Makauniyar Kaddara 4

 


Page 4


...............Ƙarfe kusan biyu na rana Zinneerah ta dawo gidan a gajiye. Duk uban riɗi da gyadan data fita da shi kaɗanne ya rage a botikin. Tun a sallamar farko na shigowa gidan dukkanin ɗan guntun farin cikinta ya gushe. Ba komai ya kawo hakanba kuwa sai cin karo da Yaya Kareema datai, wadda ta dawo daga Rimaye wajen yayarsu ta biyu dake bima yaya Gajeje dan ita acan take aure.

 

      Zaune suke a ƙarƙashin bishiyar tsakar gidan nasu sun baje kaya ita da Sa'a da Tinene. Inna na daga bakin murhu tana talgen tuwon dare. Dariyarsu suke sha cike da nishaɗi dajin daɗi.

     Sa'a ce kawai ta amsa sallamar Zinneerah tare da mata sannu. Ta amsa a ɗarare tana duban Karima data haɗe girar sama data ƙasa. “Yaya Karima ashe kin dawo, sannu da zuwa, yaya kika baro su Yaya Atinen?”.

        “To uwar iya, halan kin aikenine da kike lissaho mani wannan tambayoyin? Kai wagga ɗiya hi'ilinki yayi yawa wallahi, k.......”

        “Haba Yaya Karima, minene laihinta anan kuma? Danta maki barka da dawowa da tambayar su Yaya Atine?”. Sa'a ta faɗa cikin katse ƴar uwar tata rai ɓace.

     A fusace itama karimar ta katseta da fadin, “To kema waya saki a ciki, ALLAH ina ci maki uwa yanzun nan Sa'a. Ita ɗin uwarki ce ko mi?”.

       “Ba uwata bace, amma ƴar uwatace kamar yanda take ƴar uwarku kema. Daga hiɗin gaskiya sai laihi. Ni banga abinda Zinni ta tarema wani a gidan nanba da kuke tsangwama mata, itama fa ɗiyace kamar yanda muke ɗiyan gidan. Duk da baba baya magana akan abinda ake mata na tabbatar yanajin ciwo a rans........”

          Timmm!! Kake jin saukar dundu a bayan Sa'a. Ta gyantsare saboda azabar zafi tana sosawa. Inna dake tsaye a kanta tana huci tace, “Kaɗanma nai miki dan ubanki. Wa kike hiɗima waɗanan maganar banzar to? Sheɗaniya munahika. Anya kuwa nice uwarki Sa'a? Kodai kema Hauwar ce ta haiheki taimin mucanje ban saniba?”.

         Baki cike da iska Sa'a tace, “Amma inna dan na hiɗi gaskiya sai kimin wannan uban ƙullin a baya?”.

       “Kaɗanma nai miki shegiya ƴal bura'uba bai baki kamar na reza, hita kibar gidan nan kona sauya miki wannan shegiyar huskar da maruka”.

      Fita Sa'a tai tana ƙunƙuni da cigaba da shafa bayanta inda yasha dundun.

     Sum-sum Zinneerah ta wuce ɗakin Inna zata kai botikin tallar tata Karima ta daka mata tsawa. “Munahika dawo a lissahwa sannan”.

       Dawowa Zinneerah tayi jikinta na rawa ta  mikama Karima kuɗin da botikin. Fisgar botikin Tinene tayi, Karima kuma kuɗin ta ƙwata tana buge mata hannu.

      “Innarmu na nawa kika aza mata?”.

    Karima ta faɗa tana fara irga kuɗin.

           Daga inda Inna take ta bata amsa da, “Na jikka sha huɗu ne cir gaba daya, dan na rantse da ALLAH kona hicika ya ɓata ina miki ɓatanci da shegen bugu a gidan nan. Kuma sai ubanki ya biyani kuɗina babu ɗagin ƙahwa”.

     Zinneerah dai batace komaiba. Sai su Tinene ne suka kwashe da dariya. Karima ta gama irga kuɗin tana jijjigasu da faɗin, “ALLAH ya sota Inna sun cika. Kuɗin anan jikka goma sha ɗaya da murtala uku, sai kayan daya rage na jikka uku ba murtala uku”.

      “Ta taimaki kanta. Ga tuwo can kije ki ci idan kina so, dan nasan dai abokan iskancinki sun gama cika maki ciki da shinkahwar tasha”.

