Makauniyar Kaddara 45

 


*Page 45*


...........Sai da ya kai zaune sannan ya ɗan dubeta ya kauda kansa yana maidawa ga Hajiya iya mamaki har yanzu shimfiɗe a fuskarsa. Kansa ta shafa tana murmushi. “Mamaki ko?”. Ta faɗa tana kamo hannunsa cikin nata.

      Cikin ɗacin murya yace, “Amma Granny yanz......”

     “Shiii” ta faɗa tana girgiza masa kanta alamar kar yace komai. Badan yasoba dole yay shiru yana binta da kallo. Barin wajen Zinneerah tayi dan kasancewarsa a wajen yasa taji ya cika mata fili kamar yanda takeji a duk sanda yana a waje. Handbag ɗin Hajiya iya ta ɗauka tabi bayan su Bahijja da har sun shige, barci da gajiyar da take ciki ya haddasama tafiyar tata sanyi sosai fiye da ko yaushe. 

     Shigowar Khalipha ya sanya Ak dake binta da kallo juyawa ya dubesa. Murmushin ƙarfin hali Khalipha yayi da matsowa ya rungumesa yana jera masa kalmar “I'm sorry yayanmu”.

    Komai baice masaba, sai kansa kawai daya ɗan kaɗa yana miƙewa. “Dare yariga yayi nisa, yakamata ku kwanta ku rage gajiya”. Daga haka ya nufi ɗakinsa ransa duk babu daɗi da dawowar tasu, dan shi ba haka yaso ba.


         Ƴan gidan babu wanda yasan da dawowar ƴan london sai washe gari, a take suka rikice da murnar dawowar Granny, yayinda Baffah kuma keta mamaki, sai dai dariyar da yaga Huzaifa nayi suna magana da Khalipha ƙasa-ƙasa ya sashi fahimtar sune suka ƙulla komai. Uffan baiceba ya shiga layin ƴan murnar ganin hajiya iya shima.

    Sai da duk suka lafa da gaishe-gaishe da tambayar jiki sannan su Zinneerah suka fito suka gaida Baffah suma. Cike da jin daɗi da kulawa yake amsa, dan ƴan kwanakin da sukai acan harsun ƙara canja kala.

         Sai da kowa ya nutsa sannan Baffah ya samu zama da Granny shi da Mommy da hajiya iya keta murnar ganinta da kiranta autarta. Yanda Mommy ke nane da hajiya iya sai hakan ya birge Zinneerah har little ɗinta ya faɗo mata a rai da mamanta itama da baba. Murmushi tayi a zuciyarta tana mai begen ganinsu.

      Kamo hannunta Mommy tayi ta zaunar kusa da ita tana faɗin, “Masha ALLAHU, lallai yarona ya iya zaɓe, dan ɗiyar tawa kam badaga nanba”.

    Kunyace ta kama Zinneerah duk da bata fahimci inda zancen na Mommy ya dosaba. Sai kuma can gefen zuciyarta ke raya mata ko dai Moos'ab ya faɗa musu wani abune?. Sosai gabanta ya faɗi, taɗan saci kallon Khalipha dake ƙoƙarin fita zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Bata gama kammala tunanintaba ta miƙe ganin kowa ya fice a yaran sai ita kaɗai. Itama ficewa tai tabar su Granny dan taga alamar magana zasuyi.


        Kayan barcine wando da riga a jikinta, sai dai ta ɗora hijjab mai hannu a sama kalar pink mai haske daya kai mata har gwiwa, gashi ya ɗau guga dan da zatai salla ta cirosa ta saka.

      Fitowarta dai-dai da shigowar AK ɗauke da little a hannu, kamar daga sama taji muryar gudan jininta na ambaton, “Aunty! Aunty!”.

    Da sauri ta ɗago ta kalli hanyar shigowar duk da zuciyarta bata yarda da abinda tajin ba. Cikin sa'a kuwa sai a kan little daketa zillo daga jikin AK alamar zaizo wajenta. Shiko yaƙi sakinsa sai ma kafeta yay da idanu kai tsaye hankalinsa kwance.

        A hankali ta motsa laɓɓanta wajen ambaton “Little” da mamaki shimfiɗe a saman fuskarta. Ga wani bugawa da ƙirjinta keyi saboda matsanancin kamannin yaron nata da Yayansu da suke ƙara bayyana kansu a koda yaushe. Musamman yau da fuskarsu ke gab da juna kuma little ɗin tamkar ya ƙara girma da wayo.

