Makauniyar Kaddara 41

 


Page 41*


............Tun farkon fara ƙulla auren da yaji sunansa a ciki yay mutuwar zaune, bai dawo hayyasa ba sai da sanƙira ya ƙara tabbatarwa da babbar murya. A hankali AK ya lumshe idanunsa dake ɗauke da nauye-nauye kala-kala a cikinsu yana sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya. 

      Haɗa ido sukai da Baffah dake masa kallon nazari, kansa ya maida ƙasa yana ƙoƙarin danne ɓoyayyan al'amarin dake neman bayyana kansa a saman fuskarsa. Shima Baffa sai kawai ya ɗauke kansa zuciyarsa na masa wasiwasi.

        Koda aka mimmƙe domin fita a masallacin da ƙyar Saifudden ya iya kama Moos'ab da yay suman zaune, dan tun farkon fara ƙulla auren da yaji an ambaci Yayan nasu sai da gabansa ya faɗi, jin zancen sanƙira kuwa tamkar saukar guduma ne a bisa tsakkiyar kansa. Gefe Saifudden ya maida shi tare bashi ruwa dan yasha. Babu musu Moos'ab dake hawaye kamar wani mace ya amsa ya sha ruwan yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. 

      “Wannan shine abinda na gudar maka tun farko Moos'ab, shiyyasa nace ka bayyanama Zinneerah kana sonta, ka kuma sanarma Baffah da Granny amma kaƙi wai saita gama secondary school, gashi nan to shi Yayanmu yayi wuff da ita”.

     Murmushi mai ciwo Moos'ab yayi, cikin raunin murya yace, “Saifudden ALLAH ya ƙaddara dama shine mijinta, kuma ni wlhy na haƙura na bar masa har abada. Yayanmu yanada daraja da mutuncin da zamu iya sadaukar masa da komai, komai muhimmancin abinnan kuwa. Dan shima yayi mana abubuwa masu ɗunbin yawa da bazasu ƙirguba. Sannan nasan Zinneerah zata samu dukan farin ciki daga garesa insha ALLAH. Kuma anyi maganin wannan mahaukaciyar matar tasa da kishi ya maida zararriya, wlhy kodan kiran dataimin jiya da dare wai saina faɗa mata uwar little yasa naji daɗin ƙulla wannan auren, tunda tana kukan targaɗe ga karayanan ta samu, sai tai zaman jinya kuma”.

      Rungumesa Saifudden yayi yana share ƙwalla shima. Ya ɗagosa yana share masa hawaye da faɗin, “Naji daɗin kalamanka Moos'ab, hakan kuma ya tabbatar min yaƙin da Granny da Baffa keyi akan sanin darajar zumincinmu ba abanza sukeyiba. Tabbas Yayanmu ya cancanci sadaukarwar da tafi haka ma, inaji a jikina kuma maganar shekaran jiyace ta kawo wannan ƙulla auren, amma tabbas sun dace wlhy”.

      “Tabbas na yarda da zancenka Saifu. Da alama hauka tai musu na haƙiƙa shiyyasa Yayanmu da Baffah suka yanke wannan hukuncin, na taya Yayanmu murnar samun nutsatstsiyar yarinya mai kunya da tarbiyya ga haƙuri, sannan itama na tayata murnar samun gwarzon namiji mai haƙuri da mutunci, uwa uba ya tara qualities masu yawa da duk mace take buƙata ga mijin aure, duk da nasan akwai ta inda shima yake da rauni kodan kasancewarsa ɗan adam kamar kowa. ALLAH ya basu zaman lafiya, yasa ta zama sanadin farin cikinsa da kwaranyewar hawayensa akan rashin haihuwa”.

     “Amin ya rabbi” Saifudden ya faɗa yana sake rungumesa.

     A hankali AK dake a bayansu basu saniba ya ɗanja da baya yana lumshe idanu, tun sanda Saifudden ya kamo Moos'ab suka fito ya biyosu, dan ya jima yana zargin akwai wani abu tsakanin Moos'ab da yarinyar, ashe kuwa da gaskene. Hannu yakai bisa sajensa ya ɗan shafa, kafin ya bar wajen batare da ya bari sun gansaba.

      Moos'ab ne ya farga da ƙamshin turarensa. Yaɗan janye Saifudden yana faɗin, “Bro ƙamshin turaren Yayanmu fa kamar nakeji”.

    Saurin ja baya Saifudden yayi shima yana waige-waige, sai dai basuga kowaba a wajen, “Inaga hancin kane kawai, kaga zomuje karma a nememu”.


