Makauniyar Kaddara 42

 


Page 42*


...........Cikin farin ciki Baffah da ƙanwarsa Mommy (Bilkisu) suka tari juna, duk da kuwa basu daɗe da rabuwa a london ba duba mahaifiyarsu Hajiya iya. Sama-sama suka gaisa ya shiga ciki watsa ruwa. Koda ya fito massallaci suka fice da matasan ƴaƴansa. Sai da aka idar da sallar isha'i sannan suka sake shigowa gidan.

     Sai lokacin matan gidan suka sami damar zuwa masa sannu da zuwa da ALLAH ya sanya alkairin ɗaura aure da sukaji a bakin ƴaƴansu. 

    Hakama Mommy ta shigo har falonsa inda aka shirya musu abinci tare, cikin farin ciki sukaci abinci shi da ƴar uwarsa. Sai da suka kammala suka sami zaman yin hira sosai, inda a cikin hirar ne Baffah yay kiran Khalipha ya sakashi ya haɗasu da Hajiya iya. 

     Tsaf ya kwashe mata komai ya sanar mata game da ɗaurin aure. Duk da yasan zatai farin ciki dama dajin haka sai yaji murnar data nuna ma ta zarta wadda yay zato, dan albarka dai ya shata har babu adadin ƙididdiga. Suna tsaka da wayarne AK da Huzaifa suka shigo ɗakin. Kai tsaye wajen Mommy data ware masa hannu ya nufa. Ya zauna kusa da ita tare da ɗan hugging ɗinta ta gefe yana murmushi har haƙoransa na bayyana. Dan har ransa yana ƙaunar ƙanwar mahaifin nata saboda itama tana ƙaunarsa.

        “Ina cewa zanje na gaisheki tunda wancan zuwan ban samu shigaba sai kuma gaki?”.

    Murmushi Mommy tayi dakai hannu ta shafa kan AK mai maganar. Tace, “Ja'iri anya na yarda dakai kuwa? Yanda ka ƙwace mana Inna ka kai London bamma tsammaci zuwanka nan kusaba. Nazata sai bikin su Saffiya, ashe ma kai zaka fara angwancewa kafin su. To ALLAH ya sanya alkairi ya bada zaman lafiya na har abada”.

      Kansa ya duƙar yana murmushi, akan laɓɓansa ya amsa da amin.

    Cikin tsokana Huzaifa yace, “Aini Mommy soma nake naga wace mai sa'a ce ta shiga tsakkiyar lailah Majnoon ɗin nan haka? Dan naga alamar itama da ƙarfinta take dan tun ɗazun murmushi yaƙi barin fuskar ɗan naki”.

    Dariya Mommy da Baffah suka sanya, AK kuma ya zubama Huzaifa harara da masa daƙƙuwa.

      Cikin dariya Mommy tace, “To ai kaga ya nuna maka shi ba matsoraci bane, cikakken jarumine tunda gashi har yaje ta biyu, kai kota ɗayanma ka kasa”.

       “Faɗa masa dai Mommy. Dan wlhy ban taɓa ganin matsoracin irin wannan yaron ba, maybe sai ya tsufa mu taimaka masa da wata yafendo a dangi”.

      Filo Huzaifa ya ɗauka ya jefama AK mai maganar, saurin cafewa AK ɗin yay yana masa gwalo. Su Baffah dai nata musu dariya. Dan kowa yasan dama inhar Huzaifa da AK suka haɗu duk rashin son maganarsa sai ya takura masa yayi harma suyi faɗa. 

      Suna tsaka da wannan nishaɗin Moos'ab da Haneef suka shigo ɗauke da little daketa faman zuba musu surutun da ba fahinta sukeba sosai suna dariya. 

       Kusan a tare suka ɗago suna sauke idanunsu akan little. Yayinda Mommy ta sauke wata sassanyar ajiyar zuciya tana kallon yaron ko ƙyaftawa babu da tsarkake sunan ALLAH buwayi gagara misali daya sanya wannan kamar mai ƙarfi tsakaninsa da AK, Huzaifa kuwa hannu ya miƙa masa alamar yazo. Amma sai ya maƙalƙane Haneef yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya. 

