Makauniyar Kaddara 36


*Page 36*


..............Meenal ce tai ƙarfin halin faɗin, “Granny zazzaɓi ne a jikin Zinneerah”.

      “Ya salam, zazzaɓi kuma?”.

Granny ta faɗa tana zagayowa inda Zinneerah take. Hannu ta saka a goshinta da wuyanta da sukai zafi rau. “Kai aiko jikin da zafi Inno, sannu kinji”.

    Zinneerah da bacci-bacci ya fara figa ta ɗaga mata kai tana maida idanunta ta lumshe.

       AK na tsaye yana kallonsu kamar baiji mi Hajiya iyan ke faɗaba. Sai da ta dubesa ne ya ɗan tako inda suke shima, kanta ya ranƙwafo yasa hannu yana cire bargon data lulluɓa. “Tashi zaune”. Ya faɗa ciki-ciki.

     Tun matsota da yayi ƙamshinsa ya cika mata hanci, daƙyar taja numfashi lokacin daya ranƙwafota, duk da yanda taji maganar tasa gab da ita bata miƙe zaunen ba sai idanunta data rumtse da sauri. 

      “Baƙyaji ne?”.

Ya sake faɗa kamar bayaso.

     Idanunta ta buɗe a hankali tare daja baya kaɗan daga kusa dashi, kafin ta yunƙura da ƙyar ta tashi zaune. Shima tsaye ya miƙe da ƙyau idanunsa a kanta. “Mike damunki?”.

     Wani irin haushi tambayar tasa ta bata. Sai kace ba'a gabansa matarsa ta shaƙeta zata kashe ba yake wani mata wannan tambayar. Batare data yarda ta kalli sashen da yakeba ta nuna masa wuyanta.

        Ɗan luu yay da idanunsa da gaba ɗaya suka canja kalarsu yana ɗaukesu daga kallonta. Batare da yayi maganaba ya fice a ɗakin su Bahijja na binsa da kallo.

     Zama Hajiya iya tayi kusa da Zinneerah ta kamota jikinta tana mata sannu da duba wuyan nata. Duk da bata kasance fara tas ba ana ganin shatin hannun Farah a wuyan, saboda ba shaƙar wasa tai mataba. Gashi wajan kiciniyar ƙwaceta kuma duk an jijji mata ciwo da farce.

    Shigowarsa shi da Khalipha ta sakasu kallonsu, Khalipha ya ƙaraso inda suke ya zauna a bakin gadon shima yana mata sannu. “Tashi ga magani kisha zai saki insha ALLAH”.

    Babu musu ta tashi zaune ta amshi ruwa da maganin hannun Khalipha ɗin tasha. Tana gama sha kwanciya ta koma tayi jikin Granny. Hakan yasa ɗakin ɗaukar shiru na wani lokaci kowa da abinda yake saƙawa da kwancewa a cikin ransa game da al'amarin.......


*_DANYA_*


        Koda su Inna suka iso Danya mahaifiyar babawo ta buƙaci wucewa da Karima gidanta amma sai Inna taƙi fir. Acewarta sai sunsan miya faru tsakanin Karima da Babawo koda hakan zata kasance. Badan innar babawo tasoba dole ta haƙura aka wuce da Karima gidan su Inna. Ita kuma tace zataje gida taɗan kimtsa saboda kwanan asibiti da sukai zata samesu daga baya dan tana son taɗan haɗoma karimar kayan kunu kafin babawon ya gadama yazo.

      Baki amare Inna ta amsa mata tana jan hannun Karima suka shige cikin gidan. 

         Tun'a farkon shigowa gidan idanun Inna suka sauka akan Hajja lanti. Sosai ta waro idanu waje tana kallon hajja lanti da itama ita take kallo. 

     “Ni Asabe mi nake gani haka kamar hajja lanti? Idan mahwalki nake karku tadani dan ALLAH jama'a”.

     Cikin dariyar yaƙe hajja lanti tace, “Ba mahwalki kike ba Asabe. Ni ce dai aminiyarki a zahirance walle”.

    Jikin Inna na ɓari ta kwanto jaririyar Karima dake goye a bayanta ta mikama Sa'a data fito daga ɗaki dan yau anan ta kwana. “Ku shiga ciki, Sa'a kizo ki haɗa murhu asama ƴar uwarki ruwan wanka”.