      Koda AK yabar wajensu nufar inda su Dr Mahmud suke yayi, inda ya samu wani maroƙi yanata zabgama masa kirari duk zatonsa shine angon. Yana ganin AK ya iso ko yay saurin kamo hannunsa da nuna musu shi, “Yauwa to ga angon nan bayin ALLAH”. Ya faɗa yana ciro kuɗi ya miƙa musu yana tura AK gabansu yana dariya.

       Idanu sosai AK ya waro waje ganin sun zagayesa suna masa ihu akai, ai gudun hayaniyar tasu ya sashi babu shiri ciro kuɗi ya miƙa musu yana harar Dr Mahmud daya koma gefe yana kwasar dariyar mugunta, su Mas'ood na tayashi ƙasa-ƙasa.

          Jama'ar gari kuwa ganin ango yasa suketa sake tofa albarkacin bakinsu. Wasu suce ita cikin shege ya mata riba, wasu suce koma shine abokin tsiyar tata, wasu su tayata murna, wasu suce sakkayar ALLAH ce ga zalincin da Inna tai mata, wasu suce baisan ta taɓa yin cikiba ƙila data bar garin ta zubar ne. Wasu ko hassadace kawai, kasancewar sunso zinneerah ɗin basu samuba. Magana dai iri-iri. Har takai wani ya samu AK gefe yana masa gulmar wai kuwa yasan waya aura?.

       AK dake jingine jikin mota yana latsa waya ya ɗago ya dubi mutumin ƴar walwalar fuskarsa na ɓacewa ɓat. Amma duk da haka mutumin nan sai yay ƙasa da kai yana wani soshe-soshe. “Ayi haƙuri Alhaji, ganinka mutum mai tarin kamala da mutunci yasa naji bara na faɗa maka gaskiya, dan na tabbatar an rufekane akan yarinyarnan. Duk da kafin faruwar komai kowa yasan yarinyar kirki ce a garin nan dan har kwatance akema yara akanta. Amma daga ƙarshe ta ɓata rawarta da taalle. Dan kuwa cikin shege tayi, Katsina tabi saurayi sukayo kusan mako biyar sannan suka dawo, a dalilin cikinne ma ta gudu a ƙauyen nan babu wanda ya sake jin labarinta sai yau da kukazo wai aurenta. Nifa k........”

     Wani shegen kallo da AK ya dasa masa dai-dai ya ɗago ya sashi saurin haɗiye sauran zancen yana zazzare ido. AK ya gyara tsaiwarsa idanunsa na canja launin ɓacin rai, cikin nutsuwarsa da rashin sakewa yace, “To dakazo kana faɗamin idan kuma nine nayi cikin fa?”.

     A razane mutumin ya waro idanu waje. Sai kuma yay saurin yin ƙasa da kansa yana girgizawa. “Haba-haba Alhaji ni nasan hakanma bazata faruba. Ai daga ganinka anga mutum mai mutunci da kamun kai, kawai dai an rufekane, amma dan ALLAH karka bari so ya rufe maka ido ka ɗaukama ƴaƴanka uwar banza”.

      “Ai kaine banzan sha-sha-sha” AK ya faɗa a fusace, cikin kaushin murya yace, “Mutumin banza kawai, saboda tsabar rashin mutunci ko kunya bakajiba kai kazo kana aibantamin mata? To bara na sanar maka kaima kaje ka sanar tunda naga shine aikinka. Shi wannan cikin da kuka ganta dashi nawane. Nine nai mata kuma ta haifamin, daɗin hakannema yasa na aureta yanzu stupid ɓacemin anan”.

     Da sauri mutum yabar wajen kuwa tamkar zai kifa, AK ya rakashi da wani irin kallon tsana da takaici, tsabar takaici dole ya buɗe motar da yake a jingine ya shiga batare daya rufe murfinba ƙafafunsa a waje. Sosai launin idanunsa suka sake canjawa, badan kar ace yayi ƙarantaba da lallai saiya nunama shegen mutumin nan kuskurensa yau wlhy. Tsaki yaja da dafe kansa dahar ya fara masa ciwo ƙasa-ƙasa zuciyarsa na masa zugi. Tabbas yanada buƙatar dawowa ƙauyen nan domin wanke yarinyarnan duk da har yanzu baisan yaya ya samar da Abdul-Mutallab ba.....

         “Yayanmu!” Moos'ab ya sake kiran sunansa a karo na uku.

