Makauniyar Kaddara 38


 *Page 38*


............Sai da Khalipha yay sallama a ƙofar ɗakin aka bashi izinin shiga sanna ya shigo, zaune ya sameshi cikin kujerar dake a ɗakin kansa jingine ya lumshe ido da makarinta. Bai motsaba daga yanda yake har Khalipha ya zauna a ɗayar kujerar dake kallonsa cike da tausayin ɗan uwan nasa. ɗan jimm yayi na wasu sakanni kafin yay ƙasa da kansa

cikin lallashi yace, “Yayanmu dan ALLAH ka kwantar da hankalinka, insha ALLAH bin komai a sannu zai warware dukan aninda zuciya ke hasashe duk rintsi”.

       Wani ɗan murmushi AK ya saki yana buɗe idanunsa da gaba ɗaya launinsu ya canja, sai da ya yima Khalipha kallon wasu sakanni kafin ya tashi zaune sosai yana furzar da abinda ya tokare maƙoshinsa mai ɗaci. Cikin son danne duk damuwarsa yace, “Bestie dama kasanta?”.

    Ɗan kallonsa Khalipha yay alamar wa?.

     Idanunsa ya lumhe ya buɗe akansa, kamar bazai sake tankawaba sai kuma ya furta, “Zinneerah!”. A saman laɓɓansa.

      A bazata Khalipha ya saki murmushi, a ransa ko gulma yake (kai yayanmu kako iya faɗar sunan). A fili kam sai ya gyaɗa masa kai tare da ƙara nutsuwa sosai. “Nasanta Yayanmu, amma sanin na kwanaki goma zuwa sha ɗaya ne kacal idan ban mantaba. (A take ya fara bashi labarin haɗuwarsu a randa aka bigeta, wanda a dalilin aiken da yay masanema yaje jigawan, suna hanyar dawowa motar ta samu matsala. ya baro wanda sukaje taren da motar shiko yabi ta haya dan zuwa ya isar da saƙon karsu makara tunda yasan jira yakeyi).

         “Wannan shine dalilin dayasa na santa Yayanmu, ni duk zatona ma tanada aure wlhy, shiyyasa ban wani taɓa maida hankali akanta ba, inma baka mantaba na baka labarin accident ɗin ai a wancan lokacin. kuma ni a zuwan nan da mukaima sai ban ganetaba saboda duk ta canja, sai randa naga Gwaggo (Mmn sadiq) sannan na ƙara tabbatar da itace, inataso muyi maganama hakan bai faruba saboda ciwon Granny”.

       Ɗari bisa ɗari AK ya yarda da Khalipha, dan yason bai iya ƙaryaba, tunda suke dashi bai taɓa kamashi da wani abu na rashin gaskiya ba, zamansa ya gyara da ƙyau yana furzar da numfashi, cikin tsatstsare Khalipha da idanu yace, “Miye amsata ta ɗazun game da kamannina da yaro?”.

        Ƙasa Khalipha yay da kansa cike dajin nauyin gaskiyar abinda ke a ransa. Muryarsa a dakushe yace, “Yayanmu al'amarin akwai rikitarwa, harga ALLAH banida takamaimai amsa, dan bayan matarka nine mutum na biyu da zan iya bada shaida akanka, hakan yasa duk abinda zuciyata zata iya hasasomin ƙwaƙwalwata bazata iya ɗaukaba, shawara ɗayace shine ai gwaji kawai, maybe hakan ya kawo hasken da kowa zai iya fahimtar bakin zaren. Ka gafarceni idan nayi kuskure”.

       Murmushi AK ya sake saki mai sanyi yana gyaɗa kansa. Cikin nuna gamsuwar zantukan Khalipha yace, “Shiyyasa nake kiranka Bestie, dan mafi yawan tunaninka irin nawane, inason mutum mai gaskiya da ƙyaƙyƙyawan nazari akan komai Khalipha. ALLAH yay maka albarka, nima a raina shawarar zuwa Nigeria nake domin gwada ƙwayoyin halitarmu ni da yaron, maybe hakan zaisa na iya tuna wani abu dana manta ko samun ƙwarin gwiwar bakin zaren”.

      Khalipha dake murmushi yana jinjina masa kai yace, “Nagode Yayanmu”.

       “Nizan gode maka ai, dan ka zama ɗan uwa ɗaya tamkar da dubu. Yanzu kaje ka huta kaima, sai dai banason ka sanarma Granny tafiyata, sai na gama shiri zan sanar mata, insha ALLAH nanda awanni biyar zan wuce”.