      “To” kawai Zinneerah ta ce ta nufi hanyar ɗakinsu. Dan wani irin jiri takeji yana neman kwasarta. Tana shiga ɗakinsu ta zube a katifar su Tinene tana sauke numfashi. A hankali barci ya fara rinjayar idanunta mai daɗi. 

       “Baƙo na sallama da Zinneerah a waje”.

     Ta tsinkayo muryar yaro sama-sama da ga tsakar gida. Tsawar da inna ta dakama yaron ce ta sakata buɗe idanunta gaba ɗaya babu shiri. Sai kuma ta jiyo Sa'a na faɗin,

         “Inna bafa wani bane ba, malam badamasi ne malaminsu”.

     Tsaki Inna taja batare data tankaba. Yayinda Sa'a ta ɗaga labulen ɗakin tana kiran sunanta. “Zinni ki tashi ga Malam Bade yazo nemanki”.

      Yinƙurawa tai ta tashi zaune tana gyara hijjab ɗin jikinta. Cikin sanyinta dana barcin data fara tace, “To Yaya Sa'a”. Daga haka ta miƙe ta fiti cike da dauriya.

    

        Matashin saurayine, dan gaba ɗaya shekarun nasa bazasu wuce talatin da ɗoriya ba. Zinneerah data fito a ɗarare saboda tsoron Inna ta rissina tana murmushi. “Sannu da zuwa malam. Ina yini?”.

     Shima tashi fuskar faɗaɗe da murmushi ya amsa yana kallonta. “Zinneerah Sulaiman ashe kin dawo gida babu labari? Sai ɗazu ina bisa mashin na hangeki da botikin gyaɗa da riɗi a bakin yara”.

      Har yanzu tana a duƙe kai a ƙasa tana murmushi, cikin ƴar muryarta tace, “Na dawo Malam, dama naje wajen mamana ne gaisheta”.

       Yanzu kam da mamaki yake dubanta. Cikin kasa haɗiye abinda ke a ransa yace, “Amma a gari aketa hiɗin guduwa kikai bama asan ina kika nuhwaba? Kai mutane sai dai a barsu da halinsu. ALLAH ya ƙyauta to, kin baro maman naki lahiya ko?”.

       “Lahiya lau suke Malam”.

“To Alhmdllh, Yanzu ni bama wannan ba, nazone dama akan jarabawarku ta jsce. Ina hwata dai baki manta nanda kwanaki takwas zaku hwara ba ko?”.

      Karan farko ta ɗago taɗan kallesa ta sake maida kanta ƙasa. Kafin tace wani abu Inna ta banko ƙyauran langa-langar ƙofar gidan nasu ta fito.

            “Uhyimm! Kaji farkar taka ta dawo kazo kenan? To billahillazi bari kaji yanzu bazan ɗauki wannan sheɗancinba. Kaji da ƙyau karna sake ganinka ƙohwar gidan nan. Idan son ganinta kake ta bika can mahaɗar taku man......”

      “K dalla malama saurara, tsohuwar banza da bakinta bai hiɗin alkairi sai sheri wa ɗiyan mutane. Na rantse da ALLAH kika ƙara hiɗin wani kalmar ɓatanci garemu yau sai kin kwana ofishin ƴan sanda. Ni nazo ne akan maganar jarabawa da zasu yi ta koma makaranta....”

        “Anƙi ta koma ɗin munahiki algungumi. Dama can niya nai na barta take zuwa. da ga yau da ga yanzu kuma na hwasa. Bata sake zuwa talla zataimani”.

      “Ashe kuwa zaki gurfana gaban mai-gari......”

       “Kaini gaban sarkin katsina ma ƙarewar mai-gari mana. Ke kuma munahika dan ubanki tashi ki shige ciki, ƴal bura'uban yarinya kulin bata iya komaiba sai janyoma mutane jidali da yaye-yaye a ƙwar gida. Zanyi maganin rawar kanki ne ai...”

       Yanda ta kaima Zinneerah duka ya sata miƙewa da gudu ta shige gidan. Shima Malam Badamasi bai sake tanka mataba ya bar ƙofar gidan rai ɓace. Inna kuwa masifa ta cigaba da zazzagawa har sai da Sa'a da Karima suka fito suka shiga da ita gida.

     Tana shiga ta hau dukan Zinneerah babu ji babu gani. Sai da tai mata lilis ta barta kwance tana numfashi da ƙyar. Zinneerah akwai taurin zuciyar tsiya da kafiya wani lokacin. Duk wahalar da take sha wajen Inna akan jima ba'aga kukanta ba idan ba ita taso ba. Idan kuwa kaga ta cika yawan kuka to lallai abin ya kai babba gareta sosai.


