Makauniyar Kaddara 37


*Page 37*


.............“Tabbas Zinneerah Abdul-Mutallab, sai dai itama bayin kanta bane ƙaddarartace hakan. Zan baka ainahin tarihin rayuwar yarinyar domin ka fahimci ainahin yanda zancen yake kafin mukai inda ni nake buƙata”.

    Tamkar AK na gaban Baffah ya shiga gyaɗa masa kansa dake ƙara ƙarfin sarawa tamkar zai buɗe.

      Baffah da duk yake jiyo yanda yake sauke ajiyar zuciya a jajjere ya fara bashi labarin rayuwar Zinneerah tun daga zaman mmn sadiq a gidansu har haihuwarta da barota datai, zuwa maganar cikin little da har yanzu babu wanda yasan wa yayma Zinneerah shi, itama kuma tambayar duniya tace batasan komaiba akai. Abdul-Mutallab ban taɓa zarginka da aikata ɓarna makamancin haka ba, sai dai zuciyata ta gagara nutsuwa akan kamanin yaron nan da kai musamman a yau da naji ainahin tarihin samuwarsa. Dan haka a matsayina na mahaifinka dan ALLAH ina roƙonka ka faɗamin gaskiyar abinda ka sani, koda ace da ganganci ka aikata zan fahimceka. Kaji tsoron ALLAH mu tausayama rayuwar yarinyarnan, dan kaima kanada ƙanne gasunan cike da gidan nan, sannan uba zaka zama watarana, na tabbata bazakaso hakan ta kasance akansu ba. Na baka dama kaje kayi tunani daganan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu, na barka lafiya”.

   Baffah ya katse wayar batare da ya jira cewar AK da gaba ɗaya yakejin duniyar na juya masaba.......


        Barowar AK gidan su Mammah baifi da mintuna ashirin ba ta iso daga ƙasar China. Dan harga ALLAH zancen Farah ya matuƙar gigitata akan wai Abdul-Mutallab ya haihu da wata a waje harma taga ɗan. Tsabar tashin hankalin data shiga ko gama abinda ya kaita bataiba ta dawo dan zancen waya bazai gamsar da itaba gara azo ayi ƙuru-ƙuru.

     Maganarta da Farah taji yasa ta buɗe ɗakin data maida kaca-kaca da fashe-fashe. Rungumeta Mammah tayi tana lallashi. itako kuka take kamar zata shiɗe duk ta fita a hayyacinta. 

     Ko tsayawa taji ta bakin Mahma dake son mata bayani bataiba ta kama hannun Farah suka fito. Sanin halinta yasa Mahma itama biyosu dan batason ƴar uwarta taje ta ida zubar da sauran mutuncinta a idon mahaifiyar Kabeer (Hajiya iya) kodan darajar ƴaƴan dake a tsakani.

       

      Su Hajiya Iya duk suna a ɗaki suka dinga jin ƙwala kiran sunan Abdul-Mutallab da Mammah takeyi kamar zata fasa gidan. Babu shiri duk suka fito har Zinneerah dake barcin wahala dan zazzaɓin nata bai gama sakintaba duk da jikin babu zafi sosai yanzun.

     Cikin ɗan barcin daya fara figarsa na kiɗimar kalaman Baffah da yaketa bita a zuciya da ƙwaƙwalwa yake jiyo muryar Mammah na ƙwala masa kira. Ahankali ya buɗe idanunsa da sukai masa matuƙar nauyi ya yunƙura da ƙyar ya tsashi zaune, jin kamar muryar tata na kusanto ɗakinsa ya sakashi zira ƙafafunsa ƙasa ya sauka a gadon gaba ɗaya domin neman riga yasa, dan daga shi sai boxer a jiki. 

           Jallabiya ya samu ya saka sannan ya nufi ƙofar ya buɗe hannunsa dafe da kansa dake sara masa. Mammah da Farah na neman danna kai a ɗakin Mahma data ƙaraso gurin kusan tare da Hajiya Iya ta riƙo mata hannu tana girgiza kanta, tana mata magana da idanu akan ta kama kanta.