         Cikin waro idanu Khalipha yace, “Yayanmu ince sai nan da kamar kwana biyu?”.

     Kai kawai ya girgizama Khalipha yana miƙewa da murmushi akan fuskarsa. Ganin ya nufi toilet shima sai Khalipha ya miƙe ya fita cike da tausayin Yayan nasu, ya tabbatar jarumtarsa da ƙoƙarin iya shanye damuwane kawai ya danne dukkan halin da yake ciki, amma duk wanda ya sanshi ya kalli ƙwayar idonsa yasan baya cikin kwanciyar hankali. (Ya ALLAH ka kawo mana mafita, ka haska mana duhun da muke ciki domin rahamarka ya UBANGIJI). Khalipha ya faɗa yana nufar ɗakinsa zuciyarsa cike da rauni da ɗaci. Har ransa kuma yanajin zai iya auren Zinneerah koda ace ƴaƴa goma ta haifa, amma yanason jin ta bakinta itama harga ALLAH.


★★


     Tun bayan fitar Khalipha a ɗakin babu wanda ya sake jin ɗuriyar AK a gidan sai bayan awannin daya ambata ma Khalipha na wucewa 9ja. Duk da halin da yake ciki na tsananin ciwon kai dana zuciya jarumtarsa ta shanye kaso mafi yawa. Sam bazaka iya hasaso damuwarsa a saman fuskaba, sai dai idan ka masa sanin ƙwarai a kallo ɗaya zaka gano damuwar cikin ƙwayoyin idanunsa da rauninsu ya bayyana ƙuru-ƙuru.

        A falo ya samu su Jamal nacin abinci su uku. Yay musu kallon nazari ganin yanda suke kowa fuska da damuwa ya ɗauke kansa. Sai da yazo dab dasu suka farga da shi saboda motsin takunsa da yawaitar ƙamshin turarensa. Gaishesa sukayi, ya amsa musu yana wucewa ɗakin hajiya iya.

        Koda ya shigo bayan sallamar da yayi baiji an amsaba bai samu kowa a ɗakinba sai Zinneerah dake kwance tana barci har yanzun. Hanyar toilet ya ɗan duba saboda jin motsin ruwa, da alama Granny ce a ciki. Ya ɗauke kansa yana maidawa ga Zinneerah. Bayanta kawai yake iya gani, dan haka ya taka a hankali zuwa inda ta juya fuskarta, kansa tsaye ya zuba mata fitinannun idanunsa dake cike da abubuwa masu yawa a wannan yinin, kallo yake mata irin na ƙurulla da bai taɓa matashiba, ya kai tsahon minti ɗaya da wasu sakanni a haka kafin ya matso dab da ita, ahankali yaɗan ranƙwafo kanta, tare da kai hannusa a fuskarta ya janye mata jelar gashinta daya zubo biyu da akai mata kalba da ɗan yatsansa manuniya.

    Motsawa tayi alamar zatai juyi. Kauda kansa yayi yanaja da baya kamar bashi ya aikataba. A dai-dai nan Granny ta fito.

       “Lafiya kuwa na ganka da jikka moddibo?”.

    Juyiwa yay ya dubeta, kansa tsaye yace, “Zanje Nigeria ne Granny”.

        “Nigeria kuma? Akanmi to?”.

“Akan abubuwa da yawa. Kimin addu'a ke dai”.

       “To addu'a kam kullum cikin yimuku ita muke Moddibo, amma daka sanar dani nikam da tare muka wuce, dan zaman garin nan fa ya isheni”.

      Guntun murmushi yayi yana matsawa inda take. Ya kamo hannunta, cike da lallashi yace, “Kiyi haƙuri kinsan baki gama ganin likitaba, nima bawani jimawa zanyiba inagama 2days zanyi insha ALLAH”.

     “To ALLAH yasa haka. Amma wannan birkitacciyar matar taka tare zaku tafi? Dan bazaka barmana ita nanba”.

        Maganar tata ta bashi dariya. sai dai baiyiba. hannunta ya saki da faɗin, “Matar tawace birkitacciya Granny? To ai duk birkicewarta kin iya da ita na sani. Karki damu babu abinda zai faru insha ALLAH”. Ya ƙare maganar yana ɗan duban inda Zinneerah take ya ɗauke kansa.