      Inna na tsaka da cigaba da jarabarta aka buga sallama. Sa'a ce ta amsa tare da nufar zauren gidan nasu dan taga wanene. (Sanƙira) mai shela idan abu ya faru a garinne tsaye yana baza babbar riga. Ta rissina tana gaidashi dan dattijo ne sosai, amma Baba zai iya girmarsa. 

     “Tsohuwar taki na nan ko?”.

“Eh baba tana nan”.

“To maza sanar mata mai-gari na biɗar ganinta. inko bata zuwa cikin salama ƴan doka zasuzo su kaita da kansu. Tazo tare da ƴar uwarki zinneerah”.

      Sosai gaban Sa'a ya faɗi, amma ta daure cikin girmamawa ta amsa masa tare da juyawa cikin gidan. 

       Inna ta dubi Sa'a cikin haushin Zinneerah da bai gama sakintaba tace, “Ke kuma minene kika shigo ma mutane haka? Halan shegen nanne bai tahi ba?”.

     Kan Sa'a a ƙasa tace, “A'a Inna. Baba Lado sanƙira ne fa, wai ana kiranki gidan mai-gari ke da Zinni....”

       “Ki koma ki hiɗi masa ba'a zuwa. Ba'a kamar ana zuwa ɗin...”

    “Inna wlhy cayay fa idan baki zuwa ƴan sanda zasuzo su tahi da ke”.

       Shiru Innar tayi ƙirjinta na bugawa. Ta tsani harkar ƴan sanda, dan tun sanda sukai faɗa da Lamunde aka adashi ta kaita kusada ofishin ƴan sanda akazo har gida aka kamata sai da tai kwana biyu a kusada hannunsu take shakkarsu. Ba ƙaramin wuya taciyo a kwana biyun datai wajensu ba. Amma a fili sai ta ƙyaɓe baki zata fara masifa kuma.......

       “Shin wai Asabe saƙon mai-gari bai iso gareki bane?”.

    Karaɗin Sanƙira daga ƙofar gida ya katse mata masifar datai nufin farawa. A tsorace Karima tace, “Innarmu dan ALLAH kije, tunda kinga harda ita akace kuje. Kinsanfa mai-garin nan ba mutuncine da shi ba wlhy yana iya kira maki ƴan dokar”.

      Kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Ta kai dubanta ga Zinneerah dake kwance barci ya fara ɗaukarta. Tsawa ta daka mata wadda ta sakata tashi a firgice babu shiri.


      Ran Inna fal masifa ta tasa Zinneerah gaba Sanƙira na biye dasu suka tafi gidan mai-gari. Acan suka iske malam badamasi. Tun daga nesa Inna ta dinga antaya masa uwar harara kai kace idonta zasu zubo ƙasa ne. Shiko baima san tanaiba. Dan hankalinsa dana mai-garin da fadawa duk yana kan Zinneerah ne dake ɗingishi.

       “Ranka ya daɗe ka ga abinda nake hidi maka ko! Da alama bayan barowata gidan bugunta tai”.

      Ran mai-gari a ɓace ya wurgawa Inna mugun kallo. “Ke dai Asabe baki gamawa da duniya lahiya inhar baki canja halinki. Ace mutum shi dai baisan komaiba sai mugunta, ke shikenan zicciyarki tamkar ta kahiran hwarkon ƙarni! Kai ALLAH ya wadaran halinki wlhy Asabe. shi dai malam Sule bai sa'ar mace irinki ba. Ya auri ta arziƙin kin koreta a gidan kina kuma gallazama abunda ta haihwa. Wlhy ina mai tabbatar maki wata rana sai kinyi nadama, dan wanga ɗiya sai ta zame miki ɗan hakkin faka raina, RAINA KAMA kuma mara mutuncin mata”.

        Kan Inna a ƙasa tanata faman kumurya da kumatu babu damar magana, sai da mai-gari ya ƙare mata zagi tas da gorin asalinta kafin ya ɗora da gargaɗi.

      “To naji kince baki sake barin yarinyar nan taje makaranta. Kece kika sata ne?”.

     Kan Inna a ƙasa har yanzu tace, “ALLAH shi sawwaƙa ranka ya daɗe. Niko miya ja mani kai ɗiyana boko. Ubana bai saniba bani kai ɗiyana su tabaɗe. Can abokan cin mushenta ne suka kaita......”