      Duk yanda taso ɗaga ƙafarta zuwa garesu ta amshi little ɗin ta kasa, haka ta cigaba da tsayuwa harshi ya fara takowa a hankali yana nufota. Tsitt falon yayi kowa ya zuba musu idanu ƙasa-ƙasa, musamman su Mas'ood da sukasan mike tsakani yanzun. Su Jamal dai yanda Yayan nasu ke kallon Zinneerah ɗinne da yanda tayi itama ya basu kala suka tsaya kallo dan son ganin mike shirin faruwa.

       Gab da ita ya tsaya, batare da yayi maganaba ya kamo hannunta ɗaya ya ɗaura na little akai. Kafin ya saki yaron gaba ɗaya gareta yana motsa laɓɓansa a hankali yanda ita kaɗai zata iya jinsa, itama ɗin sai da taimakon motsin laɓɓansa. “Sai na tsone wannan idanun”.

     Sosai taji wani irin shock saboda jin hannayensa da nata na neman sarƙewa waje guda lokacin da yake sake mata little, magarsa da yanayin da ta ji ya sata tura baki da ɗan juya kwayoyin idon dazai tsokale batare da tasan tayiba. 

        Leɓensa na ƙasa ya wani cije ganin yanda ta tura baki ga idanunta sun fara tara ƙwalla suna wani farfar. Ya saki wani munafikin murmushi da ya nema sakata sakin little ɗin ƙasa yana ja da baya. Da wani irin slow tafiya ya raɓata ya wuce ƙamshin turarensa na sake bugun hancinta.

    Babu shiri ta ƙanƙame little jin zai suɓuce mata. Suko su Saifudden suka shiga sunne kawuna ƙasa suna dariyar shaƙiyanci ƙasa-ƙasa. Su Bahijja kuma da basusan dawan garinba bakuna suka saki cike da mamaki da al'ajabin abinda Yayan nasu yayi yanzun, amma ya fiske ya wucesu tamkar baisan da zamansu a wajen ba.

       Yana shigewa ɗakin Hajiya iya su Mas'ood suka shiga tafawa da juna. Khalipha yay ƙasa da kansa yana sakin murmushi da ƙoƙarin kauda komai dake ransa dan yasan dai ta ƙare. Koda ace ya furtama Zinneerah so Yayansu ya nuna yanaso wlhy zai iya sadaukar masa. Ballema ALLAH ya soshi bai taɓa koda nuna mataba duk da kuwa tun sanda ya haɗu da ita a gidan tai caraf da zuciyarsa. Dan bazai saka haɗuwarsu ta farko a lissafi ba, saboda kallon matar aure yake mata. Duk abinda yay mata kuma tausayine a wancan lokacin ba so ba.

      Moos'ab ma dai daurewa yake matuƙa wajen danne komai, dan yayi alƙawarin koda yaƙi sai ya cire Zinneerah a ransa ta koma matsayin matar Yaya da ƙanwarsa har cikin zuciya.


      Zinneerah kam ƙanƙame little tayi a jikinta da sauri mamakin abinda Yayansu yayi na neman kasheta da ranta. Ta bisa da kallo harya shige ɗakin hajiya iya ko waiwayosu baiyiba. “Aunty!!” little ya faɗa da ƙarfi cikin kunnenta yana bubbuga mata kafaɗa. Babu shiri ta juyo garesa tana sauke tagwayen ajiyar zuciya. Sai kuma ta saki murmushi da lakace hancin little ɗin tana faɗin, “Haba bawan ALLAH kashemin dodon kune zakayi ne? Waya kawoka nan?”.

      Bata da mai bata amsa. Danshi little ma dariyarsa ya saki maiban sha'awa saboda lakace masa hanci da tayi, ya kwanta a kafaɗarta yana zagayo hannunsa ɗaya a wuyanta zuwa ɗayar kafaɗarta. Hannunta ta ɗora akan gadon bayansa tana shafawa a hankali da murmushi, murya ƙasa-ƙasa tace, “I miss you my heart, ALLAH ya albarkaci rayuwarka, ya baka kariya a kowanne sakan na agogo”.

      

        

      A ɗakin hajiya iya kuwa koda AK ya shiga tararwa yay su Baffah na magana. Baffah na zayyanema Hajiya iyan yanda sukai da Mammah. Gaishesu yayi, duk suka amsa masa da kulawa. ya yunƙura da nufin fitowa ya basu waje Hajiya iya ta dakatar dashi ranta a ɓace dajin abinda Mammah tazo tayi.

     Komawa yayi ya zauna kansa a ƙasa dan yaƙi yarda ya kalli kowansu,  bayason suga damuwar dake kwance a cikin idanunsa. 