       Haneef ne dake ɗauke dashi ya ajiyesa a tsakkiyar falon yana faɗin, “Bara muga wajenwa zai je”.

        Tsit falon yay sunason suga yaya za'a kwashe? Dan yanda little ɗin ke musu kallon ɗaya bayan ɗaya dolene ya baka dariya. Kamar wanda aka raɗamawa sai ya nufi inda Baffah yake, duk zatonsu wajen Baffah ya nufa, dan haka Baffah dake murmushi ya sake gyara zamansa. Yana zuwa gab da shi sai ya zagayeshi ya miƙa hannu zai tsinki appale ɗin dake a jikin flower ɗin kusa da baffan kamarma baiga kowa a falonba.

       Hannu baffa ya kai ya dungure ƙeyar little ɗin yana faɗin, “Like father like son” fuskarsa ɗauke da murmushi.

     A take duk suka kwashe da dariya, banda AK da yay ƙasa dakai kawai yana murmushi, dan shima dai yanda Little ɗin ya wanu basar da kowa ya bashi mamaki, dan sak halayyarsa na basarwa da mutane ke yawan faɗa masa ya iya.

      Hannu Baffah yasa ya ɗaukesa ya ɗaura a cinya yana faɗin, “Ja'iri, saika mana yanga dan kaga muna son ɗaukarka?”.

    Kamar little yasan mi baffan ke nufi ya wani ƙyalƙyale da dariyar data basu mamaki, dan sanda suka shigo duk da surutu yakema su Haneef dan zuwa yanzu ya saba dasu fuskarsa a turɓune take.

    Suma dai duk dariyar sukayi kafin Baffah ya mikama Mommy shi. Zuciyarta cike da rauni ta amshesa tana murmushi, har cikin ranta jitayi so da ƙaunar yaron na shigarta. musamman yanda yake kamanni sosai da AK kamar yayi kaki ya aje.

       Fita su Moos'ab sukayi dan son zuwa su huta. hakanne ya bama su Baffah damar tattaunawa akan zancen little dake lafe jikin Mommy. AK dai baice komaiba. Sai su uku suke maganarsu da juya al'amarin. Ganin sunata jefama AK tambaya a ɗan fakaice Huzaifa yace, “Niko dai zuciyata nason min wani hasashe, amma dai kubari zan sake bincike kafin kuji minene”.

        Baffah dake kallonsa yace, “Son faɗa mana mana karka barmu a tunani”.

       “A'a Baffah, banson inyi gaggawa ne, amma dai kuyi haƙuri na ƙara nazari akai”.

       Haƙura sukai suka barshi akan yayi nazarin. AK da dai dama ba saka baki yake a zancenba sosai ya miƙe yana faɗin, “Bara naje na kwanta wlhy na gani Mommy”.

         “Ai ya isa kam agaji Babana. jeka huta kaji”.

     “Thanks you Mommy ”. AK ya faɗa yana murmushi da nufar ƙofa. Kamar an tsikari Little dake wasa jikin Huzaifa sai cayay “Abbah zanje”. Danshi kowa Abba ne a wajensa indai namijine babba.

    Cak AK ya tsaya tare da juyowa yana kallonsa. shiko da gudu ya sauka a jikin Huzaifa ya nufesa. Babu musu ya  kama hannunsa suka fice. 

       Da kallo duk suka bisu cike da sha'awa, a ransu sunajin tausayin yaron da baijiba bai ganiba, amma yaya zasuyi da ƙaddara kowa da irin tasa. ALLAH ya rubuta cewar ta hanyar daya samar da yaron yaso azurtashi da shi, ya kuma fisu sanin dalilin yin hakan, fatansu kawai ALLAH ya rayashi ya albarkaci rayuwarsa data ƙannensa masu zuwa.

        Huzaifa ne ya sake sauke numfashi, hakan yasa su Baffah dawo da kallonsu gareshi, cikin jinjina kai yace, “Ku daina zargin AK ya samar da yaron nan ta hanyar banza. Akwai wani voice recording dana taɓaji a wayar Adilah batare da itama tasan wayar ta naɗa ba, sai dai bai isa zama hujjaba sai nayi bincike”.