        “E, ai shi abokin cin mushen nata da kike magana shine kika asirce ya koma kan ɗiyanki, kinga ashe kema abikiyar cin mushen tashi ce ko?”.

     Malam badamasi ya faɗa a harzuƙe cikin katse Inna. Babu wanda ya dakatar da shi, dan kowa yasan Babawo take nufi, tunda shine yay tsaye tsayin daka har Zinneerah ta shiga makaranta saboda tana so. Amma yaran gidansu daga firamari basa cigaba. Sa'a ce ma taɗan fara sakandire ɗin itama zango ɗaya tayi ta gudo saboda wani malami ya daketa Inna taje tai masa tijara tace Sa'ar bata sake zuwa. Daga nan kuma bata sake zuwan ba.

       Mai-gari ya cigaba da faɗin, “To bara na gaya miki a gaban kowa ki riƙe a ranki yarinyarnan zata cigaba da karatunta har sai ta gama. Ni nan mai-gari zan ɗauki nauyin ɗawainiyar karatun natama daga yau, tunda ance dama yaron daya kaita ya janye dama daga yi saboda sherin da kikayo ta ƙarƙashin ƙasa. Wlhy kinji na rantse, dai-dai da rana ɗaya yarinyarnan kika hanata zuwa makaranta sai kin kwana a kusada ofishin ƴan sanda. Kowa dake nan ya shaida”.

       A take duk suka amsa masa da cewar sun shaida. Banda Inna dakeji tamkar zata haɗiye zuciyarta ta mace. Zinneerah kam a ranta wani irin daɗi ne ya lulluɓeta. 

        Sai da mai-gari ya ƙarama Inna dogon gargaɗi sannan ya sallameta banda Zinneerah.  

      Bayan wucewar Inna Mai-gari ya shiga yima Zinneerah tambayoyi tana bashi amsa kanta a ƙasa. Sosai tausayinta ya sake mamayesu, suka shiga mata nasiha akan muhimmancin haƙuri da ribar da mai yinsa kanci a duniya ko a lahira. Sannan ya damƙa amanarta hannun malam Badamasi. Tare da tabbatar masa duk abinda za'a buƙata na ɓangaren makaranta na Zinneerah yazo gunsa ya amsa. Daga haka aka sallamesu bayan mai garin ya bata ƙyauta jikka biyu da rabi (500).

       Godiya tai musu sosai cike da girmamawa itama, tare da addu'oin fatan alkairi sannan suka taso ita da malam badamasi daya rakota har gida yana ƙara mata nasiha.


      Koda Zinneerah ta dawo gida tayi tunanin inna zata hukuntata akan abinda ya faru a gidan mai-gari. Amma sai taji shiru batace da ita ƙala ba. sai dai tana ɗaure mata fuska fiye da yanda ta saba. Sannan komai ƙanƙantar aiki ita ake kira tayi koda su Sa'a na zaune a kusa da ita.


★★''★★"★★"★★


           Akwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI, haka rayuwa ta cigaba da shuɗawa. Yau fari gobe tsumma a gidan su Zinneerah. Ita dai batasan minene farin ciki ba ko jin daɗi a gidansu. 

       Tun randa sukaje gidan mai-gari da inna sai ta sake ninka gallazawar da take mata fiye da da. Makaranta dai ta barta tana cigaba da zuwa. Amma kafin ta wuce ƙa'ida saita kammala ayyukanta. Idan kuma ta dawo ta iske wasu na jiranta him. Ga tallar riɗi da gyaɗa babu fashi gareta. Tsangwama wajen Karima da Tinene sai abinda yay gaba. Idan kaga taji daɗi sai wajen Sa'a da Yaya Gajeje idan tazo gidan. Shi dama Baba ba'a sakashi a lissafi. Dan tamkar bashi da wanima amfani a gidan. Idanma baiso ba sai ya yini a gona tun safe sai yamma zai dawo. Duk abinda Inna zatai a gidan ƙala bai iya cewa saboda tsoron da yake mata.


       A haka su Zinneerah suka fara jarabawar junior waec ɗinsu. Zinneerah ba wani ƙoƙari ne da ita sosai ba. Sai dai tanada naci akan abu sosai. Duk abinda takeso takan dage a kansa domin ganin ta cimma nasara. Hakan yasa sam bata da wasa, musamman ma daya kasance itaɗin miskilace ta gaske. Ga halin gidansu ya sake maidata shiru-shiru da rashin son sakewa da mutane.

