiyata basa gane komai a wannan tafiya nima dai ba ganewa nakeba. Sai dai ina lure da komai da akeyi. Kamar sunayen wajajen da muka sauka da inda muke tafiya. Mun isa anguwar yari da tace a kaimu. Inda aka saukemu a wani gida mai matsakaicin ƙyau da girma. 

        Koda muka shiga cikin gidan mun samu kusan mutane goma a cikinsa, Sai wata dattijuwar mata da tafi hajja Lanti shekaru dajin daɗi. Yanda ta tarbemu ne yasa naji ɗan dadi ga raina. Sai dai yanda maza da mata ke shiga da fita gidan baiminba a rai. Mun jima zaune suna hira kafin a kawo mana abinci muci, bayan mun koshi aka haɗamu da wata a gidan mai suna Sadiya. Itace ta kaimu wani ɗaki wai anan zamu zauna. Nidai kallon kowa nake da mamaki da tunanin mi mukazoyi nan? Miyasa Inna tace na biyo wannan matar nan batare da Baba ma ya sani ba?. Banda mai bani amsa, shiyyasa naja bakina na tsuke. Daga wannan lokaci ban sake ganin hajja Lanti ba a gidan, ban kawo komai a rainaba sai tunanin ko taje wani wajene ta dawo tazo mu dawo gida. Amma sai naji shiru har tsayin kwana biyu. Duk da ana bamu abinci muci mu ƙoshi, ga television muna kallo hakan baisa hankalina ya kwantaba, sai dai inajin tsoron na tambayi wani ina hajja Lanti take?. A randa muka cika kwanaki uku a gidan naga an kwashi abokan tafiyata su uku aka fita dasu a gidan, daga haka ban sake ganinsuba suma. Hankalina ya tashi na shiga yi musu kuka akan nidai su maidani garinmu, danni na ɗauka kodai ƴan yankan kai ne ma. Ranar naga ruwan masifa wajen matar nan, dan kamar zata dakani a turmi saboda masufar data dinga min. Dolena shanye kukana saboda tsoronta. Da maraice aka sake kwashe sauran abokan tafiyata su biyu da suka rage aka barni ni kaɗai sai waɗanda na samu a gidan. Ranarma nayi kuka har takaini gayin masassara. 

          Magani kawai suka bani nasha, daga haka babu wanda ya sake bi takaina, sai ma da daddare kusan ƙarfe takwas hajiyar tace a tasoni zamu fita. Ina jinta daga ɗaki danba barci nakeba, tunanin asibiti zata kaini yasa ban kawo komai a rainaba na tashi na fito bayan na saka hijjab ɗina. Tsaye na sameta a tsakar gida cikin gayu, na gaisheta jikina duk a sanyaye saboda zazzaɓi dake cina. Gaba tai na bita baya batare damin maganaba. Muna fitowa ƙofar gida muka iske mota mai ƙyau.

       Motarnan muka shiga, gabana nata faɗuwa nidai inata tunanin lokacin yanke nawa kan yayi. Dan haka naita addu'a kala-kala ina sharar hawaye a ɓoye da roƙon gafarar babana a zuciya, a haka muka iso wata babbar anguwa dabansan sunantaba, sai dai yanda ko'ina ke ƙwanyar da hasken lantarki zai tabbatar maka da anguwar masu kuɗice. Katafaren gida mai blue gate aka buɗe mana muka shiga, kasancewar darene bazan iya banbance tsarin gidanba, sai dai lallai ya haɗu matuƙa. Koda muka fito a motar hajiya ce ta kama hannuna muka shiga ciki. Anan ne na sake tabbatar da gidan ya haɗu, masu shi kuma sunada kuɗi. 

     Waɗanda muka samu a falon ne sukai mana iso zuwa ciki bayan mun gaisa, an sake kaimu wani falon, inda muka zauna zaman jiran matar gidan. Munfi ƙarfin awa ɗaya zaune kafin ta fito, ƙyaƙyƙyawa ce sosai baƙa, daka ganta kaga bafulatanar bakatsiniya, dan ƙyawun nata ya fita sosai masha ALLAH. Sai da ta gama mana kallon tsaf kafin ta amsa mana gaisuwa tana sake ƙaremin kallo, cikin maganar daban ganeba hajiya tace, “Ranki ya daɗe ga wata ki duba ko zata iya, yau kwana uku da kawomin su daga wani ƙauye”.

      Kallona ta sakeyi sama da ƙasa tana ɗan yamutsa fusaka. Ta ɗage kafaɗunta cike da isa tana faɗin, “Uhm babu laifi kam, dan tafi waccan komai, girma kawai waccan zata fita. Amma ina zuwa”. Tai maganar tana miƙewa, fita tai, babu jimawa sai gata ta dawo ɗauke da waya, batare da tayimana maganaba ta shiga haskani da hasken wayarta daban fahimci ma'anarsaba a wancan karon, sai dai a yanzu inaji a raina camara ne. Bayan ta gama kuma ta fara waya, da turanci take magana shiyyasa banji komaiba, bansan dai ga hajiya ba. Ta ɗauki lokaci mai tsaho tanayi kafin ta ajiye ta dubi hajiyar, “Ba damuwa zamu gwada mu gani, bara na ɗakko miki sauran saƙonki ko, idan akwai wani matsala zan nemiki daga baya kafin ki wuce, namafison sai mun kammala komai mun fara wucewa kafin taki tafiya”.

     Baki a washe Hajiya tace, “Ato babu damuwa ranki ya daɗe, ni bani da matsala duk yanda kukeso sai ayi, fatana dai ALLAH yasa a dace akumayi nasara”.