     Duk da hajiya iya batasan manufar tafiyar tasaba bataso ya tafi ya barta ananba. Amma duk da haka sai tai masa fatan alkairi da gargaɗin karfa yaje yay zamansa.

     Shidai fita yay kawai yana ɗan murmushi. Yasan ko mi zaiyi Farah bazata sauraresaba a yanzun, dan haka baibi takantaba dan ya bar mata saƙo a ɗakinsa. A falo ya tsaya ya aika Jamal kiran Khalipha. Babu jimawa kuwa sai gashi ya fito cikin shiri.

    Tare suka fita shi da Jamal da Khalipha ɗin da zasu masa rakkiya airport.


_____________★


     Zinneerah batasan da tafiyar AK ba, koda ta tashi kuma su Khalipha sun dawo gida. Kowa yaji daɗin yanda ta farka normal, sai dai jikinta duk a sanyaye, komai yinsa take kamar mara ƙashi a jiki, gashi sam bata da walwala. Abinci ma sai da Hajiya iya ta takura mata sannan tacisa tasha ruwan addu'oin da tai mata tun ɗazun kamar yanda Mahma ta faɗa.

     Ta farka da abubuwa masu yawa a cikin rai. sai dai miskilancinta da rashin son nuna damuwa akan abu ya shanye kaso mafi yawa, dan haka yanayin ya rikiɗe mata kawai zuwa sanyin jiki da rashin son hayaniya.


      A ɓangaren Farah kam kamar yanda bata fito ta nema kowa ba babu wanda ya nemeta. Sai dai mai aikinta dake ɗan shiga da fita zuwa ɗakinta lokaci-lokaci tana kai mata abunda ta buƙata, itama batasan AK yabar gidanba sai a bakin mai aikin nata daya barma saƙon cewa ta sanar mata yabar abu a ɗakinsa. Sosai hakan yayma Farah ciwo, badan tana tsoron hukuncin Mahma ba da wlhy saita bar masa gidansa. Bata kira Mammah ba sai aunty Zakiyya. Mammah kuma saita tura mata text message akan tafiyar AK ɗin. Ta kuma tabbatar mata wani ƙullin AK ya tafi yowa a Nigeria danya binne abinda ya shuka akan yaron. Itama kanta Mammah ranta yay matuƙar ɓaci da tafiyarsa bai sanar mataba. Hakan yasa ta shiga gayama Mahma rai a ɓace.

    Murmushi kawai Mahma tayi, a nutse tace, “Duk ke kikaso hakan Hindatu, na daɗe da nuna miki tsaurinki akan Abdul-Mutallab bashike nufin zaki iya rabasa da mahaifinsa ba. Adilah mace ce zaki iya tanƙwarata ko bataso tamiki biyayya. Amma Abdul-Mutallab namiji ne, su kuma maza da kike gani kullum tunaninsu dabanne da namu, suna da saurin hango kuskure idan sun so hakan, sai dai su ɗauki mataki kosu bari wannan zaɓinsu ne, dan hakan a jininsu yake. Ni banga dalilin da zaisa kicigaba da damuwa da alaƙar da ALLAH ya haɗaba, tun ran ginifa tun ran zane, kuma da uba ake ado kema kin sani. Inba hakaba miyasa sanda Mama ta koma Morocco kika dawo london kika zauna da Daddy? Ai da saiki bita can kota hanaki zama anan ɗin wajen Daddyn. Yakamata ki dawo da hankalinki jikinki, dan amatsalarki da Kabeer daban ki daina ƙoƙarin saka yaranku a ciki, hakan bazai haifar miki da ɗa mai ido ba. Da yawan labarai a tarihi maza ke nuna ƙarfa-ƙarfa wajen amshe ƴaƴa a hannun uwa idan ƙaddarar rabuwa ta ratsa, sai dai abinda mutane basu saniba ko suke gaza tunawa idan mu mata muka sami damar nasarar karɓe yara a hannun ubansu bisa irin wannan ƙaddarar munfi mazan atsabibancin cusama yaran aƙidar ƙin uban koda ace mune da kaifi a wajen haifar da rabuwar auren. Ya kamata ki dawo cikin hankalinki, ki daina azabartar da Abdul-Mutallab da laifin Kabeer. Dan na fahimci haushin Kabeer kike saukewa akan Abdul-Mutallab akowane lokaci, wannan itace kawai gaskiyar dazan iya gaya miki dan karkiyi biyu babu. Daga lokacin da zuciyar Abdul-Mutallab ta fara raya masa tsaurinki yayi masa yawa to tabbas zaki rasashi ki kuma rasa Adilah itama dan zatabi ɗan uwanta kodan so da shaƙuwar dake a tsakaninsu mai ƙarfi”.