     Zuwa yanzu ta daina jin ciwon cikin nan da kasala. Sai wani irin ƙiba take mai ban mamaki da haske. Ɗan matashin ƙirjinta na ƙara fitowa fili sosai fiye da da. 

      Kowa ya ganta sai ya tanka canjawar tata na ƙanƙanin lokaci, dan abun na bama mutane mamaki sosai. Musamman da aka san bawani daɗi takeji a gidan nasu ba. Ita kanta Innar bata gajiya da kallon Zinneerah ɗin a ƴan kwanakin nan. Sai dai tanayi tana jan tsaki da ƙyaɓe fuska.


            A yau ma data kasance juma'a bayan tasowarta makaranta gida tayo. dan jarabawa ɗaya kacal sukayi, wadda daga ita sai ta ƙarshe da zasu zana. Cike ta iske gidan nasu da ƴan kawo lefen yaya Karima, wanda aka kawo da ga gidan su Babawonta. akwatina uku zuƙa-zuƙa ƴan yayine. Itace kuma budurwar farko da akaima akwati uku a garin, dan ɗaya sukeyi kacal su haɗa rio irin na saka kayan yara ɗin nan babba. Wasuma basayin Rio ɗin. Amma sai ga Babawo shi yayi har uku, ga kaya fal.

           Sosai hankalin Zinneerah ya tashi, dan zuwa yanzu dai ta tabbatar Babawo kam ya barta har abada. Sum-sum ta lallaɓa ta shige ɗakinsu tunda babu wanda ya ganta hankalinsu nakan ganin kayan. Hijjab kawai ta cire ta zauna tana haɗiyar zuciya da ƙoƙarin ganin hawayenta basu zuba ba. Tsawon lokaci tana zaune hayaniyar mata da yara na daɗa ƙaruwa harda guɗe-guɗe. Ganin abin nasu bana ƙare bane ta zame ta kwanta hawayen da taketa ƙoƙarin dannewa suka shiga silalowa a kumatunta. Daga haka ta lula duniyar tunani mai zurfi har barci yay gaba da ita bata farga ba.


       Timmmm!!!

Kakejin ƙarar saukar dundu. A firgice Zinneerah ta farka tana sosa gadon bayanta inda Karima ta daketa.

       “Munahika ƴar buƙulu. Ashe nan kikazo kika ɓuya kina baƙin ciki da abun hwarin cikin daya sameni ko? To bara ki ji sai dai ki mutu wlhy. Ni Karima kamar na zama matar Babawo na gama. Dan nan da sati biyu za'a ɗaura mana aure ma”. Ta ƙare maganar da ƙyalƙyalewa da dariyar rashin mutunci.

     Ita dai Zinneerah ko ɗaga kai ta kalleta batayiba. Ta kuma ƙi yarda tai kuka. Dan dama wani lokacin haka take da shegen taurin zuciya. Musamman akan abinda ta tabbatar da natane akai mata fin ƙarfi. Haka Karima ta cigaba da mata tujara har sai da Yaya Gajeje da bata tafi ba ta shigo tana zaginta sannan tabar Zinneerah.

             Karan farko da baba ya nuna tsananin ɓacin ransa akan abinda akema Zinneerah har takaisa da yima Karima faɗa. Dan duk abinda tayi ya farune a kunnensa kasancewar ya shigo gidan.

      Babu wanda ya iya magana har Inna. Dan ita kanta yau sai taji wani shakkar Baban a cikin ranta. Dama ance mai haƙuri bai iya faɗa ba.

      Ɗan Murmushi Zinneerah dake a ɗaki zaune har yanzu tayi. A ranta kuwa tana mai tsananin jin tausayin mahaifin nasu da ta tabbatar anfi ƙarfinsa ne dama game da al'amarin gidan nasa, bawai dan Inna ta gagaresa bane ba.


★★★


         Tun daga wannan rana su Inna suka hau shirin biki. Dama can a shirye suke tsaf dan sun daɗe suna jiran wannan ranar dan dai kawai Babawon nata musu yawo da hankaline kamar ma zai suɓuce. Sai kuma gashi cikin lokaci ƙanƙani hankalin nasa ya sake dawowa ga Karimar a bazata.............✍

 

No comments

Powered by Blogger.