         Cikin kaushin murya Hajiya iya tace, “Ina maka murna da samun yarinyar ƙwarai kamar Zinneerah moddibo, itama kuma ina tayata murna da samunka matsayin miji. duk da har yanzu zuciyata ta gaza hasaso ko tunanin ta yanda kuka samar da Abdul-Mutallab. Amma a dalilin wani bayani da Khalipha yaymin yasani shiga wasuwasi, zuciyata kuma ta ƙara shiga ruɗani da bayanin mahaifinka akan abinda ya faru randa aka sanar maka yaron jininka ne. Sai dai hakan dakai ba shike nuna zan yarda dakai ɗari bisa ɗari ba Moddibo har saina san gaskiyar al'amarin nan. Amma zan cigaba da roƙon ALLAH ya bayyanamin gaskiyar kafin nabar duniya. Ada nayi tunanin barin tarewar Zinneerah harta kammala karatunta na sakandire. Yanzu kuma na canja shawara saboda dalilai masu yawa. Ciki kuwa harda gadaran da mahaifiyarka keson nuna mana akanka da ƴar uwarka, tunda dai ita na fahimci batasan kawaiciba. Kaje daga yau ka fara gyaran gidanka, ka kuma shirya haɗama Inno lefe dan nan da kwanaki goma zata tare”.

     Ba AK kawai ba hatta Baffah da Mommy sai da suka ɗago suka kalli Hajiya iya. Cinkin ɗan rawar baki Baffah yace, “Amma Inna karatunta fa?”.

      “Tayi a gidansa”.

Ta bama Baffah amsa kai tsaye babu alamar wasa ko sassauci a saman fuskarta. Ɗan ajiyar zuciya Baffah ya sauke duk da shima bawai yana nufin wani dogon zango Zinneerah zata kaiba. Dama dai tunaninsa bai wuce ta gama zana jarabawarta ta ssce da zasu fara kwanan nanba. Amma kuma tunda hajiya iya ta yanke hukunci shi hakan ya masa kodan ya sake tabbatarma Hindatu shine boss.

      Mommy ce tai ɗan murmushi tana kallon hajiya iyan, cikin kwantar da murya tace, “Innarmu baƙya ganin anyi gaggawa. Mu bashi damar shiryawa a tsanake sai a haɗa danasu Ni'ima tunda wata biyu ne kawai ya rage”.

        “Na riga na gama yanke hukunci Bilkisu, ba kuma zan canjaba saboda shine dai-dai. Anjima kaɗan za'a kaini gidan Hauwa'u itama”.

       Dole Baffah da Mommy suka amsa da to, AK kuwa uffan baice mataba. Dan shi yanzuma hankalinsa ba'a kansu yakeba. Tunanin wace magana? Khalipha ya sanarma Hajiya iyan yakeyi. 

        Ganin yanda yayi ɗinne yasa hajiya iya kallonsa a ƙufule. “Saboda an manna maka abinda ka ɓata yasa kaimin shiru Abdul-Mutallab?”.

      Yanda ta faɗi real name nashi ya tabbatar masa da har zuciyarta ne. Dan haka ya ɗago ya kalleta, wani ɗan murmushi ya sakar mata yana miƙewa, “Indai nine kamar ki ɓata ranki, duk yanda kikeso haka za'ayi”.

    Daga haka ya nufi ƙofar fita abinsa.

Su duka da kallo suka bisa. Hajiya iya dake masa kallon harara tace, “Munafuki kama fito ka faɗa kowa ya sani”.

       Babu shiri dariya ta suɓucema Baffah da Mommy, dan yanda Granny tai maganar dolene ta baka dariya. Itako tai kicin-kicin da fuska kamar ba ita ta faɗa ba.


       Koda AK ya fita baiko kalli kowa a falonba ya fice, garden ya nufa kai tsaye, yana shiga ya ciro wayarsa a aljihu ya dannama Khalipha kira. Cikin sa'a kuwa ta shiga. Ring ɗaya ana biyu Khalipha ya ɗaga dan yaga sanda Yayan nasu ya fita daga falon kamar a fusace.

     “Ka sameni a garden”. Ya faɗa kawai yana yankewa.

     Miƙewa Khalipha yayi da sauri ya fice shima sauran yaran na binsa da kallo. Tun kafin ya ƙaraso cikin garden ɗin ya hango AK daketa safa da narwa hannayensa duka biyu goye a bayansa. Sai da ya iso daf da shi sannan yay sallama. Juyowa AK yayi ya zuba masa birkitattun idanunsa da suka gama tsorata Khaliphan a take. Duk yanda yaso daurewa sai ya kasa dole ya risinar da kansa ƙasa. Cikin harɗewar harshe yace, “Yayanmu gani”.