     Sai yanzu kunnensa ya ji, ɗago idanunsa yay ya dubesa, Moos'ab yay ƙasa da kansa cikin girmamawa yace, “Baffah ke kiranka”.

     Komai baicema Moos'ab ɗinba ya fito a motar ya nufi cikin zauren maigari inda su Baffah suke tattaunawa da Baba akan abinda suka sani game da ƙaddarar data afkama Zinneerah da har yau basusan mafarintaba.

     Waje ya samu ya zauna yana ƙoƙarin ɓoye ɓacin rai da takaicin da mutumin can ya cusa masa. Cikin girmamawa ya sake gaida su Baba dan yanzu dai a matsayin suruki yake. Sosai baba yaji daɗin wannan girmamawa. yakumaji a ransa AK ya kwanta masa, yana taya ƴarsa murna dajin insha ALLAH ta samu mijin marainiya.

      A nutse baba ya sake maimaita masa bayanin da yayma su Baffah game da Zinneerah, sannan a ƙarshe ya roƙesa alfarmar dawowar Zinneerah danya domin shirya mata biki nanda wata ɗaya. 

    Ɗan murmushi AK yayi kansa a sunkuye yace, “Baba karka damu, duk yanda kukaso muyi mu masu biyayyane a gareku, sai dai kayi haƙuri a yanzu bata ƙasar tana can London, insha ALLAH nan da sati biyu zata dawo”.

      Cikin ɗan waro ido Kawu Rabilu yace, “Landan kuma? Ita Zinni ɗin?”.

      Sosai yanda Kawu Rabilu yayi ya basu Saifudden dariya. duk sukai ƙasa dakai suna gumtse bakuna. Baffah ne ya amsama kawu Rabilu da cewar, “Eh suna can gidansa tare da mahaifiyata da taje ganin likita. Amma kamar yanda ya faɗa insha ALLAH nanda sati biyu zasu dawo, kuma insha ALLAH suna dawowa zata dawo nan ɗin itama a ɗauketa kamar kowace ƴa a kaita gidan aurenta”.

      Jinjina kawuna suka shigayi na gamsuwa. Yayinda bakin Baba da nasu Kawu ya kasa rufuwa. Kasancewar yamma tayi sukai haramar tafiya. Naman zabi da basuciba haka maigari yasa aka saka musu a mota hardasu tsarabar mangwaro, gwaba, kashu da nono da ƙwan zabbi. dan su Baba suma sai gasu da nasu tsarabar harda Gwaggo Laritu da labari ya kaima ta bakin ƴaƴanta.

     Lokacin da zasu wuce haka jama'a suka zagaye motocinsu anata ɗaga musu hannu. Sosai su Baffah sukaji daɗin wannan karamci, dan haka suka tafi zukatansu fes kowa na ALLAH ya sanya alkairi.


★★★


      Tun kafin Baba ya shigo gida labari ya samu su Inna. Zaune ta tashi dangangan kamar ba itace kwance kashirɓan tana kukan ciwo da ɗan nishi ba. Cikin masifa take cema mai kawo labarin, “Kukam dai annamimanci bai muku kaɗan abaki Sahware. In banda shegen munahinci yaushe kikaga wata Zinni da har za'a ɗaurama aure. Dalla hice mani agida kahin nai miki bankaɗa wlhy”.

        Baki Safare ta taɓe tana faɗin, “To oho ni dai Asabe. Koki yarda ko karki yarda yanzu na wuto ana ɗaura auren Zinni a masallacin juma'a. Banga dalilin da zaisa nazo na hiɗi abinda bashike nanba”.

      “Kai kedai Sahwar ALLAH ya tsine maki albarka bankaɗaɗɗiyar mata watsatstsiya. Ki hitamin a gida wlhy kona nafka maki shegen duka naga mai ƙwatarki”.

    Fita Safare tayi tana wata shegiyar dariya. Ana haka kuwa sai ga Tinene ta shigo gidan a guje tana hakki.

     “Ke kuma lahiya kika shigoma mutane kamar wata korarra?”.

    Yaya Gajeje ta faɗa dan shigowarta kenan gidan ko zancen Safare batajiba.

     Cikin hakki Tinene ta dafe kanta dake mata ciwo dan dama sayan paracetamol ta fita yi, tace, “Inafa lahiya Yaya Gajeje. wlhy wani labari najiyo yanzun. ga baba can a babban massallaci an ɗaura auren Zinni da wasu mutane manyan ƴan gayu al-qur'an”.

      Tsit gidan yayi na wucin gadi, sai da Sa'a tace, “Inna anya kuwa maganarnan bada gaske bane? Bara dai na hita nima na jiyo mana”.