    Cikin ɗokin ganin baby Sa'a ta amsa tana ƙwalama Tinene dake barci a ɗaki ko sallar asuba batayiba kira dan tazo taga Baby. Karima kuwa ko gaida hajja lanti bataiba ta shige ɗakin Inna dan burinta kawai ta kwanta ta hutama ranta.


          “Hajja lanti dama rai kanga rai?”. Inna ta faɗa tana zama a kusa da ita cike da jimami.

     A raunane Hajja lanti tace, “Ba lafiya bace ta ɓoyeni ai Asabe, bayan ALLAH ma ya ƙaddara da sauran shan ruwana a duniya da ba wannan zancen mukeba anan”.

     “Munga boni, mikuma ya hwaru hajja lanti? Dan ko baki hiɗi ba duk wanda ya dubeki yasan akwai damuwa, duk ƙibarkin nan ta zube kinyi baƙi”.

      Hannu Hajja lanti tasa ta sharce hawayen da suka cika mata ido. “Asabe ai tun tahiyar danai da ɗiyar gidan nan abin ƙaddara ina baro garin katsina ashe ƴan doka na biye dani wlhy sukai ram dani aka sake maidani cikin garin katsina. Ashe wata matace dana ɗauka ɗiyanta a carachi tai shune na garesu”.

      “Kai mun ɓitire. Hajja lanti kice kin auna arziƙi ke kau”.

     “Bama ƙaramiba asabe, dan nahi wata biyu a wajen ƴan doka kahin su gaji da zamana wajensu babu mai belina suka mikani gidan yari wai zasu kaini kotu. Zancen da nake miki daga ranar babu wanda ya sake bi ta kaina ina gidan yari duk tsahon zaman nan. Sai shekaran jiya wani bawan ALLAH yaje ya fiddamu mu ɗari biyu”.

     Sosai Inna keta faman tafa hannu tana sallallami da jajantama Hajja lanti dake matsar hawayen tuna azabar datasha a gidan yari. Sai da ta gama ƴan hawayenta sannan ta sake duban Inna. “Asabe yanzu abinda ya kawoni garin nan akan yaran dana ɗiba ne a tahiyar da nayi, dan nasan iyayensu hankalinsu a tashe yake. Nafara zuwa nan wajenki dan naji ko yarinyar gidan nan ta dawo ita kafin naje sauran gidajen suma naji yaya ake ciki? Dan naje can gidan hajiyar da nake kaima yaran a katsina na iske wai ta tahi saudia shekara biyu kenan”.

         Ɗan waige-waige Inna ta fara, ganin su Sa'a har yanzu suna ɗaki tare da Karima dan Tinene ma ta fito tuni ta samesu. Ƙasa-ƙasa ta maida muryarta tace, “Ta dawo tun bayan mako uku da tahiyarku ai”.

    Cikin zumuɗin dajin daɗi Hajja lanti ta ce, “Kai ALLAH na gode maka”.

    Baki Inna ta taɓe tana gyara zama. “To ai baki saniba da ɗan ƙunshi ta dawo mana, nikuma a sanadinsa na kaɗa kanta tabi duniya yanzu haka ance tana birnin ikko ta kama ɗaki”.

      “Kina nihin ciki tazo dashi Asabe”.

“Ƙwarai da gaske hajja lanti, dan ciki ma ya giyata ya hito duniya ta sani kahin nasata barin garin nan bayan na rihe bakin tambaɗaɗɗiyar gudun karta tona mani asiri dan na hiɗima duniya cewar yawan tazubar dama ta tahi tunda dagani sai ke mukasan yanda akai”.

      “Amma asabe.....”

“Karkice komai hajja Lanti, dan kema kinsan komai akan tsanar ɗiyar nan danai, kinga can wajen” tai nuni da ƙasan turminsu na daka. “Acan na binne tsiyar, kinsan malam kallamu, shine yay mani aikin nan na rihe bakin kowane shege har abada kuma babu maiji, kema na hiɗi maki ne dan nasan abikiyar cin mushe ce. Kema kuma baki rihemani komai na rayuwarki”.

     “Hakane Asabe. Amma ni abinda yaban mamaki ma a ina yarinyarnan ta samu ciki to? Kodai dashi ta tahi daman? Dan inda na kaita bawata harkar banza akeba, inbadai bayan barina ta samu wajen aiki ba acan komai ya hwaru”.