     Cike da yanga ta amsa da amin. Daga haka taje ta kawo mata saƙon da tace. Inaji ina gani hajiya ta miƙe tana faɗamin aini nan zata barni, nanne zanyi nawa aikin, dan haka sai nayi biyayya, yi nayi bari na bari.

      Sosai na fara hawayen fili saɓanin na zuci, yanda zuciyata kemin zugi da zafi ya hanani yin magana harta fice ta tafi bayan ta bani ɗari biyar a kuɗin danaga an bata masu yawa, itama haijiyar gidan ta shige batare damin maganaba. Da wannan damar nai zaman kuka na kusan awa ɗaya kafin wata tazo cikin wanda muka fara tararwa a falon farko ta kama hannuna muka fice.

        In taƙaita miki Granny tun daga ranar zazzaɓina ya ƙaru, inaga ganin yanda nake galabaita yasa Hajiyarnan ɗaukata a washe gari takaini wani asibiti mai ƙyau da alama na kuɗine. Anan aka bani gado. Sosai likitan yaytamin tambayoyi harnaji nama ƙosa dashi, amma na daure dan lafiyata nake nema ai. Kwanana shidda a asibitin nan na warke sarai aka sallamoni, sai dai kuma hajiya ta kaini wani gida ba nata da aka fara kainiba, naji tsoro sosai, dan can babu kowa sai wata dattijiwar mata mai suna Harirah. 

     Ɗaki guda aka bani a gidan, wanda yaji duka kayan more rayuwa, ni harma abin ya ban mamaki amma sai ban tambayaba tunda dai ance aiki nazoyi. Komai na nema ina samu a gidan, amma sai dai a tsorace nake, dan haka kawai na kasa yarda da sakin jiki da baba harirah, sai dai kullum sai ta shigo ɗakina ita ta sakani shan magungunana na asibiti da aka bani. Hajiyar kuma ban sake ganintaba sai bayan kwanaki sai gata. Cataimin na shirya muje asibiti likita ya sake dubani, ban kawo komai a raiba na shirya na bita zuciyata fal fargaba. Munje likita ya sakemin gwaje-gwaje, sai yace wai akwai wani ciwo dake damuna zasu ban magani. Daga wannan maganar aka kaini wani ɗaki, tunda akaimin wata allura ban sake sanin inda nakeba sai a gida. Ni kuma tunda na farka sai tsoro ya kamani ganin ko baba harirah ɗinma yanzu babu, sai wani gardi abin tsoro dake a waje. Hankalina ya tashi, da ƙyar na samu nai wanka nayi salla. ina idarwa na saka kayan danazo dasu daga gidan hajiyar farko da aka kaini, ALLAH ya taimakeni na silalo na fito daga gidan, ɗari biyar ɗin da hajiyar ta bani da zata tafi lokacin data kaini can gidan itace ta taimaka mani na koma Danya. Koda na koma kuma saina kasa bama kowa labarin abinda ya faru har Babana, duk da inason na faɗa masa kodan kalmar iskanci da Inna ke dangantani da shi sai dai inajin tsorone”.

           Shiru hajiya iya kawai tai tana kallon Zinneerah kamar mai karanto komai akan fuskarta, sai dai wani irin tausayin yarinyar da ƙaunarta na sake shigarta. Dan yanda take bata labarin a nutse sai take ƙara godema ALLAH da samunta matsayin matar jikanta mafi soyuwa a ranta. Ta ɗan murmusa cike da basarwa tana faɗin, “Uhmm lallai dole ki kasa mantawa da birnin katsina. To amma ita hajiyar data kaiki gidan baki koma gidantaba bayan kin baro can?”.

     “Wai Granny sokike na koma ta sake maidani, nifa wlhy haka kawai naji banason hajiyarnan data kaini asibiti, ta cika tsare gida da mulkin tsiya kamar sarki”.

      A karon farko Hajiya iya tai dariya da juyawa tana kallon AK datun fara maganarta da Zinneerah ya shigo ɗakin, sai dai jin labarin da Zinneerah ta fara badawa ya sakashi dakatawa batare daya shigoba. Yanda ya kafe Zinneerah da idanu yana ma labarin nata fashin baƙi da nazartarsa yasa hajiya iya faɗin, “Amma baki taɓa gamo da maikama da wancan mutumin a katsina ɗinba?”.

     Sai a lokacin Zinneerah ta farga da AK, duk da ta jima tanajin ƙamshinsa a hancinta bata kawo shi baneba. Kallo ɗaya tai masa tai saurin maida kanta ƙasa saboda yanda kwarjininsa ke cika mata idanu da zuciya. Cikin girgiza kai tace, “A'a Granny, anan na fara ganinsa nikam”.

     “Inno bafa wasa nakeba”.

Da iya gaskiyarta tace, “Wlhy kuwa Granny”.

     Hajiya iya zata sake magana AK ya katseta da faɗin, “Kin shirya ne na kaiki gidan Gwaggon?”. (mmn sadiq).

      Tsaf hajiya iya ta fahimci dalilinsa na katseta, dan haka tai guntun murmushi da cewa, “Eh bara na kimtsa, ai hada Inno ma zamuje saimu barta acan dan da safe idan ALLAH ya kaimu zata dawo akwai inda zan turata”.

    Baice komaiba sai duban Zinneerah ɗin datai ƙasa da kanta yaɗanyi, ya ɗauke idanunsa ya juya ya fice. 

    Binsa da kallo Zinneerah tayi, tana ganin ya fice ta sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya da har sai da hajiya iya tai murmushi.............✍


No comments

Powered by Blogger.