      Yaya gajeje da sai yanzu taji abinda ke faruwa cike da zumuɗi tace, “Jeki jeki maza Sa'a. Kai ALLAH ya tabbatar da wannan zance da nayi hwarin ciki mara misali wlhy”.

      Amaryar Baba da duk ke saurarensu tun ɗazun bata tsoma bakiba ta kalli Yaya Gajeje da cewa, “Wacece wai ita Zinni ɗin?”.

     Kai tsaye Yaya Gajeje dake murmushi tace, “Ƙanwarmuce itama mama........”

      A fusace Inna ta zaburo tana watsama Yaya Gajeje harara, “Ƙanwarku a gidan ubanwa. Gajeje ki kiyayeni. Ke kuma munahika da kike tambaya bara a faɗa miki, itana ƴar kishiyace da zaman gidan nan ya gagareta kamar yanda kema zai gagareki. Dan wlhy na ɗau alwashin yanda na watseta kema saina watseki a gidan nan dama garin nan baki ɗaya”.

     Murmushi amarya tayi tana ɗauke kanta batare datacema Inna komai ba. Hakan kuwa ba ƙaramin harzuƙa zuciyar Inna yayiba. Ta miƙe dingangan kamar ba ita ke ciwo ba tahau zazzaga bala'i tana zagin amarya da mmn sadiq da Zinneerah. A wannan bala'in baba ya shigo shi dasu kawu da yara ɗauke da kayan sweets dasu biscuits da huhunan goro cikin gidan. Suna shigowa Gwaggo Laritu ma na shigowa.........


★★★★


         A ɓangaren su Baffah kam tunda suka bar Danya kowa ke tattauna karamcin da akai musu da abokin tafiyarsa. Motar su AK ce kawai ta kasance shiru dan tunda suka tafi ya jingina kansa da kujera ya lumshe idanu yana tariyo maganar mutumin nan ma ɗazu daki-daki cikin ransa. Lokaci-lokaci Dr Mahmud kan kallesa yayi murmushi. Sai da suka kusa shiga cikin kano ne ya ɗan sake dubansa da tsokana, “Haba ango duk daɗine ya saka zama kurman ƙarfi da yaji?”.

     Shiru AK bai motsaba, sai da ya mula dan kansa ya ɗan buɗe ido ya harari Dr Mahmud ɗin, cikin rashin sakewarsa yace, “Dama haka kake da sa ido?”.

       Dariya sosai ta kama Dr Mahmud har yana dukan sitiyari. Hakan ya saka AK ɗan sakin murmushi ya maida kansa ya sake kwantarwa da lumshe idanu. daga nan bai ƙara tankawa Dr Mahmud ɗinba daya cigaba da tsokanarsa har suka isa gida.


     Sun iso suka iske hajiya Bilkisu da suke kira da Mommy ta iso tare da babban ɗanta Huzaifa. Huzaifa kusan sa'an AK ne, sai dai AK ya girmesa da kusan shekara biyu, amma ayanzu abokaine, dan saima suna tsokanar junane zaka iya sanin AK ɗin ya girmi Huzaifa. 

        Dr Mahmud na ajiyesa bai shigaba ya juya gida danya huta shima. Hakan yasa AK nufar sashen Hajiya Iya shi kaɗai, su Haneef kuwa duk sashen iyayensu sukai kai rahoton ɗaurin aure. Hakama Baffah ɗokin jin zuwan ƴar uwarsa yasashi nufar sashen nasa kai tsaye dan tanacan, tunda bada yara tazo ba duka bazata sauka a nata sashen ba.

     Tunda AK ya shigo yaga Huzaifa zaune a falon Hajiya iya yanacin abinci sai ya ɓata rai cikin ɗan wasan da suka saba yace, “Oh oh yaushe wannan bawan yazo mana gida”  ya faɗa yana harar Huzaifa.

    Dariya Huzaifa ya fashe da ita, saida yayi mai isarsa ya haɗe fuska yana harar AK ɗin shima. “Eh lallai ka nunamin kayi aure na biyu, ninema Bawan naka? Yaro jeka bincika ni dakai wanene bawa?”.

     Hannu AK yasa ya tallare ƙeyar Huzaifan. Yay gaba da sauri yana faɗin, “Magananne jeka bincika kaidai”. Ya faɗa yana shigewa ɗakinsa murmushi ɗauke akan fuskarsa. Dan inhar yana tare da Huzaifa kobaiyi niyyar fara'a ba sai ya sakashi yinta dole saboda shi mutumne mai barkwanci dason wasa.