     “Sudai suka sani lanti, ni dai tunda na kaɗata kuma bakin kowa ya rihe miye damuwata. matsalata kawai tahiyar malam adalilin barinta gida, amma inaji a jikina shima ya kusa dawowa gareni”.

    “Ban ganeba yimani karin. bayani”.

Babu musi Inna ta shiga bata labarin komai tana matsar hawaye, dan tana son baba so mai yawa da itama batasan adadi ba a rayuwarta. 


      Sa'a dake laɓe a bayansu tanajin komai ta sharce hawaye da fitowa kamar batajiba ta fara haɗa wutar ɗorama Karima ruwan wanka kamar yanda innar tace. tana ƙoƙarin aza garwar wankan maƙwafta suka fara shigowa ƴan barka da ganin ƙwaƙwaf dan sai yanzu labarin dawowar karima gidan ya fara zuwa kunnuwansu.

      Daga haka hirarta da hajja lanti ta watse. tashi hajja Lantin tai ma ta tafi bayan taje taga baby itama. dan mutane sai kallonta suke tunda ita ba ɓoyayya bace a garin dama tayi dillanci kafin fara ɗaukar yara tana kaiwa aikatau birni.

   Ta tafine ranta makale da zancen Inna akan cikin Zinneerah. Itakam wahalar da taci a rayuwa yasa tayi nadama. Ta nunama Inna tana tare da itane kawai danta samu bakin zaren da zata taimaki Zinneerah. dolene saita koma katsina ta binciko ainahin gaskiyar abinda ya faru da ƴar mutane kozata samu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya. Yanzu hakama zataje sauran ƙauyikan data ɗakko waɗancan yaran ne dan taji sukuma yaya suke ne? Ta kuma nema gafarar iyayensu.


     Firar Inna da Hajja Lanti tasa Sa'a kuka sosai a yinin yau, saboda ƴan barka daketa shigowa yasa taketa ƙoƙarin dannewa har dare ya rufa. Saboda ƙudirin dake ranta yasa yau tai shirin kwana a gidan nasu. Bata kwantaba kuwa har wajen sha ɗaya da ƴan barka suka gama shigowa Tinene ta dawo gidan. Kallonta kawai Sa'a tai ta watsar, dan ko uffan batace mataba akan ina ta fito ko taje. Tunda dama zance nata yawo a gari Tinene na yawon dare, amma ko an faɗama Inna saita karyata tace anama Tinene sharrine dan ba'a ƙaunarta.

    Sai da taga Tinene ta kwanta sannan ta fito kamar zata bayi, ta Window ta leƙa ɗakin Inna taga duk sunyi barci ita da Karima da jaririya.

      Kanta tsaye wajen turmin sissikar hatsinsu da inna ta nunama hajja lanti ta nufa. dana tunda rana ta jiƙa wajen da ruwa dan ƙasar tayi laushi. Aiko an dace, dan tana ture turmin ta fara tona da fatanya a hankaki tana addu'a. Cikin sa'a ALLAH ya bata damar tone ƙasar sosai har takai ga abinda take buƙata. Wata ƙaramar kwanon tasa ta tono, jikinta har rawa yake ta ajiyesa gefe ta maida ƙasar wajen da ruwa ta rufe, ta ɗebo busashen ƙasa ta zuba sannan ta mauda turmin ta ɗauka tasar taje ta ɓoye akan sai da safe zatayi abinda ya dace. Daga haka ta koma ɗaki cike da danuwa da tashin hankali ta kwanta. Barci barawo shine kawai ya sace Sa'a a wannan dare amma bawai dan taji zata iya yinsaba. 

     Kuka tasha sosai na tausayin ƴar uwarta Zinneerah da taji Inna tace wai tana Lagos yanzu tana zaman kanta. Wannan kalma ta tsaya mata a rai, itace kuma take ƙara rura wutar tashin hankalinta akan zancen fiye da komai..........


_________________★


     *_LONDON_*


Halin da Zinneerah take ciki na zazzaɓi ya hana sake tada wata magana a gidan. Duk da kuwa Hajiya Iya da taji komai akan ƙaddarar Zinneerah ita da Baffah dake anan Nigeria zukatansu basu hutaba da saƙawa da kwancewa akan little.