      Da sauri Mommy tace, “Voice recording kuma akanmi?”.

    “Kuyi haƙuri na bincika ɗin zaku sani, kudai ku tayani da addu'a ku kuma bani lokaci”.

       Cikin jinjina kai Baffah yace, “Mun baka ɗan albarka. ALLAH yayi jagora muji alkairi”.

     Da amin Huzaifa ya amsa yana miƙewa. dan shima so yake yaje ya kwanta ya huta.


________________________★


        *_LONDON_*


   Ganin yanda Hajiya iya ke murna ya saka Khalipha samun waje ya zauna danta gama ta gumtsa masa. Tana kuwa ajiye wayar ta ɗaga hannu sama tana ambaton Alhmdllh. 

    Katseta yayi da faɗin, “Niko Granny taƙaita addu'ar nan ki faɗamin minene?”.

     Hannu ta sauke tana masa daƙuwa. Sai kuma ta ƙara washe baki da gyara zama. “Burina ne ya cika Abdul-Mutallab ƙarami, ALLAH ya tabbatar da tarkon dana ɗana. Na kuma daɗe ina mafarki da addu'a. Bazan ɓoye makaba yau dama saboda Moddibo nasa aka bani Zinneerah. Dan nasan duk daren daɗewa zaizo ya ganta, ko yasota ko karya sota dama na tanadar masa itane. Sai kuma cikin hukuncin ALLAH ga wani sarƙi ya ɓilla a tsakani........ (tsaf ta kwashe masa labari ta bashi). 

        Zuciyarsa ce ta shiga tsitstsinkewa, yay saurin yin ƙoƙarin dai-daita yanayin nasa yana haɗiye abinda ke neman toshe fitar numfashinsa. Cikin murmushi da ƴar dariyar yaƙe yace, “Kai kai kai Alhmdllh da wannan daddaɗar labari Granny. Wlhy wannan haɗi yayi kuwa, dan sun dace matuƙa, sannan hakan da baffa yayi shine maganin Aunty Farah da Mammah. Sai dai kuma abinda ya bani mamaki da al'ajabi wai little jinin Yayanmu ne. kainafa ya kulle”.

       “Nima nawan a kulle yake Khalipha, amma dai ni yanzu burina jin ta bakin Inno, tunda dai ai ba'a shan ciki a ruwa ko? Sannan kuma babu ta wata hanyar da mace zata samu ciki sai da namiji, dan haka dan ubansu zasuma faɗi yanda akayine su dukansu”.

        Ɗan jimm Khalipha yay yana wani nazari saboda maganar hajiya iya, yace, “Eh hakane Granny, amma dai yanzu akwai wasu hanyoyin da mace kan iya samun ciki koda babu alaƙar namiji a tsakaninsu”.

     Cikin sauri hajiya iya tace, “Kai Khalipha kaji tsoron ALLAH ta wace hanyace kuwa? Ni dai ban taɓa jiba gaskiya”.

     Murmushi Khalipha yayi, cike da rashin damuwa ko tunaninsa kaiwa nan ɗin da wata manufa yace, “Granny karki manta nifa Doctor ne. Doctor ɗinma dakeda alaƙa da matsaloli irin na mata. Akwai hanyoyi da dama kamar su yin dashen ciki da makamantansu”.

       “Kamarya dashen ciki?”.

Dariya yayi yana miƙewa. “Oh oh Granny wannan ai bayanine mai zaman kansa. Amma dai ki sani yanzu ana iya dasama mace ciki ta haihu wlhy”.

       Baki hajiya iya ta taɓe da faɗin, “Ah kudai da shegen ƙaƙale-ƙaƙalenku na likitoci dalilin yin karatu cikin masu jajayen kunnuwa ba. Mudai ko anayin wannan sheɗancin baije manaba kaji, danni wannan ai badan karna yanke hukunciba sai nace kamar wuce wuri ne”.