       Cikin ihu Huzaifa yace, “Jeka fito ka sameni mijin mata biyu, indai maganace kuwa ka haɗu da ita yau ko barci bazan barka kayiba”.

     AK na jiyosa daga ɗakin, dan haka ya girgiza kansa kawai yana murmushi. Kayan jikinsa ya cire ya nufi toilet dan watsa ruwa a gaggauce lokacin sallar magrib karya ƙure masa.


★★

         Abba kam koda ya isa gida da albishir ɗin ɗaura auren Zinneerah da AK ga Mmn sadiq sai kawai ta fashe da kuka dan farin ciki, Abba dake mata dariya ya rungumeta yana lallashi.

     “Tabbas mutanen nan sun cancanci yabo Hauwa'u. Dan halayyarsu na mana nuni da cewar har yanzu akwai mutanen ƙwari masu mutunci da sanin yakamata a cikin masu arziƙi bakamar yanda mu mutane muke zargiba. Inda ace ana samu mutane irinsu Alhaji Kabeer Shira koda a talakawanma wlhy da duniya ta zauna lafiya. Amma yanzu zakiga kowa ɗansa kawai da mutuncinsa yake karewa. Babu ruwansa dabin gaskiya koda ace yana ganinta ƙuru-ƙuru kuwa. Sau da yawa akan ɓata tarbiyyar yarinya amma kiji iyayen yaron na amabaton ɗansu bazai auri lalatacciya ba. Bayan kuma bata lalaceba sai da taimakon ɗan nasu. Tare suka aikatafa, amma sai a nuna tsangwamar macen fiye dashi namijin dan son zuciya. Bayan kuma shi namijin yafi macen hankali, ko ya girmeta, maybe ma shine yay amfani da wayonmu na maza ya lalata mata rayuwar tata. Hakan zaluncine dason zukata muke aikatawa wajen ƙasƙantar da mace akan zunubi koda kuwa tare ta aikatashi da abokin halittarta namiji.”

         Hawaye mmn sadiq ta share tana duban mijin nata, “Yaya ai mutanen duniya haka suke tun na ƙarnin farko, suna amfani da raunin ɗiya mace akoda yaushe wajen sake raunanata, sun mance a ɓangaren zunubi da hukunci duk iri ɗaya UBANGIJI zai mana ga duk wanda ya saɓa masa. Wlhy bammasan yanda zan musalta maka daraja da kima ta mutanen nanba a zuciya ta, sukam waɗanne irin mutanene haka masu tarin adalci da sanin darajar ɗan adam?”.

        Cikin dariyar farin ciki Abba yace, “Tabbas sun cika ƴan baiwa, dan samun irinsu a cikin al'ummarmu sai an tona. Amma akwaisufa. Yawaitar masu son zuciyarne ya lulluɓe irinsu saboda ƙarancinsu a cikin mutane. ALLAH ya bamu ikon koyi dasu”.

      “Amin” mmn sadiq ta faɗa wani irin sanyi da nutsuwa na saukar mata lokaci guda.

      Abba yace, “Yauwa inaga ki shirya Abdul-Mutallab zasu aiko a ɗaukesa daga can gidan wai ƙanwar Alhaji Kabeer ɗince zatazo daga Lagos yau, itama za'a kaimata shi ta gansa”.

      Kai mmn sadiq ta jinjina masa tana faɗin, “To bara ka gani naje na tadashi a barci can kuwa sai nai masa wanka basai sunzo sunyi zaman jiraba”.

     Cikin gamsuwa da bayaninta ya kaɗa mata kai..........✍



_Kuyi manage da wannan an mana rasuwane ban samu zaman nustuwar typing ba😊🙏🏻_.



*_A page na ƙarshe na ranar Friday akwai inda nai kuskure, hakan ta farune dalilin rashin yin editin ranar, nayi typing na gaji. Inda nasa AK yayi limancin sallar zuhur nayi maganar yayi karatun salla har mutane na ambaton anyi baƙon balaraben limami. Please amin afuwa. Wannan ajizancine na ɗan adam sai daga baya na farga dalilin maganar da wata tayi na sake komawa na duba page ɗin. Ina ƙara bada haƙuri Please, mantuwa ce da rashin editin kamar yanda na faɗa tun farko😊🙏🏻_*


*Barkanmu da dawowa hutun weekend😍😍😘😘😘💃🏻*


*_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*


Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.


No comments

Powered by Blogger.