         Hakama AK duk da baisan komai game da Zinneerah ba shi nashi tunanin akan kamanninsa da little ɗin suka tsaya da kuma damuwar Farah. Dan yanason matarsa bai kuma son shigarta tashin hankali. Yaje can gidan domin lallashinta ya kuma fahimtar da ita gaskiyar zancen taƙi yarda su haɗu, saima kulle kanta datai a ɗaki.

     Duk lallaɓata da sukai shi da Mahma danya sanar mata komai itama amma fir Farah daketa kwasar kuka taƙi buɗewa. Sai ma jiyota sukai tanata fashe-fashen abubuwa tana tabbatar masa cewar ta tsanesa. bakuma zata sake zaman aure dashi ba yaje ya zauna da karuwar data haifa masa ɗan ita ta haƙura.

      Duk da kalamanta na masa zafi a rai haka ya dannesu yana cigaba da lallashinta daga inda suke tsaye a bakin ƙofa dan yasan tanada hujjar yin hakan. Sai dai matsalarta data kasa kwantar da hankalinta taji ta bakinsa sam saboda rashin man kanta.

      Duk yanda sukaso ta sauraresu taƙi, hakanne ya bama Mahma haushi tace yay tafiyarsa kawai. Idan ta gadama ta fasa gidan tunda ita batasan lallashi ba. Badan yaso ba ya baro gidan ya dawo gida. Koda ya shigo bai nema kowaba ɗakinsa ya shige kansa na sara masa na azabar ciwon da yake masa.

      Wanka yayo kozaiji sassauci, yana niyyar kwanciya kiran Baffah ya shigo masa. Batare da tunanin komaiba ya ɗaga suka gaisa. “Mike faruwa naji muryarka haka?”. Baffah ya faɗa daga can jin yanda AK ɗin ke magana da ƙyar.

      “Baffah kaina ke ciwo”. Ya bashi amsa murya a raunane. 

    “ALLAH ya ƙara afuwa, sai ka daure kasha magani dan zama da ciwo babu daɗi. dama na kirakane muyi wata magana, amma tunda naji baka da lafiya mayi daga baya kasha magani ka kwanta”.

      “Babu damuwa Baffah muyi maganar kawai, dan sai anjima nakeson shan maganin yanzu lokacin salla ya kusa anan”.

    Ɗan jimm Baffah yayi daga can, dan shima dai maganar cin ransa take yafi buƙatar suyita yanzu ɗin ko zai samu sassauci a ransa. Ya sauke numfashi da cewa, “To shikenan hakanma yayi. Abdul-Mutallab!”. 

   Baffah ya kirayi ainahin sunansa. Hakan yasa AK ƙara nutsuwa gabansa na faɗuwa. Dan ya tabbatar maganar mai girmace tunda har Baffah ya kira sunansa na ainahi. Cikin sake bayyanar nutsuwarsa ya amsa masa.

      Baffah ya cigaba da faɗin, “Abdul-Mutallab maganace mai muhimmanci ta sa na kiraka. Kuma inason ka faɗamin gaskiya kamar yanda na sanka, gaskiyar da zaka faɗamince zatasa na fahimceka kuma nai maka uziri”.

     “Insha ALLAH Baffah zaka samu kowace irin gaskiyace daga gareni inhar na sani”.

     “To Alhmdllh. Akwai yaro da ranar Gwaggonka tazo dashi, wanda na tabbatar bazai yuwu ka manta da shi ba, tunda yanzu Inna ke sanarmin matarka ta gama rikici akansa saboda ganinsa?”.

     “Eh Baffah ban mantaba”.. Ya amsa masa gabansa na faɗuwa batare da yasan dalili ba.

      Baffah da shima cikin ƙarfin hali yake maganar ya cigaba da faɗin, “Abdul-Mutallab kafin yau zuciyatace kawai kemin kaikawo akan kamaninka da yaron, amma zuwa yau da naji wanene yaron yasani cikin tashin hankali da damuwar abinda raina ke rayamin. Da farko ɗaukarmu hauwa'u ce ta haifesa, sai dai a yau suka tabbatar min da Zinneerah ce ta haifesa”.

      “Z.. Zi... Zinneerah!?”.

AK ya haɗa sunan Zinneerah da ƙyar zuciyarsa na wani ƙara kamar zata faso ƙirji ta fito dan kaɗuwar jin zancen............✍


No comments

Powered by Blogger.