Makauniyar Kaddara 31

 


Page 31*


..............Farah na kammala bin dokar AK na komawa ɗakinta shiri tai ta fita zuwa gidan Mammah, a garin suke amma ba'a street

ɗaya suke ba. Su Hajiya iya basusan bata a gidanba sunata hidimarsu. Sai dai su duba lokacin salla su tashi suyi su koma tebirin hira. Sai da Khalipha ya dawo shima ya zauna suka ɗora cike da farin ciki.

       Sunata zuba idon ganin dawowar AK gidan amma shiru, dan har lokacin dawowarsa aiki ya wuce babu shi. itama kuma Farah ɗin dawowar Khalipha gidan ya fahimtar dasu ta fita. Dan mai aikinta ta gama duk wani aikinta na wannan ranar ta tafi itama. Sai ya kasance sai su kaɗai ne a gidan kawai. Gajiya ta saka su Zinneerah kwantawa da wuri suka bar Yah Khalipha da Hajiya iya zaman jiran shigowarsa amma shiru.

     Hankalin Khalipha ne ya fara tashi, duk da yasan bawai wani abune ya samu yayan nasu ba, bazai wuce dai ɓacin rai ya hanashi shigowa gidan ba. Miƙewa yay ya fita domin zuwa can ma'aikatar tasu ya dubashi ko yanacan idan bai tafi gidan Mammah ba, tunda yaga gimbiyar gidan da alama itama tana can. Zuwanta canɗin kuma bawai zai haifar da ɗa mai ido ba ga Yayansu, dan sai ta masa haɗin da sai Mammah ta ɓata masa rai musamman daya kasance itama akan abinda bata farin ciki da shine tunda itama Farah ɗin ai karatunta take bi. Tun farko an nuna mata su ɗin basu da muhimmanci da mutunci shiyyasa take kallonsu a hakan


       Kusan a lokaci guda AK da Khalipha suka ɗora hannyensu akan handles ɗin ƙofar, shi da nufi fita, shi kuma da nufi shingowa. Sai dai AK dake ƙoƙarin shigowar ya samu nasarar turo ƙofar. Baya Khalipha yaja yana sauke ajiyar zuciya. Hakan yasa Yayan nasu binsa da kallon mamaki.

      “Lafiya kuwa? Ina zakaje?”. Yay maganar yana kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa da duban Khalipha ɗin.

     Cikin damuwar ganin yanayinsa Khalipha yace, “Yayanmu dama kai zanbi hankalin Granny duk ya tashi da rashin dawowarka akan lokaci.

      Duk da damuwar dake tattare da fuskarsa da zuciyarsa sai ya saki guntun murmushi kawai yana miƙama Khalipha ɗin kayan hannunsa. Shi kuma ya hau zame coat ɗin saman sult ɗinya yay hanging ɗinta. Takalman ma ya zame ya ajiyesu a ma'ajiyarsu ya saka Slippers ɗin shiga cikin gidan. Batare da yanzuma yay maganaba ya nunama Khalipha hanya alamar suje.

       Tunda suka shigo falon idon Hajiya iya na a kansa. Shima inda take ya nufa kai tsaye, batare da yayi maganaba ya zauna kusa da ita yana sauke numfashin gajiya da lumshe idanunsa. Hannunsa hajiya iya ta kamo cikin nata tausayinsa da ƙaunarsa na ratsata. Batare da ta damu da sanin matsalarsaba ta fara magana cikin lallashi.

        “Bansan yaushe ka fara zama mai rauni hakaba Moddibo? Dan nidai moddibo dana sani ada mai yawan haƙurine da juriya da kawaici akan al'amuran rayuwa. Sannan ba komai yakema zafi ba sai yayi nazari akansa”.

       Lumsassun idanunsa dake cike da gajiya dason yin barci ya buɗe yana ɗagowa zaune sosai, ɗayan hannunsa ya ɗora kan nata yana dubanta cike da sonta da ƙaunarta. cikin muryarnan tasa mai tarin kamala da rashin sakewa yace, “Har yanzu Moddibonki na a yanda kika sanshi Granny. Abinda kike tunanin ba shine damuwarsa ba”.