      Mahma tamkar uwa ce a garesu, dan itace babbar yayarsu, ta kuma riƙe girmanta agaresun. Sai dai a yau Mammah batajin zata iya controling kanta wajen mata biyayyar. Zatai magana Hajiya Iya datai kicin-kicin da fuska dan al'amarin Farah ya fara bata haushi ta katseta.

      “Lafiya kuwa Hindatu irin wannan ƙwala kira haka?”. Tai maganar da mata kallo ɗaya ta maida ga AK dake dafe da kansa yana kallonsu kawai.

       Mahma ce tai saurin cewa “lafiya lau Hajiya, mun sameku lafiya ya ƙarfin jiki?”.

      “Bafa lafiya ba Adda, nifa kin sanni ba ɓoye-ɓoye na iyaba”. Mammah ta faɗa kafin Hajiya iya ta amsa gaisuwar Mahma.

     Kai Hajiya iya ta ɗan girgiza, danta fahimci halin Farah dana Mammah suna kamanceceniya. “To ALLAH ya ƙyauta” Hajiya iya ta faɗa tana nufar AK.

        A harzuƙe Mammah tace, “Hajiya zai ƙyauta ne idan naji a inda wannan mara mutuncin ya samo ɗa? Auren da kuke iƙirarin masane akai masa a ɓoye ban saniba? kokuwa a waje ya samar da ɗan ga wata?”.

    Cikin sauri Mahma ta riƙe hannun Mammah ranta a ɓace tace, “Hindatu! Wai nikam yaushe zakisan kin girmane? Wane irin kalamaine haka masu tsauri akan yaro?”.

      Hawayene suka ɓallema Mammah, “Addah yaya kikeson nayi? Kema kinsan halin Abdul-Mutallab, idan ba tauri nai masaba yanzu zai maidani sakara tunda huɗubar ubansa ta fara sakashi ganina a banza, yo inba a banza yake ganinaba yanzu a ina ya samo ɗa saboda ALLAH?. Na rantse da ALLAH a wannan karon sai inda ƙarfina ya ƙare, bazan taɓa yarda a rabani da yarona ba, ance ba'a ƙaunata, to basai a barni da ƴaƴana ba tunda ni na haifi abuna. Amma sai bita da ƙulli akemin akan Abdul-Mutallab”.

     Karan farko Hajiya iya tai murmushi tana jinjina kanta, danta fahimci da biyu Hindatu tazo gidan kenan, to lallai tana dai-dai da haukarta kuwa. Juyawa tai ta kamo hannun AK da shi bama fahimtar Mammah yakeba da ƙyau, sam a rayuwarsa baison hayaniya, tada masa da hankali takeyi matuƙa gaya, shiyyasa duk irin waɗanan abubuwan yakan so kauce musu gudun shigarsa wani hali, amma a wannan gaɓar yaya zaiyi? Uwa uwace, tanada mutunci mai nauyin gaske a gareshi da baki bazai musaltaba. Sannan ya mata uzuri daga ita har Farah ɗin dan yasansu mutane ne masu wahalar fahimtar abu a lokaci ɗaya, musamman abinda basa so.

        “Zamu iya zama”. Hajiya iya ta faɗa tana jan hannun AK. Mammah zatai magana Mahma ta dakatar da ita, hannunta taja itama da watsama Farah dake kuka har yanzu wani shegen kallon ina tafe kanki kema..  


      Duk zama sukai badan Mammah taso hakanba, Hajiya iya da har yanzu take riƙe da hannun AK ta fara musu bayani akan su basuma Moddibo aure da ƴar kowa ba........

      “Mammah kinji ko, wlhy ɗan shege ne?”.

    Fara ta katse Hajiya iya dake bayani cikin fashewa da matsanancin kuka. 

     A fusace itama Hajiya iya ta dubeta zatai magana sukaji fasa ihun Zinneerah data yanke jiki ta faɗi. A zabure Hajiya iya da AK suka miƙe, hakama Mahma duk da batasan wacece ba babu shiri ta miƙe. Farah da Mammah ko ƙin tashi sukai, dansu jin daga ina ɗa ya fito shine babbar damuwarsu.