       “Na ganka ai”.

AK ya faɗa yana nufar kujera ya zauna. Fahimtar da Khalipha yayi yau a yaya yake ba besty ba sai ya nufesa shima ya zauna kusa da shi cikin rauni.

      “Yayanmu wani abu ya faru ne?”.

“Zai dai faru Khalipha”.

    Ƙara daurewa Khalipha yayi, dan shi duk tunaninsa ko Yayansu bayason auren Zinneerah ne, duk da yanajin zafin rasata bazai so Yayansu rabuwa da itaba dan sun dace. Duk da kuma yanada mata ya fisu buƙatar Zinneerah a yanzu.

         Cikin nuna damuwarsa a bayyane yace, “Yayanmu dan ALLAH miya faru? Wlhy tsoratani kake sakeyi”.

       Kamar AK bazai tankaba sai kuma ya gyara zamansa yana duban Khalipha ɗin da ƙyau. Zazzafar iska ya furzar idanunsa na sake rinewa. Kai tsaye yace, “Wace magana kukai da Granny?”.

      “Granny kuma? Ni?”.

Khalipha ya faɗa cikin jinjinawa da son tunanowa.

      Shiru AK yayi baice komaiba. Hakan ya bama Khalipha damar shiga kundin tunani na tsahon mintuna huɗu. Sai kuma ya duba AK yana ɗan jinjina kansa. “A sanina dai gaskiya babu wata magana da nayi da ita. In badai akan maganar IV......”.

     Sai kuma ya kasa ƙarasawa.

Da idanu AK yay masa alamar cigaba. Dole Khalipha ya ɗan haɗiye yawu yana maida kansa kasa. Maganar da suka tattauna da Hajiya iya akan hanyoyin iya samuwar ciki ya sanar masa. Har yakai aya AK baice komaiba, dan tun a fara bayanin ya raba hankalinsa biyu, ɗaya ga Khalipha ɗaya ga nazari da fashin baƙin dukkan kalma ɗaya dake fita a zancen Khalipha ɗin.

       “Amma kai miyasa kayi wannan hasashen?”. AK yay tambayar yana duban Khalipha cikin ido.

      “Ba hasashe nayiba Yayanmu, kawai dai yanda ita Granny tai maganar hanyoyin iya samuwar cikine sai ta dalili ɗaya yasa nai mata fashin baƙi akai cewar yanzu akwai wasu hanyoyi da suka ɓullo a likitance. Ni wlhy bamma ɗauka zata riƙi maganar serious ba sam”.

     Karan farko AK ya saki wani lallausan murmushi da ɗaura hannunsa akan kafaɗar Khalipha ya dan bubbuga tare da miƙewa. Daga haka baice komaiba ya nufi barin garden ɗin yabar Khalipha binsa da kallo.

     Sai da ya ɓacema ganinsa sannan ya sauke numfashi shima da ɗaura hannunsa akan kumatu yayi tagumi. A fili ya furta, ‘Anya kuwa nima ban cancanci yin nazari akan wannan batunba. Gashi dai na faɗama Granny ne kawai bada wani daliliba. Amma yanda Yayanmu yay serious a maganar da yanda ya dage akan shi bai aikata komai akan samuwar Abdul-Mutallab ba kamar akwai ruɗani’. 

      ‘Tabbas akwai ruɗani’. Khalipha ya sake faɗa yana miƙewa zaram tamkar wanda aka tsikara. Domin shikam dai akwai abinda dama ya tsaya masa a rai game da cikin da akace aunty Farah na dashi ranar, shi likitane, likitan ma dayake karatu akan matsalolin mata. Amma sam baiga wani alamomin mai ciki tattare da Aunty Farah ɗinba. Anya kuwa Yayanmu da Aunty Farah babu wani abu da suke ayanzu yake ƙoƙarin bayyana kansa da kansa?...........✍

       


_Sannu-sannu bata hana zuwa, sai dai a daɗe ba'ajeba. Naga wasu sun ƙagara susan yanda aka samu little da zuwan Zinneerah aikatau, karku damu zaku sani, dan kowane al'amari da muhallinsa yake tafiya, idan kuma gaggawa ta shigo sai ya koma ba'akan tsarin dazai birgeba, wata ranama labarin zamu gama baki ɗaya insha ALLAH. Kudaiyi tattalin man kanku karya tsiyaye, al'amarin mai saukine😂. Ina gaisuwa irin trillions ɗin nan.☺️🤝🏻._


No comments

Powered by Blogger.