       “Miye damuwarka idan ba matsalar matarkaba to Moddibo?”.

       “Haba Granny, ni yanzu har akwai wata matsala ta Farah da zata sakani a matsala? Wlhy sam ba itace tushen damuwataba. Ɗazunma ta taka sahun ɓarawone kawai shiyyasa kika ganni kamar a cikin zafi. Wani ɗan matsalane akan business insha ALLAH kuma komai zai dai-daita ki tayani addu'a”.

      Sosai Hajiya iya ta gamsu da maganarsa. Dan tasan shi mutumn kai tsaye da bai iya ɓoye-ɓoye ba ko ƙarya akan abinda ba haka yakeba. Tunda yace ba Farah bace matsalar da gaske ba itaɗin baceba. Ajiyar zuciya ta sauke tana sake kammo hannun nasa cikin nata. Da kulawa tace, “Muna muku addu'a a koda yaushe Moddibo, kuma zamu ƙara insha ALLAH. Duk wanda ya manta da ALLAH shike ambato yaya zaiyi”.

        Murmushi yayi dake bayyanar da gajiyarsa mai sanyi, ya jinjinama Hajiya iya kai yana duban Khalipha dake murmushi shima, “Hakane Granny, shiyyasa a koda yaushe nakeson kasancewa a tare dake. ALLAH ya ƙara miki lafiya da tsahon rai mai amfani”.

        “Amin ya rabbi”. Ta faɗa tana murmushin itama da shafa kwantaccen sajensa.

      Mikewa yay yana faɗin, “A gajiye nake Granny, bara naɗanje na kwanta ina baƙin naki ne?”.

       Khalipha ne ya bashi amsa da cewar, “Tab Yayanmu ai duk sunyi barci. dan Beauty ma da tafi kowa ragantaka tariga kowa kwanciya”.

       Kallon Khalipha yay gira a ɗage kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Gaba yay a binsa murya a cinkushe yace, “Sai da safenku nidai nayi ciki”.

      Da ALLAH ya tashemu lafiya suka amsa Hajiya iya na nufar ɗaki, shima Khalipha sai ya miƙe ya nufi nasa ɗakin bayan ya kashe komai na falon.*WASHE GARI*


       Hajiya iya ce ta tashi su Bahijja da ƙyar domin yin sallar asuba. Dan har yanzu akwai tarin gajiya tattare dasu. Suna idar da sallar ma tsaresu tai sukai zaman yin azkar. Kowa yana tura baki gaba yayi sannan suka koma suka sake kwanciya. Bata hanasuba dan tasan akwai su dason barci dama.

       Barcinsu suka sake kwasa sosai, dan basu farkaba sai kusan tara shima hajiya iya ce ta tadasu. Bayan duk sunyi wankan haɗuwa sukai suka gyara ɗakin sannan suka fito falo inda hajiya iya take. Fitowarsu dai-dai da shigowar mai aikin Farah. Cikin girmamawa ta gaida Hajiya Iya. suma su Zinneerah ta dubesu tana musu sannu da zuwa dan jiya tsoron uwar ɗakinta ya hanata musu. 

     


   ★★


         A ɓangaren Farah kuwa. Koda ta fita gidan a jiya kai tsaye gidan Mammah ta tafi, sai dai tayi rashin sa'ar iske Mammah ta wuce ƙasar China jiya akan harkokin business ɗinta. Hakan baisa ta damuba ta shige tsohon ɗakinsu da Adilah tai kwanciyarta. Dan ita tana ƙasar U.S yin wani course na shekara ɗaya da rabi. 

      Mama Zaliha da suke kira da Mahma ce kaɗai a gidan, itama Yayace gasu Mammah anan gidan take zaune tun bayan rasuwar mijinta acan Morocco. Takaicin halin Farah yasa taƙi tambayarta miya kawota gidan har sai safiyar yau. Bayan ta idar da sallar asuba ta sami Farah a ɗakin nasu itama ta idar da sallan tana karatun Al-Qur'ani. Zama tai a bakin gado tana kallon ɗiyar ƙanwar tasu da gata ya maidata kamar wata shashasha. Tabbas ta yarda da maganar hausawa da sukance gata mugun ciwo. Dan kuwa shine yayma Farah katutu har bata banbance fari da baƙi a cikin al'amuranta.