       Mahma ta miƙe tabar mata wajen tana gama faɗa. Da kallo kawai Mammah ta bita batare data iya cewa komaiba. Tabbas gaskiya Yayar tata ta sanar mata. Sai dai bataji a ranta zata ɗauka dan itafa bazatabarma Kabeer da uwarsa ƴaƴanta ba. Dan ita tasha wahala akansu bawani shege ba. Zata riƙe ƴaƴanta shima ya riƙe nashi daya tara da shegen aure-aurensa da idan ta tuna sukafi baƙanta ranta fiye da komai. Taɗau alwashin zatayi yaƙi mai girma akan tabbatar da cigaban wanzuwar ƴaƴanta tare da ita duk wuya duk rintsi.


*_NIGERIA_*


       Koda AK ya iso Nigeria Baffah yayi mami matuƙa, amma da yake shima a yunwace yake da son ganinsa sai hakan yay masa daɗi. Ko gaisuwar kirki basuyi zaman yiba AK ya sanarma Baffah abinda ya kawosa. hundred percent Baffah ya gamsu da hakan, shiyyasa ya shiga saka masa albarka. a take kuma ya kira Mmn Sadiq. Bayan sun gaisa itama kamar yanda suka saba cike da girmama juna, ya sanar mata hukuncin da suka yanke.

      Sosai mamakin hakan ya kama mmn sadiq. Cikin sanyin jiki tace, “Ya ilahi, Yaya mufa bamun faɗa muku labarin nan bane domin zargin Adnan akan kamanninsa da Little”.

     Murmushi Baffa yayi mai faɗi, ya gyara zamansa yana faɗin, “Nasani Hauwa'u, muma kuma ba hakan bane a ranmu wlhy, sai dai ki sani tun randa kukazo da yaron nan gidannan babu wanda zuciyarsa ta huta akan kamaninsa da Adnan a gidan nan. Jin gaskiyar samuwarsa tasa muke kwaɗayin yin gwajin ko hakan zai sama mana kwanciyar hankali, dan nayi alƙawarin saina ƙwatoma Zinneerah haƙƙinta awajen koma wanene. Yanzuma bayan anyi gwajin insha ALLAH gobe idan ALLAH ya kaimu zamuje can asalin ƙauyen nasune. Dan haka banason zuciyarki ta ƙara miki wani hasashe daban bayan ƙyaƙyƙyawa”.

      Sosai raunin mmn sadiq ya bayyana, tace, “Shikenan yaya, ALLAH ya saka da alkairi yabar zuminci. Bara nama Yaya magana to dan yana gida sai mu kawosa kawai”.

     “Hakan shine dai-dai, mu haɗu a shira hospital daku”. Daga haka Baffah ya yanke wayar.


      Wanka kawai AK ya samu yayi bayan Safiyya sunje sun gyara masa ɗakinsa da falon ɓangaren hajiya iya, abincima bai iya ciba sai tea yasa Ni'ima ta haɗa masa. daga haka ya fito ya sami Baffah dake zaman jiransa yana waya rai ɓace.

    Shiru yay yana nazarin wayar ta Baffah, inda kai tsaye ya gane da Mammah suke waya, runtse idanunsa yayi da ƙarfi jin yanda Baffah ke dasama Mammah baƙaƙen maganganu, wanda ya tabbatar itace ta fara masa, shiko yake maida mata murtani.

    Juyawa yay a hankali zai fita ya jiyo kalaman Baffah da suka sakashi dakatawa a kausashe.

      “Komi zakice kice Hindatu, wlhy da banma kawo hakan a rainaba game da Adnan. Amma wlhy kinji na rantse a wannan gaɓar zan tabbatar miki da cewa ni Kabeer Abdul-Mutallab Shira nine mahaifin Adnan, ba kuma tsoronkine yasa na barmiki shiba daga shi har ƴar uwarsa. Dan haka muzuba mu gani ni dake ɗan hakal ka fasa”.

   Daga haka Baffah ya yanke wayar yama kasheta gaba ɗaya dan baya buƙatar ta sake kiransa..............✍


No comments

Powered by Blogger.