        Tuni hajiya iya ta mance da jikinta na tsufa, cike da sassarfa ta nufi ɗakin dan tun zamansu a wajen Khalipha ya janye su Zinneerah suka koma ciki. Saurin rufama Hajiya Iya baya AK yayi. Hakan yasa Mammah son tsaidashi amma bai saurareta ba. A ƙufule Farah tace, “Kingani ko Mammah, a cikin ƴan iskan yaran nan nefa, na tabbatar shegen Khalipha ɗin nan ne ya haɗa drama ɗin nan, yanzu hakama harda ita tsohuwar nan kafin ta fito”.

      Miƙewa Mammah tayi tana faɗin, “Aiko sunyi ta banza, tashi muje, ni zanyi maganin kowansu, yanda sukace basa ƙaunata nima bazan taɓa son kowaba a cikisu”.

       Lokacin da suka shigo ana ƙoƙarin shafama Zinneerah data suma ruwa. Wani irin nannauyan numfashi ta kawo, sai kuma ta ƙanƙame Meenal dake riƙe da ita jikinta na wani irin rawa. Kuka ta fashe da shi tana faɗin kanta zai fashe, su taimaketa kanta kanta.

      Hankalin Hajiya Iya ya tashi matuƙa, da ƙyar ta iya janyo Zinneerah daga jikin Meenal ta maidata jikinta. Akwai sani sosai tattare Mahma game da irin waɗanan abubuwan na sammu da aljanu da sauransu, dan mijinsu da ALLAH yayma rasuwa babban malami ne akan wannan harkar, shiyyasa suka koyi abubuwa da dama agaresa musamman ita data kasance matarsa ta farko tun tanada ƙuruciya, dan ita dama ba'a nan London ta tashiba a Morocco ne hannun kakarsu, sai dai tazo yawo ta koma harma aka aurar da ita, sai dai dayake ALLAH ya ƙaddara zamanta anan bayan rasuwar mijin ta dawo da zama nan ɗin duk da mahaifiyarsu ta jima da komawa Morocco itama acanma ALLAH yay mata rasuwa, dan ko sanda Hiddatu ta kashe aurenta ta koma London mamansu tana Morocco, kuma wani daliline mai ƙarfi ya maidata zamancan ɗin dole.

       Zama tai kusa da Zinneerah itama ta ruƙo hannunta tana magana a hankali jin Hajiya Iya na cewa azo akai Zinneerah ɗin asibiti a kiɗime..   

      “Wannan ba ciwo bane na asibiti Hajiya, addu'a take buƙata dan al'amarine kamar na sammu ko jinnu”.

    Kallonta hajiya iya tai da mamaki, tace, “Sammu kuma Zaliha?”.

      “Tabbas haka nake hasashe”. Ta faɗa kanta tsaye tana ɗora hannunta akan Zinneerah daketa jujjuyashi tana kukan zai fashe.

     Sam AK baya son wannan abun, dan kusanma shine maƙasudin ɗakko Mahma da yay daga Morocco ya maido London, a wani zuwa da yay can ya samu harkokin mijin nata na neman dawowa kanta shiyyasa ya tattarota ya maido nan. Cikin ƙarfin hali dan shima kan nasa ciwo yake masa har yanzun kamar zai tarwatse ya matso kusa da su. “Mahma da ga faɗuwa kuma sai ace sammu, ita wannan ƴar yarinyar wama zai damu da lamarinta balle ya ɓata lokacinsa wajen aikata mata wani sihiri?”.

       Kallonsa Hajiya iya tai taɗan girgiza kai, muryarta cike da damuwa tace, “Modibbo tunaninka kenan, shi magauci ina ruwansa da ƙanƙantar shekarunka, sannanma hakan zai iya faruwa dan kishiyar mahaifiyar yarinyarnan atsabibiyace komai zata iya aikatawa. Kinga Zaliha nidai dubamin ita, shi ba komai ya saniba sai zama cikin masu jajayen kunne”.