         Sai da Farah takai aya sannan ta rufe Al-Qur'anin tana duban Mahma. Cike da girmamawa da shagwaɓanta ta gaidata kamar yanda ta saba. Mahma dake dubanta da kulawa itama tace, “Miya faru kikazo nan kika kwana auta?”.

      Baki Farah ta tura gaba idanunta na cika da ƙwalla. Kanta tsaye cike da gadaranta tace, “Mahma na baro masa gidanne su zauna shi da dangin nasa”.

      “Kimin magana a warware zanfi fahimta fiye da bani ita a dunƙule. Ko kina nufin har yanzu matsalar zuwan Kakar tasane bai kareba kuma?”.

       “Ni bashi bane Mahma, ai nace dai na haƙura wannan, amma yanzu dan tsabar wulaƙanci shine ya ƙara kwaso min ƙannensa da wata yarinya da bansanma miye alaƙarsuba aka kawo batare da ya sanar min zuwansuba”.

      “Humm” Mahma ta faɗa tana murmushi da girgiza kanta. Sai da ta gama yima Farah kallon nazari na kusan sakkani arba'in kafin ta gyara zamanta da ƙyau. “Farah anya kuwa kinsan mikikeyi? Gaki dai mace mai tarin ilimin addini dana boko, wayayya wadda ALLAH yayma baiwa kala-kala da ni'imomi, sai dai kuma shashasha ce. Wai sai yaushe zaki daina biyema Hindatu da Zakiyya ne? Farah kinsan ko muhimmancin nuna darajar dangin miji da mutuntasu ga miji kuwa? Kodan kina ganin kullum Hindatu na aibanta dangin Abdul-Mutallab shiyyasa kike ganinsu kamar marasa daraja a idanunki? Bara na faɗa miki gaskiya idan zaki ɗauka. Hindatu mahaifiyarsa ce, zai iya jurewa ya shanye yakumayi haƙuri akan duk wani tarkace da zata jingina danginsa da shi koda yanajin zafin hakan. Keko matarsace duk da kina ganinku jini ɗaya da kuma fawar da kike samu ga mahaifiyarsa zai iya ajiyeku akansu wlhy. Shin bazaki godema ALLAH da ni'inar da yay miki na samun miji irin Abdul-Mutallab mai kawaici da haƙuri ba. Dan wlhy na tabbatar badan soyayyar da yake miki ko tirsasawar hindatu a garesaba yake ƙyaleki. Haƙurinsa da sanin ya kamatansane kawai ke rinjayarsa wajen baki uziri kafin ki kaisa bangon da bazai iya jurewaba. Idan kuma kikai wasa zakiyi nadama a lokacin da guri ya ƙure miki ki kuma rasa samu damar gyara komai. Saboda zuwan wannan yaran kawai ya isa nuna miki gudin halinki yasa ya guji ya faɗa miki ki sanarma mahaifiyarsa ta hanashi, kinga kuwa sai ki dawo hankalinki da irin masu halinki dan mata da yawa sunada wannan bazan halin shiyyasa da yawa duk son da mazansu ke musu sai kiga yana raguwa harsu fara tunanin ƙaro musu abokiyar zama koda kuwa babu haka a tsarinsu. Ni nasan babu wani ilimin zama da miji da baki dashi Farah. Dan kuwa idan da dama ma sai dai ki koyar da wasu. Amma tun zuwan ƙaninsa gidanku kin watsar da komai na ingatacciyar rayuwar aurenku. Kin maida hankalinki wajen kawo ƙararsa kullum da kushe danginsa da nuna ƙyamatar su kusancesa. Anya baƙya tunanin cewa akwai matsala? Baƙya tunanin hankalinsa zai iya fara karkata bisaga ƙudirin dangin nasa nason ƙara aurensa. Yanzufa cikine dake, amma ki duba ko'a jikinsa. Yanda ya nuna murnarsa da farin cikinsa akan wancan cikin da kika samu ya zube bai nunaba akan wannan. Banama tunanin ya sanar da kowa a cikin dangin nasa, tunda dama wancan karon hanashi faɗa musu kukayi wai sai dai suji kin haihu. Sai gashi baki haihunba kuma sabida ALLAH ya rubuta cikin ba zaunanne baneba. Wlhy ki dawo hayyacinki, ki dawo da ingattacciyar rayuwar aurenki kamar farko domin cigaba da damƙe zuciyar mijinki. Duk wannan gantali da shirmen naki babu inda zai kaiki sai komawa baya a garesa. Dan kullum sabbin halayyarki dusashe taurarenki yakeyi a wajensa. Ki dinga daurewa wajen danne wannan zafin kishin naki da kika gada kodan tsare martabarki. Wlhy duk yanda kuke zaton kunada kishi na damaku na shanye. Amma tunda nai haƙurin zama da kishiyoyi har biyu a lokacin rayuwar aurena ya kamata kuma ku saduda. Dan rayuwarma nawa takene baki ɗaya. Daga randa UBANGIJI ya bukaci ganinka dole ka amsa kiransa koka shirya kobaka shiryaba. Duk wata dukiyarka da suna da ilimi da mulki da nasaba da koma miye da kake takama dasu bazasu amfanar dakai da komaiba sai ƙyawawan halayenka da ibadarka. Dan haka sai kisan inda ke miki ƙaiƙayi kibar wannan shirman da kika ɗakko mara hanyar ɓillewa ki koma Farah ɗinki dana sani ada mai hankali da sanin yakamata akan rayuwar aurenta. Ki kuma tashi ki shirya ki koma gidan mijinki tunkan ya fahimci kinbar gidan. Ki kuma kama kanki akan zaman dangin nasa. Ki kiyayi yawan kawo kararsa dan kina zubar masa da kimarsa a idanunmu alhalinsa dan kece sheɗaniyar. Dan wlhy idan Hindatu ta dawo naji kin kira wayarta akan wata matsalar danginsa da kaina zan saka Abdul-Mutallab ya ƙara aure......”