          “Tab Granny wlhy mutanenmu ma sunayi, duk da dai gaskiya turawa sukafiyi, amma yanzu kinga kamar a kudancin ƙasarmu sosai sukeyi, wasuma sana'a suka maidashi wlhy. A dasa musu cikin idan lokacin haihuwarsa yayi su haifa suba masu cikin ɗansu. ALLAH dai ya ƙyauta, dan wasu tsiraru a mutanenmu ma sun tsunduma wannan harkar sosai musamman ƴan gayun mata da basa son wahala, sai su bada a ɗaukar musu cikin idan ya isa haihuwa a haifa a basu abinsu. Wasuma a asibitin ake ajiye musu ba jikin kowaba. Idan ya isa haihuwa a ciresa a basu”.

       “Kai wannan masifa dami tai kama. A lallai wannan duniya tazo ƙarahe kuwa”.

     “Sosai ma” Khalipha ya faɗa yana ƙoƙarin ficewa dan bayaso halin da yake ciki yakai ga bayyana a fuskarsa har Hajiya iya ta fahimta.

      A falo ya wuce su Zinneerah dake kallo, yanda ya wuce ko kallonsu baiyiba yasa Jamal cewa, “Tofa, inaga Granny da Yah Khalipha anɗan dambacebe naga kamar ya wuce a fusace”.

       Dariya su Meenal sukayi. Zinneerah ko tayi kamar bata jiba dan tun ɗazun gabanta ke wani irin faduwa. zuciyarya na mata rauni kamar maijin tsoron faruwar wani abu a gareta. Sai dai ta daure bata sanarma kowaba tanata addu'a a zuciyarta. Dan kallonma yinsa kawai take ba fahimta takeba sam.


       Duk wannn abu dake faruwa Farah na ɗakinta cike da damuwa. Dan tunda taji AK ya tafi Nigeria zuciyarya bata samu nutsuwaba. Wannan dalilin ya sata kiran Aunty Zakiyya ta sanar mata, ta kuma turama Mammah text message. Aunty Zakiyya ce ta kira Mammah suka tattauna, duk da ba'a kano takeba Mammah ta bata damar sakawa a mata binciken zancen yaron.

      Daga haka ta kira baffa a gadarance tana tabbatar masa bai isa rabata da AK ba. Idan ma wani abu yake ƙullawa sunyi ta banza, dan ko aure suka saka AK yayi har aka samu wannan yaron ya tabbatar sai AK ya saki koma ƴar uban wacece. taji zafin maganganun da Baffah ya yaɓa mata, dan haka ta yanke shawarar Aunty Zakiyya na gama mata bincike zata tafi Nigeria ɗin da kanta, shiyyasa ta kira Farah ta kwantar mata da hankali da mata nasiha akan karta sake shiga harkar kowa a gidan harsu gama bincikensu.

     To wannan nasiha ta Mammah tasa Aunty Farah nutsuwa waje guda ita a dole ta kama kanta.😹. Suma dai su Hajiya iya daba sanin miya faru sukaiba babu wanda ya shiga harkar tata. Dan yanda bata nema ganin kowaba tun bayan tafiyar mijinta, suma sai basu nemetaba. Dan a matsayinta na matar gida ita keda haƙƙin bin yanda suka tashi ko sukaci suka sha a gidan. Amma bata taba yiba tayaya suma zasu takura kansu ne akan damuwa da al'amarinta. Gara su rike mutuncinsu ko za'a zauna lafiya.


      Su Zinneerah kam koda suka fahimci ɗunbin farin cikin da hajiya iya ke a ciki suka tambayeta catai babu komai. dan sunyi magana da Baffah akan zasubar zancen kar Zinneerah ta sani har sai sun dawo Nigeria saboda sheɗancin su Mammah. Baffah yace yana tsoron su sani subi ta wata hanyar su cutar da yarinyar mutane a ƙasar da batasan kantaba. Amma tunda nan da sati biyu zasu koma ayi haƙurin hakan kawai dan za'a haɗe bikinne da nasu Ni'ima. Hajiya iya kuwa ta gamsu da wannan shwarar ɗari bisa ɗari. Dan haka bayan Khalipha tai gum da bakinta...........✍


No comments

Powered by Blogger.