     Mahma dama ita ba tsayawa tai saurarensuba, hannunta riƙe da kan Zinneerah take tofa mata addu'oi, a hankali ta fara rage kukan da takeyi tana juya kan a hankali. Cikin abinda bai fice mintuna a shirinba sai ga wani irin nannauyan barci yayi awon gaba da ita sai ajiyar zuciya take saki a jajjere.

      Khalipha da kamar shima zaiyi kuka ya kalli su Jamal, “To kukan ya isa haka ko, kuyi mata addu'ar”. Hawayensu suka shiga sharewa. 

    Godiya Hajiya iya ta shiga yima Mahma bayan ta godema ALLAH. Mahma dake murmushi ta miƙe tana faɗin, “Babu komai Hajiya ai muma ƴarmu ce. Insha ALLAH idan ta farka mukaga yanda jikin yayi sai asan abinyi, ALLAH ya bata lafiya. Amma bara na baku addu'oin da zakuyi abata taita sha kafin gobe idan ALLAH ya kaimu, suma zame mata sune ruwa”.

      “Aiko mun gode sosai Zaliha. ALLAH ya jiƙan magabata kinji, ya raya miki zuri'arki da namu baki ɗaya”.

     Baki Mammah ta taɓe tana ɗauke kanta, dan itafa ko'a jikinta ma, tama ƙagara su gama ƙaƙale-ƙaƙalensu azo a gaya mata abinda ya kawota. Mahma data gama karantarta tsaf tana gama rubuta addu'oin da za'aima Zinneerah ta dubeta tana faɗin, “Hindatu muje gida”.

      “Adda muje gidafa kikace? Kina tunanin zanbar gidan nan banji miya kawoni ba?”.

     “Sosaima kuwa zaki barshi, tunda ita maganar ai ba guduwa zatai ta barmuba, idan yarinyarnan ta samu lafiya saimu dawo a yita a tsanake dan a yanzuma babu nutsuwar da zaki fahimta tattare dake”.

       Baki ta buɗe a hasale zatai magana Mahma taja hannunta suka fice. Farah zata bisu Mahma ta dakatar da ita. “Wlhy idan kika biyomu ko Abdul-Mutallab naso ko baya so sai na sakashi ya sakeki tunda ke hankalinki a gwiwa yake, idan zaki zauna gidan mijinki ki zauna. Idan kuma zaki biyomune ki tabbatar kin fito kenan wawuya kawai”.

     Saurin ja baya Farah tayi dan Mahma ta fito musu ne a ainahinta shiyyasa itama Mammah ɗin ta gagara cewa uffan, sai masifa take a zuciyarta kamar zata haɗiye harshenta cikin ciki.


      Daɗi sosai AK yaji akan hukuncin Mahma, danshi kanshi a yanzu filin yin nazari yake buƙatar samu akan wannan al'amarin, ALLAH shine shaidarsa bai taɓa aikata zina da ƴar kowa ba, shi baima taɓa ganin Zinneerah ba sai a gidansu wannan zuwan. Amma gashi Baffah kansa zargin yaron nasane yake. Kai shi kansa da kansa zargin kansa yake dan kamaninsa da yaron abun a dubane akumayi nazari. A yanzu kawai yana ganin shawarar da zuciyarsa ke bashi ya kamata yabi kozai fita daga ruɗanin da yake ciki daga shi har ƴan uwansa. Miƙewa yay batare da yacema kowa komaiba ya fice a ɗakin. Hakan yasa itama Farah dafa masa baya sai dai ɗakinta ta nufa tana kuka ba nashiba.

     Hajiya iya da gaba ɗaya take jin komai yana mata nauyi a zuciya ta duba Khalipha a sanyaye tace, “Ka bisa Khalipha, kasan Moddibo bai iya ɗaukar damuwa da sauƙi ba”..   

      A raunane Khalipha ya jinjina mata kansa, dan shima a ruɗan yake da komai, saboda Hajiya Iya ta bashi takardar wajen mmn sadiq ya karanta ɗazun saboda fitowar sunansa a ciki. Ya kuma sanar mata gaskiyar abinda ya sani game da haɗuwarsa da Zinneerah.............✍


No comments

Powered by Blogger.