      Da sauri Farah ta ɗago ta duba Mahma idanunta na kawo hawaye. Mahma tace, “Kalleni da ƙyau da gaske nakeyi, dan ko ita Hindatun sai dai tazama ƴar kallo bareke da kike matsayin ƴa. Idan zakije ki kama kanki kije ki kamasa kafin na saitaki a layin daya dace da ke tunda ke shashash ce. shin gata haukane ma kenan?”.

         Cikin kuka Farah tace, “To amma Mahma shima idan yazo kimasa faɗa ya daina min ihu banaso. Sannan ya daina nunamin kamar danginsa sun fini a wajensa tunda nima dai ƴar uwarsace kuma jininsa mafi kusanci”.

       “Naji zan masa. Amma sai naga gyara daga gareki sannan.”

       “Insha ALLAH zan gyara, kuma zanyi duk yanda kikace”. A karan farko Mahma tai murmushi da kamo hanunta jikinta. Tace, “Yauwa kokefa ƴar albarka. Amma duk kin wani susuata kanki tamkar wata shashasha wadda batasan ciwon kantaba da mutuncinta. Karki sake kiyi saken da Abdul-Mutallab zai kufcemiki dan zaki dawwama a dana sani har ƙarshen rayuwarki kuwa”.

     Kanta ta jinjinama Mahma cike dajin daɗin nasiharta tana kwantar da kanta a bisa cinyarta. Sake kwantar da murya Mahma tayi ta lallasheta sosai da ƙara mata shawarwari sannan ta sakata tai wanka ta shirya, ko breakfast batai zamanyiba ta kamo hanyar dawowa gida zuciyarta fal tsare-tsaren dawowa da martabar aurenta daga yau kamar yanda take ada kafin zuwan Khalipha daya susutata saboda rashin son ganin dangin AK raɓe dashi bisa huɗubar Mammah............✍

        

No comments

Powered by Blogger.